OGA HABIB Bacewa da Samuwa by Faddy baby

Author :  Faddy baby Category :  Romance

Chapter   3 / 41

6K to 9K   out of 121.2K words

Habib sosai ta nuna ma Habib in dai bai dawo da su bilya ba ranshi zai b'ace. Tana kaiwa nan ta kashe wayarta.
Habib ranshi b'ace ya kira bilya awaya, kira d'aya bilya ya d'aga, yana d'agawa Habib ya ce, "Bilya kazo Office d'ina yanzu".
Habib mai da kallan shi ya yi ga, Hassana da ke gefa tsaye arakub'e.
Doguwar rigar da Likitarnan ta bata ce har yanzu ajikinta, sai wani haif hijab da tasa.
Habib d'auke kai ya yi daga kallanta, sannan bazato ba tsammani Hassana ta ji ya ce, "Ke 'yar wata jaha ce?,kuma me yarabo da ke daga gidan ku? ".
Hassana kallan Habib ta yi taga ba'ita ya ke kallo ba hankalinsama akan laptop d'in gabansa ya ke, ba akanta ba. Hassana muryarta na cracking ta ce, "Ni yar kano ce, mamana da babana duk 'yan jahar kano ne, Babana nada mata biyu. matar Babana tana da fad'a sosai, kuma macece mai son kanta da yawa. Babana tunda ya auri mamana Allah bai bata haihuwa ba, hakan yasa kakata wato Mahaifiyar Babana ta matsama Babana ya k'ara aure. Babana ya auri Umma Rabi ba dad'ewa Allah ya bata ciki ta haifi Aunty jamila, sai da Umma Rabi ta haihu uku sannan Allah ya ba Mamana cikina, tom kuma itama Umma Rabi lokacin tana da ciki, kusan tare sukayi rainon ciki ita da Mamana. Mamana ta haihu da kwana biyu Umma Rabi ma ta haifo yarinyarta mace. Hakan yasa Babana ya ce, sai dai ahad'a sunan mu.
Tom Mamana dama tunda ta haifeni bata da isassar lafiya, hakan yasa kwanana biyar aduniya Allah ya yi ma Mamana rasuwa. Babana sosai hankalinsa ya tashi da mutuwar Mamana saboda yafi jin dad'in zama da ita fiye da Umma Rabi. Tom mamana da ma ita ma ita kad'aice awajan Iyayanta kuma Allah ya yi masu rasuwa dad'ewa, hakan yasa Babana badan ya soba sai dan bashi da yarda zai yi ya d'auke ni ya ba Umma Rabi ni, ya ce ta had'amu ta shayar damu tare da 'yarta.
Da da farko Umma Rabi ta Nuna ma Babana baza amsheni ba, amma sai Babana ya nuna mata dole ta amsheni, in da bai san Wanda zai kai ma niba. Hakan yasa dole Umma Rabi ta amsheni. Ranar suna Babana ya sa mana Hassana da Usaina ni da yarinyar Umma Rabi. Nasha wahala sosai awajan Umma Rabi dan ko kuka nake sai taga dama ta ke ban nono insha. Kuma koda zan riga Usaina tashi in dai Usaina ta tashi tom Umma Rabi sai ta d'auki Usaina ta lallasheta ta yi shuru sannan koda zata kulani.
Ahaka har muka girma. Tunda nafara wayau na fahimci Umma Rabi tafi son Usaina akaina. Babana dawuri ya samu Islamiya, ita Usaina bata cika zuwa ba saini, saboda ni kona ce ba zani ba dole za'a turani. Tun ina 'yar k'arama ta na iya duk wani aikin gida, dan hatta wankinmu Nida Usaina ni ke mana, acewar Umma Rabi ni ce babba.
Babana duk lokacin da zaizo gida ya iske ina aiki sai yi ta fad'a ya ce Usaina tazo muyi tare. Wannan abinda da Babana ke yi shiya k'ara jawo min tsana sosai gurin Umma Rabi.
Ahaka rayuwa taita tafiya har muka girma , muka shiga secondary school. Tom da akwai wani teacher mu, wanda ya ke kula da duk abinda ya shafemu Nida Usaina, sai dai yana yawan yi min complain, akan wai Usaina ta fi ni tsafta, ni dai ban tab'a fad'amai wani abuba game da gidanmu, shine ya tsinto labari acikin gari. Tunda teacher Kabir ya tsinci labarin halinda nake, ya zamana yake yawan yimin kyautar kud'i. Sosai teacher Kabir ke min hidima hakan yasa har Babana ya sanshi.
Muna gama j. S. E. Babana ya ce, bazamu cigaba da karatuba aure zai mana. Tom dama ita Usaina akwai wini dake zuwa gunta harma ya yi ma Babana magana, ni kuma dama teacher Kabir shike Sona shima ya naimi izini gurin Mahaifina ya kuma bashi. Lokacin da Babana ya je ma da teacher Kabir maganar ya turo manyasa gidanmu ai maganar aurena da teacher Kabir . Teacher Kabir rok'on Babana ya yi akan dan Allah ya barni in kamma secondary school sannan. Kasan cewar Babana na son tarayyata sosai da teacher Kabir yasa ya yarda da abinda teacher Kabir ya ce. Koda Babana ya kaima Umma Rabi maganar saina kamma secondary school sannan za ai aurena, cewa ta yi itama Usaina abarsa sai ta kammala sai ayi duka tare. Aiko haka akayi. Muna S. S. S 3 first term, Babana ya sa ranar aure na da Teacher Kabir. Ita kuma Usaina da wani Jamilu d'an layinmu. Umma Rabi bata son tarayyar Jamilu da Usaina ko ka d'an bakamarma da taga teacher Kabir na min hidimaba sosai, ita kuma Usaina babu abinda ke shiga tsakaninta da Jamilu na kyauta. Da akwai wata rana teacher Kabir ya kawo min waya. Wannan kyautar da ya yi min tab'ata ma Umma Rabi rai sosai,hakan yasa tace sai dai in maida mai wai in ya auran ya sai min agidansa. Babana koda yazo yaji abinda Umma Rabi ta ce hanawa ya yi in maida ma teacher Kabir wayar shi". Hassana shiru ta yi, tana goge hawayanta saboda wani kuka da ke son k'wace mata, saboda tunowar rabuwarta da teacher Kabir ta k'arshe da ta yi.
Hassana cikin murya mai kama da ta kuka taci gaba da magana kamar haka, "Ranar da bazan mantataba arayuwata, ita ce ranar wata laraba, Iyayan teacher Kabir suka zo gidan mu wai d'ansu Kabir ya janye maganar auran shi dani ya mai da ta kan Usaina. Bani ba har Babana ya girgiza da jin haka, mamaki da al'ajabi suka cika shi, saboda shi kanshi asanin kanshi Kabir bama sa wani jutuwa da Usaina, sai yau rana tsaka wai ace Kabir ya janye maganar auran shi da Hassana ya maida kan Usaina. Babana cema Iyayan teacher Kabir ya yi tom su bari zaiji daga bakin Kabir d'in sannan. Aiko haka akayi Babana kiran teacher Kabir ya yi ya tambayai ya akan maganar da Iyayanshi suka zo da ita".
Bud'ar bakin teacher Kabir sai cewa ya yi, "Eh hakane shi Usaina ya ke so".
Wannan maganar sosai ta d'aga hankalin Babana. Washe gari da safe Babana ranshi b'ace ya je d'akin Umma Rabi. Babana nazuwa ya kalli Umma Rabi, ya ce, "Rabi ina son kisan wani abu duk k'ula-k'ular da kika yi, ki ka maida auran Hassana ya koma kan 'yarki tom tun wurima ki warware shi, dan ni bazan tab'a aura auran Usaina da Kabir ba, garama kisani tun wuri.
Haka Babana ya gama fad'anshi Baba Rabi bata tanka mai ba.
Abu kamar wasa yazo ya zamana gaske, dan teacher Kabir idan yazo gidanmu sai inga Usaina taje suna hira, ni ko ko gaisuwata baya amsawa. Abin ya daman Sosai, hakan yasa na kaima Babana k'arar teacher Kabir. Babana kallona ya yi cikin alamun tausaya min, dan ya lura ina son teacher Kabir sosai. Hakan yasa Babana cikin lallashi, ya ce, "Hassana kinsan dai wani baya aurar matar wani ko?, haka kuma wata bata auran mijin wani, inji hausawa sunce matar mutum kabarinsa. Tom Hassana dan Allah karki tambayan dalili dan nima ban sani ba, amma ina so ki hak'ura da Kabir ".
Wannan magana da Babana ya fad'a ji nai kamar ya lumamin wuk'a azuciya, dan Allah ya sani ina son teacher Kabir sosai, kodan shine saurayina na farko.
Kuka na fashema Babana da shi jin abinda ya ce.
Babana duk wata magana mai dad'i da zai fad'amin wadda zata sa in yi shiru ya fad'amin, amma ina na kasa. Sosai kukana ya d'agama Babana hankali. Ni ko kafin kace me sai ciwan kai tsabar kukan da nayi haka kaina ya yi ta min ciwo. Aranar dai da ciwan kai na kwana.
Iyayan Kabir ko sun yi ake kamar me akan Babana ya maida auran Hassana da Kabir kan Usaina ya k'i.
Umma Rabi ko ganin Babana yak'i amsar maganar Usaina da Kabir, yasa taturasu wajan k'aninta. Tom da ya ke shima k'anin nata gashi ga irin shi. Hakan yasa batare da binciken komai ba, ya amshi maganar, nan dai ya yi jagoranci aka tsaida ranar auran Usaina da Kabir, wata biyu masu zuwa.
Wannan ranar nayi kuka kamar raina zai fita. Wannan kukan da nayi sosai ya tadama Babana hankali. Kafin kace me hawan jinin Babana ya tashi. Washe gari da safe shiri-shiru Babana be ne meniba. Hakan yasa na lallab'a na tashi dan kaina sosai ya ke min ciwo. Ina tashi d'akin Babana natura nashiga. Ganin Babana kwance kuma harna tura d'akin bai tashi ba, yasa na k'arasa gun shi ad'an tsorace. kiran sunan Babana nayi ina bubbuga k'afarshi amma shiru. Kuka na fasha dan duk da ban san Mutuwa ba jikina ya bani kamar babu rai ajikinsa. Babana ya tafi yabarni yatafi in da bazan sake ganinsa ba. Haka akai zana'izar Babana.
Nayi kuka sosai dan Babana shine abokin shawara, shine abokin firata idan yana gida, shine wanda abu in yasaman nake fad'amawa sai ko teacher Kabir, tom shima anrabani da shi.
Bayan wata d'aya da rasuwar Babama, abubuwa sun cakud'e min, ga aiki na gidan duk ni ke yi, wanke-wanke, shara, girki, wankin kayan mu.
Ana gobe d'aurin auran teacher Kabir da Usaina na gudu saboda zuciyata bazata iya jure ganin auran teacher Kabir da wata ba, ba ni ba............




idan dai kin karanta daure ki yi Comment 'yar'u.



More comment more typing 🖊
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Abokai na gaskiya suna da wuyar samu, suna da wuyar bari, suna da wuyar mantawa. Allah ka had'amu da abokai na gaskiya.


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

My Facebook group Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/


Shafi na 8&9.




Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, Oga Habib, wannan shine dalilin da ya sa, nahad'a kayana dadaddare na gudu, batare da kowa na gidanmu ya sani ba. Koda na fita gida lokacin duhu ya yi sosai. Tafiya nake amma ban san ina zani ba, ga duhun dare ya farayi, gashi tsakaninmu da titi akwai nisa sosai, haka na kama hanya ina tafiya ina sauri ga damuwa da tayi min yawa, ga yunwa rabona da abinci harna manta, sai dai in naji yunwa ta daman in dama kunu insha. Damuwa da yunwa da gajiyar da na yi ce, tasa na yanke jiki na fad'i ban sani ba, shine kuka tsinceni ainda kuka gani". Hassana kallan Habib ta yi, ganin har yanzu bai fasa typing d'in da ya ke yi ba. Ita fa gani ta ke kamarma duk surutannan tana yin shine kawai amma bajinta ya ke ba. Hassana kallan Habib ta kuma yi, cikin fargaba ta ce, "Oga Habib Wannan shine da lilin barina gidanmu". Hassana ta yi maganar da dad'ewa , dan hattacire ran Habib zai bata amsa ma.Sannan zuwa can ya d'ago kai yana kallanta, sai da Habib ya gama yima Hassana kallan cin mutunci sannan ya ce, "ya sunan ki ma kika ce? ". Hassana bakinta harrawa ya ke wajan ba Oga Habib amsa da cewa, "Hassana".
Habib Kallanta ya yi, ya ce, "Hassana ke ba abin tausai ba ce, idan ke abin tausai cema tom ni ban tausaya miki ba, kuma ni bazan tai makeki ba. Duk wadda ta gudu daga gidan Iyayanta tom yawan bariki ta fito, dan haka fitar min daga office ". Habib ya fad'i maganar cikin d'aga murya. Jikin Hassana rawa ya farayi dan sosai ta tsorata da Habib.
Hassana kuka ta farayi, cikin muryar kuka ta ce, "Oga Habib dan Allah ka yi hak'uri, Wallahi bayawan bariki na fito yi ba, kona zauna gidan b........ ". Tsawar da Habib ya yi ma Hassana ce tasa ta yi shiru.
Habib nuna mata hanyar fita ya yi da hannu, ya ce, "fitar min daga Office na ce, stupid kawai! ".
Hassana da saurin ta har tana d'an tintib'e ta fita daga office d'in. Saura kad'an Hassana su yi karo da Bilya shi kuma lokacin yazo shigowa.
Bilya da d'an damuwa ya bita da kallo dan duk da bai san labarin yarinyar ba, sosai ta ke bashi tausai, acewar shi yarinya k'arama haka ace bata san ina zata ba. Bilya cikin tausan Hassana ya k'arasa office d'in Oga Habib.Bilya cikin girmawa, ya ce, "Barka da hutawa Oga Habib, ka yi hak'uri dan Allah ka kirani banzo da wuri ba, bana kusa ne".
Habib kallan Bilya ya yi, sannan ya ce,fuskar shi a d'aure, alamun ranshi ab'ace ya ke. "Bilya me yasa ka kai k'arata wajan Momyna". Habib ya yi maganar cikin d'aga murya, dan shi aganinshi bai kamata ace yaron shiba, wanda ya ke ci ak'ark'ashin shi ya zartar da hukunci akanshi ace ya kai k'ararsa wajan mahaifiyarsa ba.
Bilya cikin kame-kame ya ce, "Oga Habib ba...... ". Habib d'agama Bilya hannu ya yi, ya ce, "ka adana kala manka, amma kabar kama k'afa da son da Mahaifita kema, dan kar hakan yasa kaji zaka iya yin koma, wannan shine last worning da zanma, duk sanda ka sake ma hajiya complain akaina, daga ranar Bilya kabar aike a k'ark'ashin Sanat yoghurt". Habib na fad'in haka ya kalli Bilya, ya ce, " Bilya da kai da Baba Lami na baku, suspension na one month". Bilya da alamun tsoro ya d'ago kai yana kallan Habib, jin wai ya da katar da shi har wata d'aya.Bilya magana zai yi Habib ya nuna mai hanyar fita.
Fita Bilya ya yi, batare da yace ko mai ba. Bilya na fita ya iske Hassana can bakin get d'in wajan tsaye, ta yi shiru ita kad'ai. Bilya gurinta ya k'arasa, kallanta ya yi sannan ya ce, "korarki ya yi ko? ". Hassana kai ta d'agama Bilya.
Bilya shiru ya yi sannan, ya ce, " Ni Wallahi duk namarasa abinda zance miki, ni kaina yanzu haka ya dakatar dani aiki harna tsawan wata d'aya, ga aurena saura wata biyu masu zuwa, ni kaina yanzu kinga in da munyi haka dashi ba damar in kwana gidansu sai dai in koma d'akin abokina da kwana. Tom kuma itama Baba Lami bata san kowa ba a Abuja, kuma kinga ya dakatar da ita aiki itama, yanzu na san sai dai ta koma garinsu. Bilya shiru ya yi, yana tunanin yadda zai yi da Hassana amma bai sani ba,hakan yasa, ya ce, "Hassana ni yanzu ma kaduna zan tafi, ki zauna nan anjima kad'an zaki ga manager ya fito, zaki ganshi da red d'in shirt da black jeans. Ki mai magana, in dai ya amince ya d'auke ki aiki shikenan, Oga Habib babu ruwansa da d'aukar ma aikata".
Hassana kallan Bilya ta yi, ta ce, "Tom Oga Bilya, wajan kwana fa?, in ya d'aukeni aikin? ".
Shiru Bilya ya yi dan shi yama manta da wajan kwana sai yanzu ya tuna. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce, "Hassana ki ci gaba da zama nan, idan kika ga Oga Habib ya fito, ki je ki sa ke rok'anshi, k'ila ya amince". Bilya na kaiwa nan, ya yi ma Hassana fatan alkairi ya tafi.
Hassana cigaba da zama ta yi kamar yadda Bilya ya ce mata, tana jiran fitowar Oga Habib. Hassana har 8:00pm tana gun zaune, tana jiran taga fitowar Oga Habib amma shiru, Hassana tunini ta rik'ayi k'ilama ya tafi bata sani ba, inda ta je sallah. Wata zuciyar ta ce mata, tom idan ko haka ne ina zata kwana,uhm tom wai in ma naganshi lallene ya taimakan d'in. Hassana na cikin wannan tunanin taga motar Oga Habib ta fito. Hassana da saurinta har tana tuntub'e ta matsa wajan motar Habib d'in, shikuma lokacin ya tsaya yana ma mai gadin gun magana.
Hassana ko kafin tak'arasa Habib ya yi ma motar shi key. Hassana tsabar furgici da rashin sanin yadda za tayi, kawai sai ta zauna gun tana kuka.
Hassana na nan zaune tana kuka kamar wata ta b'abb'a, manager gun ya fito domin tafiya gida. Tsayawa ya yi ganin mutum a zaune, kuma bisa ga alama kamar kuka ya ke ji. Tsayawa manager ya yi ya fito daga motarshi, inda Hassana ta ke zaune tana kuka ya k'arasa. Tsananin hasken gun yasa tun kafin ya k'arasa ya k'are mata kallo. Kallanta ya yi da kyau sannan cikin siririyar muryar shi ya ce, "ke lafiya?, zaki zo nan ki zauna da daddarannan? ". Hassana da sauri ta d'ago kanta tana kallan manager. Manager ko jin Hassana ta yi shiru tana kallan shi, ya sa ya k'ara cewa, ", ke bakya ji ne! ? ". Ad'an tsawace ya yi maganar.
Hassana kallan Manager ta yi, cikin muryar kuka ta ce, "Bansan ina zani ba ne". Manager da mamaki ya kalli Hassana, ya ce, "kamar ya baki san ina zaki ba?, tom waya kawoki nan? ".
Hassana kai tsaye batare da tunanin komai ba, ta ce, "Oga Habib ne ya tsinceni shida Oga Bilya, shine ya kawo ni nan, ni kuma bansan kowa ba a Abuja, kuma ya hana in sake zuwa mai gida". Hassana ta idasa maganar cikin kuka.
Manager shiru ya yi yana mai ci gaba da kallan Hassana, dan shi gaba d'aya bai gane takan maganarta ba. Manager waya ya ciro ya kira Oga Habib.
Kira d'aya Habib ya d'aga yana tambayar manager lafiya, dan manager bai cika kiran shi airin wannan lokacin ba.
Manager ko Habib na d'agawa ya ce, "M. D. Dama wata Yarinya ce nan na gani wajan get zaune tana kuka, shine dana tambayeta ta ce min wai kaika kawota, ni dai gata nan bama wai gane kan zancan nata nayi ba".
Habib ba tare da tunani wata yarinya ba ce, dan in yaga dama yanada girki. Habib shiru ya yi

3 / 41