Author : Faddy baby Category : Romance
yan zu nan ina son ka datse igiyar da ke tsakaninka da ita, dama zata dawo ne da ban tsaya jiranka ba, da yan zu mun wace, tom amma ta ce min baza ta dawo ba". Habib da zufa ke keto mai kota ina, bama duka yake gane abinda Hajiya Turai ke ce wa ba".
Hajiya Turai da ke jiran Habib ya ce wani abu, ta ji shiru babu alamun ma Habib zai tanka ma ta, hakan yasa Hajiya Turai ta ce, "Habib kai fa nake sauraro amma ka yi min shiru". "Na'am Mommy me kika ce? ". Habib ya tambayi Hajiya Turai, dan har ga Allah Habib ba duka abinda Hajiya Turai ta ce ya ke fahimta ba, shi dai kamar yaji tana cewa tana jiran shi yanzu".
Hajiya Turai cikin mafisa ta ce, "Habib ka ban takardar Hassana nace yan zu , saboda gobe zata wuce da wuri!" Habib da bai son hayaniya mai k'arfi irin wadda Hajiya Turai ke mai, dafe kan shi ya yi, ya ce, "Mommy please ki yi a hankali, kaina ciwo ya ke"., Habib ya idasa maganar cikin damuwa ".
Hajiya Turai cikin k'ara d'aga murya ta ce, "Idan kana so in yi managa a hankali tom yi abinda na saka ". Habib kallan Hajiya Turai ya yi, ya ce, "Mommy amma fa karki manta tun farko ta kurawar can ce ta sa ta ta gudu, tom yan zu idan ta koma bamu san irin wadda zata fad'a ba, ni a ganina kawai taci gaba da zaman ta nan Please Mommy'na ". Habib ka ga nifa bani nace mata ta tafi ba, ita taji zata tafi, dan haka ina gani kawai mu rabu da ita ta tafi, bana son wata doguwar mana, kawai ka aikata abinda nace ma, babu ruwanka da rayuwar da zata fuskanta, bama gara zamanta cikin dan ginta ba, akan zamanta nan kana sata aiki a Company'nka , hakan ma bai ma ba, har damar mari kaba wasu a gareta, wai matarka Habib zaka sa tana share-share da goge-! ". Habib shiru ya yi, sannan ya kalli Hajiya Turai ya ce, "Mommy ki yi hak'uri haka ba zai k'ara faruwa ba, Sanat kuma tun-tuni naso in hanata zuwa amma sai naga ita alokacin tana son aikin, shi yasa na barta, Mommy dan Allah ki fahimta ". "Habib.. ". Hajiya Turai ta kira sunan shi".
Habib d'agowa ya yi yana kallan Hajiya Turai, da yau ta koma mai wata iri kamar ba Mommy shi ba mai tausan shi. Hajita Turai kallan Habib ta yi, shima ita yake kallo, ta ce, "Habib yau ba zaka bar gidan nan ba, sai ka ban ta kardar Hassan... ".kiran wayar da akai ne ya hana Hajiya Turai idasa abinda ta ke fad'a". Hajiya Turai na duba wa taga Hajiya Murja, wato Mahaifiyar Farida".
Hajiya Turai, d'aga wa ta yi, tana sauraran abinda zata ce. Sai dai kukan da taji Hajiya Murja na yi ne ya ta da ma Hajiya Turai hankali. Hajiya Turai cikin rud'ewa ta ke tambayar Hajiya Murja, ta ce, "Hajiya dan Allah ki min baya ni mana, me ya faru ne? ". Hajiya Murja cikin kuka ta ce, "Hajiya dan girman Allah kuzo yan zu ke da Habib dan Allah Hajiya ". "Ki min ba yani lafiya dai ko? ". Cewar Hajiya Turai ".
Mahaifiyar Farida cikin kuka ta ce, "Hajiya Farida ce ba lafiya, yau kwana biyu kenan tana aman jini, ance ciwan zuciya ne, dan Allah kuzo Hajiya, muna National Hospital ".
Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Tashi muje". Habib da ya ke ya ji wayar Hajiya Turai da Mahaifiyar Farida ya ji duk abin aka ce, hakan yasa ya tashi.
Hajiya Turai ko Hassana ta kira tace tazo su je tare. Hassana da bata san zuwan Habib ba sai da ta fito falon suka had'u, Hassana kau da kanta ta yi gefe".
Habib ne yaja su a motar shi ya kaisu har National Hospital. Suna zuwa suka kira Hajiya Murja awaya, ta fad'a masu number room da suke".
Ba wai Hajiya Turai ka d'ai ba, har Habib da Hassana sai da suka tausaya ma Farida ganin halinda ta ke ciki. Hajiya Murja ko Mahaifiyar Farida, kusa da Farida ta matsa ta ce, "Farida bud'e idonki ga Habib d'in yazo". Farida mik'a hannuta ta yi, cikin murya irin ta masu ciwo ta ce, "Oga Habib kana ina?, dan Allah Oga Habib ka kama hannuna". Habib matsowa ya yi kusa da Farida yana kama d'ayan hannuta da ta ke mik'o mai ya ce, "sannu ko Farida Allah ya baki lafiya ". Farida tashi ta yi ta jingina, ta bud'e idonta da ke zubar da hawaye tana kallan Habib, ta ce, "Oga Habib sonka zai zama ajalina, ban tab'a son kowa ba, kuma ba zan tab'a ba koda rayuwata za tai tsawo. Oga Habib kai ne mutum na farko da naso, kuma kai ne mutum na k'arshe, Oga Habib duk zaman da nayi gidanku nayi shine dan kai, ko zan samu Soyayyarka, kuma dan kai naje SANAT nai aki, duk wani abu da ka gani na sa dan ya yi min kyau dan kai nake sashi, inda kai kuma ko kallo ban isheka ba, hak'ik'a Oga Habib sonka shine ajalina, ina nai man alfarma d'aya a gunka dan Allah, kace kana sona, duk da na san nina rok'eka, amma haka zai min dad'i, zan so kafin in mutu ka furta min kalmar so dan Allahhhhh ". Farida ta idasa maganar tana kuka".
Tabbas Habib yasan Farida na son shi ba tun yau ba, amma bai zaci son ya kai haka ba. Habib kallan Farida ya yi cikin tausaya mata, Saboda tabbas ya san yadda ta ke ji, wani irin zafi ne mai fita da rad'ad'in zuciya, mai karyar da duk wata gaba dake jikin mutum. Habib cikin muryarsa mai d'auke hankalin 'yan mata masu karyaryar zuciya irin su Amina๐๐.
Yace, "Farida ki yi shiru kinji, kin ga likita ya ce kina fama da ciwan zuciya, ki share hawayanki zan aureki.
Ba wai Farida kad'ai ta rud'e ba da jin abinda Habib ya ce, duk wanda ke d'akin ne, dan dai suna da ban-ban cin rud'ewa. Hajiya Murja cikin farin ciki ta kamo hannun Habib ta ce, "Allah ya yi maka albarka Habib, Allah ya faranta maka fiye da yadda ka faranta mana". Habib dai bai ce komai ba, Hajiya Turai ga banta dukan uku-uku kawai ya ke yi, inda a zuciyarta ta ke cewa, Wallahi ba zai yuwu ba.
Hassana ko ai fad'in halin da ta shiga ma jabu ne".
Zuwan likitan da ke duba Farida ne yasa duk suka fiffita. Inda Hajiya Turai tai ma Hajiya Murja sallama tare da fatan Allah ya ba Farida lafiya".
Farida ko tun ranar da suka rabu da manager ta koma gida ranta b'ace, ganin abinda Habib ya ke ma manager dan ya mari Hassana. Cikin dare Farida ta farka da aman jini, ko da zuka je a sibiti aka ce masu ciwan zuciya ne".
Hajiya Turai ko suna cikin mota suna tafiya komawa gida, ta ce, "Habib abinda ka ce ma Farida da gaske ka ke , ko-ko? ". Habib shiru ya yi sai zuwa can ya ce, "Mommy da gaske nake". "Habib idan har ni na haifeka Wallahi ba zaka auri Farida ". Cewar Hajiya Turai. "Mommy nim ba wai ina son ta bane, kawai dai na tau saya ma halinda ta ke ciki ne, kuma kin ga na riga na furta".
Habib na yin parking, fita ya yi, ya yi hanyar side d'in shi, inda Hassana ma tabi bayan shi, Hajiya Turai kuma tana ganin Hassana tai shiru ta rabu da ita,ko zata samu sassauci dan ta lura da irin furgicin da Hassana ta shiga jin wai Habib zai auri Farida".
Habib na shiga side d'in shi Hassana ma tashi ga. Hassana sai da ta d'an numfasa sannan ta samu ta iya managa, duk da maganar a rice ta ke yinta. Hassana ba tare da ta kalli Habib ba ta ce, "Na san Mommy ta sake ma magana , amma naji shiru,na bi yoka ne in fad'ama idan Mommy ka ke ma kara ka ki sakina, tom tafi kowa burin rabuwar mu yan zu, dan haka ko ka ban takarda, ko baka ban ba, insha Allah daga gobe ba zan sake kwana a gidan ku ba".
Habib in da Hassana ta ke tsaye ya k'arasa, dan d'an nesa dashi ta ke, Habib kallan Hassana ya yi ido cikin ido, ya ce, "Na san bake kika yanke wannan hukuncin ba Mommy ce, tom amma kema yan zu me yasa kike son biye mata? ". Hassana da idonta ya rufe bata san me ta ke cewa ba, ta ce, "Ni na yan ke bani na yanke ba, Oga Habib ba bu ruwanka, ni dai kawai ka ban takarda ta, kuma baka k'ara ganina har'aban-abada".
Habib jawo Hassana ya yi, ya ce, "SANAT zo ki ji muyi managa". Hassana fun cike hannunta ta yi ta ce," Oga Habib ni ba wata maganar da za muyi". Habib ya dad'e tsaye yana kallan Hassana sannan ya ce, "Idan na baki ta kardar kina ganin haka ya fi mi ki? ". Hassana tana kuka ta d'aga ma Habib kai. Habib cikin bedroom d'in shi ya shiga, ya dad'e sannan ya fito da wata farar takarda a hannun shi, Habib na zuwa Hassana ta zuk'unna ta ci gaba da kukanta, ganin takardar sakinta a hannun Habib, dan a yadda Habib ya ke nuna mata, duk da bai ta b'a furta mata kalmar so ba, ta sha ba zai iya rabuwa da ita ba".
Hassana
zuk'unnawa ta yi, tana kuka. Habib ta da Hassana ya yi, ya ce, "Sorry Sanat kukan ki ya na torching heart d'ina, dan Allah ki yi shiru, Habib shiru ya yi, sannan ya ci gaba da cewa, "Sanat ke ce ta farko, ke ce ta k'arshe da na so, na kuma so ace na rayu da ke, zuciyata ta sa ba da ke, gangar jikina zata wahala sosai da rashin zaman ta da ke, amma ke da Mommy kin matsa sai mun rabu,shikenan gashi, Habib ya saka ma Hassana ta kardar cikin hannunta....... โ๏ธ
Idan kin karanta daure ki Comment sister ๐ค.
Share
&
Comment please ๐.
๐ Oga Habib ๐
๐ซ๐ซ
*๐
๏ธARUMAI ๐
ฆ๏ธ WRITERS ๐
๏ธSSOCIATION๐๐๏ธ*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐ช*_
*๐ซ(๐
๏ธ.๐
ฆ๏ธ.๐
๏ธ)๐ซ*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
https://www.facebook.com/groups/301023561618950/
Ina ba duk wani mai bibiyar Oga Habib hak'uri na jina shiru da akayi kwana biyu, dan Allah ku yi hak'uri, haka ya faru ne saka makon wani uziri da ya rik'eni.
Albishirin ku masu bibiyar littafin Fadila Sani Bakori.
Yau gani da daddad'an albishir gare ku, insha Allah daga na kammala Oga Habib, zan nisha d'an tar da ku da sabon littafina wanda na baje basirata acikin shi. Anyi amfani da salo na birgewa acikin littafin. Labari ne wanda ya ke d'auke da madarar Soyayya, mai d'auke da ban al'ajabi. Inda ta wani b'angaran labarin ke d'auke da ban tausayi mai tsayawa a zuciyar makaranci. Duk yadda zan sanar daku ba zaku fahimta ba, ke dai karki bari abaki labari.
Zaki samu littafin akan farashi mai sauk'i da rahusa๐๐.
Summary.
Abba tin ina yaro kana yawan fad'a min, duk abinda ya yi tsanani yana tare da sauk'i. Shin ni sai yau she sauk'i na zai zo! ?. Abba me yasa muta ne basa ganina, maganata kawai su ke ji!?.Abba me yasa muke rayuwa a daji mai makon cikin gari cikin mutane !?.
Abba kana gani Husna zata aure ni, duk da halin da nake ci!?.
Abba me yasa Husna ta kasan ce ita kad'ai ke ganina!?. Abba kace kai ba Mahaifinsa bane, tom waye Mahaifina, kuma me yasa muke rayuwa a jeji!?, Sannan me yasa Abdussalam kad'ai ke zuwa gurin mu, sannan Abba waye Abdussalam ?.
Haidar duk banda amso shin tambayoyin ka, nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.
Paid book
Akan farashi mai sauk'i da rahusa ๐๐
Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan Number๐ 08063830828
Shafi na 83&84.
Habib shiru ya yi, sannan ya ci gaba da cewa, "Sanat ke ce ta farko, ke ce ta k'arshe da na so ace na rayu da ke, zuciyata ta sa ba da ke, gangar jikina zata Wahala sosai da rashin zaman ta da ke, amma ke da Mommy kin matsa sai mun rabu, shikenan gashi ". Habib ya saka ma Hassana takardar acikin hannunta".
Hassana najin ta kardar da Habib ya sa mata a hannu kukanta ya k'ara tsananta.Habib cikin damuwa ya kalli Hassana, ya ce, "Sanat dan Allah ki yi shiru mana kada kanki ya yi ciwo".Hassana cikin Muryar kuka ta ce, "Oga Habib sakanni zan wuce". Sabo da Habib na rik'e da Hassana".
Habib cikin kunnan Hassana ya yi mata magana a hankali, ya ce, "zan sake ki amma sai kin dai na kukan, tukun". Hassana cikin alamun k'osawa ta ce, "Oga Habib dan Allah kasa kan! ". "Tom bar kukan sai in sake ki". Cewar Habib ".
Hassana share hawayanta, ta yi, ta ce, "Oga Habib dan Allah ka sakan, zan wuce ne". Habib sakin Hassana ya yi ganin ta damu. Hassana kuma Habib na sakinta ta ruga da gudu zuwa Side d'in Hajiya Turai. Hajiya Turai na zau ne Hassana ta zo ta wuce ta tana kuka, dan Hassana ko kula ma da Hajiya Turai ba tai ba". Hajiya Turai kuma cikin sauri ta tashi ta bi bayan Hassana, ganin yadda Hassana ta shigo tana kuka, dan bisa ga alama ma ko kula da ita ba tai ba. Lokacin da Hajiya Turai ta shiga bedroom d'in Hassana , lokacin Hassana har ta kwanta tana mai ci gaba da kukan ta. Hajiya Turai cikin tashin hankali ta k'arasa gurin Hassana, Hajiya Turai na zuwa ta ya ye bargon da Hassana ta shiga, Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter lafiya?, mai Habib d'in ya yi miki?". Hajiya Turai duk cikin damuwa ta ke tambayar Hassana ".
Hassana tsagaita wa ta yi da kukan, ya share hawayanta ta d'ago tana kallan Hajiya Turai. Hajiya Turai kuma cikin k'osawa ta kuma cewa, "Daughter fad'a min mai Habib d'in ya yi miki? ". Hassana share hawayanta ta yi, ta ce, "Mommy ba komai". "Tom me ya sa ki kuka? ". Hajiya Turai ta tambayi Hassana".
"Mommy ba ko mai". Hajiya Turai da mamaki ta kalli Hassana, sannan ta ce, "Tom inda ba za ki fad'a min ba, bari in kira Habib ya fad'a min". Hajiya Turai waya ta ciro zata kira Habib.Hassana ta kalli Hajiya Turai, ta ce, " Mommy dan Allah karki kira shi".Hajiya Turai ta shi ta yi, ta fita. Dan tabbas ko mai Habib ya yi ma Hassana babba ne. Hajiya Turai side d'in Habib ta nufa ranta b'ace, tana zuwa zaune ta iske Habib kan caution kan shi yana kallan sama. Sallamar Hajiya Turai ce ta tada Habib ya d'ago yana kallanta. Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib me kai ma Hassana?". Habib d'ago kai ya yi yana kallan Hajiya Turai ya ce, "Mommy ban mata komai ba". "Ba kai mata komai ba zata fita tana kuka! ". Cewar Hajiya Turai ". "Mommy Allah ni ban mata ko mai ba, nima nan haka ta shigo min tana kuka,amma ni ban mata ko mai ba".
Hajiya Turai tunanin auran Farida da Habib ya fad'a zai yi ne yasa Hassana kuka, wannan tunanin ne yasa Hajiya Turai ta fita ta koma side d'in ta".
Lokacin da Hajiya Turai ta koma bedroom d'in Hassana har zazzab'i ya rufe Hassana, dan abu biyu suka taru su kai ma Hassana yawa, maganar auran Farida da Habib ya furta, sosai maganar ta firgita ta, sai kuma ga maganar sakin da Habib ya yi mata, dan sosai Hassana ta rud'e da takardar da Habib ya bata, wannan shine abinda ya hargitsa Hassana gaba d'aya".
Hajiya Turai cikin sauri ta k'araso wajan Hassana tana tambayarta lafiya, ganin rawar sanyin da ta ke yi". Hajiya Turai cikin damuwa ta k'arasa wajan Hassana tana tambayarta Lafiya ". Hassana ko tsabar rawar sanyin da ta ke ko magama gagararta ta yi. Hajiya Turai cikin damuwa ta kira Habib, Habib na d'aga wa ta ce, " kazo bedroom d'ina yan zu". Hajiya Turai zama ta yi kusa da Hassana tana mata sannu, Hajiya Turai na nan zau ne Habib ya shigo, yana shigowa da sauri ya k'arasa gurin Hajiya Turai yana kallan Hajiya Turai ya ce, "Mommy lafiya me ke da munta? ". "Kira doctor ya duba ta zazzab'i ne". Habib Family doctor su ya kira awaya"
Yana zuwa ya duba Hassana, sannan ya bata magunguna. Hajiya Turai ce ta ba Hassana maganin,Hassana amsa ta yi, sannan ta kalli Hajiya Turai, ta ce, "Mommy dan Allah zan je gida, ina son ganin 'yan'uwana"., Hassana tai maganar cikin rauni". "Ki yi hak'uri daughter zuwa gobe sai ki tafi".Hajiya Turai na fad'in haka ta fita, ta ce, "Daughter bari in kawo miki abinci ki ci". Bayan Hajiya Turai ta fita ne, Habib ya zauna gefan Hassana yana kallanta, sannan zuwa can ya ce, "Sanat! ". Hassana ban za da Habib ta yi. Habib ya kuma ce wa, "Sanat ki bar tafiyar ni zan kai ki ". Hassana da gaba d'aya haushin Habib ta ke ji, na sakinta da ya yi, banza ta yi da Habib, Habib kuma bai gaji ba ya kuma cewa, "Sanat please ko da Mommy tai miki maganar tafiya gobe ki ce mata ni zan