Author : Zainab Habib Category : Romance
idan har kika yarda to babu ke babu fita a gidansa sbda kina aihuwa kin zamo ahalin gidan "
"Abu na biyu kuma karki sake ki zura jikinki da yawa ki dingayin baya-baya da ƴan gidan sauran kuma ni nasan mai zanyi " Pooja tace "tana cije leɓenta , ta ƙara da cewa "maza share hawayenki karki wani sanya damuwa a ranki itama Mommah nasan ya zamuyi da ita muje "bin bayan Pooja tayi suka koma bedroom ɗin nasu a lokacin Mommah ta shigo nemansu basa nan , tsaye suka ganta tana faɗa suka sunkuyar da kansu Mommah ta riƙe hannun Nisha suka fice , kai tsaye ɗakin Imaam ta kaita yana zaune shi kaɗai , Nisha ta zauna tare da sunkuyar da kanta ƙasa Imaam yace "burin ko wanne iyaye suga sun aurar da ƴarsu idan ta isa aure ,alhmdulilh tunda kin sami mai sonki kuma har an ɗaura aure ina farinciki "ya ɗora hannunsa a kanta yayi mata adu'a tare da nasihoyi masu shiga jiki , Mommah ce ta ƙara da cewa "kuma shi zaman aure ɗan haƙuri ne , tabbas duk da nasan babu abinda zaki nema ki rasa dole wataran zakiji wanu ya ɓata miki rai kiyi haƙuri "duk Nisha najin abinda suke faɗi har Mommah ta riƙe hannunta ta kaita ɗakinta wata yayarta da sauran ƴan uwa suka sanya mata albarka .
Wata fitinanniyar mota ce tayi parking a ƙofar gidansu Nisha tare da yin horn mai ƙarfi ,Ammar ne ya fito yana sanye da wani yadi mai tsadar gaske ya jingina jikin motar sai tashin ƙamshi yake da alamu shine ma zai ɗauki amaryar , kan kace me motoci sun taru dan a ƙallah sunfi goma gashi mutanen gidan ma motoci goma sunyi musu yawa , haka mutane suka dinga fitowa ko wacce tana zaɓar motar da zata shiga har aka tashi tafiya , ana fito da amarya aka sanyata a motar Ammar dole dai da aka bari Pooja ta shiga sanan Nisha ta shiga itama duk da haka kuka take kamar me , hannunta Pooja ta ruƙo tana ɗan mammatsawa tana bata haƙuri har tayi shiru cikin ikon Allah sai gasu a layin , bayan drivers sunyi horn an buɗe musu get suka shiga ko wanne yayi parking aka fara fitowa , kai tsaye part ɗin Ummi aka kaita suna zaune a babban palo Hajiya na ganinta ta hau mata tsiya tana cewa "kamar ba kece na gani jiya ƙirr ba yau gashi harda rufe fuska kinyi min ƙwacen miji "su Ummi da mutanen dake palon suka sanya dariya , bayan an gama gaisawa sai ga Mheera nan ta shiga sanye da pink ɗin sari tayi kyau sosai ta kamo hannun Nisha tace "ƙyale Hajiya ta cika surutu idan kikaci gaba da kulata zata bki haushi "kama baki Hajiya tayi kana tace "wanan yarinya kin rainani fa shine kika ɗauke amaryar ko ?"ko saurararta Mheera batayi ba ta wuce da Nisha part ɗinta da ke can wajen gidan sai ka fito daga na su Ummi sanan ka shiga nata , wow tsaruwarsa ba'a magana dan ya haɗu ta kowanne fanni babu makusa gaskiya yayi kyau , tsayawa yi muku kwatancen sa ma zamu shafe lokuta dan haka ku ƙaddara Nisha ta sami aljannar duniya , kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujeru Mheera ta zaunar da Nisha tare da cewa "kinga part ɗinki nasan bakisan ko ni wacece ba ko ?"gyaɗa kai Nisha tayi tare da cewa "eh "ni sunana Mheera ƙanwar Ammar ce mu biyu Allah ya bawa iyayenmu , ina karatu a singapore amma a wanan shekarar zan kammala da zarar kasancewar munyi hutu "zata ƙara magana taji sallamar ƴan uwan Nisha sun shigo ta miƙe tare da ɗagawa Nisha hannu tace "zan dawo gobe bye "itama Nishan hannu ta ɗaga mata ,aka riƙewa Nisha hannu zuwa bedroom ɗinta aka zaunar da ita kan tsaddun kayan alatu , ƙarfe goma ƴan uwan Nisha sukayi sallama zasu tafi , Pooja dake zaune a mota sai da ta tabbatar ƙarfe goma tayi sannan ta fito ta shigo bedroom ɗin Nisha..
Yau Abba ya koma Egypt shi da Bashir kai tsaye gidan Boka suka wuce suna isa suka tarar da mutane a ciki , dole suka jira har sai da ya sallamesu sanan suka shiga ,zama sukayi Abba da Bashir suka gaida Boka bayan ya amsa Abba yace "nayiwa ɗana aure da zarar matar tasa ta samu ciki ta aihu to nabaku yaran dama kace biyu ko ?"eh Boka yace "amma fa kyan alƙawarii ?"Abba yace "cikawa"Boka ya ɗaga wata ƙwarya ya ɗibo wani magani a wasu kofuna na tangaras ya miƙawa Abba yace "dama na hanaka kusantar matarka to har ila yau na ƙara hanaka har sai nan da wata huɗu sanan "waro ido Abba yayi babu magana ,Boka ya kuma cewa "wanan maganin ka yawaita sanyashi a bakinka sbda magana da jama'a bayan haka ka cika mana alƙawari sauran aikin namune "ku tashi kuje "Bashir ne ya ajiye maƙudan kuɗi masu yawa kana suka wuce .
Koda suka dawo gidan Abba dake Egypt tagumi Abba ya zuba yace "Bashir kana ganin wanan harkar zata yiwu kuwa ? Eh man ko tunanin matarka kake ?"eh man Bashir dole inyi tunaninta yaushe rabona da bata haƙƙinta har ma mance ga kuma wasu sababbin sharuɗan "dariya Bashir yayi kana yace "idan babu damuwa ai sai mu tambayi Boka zaka iya yin harka da ƴan mata ? dariya suka sanya dukkansu Abba yace "tambaya min shi dan ko jiya da naje gida naji muradin matata haƙura nayi itama haka "Bashir ne ya danna number Boka ya tambayeshi maganar ƴanmatan "Boka ne ya tuntsure da dariya kana yace "ai an kusa zuwa gurin sbda dama akwai wani aiki da zaiyi idan siyasar ta kankama dole ya dinga haɗuwa da ƴanmata kamar uku kuma wa'inda basu wuce shekara sha takwas ba , gaban Abba ne ya bada dumm sai Bashir yace "za'a iya farawa ko Boka ?".
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: this book is not free pay 200 only -08141799224.
17-18
Zama Ammar yayi a kan gadon tare da shafo gefen fuskarta yace "barka da safiya my Noor "barka Nisha tace "dan a halin yanzu tunanin abokinta take sosai tama zurfafa bata san Ammar ya ƙara yi mata magana "Nisha "Ammar ya kira sunanta "na'an tace "tare da ɗago manyan idanuwanta masu ɗaukar hankali ta kallesa "tunanin me kike ?"babu komai "Nisha ta bashi amsa , daɗa matsowa yayi ya ɗagata cak ya ɗora kan cinya tare da cewa "bana son in dinga ganinki cikin irin wanan halin gashi kinƙi faɗamin damuwarki "ko har yanzun bakya sona "kuma kallonsa tayi shi kuma bai bari sun haɗa ido ba ya kawar da kansa gefe , shiru ne ya wakana na tsawon wasu mintuna sukaji ana nocking , sauketa yayi daga kan cinyar tasa ya miƙe ya je dai dai saitin ƙofar yace "waye ?"Mheera ce tace "nice pls bro buɗe man "ke bazan buɗe ba me zakiyi da asubar nan ?" gari fa yayi haske bro "wlh ki koma dan bazan buɗe ba "Ammar ya faɗa yana mata dariya ,juyin duniya yaƙi buɗewa daga ƙarshe dole ta koma nata ɗakin.
Kawance yake cikin bola yana kuka kowa ya gani yazo wucewa sai ya miƙe yaje gurinsa ya dinga yi musu alamar yunwa yakeji babu mai kulasa bare a taimaka masa , idan yayi kukansa ya gaji sai ya miƙe yaci gaba da tafiya ,da yamma misalin ƙarfe 5:pm ya fito cikin kasuwa kowa na hada hadar kasuwancin sa ya dinga nuna musu alamun yana jin yunwa amma babu wanda ya tanka masa kuma sarai sun gane abin da yake nufi ,ganin yunwa na neman yi masa illah ya sashi zuwa gurin mai shayi yana kuka yana magana kamar ta kurame duk dan suji tausayinsa amma ina , an zubawa wani mutumi dayayi parking motarshi soyayyar taliya da kifi a ciki gefe kuma ɓaƙin shayi ya ɗauke duka ya zuba da gudu ,mutumin yana cewa "ka barshi man kazo kayi min wani "ina sai da yabi mahaukacin amma ya kasa cimmasa dole ya dawo.
Ganin yayi nisa kuma babu mai gano lungun saya ɓuya yasa shi ajiye farantin kofin shayin ya faɗi garin gudu ya dingaci hannunsa duk datti haka ya dinga kaiwa bakinsa , shaƙuwa ya kamayi amma babu ruwan da zaisha cikin ikon ubangiji yayi gyatsa ya tashi tare da barin farantin a gurin ya dawo gurin kwanciyarsa ya kwanta .
Kaya Mommah ta fara haɗawa kasancewar Hajiya Faɗima tace "tun jiya ta bar gidan , babu wanda yayi yunƙurin tayata Abid da Asim basuji daɗin abin da Mommah tayi ba na siyarwa da Nisha mota , amma tunda Uwa ce babu inda suka iya Imaam kam fushi yake da ita sosai haka Pooja rabonta da taka babban palonsu tun jiya ,bayan Mommah ta gama tattara kayan ɗakinta tace "wa Abid kaje ka hayo mana mota ta kwashe kayannan "to yace "ba tare daya musa mata ba ya tafi , ba'a ɗau lokaci ba sai ga morar nan tazo ya shigo yace "Mommah motar na waje "hararar Asim Mommah tayi kana tace "maza kwaso na ɗakinku shi kuma Abid ya ƙarasa tattaro na Imaam "Imaam dake zaune yace "karki sake ki taɓamin kaya wlh ko da wasa "yaushe rabonka da shiga ɗakin ina tunanin bakaje kaga ɗakin ba ko ?"to ai angama tattara kayan tun jiya "waro ido Imaam yayi ta gama tattara kaya ita da ƴaƴanta yana zaune yama kasa cewa komai, sai da a kazo ɗakin Pooja Mommah tace "a barta ta shiga da kanta ,zaune ta sameta tana chart ta mayar da hankalinta sosai "Pooja "Mommah ta kira sunanta na'am Pooja tace "ta ci gaba da dane-danen ta "ki tashi za'a kwashe kaya "babu inda zani "Pooja tace "aiko dole kije tunda babu wanda zai zauna "ficewa Pooja tayi a zuciye ta isa babban palon su ta samu Imaam a zaune sai bin kowa da ido take ta durƙusa a gabansa tace "Imaam kana gani zata rabamana farinciki yaushe rabon ahalin gidannan da farinciki Imaam kayi wani abu "ta jijigashi tana kuka "ko yayi ko karyayi duk da nasan gidan nasa ne to na siyar da gidan nan da kuɗin ne na cika na siyi wancan ragowar kuɗin zamuje Super market siyayya "har yanzu Imaam ya kasa magana sbda baƙincikin daya tokareshi gashi bai san inda ƴan uwansa suke ba bare su bashi shawarar wani abun yana ji yana gani aka tattara kayan gidan da ƴar aikin gidan guda ɗaya da samarin gidan da Pooja da Mommah ta lallaɓata , dole shima ya miƙe ya bisu suka tafi .
Sunyi tafiya mai nisa sanan suka iso wata anguwa ana ce mata SHABAB , a wani tangamemen get Mommah tasa akayi parking suka sauko ta ciro keys a hand bag ɗinta ta buɗe kwaɗon ƙofar suka ɗunguma , ƙarewa gidan kallo suke sosai saboda kyau da tsaruwar da yayi harda gurin hutawa daga gefe ga swimming pool a can gefe kai gida dai masha Allah yayi kyau , suka ɗunguma zuwa ciki wata ƙofa Mommah ta buɗe mai ɗauke da mudubi mai kyau suka shiga ,palon ɗauke yake da kayan kallo da spiku da kujeru masu tsada ,nunuwa kowa ɗakinsa tayi ta nunawa Imaam ɗakinsa tayi da to ya bita sbda lamarin ya wuce tunaninsa , kasancewar Mommah ta shiga watsa ruwa yasa Pooja da Imaam da Abid da Asim kallon juna Pooja tace "bros wai kuna ganin abin da Mommah tayi yayi kuwa ?"murmishi sukayi a tare sukace waye yaƙi hutu wlh ni jina nake a sama kamar ɗan ambassador "suka tuntsire da dariya banda Pooja da ta cika tayi fam da ita , Imaam yace "ko ni yanzu na ɗanyi farinciki ko ba komai an ragemin jigilar wani abun "tabbas kun ɓat" Pooja ta faɗa a fusace ta shige inda akace ɗakinta ta zauna kasancewar iya kayan jikinsu suka ɗibo sai abubuwan da ba'a rasa ba yasata kwanciya a kan bed ɗin sai kuma tunanin ƙanwarta ya faɗo mata.
Yau kwanan Hajiya uku a gidan su Ammar cikin sa'a ta shigo da rana part ɗin su Ammar kasancewar baya nan sunje bikin abokinsa ƙanwar abokin kuma ƙawar Mheera ce shiyasa suka tafi tare dama kiran da take yi masa kenan.
Ganin Nisha na sallahr azahar a palo ta ɗaga hannu sama tana adu'a yasa Hajiya riƙe baki , tana ganin Nisha ta juyo tai saurin neman guri ta zauna tare da ƙaƙalo murmushi tace "barka dai ƙawata "itama Nishan murmishi tayi tace "yawwa barka Hajiya ina yini "lafiya Hajiya tace "sai ta ƙara kallon Nisha tace "ɗan miƙomin ruwa a fridge "kasancewar da nisa tsakaninsu da inda fridge ɗin yake yasa Nisha takawa a hankali ta isa gurin ,Hajiya kam dama abin da take so ta gani kenan , Nisha na kawo ruwan ta karɓa tace "na gode ta ɗan jima sanan tayiwa Nisha sallama tana isa part ɗin Ummin Ammar ta hau zabga salati tana cewa "jama'a karfa bazawara ya auro mana "Ummi dake ɗaki damuwar rashin mijinta na bijiro mata ta fito a tsorace tana cewa "Hajiya mai ya faru ?"mai kuwa ya faru kina gani ni banga alamun ancika aiki ba "Ummi dai bata gane abin da Hajiya ke faɗa ba tace "cika aikin me kuma Hajiya ?"ke bari inyi miki gwari gwari matar ɗanki nake nufi ai nace yazo ya karɓi farin ƙyalle idan zai kusanceta ni to banga alamun budurwa bace ma dan idona idonta tana sallah yau "murmishi Ummi tayi kana tace "kika sani ko yau ta fara "wlhi ban yarda ba a kiramin shi duk inda ya shiga dan uwashi yazo tun wuri "juyawar da Hajiya zatayi taga babu Ummi tama wuce ,Hajiya tace "ku kuke ɗaukar abin wasa daga haka sai a shigo maka da cikin wani gidanka "ta nemi guri ta zauna tare da rafka tagumi , shiru shiru babu Ammar babu labarinsa har ƙarfe takwas na dare Hajiya na zaune a palo ta baza ido tana jiran taji an shigo , ƙarfe goma da rabi tana darara hamma harta miƙe zata je ta kwanta taji an turo ƙofa ,ganin Ammar ne yasa ta ƙarasawa da sauri tace "kai sai yanzu kake dawowa a ina ka tsaya ?"nidai ba yaro bane da zaki dinga titsiyeni haka dan Allah ki barni ni bansan ma mai ya kawoni nan ba "riƙe baki Hajiya tayi tace "yanzu dai duk ba wannan ba matarka ta fara sallah? a'a wlhi ,Ammar yace " cikin serios to yau ɗinnan na ganta tana sallah wlh kuma nabaka nan da kwana uku ka bi umarmin amfani da farin ƙyalen nan idan kuma ba haka ba nidai gata nake maka "to bani "Ammar yace "fuska a turɓune zo muje "Hajiya tace "masa ya bita ɗakin da yake nata imhar tazo gidan nanne ɗakinta ,suna isa ta zauna shima ya nemi guri ya zauna ta ɗauko wata samira mai ɗauke da zuma a wata roba ta bashi tace "maza shanye gata nake maka dan kartace maka rago "ba musu Ammar ya shanye ta miƙa masa farin yadin ya fita dashi , yana fita kai tsaye part ɗinsu ya shiga ya kulle ƙofar ya ƙarasa bedroom ɗinsa ya watsa ruwa ya fito daga shi sai boxer ya nufi bedroom ɗinta , bacci ya sameta tanayi dan haka baiyi yunƙurin tashinta ba ya ɓoye farin ƙyallen a inda yasan bazata bincika ba ya kwanta shima sbda gajiyar daya kwaso yana kwanciya bacci ya kwashesa .
Islamiya ta ƙara yiwa Pooja nisa sosai a bakacin da suke wancan gidan a ƙafa suke zuwa yanzu kam dole sai mota .
Zaune suke a parlo ko wanne da plet ɗin farfesu a gabansa gefe kuma tissue ne duk wanda ya gama ya goge baki , wani nishaɗi Mommah takeji sbda shi kansa tebur ɗin da suke cin abinci abin kallo ne ga friza dake cike da kifi a nama da kayan miya tana jin kata a sama .
Imaam dake shan tea ya kalli agogon dake manne jikin bango yace "Pooja yanzu fa ƙarfe 9:5 am bazaki islamiya bane ?"cuno baki Pooja tayi kana tace "Imaam wlh ni makarantar tayi min nisa dama mai maicin karatun nakeyi na haƙura "waro ido Abid yayi yace "ke baki da hankali ne da zaki haƙura da karatu Asim saukarsa uku ni biyu ke kumafa ɗaya kikayi "dakatar dashi Imaam yayi kana yace "to ki kawo miji inyi miki aure "dum taji gabanta ya faɗi tace "miji kuma ?"eh man Mommah tace "tunda kina buƙatar zaman gida "uhm "Pooja tace "sai kuma tace "Allah ya kawo.
Yau kwanan Nisha biyar da aure kullum mahaukacin nan sai ya bi hanyar da yake gani Nisha tana biyowa amma ko almarta baya gani bare yaga wacce suke tahowa da ita tare wato Pooja , wani lokacin yayi kuka wani lokacin ya zuba tagumi ,idan ya tuno lokacin da take kawo masa abinci yayi ta kuka .
Wata haɗaɗɗiyar mota ce tayi parking a cikin gidan su Ammar lokacin yana fitowa ya shirya cikin shirinsa na larabawa sayawa yayi yana so yaga waye , abokinsa ya Hango wato Mubin ya ƙarasa da sauri sai ga Mheera ta fito tana dariya tace "bro naga kanata kallon motar ne ?"eh man ai ban ganeta bane "Ammar yace "yana murmishi ka canza mota ne ?"Ammar yace "wa Mubin "eh man yau one week kenan "Mubin yace "wa Ammar ina son Mheera da fatan zaku bani "faɗaɗa murmishi Ammar yayi kana yace "insha Allah yaushe kuka fara soyayya ne ban sani ba ?"dariya Mubin yasa yace "jiya a gurin bikin Yaya Jamal "masha Allah Ammar yace "wa Mubin "kana ya wuce palon su Ummi , ya barsu a gurin .
"Kin zamo tauraruwa a cikin zuciyata ina matuƙar farinciki idan har kika zamo rabona "rufe fuska Mheera tayi kana tace "nima haka burina shine ganin ranar auranmu "wow "Mubin ya faɗa tare da tafawa yace idan har kin amince zan yiwa Dad ɗina magana suzo gurin Abbanki akan maganar auran mu "rufe fuska ta sakeyi tace "na 'amince "Mubin ya fara rawa ,suka ɗan taɓa