Author : Zainab Habib Category : Romance
fito tana yiwa driver godiya ,ya juya ya tafi ita kuma ta shige ciki , da sallama ta shiga fuskarta shimfiɗe da fara'a ta zube a palo kasancewar bata ga kowa ba , Pooja -Pooja Mommah ta ƙwala mata kira ,da sauri suka zubo Pooja sa Nisha har suna rige rige ,Mommah na ganinsu tayi dariya tace "ƴan biyu na "Nisha ce tace "Mommah ina kika shiga munata nemanki ? "wlh gidan wata ƙawata naje tun muna primary rabona da ita tare da yi mata gaisuwar rasuwar iyayenta naje na samu batada lafiya ma kuma babu kowa a gurinta shine na zauna ,wayata kuma ta ɗauke babu chaji "Pooja dake kallon Mommah tace "ai Mami nata faɗa tace "dama tasan ba dawowa zakiyi ba wai baki damu da mahaifin....katseta Mommah tayi a zafafe tace "baki da hankaline idan Mami ta faɗamin haka kema sai ki mai maita ?"sunkuyar da kai Pooja tayi kana tace "yi Haƙuri Mommah "Imaam ne ya shigo hannunsa riƙe da leda yana ganin Mommah yace "ke kuma ina kikaje "Mommah na washe haƙora tace "haba Imaam kana yimin tambaya kamar ƙaramar yarinya "zama Imaam yayi yana kallon Mommah yana kuma buƙatar amsar tambayarsa , abin da ta gayawa su Nisha shi ta faɗa masa , kasancewar ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗora mata yasa shi cewa "amma dai kinsan baki kyauta ba ko ?"eh zani gobe "Mommah ta faɗa a taƙaice .
Ko da Mheera taje gidan Hajiya ta samu Hajiya zaune ita da wata yarinya mai suna Aisha tana danna mata ƙafa ,Hajiya na ganin Mheera tace "kaga sarauta "Mheera tayi dariya tare da faɗawa kan sofa tace "Hajiya Ammar ya saki Nisha fa "a zabure Hajiya ta miƙe tare da cewa "saki fa kikace ?"bana son wasa daga zuwanki ko jaka baki ajiye ba zaki tayar min da hankali ?"dariya Mheera tasa kana tace "yanzu dai kisa ƴan aiki su kawomin abinci inci dan yunwa nakeji "to acici kin sanyani cikin tunani kuma kice yunwa kikeji wanan ai ƙarya ce "Hajiya ta faɗa tare da gyara ɗaurin zaninta ta nufi cikin gidan tana ƙwalawa ƴan aikin gidan kira , Mheera dake nazarin suɓul da bakan da tayi wa Hajiya yasa ta rufe baki tace "na shiga uku ai Ummina na tonawa asiri yawo ga Hajiya masifatu ".
Dawowa Hajiya tayi hannunta riƙe da food flaks ta ajiye gaban Mheera tace "maza kici ki bani labari "Zaro ido Mheera tayi tace "nifa wasa nake miki so karma ki ɗauka da gaske ne "cikin rashin yarda Hajiya tace "wato ni kika mayar abokiyar wasanki kuma kalmar saki da kika faɗa akwai wata a ƙasa tabbas nasan cikin biyu anyi ɗaya ".
Ba tare da ta kuma kula Hajiya ba taci gaba da cin abincin ta .
Bayan ta gama cin abinci Hajiya tace "ke Mheera ina saurararki "farr da ido Mheera tayi wa Hajiya kana tace "wasa ne fa " Hajiya tace "ke Aisha miƙo min waya ta "Aisha na miƙowa Hajiya waya Hajiya ta danna number Abba tace "Umar kana gida ne ?"Abba dake zaune gaban Boka ,yace "ai nayi tafiya Hajiya ina wuni "lafiya Hajiya tace "wai Mheera ce tace "min wai Ammar ya saki Nisha "a zabure Abba ya miƙe tare da cewa "Nisha fa kikace ?"saki ? har zai fice Boka ya dakatar dashi Abba ya kashe wayar .
"Zauna muyi magana zan duba maka komai yanzu "hankalin Abba ne ya fara kwanciya yana jin a jikinsa Ammar bai saki Nisha ba sbda yasan da anyi sakin da Ummi ta faɗa masa , wani irin siddabaru Boka yayi kana ya ɓata rai yace "tabbas an saketa takai sati biyu bata gida "zaro ido Abba yayi yace "na shiga uku burin bazai cika ba tabbas bazai cika ba waaayo "zai cika inhar kabi abinda zan faɗa maka "Abba yaji muryar Boka na magana "zanyi koma menene idan har zan mallaki kujerar Governor ,zan kashe koma waye zan lalata koma waye Boka umarninka nake jira "kecewa da dariya Boka yayi kana yace "kasan dai daga wanan election ɗin sai hawarka kujera ko ?"Abba yace "eh "Boka yace "an sami ciki a gidanka da gudan jinin mukayi amfani gurin shayar da DODO jini kuma mun gano jininka ne ya haɗu yai ƙarfi sosai inda hakan zata sake kasancewa da munyi farinciki nayi maka alƙawarin hawa kujera nanda sati biyu "cikin rawar jiki Abba yace "na yarda indai Nisha ce zan koma yau in dawo da ita sbda cikar burina " dariya Boka ya kuma sawa a karo na biyu kana yace "a cikin ɗiyarka muka kwaso abinda mukayi alƙawari da kai "rassss gaban Abba ya bada yace "ɗiyata kuma wacce ?"badai yarinyar cikina ba ?"eh ita "Boka yace "alamar tabbatarwa , a razane Abba ya kuma kallon Boka yace "kenen Mheera ta lalata rayuwarta ? a jinina ! "ka maida komai ba komai ba idan hakan ta sake faruwa kahau kujera to zamuyi mata aikin da zamu kulle bakin wanda ya aureta bama zai tabbatar ba budurwa bace "nazari Abba ya fara shikam yama zai yi wanan lamari ya kasance yasan dai a zahiri babban saɓo ne mafi muni idan yayi haka ya saɓi Ubangiji da yawa , wata zuciyar tace "ka aikata abin da boka ya umarceka kawai shine mafita "zan tafi Boka zuwa gobe zan dawo "da kallo Boka ya bishi har ya fice ,bayan Abba ya koma masaukinsa ya buɗe door ɗin palon zai shiga Shukra tazo da saurinta zata karɓi jakar hannunsa ya dakar da ita , ƙara tahowa tayi ta rungumeshi ta baya tana mai sanya tafin hannunta a nashi ,bai yi wata wata ba ya tureta har tana faɗuwa ƙasa , niko nace karuwanci bai yi ba.
Kai tsaye ya wuce bedroom ya kwanta kan bed ya ɗora hannayensa a kai yana mai jin wani iri a jikinsa tashi ɗaya gumi ya karyo masa tambayoyi suka taho masa a tare "shin waye yayiwa Mheera ciki ?badai nufin Boka Ammar ne ya lalata mata tarbiya ba ?kai ina wlh ban yarda ba Mheera nada tarbiya saukar alƙur'anin ta biyu haka ma Ammar kullum cikin tsoron Allah suke "wasu zafafan hawaye suka zubowa Abba ya ƙara da cewa "dama haka masu neman shugabci ke shan wuya kafin su samu lol (wasu ba ?).
Abba na tafiya boka yasa dariya yace "na gama aikinka tun satin daya wuce sbda da zarar zaɓe yazo kaine ma mai ci ba sai ansha jini ba ,wanan aikina ne inason a bani SARKIN BOKAYE, kuma sai na kuma haɗa ƴarka da ɗanka sun kuma samar min da abinda DODO ya buƙata "ya kuma tuntsurewa da dariya a ƙaro na biyu.
Tunda Mommah ta dawo taji gidan nata yama fitar mata a ka sabda gidan Hajiya Faɗimatu data gani ya mugun tafiya da ita , kasancewar rana ce kuma yanzu sukayi azhar ana shirin zuwa duning cin abincin rana taji bazata iya ci ba idan har bata kira Hajiya Faɗimatu ba ,batasan ko wanne irin aiki bane amma tana da yaƙinin baya wuce safara daga wani gari zuwa wani gari ,tana tsaka da tunani Nisha ta turo ƙofa ,ɗago kai Mommah tayi tare da cewa "yawwa zonan "ƙarasowa Nisha tayi Mommah tace "yaushe zaki koma gidanki ?"sai Ammar ya dawo "Nisha taba Mommah amsa "ina fatan dai babu abin da ya haɗaku kinfa daɗe "eh Nisha tace "Mommah tace "kicewa "Pooja tazo "ficewa Nisha tayi ta isa bedroom ɗinsu tana shirin ƙwalawa Pooja kira taganta tana bacci , dawowa gurin Mommah tayi ta sanar mata , kana ta dawo palo ta kunna kalo .
Mommah najin Nisha shiru bata dawo ba tayi hamdalah tare da ɗaukar wayarta ta danna number Hajiya faɗimatu , wayar tana ta ring ba'a ɗauka ba ,gaban Mommah ne ya tsananta faɗuwa tashi ɗaya ta kama ambaton sunan Allah , kuma bata fasa kira ba , sai da ta yi kira wajen sau biyar sanan Hajiya Faɗimatu ta ɗaga cikin fara'a tace "afuwan Hajiya Khadija muna meeting ne shiyasa ban ɗaga wayarki ba "murmishi Mommah tayi tace "dama ina so in sanar miki da na amince da kalar sana'arki "dariyar farinciki Hajiya Faɗimatu tayi kana tace "ina mai tabbatar miki da bazakiyi dana sani ba " washe baki Mommah tayi kana tace "kamar yaushe zan fara zuwa kuma wane irin aiki ne ?"karki damu aikin ba wani mai wuya bane da zarar an fara zan sanar dake kedai ki fara neman izinin mijinki "cewar Hajiya Faɗimatu "to Mommah tace "cikin sa'a taji sallamar Imaam , amsawa tayi tare da miƙewa ta rungumeshi Imaam yasha mamaki yaushe rabon Khadija da haka har ya mance ,ya ɗan faɗaɗa murmushinsa yace "naga yau sai farinciki kike me muka samu ?"washe baki Mommah tayi kana tace "zauna in baka labari "zama Imaam yayi tare da tattaro nutsuwarsa ya mayar ga Mommah -Mommah tace "safara zamu dingayi nida ƙawata aikinta kenan siyarda kaya na yara da su zanuwan gado muna zuwa ƙasashe muna sarowa "jimm Imaam yayi sai kuma yace "wanan ba sana'a bace ki sauya wata kina matar aure kina yawo a titi? "faɗa Momma ta fara tana cewa "amma dai ba saɓo nacema zanyi ba ko ? "banda abunka yaushe rabon da ka bada kuɗin cefane nike ciyar damu kasha mai kyau kaci mai kyau duk nice amma nace zan kama sana'a kana wani yimin faɗa "kinga jekiyi -jekiyi Allah ya bada sa'a "Imaam ya faɗa tare da ficewa ya barta a gurin , yana fita Mommah tayi wani murmishin farinciki tace "idan naje gidan mu sai in wuce gidan Hajiya Faɗimatu inji "wanka ta shiga tana fitowa ta gyara jikinta ta fito kai tsaye part ɗin su Nisha ta nufa tana shiga ta samesu zaune suna karatun alƙur'ani ,cikin fara'a Mommah tace "zani gidan mu dan Allah ku kula da gida "to Pooja tace "Nisha tace "sai kin dawo "ficewa Mommah tayi ta ɗauki jakarta ta fice ko side ɗin Imaam bata koma ba.
"Kaji rainin Hankali Umar ya kashemin waya".
Mheera dake tuntsurewa da dariya tace "dama ai nace miki ba gaskiya bane kece kika ɗauki ɗumi ".
Hajiya dake gyara ɗaurin ɗankwali tace "wanan zancen banza ne ai dole in yarda a ina kika tama jin ance anyi saki da wasa ?" ganin Hajiya zata wuce gona da iri akan maganar kar tasa ta ɓallo liƙi yasa Mheera cewa "nama fasa kwana tafiya zanyi" aiyya ƴar albarka ki ɗaɗa kwana sai mu tafi gidan naku gobe "waro ido Mheera tayi kana tace "wlh bada ni zaki tafi ba tabbas kima nemi wanda zakibi ".
Mheera tasan inhar Hajiya tabi ta gidansu to sai ran Ummi ya ɓaci ,bayan ɓacin rai ma sai tasa an dawo da Nisha
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: 35-36
Miƙewa Imaam yayi ya fice ba tare da ya ƙara yi mata magana ba .
Imaam na fita Mommah tayi tsaki tare da cewa "shi sam baya ganewa da har zai hanani mallakar wanan gidan da motocin cikinsa wlh koda wani abu zai faru sai dai ya faru bazan bari ya wuceni ba".
Washe gari Mommah ta kira ƴar aikin gidan suka hargitse gidan da kaya , Nisha kam tana ta farinciki Mommah ta sami sana'a , fitowa Pooja tayi a yanzu ne ta tabbatar da zasu bar gidan sabda taga zahiri an fara haɗa kaya.
Ring wayar Mommah ta fara , dubawa tayi taga mai kiran nata taga number Mami ne ,yatsina fuska tayi tare da taɓe baki ta ɗaga wayar haɗi da yin sallama , daga can ɓan garan Mami tace "yau sadakar bakwai Khadija baza kizo kiyiwa mahaifinki adu'a ba ?kai ni wlh aiyuka sunyi min yawa amma dai gani nan zuwa "Mommah ta faɗa tana kita , Nisha da Pooja dake tsaye suka ce "Mommah muma zamuje "a'a ku zauna ku ƙarasa tattare kayan "Mommah tace "kana ta wuce bedroom ɗinta , Nisha da Pooja badan sun so ba suka amsa da toh " Mommah ta faɗa toilet yin wanka , bayan ta fito ta shafa mai da powder ta sanya kaya ta ɗauki ƙaton hijab da wayarta da kuma pos (jakarta) ta fice palo , to sai na dawo bama daɗewa zanyi ba dan Allah ku ƙoƙarta "tom Pooja tace "tare da cewa "sai kin dawo Nisha ma haka.
Bayan sun gama tattara kayan Imaam ya shigo ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun da ba'a ɗaga ba ya kalli su Nisha yace "yau watan mu nawa da dawowa gidan nan ?"watan mu huɗu Imaam gashi zamu canza wani gidan "Pooja ta faɗa cikin rashin jin daɗin sauyin gidan "murmishi Imaam yayi tare da wucewa side ɗinsa .
Mommah na isa gidansu tun daga ƙofa ta fara ƙirƙiro kukan dole , kuka tana shiga cikin gidan ta kurma ido tana cewa "wayo Abbana Allah yaji ƙan ka yayi maka rahamab yasa mutuwa hutu ce a gareka "ta ƙarasa gidan kai tsaye ɗakin mahaifiyarta ta nufa , tana shiga ta samu maman nata zaune tana ta karɓar gaisuwa , zama Mommah tayi kusa da Mami ta ruƙo hannun Mami tace "haba Mami fushi kike dani ?ture hannunta Mami tayi tare da cewa "kinyi asarar a rayuwarki "mutanen gurin suka rafka salati suna yiwa Mami faɗan wanan mugun alkaba'in da take yiwa ƴarta , kuka Mami ta fashe dashi tana cewa "ace mahaifinka guda ya rasu amma mutum bai nuna damuwa ba ?"shima mijin naki sau biyu yazo sbda kuna wasa da rayuwa ko ?Mami ta fashe da kuka mai sauti tare da toshe bakinta da hijab ɗin jikinta , ci gaba da kuka Mommah tayi sai da mutanen gurin suka bawa Mami haƙuri suka bawa Mommah rashin gaskiya sanan Mami ta amsa gaisuwar Mommah .
Ba ita tabar gidan ba sai wajen la'asar ta bawa Mami kuɗi masu yawa tace "tasi kayan abinci "kuzo kuga washe baki a gun Mami har da rungumo Mommah.
Tsokaci:
Ina mai tunatar daku akan yawan kyauta ,tana buɗe ƙofofin alkhairai da dama , musamman ma ga iyayenka ,idan ka samu suma ka sammusu hakan zai daɗa kara maka haske a idon su ,ina fatan kun fahimta iyaye suna jin daɗin suga ƴaƴansu sunyi musu kyauta.
Mami har da raka Mommah bakin titi ta hau mota .
Su Nisha sun gama tattare kayan tsaf sun ɗaya ta shiga wanda ɗaya na zaune a kan bed wato Pooja , Nisha na fitowa Pooja ta shige Nisha ta zuba tagumi a cikin zuciyarta tace "ko yaushe zan ganka ban sani ba Allah yasa kana raye Allah yasa babu wanda ya cutar dakai"ta ƙarashe maganar idonta ɗaya na fitar da hawaye "kar Pooja ta zargi tana ɓoye mata wani abu yasa Nisha saurin shafa mai ko powder bata saba ta sanya kaya ta fito palo zaune ta sami Mommah a kujera guda ita da Imaam , suna hira har da dariya "mamaki ne ya kama Nisha ,a ranta tace "ba Imaam baya son barin gidannan ba to ya akayi hakan ?"to ance tsakanin mata da miji sai Allah mudai namu ido "Mommah ta kalli Nisha tace "zuwa yau da yamma insha Allah zamu koma kun gama haɗa kayanku ?eh Nisha tace ".
Tsabar tafiya har ƙafarsa na daɗewa ya rasa inda zai ga abokiyarsa a halin yanzu inda zai ganta zai tabbatar mata da shi ba kurma bane yana iya magana , zama yayi da yagaggun kayansa ya zuba tagumi a fili yace "yaushe zan ganki mai taimako na Allah ya sanyaki farinciki kamar inda kika sani "ya fashe da kuka , ya koma gurin da in tazo wucewa islamiya take ganinsa ya kuma zuba tagumi a karo na biyu .
Zuwa yamma Hajiya Faɗimatu ta kira Mommah tare da shaida mata ta turo motar ɗiban kaya yanzu zata wuce india nan da sati biyu zatayi wa Mommah bayanin kasuwancin nasu ,Mommah tace "to tare da kuma yiwa Hajiya Faɗimatu godiya .
Ƙarfe biyar da arba'in wata ƙatuwar mota ta ɗiban kaya ta shigo cikin anguwarsu Mommah already anyi ma mai motar kwatancen gidan ,horn kawai yayi aka buɗe get ɗin gidan su Mommah ya shiga , Mommah najin shigowar Mota ta fara jidar kaya tana fita dasu haka ma Imaam da su Nisha sai jida suke , kasancewar ba wani tarkace suka ɗauka ba a cewar Mommah sabon gida ne yanzu tana da kuɗin da zata siyi sababbin kaya , Imaam ya koma kamar mijin tace "baya um baya um-um, suna gama loda kayan motar ta tafi Mommah tace "Imaam ka taro mana mota mu shiga "inada magana ! Imaam ya faɗa tare da zama kan tails ɗin ɗakin "ina jinka "Mommah tace "tana jiran taji abin da zai ce ,Imaam ne yace "shin wanan gidan an siyar dashi ne ? a'a Mommah tace "ba'a siyar da zadai a siyar "waro ido Imaam yayi kana yace "idan an siyar ki ware min kuɗin gidana ki bani "cike da masifa Mommah take kallon tace "ai ka riga da ka gama cinye kuɗin gidanka "faɗa na neman kaurewa a tsakaninsu Pooja ta taho gabansu idonta na zubar da hawaye tace "haba Imaam hakan yana da kyau ku dinga faɗa a gaban mu ?Nisha ma tazo da kuka tana jijiga Mommah tace "baki san mata ba baki san halinta ba bakisan asalinta ba kin ɗauki yarda kin bata kin mayar da ita aminiya ta ƙwarai "wanketa da mari Mommah tayi kana tace "kunzo gayamin magana ne ?"to idan kun fass kaf ɗinku zan ci muku mutunci"ficewa Imaam yayi yana fita ya samu wata mota babu kowa ,tsayar da ita yayi kana ya dawo gidan yace "na tare mota "cikin hanzari Mommah ta rataya jakarta tacewa "su Nisha su wuce gata nan ,kai tsaye motar suka shiga har da Imaam ɗin daga ƙarshe Mommah ma ta shiga suka tafi , tafiya sukayi mai nisa sosai kana suka iso anguwar, kale-kale su Imaam suka fara tare da jinjina anguwar anguwar babu ginin talaka kaf ginin masu kuɗi ne ,a razane Imaam ya kalli get ɗin da Mommah ke bubugawa a zuciyarsa yace "badai wanan gidan bane "ganin Nisha da Pooja da Momma sun shige gidan yasa Imaam shima ƙarasowa ya shiga , suna shiga