Author : Zainab Habib Category : Romance
wani abun ne ?"girgiza mata kai Ummi tayi alamar a'a ƙar aikin ta fice .
governor ne zaune akan wata kyakkyawar kujera ana ta shirye shiryen zaɓe "bayan sun kammala taron da aka gaiyyata mutane sun watse sai iya na hannun damansa , suka ɗora hannu kan ƙaton table ɗin daya zagaye gurin ,wani daga cikinsu yace "mai girma governor kasan munyi alƙawarin yin adalci amma ba'a kwatanta hakan ba ,yanzu gashi zaɓe ya ƙarato mun rasa tudun dafawa "buga table governor yayi tare da cewa "kai Bashir ka iya bakinka ubanwa yace "bamuyi adalci ba ?"dai daita nutsuwarsa Bashir yayi kana yace "afuwan shugaba mai adalci "wani daga gefe mai suna Adamu yace "nidai ina ganin ya kamata ace munbi ko wane lungu na jahohinmu mun raba musu kuɗi da Abinci "jinjina masa governor yayi kana yace "shawararka tayi aje store a kwashi buhun hunan abinci a rarrabawa mutane tare da poster , angama shugaba mai adalci "mutanen gurin suka faɗa tare da ficewa ya rage daga shi sai Bashir "Bashir yace "inada shawara " Governor yace "ina jinka "akwai wani hatsabibin boka wanda aikinsa yake kamar yankan wuƙa nasan idan mukaje gurinsa zamuyi nasara ,dalilin da yasa nace maka haka shine ,tun yanzu naji mutane suna cewa "wanan karan basa time ɗinmu "waro ido governor yayi kana yace "musa rana sai mu tafi "cikin jindaɗi Baahir yace "ai kaine da sa rana " Governor yayi murmishi kana yace "zan duba in gani "Bashir ya fice ,bayan ya fita sai ga kiran wayar Ummi ɓata rai yayi yace "ana tunanin inda za'a ɓullowa lamari kina wani kirana "ya ɗaga tare da sallama ,bayan Ummi ta amsa tace "yau satinka ɗaya yaushe zaka dawo ?"ke wai maiyasa baki da fahimta ne ?"so kike in dawo ban gama abubuwan da nake ba ?"Uhm Ummi tace "to zan biyoka "waro ido yayi yace "banfa lamunta ba sbda maza zasu dinga kalleki "murmishin takaici Ummi tayi kana ta ajiye wayar ba tare data kashe ba , Governor ya riƙe baki tare da cewa "babu inda zani dake daga gida sai gida so nake in sami farar mata wacce zata dinga tarai rayata ,ke gashi kinyi boko amma ustazanci yasaki a gaba kije ki bani kunya "yanata magana shi kaɗai "daga ƙarshe yaci gaba da tunanin zaɓe ,kullum sai Ummi tayi hawaye sosai take jin zafin rashin tafiya da ita ƙasashe da bayayi , zuwanta makkah biyu bayan nan bata taɓa zuwa wata ƙasa mai nisa sosai sai wace ke maƙotaka da tasu.
Yau su Mommah suke ta shirye shiryen zuwan iyayen Ammar kasancewar har anyi sati uku , tun asbha Mommah ta fara gaganiyar girke girke harda su Pooja da Nisha , zuwa ƙarfe 11:am an gama komai an kai ɗakin Imaam , Mommah tasa Nisha wanka ta zaɓo mata material mai kyau ɗinkin riga da wando ,kasancewar basu wani fiye mu'amala da atamfa ba , iya kyau Nisha tasha shi , bayan sun gama kintsa komai zuwan baƙin ake jira sukayi durum durum a palo ,Abid da Ansar sun fita tun ƙarfe goma ,shiru shiru har ƙarfe biyu tayi har uku babu alamarsu ,damuwa Mommah ta fara shiga ita babbar damuwarta ma maƙudan kuɗin data kashe gurin wanan girkin ,har akayi la'asar shiru ta kasa haƙuri ta ɗaga waya ta kira Umm Ammar , Umm Ammar na kwance damuwa ta mamaye zuciyarta taji watarta na ring ɗagawa tayi sbda taga sunan Mommah tace "Y Umm Ammar naji shiru ne masu zuwan "zaro ido Umm Ammar tayi kana tace "masu zuwa ina ?"Mommah tace "masu zuwa gurin maanar auran Nisha man "oh "Umm Ammar yace "ai Abban nasa baya nan shi yasa "bugar goshinta Mommah tayi kana tace "to Allah ya dawo dashi lafiya "Umm Ammar tace "amin ya rabbi"Pooja dake kusa da Mommah tace "wai lafiya kuwa Mommah ? inafa lafiya duk wanan uban maƙudan kuɗin da muka narka gurin yin abinci wai ubansa yayi tafiya wanan ai wulaƙanci ne "Nisha dake dane dane a waya tayi dariya ƙasa ƙasa , Imaam ne ya shigo da sallama yace "ya dai har baƙin sun ƙaraso ne ?"tagumi Mommah ta zuba kana tace "inafa wai Governor baya gari "Imaam yace "Pooja bani foodflaks ɗaya in fara ci Allah ya mayar da alkairi "kuma cika tayi tai famm kamar wacce zata fashe , ta tashi fuuu tayi bedroom ɗinta Imaam na dariya .
Washe gari ta kama Monday yau Governor suka shirya zuwa gurin wani hatsabibin boka sbda wacce suke takara da ita mace ce take neman hawa kan kujerarsa , guri ne daya amsa sunansa kasancewar gashi dai wani katafaren gida ne mai kyau wanda yake zagaye da furanni amma boka ne a ciki ,bayan sunyi parking Bashir ya fara shiga kana Governor shima ya shiga , da zamansu bokan ya fara wasu surkulle kana yace "mai ke tafe daku ?"Bashir ne yayi masa bayanin komai ,boka yace "akwai buƙatar shan jini "Governor ne yace "idan har buƙata ta ...Bashir ya katse shi tare da cewa "jinin wa zaka bada ?"wanda yayi min gautsin baki "Governor ya fada tare da shafa gemunsa ,dakatar dasu boka yayi kana yace "ku saurareni , munason jinin na kusa dakai wato wanda yake jininka sai ka kawo kafin nan mu fara aiki "nisawa Governor yayi kana yace "to "Bashir ya ajiyewa boka maƙudan kuɗi suka fito daga gidan suka shiga mota Bashir ya tuƙashi suka dawo gidansu , suna parking Governor ya fice da sauri ya nufi bedroom dinsa cike da fargabar alƙawarin daya ɗaukarwa boka ,Bashir ne yayi nocking yana jiran amsa ,sai da ya ɗau mintuna kana Governor yace "shigo "shigowa yayi da sanyin jiki yace "Allah ya temaki Governor na yau dana gobe yanzu ya kake ganin ya dace ayi ?"kaina ya kulle ina buƙatar keɓewa ni kaɗai "Governor yace "yana mai shafa sumar kansa , ficewa Bashir yayi tare da rufo masa ƙofa ya tafi nasa sashin.
Tunda Ammar yaga har an ƙara sati ɗaya akan alƙawarin da yayi gashi Abban yaƙi dawowa yace "wa Mheera wlh zani in kai sadakina da kaina nasan kuɗi babu abinda basa iya yi tabbas sai nayi aure a watan nan ko ta halin yaya "shafo ƙirjinsa Mheera tayi kana tace "haba bro kabi komai a hankali insha Allah zaka sami abinda kake so "rai a ɓace yace "rainamin hankali ake idan na aikata zaki tabbatar "ya fice " kai tsaye ɗakin da mahaifinsa ke ajiyar kuɗi ya nufa ɗakin da babu wanda yasan da zamansa daga Ammar sai mahaifinsa yaje ya ɗibi LAK biyar a wani akwati ya fice dashi , har ya kai bakin get ko mota bai buƙata ba yaji Mheera na ƙwala masa kira ,juyowa yayi ya kalleta ta ƙaraso har gurin da yake ta riƙe hannunsa tace "a matsayina na ƙanwarka na baka shawara kaƙi karɓa ko ?"ya kamata ace kafin ka aikata abu ka nitsu sosai "nace zan shawo kan matsalar kana ganin bazan iya bane ?" nasan zaki iya nima ina son gwada jarumtaka ta ne "no bro wanan ba jarumtaka bace kuma bata haka ake gwada jarumtaka ba "waro mata ido yayi ta gyaɗa kai tare da cewa "yes"kamo hannunsa tayi suka dawo babban palon gidan ,Mheera tace "ni babbar damuwata Ummi tunda na dawo naga bata cikin walwala kodai anyi mata wani abun ne ?"tsaki Ammar yayi mtsw tare da cewa "tunda akace nima bazanyi farinciki ba to tabbas kowama haka "cikin yanayin damuwa Mheera tace "uwa fa "bro a ganina damuwar Ummi ta zamo tamu tunda ita ce mahaifiyarmu , share pls ba muci gaba da maganarmu "Ammar yace "yana dariya , Mheera ce ta miƙe tare da wucewa bedroom ɗin Ummi ta ganta kwance tana kuka , ya subhanallah ya Ummi pls Ummina mai ya sameki ?"babu komai Ummi tace "tare da tashi ta zauna " Mheera ta share wa Ummi hawaye ta tsaya tana kallonta , murmishi Ummi tayi tace "kinci abinci kuwa ?"eh Ummi "amma kinƙi gayamin matsalarki "girgiza kai Ummi tayi kana tace "babu komai karki damu "Mheera ta miƙe ta fita cikin fushi tana fitowa taga Ammar ya fice.
Sanye suke da kayan islamiya yasa guga Nisha tace "anty Pooja wane irin farinciki kikayi da kikaji ance baƙi basu zoba ?"dariya Pooja tayi tace "ai inaga ma na fiki farinciki wlh gashi munci kayan daɗinmu hankali kwance "suna tafiya suna hira har suka iso islamiyarsu , bayan malamai sun shigo anyi karutu an gama aka tashesu , a hanyarsu ta dawowa gida suka ga wani saurayi fari kyakkyawa yana tafiya kayansa duk sun yage wandonsa ne kawai bai yage ba amma yayi datti sosai fuskar saurayin har tana jirwaye , Nisha ce tace "Pooja tsaya mu taimaki wanan man "cikin nuna ƙyama Pooja ta tofar da miyau tace "Allah ya kyauta in rasa wanda zan taimaka sai wanan kafin ma ya matso kusa dani wari yake "Pooja ta toshe hanci "Nisha ce ta ƙarasa har inda yake tace "Aslamu alaikum "wlkslm saurayin yace "tare da ƙanƙance idonsa yace "waye ke waye ke , waye ke cikin tsoro tace "nice Nisha "dariya ya tuntsure dashi kana ya fara cewa "Nisha, Nisha janyo wuyan hijab ɗinta Pooja tayi kana tace "kinda hankali kuwa ?"wanan da kike gani mahaukaci ne wlh idan baki fita harkarsa ba sai ya fashe miki kai , cikin rashin tsoro zata fincike ta koma gutinsa Pooja ta zuba mata mari tare da cewa "kinada hankali kuwa ?"ta jata suka wuce gida , suna isa Pooja tace "sai na gayawa Mommah "haɗe hannu Nisha tayi alamun bada haƙuri tace "dan Allah kiyi haƙuri karki faɗa na roƙeki "to naji amma kinsan zaki zubar mana da ajinmu da zarar kina tsayawa gurin mahaukacin nan ?"mahaukaci ba masoyi ba mai zanyi a gurinsa "Nisha ta faɗa tana kallon Pooja , koma mai zakiyi ya kamata ki dinga nemawa kanmu mutunci ace kamar mu muna tsayawa gurinsa ?"shiru Nisha tayi tunda Pooja ta kasa fahimtar ta.
Suna isowa palon suka zauna kan sofa tare da kallon yayun nasu dake zaune Nisha tace "yah Abid kabamu labarin rayuwar makatantar ku "Ansar da yai fushi yace "wato Abid shine naki ko baku ganni a zaune bane ?"rufe baki tayi tare da cewa "Afuwan ya Ansar pls kubamu labari "Pooja dake dariya tace "idan suka baki labari ya zakiyi ?"inji daɗi "Nisha tabawa Pooja amsa ,Abid ne yace "to yanzu dai Ansar kai ne mai bada labari ni dama kasan bani da budurwa "dariya suka sa dukkansu ,Ansar yace "a gaskiya nidai nayi budurwa amma fa ƴar sarkin Misra ce , sunanta Princess Marwa doguwa ce fara tana da hanci sosai kana kuma tanada yalwar gashin gira dana kai gata da point a kumatunta tana da yawan fara'a ,daga Egypt muka tafi Misra nida ita mukaje masarautar mahaifinta dattijo ne amma a maganar auran nasu sunada al'adu masu yawa wanda sai daurarre wanda ko kuɗi ne bazai yi maka aikin ba "nisawa Ansar yayi yaci gaba da cewa "koda na barta a can na dawo Egypt da tunaninta na dawo amma ina tunanin al'adarsu shin zan iya kuwa ?"Nisha da ta baza masa fararen idanunta tace "Yah Ansar to su wane yare ne ?"ajiyar zuciya Ansar ya sauke kana yace "wlh bani da tabbacin yarensu dan banyi bincike a kai ba " to muna jinka Pooja tace "tana murmishi , kwana biyu da dawowata ta kirani a waya take cemin baza 'a barta ta dawo makaranta ba sbda taje dani a matsayin wanda take so kuma shi mahaifinta wato sarkin yace "zai haɗata aure da ɗan yayansa , ita kuma tace "ni takeso "shine nace ta kwantar da hankalinta shi aure nufi ne na rabbi idan yaso sai taga munyi auran mu cikin kwanciyar hankali ,ya kalli Nisha yace "nasan da kamar wuya in aureta ba tare dana jikkata ba kawai na kwantar mata da hankali ne "Abid da sai yanzu yayi magana yace "to wai dole ne dahar zaka tafi wata uwa Misra neman auran ƴar sarki ?"chiii "Ansar yace "nasan bakazo fagen gwagwarmaya ba yabbas bakasan so ba kuma bakasan mai ake nufi dashi ba , dariya Abid yasa yace "to lovers asha soyayya lafiya "su Pooja suka sa dariya ,Mommah ce ta shigo tana sanye da abaya baƙa ta nemi guri ta zauna dukkan su suka yi mata barka da shigowa ,yawwa tace "musu tana fara'a kana tace " naji hirarku wato ƴar sarki kai Ansar kaje nema "dariya Abid yayi shi kuma Ansar ya sunkuyar da kai.
Washe gari Ammar ya tashi da tsananin sha'awa ya rasa inda zaiyi rabonsa da harka da mata tunda yaje England karatu yana tunanin ma Umminsa ce ta rabashi da harka dasu ,dan yasha ganinta tana sallahr dare tana adu'a a fili tana cewa "Allah ka ashiryamin Ammar ka cire masa son aikata saɓonka.
Yau kam abin ya ta'azzara , kai tsaye ya nufi fridge ɗinsa ya buɗe tare da fito da golden B ya bu ɗe murfin tare da tutulawa a bakinsa ya wurgar da robar gefe , tashi ɗaya yaga gidan na juyamasa yana jinsa kamar a saman jirgi yaje , tashi ɗaya ya kwanta ƙasa yama rasa yanayin da yake ciki , Mheera ce ya shigo da gudunta tana cewa "bro bro kazo Ummi na kuka tun ɗazu "shiru bata ji ya amsa mata ba , ƙara mai maitawa tayi ta kuma jin shiru , kai tsaye ta faɗa ɗakin da sauri , ganinsa tayi a kwance kan kafet , mamaki ne ya kamata shida ko kwanciyar kujera bayayi sosai amma yau shine da kwanciya a nan ?"kodai bashi da lafiya ne ?"ta tambayi kanta , taɓa shi tayi taji shiru sai da ta jijigashi sanan taji yace "haba Nisha nifa mijinki ne dan mai zaki dinga guduna ko basu yarda ba zamuyi auran mu "Mheera dake tssugunne a gabansa taji muryar tasa kamar ta mashayi tasa kuka tare da cewa "bro kar kace min giya kake sha ,pls bazan ji daɗi ba " ga damuwar Ummi ga damuwarka da wanne zanji ?"shidai Ammar na kwance bacci ma ya ɗibesa , taji wayarta na ring ɗagawa tayi a hankali tace " Ummi gani a gurin Ammar "Ummi ce tace "kizo ina son ganinki "da sauri Mheera ta fice daga ɗakinsa ta nufi na Ummi ,bayan tayi sallama ta shiga Ummi tace "Mheera ya kamata kije ki gaishe da Hajiya dan tunda kika dawo babu inda kika leƙa "murmishi Mheera tayi kana tace "Ummi sai gobe zani yau inason hutawa "to Ummin tace "suka ɗan taɓa hira ana kiran sallah kowa yaje yin alwalah.
Yau ma kamar kullum sunyi shiri zasu islamiya ciwon marar Pooja ya tashi bata sami damar zuwa ba "Nisha ita kaɗai ta fito tana isowa palo Imaam dake zaune ya miƙa mata kuɗi yace "ta hau mashin durƙusawa tayi ta karɓa tare da yi masa godiya ta yiwa Mommah sallama ta fice ,bata tsaya hawa mashin ba ta tafi a ƙafa ,tana cikin tafiya taci karo da wanan saurayin mai kamada mahaukaci ,yana ta tsince -tsincen ledoji a bola , tsayawa tayi tana ƙare masa kallo , fari ne dogo amma ba sosai ba yana da faffaɗan ƙirji kana yana da madai daitan idanu laɓɓan bakinsa pink ne yayinda girarsa ta cika da gazar gazar ɗin gashi , ɗaga masa hannu tayi tace "abokina "dariya yasa yace "ke ina zaki ?"itama dariyar tayi tace "wai dama kana magana shine kaƙi yimin ?"murmishi yayi wanda ya baiyanar da sihirtaccen kyawunsa yace "zoki goyani "tuntsirewa Nisha tayi da dariya wacce rabonta dayi tun kafin Ammar ya shigo cikin rayuwarta , amma yau kam tasha dariya iya dariya , ta nemi guri ta zauna shi kuma ya zauna a ƙasa ya mimiƙe ƙafa yana tafi ,turɓune fuska tayi tace "to ka dena haka man sai kace "ƙaramin yaro ? yanayin inda tayi dariya ya bashi dan haka ya kuma tuntsirewa da dariya mai sauti , ta miƙe wai a dole tayi fushi tace "ni na tafi da gudu ya kamota tare da cewa "zaki bani abinci "zuciyarta kamar an buga mata guduma 'a zuciyarta tace "kar dai baici abinci ba tun safe ko jiya ?"juyowa tayi tace "zakaci wani abin in siyo maka ?"a'a yace "sai dai abinci , ta rasa inda zatayi gashi kuɗin hannunta bai kai na siyan abinci ba ,ta hango mai siyarda cin cin da gudu ta ƙarasa gurinsa tace "abani na duka "guda ɗaya aka bata ta dawo gurinsa ta tsuguna tare da cewa "gashi kaci "da sauri ya kamo hannunta yakai bakinsa yanaci yana kuka , sai daya cinye ya haɗe hannayensa biyu alamar godiya ,itama hawayen take tana ta kallonsa , haka ta shashance a gurin babu batun islamiya har lokacin tashi yayi , tana gani an fara wucewa "ta miƙe tare da ce masa sunanka fa ?"babu "yace "mata to shikenan zan dinga kiranka da bawan Allah kaji "ya gyaɗa mata kai alamar eh " ta wuce tana tafiya tana waigensa har ta bace da ganinsa .
Bayan ta koma gida lokacin ana kiran magrib tayi alwalah tayi sallama tace "anty Pooja ya jikin ?"yayi sauƙi Pooja tace "Nisha ta kuma cewa "kizo muci abinci "no sai zuwa anjima bakina babu daɗi jekici "Pooja tace "tana yamutsa fuska ,miƙewa Nisha tayi dama hakan takeson ji ta nufi dining tana zuwa taga babu kowa Mommah na ɗakin Imaam ta wuce kitchen ta ɗauki wata kula ta zuba abinci da nama ta sanya a hijab ta fito waje , tafiya ta dingayi har tazo gurin bawan Allah ta gansa kwance cikin bola yana bacci , da kallon tausayi ta bishi ta tashe shi kana tace "ga abincinka "da sauri ya tashi jin an ambaci abinci yafara murmishi tare da haɗe hannayensa biyu alamar godiya bye bye tayi masa ta koma gida , tana shiga palo ta wuce dining dan cin abinci Imaam ta sami shida Mommah a zaune suna cin abinci Imaam yace "Nisha ina