ƘANIN UBA Sirrin Jinin Gida by Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  Romance

Chapter   11 / 18

30K to 33K   out of 53.2K words

ba iyayen nasu duka suka hallara sukaji faɗan da su Jalilah sukeyi ,sosai suka dinga yiwa Jalilah faɗa tare da ce mata" wani ma da kuɗi yake neman aihuwa bai samu ba amma ke kin samu kina neman butulcewa ubangiji "badan faɗan ya shigeta ba ta bisu da toh sbda wanan cikin ba sonsa take ba ,iya Imaam ya isheta rayuwa .
Bayan anyi mata ƙarin ruwa da magunguna zuwa yamma suka koma gida ,iyayen nasu ma suka wuce gida kana naka Allah na nashi ciki nata daɗa fitowa duk inda taji maganin zubar da ciki sai ta sha amma ko amai batayi sai ma lafiya da take ta ɗaɗa samu , har cikinta yakai wata bakwai tana shan maganin da zai zube kuma Sabir ya lura da hakan bai yi mata magana ba ,sai dai kullum cikin dare yana tashi ya gayawa Allah damuwarsa sanan ya koma ya kwanta .
Kwanci tashi asarar mai rai cikin Jalilah yau ya cika wata tara da kwana tara , ta tashi da ciwon ciki ba wani mai tsanani sosai ba , lokacin shi kuma Imaam yana da shekara goma a duniya , kaɗan kaɗan take jin ciwon ,tazo kwanciya taji babu hali tsugunawa tayi zata ɗauki waya a ƙasa kasancewar ɗazu da Imaam yake rikici ya wurga mata nan taji wani abu ya buɗo ta gabanta , salati ta fara da sauri ta ajiye wayar hannunta ta dafe kujerar cikin ikon Allah nishi yazo mata sai ganin ɗa tayi ya faɗo yana tsandara ihu , ɗan na faɗowa taji tsanarsa ta daɗu a cikin zuciyarta , jikinta na rawa ta ɗaga waya ta kira Sabir Allah yayi taimako yana gidansu data faɗa masa shi kuma ya faɗawa mahaifiyarsa suka taho tare , ganin Jalilah a durƙushe shi kuma yaron na gefe yana kuka yasa mahaifiyar Sabir ta ɗauka ko Jalilah ta suma ne , taɓota tayi taga ta kalleta tace "masha Allah nan ta ɗauko reza ta fara yanke cibi da saurans.. ta haɗawa Jalilah ruwan wanka taje ta gasa jikinta shima yaron aka gyarashi , da ka kalli yaron zakaga yafi Imaam kyau sosai ranar suna yaci suna Munim ,tun da akayi suna bayan tafiya maman Sabir daga gidansu yaron ya dena samun kulawa ta ɓangarenta , Imaam ko kullum cikin shigar kaya masu kyau yake , wanan abu yana damun Sabir har Munim yakai zama bata daina nuna musu ban banci ba haka Imaam ya taso babu soyayyar ɗan uwansa a ransa , lokacin da Munim ya fara rarrafe ɓarna kamar me daya taɓa kayanta zata bige masa hannu har Allah ya rayasa ya fara tafiya da gudu ko ina , daga ƙarshe ma Sabir ne ya koma siya masa duk wani abu da aka siyawa Imaam gudun kar ya gano uwarshi bata sonsa ,dayake yaro ne mai wayo ya riga da ya gano ba sonsa take ba , a lokacin da Munim ya kai shekara biyu shi kuma Imaam yana da shekara goma sha biyu a duniya ,Sabir da kansa yake kaisu makaranta a hanya yayi ta yiwa Imaam faɗa akan yaso ɗan uwansa ,kasancewar huɗubar uwa yafi shiga yasa maganar mahaifinsa ya tafi a iska yake bin na uwarsa .
***********
Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah Imaam nada shekara ashirin a duniya shi kuma Munim yana da shekara g takwas , ya fara sanin duniya idan yana da damuwa mahaifinsa yake gayawa baya tunkarar mahaifiyarsa , wata rana ranar Asabar da safe aka aiko wa Sabir da saƙon mutuwar iyayensa duka biyu sakamakon hatsarin mota da sukayi suka rasu , Sabir yayi kuka sosai har akayi arba'in idan ya tuno da iyayensa sai yayi kuka , ranar da akayi kwana sittin da rasuwar iyayenshi suka koma DUBAI da zama , har Imaam ya kai shekaru talatin a duniya mamansu Jalilah bata daina nuna musu ban banci ba , ranar juma'a da yamma Sabir ya kanta rashin lafiya tari mai tsanani sunyi yawon asibitin har sun gaji washe gari da safe rai yayi halinsa , Jalilah tayi kuka sosai kasancewar itama nata iyayen sun rasu ,mai makon ta rungumi ƴaƴanta sai taƙi taci gaba da nuna musu waraki har Allah ya haɗa Imaam da Mommah wato Khadija , sunsha soyayya daga nan akayi maganar aure babu binciken dangi kasancewar Jalilah ta kama safarar kayayyaki tana kaiwa garuruwa , maganar auren Imaam da Khadija tayi ƙwari sosai ,Jalilah tayiwa wani maƙocinta magana akan ya taimaka ya kaiwa iyayen Khadija kuɗin aure , ba musu ya karɓa ya kira abokinsa suka tafi , a ranar aka sanya ranar biki wata ɗaya , suka dawowa da Jaliliah labarin ranar bikin tayi farinciki sosai , shiko Munim kullum cikin neman abinda zai samu yake wato sana'a duk inda yaje zai yi aiki sai a koresa ya rasa dalili gashi kusan kullum wuni yake da yunwa ,har ya fara tantamar anya Jalilah ba satoshi tayi a asibiti ba dan yana ganin kamar ba mahaifiyarshi bace , rana bata ƙarya inji hausawa wai sai dai uwar ɗiya taji kunya.
Yau ya kama ɗaurin auran Khadija da Imaam ansha kyau da hotuna Munim kam baya ma ɗokin komai kayan kirki dazai sanya bashi dasu dan haka ya tafi yawonsa , watan satin amarya Khadija biyu ta sami ciki ta fara laulayi , sune wanan asibiti wancan asibiti , har Allah ya raya cikin ya isa aihuwa ta haifi yaronta ƙato Asim shekara ɗaya da aihuwar Asim ta sami cikin Abid , ana gobe suna Jalilah ta kwanta rashin lafiya , takai wata ɗaya tana ciwo asibiti sunce basuga abin daje damunta ba ,da asubha ta tashi da shaƙuwa Imaam da Khadija dake zaune a gurinta sun tsorata da yanayin jikin nata sosai sbda jikin yayi tsanani , suna zaune likita ya shigo yana ganin Jalilah ya girgiza kai tare da rufe mata fuska yace "kuyi haƙuri "kuka Imaam ya fara yana cewa "kece gatana idan kika tafi bani da kowa , yana ta sumbatu Khadija ta riƙeshi har aka fita da gawar Jalilah Imaam na kuka kamar ƙaramin yaro aka wuce da ita gidanta mutanen anguwa sukayi mata wanka an sanyata a makara za'a kaita kenan Munim ya dawo daga yawonsa yaga gawar jalilah ana mata sallah , Allah yayi miki rahama ya faɗa a fili ya shige gida , bayan an kaita an dawo Munim na zaune Imaam ya shigo ya gansa a takure ,cikin kakkausar murya Imaam yace "uban mai kazo yi ka fice ai ba gidanku bane "dariya Munim yayi yace "to nunamin gidan mu "lokacin da Imaam ya binciko wata jaka ta Jalilah wacce take cike da kuɗi ya firgita a take a gurin ya bugawa Munim ƙarfe a kansa ,ya fice da jakar kuɗin bai zarce ko ina ba sai gidansu ,ya nunawa Khadija cikin kissa ta rabashi da rabin kuɗinnan yasan dai ya siya musu gida amma ragowar ta sace haka kuma yake zaune da ita .
Kwanci tashi babu wuya Abid yayi wayo yanada shekara biyu Khadija ta sami cikin Pooja -Pooja nada shekara uku aka sami cikin Nisha , daga nan aihuwa ta tsaya musu...!
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: 23-24

Yana yana tsaye da biron a hannunsa har Ummi ta shigo ranta a ɓace tace "wlh ko ka saketa ko in saɓa maka "cikin sauri ya ɗora hannunsa kan takarɗar dake shimfiɗe kan table ya rubuta ni Ammar na saki Nisha saki ɗaya ,har yana hawaye ya duƙunƙune takardar yaba Nisha ya fice da sauri , mirmishi Ummi tayi ta shiga bedroom ɗin Nisha ta wurgo mata akwatinta kasancewar ba'a kawo kayan auran ba tace "masiyaciya kibar mana gida auranki ya janyo dalilin tarwtsewar fatincikin mu tabbas nayi nadama "Nisha na kuka ta miƙe ta ɗauki akwatin tare da raɓawa ta gefen Ummi zata wuce Ummi ta jawota tace "ko kayan ɗakin nakine ?girgiza kai Nisha tayi alamar a'a ta dawo da baya ta ɗauki mayafinta dake kan sofa ta fice tare da durƙusawa ta ɗauki akwatinta , tunowa tayi da kuɗin da Hajiya ta bata yana nan a palo dan haka ta faki idon Ummi ta ɗibe ta fice ,
Tana fita ta sami mai mota kasancewar Pooja tayi mata kwatancen gidan nasu , suna isowa ta biya mai mota kuɗinsa ta tsaya a bakin get ɗin tana saƙe - saƙe a zuciyarta ,a fili tace "ko waye yaba Mommah kuɗin siyan danƙareren gida irin wanan oho "ta fara nocking mamaki ne ya isheta gidan harda mai gadi bata gama ruɗewa ba sai da aka buɗe mata ta shiga ciki tsayawa kallo tayi tana mamakin inda su Imaam suka sami kuɗi haka , turo door ɗin palon tayi tare da sallama ta tarar da Imaam da Pooja da Mommah zaune suna kallo , da gudu ta isa gurin Imaam tana dariya tace "Imaam ko kazo gidan ? murmishi mahaifin nata yayi kana yace "afuwan ƴar albarka zanzo ba yanzu ba .
Mommah dake washe baki tace "kaga Hajiya Nisha ikon Allah" Pooja kam kama hannunta tayi suka nufi bedroom ɗinta ,suna shiga suka zube kan gado Pooja tace "wato shine kika turomin faɗan da mahaifiyar Ammar take yi miki ta whtsapp ko ? murmishi Nisha tayi ta buɗe takardar da Ammar yayi mata saki ta rungume tare da miƙawa Pooja , karɓa Pooja tayi kana tace "saki ɗaya fa yayi ?"eh man ai yanzu dai naji daɗi "Nisha ta faɗa tana dariya , Pooja ce tace "kinko sanya masa maganin ? eh nasa amma ni banga yayi komai ba "Nisha ta faɗa tana son jin maganin meye Pooja ta bata , Pooja zata ƙara magana sukaji sallamar Mommah da ƴar fara'arta tace "na ganki da ɗan aiwati kwana zakiyi ne ?eh Nisha tace "kana ta ɗanyi murmishi tace "Ammar ɗin yaje " Singapore "to Allah ya dawo dashi lafiya "Mommah ta faɗa , suka amsa da amin.
Har ta fita ta dawo tace "ƴar albarka mai kikeso a dafa miki ? duk dan Mommah ta basu guri suyi hira yasa ta cewa "kome kika dafa Mommah zanci "Mommah ta fice jiki na rawa ,Nisha ta kari Pooja tayi rau rau da ido sai kuma tace "anty Pooja kina ganin idan Mommah taji gaskiyar abin da ya faru bazamu shiga tashin hankali ba ?tsaki Pooja tayi kana tace "tunda an ƙetare waccar gadar saura ragowa dole ki shiryawa koma menene "ywwa anty Pooja inada tambaya "Nisha tace "tana dariya "naga kun koma gidan ƴan gayu ne waye yayi muku sabil ?"gaban Pooja ne ya faɗa tana gudun tace "motarta aka siyar a sami matsala amma dole zata gaya mata gaskiyar zance ,my lil sis ?"na'am Nisha tace "tana kallon Pooja "Mommah ta siyar miki da motar da akayi miki kyauta a kayan aure "murmishi Nisha tayi ba tare da nuna damuwa ba tace "dashi ne akasi wanan gidan ?"eh man Pooja tace "tana rungumota Pooja ta fashe da kuka ,can kuma tayi shiru .
Mommah dake kitchen yau da kanta take haɗawa Nisha abinci mai rai da lafiya bayan ta gama ta jerashi da juice a dogon tirai ta kawo dining ta ajiye kana taje ta kira Nisha , tasowa Nisha da Pooja sukayi a tare sunata hirarasu lokacin Imaam ya fice ,har dare yayi suna hirar duniya sai da ɗaya tayi bacci sanan sukayi shiru.
Washe Ammar na zaune a ɗakinsa abin duniya ya damesa musamman da idan yaje part ɗin Nisha yaga wayam sai ya dawo nasa part ɗin da kuka .
Yau satin Mheera Uku ,da safe ta tashi da amai kamar zata amayar da ƴa ƴan cikinta ,kasancewar Ummi na ɗakinta ko jinta batayi ba ,sai da tayi amai sau uku ta wanke fuska ta dawo ta kwanta , har bacci ya fara ɗaukarts Ummi ta shigo riƙe da shayi a hannu ta tama jikinta taji yayi zafi sosai , family doctorn su ta kira cikin ƙan ƙanin lokaci sai gashi yazo Ummi tayi masa iso zuwa ɗakin Mheera ya shiga tare da zama a palo Ummi ta ɗagota ta riƙe mata hannu suka taho palon , zaunar da ita Ummi tayi suka gaisa da doctorn ya tambayi meke damunta "wlh ban sani ba Ummi tace tana dai yawan zafin jiki sosai "kodai maleriar tata ce ?doctor yace "yana fitoda abin gwaji ,miƙawa Ummi yayi yace "tayi fitsari a nan ta kawo mu gani "gaban Ummi ne ya bada rass tunowa da aika aikan da Ammar yayi ta ƙarɓa jiki a sanyaye ta riƙe hannun Mheeera suka wuce bedroom ta shiga toilet tayi fitsarin , bayan ta gama Ummi ta sake riƙeta suka dawo palo ta miƙawa doctor robar suka zauna , abin gwaji yasa yaɗan jima can anjima ya ciro ganin abin ya zana layi biyu ya sashi dubawa da sauri ya ajiye wanan ya kuma buɗe sabo ,shima layi biyu ya nuna a firgice doctor ya ɗago kai yace "ciki fa!! "ciki !! Ummi tace "ido a waje kamar zai faɗo lokaci ɗaya hawaye suka fara zarya a fuskarta tace "innalilahi wa'innaɗihairraji'un wanan wacce irin rayuwace ?doctor yace "ke Mheera a ina kikayi ciki ?"amai ne ya taso mata da gudu ta koma bedroom ɗinta ta faɗa toilet ta ɗinga kwararawa sai da ta gama ta buɗe famfo ta kora sanan ta dawo kan gado ta kwanta sam taƙi komawa palo .
Ummi da tagaji da jiran dawowar Mheera a zuciyarta tace "kota dawo ma me zata ce barin samu in rufe bakin doctor "doctor ina zuwa "Ummi tace "tare da miƙewa ta fice kai tsaye bedroom ɗinta ta wuce ta buɗe bed side drower ɗinta ta ciro kuɗi masu yawan gaske ta dawo gurin doctor tace "idan har ka rufamin asiri ka zubar da wanan cikin zan baka wanan ƙuɗin "washe baki doctor yayi kana yace "hajiya ai mun saba kashe wanan case ɗin babu damuwa tazo muje "ɗakin Mheera Ummi ta shiga ta sanya mata hijab tare da ɗauko wayar Mheeran ta ruƙo hannunta suka fito , a motar doctorn suka wuce kai tsaye hospital ɗin da yake aiki suka nufa , suna isa yayi parking suka fito tare da ce musu su shiga shi zai duba abu a office yazo ,nuna musu wani ɗaki akayi kamar na tiyata Ummi ta shigar da Mheera suka zauna suna jiran isowar doctor , bai ɗau lokuta masu yawa ba sai gashi ya shigo hannunsa riƙe da wani abu da magunguna cewa "yayi Hajiya bari a ƙara yin gwajin nan mugani anya cikine kuwa ?"zuba masa ido Ummi tayi yayi gwajin cikin ikon Allah yaga yanka ɗaya ,a firgice ya miƙe tare da cewa "na koma kamar zautacce "ɗazu fa naga ciki yanzu ya nuna babu "ɗaga hannu sama Ummi tayi harsa hawayen farinciki a haka sukabar asibitin bayan an haɗa mata maganin zazzaɓi , a motar su ta komawa kasancear doctor ne ya kawosu bakin Ummi baya rufuwa .
Washe gari Nisha ta fito dama tace "wa Mommah zataje anguwa Mommah tayi mata Allah ya tsare , kai tsaye mota ta hau tare da faɗar inda zai kaita ,sunyi tafiya mai nisa sanan suka iso gurin bolar da mahaukacinnan yake zama....!

Afuwan babu yawa
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: 25-26
Kuɗi ta ciro ta miƙawa mai motar kana ta fito tare da dube dube abda bata gansa a inda ta saba ganinsa ba , guri ta samu ta zauna tare da zuba tagumi tana nazarin ta ina zata fara nemansa , lokaci nata tafiya har yamma tayi babu shi babu alamarsa ta miƙe tare da share hawayen fuskarta ta kuma tarar mota ta shiga , suna barin gurin shi kuma yazo ya zauna yana tunanin inda zai bi ya haɗu da abokiyarsa , tana cikin mota tana nata tunanin har aka wuce get ɗin gidansu kasancewar gidan a bakin titi yake , kuɗi ta miƙawa mai mota ta shige gida ,tana shiga ta samu Pooja bata nan taje kitso sai Mommah ita ɗaya da ƴan aiki dama samarin gidan hutunsu ya ƙare sun koma makaranta , faɗawa jikin Mommah Nisha tayi tare da cewa "na gaji Mommah "murmishi Mommah tayi kana tace "to sannu ya kika samesu ?"suna lpy Nisha tace "tare da cire mayafin kanta tace "ina anty Pooja ?"taje kitso "Mommah ta bata amsa , har ta miƙe zata wuce bedroom ɗinsu taji Mommah ta kira sunanta , gabanta na faɗuwa tace "na'am "naga kuɗaɗe masu yawa a jakarki mai zaki siya ?"ajiyar zuciya Nisha tayi dan ta ɗauka Mommah ta gano auranta ya mutu ne tace "lahh Mommah ai kakar Ammar ce tayimin kyautarsu "washe haƙora Mommah tayi kana tace "aiko ki kawo a adana miki inba haka ba zaki gantalar dasu "no Mommah akwai uzurin da zanyi dashi "Nisha ta faɗa tana wucewa "dan batason ƙara jin wata shawarar tasani sarai Mommah na son karɓar kuɗin ne tayi wasu uzuri dasu , Nisha na tafiya Mommah tayi tsaki kana tace "wayon tsiya yayi miki yawa aiko sai na ɗibi wani abun dan ana bina bashi .
Zaune Abba yake a gaban boka ,boka ya gama surutansa na tsafi kana yace "mun cire ciki kuma jininka ne yanzu saura ɗaya , dazarar mun samu tabbas ka haye kujerar mulki an gama washe baki Abba yayi kana yace "Boka babu matsala shima za'a samu "Abba ya miƙe tare da yiwa Boka sai anjima kasancewar Bashir baya nan da kansa yazo yasa shi surutai a mota yana cewa "tabbas nayi dabara da na haɗa auran Ammar da yarinyar Imaam dama dalilin da yasa bana son auran shine babu wanda yasan inda ƴan uwnsa suke wanan shine dalili , amma indai har zata dinga samo min biyan buƙata ta ai shikenan "Abba ya cigaba da tuƙi yana dariya.
Mheera taji sauƙi sosai kasancewar yanzu ta daina jin laulayin ,kuma jikinta yayi ƙarfi ,taci kwalliya ta fito sanye da sari mai ruwan madara sai takalminta baƙi da mayafins ,bakin nan yasha janbaki tayi kyau sosai tazo gurin Ummi tace "Ummi ni yau gidan Hajiya zani kuma sati ɗaya zanyi "to Allah ya tsare dama Hajiya tace

11 / 18