Author : Zainab Habib Category : Romance
color ya matuƙar haska ƙafar kasancewarsa mai tsini , pink ɗin riga ce a jikinta sai skel mai ruwan ƙwai ta janyo skel ɗin saman cikinta kanta na sanye da hula baƙa kafaɗarta kuwa wani yalolon mayafi ne wanda tayi matuƙar ƙarawa shigar tata kyau ɗayar kafaɗar kuma hand bag ɗinta ce ƴar ƙarama a rataye , sai babbar wayarta dake hannunta ,cikin rawar kai ta ƙaraso tare da cewa "aslamu alaikum "Abid da sai yanzu ya ɗaugo yaga wacce ta shigo yace "Zeena "waro masa manyan idanuwanta tayi kana tace "abokina ya garin ya shirye shiryen kammala makaranta ?"zauna Abid yace "ba tare da ya bata amsa ba ,zama tayi nesa dashi tace "nazo muyi wata magana ne "Asim dake kitchen ya gama girki amma tsabar son yaji gulma ya tsaya harda neman gurin zama
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: 39-40
Zeena tace "Abid ina son ka bani aron hankalinka "a kai kaice Abid ya kalleta yace "nabaki kuma ina jinki "fararen idanuwanta da kafesa dasu tare da cewa "ina sonka! wanan kalmar ta daki Abid sbda bai ma kawo wanan abin ya kawota ba , shiko Asim dariya yasa tare da toshe baki "tun time ɗin da kuka zo india karatu da nayi ido biyu da kai nake jin soyayyarka a raina ,nasani zakayi mamaki dan nace ina sonka amma ba abin mamaki bane idan kana son mutum ka faɗa masa ni a ganina "ta ƙarashe maganar tare da cewa "kaina zaɓin raina ina sonka Abid "ajiyar zuciya Abid ya sauke kana yace " naji amma ki sani a tarihin rayiwata bana sha'awar zama india sam "ko me yasa ?"Zeena ta tambayesa , kawai "Abid yace "shigowa Asim yayi tare da tafa hannunsa yace "new life wlh kin burgeni Zeena nima ina maraba da wanan soyayyar "hararsa Abid yayi kana yace "kai kuma waye yace "kazo ?"dariya Asim yayi yace "ana so ana kaiwa kasuwa "Zeena da ta miƙe tare da cewa "Abid ni na tafi ina yi maka fatan alkairi a rayuwarka ina fatan ko baka sona zamu iya zama abokai ?"no problem"Abid yace "Zeena ta fice , tashi Abid yayi shima ya fice bai saurari Asim ba, ƙwala mata kira yayi ,Zeena data fara tafiya ta tsaya ba tare da ta waigo ba , kallon zubun halittarta ya fara doguwa ce ,ɗƴar india amma ba musulma ce shi kuma Abid larabawa ne musulmi.
Takowa yayi har gabanta yace "Zeena inaso ki sani aure nufi ne na Allah idan har zaki musulunta ni kuma zan aureki "dum dum gaban Zeena ya bada sbda a zahiri idan da abin da mahaifinta Mr Robat ya tsana bai wuce musulunci ba har danginta kuma ita tana jin akan Abid zata iya rabuwa da kowa , kuka ta fashe dashi bayan ta dawo daga duniyar tunanin data tafi tace "Abid ina matuƙar sonka badan komai ba , babu macen da zata ganka ta ƙyaleka dalili kuwa shine kana da kyau cikar zati kai komai naka mai kyaune "kema haka ai "Abid ya faɗa yana kashe mata ido , wasu mutane ne suka iso gurin cikin harshen india sukace "me kikeyi a nan waye wanan zatayi magana wani daga cikinsu yana da ƙaton ciki ya ɗauke Abid da mari tare da naushin sa a ciki , ihu Zeena take kamar zata fiddo maƙogwaron ta amma basu saurareta ba suka riƙe mats hannu tare da sanyata cikin wata rantsatsiyar mota mai tsadar gaske , Asim dake zaune yana cin abinci kasancewar tunda yaga Abid ya fita yayi zaton ba yanzu zai dawo ba ya fara cin abinci.
Yana cikin ci ne yaji ihu a fili yace "wanan muryar kamar ta Abid ya miƙe tare da ficewa da sauri ,ya hango Abid kwance riƙe da ciki ,da sauri Asim ya ƙarasa ya tallafosa tare da taimaka masa ya shigo dashi ɗakinsu ya kwantar kan kujera yana cewa "lafiya kuwa mai ya faru ?"amsa ɗaya Abid ya iya bawa Asim shine mutanen Robat ne "waro ido Asim yayi kana yace "wlh gobe da wuri zamu bar garin nan tabbas idan ba haka ba zasu iya illataka ".
Zeena dake cikin mota sai kuka take tana cewa "note ɗina zan karɓa a gurinsa shine kuke son ku kashesa ko ?"jin anyi parking a kyakkyawan gidan nasu wanda faɗar kyawunsa zai iya zama ɓata lokaci sai dai mai karatu ya ƙaddara kyan gidannan ya isu , buɗe mata kofar motar akayi ta fito da hand bag ɗinta a rataye ta nufi cikin gidan , kai tsaye saman bene ta haura tana cewa "Mam-Mama, wacce aka kira da mama ta fito tana sanye da doguwar riga fara mai kyau tazo ta rungume Zeena ta shafi fuskarta tace "yau kuma me ya faru naga hawaye a fuskarki ?"ƙara fashewa da kuka Zeena tayi kana tace "Mama nike nan bazanyi rayuwar farinciki ba ?sam hakan bai dace ba note nake karɓa a gurin wani abokina shine su Papu suka zo suka turani a mota tare da yi masa duka "ta ƙarashe zancen tana kuka "kiyi shiru ƴata mahaifinki ne ya basu damar yin hakan kije ki huta "Zeena na bubuga ƙafa ta wuce haɗaɗen bedroom ɗinta ta faɗa bed tare da fashewa da kuka a karo na uku a fiki tace "dole sai nayi soyayya da Karam nace bana sonsa anbi an takura min "a ban bacci ya kwasheta .
Washe gari sai ƙarfe goma Zeena ta tashi daga bacci tayi wanka ta gyara gashinta kana ta gyara fuskarta da simple makeup tare da buɗe driwer ta ciro wata jar riga iya guwai wa da takalmi fari da jakarsa ta sanya ɗan kunne da sarka da zobensa ta sauko ƙasa ,Robat da Mama suna zaune a palo gefe kuma Karam ne ya haɗe cikin riga da wando wanda sukayi masa kyau sosai ,hararsa ta gefen ido Zeena tayi kana ta gaishe da iyayenta taje kusa da mahaifinta ta zauna ,shafa kanta Robat yayi tare da cewa "ƴata baki ga Karam bane ?na gansa Baba "Zeena ta faɗa tare da ƙara hararar Karam a kai kaice , miƙewa Karam yayi ya fita Robat yace "maza ki bishi shine mijin dana zaɓa miki tun kuna yara "da ko ƙara kallon mahaifin nata batayi ba suka haɗa ido da Mama -Mama ta ɗan harareta ta miƙe tare da fucewa "tasan baya wuce gurin hutawa ,ta isa gurin tana karai raya da murmushi taje har inda yake tsaye , ya ɗauka ta sauya ƙuduri ne har da rungumota yana shin shinar gashin kanta ma'abocin ƙamshi yace "haba Zeena haka nakeso mu rayu cikin farinciki "wani shu'umin murmishi tayi tare da tofe fuskarsa da miyau tace "na faɗa maka bana sonka ko ana so dole ne ?"dunƙule hannu Karam yayi ko me ya tuna sai ya sake hannun nasa yana mai cewa "dole sai na aureki ko mahaifinki bai isa ya hana ba "duk kuɗinsa duk wani girma nasa a idon mutane ki sani mahaifina yana da ikon hana komai a ƙasar , farr Zeena tayi masa da dara daran fararen idanunta tace "ko duniya mahaifinka ya tara ni babu ruwana nace bana sonk bana sonka "waro ido Karam yayi tare da cewa "thnks yayi "ya fice ya bar gurin ,kai tsaye gurin Robat dake zaune a palo ya nufa ya wuce mama yaje har gaban mahaifin Zeena yace "tace "bata sona kuma wlh sai na aureta sai na aureta "jikin Robat na rawa yace "ka kwantar da hankalinka a satin nan za'a ɗaura auranku "Karam yasa dariya tare da ficewa yabar gidan, Mama dake zaune ranta a ɓace ta dubi Robat tace "wai mai yasa kake nuna kafijin tsoron su akan farincikin ƴarka "dakatar da ita Robat yayi tare da cewa "ki tsaya a haka "tagumi Mama tayi tare da tashi tabar palon ,Zeena na shigowa idonta cike da hawaye tace "haba Baba mai nayi muku kuke ƙoƙarin rabani da farinciki ni nace bana sonsa bana sonsa ko ana so dole ne ?"marin ta Robat yayi tare da cewa"wanan kalmar ta tsaya a iya nan sbda idan ya fito waje har mai girma MINISTER yaji labari zan iya kasheki "kisa ?Zeena tace "jikinta na rawa ta fashe da kuka cikin zafin rai tace "Baba yanzu har akwai abin da zai sanya ka rabu dani akan wani can wanda ba ɗan uwanka ba !kullum kana cewa "nice rayuwarka nice rayuwarka Amma ko kaɗan baka gwadamin so".
Ta fice a palon ta nufi ɗakinta ta fara haɗa kaya , har ta cika akwati babba da kaya sai ga Mama ta shigo tace "Zeena mai kikeyi haka ?"Mama bakwaso na bakwa son farinciki na gara in mutu kawai ko inje mota ta kaɗeni "waro ido Mama tayi tare da ƙarasowa da sauri ta riƙe hannun Zeena kana tace "akwai wani SIRRI a tsakanin mahaifinki da mahaifin Karam wato Minister , wanan sirrin ba kowa ya sanshi ba sai ni da mahaifinki da kuma miinister ko shi kansa Karam bai sani ba"...!
Koda Asim ya kawo Abid ya kwantar ya tafi chemist ya siyo masa magani ya ɓallo ya basa tare da yi masa sannu "cikin murya irin na wanda yaji wuya yace "Asim samin wayata a caji gobe da safe zamu tafi tunda yau mun gama karɓar komai "miƙewa Asim yayi yasa masa wayar , washe gari da asbha kasancewar jikin Abid yayi sauƙi sosai yasa su shiryawa suka fito tare da zuwa tashar jirgin ƙasa sai DUBAI , sunyi tafiya mai nisa amma cikin ikon Allah sai gasu a Dubai ,bayan kowa ya sauka suma su Abid suka fito tare da tarar mota zuwa gidansu kasancewar Pooja ta turo musu da adreshin inda suka koma , bayan sun sauka suka kalli get ɗin gidan Asim yace "anya kuwa nan ne ?Abid yace "eh man gashi lambar gidan ma "to haya su Mommah suka kama ko kuma a ina suka ma sami kuɗin wanan fitinannen gidan ?"tuntsurewa da dariya Abid yayi tare da cewa "koma dai mene ne tare fa muka zo amma kake tambayata "Asim ya sosa kai yace "sorry "sukayi nocking aka buɗe musu suka shiga , da shigarsu suka hango Nisha a harabar gidan tana waya suna haɗa ido dashi taje da gudu ta rungumeshi tana oyoyo my lovly bro "kinfa girma amrya naga kin rame ne "dariya Nisha tasa kana tace "kai kuma kayi ƙiba "Asim yace "bakuda aikin yi nikam na shiga ciki "da shigarsa yaci karo da Mommah tana sanye da doguwar riga milk color mai duwatsu tayi kyau sosai tayi ƙiba yaje da sauri ya rungume Mommah tare da cewa "munyi kewarku Mommah "itama Mommahn rungumesa tayi tace "nima haka yarana "Pooja da ta fito hannunta riƙe da wayarta ta ƙaraso da gudu tana cewa "oyoyo brothers "su Abid suka sanya dariya cike da farinciki sukace "to ina ne part ɗin mu ?"Asim ya tambaya yana dariya "Pooja dake tsaye ta ruƙo hannunsa tace "bro gashi can muje "suka tafi ta nuna musu haɗaɗɗen ɗaki kowa da nasa kuma komai nasu iri ɗaya , cikin farinciki Asim ya ƙwalawa Abid kira yace "bro ya kaga gidannan amma dole mu tammbayi Imaam koya ka gani ? yes tabbs "suka tafa.
Washe gari Hajiya nayi sallahar Asbha ta zari hijab ɗinta tare da cewa"yau sai gidan su Nisha koo zamu kwana a hanya sai na nemo gidan "ƙwalawa driver kira tayi yana zuwa tace "gidan Umar zaka kaini "to an gama ya durƙusa yace "Hajiya barka da safiya "ywaa maza ɗauko mukulli mu wuce "to Hajiya driver yace "tare da zuwa tada mota hajiya ta fito , kai tsaye motar ta shiga tare cewa "jani a hankali "suka ɗauki hanyar zuwa gidan su Ummi , cikin ikon rabbi suka iso driver yayi horn aka buɗe suka shige ana parking Hajiya ta fito tare da tambayar ƴan aikin "Ammar yana nan?"eh yana ciki ƴan aikin sukace ya ƙarasa side ɗinsa babu sallama ta tura ƙofa , ganin Ammar tayi tsaye dagashi sai gajeren wando da kwalbar beer a hannunsa , waro ido Hajiya tayi tace "ya subhanallah mai zan gani ?.
"Barka da zuwa matata Nisha da fatan kin iso lafiya yaje da sauri zai kaiwa Hajiya hugg ta kauce tana rafka salati tare da cewa "ni jikar mutum biyu ace ni Ammar zaka runguma kana cemin wai Nisha...!
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: 41-42
Ci gaba da dosota yayi Hajiya taga babu sarki sai Allah ta zuba da gudu tare da cewa "ɗan jakar uba ai ko banyi niya ba naje in nomo maka matarka kan ka hallakani "ta fice da gudu tana kiran driver -driver da yaji kiran Hajiya ya rugo da gudu tare da cewa "Hajjaju gani "maza kawo mota yau zamu koma neman wanan gidan "Hajiya ta faɗa tana gyara ɗaurin zaninta , da sauri yaje ya ɗauko mota tare da buɗewa Hajiya suka fice , suna tafe a mota tana ta jinjina halin da taga Ammar cikin zuciyarta tace "yaushe Ammar ya fara shan giya na shiga uku ni uwale "ta rafka tagumi ,driver yaga tafiya taƙi ƙarewa yace "Hajiya wace anguwar zamubi ne ?"nuni Hajiya tayi masa da hannu tare da cewa "tsohon gidan nasu zamu kuma zuwa muyi tambaya" to driver yace "sukaci gaba da tafiya har suka iso anguwar , parking yayi a gefen hanya ya fito tare da tambayar gidan da su Imaam suka koma ,wani mutumi ne yayi musu kwatance har da lambar gidan ya basu , suka miƙi hanya cikin ikon Allah sai gasu a anguwar , Hajiya ce ta tsaya ƙarewa gidan kallo a fili tace "yaushe Imaam yayi kuɗi ?"da har ya ƙera wanan katafaren gida ko nawa ma albarka "ta riƙe haɓarta suka fara nocking , mai gadi ne yazo ya buɗe tare da tambayar daga ina suke ?Hajiya dake gyara mayafi tace "kabarmu mu shiga inyaso sai ka biyomu daga baya "mai gadi ya kafe akan sai Hajiya sun faɗi daga inda suka fito ,Hajiya ta bangaje shi ta shige gidan tare da ɗaga murya tace "salamu alaikum "wlkslm taji muryoyi an amsa ta buɗe door ɗin palon tare da cewa "kunyi baƙi "Mommah ta fito da gudu sabda ta gane Hajiya tace " barka da zuwa Hajiya bismillah ki zauna "Hajiya ta zauna tare da cewa "ina Nisha ne ? Mommah tayi murmishi tare da ƙwakawa Nisha kira tace "Hajiya tazo maza kizo ku gaisa "da sauri Nisha ta fito tare da zubewa gabab Hajiya tace "barka da zuwa ya gida ?"lpy lau Hajiya tace "kana tace "zauna man" bayan Nisha ta zauna Pooja ta iso gurin hannunta riƙe da babban faranti dake cike da kayan motsa baki ta direshi gaban Hajiya a kan table , ta gaisheta tare da wucewa ,Hajiya ta ɗauki Apple ta gutsura kana ta ajiye tare da cewa "gaskiya banji daɗi abin da Ammar ya yiwa Nisha ba "sbda Nisha yarinya ce mai hankali ga nutsuwa amma Ammar yayi haka ? Mommah da bata gane inda Hajiya ta dosa ba ta katse Hajiya ta hanyar cewa "wai meke faruwa ne Hajiya ?kuka Hajiya ta fashe dashi tare da cewa "Ammar mana da ya saki Nisha "idon Mommah a kafe ta dafe ƙirji Hajiya nata magana ina Mommah babu nunfashi...!
Dan Allah kuyimin haƙuri plx 👏nasan yayi kaɗan
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: 43-44
"Yah sunbahanallah" Hajiya ta ambata tare da miƙewa da gudu ta buɗe firdge ɗin dake gefensu ta ɗauko ruwan gora ta kwarara wa Mommah ,Nisha kam da biyu taƙi tashi ɗauko ruwa sbda kar Mommah ta farka ta zartar da mumunan hukunci a kanta.
Watsa mata ruwan Hajiya ta farayi tashi ɗaya Mommah ta nunfasa tare da sauke ajiyar zuciya tace "alhmdulilh "Hajiya ce tace "sannu Mommah tace "ywwa " Mommah tace "ina jinki Hajiya kikace Ammar ya saki Nisha ?"eh tabbas amma fa ba asan ransa akayi sakin nan ba uwarsa ce tasa "Mommah ta zaro ido tare da cewa "abin da Ummi zatamin kenan ? "Hajiya tace "nidai yanzu ina roƙon alfarmar kubar Nisha ta koma Ammar yace "ya mayar da ita tun kafin mu gano gidanan "sallamar Imaam ce ta katse musu maganar da sukeyi Hajiya tace "ywwa Imaam dama ina son ganinka in baku haƙuri dukkan ku har ita Nishan dan Allah kuyi haƙuri "Imaam da bai san inda maganar ta Hajiya ta dosa ba yace "wani abun akayi Hajiya ?"Mommah tace "ashe Ammar ya saki Nisha ne bamu sani ba "zaro ido Imaam yayi kana yace "amma shine kullum ta dinga cewa yaje aiki ne ?"Imaam ya jinjina kai sbda abin ya mugun bashi mamaki ,Hajiya tace "nidai ina mai ƙara baku haƙuri "Imaam yace "tabbas sai dai Ammar yazo da kansa ya faɗa muji "Hajiya ta riƙe baki tare da cewa "kana nufin ni zanyi maka ƙarya ne ?"Mommah dake zaune tace "ai ni a ganina Imaam tunda yace "ya mayar da ita to sai su koma "keee dakata "Imaam ya dakawa Mommah tsawa tare da cewa "aure fa ba abin wasa ba kin ɗaukeshi wasa ko ?hararasa Mommah tayi tare da turo baki , Hajiya ta miƙe tare da cewa "bara inje in turo Ammar ɗin yazo da kansa "Imaam yace "da dai yafi "Hajiya ta miƙe jiki babu ƙwari tace "to ni natafi "Mommah ta miƙe tare da bin bayanta ,har sai da ta rakasu bakin get taga tafiyar motarsu sanan ta dawo ciki tana cika tana batsewa "Nisha kam farinciki fal zuciyarta .
Imaam dake zaune yana jiran shigowar Mommah har ya tashi ta shigo ,ya koma ya zauna Nisha na ganin haka ta miƙe tare da komawa bedroom ɗinsu ta sami Pooja na kwance tana kuka , ficewa tayi gudun kar nata kukan yazo ta nufi ɗakin su Abid ,samun Abid tayi yana bacci taje kansa da kuka tana cewa "Yayana ka tashi ka taimakeni "da sauri Abid ya buɗe ido yace "mai ya faru lafiya " Nisha tace "banason komawa gidan Ammar ka taimakeni !Ka taimakeni ! gabansa ya tsananta faɗuwa ga wani gumi dake karyo masa a zuciyarsa yace "my lovely sis yanzu wane irin taimako kikeson inyi miki ?"so nake ka ƙaramin kuɗi akan nawa wanda nakedashi zan bar