Author : Zainab Habib Category : Romance
gado tare da cewa "da alamu yarinyar nan bata soyayya nikuma zan koyar da ita kalar tawa soyayyar"ya kwanta.
Abba da Ummi ne zaune a bedroom Abba na farko Ummi na nesa dashi , miƙewa tayi ta dawo kusa dashi ta dafa kafaɗarsa tace "haba my Governor ya kake min haka ?yaushe rabon da ka bani haƙƙina ? dariya ma ta bashi amma sai ya gimtse yace "inason ki gane nayi miki wani tanadi ne nan da wasu kwanaki har sai na gundureki "murmishi Ummi tayi tace "to shikenan ya wuce ".
Ganin kwanciyar bazata yiwa Ammar ba ya sanyashi kiran Mheera a waya tana ɗagawa yace "my lovely sis maza fito muyi shawara "duba agogo tayi ƙarfe tara na dare kuma bacci takeji tace "bro mu bari sai gobe "no "Ammar yace "ina jiranki " kifa kai tayi a kan bad har bacci ɓarawo ya ɗauketa.
Washegari Ummi ta tashi da tsananin sha'awar mai gidanta kasancewar wani sanyi dake ƙaɗawa ya haifar mata da jin sanyi , miƙewa tayi daga kan sallahyar da take kai ta cire hijab ɗinta tare da cire rigar sallahnta ta sanya kayan bacci riga da wando masu shara shara ta mayar da ƙaton hijab ta nufi bedroom ɗin Abba , zaune ta sameshi yana duba wasu takardu ,tazo gefensa ta zauna tare da cewa "barka da safiya Hubby"murmishi Abba yayi kana yace "ywwa barka ina fatan kin tashi lpy ?"lpy Ummi tace "tana matsowa gareshi shima yana matsawa , ganin yana mata haka ta saki kuka ta fice zuwa nata bedroom ɗin , hamdala Abba yayi kana yace "idan fa tana zuwa min a irin haka wlh komai zai iya faruwa tabbas gara in tattara in koma India "kayansa ya fara haɗawa a ɗan wani madai daicin akwati kana ya shiga wanka ,yana fitowa ya shafa mai ya sanya kayansa ya ɗauki abubuwan buƙata ya fito kai tsaye bedroom ɗin Ummi ya tafi yana shiga ya sameta ta kifa kai har yanzu kukan take , gyaran murya yayi tare da ɗago kanta yace "haba kina abu kamar ƙaramar yarinya ni zan tafi insha Allah ba jimawa zanyi ba munada meeting "ya ajiye mata kuɗaɗe masu yawa , Allah ya kiyaye hanya Ummi tace "ba tare data kallesa ba , sa kai yayi ya fice .
A mota yana ta tunanin rashin adalcin da yayi wa Ummi ,a zahiri kuma yace "bazata gane gata nake yi mata ba sai nan gaba "ko airport basu isa ba yaga kiran Ummi , ɗagawa yayi yana shirin magana Ummi tace "har bikin Ammar ɗin ma baka nan za'ayi ?"kan Abba ya kulle ashe yanada bikin tilon ɗansa yanzu ya zaiyi ?"tsaki yayi ya ajiye wayar Allah yasa Ummi bata jisa ba , wani kiran ne ya ƙara shigowa wanan karon Ammar ne yace "Abba ashe ka tafi bazaka tsaya bikin ba ?"jikin Abba ne yayi sanyi shi a ganinsa da ya saɓa alƙawarin Boka gara yabar garin kawai , Abba yace "my son afuwan kana raina zan dawo ba jimawa zanyi ba ai saura kwana huɗu bikin ni kuma zan dawo nan da kwana uku "to Ammar yace "tare da yiwa Abba fatan nasara Abba ya ajiye wayar .
Tunda Pooja ta fara period bata je islamiya ba yau kwana uku kenan , Nisha ta shirya cikin kayan islamiya tare da kallon Pooja tace "anty Pooja yau zan sanar da Ustaz ɗin mu zanyi aure "zaro ido Pooja tayi kana tace "ke zaki gaya masa ko ?"rufe baki Nisha tayi tare da ficewa da gudu ta ɗauki wayarta dake jone a chaji ta fice bayan ta yiwa Mommah sai ta dawo ,tunda ta fito take ta baza ido a gurin mahaukacin nan tana dube-dube amma bata gansa ba , gabanta ne ya shiga faɗuwa tana cewa "Allah yasa ba wani gurin ya tafi ba "tana ci gaba da tafiya ta hangosa tsaye yana ta dariya point ɗin kumatunsa na loɓawa ta ƙarasa da sauri tana ɗaga masa hannu tare da cewa "abokina "da gudu ya taho yana murmishi , hannu ta haɗa tare da cewa "barka da wanan lokaci "barka kawai yace "mata ya nemi guri ya zauna ita kuma tana tsaye ,kuɗi ta ciro ta bashi kana tace "zan tafi islamiya sai na dawo "murna yake sosai yana ɗaga mata hannu har ta ɓace masa ,bayan taje islamiya an gama biya musu karatu da wa'azi ana tashi ta kuma dawowa gurin abokinta , lokacin da leda a gabansa yana cin gurasa kasancewar da ta bashi kuɗin yana ganin mai gurasa ya siya , zama tayi gefensa ta zuba tagumi tana ƙare masa kallo sosai har ya cinye ya ɗago yana kallonta , ganin lokaci ya ƙure sosai kuma in ba sa'a ba sai an tuhumeta wanan daɗewar da takeyi yasa ta miƙewa tare da cewa "abokina sai gobe "ɗaga mata hannu yayi tare da cewa "na gode a hankali ta tafi .
Tana komawa gida ta samu su Asim da Abid da Imaam sunyi alwalar magrib zasu masallaci , Abid ne yace "ke kuma daga ina kike ?" sosa kai ta hau yi tana in ina Imaam yace "nafa lura dake yanzu bakya dawowa gida da wuri ko lafiya ? nazarin abin da zata faɗa ta fara cikin samun ƙwarin guwai wa tace "Imaam na rasa wanda ya faɗawa malamin mu zanyi aure shine fa kullum sai yayi min wa'azin zaman lafiya "Mommah dake gefe ta washe baki tace "aiko ya kyauta ina yi masa godiya "Nisha ta shige ciki ba tare da ta kulasu ba .
Bikin Nisha saura kwana biyu Mommah baki yaƙi rufuwa murna ba'a magana ƴarta zata auri govenor sai gyara Nisha ake sosai , danginta duk sun hallara kasancewar sunji mijin ,gida ya cika sosai .
Ammar ya kira wayar Abba yakai sau goma amma shiru bai ɗaga ba , kai tsaye ya tafi bedroom ɗin Ummi ba tare da sallama ba ya tura ƙofar ya sameta tana share hawaye , kasancewar ba damuwarshi ne hakan ba yace "Ummi tun ɗazu nake gwada number Abba shiru bai ɗaga ba?"uhm ƙila baya kusa ne "Ummi tace "a taƙaice ,zai kuma magana Ummi ta dakatar dashi shi kuma yayi zuciya ya fice fuuu, yana fita Mheera na shigowa ta kalli Ummi tace "Umm akwai abinda ke damunki "mai kika gani ?"Ummi ta tambayeta "babu komai kawai na tambaya ne "Mheera tace "tana zama kusa da Ummi , kamo hannun Ummi tayi tace "Ummi jibi ɗaurin aure amma Abba bai dawo ba "suna cikin magana sukaji kira a wayar Ummi , cikin sauri Ummi ta ɗaga tare da cewa "ka taho ne ?insha Allah Abba yace "amma ana ɗaura aure zan wuce "badan taji daɗin abin da ya faɗa ba tace "to Abba ne yace "akwai motar da zatazo yau naji su hajiya sunce suna nan tahowa nayi musu bayani "to kawai Ummi ta ƙara cewa "a karo na biyu ya kashe wayar .
Zuwa la'asar ƴan uwan Ummi suka iso dana Abba suma gidan nasu ya cika da jama'a ƴan aiki sai kaiwa da komowa suke .
Lokacin da motar kayan ta iso kai tsaye wa inda suka kawo kayan suka fara aikisu aka nuna musu ɗakin da zasu haɗa kayan , duk da ganin irin wanan samprin ba sabon shiga bane amma ko wacce a cikinsu sai da ta yaba da tsadar kayan da kuma kyansu , su Hajiya komawa babban palo sukayi sai dai a gyara su shiga ba'a aikin komai a gidan cin cin ma bayarwa akayi abinci kuma kawoshi za'ayi daga Hotel da su drinks .
Ummi ce tasa a kira mata Hajiya -Hajiya na zuwa Ummi ta buɗe mata wani ɗaki buɗe baki Hajiya tayi tare da zaro ido tace "duk wanan mai gidan nawa ne yayi ?"Allah ya sanya alkairi "akwatuna ne masu tsadar gaske sunkai guda ashirin kuma ko wanne cike yake da kaya a ɗan ƙaramin har da mukullin mota ,Abba kuma yasa a rubuta idan sun gama cin amarci zasu tafi hajji aka sanya a akwatin .
Washe gari yau saura kwana ɗaya kwanci tashi babu wuya gobe ɗaurin aure har Abba ya iso tun jiya ana ta hidima.
Hajiya ta tashi ƙanwar Abba da yayarsa su kai akwati , sai da akayi motoci biyu sanan suka tafi ,
Mommah na bedroom ɗinta taji ƙarar motoci na shigowa ,ta wundo ta leƙa sai da ta tabbatar na surukanta ne sanan ta rugo palo da gudu tana yiwa ƴar aikin gidan magana akan ta gyara ɗakin Imaam kasancewar gidan daga ɗakinsu Pooja sai nasu Abid da Asim sai na Mommah dana Imaam sai kuma na ƴar aikin gidan guda ɗaya da babban palonsu , cikin sauri ta gyara dama a gyare yake gyaran da tayi kaɗan ne .
Da sallama suka shigo daga ganinsu kasan nera ta zauna duba da kyan fatarsu da irin shigar da sukayi irin ta larabawa ,dama larabawan ne .
Amsawa Mommah tayi tana nuna musu guri bata kaisu ɗakin Imaam ɗin ba , bayan sun gaisa ne suka yi mata bayani daga gidansu Ammar suke ,su Abid da suka shigo yanzu da Asim da drivern daya kawo baƙin suka fara shiga da kaya , ganin anata shigowa da akwatuna yasa Mommah jikinta ya hau tsuma ta shiga kitchen ta kwas musu abinci iri iri ta jere a gabansu , hira suka shigayi kamar ba baƙi ba daga ƙarshe suka ɗan taɓa abin da aka kawo musu suka yiwa Mommah sallama , a irin kuɗin da Ammar ya taɓa bata ta kwaso wasu masu yawa ta basu suna dariya sukace ta barshi ,tayi musu godiya suka wuce.
Koda suka shiga mota suka hau gulmar Mommah suna cewa "wanan zatayi son abin duniya ,amma Ammar ya iya iskanci da zai auro ƴar talakawa sukayi tsayi can kuma suka tuntsure da dariya tare da cewa "matsiyata mu da zamu bata kuɗi shine mu take ɗibo wasu tsummokaran kuɗinta take bamu "basu suka bar magana ba har sai da suka iso gida sanan .
Tsalle Mommah ta doka tana cewa "auran ɗan Governor wajibi ya tabbata "Asim da Abid sukace "yanzu Mommah wanan duk kayan Nisha ne ?"eh man ai ba'a gama ba ma " tana rawa tana basu amsa .
Jin hayaniya a palo Nisha da Pooja suka fito suna cewa "wai lafiya "kafin a basu amsa sukaci karo da akwatuna mamaye a palon , zaro ido Pooja tayi tace "wanan kuma na waye Mommah ?"nuna Pooja Mommah tayi kana tace "na ƴar albarka ne "taɓe baki sukayi a tare Nisha kam jinta tayi kamar wacce akace gobe zata mutu sbda wani ƙululun baƙinciki daya tokare ta , dariyar yaƙe Pooja ta ƙirƙiro taje kusa da kayan ta buɗe akwatin farko ta buɗe na biyu ta tashi a gurin tare da cewa "duk ranar juma'a zamu ringa zuwa make -up "ɗan ƙaramin murmushi Nisha tayi wanda bai kai zuci ba , wayar Mommah ta fara ring ɗagawa tayi tana washe baki sbda taga number Ammar ,Ya Ammar ya hidima ?"Mommah ta faɗa , lpy lou dama inason in turo driver ya ɗauki Nisha ne tazo ta gaida Ummi na "to-to to ai babu komai "Mommah ta faɗa cikin rawar murya , yana kashe wayar ta kalli Nisha tace "maza ki tashi ki shirya zakuje gaida mamanki driver zai zo "shan gabanta Pooja tayi Asim da Abid suka mayar da kallonsu ga Pooja Mommah ta daka mata tsawa tare da cewa "ya zaki tare mata hanya ?"Pooja ce ta fara magana tana kuka tace "sam wanan baiyi ba ,shifa a halin yanzu yana shirin zama mijinta ne fa "zaro ido Mommah tayi kana tace "ba muƙami bane ma zai sanya driver yazo ɗaukarta ?"ce miki akayi a gida yake ?"koma dai meye babu inda zata "Pooja ta faɗa tana turo baki "har Mommah ta miƙe zata wanka mata mari Abid ya riƙe hannun yana cewa "afuwan ya Mommah "ya zaunar da ita tare da cewa "ke Nisha maza ki shirya kafin driver ya ƙaraso "Yah Abid kufa nema mata aji so kuke yaga kamar muke binsa sabda dukiyarsu ?"shittt "Asim yayi mata tare da harararta ya jata zuwa bedroom ɗinsu .
Ƙarfe ɗaya 1:pm driver ya iso tare da yin sallama , Mommah tace "gata nan fitowa "Mommah ta rasa mai zata bawa Nisha ta kaiwa Ummin Ammar sai ta ɗauko wasu turaruka da ta siyawa Nisha na wuta ta sanya mata a leda mai kyau tace "ta kaiwa Ummin .
Shiga bedroom ɗinsu Mommah tayi taganta ta shirya tana ɗaura agogo a hannunta , murmishi Mommah tayi kana tace "tun ɗazu driver na jiranki "murmishi Nisha tayi wanda ya baiyayyanar da kyawunta tace "na gama "a ƙasan zuciyarta tsanar Ammar ce ta kuma samun gurbi .
Fitowa tayi tana tafiya a hankali da ledar da Mommah ta bata har ta iso mota , ta shiga gaba driver yace "afuwan Hajiya sai dai ki shiga baya "ya fito ya buɗe mata ta shiga ya rufo ƙofar suka ɗauki hanya , sunyi tafiya mai nisa kana suka iso gidansu Ammar bayan an buɗe get suka shige tare da parking ya buɗe mata ta fito yayi mata jagora har bakin ƙofar da zata sadata da babban palon nasu , jikinta ya hau rawa tanajin kunya sosai kuma yanzu ne ta fara ji , jin an buɗe ƙofa ta tsorata tare da ɗora hannunta a ƙirjinta , ganin Ammar yasa ta saukar da sassanyar ajiyar zuciya ta kallesa , riƙo hannunta yayi suka shiga ciki duk ahalin gidan suna palo , ya zaunar da ita kai ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun dake palon , Hajiya tacee...!
😩Bakwa shar'hi fa , a ganinku burin Abba zai cika kuwa?.
08141799224
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: Wanan littafin na kuɗi ne akan farashi mai sauƙi #200 👉08141799224
P 15-16
Sheƙewa da dariya boka yayi kana yace "aikinmu ma zaifi kyau"Bashir yace "to godiya muke "Boka ya basu izinin tashi sukayi masa godiya shidai Abba da ido yake binsu, suna komawa gida Bashir ya tafi wani meeting da zasuyi shi kuma Abba ya kwanta.
Pooja na shiga ta tarar iyaye da ƙawaye na shirin fita , wata yayar Mommah ce tace "ni na ɗauka kin koma ne ai "dariya Pooja tayi kana tace "Mom ina mota yanzu zaku tafi ? eh wacce aka kira da Mom tace "harda kema kinsan dai yanzu ba 'a kwanan gidan amarya "turɓune fuska Pooja tayi kana tace "ni gaskiya sai gobe zan tafi "suna cikin magana sukaji sallamar Ammar lokacin ƙarfe 11:pm na dare cikin sauri suka fice Pooja ta damƙawa Nisha wata takarda wacce take da rubutu ta fice idonta na fitarda hawaye , kai tsaye mota suka shiga aka wuce dasu gida .
Suna isa gida Pooja ta fice da gudu ta nufi bedroom ɗin da ya zamo nata ita kaɗai ta faɗa kan gadonta tana mai sakin kuka mai tsuma zuciya , ita kaɗai tasan mai takeji a wanan rana tama rasa ya zatayi da rayuwarta shin ƙanwarta zata bari tabi zaɓin ranta koko zatabi zaɓin iyayenta ?".
Mommah ce ta shigo tana murmishi tace "haba ƴar albarka kin raka ƙanwarki lafiya kuma kin dawo da kuka ko kina tunanin zaman kaɗaita ne ?"girgiza kai Pooja tayi tare da cewa "a'a Mommah kawai sabo ne yasa haka "Mommah tace "to maza ki kwanta kinga gobe islamiyar safe ce dake"tom Pooja tace ".
Washe gari bayan sun gama karin kumallo Mommah ta kalli Abid tace "saura ku "mu me ?"Asim yace "yana kallon Mommah , Imaam dake shan shayi yace "aure man "dariya suka sa Asim yace "nidai inada budurwa amma ƴar sarkin Misra ne "waro ido Mommah tayi ita da Imaam a tare sukace Misra ?" eh Asim yace "wanan hutun da zamuyi idan mun koma zamu haɗu da ita dan naje har Misra na gana da mahaifinta akwai wani ɗan uwan mahaifinta dake sonta kuma idan za'ayi biki akwai gasar da akeyi "sudai kallonsa suke Pooja ta miƙe da shirinta na islamiya tace "musu na tafi "to Allah ya bada sa'a suka ce mata tace "amin ".
Imaam ne ya nisa kana yace "Asim nidai abin da nakeso da kai shine ka haƙura da neman auranta "wani mumunan faɗuwar gaba Asim yaji kamar wanda akace gobe zaka mutu yace "Imaam a gaskiya a akwai alƙawarin aure a tsakaninmu "murmishi Mommah tayi jin ance ƴar sarki ce sbda tanajin labarin sarautar sarkin da kuma tarin dukiyar da yake dashi tace "ai ni a ganina shi namiji ne kuma yana da right ɗin da zai nemo mata ko a ina take "murmishin yaƙe Imaam yayi kana yace "wato ke har yanzu bakisan duniya ba kenan ?idan ya aurota yanada dukiyar da zai dinga ciyar da ita ?kokuma yana wani aiki mai tsoka ne ?ɓata rai Mommah tayi tace "ko ba haka ba idan da so da ƙauna ai maganar aiki duk mai sauƙi ne "Imaam yaga musun nasa zaiyi tsayi ya miƙe yace "ni natafi gurin aiki "ragowar mutanen biki da suka rage dama suna shiryawa suka fito , suka gaishe da Imaam tare da sama kan dining domin karyawa ,suna gama karyawa suka miƙe Mommah tabi bayansu tare da basu kyaututukan da aka raba a bikin .
Asim da Abid ma miƙewa sukayi Abid ya fita Asim ya wuce bedroom ɗinsa.
Da sallama Ammar ya ƙarasa ɗakin Nisha ya sameta a kwancce kan bed da alamun gajiya a tattare da ita hannunta a dunƙule ,taɓa hannun da ta rufe yayi ta farka a razane tare da cewa "zanyi sallah "wacce sallahr Ammar ya tambayeta ?"sallahar isha'i "ta bashi amsa okay to jekiyi ki fito "tom tace "tare da saukowa daga gadon ta buɗe ƙofar toilet ɗin ta shiga , tana shiga ta rufo da sauri tare da jingina a jikin bango tana sauke sassanyar ajiyar zuciya ta buɗe wasiƙar saƙo ta gani kamar haka..
_Aslamau alaiki ƙanwata ina fatan bazaki saki jiki da Ammar ba ,sbda ƙudirinki da kuma burinki na auran wanda kikeso ,karki mance da wulaƙancin da yayi mana duk da nasan Mommah ce ta janyo hakan ,abu na ƙarshe