ƘANIN UBA Sirrin Jinin Gida by Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  Romance

Chapter   12 / 18

33K to 36K   out of 53.2K words

"bana tilasta miki ne nama ji sauƙin magana ,akwai kuɗi a bankin ki ko ?"eh "Mheera tace "ta janyo ƴar jakarta mai kyau data zuba kayanta ta fice ,drivers na ganinta ɗaya ya rugo da gudu tare da karɓar jakarta suka jefa mota ta faɗa musu inda zasu kaita aka buɗe musu get suka tafi .
Bayan tafiya Mheera wayar Ummi ta fara ring ,ganin baƙuwar number ya sata ƙin ɗagawa sai da akayi kira wajen sau biyar sanan ta ɗaga a hankali tace "waye ?"Abba dake wasa da gashin Shukra yace "au bama kiyi saving ɗin number ta ba kenan ?"murmishi Ummi tayi kana tace "to ai Habiby ka fiya sauya layi ne "tace ya garin ya aiyuka ?"komai lafiya Abba ya faɗa yana yiwa shukra alamar taje gefe zasuyi magana da wacce yake waya , Ummi ce tace "yaushe zaka dawo ?"dariya Abba yasa kana yace "ki daɗa haƙuri insha Allah na kusa dawowa zan kai sati uku nan gaba "ran Ummi ne ya ɓaci ta tsinci kanta da kashe wayar ta ajiye , Abba kam yayi nisa ko a jikinsa bai ƙara kira ba ya ajiye wayar sukaci gaba da sha'aninsu .
Rabon da Ummi tasa Ammar a ido yau kwana biyu kenan yama kulle ƙofarsa , damuwa tayi mata yawa sosai gata miji gata ƴaƴa ta zauna ta zuba tagumi .
Tana cikin tunani ne taji wayarta na ruri , babu suna ta yanzu ma a fili tace "ko waye oho "sai ta ɗaga , jin ance Hajiya barka da fatan kin wuni lafiya ko ?"eh lafiya kamar Bashir ?"eh nine tabbas dama ina son ƙara tunatar dake ne hanya a buɗe take am free ko wane lokaci "saheɗan ne ya fara yiwa Ummi huɗuba da ta amince , cikin sa'a kuwa tace "na amince amma bazai yiwu kazo gidana ba sai dai mu haɗu a naka gidan "murmishi yayi kana yace "babu damuwa zan turo miki adreshin gidan da zakizo "to Ummi tace "ta miƙe tayi wanka tare da feshe jikinta da turare ta ɗauki jakarta da take cike da kuɗi ta ɗau wayarta ta fice sai da takai bakin Ƙofa sanan tasa hijab ,drivers na tambayarta tafiya ne Ummi na ce musu yanzu zata dawo , tana fita ta tari mai mota zatayi wa mai mota magana ƙarar saƙo ya shigo wayarta na adreshin gidan , kwatance ta yiwa driver sanan ta shiga , su shafe awa ɗaya da rabi suna tafiya sanan suka iso gidan , bayan mai motar yayi parking ta fito tare da bashi kuɗinsa , har zatayi nockiing ta tuno abin da zatayi fa zina ne ba alkairi bane "to ni ina zansa rayuwata miji ya mai dani kamar dutse "Ummi ta faɗa tare da ƙwalawa mai motar daya kawota kira tace "ya mayar da ita , shiga tayi ya koma da ita gida ta ƙara masa kuɗi.
Bashir dake zaune kan danƙareren gadonsa wanda ke malale da bed sheet ya baje yana jiran shigowar Ummi , tun tana yana duba lokaci har yaji ana kiran sallah yau kam ko masallaci baije ba a gida yayi sallahar yana jiran Ummi har akayi isha'i shiru , number wayarta ya fara kira yaji a kashe , tsaki yayi tare da wurga wayar gado .
Ummi na komawa gida ta fara kuka , a fili tace "Allah na gode maka daka nusar dani gaskiya Allah ina daɗa gode maka .
Washe gari Zaune Ammar yake a wani ƙayataccen club wanda daga ganinsa kasan ƴaƴan masu faɗa aji ne a cikinsa , hannunsa na dama riƙe da beer daga gefensa kuma budurwa ce matashiya da bazata wuce shakara ashirin ba , kiɗa ne ke tashi a gurin kamar ginin zai tsage mutanen ciki komai harkar gabansa yake yi , Ammar dake zaune ya miƙe tare da riƙe hannun budurwar suka fara rawa ,wayarsa ce ta fara ring ya ciro ta a aljihu ganin number Ummi yasa shi ɗan ɓata rai yace "barka Ummi "Ummi bata jin abinda yake faɗa kasancewar ƙara da gurin ya kaure dashi sai magana take ama baya jinta ,mai makon ya kauce daga gurin hayaniyar sai daɗa shiga yake Ummi ta kashe wayarta tana tunanin ina to Ammar yaje haka ?shi da baya son kwana a wani guri idan ba gidansu ba.
Yau kwanan Nisha uku da zuwa , zaune suke a bedroom ɗinsu suna hira Pooja na shafa powder tace "sis kinsan me "a'a Nisha tace "Pooja tace "naga kwana biyu Mommah na yawan waya da wasu nutane idan na shiga sai inga ta katse ko kuma ta daina maganar ,a ganina babu abin da zata ɓoyemin "hmm Nisha tace "kana ta ƙara da cewa "amma dai kinsan Mommah idan tana magana akan wani abun musamman ma na kuɗi bata son koda Imaam yaji ?"kinsan haka meye na damuwa ? suna tsaka da hira sukaji Mommah ta shigo da kuka tana rafka salati tana cewa "duniya ba gidan zama ba Allah ya karɓi baƙuncin ka "da sa sauri su Pooja suka miƙe tare da cewa "waye Nisha dafe da ƙirji tace "Mommah waye ?...!

Kuyi haƙuri daga gobe insha Allah zaku dinga samun typing akan lokaci nagode da adu'oinku Allah yabar ƙauna 😘.

Wa kuke ganin ya mutu ?.
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: 29-30
Rayuwa taci gaba da tafiya suna kula da ƴaƴansu ta fannin islamiya da boko shiko Munim tunda ya tashi ya tsinci kansa a wanan yanayin ya rasa inda zashi dan haka ya dinga tafiya babu gajiyawa.
CIGABAN LABARI.
Mommah na matsar ƙwallah ta miƙe tare da ficewa waje , sai da tayi nisa da gidan su sanan ta ɗauko wayarta a hand bag ɗinta ta danna number Hajiya Faɗimatu ,sai da tayi ring sau biyu sanan ta ɗaga tace "kin kira ɗazu ina tare da mutane ne Hajiya nayi miki tambaya kinƙi bani amsa "dariya Hajiya Faɗimatu tasa kana tace "yau zan shigo gari insha Allah zan baki sirrin komai "cikin jin daɗi sukayi sallama Mommah ta kashe waya ta koma cikin gidan , zuwa ƙarfe biyar na yamma Mommah tace "wa Mami zamu koma gida "kuka Mami ta kuma fashewa dashi tana cewa "anya Khadija kina neman gamawa da duniya lafiya kuwa ? mahaifinki ya mutu amma kina nuna rashin damuwa "Mami gaskiya ki daina yimin haka ya zaki dinga yimin mugun fata bayan kinsan mutane da yawa suna jin abin da kike faɗa ,kuma nace nasan nayi kuskure zan gyara "Mommah tace "tana kallon Mami , cewa tayi "Pooja ku tashi mu tafi "Nisha da Pooja da suka riƙe hannun juna a tare sukace "anan zamu kwana "ko sallama bata yiwa mahaifiyar tata ba ta fice.
Washe gari tun asbha Mommah tayi wanka ta sauya kaya ta kame a palo , Imaam ne ya dawo daga masallaci ya kalli Mommah yace "yau an tuno da sabuwar soyayya kenan ?"murmishi Mommah tayi kana tace "barka da safiya "ywwa barka da fatan kin tashi lpy ya ƙarin haƙuri ?"alhmdulilh Mommah tace "bayan Imaam ya wuce ɗakinsa ta miƙe zuwa kitchen taga ƴan aikin gidan basu ma fito ba ,da sauri taje ta tasosu tare da ce musu ku haɗa break fast da wuri zani anguwa "da sauri suka fito dama su biyu ne suka fara aiki cikin sauri ita kuma ta koma ɗakinta , ganin wayarta tayi tana kawo haske ya sata dubawa gani tayi Hajiya faɗimatu ta kirata har sau uku ,da sauri ta danna kira ring ɗaya Hjiya faɗimatu ta ɗauka tace "Khadija tun jiya na shigo gari ya kamata yau kizo "dama na shirya kiranki nake jira "Mommah ta faɗa tana murmishi , yauwa bara in tura miki adreshin gidan "Mommah tace "to tare da ajiye wayar , ƙara kawo haske wayar tayi a karo na biyu tare da alamar shigowar saƙo ,Mommah ta duba taga adreshin da komai da zai sadata da gidan kai tsaye , jinjinawa tayi a fili ta kama haɓarta tace "ni ƴasu a ina wanan mata take samun kuɗi haka , nasan anguwar nan sosai dan manyan masu kuɗi ne a nan to Allah yasa a barni in shiga "ta fito palo ta nufi dining taga an jere abinci cikin sauri ta fara ci har ta gama ta goge bakinta ta nufi ɗakin Imaam , zaune ta samesa da alƙur'ani a hannunsa yana karatu yana ganinta ya tsaya tare da ɗago kansa yace "zaki koma gidan rasuwar ne ?"ni jiya naje da yamma nayi gaisuwa anjima zan koma "eh Mommah tace "naso kwana tunaninka ya hanani shiyasa yau zanyi sammako "to a dawo lafiya "Imaam yace "baka bani kuɗin mota ba "Mommah tace "tare da kallon Imaam , kiyi haƙuri bani da kuɗi yau nasan bazaki rasa ba "yana rufe baki Mommah ta fice fuuuu.
Tana fita ta samu mai mota tayi masa bayanin inda zai kaita , faɗa mata kuɗin motar yayi tace "zata bashi yace "ta shiga suka tafi, sunyi tafiya sosai sanan suka iso anguwar mai mota yayi parking ta fito ta miƙa masa kuɗinsa ya tafi .
Lambar Hajiya Faɗimatu ta danna amsawa Hajiya Faɗimatu tayi tace "ki juyo ga gidan nawa nan yana kallonki mai pink ɗin get , juyowar da Mommah zatayi taga wani haɗaɗɗen gida mai kyau sosai ta waro ido tare da cewa "wayo tunda nazo duniya ban taɓa ganin gida mai kyan wanan ba "duk a cikin zuciyarta take wanan maganar ,takowa tayi a hankali ta isa bakin get ɗin ta hau nocking mai gadi ne ya buɗe mata tare da cewa "Hajiya tace "ki shiga "washe baki Mommah tayi tace "to nagode "ta kutsa kai cikin gidan , tun daga harabar gidan ta fara kale kale har ta isa bakin wata ƙofa mai kyaun sosai ta hau nocking , Hajiya faɗimatu dake shirin fitowa ta turo ƙofa tare da faɗaɗa fara'arta tace "barka da isowa ki shigo "shiga Mommah tayi ta zauna kan ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun palon tahau kale kale , wata ƴar aiki ce ta shigo hannunta riƙe da babban tirai mai cike da kayan motsa baki ta ajiye kan table ɗin dake gaban Mommah tare da gaishe ta , amsawa Mommah tayi tare da tambayar ƴar aikin ina Hajiyan tayi ?"ta shiga ciki ƴar aikin tace "ok "Mommah tace "ƴar aikin ta wuce , an lau tsawon mintuna talatin sanan Hajiya Faɗimatu ta shigo hannunta riƙe da wasu maƙudan kuɗaɗe ta zubesu kan cinyar Mommah , cikin rashin fahimta Mommah tace "wanan fa ?"naki ne dukka kuma inhar kina tare dani zaki samu sama da hakan "murmishi Mommah tayi na jin daɗi tace "aikuwa kamar kinsan bani da kuɗi godiya nake ƴar uwa ,na gode wa Allah daya haɗani dake a lokacin da nake neman taimako "murmishi Hajiya Faɗima ta kuma yi batace komai ba , Mommah ta dinga cin abinci kamar mai yunwa ko wanne sai da taci taji irinsa tun ƙarfe bakwai na safiya tazo a burinta bama yanzu zata koma gisa ba sai nan da ƙarfe shida na yammah , bayan anyi azhar sunyi sallah suka wuce dining room cin abinci nan ma Mommah tasha kalo sosai dan gani take idan ta sami irin wanan gidan ta gama samun komai na rayuwa , bayan sun gama cin abinci Hajiya faɗimatu takai Mommah bedroom ɗinta ,anan kalo ya koma sama iya rikicewa Mommah tayi dan gani take kamar karta koma nata gidan kasancewar kayan alatun daya haska ɗakin duk iya baƙincikin mutum dole ɗakin ya burgeshi , zama sukayi kan bed Hajiya faɗimatu tace "Khadija yanzu meneme burunki a rayuwa ?"burina shine inga nayi kuɗi na gida gida ko kuma na siya kamar wanan nakin da kike ciki ya zamo komai sai dai ayimin shine burina amma nafiso nayi kuɗi "Mommah ta fashe da kuka tace "ƙila bamu da rabon yin arziƙi ne a duniya "taɓo kafaɗarta Hajiya Faɗimatu tayi tare da jijigata tace "haba meye na kuka kinada ni fa to mai zai sa ki dinga kuka zan zame miki gatanki "washe haƙora Mommah tayi tace "nagode sosai nasan ke aminiyar ƙwarai ce tabbs kinada hali na gari "barin kira driver yazo ya kaiki gida "zaro ido Mommah tayi kana tace "sai dare zan koma ai "to Allah ya kaimu .
Tun safe Pooja da Nisha suke saka ran zuwan Mommah amma shiru dama Mami ta gaya musu baza tazo ba sun musa , har ƙarfe biyu shiru har akayi sallahar la'asar ganin bata zo ba yasa su shiryawa suka dawo gida .
Bayan sun sauka a mota suka buɗe get ɗin gidan nasu suka shiga a palo suka zauna suna ƙwalawa Mommah kira amma sunji shiru bata amsa ba , Pooja ce ta miƙe ta wuce bedroom ɗinta nanma shiru bata nan ,da mamaki ta dawo gurin Nisha tace "Mommah fa bata gidannan ko lafiya ?"Nisha dake jona waya a caji tace "ina ta shiga ne ?"suka tafi side ɗin ƴan aiki tambayarsu sukayi ko sun san inda Mommah taje ?"ɗayar ce tace "tadai yi breakfast da asubah tafice , gabansu ne ya faɗi a tare suna tunanin to ina Mommah taje ?"basu da mai basu amsa yasa su yin shiru , har sallahar magrib bata dawo ba ,sukaji sallama da gudu suka rugo sun ɗauka Mommah ce sai sukaga Imaam ne sannu da dawowa sukayi masa tare da ce masa kasan inda Mommah taje ?"ban gane ba ina ce taje gidansu ne kuma kuna can kuma ?"a'a bamu ganta a can ba yau "Pooja ta faɗa tana kallon Imaam , to kun gwada wayarta ?"eh Nisha tace "wayarta a kashe wlh taƙi shiga "Yah subhanallah Imaam yace "tare da neman guri ya zauna ,ya ciro wayarsa a aljihu ya danna number Mommah a kashe , tunani ya fara to ina taje gasu Nisha sun zuba tagumi suna kallonsa ,har ƙarfe takwas da rabi tayi suna gwada number Mommah shiru bata shiga ba .
Tun Hajiya Faɗimatu na ganin dare nayi Mommah zata tafi taji batayi maganar tafiya ba gashi har ƙarfe goma sai hira suke , hamma Mommah ta fara tace "wa Hajiya Faɗimatu nifa anan zan kwana "ba tare da musu ba Hajiya Faɗimatu ta amince mata tare da bata ɗaki mai kyau iri ɗaya da nata , tunda Mommah ta shiga ɗakin nan sanyin A.C ya fara ƙaɗata ta lumshe ido tana cewa "tabbas kuɗi sunyi a rayuwa Allah ka ɗorani a kanta ta ƙaramin kuɗi bayan wanan wanda ta bani "Mommah ta kwanta kan royel bed wanda yaji bed sheet mai kyau sai ƙamshi yake , tunani ta fara idan tayi kuɗi akwai abubuwan da zatayi masu yawa tama mance da tabar mutane a gida , sai da bacci ya fara shirin ɗaukarta ne ta tuno da ai yau su Pooja zasu dawo Allah ma ya taimaketa ta kashe wayarta ,
da tunanin duniya bacci yayi gaba da ita.
Pooja da Nisha kuka suka dingayi bacci ɓarawo ne yayi gaba dasu a palo ma suka kwana Imaam ko yayi zaton Mommah ta ɓata ne ,ƙarfe ɗaya na dare ya tashi ya ɗauro alwalah ya fara nafil fili yana roƙon Allah akan Allah ya baiyanar da Mommah har yana haɗawa da kukansa ,a kan sallahya bacci ya ɗaukesa , ba shi ya farka ba sai wajen ƙarfe biyar da rabi lokacin an fito daga sallahar asbha , bayan yayi alwalah ya fito zashi masallaci ya tarar da su Nisha a palo suna bacci , da kallon tausayi ya bisu kana ya tashe su yace "suyi alwalah ya wuce masallaci , tagumi Nisha tayi sai kuma ta fashe da kuka tana cewa "Allah sarki Mommah Allah ya baiyanaki ko kuma ta tafi wani gurinne da kanta oho "miƙewa Pooja tayi ba tare data kula Nisha ba ta wuce bedroom ɗinsu ta shiga toilet ta ɗauro alwalah ta shimfiɗa sallahya ta kabbara sallah.
Nisha dake zaune bata ko tashi ba har Imaam ya shigo ya sameta ,tambayarta yayi mai yasa bataje sallah ba ?"miƙewa tayi dan bata da amsa ta tafi yin alwalah , bayan sun idar da sallah suka gaishee da Imaam ,ya kira sunan Nisha yace "Nisha "tace "na'am "yaushe zaki koma gida kwanakin sunyi yawa har yanzu mijin naki bai dawo ba ?"eh Imaam wata biyu zaiyi wani aiki suke "to amma dai kafin ya dawo zaki koma gidanki ko ?"sunkuyar da kai tayi tace "Imaam bama jituwa da mamarsa shiyasa yace "inzo tace "bata sona "ƙura mata ido Imaam yayi kana yace "to akan me amma ai naga kamar ƙawar mamanki ce ko ?eh Pooja da sai yanzu tayi magana tace "to kuje Allah yayi muku albarka "suka amsa da amin suka fice .
"Ke a tunaninki ina Mommah taje ?"Pooja ta tambayi Nisha .
"Nasan duk inda zataje zata dawo sabda ita ba yarinta bace kuma ina ji a jikina Mommah tana lafiya lou "Nisha ta bawa Pooja amsa.
Gidan Hajiya Faɗimatu .
Washe gari aka jere abinci sunkai kala biyar a dining room ,Mommah na tashi daga bacci ta ɗauki sabon brush ta matsa man goge baki tayi wanka tana fitowa ɗaure da towel ta goge jikinta ta zauna gaban dress mirorr ta shafa mai da hoda ta sanya turare mai ƙamshi ta fito palo , lokacin Hajiya Faɗimatu bata tashi daga baccin data koma ba har ƙarfe bakwai tayi Mommah na zaune a palo tana kallo .
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: 31-32
Hajiya Faɗimatu tace "barka dai Khadija na ɗauka shirin gida zakiyi "Mommah na ɗan sosa kai tace "yanzu ma kuwa "ta miƙe tare da komawa bedroom ɗin da ta kwana ta ɗauko hand bag ɗinta ta fito , muje kiyi break fast sai ki tafi "Mommah jiki na rawa ta miƙe suka nufi dining room tayi break fast ta cika cikinta damm tana son tambayar Hajiya Faɗimatu ta kasa ,daga ƙarshe dai ta miƙe tare dayiwa Hajiya Faɗimatu godiya ,a harabar gidan suka tsaya Hajiya Faɗimatu tace "idan kin shirya yin aikin kya kirani gobe zan koma india "to Mommah tace "cikin rawar jiki ,Hajiya Faɗimatu tasa driver ya kai Mommah gida , kasancewar gidansu Mommah akwai mai gadi motocin ne babu yasa driver nayin horn aka wangale get ɗin suka shige ,bayan yayi parking Mommah ta buɗe ƙofa ta

12 / 18