ƘANIN UBA Sirrin Jinin Gida by Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  Romance

Chapter   2 / 18

3K to 6K   out of 53.2K words

yayi sallama ya shiga , zama yayi a kan sofa tare da ajiye wayar hannunsa a gefe kana ya mayar da kallonsa ga Nisha da kanta yake a sunkuye zuciyarta take saƙa mata wani lamari , janyo table ɗin da Mommah ta ajiye abinci Nisha tayi tare da ɗaukar ludayin zuba abinci ta zuba masa, kana ta ajiye masa a gabansa tare da zuba masa juice ,ta dawo ta zauna ,ko wane motsi tayi idonsa na gurin ya kasa ko da ƙiftawa ,cokali yasa ya fara cin abincin cokali uku yayi yace "alhmdulilh kana ya kalli Nisha yace "da farako dai sunana Ammar nasan kinada labarin mahaifina ko ?"
eh Nisha tace "ya ci gaba da magana , inason ayi bikinmu nan da sati biyu so banaso a ɗauki long time "wani wahalallen ajiyar zuciya tayi kana tace "ai babu matsala "ba wata hirar kirki sukayi ba shiru yafi yawa a cikin hirarar tasu ,ya miƙe tare da cire wasu maƙudan kuɗi a aljihunsa ya miƙa mata , a'a bazan karɓa ba "Nisha tace "cikin tsoro....!


*MOM ISLAM*
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: *🪂🪂ƘANIN UBA🪂🪂*

*Zainab Habib{Mom Islam}*


🪂🪂🌼🌼🌼🌼🌼🪂🪂



Elegant online writers

Kuyi haƙuri anan zan tsaya da free page 🥰 Inaso inga masoyana 👍.

🅿️ Page 5-6
Kana nufin Imaam Ali? eh Ammar yace "cike da ƙwarin guwaiwa ,hmm tabbas babu kai babu ƴar Imaam kaji na gaya maka "Abba ya faɗa cikin ɓacin rai , jijiyoyin kan Ammar ne suka tashi haɗi da dunƙule hannu alamun ɓacin rai ya tashi yabar gurin.
Ummi na zaune Ammar ya shigo cikin ɓacin rai , daga ganinsa tasan ba lafiya ba duba da yanayinsa sai huci yake ,kamo hannunsa Ummi tayi tare da zaunar dashi tace "haba yaron kirki wai maike faruwa ne ?"naga duk mood ɗinka ya sauya "Ammar kamar zaiyi kuka yace "Ummi mai yasa Abba yake son ƙin aure na da Nisha ?"ko akwai wani abunne "murmishi Ummi tayi kana tace "koma menene ni zanji da komai karka wani damu kanka ka kwantar da hankalinka ,a zuciye ya miƙe tare da cewa "ba kuɗi bane yake aure, to ni a yau ɗinnan zankai sadaki "dafe ƙirji Ummi tayi kana tace "Ammar a ina ka taɓa jin ance kuɗi yasi mutunci ?mu tsaya mubi mahaifinka a hankali nasan yanada hujja akan faɗar hakan "shikenan Ammar ya faɗa cikin fushi kana ya fice , Ammar na fita Ummi ta zurfafa cikin tunani to mene ne dalilin da zai sanya Abbansa cewa "bazai aureta ba ?".
Mommah ce zaune ita da Imaam tace "Habiby ina ji a jikina auran Nisha da Ammar alkairi ne "to Allah ya tabbatar mana "Imaam yace "suna zaune shiru ya biyo baya na ƴan mintuna sai ga Nisha ta shigo sanye da Hijab ta durƙusa gaban su Imaam tace "ya Imaam zani islamiya "masha Allah fatan nasara Allah ya dawo daku lpy ina Pooja ?"tana ciki "Nisha ta faɗa kanta a ƙasa , Imaam zai ƙara magana yaji sallamar Pooja amsawa sukayi Pooja ta zube a gabansu itama tayi musu sallama , suka sanya musu albarka Pooja da Nisha suka fice ,kasancewar a ƙasa suke tafiya islamiyar babu nisa sosai , suna tafe Pooja tace "wa Nisha "wai ni nayi miki laifi ne naga 2days kina shareni?"no bakiyimin laifi ba anty "amma mai yasa kikace haka ?babu komai "Pooja tace "har suka isa makarantar , suna shiga suka tarar har an fara karɓar hadda bayan sun bayan anyi karatu zuwa ƙarfe 6:10 suka kamo hanyar dawowa gida , haka suka dawo babu wata hira ta kirki a tsakaninsu , samun Mommah sukayi a palo tana zaune da wasu ledoji a hannunta , wayar Nisha ce ta fara ring ta matsa daga gurin nasu tayi gefe inda bazasu jiyo mai take faɗa ba ,fuskar Mommah ɗauke da murmishi tace "Alhmdulilh ƴata ta fara son yaron governor masha Allah mukam mun warke "Pooja dake gefe tace "Momma akwai abinci kuwa ?"eh Momma tace "duba kitchen idan babu sai kisa su Hanni su dafa miki "miƙewa tayi ta nufi kitchen ɗin daga nesa taji muryar Nisha tana cewa "mai yasa kake neman shigowa cikin rayuwata ?mai yasa kake son rusa farincikin gidanmu , gashi tun yanzu antyna bata shiga safgata "hawaye ne ya kwaranyo a fuskar Pooja tayi saurin barin gurin , Nisha taci gaba da cewa "ko a tsari bamu dace ba ,idan kayi duba da matsayin mahaifinka da ni da ban wuce ƴar aikin gidanku ba duk da mahaifina yanada dukiya mai yawa duk da haka naku yafi namu kaga kuwa bamu dace ba "keeee"Ammar ya daka mata tsawa yace "kina wani yimin magana kamar kina magana da sa'anki ,ga kunan a gidan kunyi kwantai babu mai tayawa dan an tilasta min auranki shine zaki dinga gayamin abin da ranki keso ?" wlh last warning ba ayimin magana da ƙarfi ko tsawa ko faɗa Ammar nake bin Umar "zato ido tayi kana tace "mai ka isa kayi ?"ta kashe wayar ,zuciyar Ammar ce ta fara tafasa a fili yace "lallai yarinyar nan ta taro ruwa wlh ko da tsiya ko da arziƙi sai na nuna mata tsira da fifiko zata san ta taɓo Ammarrr.
Soyayyar soya Pooja ta sako a plet da miyar ganye wacce taji kifi , ganin Nisha ta wuce yasa ta sami ƙwarin guwaiwar wucewa ta dawo palon , again Nisha bata palon , Pooja ta kalli Mommah tace "Mommah miye a ledar ne ?" kamar jira Mommah take ta fito da kayan ledar materials ne masu tsadar gaske guda huɗu biyu kala biyu ,wow Pooja tace "tare da cewa "Mommah siyarwa ake ?"naku ne wanda zakusa ranar biki "Mommah tace "tana murmishi ,mungode Mommah Allah ya ƙara soyayya Pooja tace "wa Mommah tare da rungumota ,fitowar Nisha ne ya katse su , Nisha ta miƙawa Mommah waya tace "ance in baki "waye ?"Mommah ta tambayeta "Ammar "Nisha tace "a taƙaice , jiki da hannu na karkarwa Mommah ta karɓi waya tace "ya Ammar barka da wanan lokaci "cikin isa da gadara Ammar yace "kiyiwa yarinyarki gargaɗi tana cimin mutunci !!ya kashe wayar ɗif ɗif, wayar ce ta zame daga hannun Ummi tana shirin faɗuwa ƙasa Pooja ta riƙe tare da cewa "haba Ummi zaki yar mata da waya akan wanan marar mutuncin ,sbda Pooja taji maganganun da ya gayawa Mommah , tasss Mommah ta wanketa da mari tare da cewa "wanan furucin kike yi masa ?"kema kin zamo Nisha ne da bakwajin tsoron ɓacin raina ?"riƙe gurin marin Pooja tayi cikin tsananin mamaki wanan shine karo na biyu da Mommah ta duketa akan Pooja kuma wlh sai ta ɗau mataki babu makawa , tashi tayi a zuciye tabar gurin zuciyarta na tafar fasa ,idon Mommah ya kaɗa yayi ja sosai ta nuna Nisha da hannu kana tace "da tun farko kin nuna amincewa da buƙata ta da duk haka bata faru ba "har yanzu idon Nisha bai dena zubar da hawaye ba tace "afuwan Mommah bazan sake ba "miƙewa Mommah tayi tare da rungumo Nisha tayi mata kiss a goshi.
Pooja dake zaune kan bed tana saƙa irin rashin mutuncin daya kamata suyiwa Ammar ,shigowar Nisha yasa ta yin murmishi Nisha ta zauna tare da cewa "anty Pooja a gaskiya banajin daɗin rashin zaman mu lafiya ,tun da Ammar ya shigo rayuwar mu ya tarwatsa mana farinciki "tafin hanunta Pooja tasa ta share hawayen dake zubo mata kana tace "karki damu akwai lokaci " suka rungume junans.
Mommah dake zaune tana ganin ai yanzu shiri za'a fara babu kama hannun yaro tunda har Nisha ta buɗi baki tace "ta amince kuma ta fanin Imaam bata da wani matsala ,tellan su ta kira namiji wani balarabe ta nuna masa rigunan su Pooja tace "komai iri ɗaya zaka yimin "faɗar abin da za'a bashi yayi Mommah tace "karka damu akwai wasu ma kai dai kaje da wanan "sallama telan yayi mata kana ya tafi.
Governor Umar wato mahaifin Ammar ne zaune yana nazarin maganar auren Ammar ,shi dai har ga Allah bazai bari ɗansa ya haɗa jini da Imaam ba , daga ƙarshe ya miƙe tare da barin gurin.
Ganin yau sati kenan babu maganar Ammar zai turo magabatansa yasa Mommah kiran Umminsa tace "Slamu alaikum "bayan Ummin ta amsa Mommah tace "dama akan maganar su Nisha da Ammar ne , naji yace "dan da sati uku amma shiru "ga mamaki Ummi ta kuma kallon wayar a zuciyarta tace "wanan wace irin uwa ce da take neman kai da ƴarta "a fili tayi murmishi kana tace "ana shiryawa ne ,bayan Ummi ta ajiye wayar ta shiga kogin tunani ta miƙe tare da zagaye makeken palon tana saka da warwara akan anya itama zata yarda Ammar ya auri ƴarsu kuwa?"duk da batasan musabbabin da yasa Abba cewa "bazai aureta ba ita kam tana ganin mutuncin su zai zube a idan duniya, Abba ne ya shigo tare da cewa "haɗamin kaya india zan wuce yanzu "yabi ta bedroom ɗinta tare da zama a bakin gado , Ummi dake haɗa masa kaya a akwati mai tsadar gaske tace "haba ranka shi daɗe ya zakayiwa Ammar haka kace bazai auri ƴar Imaam ba ?"nisawa Abba yayi kana yace "yanzu ba time ɗin magana bane so ki bari idan na dawo zamuyi magana one week zanyi "zaro ido tayi tace "gaskiya baka tsayawa kana bani lokaci , daga ka dawo daga india sai kace zaka Egypt daga nan ma kace gaba zakayi "tsayawa yayi yana ƙare mata kalo yace "mai na rageki dashi ?ci ko sha kokuma tufafi ko ziyarar danginki "ya kamata kisan dawa kike magana "cikin ɓacin rai Ummi tace "koma da waye nake magana ai muƙaminka a waje yake ba a cikin gida ba "dakatar da ita Abba yayi da cewa "keee MARYAM kisan dawa kike magana "ya fice bodyguard ɗinsa suka zo suka ɗaukar masa kayansa , kifa kai Ummi tayi a gado tana kuka tana cewa"wanan wace irin rayuwa ce ace mutum bashi da lokacinka dana gifta guri a dinga cewa"ga matar governor nan amma babu maganar sauke min haƙƙina " tana cikin kukan batayi tsammani ba taji shigowar Ammar babu sallama ,ɗago jajayen idanunta tayi kana tace "haba Ammar sallamar ma ta gagara ?"cike da isa dan shi a ganinsa idan ya fara yi musu iskanci shine zasuyi masa aure , yace "Ummi ya naga idonki yayi ja ne ko duk akan maganar aurena ne ?"girgiza kai Ummi tayi kana tace "ba haka bane "ficewa yayi bayan ya ɗage kafaɗa alamun ita ta sani ya wuce abinsa.
Mommah nata shirye shirye kamar ance mata ga ranar bikin , Imaam ya shigo hannunsa riƙe da kaji guda huɗu Mommah ta karɓa tare da rungumesa tace "masha Allah "miƙawa ƴar aikin dake tsaye a palo tana goge tils tayi kana ta dawo bedroom ɗinta gurin Imaam ta zauna , Imaam ne yace "ina su Nisha ne ?"suna ciki Mommah ta bashi amsa "masha Allah Imaam yace "Ummi tace "Imaam bakace komai ba game da shirye shiryen bikinnan "to mai kikeso ince "Imaam ya bata amsa "au mai nakeso kace "bazaka ko ɗan kawo wani abu ba inje kasuwa inyi cefane ?"mai kike ci na baka na zuba "Imaam yace "yan kallonta kana yaci gaba da cewa "kibi komai a hankali na fara shiri nima "cikin fara'a Mommah tace "masha Allah su Ansar da Abid suna hanya yau "wani irin farinciki ne ya lukumɓe Imaam yace "ashe na kawo kaji a dai dai maza kisa ayi a yi musu abinci mai rai da lafiya "Imaam ya faɗa tare da shigewa side ɗinsa.
Pooja dake kwance taji wayarta na ring number Ya Ansar ta gani tayi murmishi tare da cewa "taɓɓ yaushe ranbon da muyi waya "Nisha dake gefe tace "waye ?"Pooja tace "Ya Ansar ne "suka yi murmishin jin daɗi , amsawa tayi da sallama tace "Ya Ansar "daga can ɓangaren yace "kin fara rainin wayon naki ko ?"da har zan kira wata kiƙi ɗagamin afuwan my bro wlh muna mamaki ne ,au mamaki ?"Ansar ya faɗa ?"yaci gaba da cewa "to kuci gaba da mamaki yau muna hanya nida Abid "tsalle suka buga yanata magana basu jiba ,kasancewar hayaniyar da sukeyi daga ƙarshe dai ya kashe wayar , da gudu suka fice sun mance ɓacin ran da suke ciki suka rungume Mommah tare da sanar mata da yayun nasu na hanya ,itama Mommahn mrmushi take tace "ai na rigaku sani ganin baku fito bane yasa na ƙyakeku ,yanzu abin da za'ayi ke Pooja jeki gyara ɗakin Abid, ke kuma Nisha ki gyara ɗakin Ansar , da sauri suka tafi harda cewa "ayi rige rige.
Ammar na komawa ɗakinsa ya kwanta rigin gine tare da ɗora hannunsa a kan goshinsa yana mai jin zafin maganar da Abba yayi masa , tunowa da yau ƙanwarsa Mheera zata dawo ya buga tsalle dan a duniya idan ka cire iyayensa to Mheera ce a gabansu sai kuma yanzu wacce yake so , dawowa part ɗin Umminsa yayi yaga ta sake wanka ta haɗe cikin wata koriyar amfa mai flowers yellow tayi kyau sosai "Ummi yau Mheera zata dawo ko ?"Ammar ya faɗa yana kallon fuskar Ummi "eh yau zata dawo jirginsu ya kusa sauka ma "wow na matsu inga ƙanwata "Ummi dai babu walwalah ta shige bedroom ɗinta ta barshi a gurin , yana shirin tashi yaji ƙarar takalmi ta shigo da gudu ta rungume Ammar tana cewa "ashe kana nan "baiga fuskarta ba kasancewar ya faɗa kogin tunani sai dai muryarta daya gane , ƙara rungumeta yayi yace "wlh nima nayi kewarki ƙanwata ya karatu inayi miki farinciki kin gama lafiya ?"bro ka barni in huta man "Mheera ta faɗa tare da cuno baki ,zaunar da ita yayi kan sofa ya tafi bedroom ɗin Ummi ,a karo na biyu ya kuma samu tana kuka ,farincikin fuskarsa ne ya fara gushewa yace "haba Ummi bakison dawowar Mheera ɗin ne ?"no ba haka bane samuwata daban Ammar kace ta shigo "juyawa yayi yaje gurin Mheera yace "kinma mance da Ummin kenan ko ?"rufe bakinta tayi kana tace "ina banfa mance ba tana raina ,ganinka da nayi ne wlh nake jina cikin nishaɗi ,drivers ne suka shigo mata da kayanta tare da kaiwa bedroom ɗinta daya kasance mai kyau komai nasa pink and milk color ne ,suka jere mata kayanta a drower tare da haɗa mata ruwan wanka , suka dawo gabanta suka zube kai kace sarauniya sukace ranki ya daɗe an haɗa ruwan wanka "bata bata ma kalkesu ba bare susa ran zata amsa sai dariya da take yiwa Ammar ta wuce bedroom ɗin Ummi , ta sami Ummi zaune da waya a hannunta ,ta je da gudu ta tungumeta tare da cewa "Ummi na aimiss you wlh sosai "shafa gefen fuskarta Ummi tayi kana tace "nima daughter nayi missing ɗinki ,zuwan Mheera ya ragewa Ummi damuwa gashi tunda Abba ya tafi bai kira ba hakan yasa tayi saton daga faɗar gaskiya sai ransa ya ɓaci "hira suke ta ɗa da Uwa Ammar ma ya shigo aka dinga wasa da dariya ,yake cewa "ke aurena ya kusa nan da 2 weeks "kallonsa Mheera tayi kana tace "aure kuma Abban zai yima ?"taɓɓ wlh ba yanzu ba bro ka bari nan da 7yrs "haɗe rai yayi kana yace "wato na gano kema kina daga cikin masu yimin baƙinciki ko ?" dariya tasa kana tace "ba zancen baƙinciki bane bro gani nayi shekarunka nawa ne , Ummi dake jinsu bata ce musu komai ba .
Pooja da Nisha sunci kwaliya suna jiran isowar yayun nasu haka ma Mommah Imaam dama yazo kawo kaya ne ya koma , suna cikin hira sukaji sallamar Abid da Ansar da gudu Nisha ta miƙe ta rungume Abid ita kuma Pooja ta rungume Ansar , cikin farinciki suka ƙaraso bakin Mommah yaƙi rufuwa ,suka zauna suna cewa "Mommah kin ƙara ƙiba "dariya dukkansu suka sa Mommah tace "kuna neman ku mayar dani kakarku ko ?"Abid yace "ke Nisha ya naga kin rame ? murmishi tayi ta sunkuyar da kai ƙasa ,Pooja tace "auranta ya kusa shi yasa tana tunanin rabuwa da Mommah "Momma naso taji an taɓo maganar aure har wani nishaɗi take ji...!
Wanan littafin na kuɗi ne ,akan farashi mai sauƙi #200 ɗari biyu ne kacal, zaki iya turo da kuɗinki ta wanan account ɗin 3175689751 Zainab Habibu first bank ,ko hoton katin waya ta mtn ɗina , ta wanan number 08141799224 ƴan Niger kuyi magana ta wanan number 84506476 , karku manta siyan nagari ...💃.


Momislam
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: *🪂🪂ƘANIN UBA🪂🪂*

*Zainab Habib{Mom Islam}*

🪂🪂🌼🌼🌼🌼🌼🪂🪂

AREWA WRITERS ASSOCIATION

🅿️ Page 3-4

Murmishi Ammar yayi kana yace "idan har kina sona wanan ba komai bane zaki more a rayuwa " uhm Nisha tace "cike da takaici ta wuce ta bashi guri , a ransa ya ƙaddara kunyarsa ce tasa ta barin gurin ,ya kira wayar Mommah , ring ɗaya Mommah ta ɗaga jiki na rawa tace "Aslamu alaikum ya Ammar"wlkslm Nisha ta wuce inason bata wani abu "da gudu Mommah ta zubo ta nufo ɗakin Imaam taga kuɗi zube a kan table , waro ido tayi kana tace "son da fatan Umminka na lafiya ko ?"eh lpy gashi a bawa Nisha "cikin rawar Hannu Mommah ta karɓa tare da godiya sosai ya fice cikin takunsa na ƙasaita , binsa da kallo Mommah tayi tana rungume da kuɗaɗe a hannunta ,har zata zauna sai ta ruga side ɗinta da gudu ta zube kuɗin a kan bed ɗinta tana mai jinjina yawan kuɗin a fili tace "na warke aihuwar ƴa mace ni'ima ce , sai kuma ta fashe da kuka , ta ɗau lokaci tana kuka bugun ƙofar dataji ne ya sanyata tattara kuɗin ta tura cikin hijab ɗinta tare da zama a kansu , tana daga zaune tace "masha Allah shigo "Pooja ce ta shiga fuskarta tayi ja tsabar kuka ta durƙusa gaban Mommah tace "Mommah afuwan ya zakiyi haka sam baki kyauta ba "hannu Mommah tasa a haɓarta kana tace "da nayi miki me ?"Pooja da har yanzu kuka

2 / 18