ƘANIN UBA Sirrin Jinin Gida by Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  Romance

Chapter   5 / 18

12K to 15K   out of 53.2K words

kika shiga nayita kiranki shiru?....!

Wanan littafin na kuɗi ne ,akan farashi mai sauƙi #200 ɗari biyu ne kacal, zaki iya turo da kuɗinki ta wanan account ɗin 3175689751 Zainab Habibu first bank ,ko hoton katin waya ta mtn ɗina , ta wanan number 08141799224 ƴan Niger kuyi magana ta wanan number 84506476 , karku manta siyan nagari ...💃.
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: *🪂🪂ƘANIN UBA🪂🪂*

*Zainab Habib{Mom Islam}*


🪂🪂🌼🌼🌼🌼🌼🪂🪂

Elegant online writers

😘Ƙarshen free page ,kar ayi babu ku nasan kuna son kuji za'ayi bikin Nisha da Ammar kuwa ? da kuma ƙudirin Governor.

️ Page 9- 10
Naje toilet ne "kallonta Mommah tayi ba tare da tace "komai ba.
Ansar daya ƙunshe dariya yace "kodai cikin ya rikice ne ?"itama dariya tayi tace "Yah Abid kaga Yah Ansar na tsokanata "ta ƙarashe maganar a shagwaɓe , Abid dake shirin tashi wayarsa na ring yace "haba bro sai mun kai ka ƙara fa "sukasa dariya dukkansu .
Abba ne zaune a kan bed ya zuba tagumi ,yana shawarar wama zai bada ? kansa ya kulle yama rasa mafita gashi yau zasu koma gurin boka , Bashir ne ya kirasa a waya tare da cewa "mai girma Governor na shirya ina jiranka a parking space , gaban Abba ne ya bada dumm ,ya shirya cikin boyel fari mai tsada ya sanya baƙar hula da takalmi ya fito ya kwashe wayoyinsa a parlo ya nufi gurin Bashir, yana zuwa aka buɗe masa mota ya shiga shima Bashir ɗin ya shiga suka tafi, sunyi tafiya mai nisa sanan suka iso gidan nasa , akayi parking bayan sun fito suka kutsa kai ciki , gaban Governor na faɗuwa haka suka shiga da baya ,suka nemi guri suka zauna, suna zama bokan yace "ka gama shawar wanda zaka kawo ?" eh am uhm e....Abba ya fara kame kame , Boka yayi dariya tare da cewa "nifa aikina babu wasa a ciki kuma idan ba'a bamu jini ba wlh baka babu zama Governor "wani gigitaccen faɗuwar gaba Abba yaji cikin rawar murya yace "matata ta dena aihuwa fa bare ince idan ta aihu ka riƙe jariran "boka ne ya kallesa kana yace "sirikarka fa ?" ɗana har yanzu bai yi aure ba "Abba ya faɗa , aikuwa akwai yiwuwar dole yayi aure inba haka ba nan da sati sai ka faɗi a zaɓe mace ta haye kujerarka "bakin Abba na rawa a karo na biyu yace "an gama idan har buƙata ta zata biya ko mata biyar ne zan aura masa "dariya boka yayi yace "ai ƴaƴa biyu mukeso ,idan yayi aure matar ta aihu to ƴaƴan sun zamo namu ka amince ?"eh Abba yace "Bashir ya zube wa boka maƙudan kuɗi suka muƙe suka fita , suna fita Bashir yace "to wa kake ganin zaka aurawa ?"ai yanada wata budurwa mai suna Nisha a da naƙi auran yanzu kam na amince ,haɗa mana kaya mu koma Nigeria yau ɗinnan "kasancewar da safe ne .
Bayan Bashir ya kammala haɗa kaya suka nufi airport , kasancewar Governor ya kama kammala komai suna zuwa jirgi ya kusa tashi bayan sun shiga jirgi ya ɗaga zuwa Nigeria.
Cikin ikon Allah sai gashi sun iso jirgi na sauka mutane suka fara shirin fita , shiko Abba ransa cike da jimamin abin da yake shirin aikatawa , Bashir ya riƙo hannunsa tare da cewa "insha Allah nifa nasan zakaci musamman idan kabi abinda boka yake so , Abba bai ce komai ba ya shiga motar da tazo ɗaukarsu , suna ciki kowa da tunanin da yake har aka sauke Bashir a ƙofar gidansa ,kana aka wuce da Abba gida , ba wata tafiya sukayi mai nisa ba suka iso gidan tare da yin horn mai gadi ya buɗe get suka shiga ,anayin parking aka buɗewa Abba ya fito tare da nufar cikin gidan da sauri , yana shiga ya sami Ummi da Mheera da Ammar a zaune suna kallo a TV , sai da ya dai daita nutsuwarsa cikin sauri sanan ya washe baki tare da cewa "Mheera na har anyi hutun kenan ?"Ammar yace "barka Abba "ywwa barka son ya ƙoƙari ?"Almdulilh Ammar yace "Mheera tace "Abba amma ka sauya sim ne ko ?" mai kika gani ?"Abba yace "wa Mheera ,naga ko na kira bata shiga "eh Abba yace "wacan layin mutane ma damuna shiyasa "Ummi tayi murmishi tace "barka da shugowa "ywwa barka"Abba yace "yana ƙare mata kallo yaga ta rame sosai ,ya wuce bedroom ɗinsa tare da zubewa kan lallausan gadonsa ya zuba tagumi , yana jin an turo ƙofa alamar shigowa yai saurin cire tagumin ya sake fuskarsa , Mheera data lura kamar yana cikin damuwa ta zauna kusa dashi tace "Abba lafiya kuwa ?"eh lafiya my daughter da fatan kin dawo lafiya ya karatu ?"badan ta yarda da maganarsa na cewa lafiya ba tace "almdulilh "zata fice ya kamo hannunta tare da cewa "kiramin Umminki "tom tace "ta fice tana isowa parlo ta sami Ummi a zaune tana kallon TV a zahiri kuma ta faɗa kogin tunani ne ,durƙusawa Mheera tayi kana tace "Ummi na ki daina tunani Abba na kiranki "miƙewa Ummin tayi ba tare da tace "komai ba "Abba na zaune yana jiran shigowar Ummi yaji an kwaɗa masa kira a waya ganin number Bashir ya sashi ɗagawa da sauri yace "ya akayi ?"Boka yace "karka sake ka kusanci matarka har sai an gama aikin da ake maka "to to "Abba yace "sbda yaji alamun za'a shigo ya kashe wayar gabaki ɗaya , shigowa Ummi tayi da sallama ta sunkuyar da kai "wai nikam nayi miki laifi ne Umm Ammar ?"girgiza kai Ummi tayi tare da cewa "mai ka gani ?"no babu komai Governor yace "wato Abba tare da ɗage kafaɗa , ɗan karkatawa tayi tare da shafo gemunsa tace "nayi missing ɗinka mijina "nima haka "Abba ya faɗa a taƙaice , ganin Ummi na ƙoƙarin wuce gona da iri ya sashi riƙe hannunta jin ta taɓo sandar girmansa yayi yayi ta sake taƙi sai shafawa take a hankali , hakan yasa jikinsa yayi mugun mutuwa kasala da sha'awa ta saukar masa lokaci ɗaya yaji yana buƙatar kasancewa da ita , har ya fara shafo mararta ya tuno da umarnin Boka hakan yasa shi saurin sai ta kansa ya wayance da cewa "dama akan maganar auran Ammar ne ,kina ganin har yanzu suna tare da wanan yarinyar ?"ran Ummi ya fara ɓaci tace "haba Abban Mheera ya kake ƙoƙarin danne min haƙƙina ne ?"basar da zancen yayi ta hanyar cewa "na biya miki makkah keda Mheera "wani tsale Ummi tayi tare da cewa "Alhmdulilh barinje in sanar da Mheera " Abba ne yace "ki zauna zamuyi magana dake albishir zanyi miki "dawowa Ummi tayi tana washe haƙora tare da zama daf da Abba tace "ina sauraronka "gyaran murya Abba yayi yace "inaso gobe insha Allah muje gidan Imaam mu jiyo maganar auran Ammar "wani sabon farinciki ne ya kuma luluɓe Ummi tace "kai yau daɗi ya isheni "cikin zuciyar Abba kuwa kamar ana buga masa ganga , Ummi ta miƙe ta fita shi kuma ya kwanta yana kallon sama ,
Tana fitowa palo ta samesu suna zaune suna hira , da ganin fara'a a fuskar Ummi Mheera taji wani daɗi marar misaltuwa ,Ummi tace "albishirinku ?"goro dukkansu suka ce "Ummi tace "Abbanku ya miya mana Makkah nida ke ,kai kuma Ammar gobe za'aje jin maganar auranka "tsalle Ammar ya doka tare da cewa "dan Allah fa Ummi wayo daɗi "harda ƴar rawarsa , nan dai sukayi ta farinciki sosai.
Washe gari su misalin ƙarfe 12:pm bayan sun kammala break fast Abba ya kira Bashir akan maganar tafiyarsu gurin Imaam , Bashir ne yace "ai gani nan ni har na fito nama kusa ƙarasowa ƙofar gidanka "wayoyinsa Abba ya ɗiba tare da cewa "sai sun dawo bayan ya ɗibi kuɗaɗe masu yawa "bai ma san adadinsu ba , kai tsaye ya nufi parking space aka buɗe masa mota driver ya tuƙashi suka fito bayan an buɗe musu get motar Bashir da ban haka ma ta Governor suka ɗau hanya sai gidansu Imaam , suna isa aka buɗe musu get suka shiga tare da parking ,aka buɗewa Abba shida Bashir duka suka fito ko wanne na gyara manyan kayan jikinsa suka turo drivern gidan yayi musu sallama da Imaam , cikin sa'a ya samu yana nan ya dawo yace "musu wai yana nan zuwa "to sukace "ɗaya daga cikin masu shara sukace ai naga kamar Governor "cikin sauri suka miƙa masa wata kujerar roba kana suka miƙawa Bashir shima ya zauna , Imaam ne ya fito cikin rawar jiki yana cewa "kai ne da kanka mai girma gwamna ?"murmishi Abba yayi Imaam yayi musu iso har palonsa , ta window Ummi take leƙensu zuciyarta fal farinciki a fili tace "kakarmu ta yanke saƙa "ta wuce kitchen tare da umartar ƴar aiki da ta dafa musu abinci mai sauri ta wuce ciki.
Bayan Imaam sun gaisa da su Bashir Governor yace "dama maganar aure ce ta kawomu "cikin fara'a Imaam yace "auran wa kenan ?"ko Nisha ?"eh Bashir yace "munaso a yanke mana dukiya "Imaam yace "duk abinda kuka bada Allah ya sanya masa albarka "Abba ne yace "Bashir akwai kuɗi a mota maza ka ɗauko "tom Bashir yace "tare da zuwa ya ɗauko kuɗin ya dawo "Lak talatin ne nan "waro ido Imaam yayi sai yaji jikinsa yayi sanyi a ransa yace "karfa siyar da yarinyr nan zanyi "sai wata zuciyar ta kawar masa da tunani Bashir yace "Imaam tunanin mai kuma kake ?"babu komai Imaam yace "tare da yin dariyar yaƙe "muna so a sanya mana rana "Bashir ya faɗa cikin siyasa ,gaban Imaam ne ya kuma faɗuwa kasancewar bai riƙi ƴan uwansa da muhimmanci ba yasa basa nemansa shima baya nemansu , Imaam yace "nan da zuwa yaushe kenan ?"an sosawa Abba inda yake masa ƙaiƙayi yace "sati ɗaya , tunda dama Ammar ɗin ya daɗe yana nemanta "kuma idan bikin ya tashi ko tsinke kar a kawota dashi mu zamu siyi komai ai ɗa na kowa ne "cike da farinciki Imaam yayi murmishi kana yace "to alhmdulilh Allah ya kaimu lokacin "suka amsa da amin, suna shirin tashi ana kawo abinci Imaam yayi yayi akan su tsaya suci amma sunce a'a , haka suka tafi cikin farinciki .
Suna tafiya Mommah dama tana leƙensu har kuɗin da aka bada ta faɗo ɗakin da sauri tana cewa "Imaam har sun tafi ne ?"jikin Imaam a sanyaye yace "eh "kallon akwatin dake ɗauke da kuɗin tayi tace "har an kawo kuɗin aure alhmdulilh ta hau rawa "shiko Imaam yana yi mata kallon rashin tunani .
Zuwa yamma Mommah ta sanar da Abid da Aseem da Pooja da Nisha maganar ranar biki "kowa yayi farinciki banda Nisha da takejin kamar za'a cire mata rayuwa ,Mommah ta lura da yanayinta dan haka batayi yunƙurin kulata ba .
Koda Abba suka koma gida ya sanarwa ahalinsa maganar biki kowa yayi sambarka tare da fatan alkairi Ammar kam baki baya rufuwa.
Yau biki saura kwana biyar ,kuma yau kwananta biyu bata ga abokinta ba wato mahaukaci , bayan tayi wanka tayi breakfast ta fito da zumbulelen hijab hannunta riƙe da wata leda mai ɗauke da abinci a cikinta ta fice a gidan , ta ɗanyi tafiya kana ta iso gurin da yake zama , waige waige ta fara taga bata gansa ba sai da ta ƙwala kira tace "abokina "da gudu ya rugo yana mata dariyarsa mai kyau ,da kallon tausayi ta bishi sbda tunda suka haɗu da wanan kayan take ganinsa gashi duk sun yage , miƙa masa ledar tayi ya karɓa yana dariya tace "ni zan tafi ka dena yawo anjima zan kawo maka abinci kaji ?"jiki na rawa ya ɗaga mata kai bai ce komai ba sai dai murmishi da yake yi , miƙewa tayi tana yi masa bye bye har ta ɓace masa ya buɗe ledar ya fara cin soyayyar taliyar data kawo masa.
Tana komawa gida tazo buɗe get ta shiga taci karo da Pooja a bakin get idonta yayi ja , a tsorace Nisha tace "anty Pooja wani abin ne ya faru pls ki gayamin dan Allah "girgiza kai Pooja tayi kana tace "ƴar uwata wanan ai shine auran dole babu neman shawara kawai sun karɓi kuɗin aure "amma idan sunsan wasu basu san wasu ba nayi miki alƙawari " ta raɗa mata magana a kunne , murmishi Nisha tayi suka dawo palo suka zauna .
Da su Abba suka dawo gida ,ya sanarwa Ummi abin yayi mata daɗi sosai ,musamman Ammar da yau yayi shiri na musamman , kafin ya tafi sai da yaje yayiwa Abbansa godiya ya wuce gurin motarsa bai buƙaci driver ba sbda farincikin da yake ciki yau ɗinnan na musamman ne ,bayan ya iso gidan su Nisha an buɗe masa get ya shiga ya aika a ce mata tayi baƙo ,ɗan aikan ne ya dawo tare da cewa "mahaifiyarta tace "ka shigo , shiga yayi cikin takunsa na ƙasaita ya durƙusa har ƙasa ya gaida Mommah , Mommah na washe baki kanta ya ƙara girma yau ɗan gwamna ne a ɗurƙushe a gabanta tabbas akwai ƙamshin arziƙi a tare dasu , iso Mommah tayi masa da kanta zuwa ɗakin Imaam kasancewar bayanan , zama yayi yana dana wayarsa har na tsawon wasu lokuta , Mommah taje ɗakin su Nisha tace "maza taso mijinki yazo gashi can a palon Imaam "kuka Nisha tasa tace "Mommah nifa nace miki bana sonsa bana sonsa dole ne "baki buɗe Mommah take kallonta tace "tabbas wuyanki ya isa yanka Nisha ,ina burin inga ana kiranki hajiya ke kina burin watsamin ƙasa a ido ?"kasancewar tayi wanka Pooja ta janyo hannunta ta ɗauko mata wani sari mai ruwan malmo purple ta sanya mata ta kuma gyara mata fuska sosai , Mommah tace "yawwa Pooja na wlh shiyasa nake ƙara sonki kina somin abin da nake so WOW ƴar kirki kama hanunta ku tafi daga nan ki gaishe sa "ɓata rai Pooja tayi tace "gaskiya Mommah ba zani ba wlh sai dai ita ta tafi "gudun kar Pooja tayi fushi a sami matsala tunda tafi Nisha zuciya Mommah taja baki tayi shiru , a hankali Nisha ta zura farin takami a kyakkyawar ƙafarta tare da gyara mayafinta idonta na ƙoƙarin fitarda hawaye ta fice "kai tsaye palon Imaam ta shiga da sallama a bakinta , jin daddaɗan muryarta yasashi lumshe ido yace "wlkslm Yah Habibaty "hakan yasa tayi murmishin da fararen haƙwaranta suka baiyyana ta nemi guri ta zauna , Ammar ya taso daga kujerar da yake yazo wacce take zaune a hankali yace "yanzu na zamo mijinki babu abinda bazan iya yi ba " waro ido tayi kana tace "ba dai komai ba sbda kai ba muharra...ya haɗe bakinsu guri ɗaya ya ƙarasa mata yace "nine muharraminki so ya kamata ki dai daita maganarki "tsit tayi daya saketa ta galla masa harara , ƴar aiki ce ta kawo masa su drinks da kayan ƙwalama ta fice ,Nisha ta miƙe tare da cewa "zan iya tafiya ?"no Ammar yace "yana zuba juice a kofin glashi , tsayawa tayi cak ita bata dawo ba kuma ita bata tafi ba , zaki je ki gaida Ummina yau "banyi shawara ba "Nisha ta faɗa a taƙaice ,dama ba saikinyi ba ai umarni ne "Ammar ya faɗa yana kallonta ,Nisha dake tsaye tana nazarin abin da zatayi masa yaji haushi sai kuma ta tino ai zai iya gayawa mahaifiyarta tunda suna waya da ita , ta dawo ta zauna ta cika tayi fam kamar zata fashe...!
Wanan littafin na kuɗi ne ,akan farashi mai sauƙi #200 ɗari biyu ne kacal, zaki iya turo da kuɗinki ta wanan account ɗin 3175689751 Zainab Habibu first bank ,ko hoton katin waya ta mtn ɗina , ta wanan number 08141799224 ƴan Niger kuyi magana ta wanan number 84506476 , karku manta siyan nagari ...💃.
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: ƘANIN UBA
Dan Allah idan baki siya ba kada ki karanta , na kuɗi ne ɗari biyu kacal 08141799224.


P 11-12
Yace "yanzu zamu tafi ?"hararsa tayi kana tace "oho "Mommah dake shigowa taji amsar da Nisha take bawa Ammar ta gallama mata harar , Nisha suna haɗa ido ta sunkuyar da kai ƙasa ,Mommah ta ajiye wani plet mai ɗauke coffee a ciki , wani baƙinciki ne ya tokare zuciyar Nisha a ranta tace "duk ƴan aikin gidan sai ta wani kawo da kanta ko mai ya kawota oho "har Mommah zata fice Ammar ya cire wasu kuɗaɗɗe masu yawa ya miƙe tare da bawa Mommah , cikin in -ina Mommah tace "kabarshi haba kullum ana hidima damu a'a bazan karɓa ba ,a can ƙasan zuciyarta kuwa adu'a take Allah yasa kar Ammar ya mayar da kuɗin nan Allah yasa rabonta ne , dawowa Ammar yayi ya zauna Mommah ta fice zuciyarta cike da takaicin tauye kanta na rashin karɓar kuɗi , kasancewa yaga lokaci ya ƙure ya miƙe tare da zura hannunsa a aljihu ya ciro kuɗin da yaba Mommah ya miƙa mata , banzan kallo tayi masa ta shige ciki , ashe Mommah na leƙensu tana isowa shi kuma ya fice da mota ta sharara mata mari ,ta ƙara da cewa "ke wacce irin ƴar baƙinciki ce ?"arziƙin yazo mana har gida amma ki koresa ?"riƙe gurin marin Nisha tayi tana kallon Mommah cike da mamaki ta wuce "side ɗinsu tana shiga ta faɗa kan anty Pooja dake dane-dane a waya , ajiye wayar Pooja tayi tace "mai kuma ya sake faruwa ?"Nisha na kuka tace "anty Pooja Mommah bata so...Pooja ta rufe mata baki tace "kul my lil sis karki ƙara cewa "Mommah bata sonki sbda babu uwar da zata haifi ɗa ta tsanesa "banƙaɗo labule Mommah tayi tana haki tace "wlh kikace idan kikayi auran ma haka zakiyi wlh sai nayi bala'in saɓa miki "ta juya fuuu , rungume juna sukayi Nisha da Pooja .
Ammar na komawa gida kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa yana shiga ya zube kan

5 / 18