Author : Zainab Habib Category : Romance
da kuka "kamo hannun Ummi Abba yayi ya wuce da ita babban palonsu ya zaunar da ita ,kana yace "wanan fa zubar da girma ne ,idan wani abun ne ya faru bazaki sa ayi miki kiranta ba ?"hawaye Ummi ta share har zatayi magana sai kuma ta fasa ,ta ɓige da cewa "kaje ciki ka huta "miƙewa sukayi a tare Abba ya shiga bedroom ɗinsa ya zauna kan bed Ummi ma ta zauna tare da kai hannunta kan nasa "haba kekam ko hutawa banyi ba ko ance miki tuwo ne "Abba ya faɗa ya kallon Ummi shima a halin yanzu yana da buƙatarta amma babu hali ,hmm Ummi tace "kana ta miƙe tana jin zucitarta na tafarfasa a halin yanzu ta riga da ta yanke shawarar da zuciyarta ta bata , harta kai bakin ƙofa Abba ya kamo hannunta tare da cewa "kiyi haƙuri na sani bana baki haƙƙinki inada larura ne "dariyar yaƙe Ummi tayi kana tace "Allah ya baka lafiya tasa kai ta fice .
Tunda Ummi ta fita Nisha ke rakuɓe a palo kan tails tana kuka idan ka ganta zaka rantse marainiya ce ,bayan anyi salhar magrib Ammar ya shigo kasancewar bai san Abba ya shigo ba hannunsa riƙe da takarda da biro har ya ɗora kan table zai fara rubuta sakin da Ummi ta buƙata yaji wayarsa na ring da sauri ya fice sabda yaga Abba ne mai kiransa ,ita dai Nisha bin takardar tayi da ido a zahiri tana buƙatar sakin nan .
Yana zuwa baiga kowa a palo ba ya wuce bedroom ɗin Ummin ya fara nocking "waye "Ummi tace "murya irin ta mai kuka "nine Ummi Abba ne ya kirani "bayan ban ɗakin yana ɗakinsa "Ummi tace "tare da komawa ta zauna , kai tsaye ɗakin Abba Ammar ya shiga tare da sallama , amsawa Abba yayi ya kalli Ammar yace "my son akwai abin dake damunka "no Abba kawai rayuwarce "Ammar ya faɗa yana ɗage kafaɗa , rayuwa kuma !mai ka nema ka rasa kuɗi sai dai ka ɗiba amma zakace rayuwa ?Ammar daya rasa makama yace "am sorry dad Abba yace "ina fatan dai amaryar lafiya ko ?"eh Abba Ummi ce dama tace "sai dai in saketa "cewar Ammar ,waro ido Abba yayi kana yace "har wane laifi ta aikata muku haka da zaku yanke wanan tsatsauran hukuncin ?Ammar zai yi magana wayar Abba ta fara ruri , ɗagawa yayi gami da sallama daga can ɓangaren akace "barka da cin primary election "farinciki da annashuwa ya baiyana a fuskar Abba sabda suna jiran sakamako ne dama Abba ya hau haɗa kaya zai koma gurin boka ,riƙe hannunsa Ammar yayi kana yace "Abba wai lafiya naga sai dariya kake ?"naci zaɓen farko saura na gaba "Abba ya faɗa yana riƙe da jaka a hannunsa , ƙarɓa Ammar yayi suka fito Ammar ya kuma cewa "Abba ɗazu fa kazo ko hutawa bakayi baaaqqq a "dafa kafaɗarsa Abba yayi kaik ,,oo,,,,uu, na yace "ai babu batun hutu yanzu kam inajin ma idan na tafi sai ke un ganni zadai mu dinga waya "Abba ya shige bedroom ɗin Ummi samunta Ammar shikuma ya fice ,samunta yayi kwance a kan sallahya hawaye na gangarowa daga idonta ya durƙusa tare da cewa "wai dan Allah me kika nema kika rasa a gidannan ci ko sha ko tufafi ?miƙewa Ummi tayi kana tace "na gaji da zaman rashin walwalah kai sam baka san haƙƙin matarka ba ,alhalin da ba haka kake ba "murmishi Abba yayi dan ya kawar da maganar ya ɓige da cewa "albishirinki munci zaɓen farko "ko kallonsa Ummi batayi ba ta kawar da kai kana tace "kuma wlh yarinyar nan sai ta bar gidannan koda tsiya ko da arziƙi "cikin kakkausar murya Abba yace "to ni nace sai ta zauna "Ummi tace "zamugani "ta fice ta barshi a gurin ,fitowa yayi yana ƙwalawa Mheera kira amma shiru ,yasan dazarar ya dawo itace ta farkon yi masa oyoyo yau kam har yanzu bai ganta ba ,a fili yace "kodai ta tafi gidan Hajiya ne "bashida mai basa amsa yasa shi ficewa kai tsaye zuwa ɗakinta , yana tura ƙofar ɗakin ya hangota kwance cikin bargo ko kanta ba'a gani da sauri ya ƙarasa gareta yana kiran sunanta Mheera -Mheera amma bata amsa ba ,ɗan bubugata yayi cikin yanayin rashin lafiya ta buɗe idonta da take jin zafi tace "Abba yaushe ka dawo ?"bakida lafiya ne Mheera kunje hospital kuwa?mai yasa Umminki bata faɗamin ba ?"ya dinga jero mata tambayoyi tsabar zazzaɓin dake damunta bata iya bashi amsa ba sai cewa da tayi ɗazu ne fa na farajin ciwon kai kuma yanzu nasha magani "ajiyar zuciya Abba ya sauke kana yace "to Allah ya baki lpy ko a kirawo doctor ne ?no Abba nasami lpy "Mheera tace "tana ƙoƙarin tashi ta zauna ya ajiye mata kuɗi a gefenta ya fice ransa a ɓace , har zai koma ɗakin Ummi ya tuna boka fa na jiransa yau babu batun jirgi a mota zashi dukda jirgi yafi sauri amma kansa a kulle yake .
Sunyi tafiya mai nisan gaske sanan suka iso ,kai tsaye gidan boka suka wuce ,cikin sa'a yaga babu layi ya shiga ,yana shiga bayan ya zauna boka yace "kaga aiki ya fara ko ?saura na ƙarshe "eh kam nagode sai dai wani hanzari ba gudu ba boka "ina jinka Boka yace "wa Abba "Boka akwai matsala mata ta tana burin korar amaryar ɗana gashi ba'a gama aiki ba "dariya boka yayi kana yace "ai ɗanka bai kusanceta ba amma dai mun hango jininka kuma zamuyi amfani dashi "waro ido Abba yayi kana yace "kana nufin yau kwanansu takwas amma babu abin da ya shiga tsakani ?"eh Boka yace "Abba ya ƙara da cewa "to a ina ne jinin nawa yake ?"kecewa da dariya Boka yayi kana yace "ai mun gama sai jinin na biyu da mukeso shi wanan yana ƙwari zamu cireshi wato nanda sati uku "kasancewar Abba ya sami biyan buƙatarsa yasa shi miƙewa yana washe baki ,ya sanya hannu a aljihu ya ciro wasu bandir bandir na kuɗi ya zube gaban boka yace "wani abun ma sai munci "suka saka dariya yayi godiya ya fice , yana komawa gida already dama kafin Bashir ya tafi ya nemo masa wata balarabiya ta dinga ɗebe masa kewa ,yana shiga ya sameta zaune da mini skert a ƙugunta daga samanta kuma rigace mai shara shara sosai tayi mata kyau sai dai ana ganin ilahirin komai na jikinta yana ƙarasowa ta rungumeshi tana wani karairaya tare d bashi kiss a kumatu ta kamo hannunsa suka ƙarasa bedroom ,da kanta ta cire masa kaya ta fara bin ko ina na jikinsa da tausa shiko ya wani baje kamar ɗan shayi .
Tsokaci matan aure gareku .
Tabbs nasani wani lokacin idan namiji ya ɓata maka rai kanajin ya fitar maka sam ,to ga shawara misali-kuyi duba da Ummi bataga damar karɓar haƙƙinta bane dalili kuwa da taga dama lokacin da zata rikita Abba ya bata haƙƙinta bai sani ba ,ba boka ba koma waye mancewa zaiyi sai ya dawo dai dai zai tuna .
Abin da nakeso ku gane shine kamar Ummi ai bata iya tarai raya ba ,sbda yanayinta kamar daga ƙauye take .
Ƙamshi -shima yana taka muhimmiyar rawa ga ma'aurata.
Kwalliya-kullum ya kasance kina cikin kwaliya tabbas wanan shima wani sirri ne. akwai lokacin da mai gida zai dawo ransa a ɓace , pls sis karki ɗaure taki fuskar ki san inda zakiyi ki shawo matsalar ta hanyar yi masa abubuwan da kikasan yana so.
Babban abu kuma -kula da danginsa da mahaifiyarsa karkiga dan ya auroki idan bai yiwa mahaifiyarsa abu ba kice babu ruwanki , kemafa mai sashi a hanya ce ,kice wane baka yawan kiran mama ko kuma kisa yayi mata alkairi ,kema idan kina dashi kiyi mata , idan kuma dangin mijin ne basa sonki ki dage da adu'a kina gayawa Allah da sannu Allah zai amsa adu'arki ,ina fatan zaku fahimceni.
Wayar Abba ce ta fara ring ,budurwar dake zaune a gefensa mai suna Shukra ta muƙo masa ,ganin number Bashir ne yasa Abba sakin dariya yace "ɗan iska sai yau zaka tayani murnar "ya ɗaga wayar ,daga can ɓangaren Bashir yace an gaida gwamna mai zaman kansa ya hutu ya jindaɗi gami da cewa "yaushe zaka dawo ?Abba dake kwance yace "ai zankai one week ko fima ban dawo ba wlh "waro ido Bashir yayi yace "to Allah ya kaimu ya kashe wayar.
Tunda Ummi taga tafiyar motar Abba ta tsaya jikin wundo tana kuka kasancewar ta leƙa taga Mheera kwance babu lafiya ga Abba kamar wanda baya haiyacinsa ,fitowa waje gidan tayi taga ma'aikatan gidan kowa na harkar gabansa yake ,ta dawo palo ta zauna ,sai kuna ta janyo wayarta ta kira lambar Ammar , kira ɗaya ya ɗaga tare da sallama yace "Ummi "kana ina?"Ummi tace "rai a ɓace ,wlh nayi nisa amma zuwa mgrib zan dawo "kashe wayar Ummi tayi ta zuba tagumi , sallamar da taji ne yasa ta ɗago kanta ta kalli waye Alhaji bashir ta gani tsaye yana jifanta da wani murmishi mai wuyar fassaruwa , tace "barka "shima barka yace "kana ya zauna tare da ce mata ina yini "lafiya Ummi tace "shiru ya wanzu na ƴan wasu mintuna Bashir yace "kin ganeni kuwa ?"murmishi Ummi tayi kana tace "na ganeka man kaine Bashir ko ?"eh nine tabbas dama wata magana ce ta kawoni amma kafin nan zan ɗan yi miki tambaya "to Ummi tace "tare da tattara nutsuwarta ta kallesa "naga kamar kina cikin damuwa ko ?"Bashir ya jefowa Ummi tambaya ,tsintar kanta tayi da faɗa masa damuwarta tace "kasan yau Governor ya dawo ko jimawa baiyi ba ya tafi gashi yarinya babu lafiya "Ummi ta ƙarashe maganar tana share hawaye kasancewarta mai saurin kuka .
"Allah sarki amma ga shawara idan bazaki damu ba "Bashir ya faɗa yana dube dube alamun rashin gaskiya " ina jinka Ummi tace "ywwa dama nace mai zai hana tunda shi mai gidan baya nan inzo in dinga ɗebe miki kewa ?"innalilahi Ummi ta ambata a zuciyarta tare da miƙewa tana aatagfirullah ta shige bedroom ɗinta tasa key tasan idan taci gaba da zama sheɗan kugu ne zai iya kitsa mata wani abun.
Ganin ta shige ɗaki yasa Bashir muƙewa tare da cewa "mtsw zata bani matsala wanan ya fice .
Zuwa bayan sallahar isha'i Ammar ya shigo ya sami Ummi a parlo ita da Mheera kasancewar ta ɗanji sauƙi ta fito kasa haɗa ido da Mheera yayi ya juyar da kansa ga Ummi itako tunda ya shigo idonta na kansa mamaki ne ke isarta , Ummi tace "maza ka saki waccan ƴar matsiyatan ta wuce ta tafi gidansu "waro ido Ammar yayi yace "Abba fa ya hana Ummi "mari Ummi ta zuba masa kana tace "wato ni baka jin maganata har da yaushe kayi riƙar da zaka dinga ƙetare umarni na ?"to walh kafin safiya kar in buɗe ido in ganta a gidannan "miƙewa Ammar yayi rai a ɓace ya tafi part ɗinsu ya sami Nisha kwance a palo kan sofa tana kallo a wayarta ,ya nem guri ya zauna kana yace "nisha ina matuƙar sonki bansan mai nayiwa Ummi ba take son rabani dake "shiru Nisha tayi bata ko tanka masa ba ,ya ƙara cewa "ni banma san inda ake rubuta saki ba "dariya Nisha tasa sai kuma ta gimtse fuska ...!
Afuwan yarona babu lafiya daga asibiti nake wlh jiya ma haka amma da sauƙi kuyi hkr.
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: 27-28
"Alhaji ne ya rasu jiya "innalilahi suka dinga mai maitawa kowanne idonsa na fitar da hawaye suka ɗauko mayafi sukabi bayan Mommah da ta juya zuwa bedroom ɗinta , itama mayafin ta ɗauka suka fito Imaam dake shigowa yanzu ya tsaya sbda ganin Mommah da Nisha da kuma Pooja ko wacce da mayafi ga idonsu yayi ja cikin tashin hankali yace "mai ya faru ?"Nisha na kuka tace "Alhaji ne ya rasu ɗazu aka bugowa Mommah waya "salati Imaam yayi kana yace "Allah ya gafarta masa ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙawa Mommah yace "ku hau mota "karɓa tayi suka wuce , suna fitowa daga gidan cikin sa'a suka sami abin hawa bayan sun shiga motar ta fara tafiya watar Mommah ta fara ring wayar na hannun Nisha hakan yasa taga mai kiran an rubuta Hajiya Faɗimatu ta miƙawa Mommah , karɓa Mommah tayi tare da amsawa ta kara a kunnenta tana murmishi , Mommah tace "yanzu ina mota ne bari idan na sauka zan kiraki "tom Hajiya faɗimatu tace "Mommah ta ajiye waya.
Mai karatu idan bai mance ba Hajiya Faɗimatu itace "Mommah tasiyi gida a gurinta.
Suna isowa mai motar yayi parking suka fito tare da bashi kuɗinsa , ƙofar gidan cike yake da mutane ƴan zaman makoki suka kutsa kai cikin gidan , gidane madai daici baza'a kira gidan da masu kuɗi ba sbda ginin ƙasa ne ma yana ɗauke da ƙofa wacce ita zata sadaka da cikin gidan , wani ɗaki Mommah ta shiga ta zube gaban wata dattijuwa tana kuka tana cewa "Mami shikenan Alhaji ya tafi ?yaushe rabona da inzo watana biyar "wacce aka kira da Mamin ta goge hawaye tace "ni babu abin da zance miki Khadija sai dai adu'ar shirya sbda shi kansa Alhajin kafin ya rasu ya dinga ambaton sunanki "tabbas hakan bai yiwa su Pooja daɗi ba suka fashe da kuka sun san tabbas Mommah bata ga miciji da talaka bata so su haɗa inuwa ɗaya.
FARKON LABARI.
Gidan Alhaji muhseen yana da ɗa ɗaya mai suna Sabir -Sabir ya taso cikin gata da nuna kulawa tun daga aihuwar Sabir matarsa bata sake aihuwa ba ,gata suka dinga nuna masa har ya isa sawa a makaranta , kwanci tashi babu wuya a gurin Allah ya kammala pramari ɗinsa ya shiga sakandiri cikin hukuncin ubangiji ya kammalah ya shiga ta gaba daga nanne Allah ya haɗashi da budurwa mai suna Jalila -Jalila fara ce doguwa bata da ƙiba gashinta dogo ne har gadon baya kasancewarsu larabawa.
Suna soyayya har ta kai ga an fara maganar aure .
Ba tare da ɓata lokaci ba akayi auran Sabir da Jalilah sosai ko wanne yake burin farantawa ɗan uwansa , watan ta uku da aure Allah ya bata ciki suka ɗauki son duniya suka ɗorawa wanan ciki gata iri iri har Allah yasa cikin yakai wata tara ,a ranar daya cika wata tara da kwana goma ne Jalila ta tashi da ciwon mara da baya ,suna ganin abin kamar wasa har sai da takai ga ƙarfinta na neman ƙarewa suka ɗunguma zuwa asibiti , suna ganin halin da take ciki likitoci sukace aiki za'ayi mata , hankalin Sabir dana iyayensa ya matuƙar tashi suka duƙufa roƙon Allah kwatsam Allah ya kawo aihuwa gadan -gadan ta sumɓulo ɗanta balarabe fari kyakkyawa mai kama da Sabir , bayan an gama gyarata a asibiti suka dawo gida kai tsaye Maman Sabir ta zo gidan su Jalila lokacin kwana biyar da aihuwa ta buƙaci tafiya da ita , kasancewar mahaifiyarsa ce bai hana ba amma da ya ƙuduri aniyar hanata zuwa gida , ta sami kulawa ta ɓangaren mamanta da iyayen Sabir , ranar suna yaro yaci sunan Abdullahi suna kiransa da Imaam -Imaam ya taso cikin so da ƙauna sun ɗauka daga Imaam bazasu ƙara samun aihuwa ba sbda Jalilah ta kai shekara shida ko ɓatan wata bata yi ba , gashi Imaam yayi girma sosai an sanyashi a islamiya , wata rana da safe Sabir ya tafi gurin aiki ta shirya domin kai Imaam makaranta har ta fito taji amai ya taho mata ,da gudu taje ta dinga kwarara wa har tana ƙwallah ta nemi guri ta zauna tana mayar da nunfashi tashi ɗaya taji sanyi takeji jikinta har ɓari yake , wayarta ta janyo ta kira Sabir tayi masa bayanin halin da take ciki , da sauri ya ajiye abin da yake ya hayo mota ya dawo gida ,ya sameta kwance a kan gado tana rawar sanyi shi kuma Imaam na zaune da kayan wasa a gabansa , shafa kansa Sabir yayi yace "ɗan albarka taso in kaika makaranta "kuka Imaam yasa yana nuna mahaifiyarshi yace "Ummu babu lafiya "tausayinsa Sabir yaji dan haka ya cire masa kayan makarantar ya sanya masa na gida , Sabir yaje kusada Jalilah yaji jikinta yayi zafi ɗau , a tsorace ya fice ya tsaya a ƙofar gidansu yana jiran mai mota , cikin ikon Allah mai mota yazo wucewa Sabir ya tsayar dashi yace "asibiti zaka kaimu "mai mota yace "a fito da mara lafiyar amma wanne asibiti ? An Nass special hospital.Sabir yace "tare da shigewa gida da gudu ya kinkimo Jalilah yasa a mota ko hijab ɗinta bai ɗauka ba , sunyi tafiya sosai sanan suka iso asibitin har ciki ya shiga dasu yayi parking Sabir ya ɗaga Imaam dake cinyarsa ya ciro kuɗi yaba drivern tare da buɗe murfn mota suka fito , wata likita ce ta zo ta kamo Jalilah suka shiga ciki , bayan an bata gado wani likita ya shigo yana tambayar Jalilah abinda ke damunta , ce masa tayi iya amai ne sai jin sanyi "malam ga roba ka bata tayi fitsari kuma zamu ɗibi jininta "likita yace "wa Sabir , to Sabir yace "ya zaunar da Imaam a kujera ya riƙe hannun Jalilah sukaje toilet tayi fitsarin suka fito , likitan ya shigo da abin ɗiban jinin ya karɓi fitsarin ya fice ,a na'urar gwaji yasa yaga alamar ya nuna ciki ne da Jalilah , likita ya miƙe da takardar sakamako ya wuce ɗakin da su Sabir suke , yana shiga ya muƙawa Sabir yana murmishi ya fita , Sabir na dubawa yaga ai ciki ne har na tsawon wata ɗays yayi wa Allah godiya , ko da Jalilah ta tashi taji albishir ɗin da akayi mata taji baƙinciki sosai ta dinga kuka tana cewa "Sabir sai dai a cire mata wanan cikin bata sonsa , faɗa suka dingayi da Jalilah har ya kira iyayensu ya faɗa musu gasu a asibiti , ba'a ɗauki lokaci