Author : Zainab Habib Category : Romance
Munim basu zarce ko ina ba sai wani gurin cin abinci mai cike da mutane iri-iri , Nisha ta kalli Munim tace "mai za'a kawo maka ?"kashe mata ido ɗaya yayi kana yace "gurasa "kwai kwayon maganarsa tayi tana dariya ,aka kawo masa takardar zabar abinci , cikin sauri Nisha tace "gurasa zaka kawo mana "ok mutumin yace "tare da wucewa ,sai gashi ya dawo da gurasa a hannunsa , ya ajiye a gabansu .
Bayan sun gama ci ne Munim ya zuba tagumi Nisha tace "haba Munim ya zaka dinga sa kanka cikin damuwa "shiru yayi sai kallonta da ido da yake yi ,har ta kamo hannunsa suka nufi , wani guri mai ciƙe da furanni masu kyau gunin birgewa , juyi Nisha ta dingayi da hannunta tana ɗan rawa , ganin Munim yaƙi magana ya sanya tayi tsalle ta kamo bakinsa ta yi masa kiss , wani irin yanayi Munim ya tsinci kansa a ciki mai wuyar fassara ,dan danan yaji jikinsa ya mutu sabda karo na farko kenan da wata ƴa'mace ta sumbacesa a duniya kuma a iya tsawon rayuwarsa , lumshe ƙananun idanuwansa yayi tare da kwantar da ita a kan teburin da ke gurin ya yi mata rumfa da ƙirjinsa a hankali yace "i love you "wani irin sanyi haɗi da iska mai ƙashi hhh irin tasu ta masoya Nisha taji , ta rungumeshi ya ƙam ƙameta yana cewa "ashe haka soyayya take ?"jin tudun boobs ɗinta ya sanyashi saurin miƙewa a hankali yace "maza tashi "cikin rashin fahimta Nisha ta miƙe tana kallonsa "zaki aureni ?"zirr taji abu ya tsirga mata daga tafin ƙafarta har tsakiyar kanta ta lumshe ido kana tace "mai zai hana muje mu sami limami ya ɗaura mana aure " murmishi Munim yayi kana yace "ai bamusan kowa ba "jan hannunsa Nisha tayi suka nufi bakin wani tsararrren masallaci mai kyau da ƙawatuwa, suka nemi guri suka zauna kasancewar sunji gurin shiru babu kowa .
Ina jinka tunda bamu samu kowa ba ka bani labari " uch "Munim ya faɗa tare da cewa "zaki famomin ciwon da na daɗe ina ɓoyewa amma tunda muka kusan zama ɗaya ni dake kuma ma'aurata dole in sanar dake asalin labarina .
Sunana Munim ,muna zaune da mahaifiyata a DUBAI sunan yayana da na rasashi sbda son duniya Imaam " gaban Nisha ne ya bada rasss har wani girgiza tayi , Munim yaci gaba da cewa "sunan matarsa Khadija mahaifiyarmu ta rasu tun tuni haka mahaifinmu ya rigata mutuwa , a lokacin da muka rabu da yayana sunan matarsa Khadija dan yayi aure har sun haifi Abid da Asim "zai ci gaba da magana yaga Nisha ta ɓingire a gurin sumammiya ya hau salati tare da kwarara mata ruwan dake hannunsa ta buɗe ido, sai kuma ta fashe da kuka tana cewa "ko kwana bazamuyi ba zamu koma wlh gidan mu zan koma " ban gane ba Nisha mai kuma ya faru ? Nisha dake kuka tace "kaine *KANIN UBA..* sai kuma tayi shiru , cikin rashin fahimta tace "Imaam shine mahaifina !! zaro ido Munim yayi kana yace "Allah na gode maka daka haɗani da ɗan uwana ,sai kuma ya share hawayen dake kwaranyo masa ,ya rungume Nisha , lokacin ƙarfe huɗu na yamma kasancewar duk a ranar dasuka tafu abubuwan suka faru yasa Nisha cewa "mu bari zuwa gobe mu tafi "no yanzu ai baza'a rasa jirgi ba idan babu jirgi akwai mota "Munim ya riƙe mata hannu suka miƙe tare da zuwa gurin hiran jirgi suka ga wayam babu shi babu dalilinsa , suka koma gurin motoci suka hau zuwa DUBAI , basu wani yi tafiya mai nisa ba Nisha ta fara bacci har da rungume Munim , sunyi tafiya mai nisan gaske dan basu isa da wuri ba sai ƙarfe ,goma na dare suka isa , suna sauka Munim ya tashi Nisha kana yace "bani da kuɗi "cirowa tayi a hand bag ɗinta ta bashi yaba mai mota suka fito, har sun fara tafiya Nisha ta kalli Munim tace "inada t ambaya ?"ina jinki "Munim yace "yana kallonta "shin da naga baka cikin haiyacinka har a bola kake kwana yanzu kuma naga ka koma normal ?"nisawa Munim yayi kana yace "lokacin da mahaifiyar mu ta rasu Imaam ya zo ya sameni a ɗakin , ya ƙwala min wani ƙarfe shine yai sanadiyar rashin lafiya ta , kuma lokacin da nayi shekaru biyar da ciwon na haɗu da wani likita yayi koƙarin taimaka min ni kuma naƙi dan ya cemin inhar na sami abin da ya sanyani farinciki to komai nawa zai dawo , kinga kuwa kece silar komai "ba tare da Nisha tayi magana ba taja hannunsa suka ci gaba da tafiya , kasancewar da gurin da aka saukesu da gidan nasu babu nisa ,yasa Nisha nunawa Munim gidan tace "kaga gidan mu nan "waro ido Munim yayi yace "yaushe Imaam yayi kuɗi haka wace sana'a yake ?"ko kulasa Nisha batayi ba ta fara nocking , leƙowa mai gadi yayi kasancewar anguwar mamaye take da haske ta ko ina yasa mai gadi kallon ,fuskar Nisha yace " oyoyo alhamdulilh "buɗe mata yayi ta shiga Munim ma ya shiga kai tsaye suka nufi cikin gidan , sallama sukayi ,sukaji shiru babu wanda ya kulasu ,bubuga ƙofar Nisha tayi Pooja da bacci ke idonta ta miƙe tare da ɗauko ɗa kwali ta ɗaura ta fito palo ta buɗe ƙofa , gani tayi kamar gizo fuskar Nisha tayi mata ya sata zata ruga da gudu Nisha ta rungumeta ta baya tana cewa "anty Pooja ki yafeni ga Munim "ku shigo Pooja tace "duk da ɓatan Nisha da wulaƙancin da ta yiwa Pooja bai sa ta juyawa ƙanwar tata baya ba , suka shiga ciki tare da zama kan sofa , da gudu Nisha ta fara bubuga ƙofar su Mommah tana cewa "Nisha ta dawo "Allah sarki abinka da iyaye da gudu Mommah ta buɗe ƙofa tare da fitowa palo taga Nisha zaune ta kalli inda Munim yake tace "Mu mu mu Munim !!! fuskar Munim ɗauke da Murmushi yace "Khadija "Mommah tace "na'am , Imaam ma ya fito yana shirin zama sukayi ido biyu da Munim ,jikin Imaam na rawa yace "sai naga kamar ɗan uwana Munim"eh zahiri Imaam shine "Pooja ta faɗa tana dariya , kuka Imaam ya fashe dashi yana cewa "na cuci kaina na cuceka na zaɓi son duniya fiye da zumunci ,har Imaam ya matso kusa da Munim zai durƙusa Munim ya riƙe hannunsa tare da ce masa haba mana Imaam Alllah ya yafe mana nayi farincikin haɗuwar mu "daga nan Pooja taba su Mommah labarin inda suka haɗu da Munim a hanyar islamiya.
Kuka Nisha tasa tare da durƙusawa gaban Mommah tace "dan Allah ku yafemin "mun yafe miki Mommah tace "tashi Allah yayi miki albarka , ko da taje gaban Imaam zata roƙesa ya dakatar da ita tare da cewa "ni zan yi miki godiya tunda har kika sadani da ɗan uwana....!
Ya kuke gani ?
[06/12, 2:53 PM] Mom Islam Ce💃: 53-54
Abid da Asim da sukaji hayaniya tayi yawa suka fito a tare suna mutsike ido ,ganin Nisha da wanda basu gane ba amma Asim yana yiwa Munim kallon sani ya sanya Asim cewa "kamar na gane ka ?"ya nuna Munim da yatsa ,eh zaka sanyi Munim ko ?"da sauri Asim yace "kawona sai kuma ya ƙarasa da kuka ya rungume Asim , suna zaune har ƙarfe ɗaya tayi ,Imaam yace "hirar nan bazata ƙare ba kowa yaje ya kwanta sai zuwa safiya "haka suka tashi Munim ya nufi ɗakin su Asim suka kwanta cike da farinciki .
A ɓangaren su Nisha ma haka su kam kusan kwana sukayi suna hira dukda a yau ta gudu kuma ta dawo , Pooja tace "wato ke da ƘANIN MAHAIFINKI kike son yin soyayya ko ? Nisha tayi murmushi lokaci ɗaya kuma murmushin nata ya ɓace tace "Anty Pooja Allah ya jarbceni da son ƘANIN UBA na idan har ban auresa ba zan iya mutuwa "a zabure Pooja ta kalleta kana tace "wanan wane irin banzan magana ne ?"kina abu kamar ba musulma ba ,ya kamata ki dingayin magana a cikin muhallinta so wanan zancen ma kada ki bari Mommah taji ko Imaam "kuka Nisha ta fashe dashi tana cewa "ni ba'a sona "Pooja cikin fushi tace "da alamu kanki ya fara kuncewa da zaki dinga abu kamar wawuya "daga nan sukayi bacci .
Washe gari su Mommah ne suka fara fitowa bayan sunyi sallah suka zauna a palo ,sai ga Munim da Asim da Abid sun shigo suka gaishe su , bayan sun amsa ,Imaam yace "wai yaranan basu tashi ba ne ?"bai gama rufe baki ba suma suka fito sanye da Hijab har ƙasa suka durƙusa suka gaishe da Imaam da Mommah , bayan sun gaisa suka nemi guri suka zauna .
Zuwa ƙarfe goma 10:am su Mommah sun gama break fast a dining tana shirin ajiye cokali taji wayarta na ring ,dubawa tayi tare da sakin murmushi a fili tace "hajiya Faɗimatu na "ta miƙe tare da barin gurin ta wuce bedroom ɗinta , ɗagawa tayi tare da sallama kana tace "Allah ya taimakeki Hajiya kwana biyu na jiki shiru "daga can ɓangaren Hajiya Faɗimatu tace "hamm bari kawai wlh aiyuka ne aukai min yawa amma yanzu idan babu abin da kike kizo "jiki na rawa Mommah tace "to tare da ɗaukar mayafi ta fito kai tsaye inda taji muryar su Imaam na hira nan ta nufa , har da ɗan durƙusawa tace "Imaam Hajiya Faɗimatu babu lafiya yanzu zani "to a dawo lafiya Imaam yace "mata Munim ko ya girgiza kai a zuciyarsa yace "wanan matar har yanzu bazata sauya halinta ba "su Pooja suka ce a dawo lafiya ta fice .
Kai tsaye bakin titi Mommah ta nufa ta tari mota zuwa anguwar Hajiya Faɗimatu da tayi mata kwatance , cikin ikon Allah mai mota ya kawota haɗaɗɗiyar anguwar da babu mutane da yawa ,ta biya mai mota kuɗinsa ,ta ƙwanƙwasa ƙofar , mai gadi ne ya fito ya buɗe mata zata yi masa bayani yace "ai Hajiya tayimin ki shiga , shiga Mommah tayi da sallama ta tura door ɗin katafaren palon Hajiya Faɗimatu ...Abin da tagani ne yayi matuƙar girgizata sbda ita a duniya bata taɓa ganinhaka ba...
Ganin Hajiya Faɗimatu tayi tsirarara kanta ɗaure da jan ƙyalle bakinta yayi ja sosai da wata ƙwarya a hannunta , tsoro ne ya kama Mommah cikin takaici da nadama ta fara faɗin o o o wlh nafasa bazan sake ba dan Allah kiyi haƙuri zan biyaki komai naki ".
Magana Hajiya Faɗimatu ta fara da muryarta wata iri mai wuyar gane kuwwarta ,har Mommah zata gudu Hajiya Faɗimatu tace "ai mun riga da mun saki a ƙungiyarmu dole ki bi dukan dokokin mu "mun baki kuɗaɗe mun baki gidaje dan haka kin shiga ƙungiyarmu , a halin yanzu jininki muke buƙata da shi zaki biyamu "waro ido Mommah tayi ido cike da hawaye tace "na shiga uku na lalace ni waye jinina bani da yara "tsawar da aka daka mata ne yai sanadiyar ɗaukewar jinta na wasu lokuta can kuma taji ana cewa "kin amince ? ja da baya Mommah ta fara Hajiya Faɗimatu ko tana tuntsirewa da dariya .
Ficewa Mommah tayi da gudu bayan ta bangaje mai gadi , Allah ya taimaketa tana fita ta sami mota ta hau sai anguwarsu , ana sauketa ta biya mai mota kuɗi bata ma san nawa ta bashi ba ,yana cewa "Hajiya ga canji ina ta buɗe get ɗin gidansu harda taka ƙafar mai gadi ta wuce da gudu ciki , tana shiga ta sami Imaam da Munim su biyu a zaune ta zuba a gurin ragwab tare da fashewa da kuka tana cewa "wayooo Allahna na shiga uku ku taimaka min ".
Kallonta Imaam yayi kana yace "ba anguwa kikaje ba mai kuma ya faru ?"Mommah da taji takaicin maganar Imaam tace "bansani ba "Munim yace "yi haƙuri anty mai ke faruwa ne ? labarin kaf abin da ya faru har sanadin gidan da suke ciki Mommah taba Munim labari da abin da Hajiya Faɗimatu tace "mata duk ta gaya masa ,a zabure Imaam ya miƙe kana yace "kice harda mu mun shiga uku " hararsa Mommah tayi kana ta shige bedroom ɗinta ta kifa kai tana kuka .
Zuwa dare Mommah ta kwanta bacci ,can cikin dare taji ana cewa "zan sha jini "a guje ta miƙe tare da buɗe ƙofa bata zarce ko ina ba sai ɗakin Imaam ta faɗa jikinsa tana cewa "wlh suka matsamin jininka zan basu "Imaam ya miƙe tare da kwaɓe fuska kamar zaiyi kuka shima ya fara jiyo maganar kamar na mace tana cewa "zansha jini "dagudu ya miƙe ya shige toile yana tunanin ya tsira ya fara ganin tsartuwar abu kamar jini ta jikin bango ,ya fara ihu yana cewa "taimako jama' a wlh gidansu na shigo " Mommah dake jikin ƙofar toilet ta sanya key a ƙofar Imaam ya dinga zunduma ihu dan shi kaɗai yasan abin da yake gani amma taƙi buɗe masa , har ƙarfe 12:30 na dare Imaam na ihu kuma Allah bai sa su Asim zasuji ba ,kaf adu'oin dake bakinsa suka ɓace masa yama rasa wane zaiyi ,daga ƙarshe ya fara faɗin lahaula wala ,la haula wala yana yi yana shan majina ,cikin ikon Allah abun ya ɓace "sai a lokacin Imaam ya sami damar jan ƙofar da ƙarfi Mommah dake tsaye batasan lokacin da hannunta ya murɗa key ɗin ba ta buɗe masa ya fito , yana fitowa ya fice a ɗakin ya koma palo , tare da wucewa toilet ya ɗauro alwalah ya fara gabatar da sallahar nafila .
Mommah kam jin komai ya lafa yasa ta kwanta a ɗakin Imaam bacci ya ɗauketa,
Washe gari Imaam a kan darduma ya kwana bai ma san lokacin da bacci ya ɗaukesa ba .
Asbha nayi iyalan suka tashi bayan sun dawo daga masallaci suka gaida iyayensu haka ma su Nisha .
…………………………………
Tun da Abba ya dawo daga tafiya yake nan-nan da Ummi , Ummi da bata gane inda ya dosa ba tace "ni kuwa ya maganar zaɓen ku ?ɓata rai Abba yayi kana yace "daga rana mai kamar ta yau karki ƙara yimin wanan maganar a sanadin son duniya Mheera ta rabu da martabarta , yanzu gashi ni banci riba ba , kafin in taho mukayi faɗa da Boka har cemin yayi inje zangani wai ,dama kansa yake yiwa aiki ba niba ,tun daga ranar muka raba hanya ,
A can na sami Bashir yana ganina ya fara kuka yana cewa "in yafe masa wai yasan ya cuceni "nidai ban san mai yayi min ba amma nace na yafe masa , yanzu bana fatan wani nawa ya shiga harkar dana shiga a baya , rungumeshi Ummi tayi tana kuka kana tace "alhmdulilah Allah muna yi maka godiya daka yimu a musulmai".
Washe gari ta kama monday bayan Mheera da Ammar da Abba da Ummi sun gama break fast Abba yace "mun yanke shawarar sanya ranar bikinku tunda mun ga kuna son junanku "a kunyace Mheera ta miƙe da gudu ta wuce nata side ɗiin tana dariya ,Ammar kuwa kunya ya kamashi sai murmushi yake , Abba yace "bandai nemi shawarar Hajiya ba amma mun yanke sati uku insha Allah "Ummi tayi farinciki sosai ,
Kwana bakwai da maganar Ummi ta fara gyara Mheera sosai , jiki da waje , kwana takwas da maganar Abba yaje ya sami Hajiya , itama farinciki ba'a magana tace "ni da na fara ma tunani sai nace kar inyi muku shishigi a lamuranku ashe kuma kunyi tunani "to masha Allah haƙiƙa nayi farinciki "Abba yace "masha Allah tunda kin amince Hajiya yau saura sati biyu kenan ko kuma ince kwana goma sha uku "to Allah ya kaimu "Hajiya tace "tana sanyawa Abba albarka ....!
*KANIN UBA*
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂
End end end
Lokaci na tafiya yayin da rayuwa ake samun ci gaba , ta ɓangarori da dama.
Kwanci tashi babu Wuya a gurin Allah , lokaci na tafiya kwana na ƙarewa ,
Ana i' gobe ɗaurin auran Mheera da Ammar Alhaji ya rakasu sabon gidansu wanda ya amsa sunansa, murna gurinsu ba'a magana ,kai idan ka gansu sai ka rantse sun daɗe da fara soyayya ,sbda kulawar da suke bawa junansu abin ya ƙayatar.
Mommah ce zaune a palo ido yayi luhu luhu da alamu kuka taci , Imaam dake zaune yace "Pooja jiya naji wani yayi sallama dake shin waye shi ?murmishi Pooja tayi kana tace "Imaam yau kwanan mu huɗu da haɗuwa "Abid yace "ai kuwa idan kina sonsa kice masa ya fito"rufe fuska Pooja tayi kana tace "toh Imaam "Mommah ta kalli Nisha cikin fushi tace "ke kuma da kika kashe auranki hankalinki ya kwanta sai ki koma zawarci " Munim dake zaune gefen Imaam yace "ayi haƙuri mu kaiwa Allah kuka "shiru ne ya biyo baya can kuma Imaam yace "kai ma Asim lokaci yayi da zaka fito da mata kai da Abid "Asim ne yace "ni dai har yanzu ban koma misra ba bare mu haɗu da ita "kul "Mommah tace "wlh ban lamunta ba inma zaka nemi mata a nan garin gara kaf ɗinku ku nema.
Bayan tafiyar Mommah Hajiya faɗimatu na tsaye aka kifota ƙasa , wani mutum ne ya fito jikinsa sanye da jajayen kaya yace "kin tona mana asiri hankalinki ya kwanta , dama mun faɗa miki wanan matar da kika kawo bazamu iya da ita ba ,mutanen kanta sunfi ƙarfin mu "Hajiya Faɗimatu na ja da baya tana cewa "kuyi haƙuru ku barni da raina "hahahaha "mutumin ya ttuntsire da dariya kana ya damƙo wuyanta yana cewa "kin bamu jinin mahaifinki kin bamu na babarki kin bamu na ƙanwarki baki da wanda zaki ƙara bamu yanzu jininki zmusha "wata irin razananniyar ƙara Hajiya Faɗimatu tayi wanda daga wanan ihun sai mutuwa "suka janyeta ya jefata cikin wani abu wanda cikinsa cike da jini .
Zaune Robat yake a tangamemen palon su , gefe kuma mama ce zaune ita da Zeena , Robat yace "Zeena gara ma ki amince da auran Karam dan na