ƘANIN UBA Sirrin Jinin Gida by Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  Romance

Chapter   3 / 18

6K to 9K   out of 53.2K words

take tace "kina sane wanan ɗan akuyan yana maganar wai ayi bikin Nisha nan da sati biyu ko uku har da yaushe suka haɗu ?" cikin masifa take maganar tsabar ɓacin rai ,kallonta Mommah ta tsaya yi daga bisani tace "zaki hana ne ?inajin ko Imaam bai isa ya hana ba ubanku kenan bare ke ƴar cikina "Mommah ta faɗa tana nuna Pooja cikin zafin rai , da sauri Pooja ta fice ta koma side ɗinsu ,samun Nisha tayi a kwance tana kuka ,ta rungumota a hankali tace "kibar kuka lil sis inda na gaya miki shi za'ayi amma sai time yayi share hawaye tayi ta miƙe tare da gyara zama ta ƙurawa yayar tata ido tana ganin kamar tama fita shiga tashin hankali.
8:pm suna zaune a palo Imaam ya shigo hannunsa riƙe da ledoji manya da sauri Mommah tayi gurinsa tana cewa "barka ya Habiby ,murmishi Imaam yayi kana ya rungumeta yace "ya aiyuka ?"Mommah tace "lafiya lau ,kallonsa ya kai ga ƴaƴan nasa da suka takure guri ɗaya ,yace "Pooja lafiya kuwa ?"haɗa ido da Mommah Pooja tayi Mommah ta sakar mata hararar Pooja tace "lafiya lau Imaam ,Nisha tayi carab tace "Imaam wlh ....Mommah ta katse mata zancen da cewa "ai ba sai kin faɗa masa ba ni kaina zan sanar dashi yayi suriki "zaro ido Nisha tayi cikin mamaki ta kalli Mommah , kana ta sunkiyar da kanta ,Imaam bai fahimci komai game da su ba ya wuce side ɗinsa , ko zama baiyi ba Mommah ta shigo fuskarta ɗauke da murmishi tace "ya Habiby munyi baƙo fa "murmishi Imaam shima yayi yace "masha Allah daga ina ?"to zauna man Imaam kasha labari "Imaam na cire doguwar rigar jikinsa ya zauna tare da sauraronta ,tama rasa ta ina zata fara sai ta tsinci kanta da cewa "wanda yake son Nisha ne yazo " so kuma ?dama akwai mai sonta ne tun tuni ?"a'a Mommah tace "ɗazu fa yazo amma suna yawan waya da ita ko da yaushe "masha Allah Imaam yace "daga ina yake ?"sai da ƙirjin Mommah ya bada dumm sanan tayi ta maza tace "yaron governor ɗin garinnan "a zabure Imaam ya miƙe tare da cewa "wai da gaske kike ?"eh man wayata babu caji dana nuna maka photonsa ka tabbatar "Mommah ta faɗa cikin sanyin zuciya tana ganin maganarta ta sami ƙarɓuwa "ya akayi suka haɗu ? Imaam ya tambaya yana jiran amsar Mommah -yanzu dai duk ba lokacin wanan bane yace "yanaso ayi bikin nanda sati biyu ko uku "Mommah ta faɗa tana washe haƙora kamar gonar auduga ,kallon baki da hankali Imaam yayi mata kana yace "wanan wacce irin magana ce kin tambayi yarinyar kinji tace "tana sonsa ?" Mommah da gabanta ya fara lugude tace "eh eh man dama za'ayi abu ne yarinya bata so ,ita da kanta taje ta shigo dashi kaga ko ai tana sonsa , uhm Imaam yace "yana murmushi , haɗamin ruwan wanka Imaam ya yace "yana kallon fuskar Mommah farincikin yau yafi na kullum , jiki na rawa ta shiga toilet ɗin tare da haɗa masa ruwa ta dawo palo ta zauna shi kuma ya shiga wanka , tunani tayi karfa su Pooja su tafi bedroom ɗinta su hango ajiyar da tayi ,ta fice da sauri ta buɗe ƙofar bedroom ɗin tare da ɗaga gurin da tayi ajiya tace "Alhmdulilh ,kwashe kuɗim tayi ta zubasu cikin wani ɗam ƙaramin akwati tasa kwaɗo ta kulle tare da kwanciya sbda ta fara duba abubuwan daya kamata a tsara tunda bikin na sharp sharp za'ayi, tana kwance taji wayarta na ring da sauri ta janyo wayar tare da karawa a kunnenta tace "Asslamu alaikum "daga can ɓangaren akace wlkslm "Ammar yazo min da kyakkyawan albishir akan maganar auransu ,sai yanzu Mommah ta fahimci mai maganar kasancewar bada layin data kirata ɗazu ta kirata ba , hmm eh wlh Allah ya tabbatar mana da alkairi Mommah tace "Umm Ammar tace "amma ya kukayi da mahaifinta ?"bashi da matsala Mommah tace "a taƙaice ,Umm Ammar tayi mata sallama tare da kashe wayar , kan Mommah ya ɗau zafi a halin yanzu idan da wacce zata bata matsala bai wuce Nisha ba .
Bayan Imaam ya fito daga wanka yaga wayan babu Mommah ,da mamaki ya ɗauki mai ya shafa ya zauna yana ɗaure da towel ,tunani ya fara yau kuma mai yake damun Mommah ne da har ta tafi ba tare da tayi masa abubuwan data saba ba , ganin ba dawowa zatayi ba yasa ya miƙe tare da buɗe drowa ya ciro wani yadi mai santsi baƙi mai tsada ya sanya ya dawo kan sofa ya zauna tare da ɗaukar alqur'ani ya fara rero ƙira'a da muryarsa mai daɗi , har ya idar Mommah bata dawo ba yama fitar da rai akan zata dawo ya kulle ƙofarsa tare da dawowa ya hau bed ya kwanta ,kana ya fara adu'oi bacci ya ɗaukesa.
Har ƙarfe 2:pm na dare idon Mommah biyu bacci yayi wa idonta ƙaura ta wani gefen tunanin alƙawarin data ɗaukkkarwa Umm Ammar take ,ta wani gefen kuma babbar damuwarta itace Nisha , ya zata ɓullowa kamarin ?"bata da mai bata amsar tambayar dan haka ta kwanta yau ko adu'a bata sami damar yi ba .
Ammar na dawowa gida ya sami Umminsa zaune kan wata haɗaɗɗiyar kujera tana sanye da wani tsadadden leshi fari wanda yaji aiki , zama yayi a ɗaya daga cikin tsala tsalan kujerun kana yace "Umm baki tambayeni ya mukayi da yarinyar ba "murmishi matar da bazata wuce 65years ba tayi kana tace "muna magana da mahaifiyarta ai nji komai amma inaso lokacin da kace akan bikin a ƙarashi sbda idan Abbanka ya dawo za'ayi wasu shirye shirye "ɓata rai Ammar yayi kana yace "Umm nidai a time ɗin nakeso wlh na matsu in ganni da mata "zaro ido Umminsa tayi tare da buɗe baki tace "ni kake gayawa haka ?"ni Ammar ko kunya babu "sadda kansa ƙasa yayi yana sosa kai yace "afuwan ya Ummi "ya miƙe zai fice Umm tace "akwai motoci da aka shigo dasu ya kamata kaje ka zaɓi wacce tayi maka "yamutsa fuska Ammar yayi kana yace "Umm ni yanzu bani da isash shen lokaci ki zaɓa min kawai "dariya ma ya bata tace "aure manya "bai kulata ba ya fice "yana fita ya tafi part ɗinsa kasancewar gidan part part ne kuma ko wanne tsakaninsa da nisa , buɗe wata haɗaɗɗiyar ƙofa yayi ya faɗa ɗakin nasa ,a palo ya zauna tare da ƙara tashi ya ƙara gudun AC ,ya fara magana yace "ace kuwa a hanani wanan yarinyar walh akwai bala'i "sai kuma ya kwanta kan 3sitter yana tunanin kyakkyawar fuskar Nisha har wani murmishi yake.
Tunda ya shigo bai fita ba sai abinci daya ci yayi sallah ya kwanta .
Washe gari da safe misalin ƙarfe 1:pm sun gama break fast , Ammar ne ya fito tare da nufar part ɗin mahaifiyarsa , jiniyar da yaji ne yasa shi dawowa da baya ya dawo har kusa da bakin get ya tsaya , motoci ne suka dinga shigowa sunkai su shida , ta tsakiya itace wacce governor yake ciki wato mahaifin Ammar , bayan sunyi parking an buɗe musu motocin mahaifin Ammar ya fito yana sanye da brown ɗin shadda wacce tasha aiki kamar ba mutum bane yayi , fitowa yayi cikin takunsa ya tungumi Ammar dake tsaye yace "my lovely son fatan kana lafiya ?"ƙara rungumesa Ammar yayi kana ya ɓata rai yace "Abba i miss you "murmishi Abban yayi yace "nima fa haka my son "suka shige ciki , da shigarsu palon ya cika da mutane ko wanne da abinci a gabansa ,kuma gaishe da Ammar ɗin suke har da wanda yayi sa'an babansa ,sai yaga dama yake amsawa suka shige ciki shi da Abba , samun Ummi sukayi a ɗayan palon tana riƙe da waya ga dukkan alamu bata son kowa yaji maganar , da sallama Abba da Ammar suka ƙarasa Abba ya rungumi Ummi ,wanan lamari na matuƙar burge Ammar amma idan har hakan ta faru a idonsa to tabbas sai yayi wanka , kawar da kai gefe yayi ,tare da cewa "Abba Ummi ta faɗa maka koh ?"Ummi da ta fahimci mai yake nufi tace "to ganɗoki ai dai ka bari ya huta ko ? turɓune fuska yayi zai ƙara magana Umm tace " pls ka wuce ka bani guri "yana fita ya bugo ƙofa da ƙarfi ya tafi part ɗinsa tare da buɗe fridge ya ɗauki kwalbar golden b ya buɗe murfin ya shanye duka ya ajiye robar a gurin , lokaci kaɗan yaga ɗakin na juya masa a hankali ya dafa bango ya ƙarasa bedroom ɗinsa yana tangaɗi ya faɗa kan bed , idonsa ya kaɗa yayi ja sosai , yana kwance yana zuba surutai mahaifin nasa ya turo ƙofa yana kwaɗa sallama yaji shiru ,ƙarasa shigowa yayi yaci karo da gorar golden b ya waro ido kana yace "Ammmaar "kamar a mafarki Ammar yaji ana kiransa da ƙarfi yace "indai aure ne gobe a ɗaura shiiiii, da sauri Abba ya ƙarasa bedroom ɗinsa ya gansa kwance ƙafarsa da takalmi , ya illahi Ammar dama kana shaye shaye mahaifiyarka bata sabar dani ba " good "Abba yace "kana ya fice a fusace ,yai part ɗin Ummi , a tsaye ya sameta tana son ta faɗa masa maganar auran Kamal ,yana shigowa ta kawar da tunanin ta hanyar yin mirmishi ,wato kinada masaniya akan wanan yaron yana shaye shaye shine baki danar dani ba ?"cikin rashin fahimta Ummi tace "Allah ya taimakeka wane yaro kenan ?"Ammar"jin Abba yace "Ammar Ummi taji kamar an buga mata ƙarfe tace "whay Ammar ?"ta saka kuka , zata fita Abba ya ruƙota tare da cewa "muje ciki "kai tsaye part ɗinsa ya wuce da ita suka zauna a palo Abba ya kalleta a tsanake yace "menene matsalar Ammar dahar ya fara shaye shaye ?"shiru Ummi tayi can kuma tace "aure yace min yana so "aure kuma ?har da yaushe ya kammalah karatunsa ?"shiru Ummi tayi batace komai ba , Abba ya gyra zama tare da harɗe hannayensa a ganinsa Ammar yayi yarinta da aure "zuwa gobe zamuyi magana "tom Ummi tace ".
Washe gari Ammar ya tashi rass dashi ya yafito kamar bashi ba ya tafi part ɗin su Umminsa , masu hidimar gidan ya samu a palo wanan na goge TV wanan na goge dining da sauransu , zubewa gabansa sukayi suna kwasar gaisuwa , sai da Ammar ya ɗau lokaci kana yace "lafiya ya wuce "yana shiga ya sami Abba da Umma kwance suna rungume da juna ya zaro ido Allah ya taimakesa basu gansa ba ,nan fa hankalinsa ya kuma tashi ya koma ɗakinsa tare da zama ya zuba tagumi a ya bugi teburin gabansa yace "wlh bari Abba ya fito ayi wacce za'ayi kuna can kuna jin daɗinku ni kun barni cikin ƙunci wlh inaa.
Imaam na dawowa daga masallaci ya wuce side ɗin Mommah , kwance ya sameta ko sallahar ma batayi ba ya ɗan bubugata ,a hankali ta buɗe ido ta ɗorasu kan Imaam murya ta mai bacci tace "wai har an kira sallah ?eh man har an fito tun tuni "tashi tayi ta zauna Imaam ya taɓa wuyanta ya ɗauka rashin lafiya take yaji babu alamun zafi "lafiya Imaam ?"Mommah ta tambayeshi "lafiya mai kika gani ?"Imaam ya faɗa yana kallonta , naga kana taɓamin wuya ne "Mommah tace "tana sauka daga kan bed "jekiyi alwalah dai "Imaam ya faɗa tare da miƙewa ya nufi gurin su Pooja , yana shiga ya samesu a jere sun ɗaga hannu suna adu'a da alamu sunyi sallah , cikin farinciki ya nemi guri ya zauna da murmushi a fuskarsa , bayan sun shafa adu'ar shima ya shafa , suka juyo garsa ko wacce ta gaishesa , amsawa yayi tare da cewa "mai ke faruwa a gidannan ne ?naga abubuwa suna neman sauyawa "Nisha zatayi magana Pooja ta rigata da cewa "aure Mommah take son Nisha tayi tunda ta sami miji "cikin fahimta Imaam yace "Nisha ta amince ne ?caraf Pooja ta amshe da cewa "eh ta amince "gaban Nisha ya bada rasss cikin rashin fahimta ta ɗago kanta ta kalli Pooja dake kallon gefe batace komai ba ta sunkuyar da kanta idonta na zubar da hawaye , kasancewar Imaam ba ita yake kallo ba yace "to Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa "Pooja tace "Amin "ficewa Umaam yayi ya koma ɗakin Mommah ya samu har tayi wanka ta sauya kaya taci kwaliyayaje gareta ya rungumeta tare da cewa "ke ashe har yarannan sun shirya kansu shine baki gayamin ba ?"sun shirya kuma ?wane yara kenan ?Mommah ta tambaya Nisha da Ammar mana "wani irin farinciki da nishaɗi ne ya dirar wa Ummi tace "Nishar ce take gaya maka ?"a'a Imaam yace "Pooja ce wlh kinsan Nisha akwai kunya "kamar Mommah tayi tsalle haka takeji ta kalli Imaam tace "nafi kowa farinciki da hakan "Imaam yace "badan ita tace "tana sonsa ba da bazan yarda da auran ba "Mommah dake murna ta haɗe rai tare da cewa "kamar ya ban gane ba "Imaam yace "sbda daka kai ƴarka gidan gwamna gara ka kaita gidan mai rufin asiri , nasan muma munada arziƙi amma a zahiri nasu ya taka namu abin tunani shine shin zatayi rayuwar jin daɗi kuwa ?"ko kuma rayuwar ƙunci zatayi ?, mtsw Mommah taja tsaki kana tace "Imaam an fa wuce nan gurin ni inada tabbacin muma zamuyi alfahari da hakan dan haka ka kwantar da hankalinka "uhm Imaam yace .
Umaam na fita Nisha ta ɗago kai da jajayen idanuwanta ta kalli Pooja tace "haba anty Pooja mai yasa zakimin haka ?kinsan ko ganin mutumin nan bana son yi dan mai zakice wa Imaam ina sonsa ?haba ƴar uwa sakko man kin mance ni antynki ce wacce a koda yaushe take ƙoƙarin sanyaki farinciki ko kin mance ?inaso ki nutsu ki saurareni , akwai dalilin da yasa nayi haka idan lokaci yayi zaki san komai "Nisha ta kasa cewa "komai sai ambaliyar da hawaye suke a fuskarta ,ta share wani ya zubo haka take tayi .
Yau Pooja ita kaɗai taje dining ko da Imaam ya tambayeta ina Nisha cewa "tayi tace "a kai mata ,Mommah ta miƙe da kanta ta zuba mata soyayyar taliya da naman kaza ta tafi kai mata ,tana shiga ta sameta a zaune da waya a hannunta tana game , bawai dan tana jin daɗin yin game ɗin ba , sai dan kawai ta samu ta kawar da damuwar da take ciki , dafa kafaɗarta Mommah tayi kana tace "naji wani abun farinciki ashe kin cewa "Imaam kina son Ammar ? Nisha batace komai ba illa karɓar tiren dake hannun Mommah da tayi sbda wata fitinanniyar yunwa takeji , murmishi Mommah tayi tace "a'a ni zan baki a baki ƴata "ta fara ba tana murmishi har sai da Nisha ta ture sanan Mommah ta tsaya ta miƙe ta buɗe fridge ta ɗauko mata faro ta bata tasha , alhmdulilh Nisha tace "tare da kallon Mommah sai kuma ta sunkuyar da kai , rungumeta Mommah tayi tace " haba ƴar albarka na dan kince kina son Ammar shine abin jin kunya kuma kibi ki damu kanki , Nisha dai ta kasa magana har Mommah ta miƙe ta tattara plet ɗin ta fice dasu , Nisha ta faɗa gado tare da sakin kuka .

Pooja na dawowa ta sameta a inda ta barta , rungimeta tayi kana tace "wai baki yarda da maganar dana faɗa miki bane ?"na yarda Nisha tace "cikin kuka dan a halin yanzu gani take kamar Imaam da Mommah ba sune suka haifeta ba.

Zuwa yamma Abban Ammar na zaune a garden shi da bodyguard ɗinsa Ammar ya iso gurin , alamun su basu guri Abban yayi musu suka wuce tare da ɗan risinswa , Ammar ne ya zauna kusa da Abban nasa yace "Allah ya ƙara girma nifa ina son aure "dariya ma zancen yaba Abba amma sai ya saki murmishinsa na manya yace "kana da wacce kakeso ne ? eh akwai ta Abba "wanene mahaifinta ?"wani rass gaban Ammar ya bada a hankali yace "Imaam...!
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: *🪂🪂ƘANIN UBA🪂🪂*

*Zainab Habib{Mom Islam}*


🪂🪂🌼🌼🌼🌼🌼🪂🪂

Elegant online writers

Ga ƙarin free pages nan


🅿️ Page 7-8
Mommah tace "ai kuwa Allah yasa za'ayi bikin daku "riƙe baki Ansar yayi kana yace "wato shine za'ayi bikin babu ko sanarwa Mommah ?"shigowar Imaam ne ya katse musu hirar Abid ya gaishe da Imaam haka ma Ansar,bayan sun gama gaisawa Imaam yace "anci abinci kuwa ?"dukkansu auka gyaɗa kai alamar a'a Imaam yace "to kutashi muje "kai tsaye dining suka tafi kowannen su yana cike da farinciki ,Pooja ce ta zubawa kowa kana ta zuba nata suka fara ci suna hira cikin nishaɗi Nisha kam sai eh da a'a.
Mheera ce zaune a ɗakin Ammar ta kwanta kan cinyarsa ,yace "sis "na'am tace "tare da tashi ta zauna sbda a inda taji ya kira sunan kamar akwai magana mai muhimmanci da zaiyi mata , kallonsa tayi kana tace "ina sauraronka bro "am Mheera ina da budurwa ,ina sonta sosai har ma inajin idan ban sameta ba komai zai iya faruwa ,ya riƙo hanunta idonsa yayi ja yace "ki taimaka min Abba ya yarda pls ƙanwata "itama riƙe nasa hannun tayi kana tace "Insha Allah duk da nasan Abba idan ya turje akan abu baya dawowa zanyi ƙoƙari "ɗagata sama yayi yana juyi yana cewa "anayin bikina sai naki "dariya tasa tare da wucewa part ɗin Ummi ,tana shiga taga Ummi a kwance tana bacci , fitowa tayi ta koma bedroom ɗinta itama ta kwanta.

Ummi najin fitarta ta rungumo pilo ta matse tare da ambaton sunan Allah ,idonta ta gefe yana zubar da hawaye miƙewa tayi ta ɗauro alwalah tazo tayi nafila ,lokacin 12pm na rana ta dinga adu'oi kana daga ƙarshe ta shafa ta kuma kwanciya , wata ƴar aiki ce ta shigo da sallama tace "Hajiya akwai buƙatar

3 / 18