Author : Zainab Habib Category : Romance
riga da na gama komai gobe za'a gabatar da auranku a majami'a "cuno baki Zeena tayi tana shirin kuka taji Robat na wani irin tari har da jini da alamu ciwonsa ne ke shirin tashi ,da sauri Zeena ta nufi gurinsa tana kuka tace "ka tashi dady na amince na amince "da sauri ya ɗago kansa tare da cewa "haƙiƙa nayi farinciki marar misaltuwa ,ubangiji yayi miki albarka "mama dake zaune tace "Amin "cikin jin daɗi Robat ya fice kai tsaye gidan mahaifin Karam ya nufa ,bayan sun gaisa kowa ya basu guri ,Robat yace "ƴarka fa ta amince da auran Karam ,da sauri mahaifin Karam ya miƙe cikin jin daɗi yace "burinmu ya cika ,dama sirrin da muka ɓoye yayi tasiri ,tunda malamin duban taurari yace "Zeena ce haske a kasuwsncu na yanzu arziƙinmu zai ƙara yin gaba , yaushe kake ganin ya kamata ayi bikin ?"Robat yace "ni gobe ma nasa tunda akwai komai "yea suka dinga taka rawa ,har Karam ya shigo aka sanar mass da gudu ya fice zuwa gidan su Zeena ,yana zuwa ya sameta a palo abinka da masu hannu da shuni har ƴan uwa an hallara ana ta gyara Zeena , yana zuwa ya sunkuceta ya fice da ita , kissing ɗinta lumshe ido Zeena tayi a fili tace "haka soyayya take da daɗi "Karam yace "kekika ɗauki so bashi da daɗi "daga nan ya mayar da ita gurin da ake shiryata ,
Washe gari bikin ya kan kama ,bikin Zeena da Karam ƴan uwa sai sam barka , farinciki a fuskar kowa daya hallara a gurin , bayan an gama sha'anin biki zuwa dare aka kaita gidanta wanda ya haɗu har ma ya gaji da haɗuwa , sai dai muyi musu fatan alkairi.
Yau assabar ta kama ɗaurin auran Ammar da Mheera , ɗaurin auran daya sami halartar manyan ƴan kasuwa da kamfanoni ,har da gidajen redio da TV ko ina sanarwa ake , anyi wasanni kamarsu Mothers day bridal shower arabiyan night da sauransu ,nera tayi kuka sosai , zuwa dare aka kaita kusa da ɗakin Nisha a nan cikin gidan nasu , ba wasu ƙawaye ta gayyata ba kasancewar ba ko ina take zuwa ba kuma daga secondary har sama ba a nan tayi ba , bayan kowa ya watse Ammar ya shigo shi da Mubin wato saurayin Mheera na da wanda a halin yanzu shima yayi aure , bayan an gama adu'oi ya gama tsokanar Mheera ya fice tare da yi musu sallama , murmishi Ammar yayi dan har yanzu yana tuno daren auransu da Nisha kuma har yanzu yana jin sonta a zuciyarsa , miƙewa yayi yaje ya ciro gasashiyar kazar dake cikin oven ya ɗauko plet ya ajiye kana yasa kazar a ciki ya sanya wuka , ya nufi bedroom , samun Mheera yayi ta shiga toilet ,bata jima ba ta fito tare da alwalah ,Ammar yace "sallahar me zakiyi ?Mheera tace "isha'i wlh banyi ba "okay "Ammar yace "shimfiɗa mata sallahaya yayi ta kabbara sallah bayan ta idar , yace "suyi nafila suna idarwa ,ya dafa kanta tare da kwararo adu'oi kana ya janyo kaza da Fresh milk ya tsiyaya mata a glass cup zai fara bata ,ta ɗauka ta sanya masa a baki ,da haka suka ciyar da junansu har suka ƙoshi , suka je toilet a tare sukayi brush tana shirin fitowa ya sunkuceta sai bed , pls ban sauya kaya ba "Mheera tace "a hankali dariya Ammar yasa cikin ƙasa da murya kana yace "ni a haka nake son ganinki , ya fara shafo fuskarta yana cewa "haƙiƙa na yiwa Allah godiya daya bani ke a matsayin mata "rungumesa Mheera tayi tana dariya , kamar an zaburi Ammar ya fara rabata da komai na jikinta jikinsa na rawa ya haɗe bakinsh guri ɗaya ,ya fara aika mata da saƙonni na musamman ,har wani banƙarewa take , cikin hikima da salo na jan hankali ya fara ƙoƙarin neman hanyar da zai karɓi haƙƙinsa , bata ji zafi kamar na farko ba amma taji kaɗan , runtse ido tayi tana salati , a hankali ta jiyo Ammar na sauke nunfashi yana cewa "Allah na gode maka ,bai wani daɗe yana yi ba ya mirgina gefe sakamakon ciwon cikinsa daya tashi , shafamasa jiki Mheera ta shigayi jin kamar tana tayar masa da sha'awa yasa shi ƙara komawa yaci gaba da aiki.
Gidan su Nisha , Washe gari Pooja tana tsaye da saurayinta a ƙofar gidan su ,tace "masa Imaam yace "ka turo da iyayenka idan har da gaske kake sona "lumshe ido yayi kana yace "gaskiya ni karatu nake amma ina da burin yin aure idan har zaki jirani nan da 5 months insha Allah amma wlh ina sonki soyayyar da ta kasance jinin jikina ,a sanyaye Pooja ta kallesa tace "ai duk ɗaya ne a gurin Allah.
****************
Bayan wasu watanni .
Yau watan su Mheera uku da aure , Mheera da Ammar na zaune a palo kanta a kan cinyarsa tace " Mijina ina roƙon wata alfarma "mayar da hankalinsa yayi gareta yace "na baki dama "murmishi tayi kana tace "so nake ka mayar da Nisha dan Allah sbda naji labarin ta dawo da daɗewa "gyara zama Ammar yayi tare da ɓats rai yace "idan kina kusa dani bana kallon ko wacce mace ,a zuciyarsa kuwa yace "dama wanan ranar nake jira inji "Mheera ta tallafo haɓarsa tace "dan girman Allah kayi haƙuri ka mayar da ita "shittt naji zan mayar da ita amma sai kin mai maita wanan kalmar a gaban su Hajiya da Ummi da Abba "zan faɗa "Mheera tace "tare da ruƙo hannunsa.
Tun bayan biki Hajiya dama bata koma ba , suka shigo sashen su Ummi a falo suka zauna kasancewar tatar dasu da sukayi a falon , Ummi tace "ƴata ya hutawa "dariya Mheera tasa kana tace "nazo gurin Hajiya ne "Hajiya dake gyara ɗankwali tace "ina sauraronki ƴar nan mai ya faru ?"Mheera ta kalli Abba dake zaune yana waya fuskarsa sanye da farin glass ta durƙusa tare da cewa "ina roƙon alfarmar Ammar ya mayar da Nisha dan Allah "Hajiya da Abba sunji daɗin hakan ban da Ummi data haɗe rai , Abba daya lura da hakan ya shiga yi mata nasiha akan abubuwan da suka faru , cikin gamsuwa Ummi tace "Allah ya zaɓa mana abin dayafi alkairi "Hajiya ta kalli Ammar tare da cewa "to goga kai kuma me kace ?"Ammar ya sunkuyar da kai ƙasa tare da cewa "babu komai sai abin da kukace "Abba yace "tashi kuje Allah yayi muku albarka "suka miƙe .
Washe gari Abba da kansa bai gayyaci kowa ba yasa Ammar a gaba suka je gidan su Mommah bayan sun gaisa ya roƙi arziƙin Ammar yaxo mayar da Nisha "kiran Nisha Imaam yayi bayan tazo ya tambayeta tana son Ammar har yanzu kuwa ? sunkuyar da kai Nisha tayi tana dariya hakan ya tabbatar musu da eh tana sonsa .
Abba yace "sai dai wani hanzari ba gudu ba Ammar a halin yanzu yana da mata ya auri Mheera "Nisha ce ta tsinci kanta da cewa "Mheera ƙanwarsa ?"Abba ya basu labarin komai , Imaam da Mommah sukayi fatan alkairi , Mommah tace "to yaushe zata koma ? Abba yace "ai ni bazan fita ba sai da Nisha yau ɗinnan , dukansu suka sanya dariya , Munim daya shigo yanzu ya gaishe da Abba -Abba yace "wanan ɗanka ne Imaam ?"a'a Imaam yace "Ƙanina ne bari a kira maka su Asim sune ƴaƴan "Munim ne ya ƙwala musu kira sai gasu sun fito a tare suka surƙusa suka gaishe da Abba bayan ya amsa yace "akwai wani kamfani nawa da suke buƙatar yan aiki kamfanin ana siyar da kayan sawa na mata ne kama daga sarƙoƙi da takalma da kaya , inba damuwa zan ɗaukeku aiki dukanku "ji sukayi kamar suyi tsalle tsabar murna , Imaam yayi masa godiya haka Mommah yace "ranar lahadi suzo da yamma zasu tattauna a kai .
Har ya tashi zai tafi Pooja ta fito ta gaishe sa ,ya amsa cikin sakin fuska yana cewa "wanan kuma waye ban santa ba ?"Abid yace "yayar Nisha ce "Abba yace "karatu takeyi ne ? a'a Abid yace "ai ta gama "Abba yace "har dake kuzo tare insha Allah zamu ɗaukeku aiki , haka suka bar gidan tare da Nisha cikin farinciki.
Bayan sunyi parking suka fito dukkansu kai tsaye palon Ummi suka nufa akayi wa Nisha da Mheera faɗa kana Ummi da kanta ta raka Nisha ɗakinta , a ranar dai Ammar a ɗakinta ya kwana ansha soyayya iya soyayya dan ji yayi Nisha tafi Mheera komai amma sbda , son a dawo da Nisha da tayi ya bata babban matsayi a zuciyarsa , haka gidan suka zauna cikin farinciki da ƙaunar juna ,basa faɗa ko cacar baki kullum cikin nishaɗi suke .
Sai dai muyi musu fatan samu zuri'a ɗayyiba .
Ɓan garensu Abid ma sun ziyarci Abba inda ya bawa ko wannensu aikin yi Pooja kuma ya buɗe mata katafaren shago na siyar da kayan kitchen a kusa da gidansu .
Bayan komawar Nisha Mommah ta zitarci gurin Mamy ta bata haƙuri tare da nuna mata tayi nadama .
Tammat bi hamdillah anan na kawo ƙarshen littafin KANIN UBA kura kuran dake ciki Allah ka yafe man ,ina son kuɗauki abubuwa masu kyau daga cikin littafin nan kuyi watsi da wanda bashi da kyau .
Sai kuma Allah ya haɗamu a sabon littafina mai suna NIDA YARINYA zallar cin dariya soyayya da sadaukarwa .
Amma bazan fara sakinsa da wuri ba sbda bana son a ƙara samun akasi kamar yadda kukayi haƙuri da rashin typing ko da yaushe ,ina son sai nayi nisa zan fara sakinsa ,ina fatan zaku nunamin soyayya 👏🥰ta hanyar siyan fitaccen littafina , zai zo a 1&2&3 insha Allah.
Na gode muku da kuka nuna min ƙauna ta hanyar farantamin ina yinku sosai 🥰.
*ƊAN ƊANO daga littafin NIDA YARINYA*
🤦🤦♂️🤦♂️🤦♂️🤦♂️🤦♂️🤦♂️🤦♂️
*NIDA YARINYA*
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂
_Zainab Habib /Mom islam_
*Bismillahir rahmanir rahim*
🆓p 1-2
Wata yarinya ce ƴar kimanin shekaru goma sha huɗu na hango , zaune take a bakin ƙofar wata tsohuwa tana karkaɗa ƙafarta , tsohuwar dake zaune a cikin ɗaki tace "Ramu maza kije ki karɓo min fatari na idan Adamu ya ɗinke "cikin tsiwa Ramu tace "ka jiki dai ke baki da aiki sai aikan mutane ,ni yanzu ma zanyi kwaskwarima in fice "riƙe baki tsohuwa tayi kana tace "ke karki kawomin rashin arziƙi ,ubanki ma sai in aikeshi yaje balle ke "miƙewa Ramu tayi kana karkaɗe koɗaɗɗen zaninta tace "idan yazo kya aikeshi nikam dandali zani ".
Tsintsiyar dake bakin ƙofa ta wurgawa Ramu tana cewa "shegiya irin Dije irin tsiya ,baku san mutunci ba ,tsohuwa ta rarako Ramu da gudu taci karo da wani dutse tayi tuntuɓe ,Ramu dake tsaye tana jiran tsohuwa ta zo gurinta ganin ta faɗi yasa ta tu tsirewa da dariya tace "bani da alhakinki har da tafawa , a hankali tsohuwa ta rarrafa ta miƙe tana ɗingishi tace "shegiya irin tsiya kin yiwa Dije "oho dai kindai faɗi sai ki koma ɗaki "Ramu tace "tana tuntsirewa da dariya ta fice .
Tafiya taci gaba dayi tana yi tana ranguwaɗa harda yarfe hannaye taci karo da wani mai kwsar kwata , toshe hanci tayi taci ɗammara kana tace "jibeka zankaɗeɗe da kai amma ka ƙare a kwasar kwata ?" saurayin ne ya kalleta a kai kaice kana yace "ke dan uwarki ni kike gayawa haka ?"lura da tayi idanunsa sun juye alamar yana shaye shaye ya sanyata cewa "an faɗa mai shan giya kawai "ajiye baron dake gabansa yayi ya zubo da gudu , mai makon ta miƙe hanyar da take bi sai ta dawo hanyar gidan tsohuwa , da gudu ta shigo tana cewa "tsohuwa ki taimakeni zai kasheni "tsohuwa da ta gama kiɗimewa ta turo ƙofa da ƙarfi tana cewa "ya kasheki "dan Allah tsohuwa ki buɗe wlh ya biyoni "ya kasheki "tsohuwa ta faɗa tare da hayewa gadonta mai rumfa , fitsari Ramu ta saki a wando ƙafafuwanta har rawa suke tana ihu , wani wawan cafka yayi mata kana yace "ubanwa kike zagi ?"cikin suɓutar baki tace "badai ubana ba "buge mata baki yayi kana yace sai uban wa ? ya wanketa da mari ta riƙe gurin a hankali tace "Allah ya isa "waro ido yayi kana yace "waye wai ubanki ne ?"cikin tsiwa tace "kaje ka dubashi "tsohuwa dake ɗaki ta ɗaga murya tace "wlh kaci ubanta dama maganinta irinka mahaukaci "bugu ɗaya yayiwa ƙofar ta buɗe ya faɗa ɗakin da gudu yana cewa "ke gyatuma ki iya bakinki wlh zan mugun saɓa miki "nayi shiru "tsohuwa ta faɗa tare da toshe bakinta , mai kwasar bola yace "dena kallo na "cikin sauri ta sunkuyar da kai yace "tari naji kinyi sai na buge bakinki "Ramu dake bakin ƙofa tana jin diramar da sukeyi ta sanya dariya mai sauti tare da cewa "yau a dandali akwai labari mai daɗi ,ta fice da gudu .
Fitowa yayi ya tsaya a tsakar gida yace "wlh idan na kama jikarki sai nayi mata dukan tsuguna kaci doya "wlh kayi mata dukan sumewa ma "tsohuwa ta faɗa tana gwalo ido...!
O8141799224 domin neman ƙarin bayani .
😢