ƘANIN UBA Sirrin Jinin Gida by Zainab Habib

Author :  Zainab Habib Category :  Romance

Chapter   14 / 18

39K to 42K   out of 53.2K words

kallo ya koma sama ,Nisha Imaam Pooja mamaki da tsoro ne suka dirar musu sbda ganin tsaruwar gidan da kyansa ya zarce gaban kwatance sai dai gani da ido "ku shigo mana sukaji muryar Mommah na amo cikin kunuwansu , ba tare da sunyi magana ba suka ƙarasa cikin palon a nan ne sukayi mutuwar tsaye Nisha kam gani take kamar siyar dasu za'ayi sbda wanan gidan duk kale kalenta na tsararrun ginunuka bata taɓa cin karo da irin wanan ba kuma gashi wai sune zasu shigeshi , kaf su ukun tsoro ya kamasu , Imaam yace "Allah yasa da zuciya ɗaya ta bada wanan gidan idan kuma dan ta wukaƙantamu ne Khadija ta cucemu "
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: 33-34

Haka dare yayi Hajiya na tunani Allah-Allah take gari ya waye taje gidan su Mheera , zuwa ƙarfe huɗu na gabannin asbha Hajiya ta buɗe ido su Mheera kam bacinsu suke ita da Aisha , kai tsaye ɗakin ƴar aikin gidan ta nufa itama baccin take Hajiya ta fara bubuga mata ƙofa da ƙarfi tana cewa "ki tashi ki haɗamin shayi yau sammako zanyi "da gudu ƴar aikin ta duro ta buɗe ƙofa a tsorace "ta sadda kanta ƙasa ta wuce kitchen ba tare da tace "wa Hajiya komai ba , na gama da wanan saura na gaba "Hajiya tace "tare da wucewa bedroom ɗinta ta tarar da su Mheera har yanzu suna bacci ,faɗawa toilet tayi tare da tara ruwan ɗumi tayi wanka ,tana tsan tsame jikinta ta shafa mai ta buɗe drower tasa kaya tare da ɗaukar mayafi ,lokacin ana kiran sallahar asbha tayi alwalah tayi sallah ta fito ,dining ta nufa sbda tasan an gama haɗa mata abin karyawa ,tana zuwa ta buɗe jug ta tsiyayi shayi ko bredi bata ci ba ta miƙe ta fice harabar gidan tana ƙwalawa driver kira , da gudu ya taho yana cewa "hajaju dawowata daga masallaci kenan barka da safiya "yawa barka Hajiya tace "ka kaini gidan Umar yanzu "to driver yace "tare da ɗauko key ya buɗe mata ta shiga , yasan Hajiya bata son ana gudu da ita ya fara tafiya a hankali ,tsawa Hajiya ta daka masa tare da cewa "kamar wanda ƙwai ya fashe wa a ciki maza ka jani muje "wani wawan gudu driver ya ɗiba kamar zai tashi sama , jin ya taka wani uban burki jikake ƙiiiiii, sai da Hjya ta buga goshi da hannun kujera kamar zatayi kuka tace "kai driver jani a hankali "bai saurari abin da take faɗa ba yaci gaba da gudu har suka iso gidan ,koda aka buɗe get ma bai daina gudun ba kasancewar gidan nada faɗi har tangal tangal ya dingayi ,Hajiya ta rasa tacewa bai ƙarasa tsayuwa ba ma ta fice a motar tana ce masa mugu kawai ta shige part ɗin Ummi .
Da sallama ta buɗe kofar palon ta shiga kana tayi wa kanta mazauni a kan sofa .
Ummi ce ta fito tana murmishi tace "Hajiya sammako akayi mana ne yau ?"rufamin baki tsohuwar munafuka ance min kinsa an saki wanan yarinyar ko ?"Hajiya ta faɗa tana nannaɗe mayafinta a kai ,girman kalmar Umma taji wai munafuka "murmishin yaƙe Ummi tayi kana tace "ni na isa insa Ammar yayi saki waye yake gaya miki ?"ba tare da Hajiya ta kuma Ummi ba ta nufi side ɗin su Nisha , tana zuwa ta ganshi a garƙame da kwaɗo ,riƙe baki Hajiya tayi kana tace "naga dil tabbs akwai rikici dole a dawo masa da matarsa " tana cikin masifa ne taji muryar Ammar na cewa "ƴar tsohuwa sammako kikayi mana ? juyowa Hajiya tayi kana tace "ba dole ba naji ance wai ansaka sakin mata ?"nima rabona da gidannan na kwana biyu yanzu ma a titi naga motarku shine na biyoki ai Nisha na gidan su "gyara ɗaurin zani Hsjiya tayi ta koma side ɗin Ummi ta kuma zama a karo na biyu ta ƙwalawa Ummi kira , fitowa Ummi tayi fuska sake tace "Hajiya gani "yayi dai dai da shigowar Ammar ya zauna tare da gaishe da mahaifiyar tashi ,amsawa Ummi tayi tare da ce masa ya kwana biyu "lafiya "Ammar yace "kansa a ƙasa .
"Ammar waye ya korar maka mata?
Ammar ya nuna Ummi.
"A kan wane dalili?".
Shiru Ammar yayi ba tare da ya bawa Hajiya amsa ba .
Murmishi Ummi tayi kana tace "yarinyar bata da kunya ne wlh bata da tarbiya "
Hajiya dake kallon bakin Ummi tun daga fara maganarta har ƙarashe ta yatsina baki tare da cewa "yau ɗinnan za'a dawo da yarinyar nan ,maza kira min driver".

Wata irin dariya Hajiya Faɗimatu tasa kana tace "Allah ya kawo Khadija itama taci arziƙi.

Nisha da Pooja ne zaune a palo ko wacce tana danna waya , Imaam ne ya shigo ya zauna a kujerar dake gefe ya kalli Nisha yace "ko Mijinki bai dawo ba tilas ki koma gidansa "gabanta na lugude ta sadda kanta ƙasa tare da cewa "Yah Imaam afuwan yana dawowa zan koma "Pooja tayi murmushin gefen baki .
Saura kwana nawa ya dawo ?"Imaam ya tambayeta "saura kwana goma insha Allah "Nisha tace "gabanta na faɗuwa ,Pooja kam dariya abun ya bata sbda tasan Nisha ta rasa mafita ne ya sanyata cewa haka, Mommah da ta fito yanzu tana jin tattaunawarsu tace "gara kam ta koma ".
Washe gari da safe bayan su Mommah sun gama breakfast ƙarfe goma Imaam ya fita zuwa gurin aiki sai ga kiran Hajiya Faɗimatu ,jiki na rawa Mommah ta ɗaga tare da cewa "Allah ya taimakeki barka da safiya "ywwa barka ya iyali ?"Hajiya Faɗimatu tace "wa Mommah "kowa lafiya "Mommah tace "tana jiran abun da Hajiya Faɗimatu zatace "yawwa Khadija kizo da misalin ƙarfe biyar ba wani daɗewa zakiyi ba magana ce sai kuma takardu "tom Mommah tace "jiki na ɓari kana ta ajiye wayar .
Tunda Hajiya Faɗimatu tace "Mommah tazo a wanan time ɗin Mommah take ganin lokaci ma yaƙiyi ,bayan tayi wanka ta sanya sababbun kayanta ta fito palo ta kunna kallo wai duk dan lokaci yayi saurin yi.
Ganin ƙarfe uku tayi yasa ta zumuɗi ta miƙe ta nufi bedroom ɗin su Nisha ta gansu a kwance suna ta bacci , tsaki tayi a fili tace "zan kirasu a waya yau Imaam sai ƙarfe goma zai dawo "ta fice tare da cewa "ina hanya lokaci zai yi .
Jakarta ta ɗauka tare da takalmi ta ɗauki wayarta ta fito kai tsaye fita tayi zuwa bakin titi , ta tari mota zuwa gidan Hajiya Faɗimatu sunyi tafiya mai nisa kana suka iso anguwar ,taba mai mota kuɗinsa ta fito , bayan tafiyar mai mota Mommah ta juya tana kallon gidan Hajiya Faɗimatu ta daɗe a tsaye tana kuma ƙarewa ginin kallo , daga ƙarshe ta dinga tafiya a hankali har ta isa bakin get ɗin ta fara nocking , buɗewa mai gadi yayi tare da rufewa ya koma ciki ya faɗawa Hajiya Faɗimatu ,ya dawo da gudu tare da cewa "ance ki shigo "shigowa Mommah tayi tana kallon cikin gidan idan kaga kallon da take sai ka rantse yau ne zuwanta na farko gidan , har takai bakin ƙofar da zata sadata da palon Hajiya Faɗimatu bata sani ba sai da taji ta ɗan bige da bango tace "ashe ranar ban kalli gidannan da kyau ba "ni yanzu babban buri na ingan ni cikin makeken gida da manyan motoci da babbar waya , sai kuma ta buɗe ƙofar ta shige "Aslamu alaikum "Mommah tace "tare da daɗa ƙarewa palon kallo .
Fitowa Hajiya Faɗimatu tayi tana cikin shiga ta alfarma ta zauna kan sofa tace "barka Khadija ina fatan zakiji daɗin sana'ar ?"Mommah na murmishi tace "insha Allah "miƙewa Hajya Faɗimatu tayi tare da shiga bedroom ɗinta tace "zan mallaka miki wanan gidan d motocin cikinsa zan ɗauki ɗaya a cikinsu ni nariga da na siyi wani gidan "a zorace kuma ido a waje Mommah tace "ni ina na isa siyan wanan danƙareren gidan ko kwatan kuɗin bani dashi "murmishi Hajiya Faɗimatu tayi kana tace "karki damu da zarar kin fara sana'a zaki sami kuɗin da ya ninka na gidannan zan ranta miki ne "nisawa Mommah tayi tama rasa inda zatasa kanta tsabar farinciki ji takeyi kamar ta kwanta tayi ta burgima tana ihu , dan kar ta fiya zaƙewa da yawa yasa ta sai saita nutsuwarta ta durƙusa gaban Hajiya tace "nagode Allah ya saka da alkairi Allah yaji ƙan iyayenki Allah yasa aljanna ce makomarki" amin -amin Hajiya tace ".
Kana ta zubewa Mommah wasu maƙudan kuɗi kan cinyarta tace "wanan kuɗin ya kai LAK talatin ,yau muna 20 ga wata saura kwana goma in bar gidan ke kuma ki dawo "Mommah dai ta rasa wacce irin godiya zatayiwa Hjya sai ta fashe da kukan daɗi ta ruƙo hannun Hajiya tana sumbata , lokacin ƙarfe shida tayi ta tura kuɗin a ƙatuwar hand bag ɗinta tace "nagode Hajiya sai munyi waya "Mommah ta fice .yau babu batun hawa mota Mommah tayi tafiya mai nisa bata ma san tayi ba tsabar farinciki jin mai mota nata yi mata horn ne ya sata tsayawa ta taresa tace "ya kaita Shabab wato anguwarsu , basuyi wata tafiya mai nisa ba sai gasu sun iso driver yayi parking Mommah ta ciro kuɗinsa ta basa , buɗe get ɗin gidan tayi taga mai gadi zaune yana ta rusa uban gyan gyaɗi ta wucesa kasancewar yau babu faɗa ,kai tsaye kofar babban palon ta buɗe tare da rafka sallama Nisha dake zaune hannunta riƙe da cup ɗin shayi tace "wlkslm "zama Mommah tayi tare da cewa "ina Pooja ne ?"ta shiga wanka "Nisha taba Mommah amsa ,gyara zama Mommah tayi kana tace "albishirinki my daughter "goro Nisha tace "tana mai kai cup bakinta , na sami sana'a "Mommah ta faɗa tana faɗaɗa fara'arta , cike da murmishi kana da kuma farinciki Nisha tace "Mommah wacce sana'a kenan muna tayaki murna "cikin zumuɗi Mommah tace "siyar da kayayyaki zuwa birane "wow msha Allah Mommah fatan alkairi ,cikin zuciyar Nisha tace "Allah yasa Imaam ya hanaki zuwa " suka ɗan taɓa hira aka kira sallahar magrib.
Washe gari da asbha bayan su Nisha sunyi sallah Pooja ta koma bacci Nisha ta haye kan kujera tare rungume ɗan ƙaramin filo tana tunanin abokinta ,kasamcewar tun dare take tunaninsa a fili tace "Allah kasa yana cikin ƙoshin lafiya "sai kuma ta kai dubanta ga Pooja da take bacci .
Bayan gari ya ɗan ƙara haske Imaam ya dawo daga masallaci lokacin har sunyi wanka suka fito a tare suka nufi palonsa tare da durƙusawa suka gaishe sa ,amsawa yayi cikin fara'a suka juya ga Mommah dake gefe suka gaisheta itama ta amsa , ficewa sukayi suka koma bedroom ɗinsu ,Nisha kam yau duk wanda ya ganta yasan bata cikin nutsuwa duba da yadda idonta yayi ja kamar wacce aka duka , Pooja data lura da yanayin Nisha ta taso ta dawo kusa da ita tace "haba lil sis ,har akwai damuwar da zata dameki ki ɓoyemin ?"bazaki gane ba anty Pooja da zarar kinsan wanda nake tunani bazaki sassauta min ba "a fili tace "ina yawan fama da ciwon kai kullum kuma ko nasha magani baya dainawa shine damuwata "murmishi kawai Pooja tayi tasan akwai abin da Nisha take ɓoye maata .
Su Nisha na fita Mommah ta matso ga Imaam tace "Imaam wani abun alkairi yana nneman samun mu amma fa idan ka yarda "ina jinki mai ya faru ?"Imaam ya tambayi Mommah ,idan baka manta ba ai nace maka zan fara safarar kaya ko ?"eh Imaam yace "ban manta ba "to wacce zamuyi sana'ar da ita shine ta ranta min kuɗi na siyi gidan da take ciki "cikin faɗa Imaam yace "soyan gidan banza ne ? "kin mayar da siyan gida kamar wasan yara kuma ban yarda da aron kuɗi ba "waro ido Mommah tayi kana tace "ai ba ta haram ma samesu ba yaushe rabonka da ka bani kuɗin cefane ?
[02/12, 7:45 PM] Oum Arfat: ,37-38

Suka ƙarasa shiga tare da zama kan luntsuma luntsuman kujerun da suka mamaye parlon , Nisha da Pooja sai da suka leƙa ko ina na gidan sannan suka dawo suka zauna can anjima motar kaya ta iso suka fara kintsa kayansu .

"Ammar maza fito ka rakani gidan su Nisha yau ɗinnan bazan dawo ba sai da ita "jikin Ammar na rawa ya kamo hannun hajiya suka tafi parking space tare da kiran driver ya tuƙasu suka wuce anguwar su Nisha , ana isowa driver yai parking a bakin get ɗin tare da cewa "mai gida ai gidan a rufe yake da ƙwaɗo "to ina sukaje ? Ammar yace "fita ka tambayar mana mutanen can ko sun san inda sukaje "an gama ranka ya daɗe driver yace "tare da ficewa ,sallama yayi wa mutaneb dake zaune tare da gaishe shi ,bayan sun amsa ya tambayesu ko suna da masaniyar inda su Mommah sukaje ?ɗaya daga cikin mitanen ne yace "ai sun daɗe da tashi sun koma SHABAB , gida mai lamba takwas yana ɗauke da farin fenti "godiya su Ammar dake cikin mota sukayi, driver ya ƙara ɗaukar hanya sunyi tafiya mai nisa kana suka iso anguwar driver ya kuma parking suka hango gidan shima rufe da kwaɗo wani ɗan saurayi dake tsaye drivern ya tambaya yace "ina ne su Nisha sukaje naga gidan su a kulle ?"ai sun tashi "yaron ya faɗa tare da yin tafiyarsa , mu koma gida gobe ma dawo "Hajiya ta faɗa da alamum gajiya a tare da ita .Tsaki Ammar yayi suka juya zuwa gida "gashi tun ɗazu yake guwada numberta shiru taƙi shiga ko lafiya oho "Ammar ya faɗa a fili "kwantar da hankalinka yaron kirki insha Allah matarka ko kwana uku baza'ayi ba zamu dawo da ita Suka juya zuwa gida .
Time ɗin da aka buɗe musu get lokacin motarsu Mheera na baya aka shigo da ita tacewa drivern ya koma , shigewa ciki tayi da sauri dan taji wutar da ta hura ko zata iya kawowa mahaifiyarta ɗauki ?.
Tana shiga ta sami Hajiya a tsaye Ummi na zaune kan bed tana kuka Hajiya na cewa "kina yimin baƙinciki da samun jikoki ko to ta Allah ba taki ba "wanan kalmar ta doki dodon kunnen Mheera , a fusace Mheera ta shigo tare da cewa "nice sanadin barin Nisha cikin gidan nan ba Ummi ba ,dalili kuwa shine...! katseta Ummi tayi da wata gigitacciyar tsawa tace "kar in ƙara jin bakinki a nan gurin karki sake kinji na faɗa miki "kuka Mheera ta fashe dashi tare da ficewa daga ɗakin ta bugo ƙofa gafff , Hajiya dake riƙe da haɓa tana kallon rashin kunyar da Mheera tayi mata ta hau tafa hannu tana cewa "nidai na shiga uku ashe ma ba jikoki Ammar zai haifo min ba amma wanan anyi banzar yarinya bata da ladabi sam ,ke kuma idan mukaje gobe muka dawo da Nisha kika kuma korata kema...Ammar ya rufe bakin hajiya tare da cewa "haba Hajiya yau kuma ƴan faɗan ne suka taso ?fincike hannun Ammar Hajiya tayi tare da galla masa harara tace "kauce ka bani gu gida zan koma na gaji da ganin baƙinciki "ta fice ta nufi gurin drivern ta tare da shigewa mota ,har an tayar Ammar shima yazo ya shiga suka wuce .
Abba ne zaune gaban boka yace "Boka gaskiya wanan abin da kace bazan iya amincewa ƴaƴana su aikata hakan ba wlh koda a mafarki "hha ha ha ha "Boka yasa wata shu'umar dariya tare da cewa "to kuwa baka bab cin zaɓe muddun kace haka "rikicewa Abba yayi tare da haɗe hannayensa jijiyoyin kansa na tashi yace "boka babu wata dabarar "shiga wancan ɗakin Boka yace "tare da cewa "ga kaya can jajaye maza sanya a jikinka "jikin Abba na rawa yace "sam tsoro nakeji Boka "kar kaji tsoro bayan nine nake da ikon aikata komai a ɗakin "
Gaskiya bazan shiga ba "Abba ya faɗa tare da miƙewa zai fice boka yace "idan har ka tafi kana wasa da kujerarka "ko juyowa Abba bai yi ba sai da ya kai gurin motarsa sanan ya juyo ya shiga a guje yabar gurin .
Yana dawowa gida Shukra na shafa masa jiki ya hankaɗeta tare da nufar table ɗin dake ajiye a tsakiyar ɗakin yayi watsi da kayan kai suk suka faffashe ya dinga buga kansa a bango yana kuka ,a fili yace "babban burina in zamo shugaba amma anata yimin yawo da hankali anya kuwa ƴaƴana na cikina ,a baya nace zan iya aikata komai amma a yanzu banajin zan iya wayo rayuwata ina son zama governor ya janyo Shukra ya rungume tare da kwantar da ita ya cire mata komai na jikinta ya fara aikata masha'arsa da ita.
Washe gari Abba ya shirya dawowa DUBAI da wuri sbda yaji labarin wani shahararren malami kuma election saura kwana goma dalilin da yasa Abba ya ƙara rikicewa kenan .

Abid da Asim ne zaune a gurin hutawa Abid yace "niko ina babynka ne ?"kana nufin wacce mukaje Misra ?"eh Abid yace "kasan saura 3 days mu kammala komai ko ka fasa ne ? "ban fasa ba sai dai ina tunanin ƙalu balen dazan fuskanta a gurin iyayenta tunda an cemin ɗan wan mahaifinta ke sont kaga ni ba wani kuɗi ne dani ba bare ince zanyi takara dashi "Eh kuma fa haka ne amma Asim mai zai hana kaje Dubai ka nemi aure ?"dariya Asim yayi kana yace "kai mafa ka isa auran haɗamu za'ayi ai "suka sanya dariya tare da miƙewa suka shiga room ɗinsu suna tattara kayayyakinsu .
Washe gari Abid na zaune a palo yana saye da gajeren wando da riga fara mai gajeren hannu wata budurwa ta fara nocking a ƙofar ɗakinsu , Asim dake girki a kitchen ya leƙo tare da kallon budurwar ya jinjina kai a zuciyarsa yace "to gurin wa tazo ?"kasancewar ƙofar tasu ta ko ina glass ne mai haske yasa kana iya ganin mai shigowa amma na waje balalai ya ganka ba , Abid da bai ɗago kansa ba bare yasan ko wacece yace "come in "buɗe ƙofar tayi tare da ziro fararen ƙafafuwanta dake sanye cikin takalmi golden

14 / 18