Author : Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category : Romance
bada ware ido sukayi su na kallon Ubaidullahi.
"Lafiya kuwa zaka dawo gida Ubaidullah?"
"Eh My Momma lafiya sai nazo" ya katse wayar.
Yana katse wayar suka hau rige-rigen tambayarsa.
"Ubaidullah me kake nufi da zaka koma gida gobe? Aikin naka kuma fa? Dan Allah karkayi haka,hakika al'umma su na bukatarka a cikin jami'an Sojoji ,dan Allah Ubaidullah karka aikata abun da kake shirin aikatawa, barracks tana bukatarka"
A hasale Ubaidullah ya ce.
"Karya ne! Barracks bata bukatata Zaidu KB karku yaudari kanku, dukkanmu abun da muka sanine a fili zai biyo baya gobe dan ko sama da kasa zasu hade ne na rantse da Allah bazan auri Rumaisa ba, idan kuwa haka ne,gwanda tun da sauran ɗan guntun mutunci ne na ajiye aikin da kaina kafin amin koran kare, wanda idan hakan ta faru zan tsani aikin soja, kuma ni bazan so na tsani aikin soja ba, saboda burinane tun ina ɗan karamin yaro na gaji mahaifina, ko ba komai alhamdulillah na cika burina na aikin soja, nayi yaƙi da jinina da lafiyata , hakan ma na godewa Allah, wannan jarabawatace ina adduar Allah ya bani ikon cinyeta, ku tayani da Addua Allah ya baiyanar da gaskiya dan bana so na mutu da tabon zargi a idon mutanen dake wannan nahiyar" Kawai Ubaidullah ya fashe da kuka,nan take shima KB ya fashe da kuka,cikin ɗauriya Zaidu ya ce.
"Ubaidullah u mean gobe zaka tafi bauchi?" Ubaidullah ya jinjina kai alamun eh,a zabure Zaidu ya miƙe kamar wanda aka tsikara da allura, nan suka bisa da ido wardrope Zaidu ya bude yaja akwatinsa ya hau zuba kayansa a ciki, da sauri, Ubaidullah ya mike yana riko gami da tambayarsa me yake shirin aikatawa, me zaiyi yake tattare kayansa,amma sam Zaidu ya ƙi sauraron Ubaidullah tamƙar mahaukaci haka Zaidu ya koma yana kwashe kayansa.
Da karfi Ubaidullah ya fizgosa gami da daka masa tsawa.
"What's wrong with you Zaidu!!?"
Ɗago idonsa Zaidu yayi wanda yake cike da kwalla ya kaɗa yayi ja ya ce.
"Tafiya zamuyi Ubaidullah, ba zaka tafi kabarni ni kaɗaina ba anan, yanda muka zo tare haka zamu koma tare"ya karasa maganar yana shirin fizge hannunsa daga na Ubaidulllah zai ci gaba da kwasar kayansa, Ubaidullah ya sake fizgosa gami da cewa.
"No Zaidu karkayi haka,tabbas na san tare muka zo,amma ita aiki tamƙar rai ce ,bai zama lallai dole mu mutu tare ko lokaci ɗaya ba, dan haka ni kwanan nawa aikin ne ya kare, nasan kai din amininane na gasken-gaske, amma bazan tabbatar da kana sona tsakani da Allah ba, har sai kamin alƙawarin bazaka taba kabar aikinka ba Aminina" nan take suka fashe da kuka suka rungumi juna, Shima KB kuka yakeyi yazo ya rungumesu duka.
"Kafi gaban haka Abokina, nayi maka Alkawarin babu inda zani tunda haka kakeso amma inaso kasani rayuwar aikin soja wajan Zaidu ba zatayi dadi ba indai ba Ubaidu a tare dashi domin Ubaidu shine garkuwan Zaidu"
Murmushin Ubaidullah yayi ya ce.
"Karka damu aboki ne komai zaiyi Normal zaka saba In sha Allah, kuma ma ai ga KB ne" ya fada yana kaiwa KB naushin wasa a kafaɗa, KB ya share hawaye dan ya kasa magana, haka ranar suka zauna a bedroom su ja jimami.
Ta bangaren Mama kuwa faɗawa su Hafiza da Na'ila tayi akan cewa Yayansu Zaizo gobe, Murna suka hauyi su na tsalle,Na'ila ta ce.
"Mama ki bamu kuɗi muje nan Jahun muyi siyayyar kayan abun da zamu girkawa Yaya gobe" Hafiza ta ce.
"Eh kuma hakane Sismie kin kawo shawara Mama bamu kuɗin muje"
Murmushi Mama tayi ta ce.
"Wannan yara, to kuje ku buɗe jakata ku ɗauki kuɗin yadda zai muku" suka amsa da to suka miƙe da sauri,Hafiza taje ɗauko kudin, Na'ila kuma taje ɗauko musu hijabansu.
Mama ta ce.
"Karku jima fa kunga yamma tayi, dama kun bari sai gobe ne tun da babu makaranta"
" a'a Mama tun da mun ɗauko kudi bari muje mu dawo kawai" cewar Hafiza.
Mama ta ce .
"to a dawo lafiya driver ne zai kai ku?"
"A'a nan da Jahun din da zamu ɗan taka kawai"
"To ai Hafiza naga yamma tayi ne ai"
"Karki damu Mama yanzu zamu dawo In sha Allahu"
"To Allahu yasha adawi lafiya" suka amsa da ameen suka fice.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Tsaye take akan titi fara ce amma ba zaka ce mata sol ba domin kuwa boyeyyan haske gareta,tana da ƙaramin jiki sosai bata da tsayi kuma ba zaka ce mata gajera ba,gashi bata da ƙiba kuma ba zaka sakata alayin ramanmu ba, idan ka kalli fuskata zaka ita karantar yanayin fuskarta,tana da son fara'a dan ko a yanzu fuskarta dauke yake da murmushi ga wani farin tabarau da ta saka a idonta tamƙar doctor.
Su Hafiza ne suka zo wucewa, handbag din hannun Hafiza wani Almajiri ya fizge yana shirin ya zunduma da gudu yazo giftawa ta gaban wannan budurwan take ta saka masa kafa ya fadi sannan tayi hanzarin ɗaukar jakar yayinda Hafiza da Naila suka saka kururuwa a cikin jama'a nan aka taro akan wannan almajiri ana shirin a masa rufdugu, kuka ya fara yana bada hakuri akan cewa ba halinsa bane sata yunwace ta saka shi haka.
Nan Hafiza ta hana a dakesa sannan ta ciro dubu 2 a cikin jakar tata ta miƙawa almajirin ya karba ya mata godiya,wannan budurwan ta ce.
"Kai gaskiya kasarmu ta lalace , innalillahi wainna ilayhirrajiun! Ba dole yara kanana su fara sata ba saboda wahala Allah ya kyauta amma dole nayi rubutu na buga akan hakan" jama'ar wajan suka amsa da ameen, kafin ta mai da kallonta kan su Hafiza nan ta hango tsananin kamannin da suke da juna,murmushi ta sakar musu,haɗa baki sukayi gami da cewa.
"Mun gode Anty"
Dariya tayi ta ce.
"Sunana *ABI'ATU*"
Su ma dariyar sukayi.
"To Anty Abi'atu"
Ta ce.
"No ku daina cemin Anty kawai ku kirani da Sunana, baku ga tsawon mu daya ba?"
Murmushi Hafiza tayi ta ce.
"Eh hakane amma ai kin girme mu"
Ita dai murmushin tayi dan ɗabiar fuskarta ce murmushi ta ce.
"To shikenan baku faɗamin sunayen ku ba?" ta fada maganar tana kallon Hafiza.
Hafiza ta ce.
"Sunana Hafiza sismie kuma sunanta Na'ila"
Murmushi tayi ta ce.
"Nyc to meet urs, ni bakuwa ce a wannan unguwar gidan mu yana can wajan bayan masallacin sallar Jumma'a yanzu kuma na fito siyayya ne amma fa kun burgeni ku twins ne?"
"Aa mu ba twins bane ,amma ratan dake tsakaninmu ba yawa, muma gidanmu yana can wajan masallacin"
Ta ce.
"Da gaske?" suka jinjina mata kai, nan ta ce.
"To muje mu gama sai naje naga gidan ku kuma ku ga namu ko za'adinga gaisawa ko?" suka amsa da to.
Bayan sun gama siyayyar tasu sai da suka fara biyawa gidan su Abi'atun wanda gida hudu ne ma kawai a tsakaninsu kafin suka wuce gida daf da magriba.
Da sallama suka shiga parlorn Mama ta rufe su da faɗa kan cewa sai yanzu suka dawo, Abi'atu kuwa tun da ta ga Mama taji wani bala'in kunyar Mama ya kamata wanda bata san dalilin hakan ba, ga kwarniji da Mama ta mata.
Hakuri suka bata sannan suka bata labarin abun da ya faru da suka fita ,har haduwar su da Abi'atu da zuwa gidan su da sukayi yanzu.
Sai a lokacin tukunna Mama ta lura da Abi'atu wacce ra rakub'e a gefen kofar parlour, Mama ta ce.
"Sannu ko ƴata ya kike da Mamar taki?"
Zubewa kasa Abi'atu tayi tana dukar da kai kasa ta gaishe da Mama.
Take Mama taji yarinyar ta kwanta mata a rai.
Na'ila ta ce.
"Mama wannan gidan da aka ginasa kwanan nan, wanda gida hudu ne a tsakanin mu na wancan kwanar shine fa ashe gidansu"
Mama ta ce.
"Ayyo ai kuwa ranar da zanje gidan su Umma mun haɗu da Mamanki mun gaisa"ita dai Abi'atu kanta a sun kuye ta kasa sakewa.
Mama ta ce.
" ku tashi ku shiga ciki kuyi sallar magriba, sai ku kawo mata abinci da abun sha, ku kwashe wannan kayan kuma ku kaisu kitchen" suka amsa da to,sannan suka ɗibi kayan sukayi kitchen, sai da Abi'atu ta ga Mama ta shiga bedroom kafin ta sauke ajiyar zuciya, kamar ance ɗaga kanki nan ta hango ɗan wani lungu tsakiyar TV wanda lungu anyisa dan ajiye pictures, pic din da ta fara tozali dashi wanda ya haifar mata da faduwar gaba wanda harta miƙe taja gaban pic din tana kallo tana shafawa a hankali.
Pic din Ubaidullah ne da kakinsa na sojoji yayi matuƙar kyau duk da fuskarsa a pic din babu murmushi, dan guntun tsaki tayi dan ta tsani mutum wanda baya murmushi ya fiye haɗe rai ita ana zubin kenan.
Sake ɗaga kai tayi ta ga wanda sukayi ga Mama da Anty Ummu dasu Hafiza nan ta ga yayi murmushi sai da fararen teeth dinsa suka bayyana, itama murmushin tayi ta ce.
"Yauwa jarumin maza ko kai fa anan kafi kyau"
Gefe ta sake kalla ta gansu su biyu da kaki, a zuciyarta ta ce to wannan kuma fa ko shi da waye, bata san a fili ta faɗa ba sai ji tayi Na'ila ta ce.
"Shi da Babban amininsa ne dukkan su Sojoji ne" da sauri Abiatu ta juyo ta kallesu su na mata dariya taji kunya ya kamata ta ce.
"Lah kuyi hakuri " ta juya da sauri Na'ila ta riƙota ta ce.
"A'a Anty tsaya ki gani, kinga wancan pic din" tayi mata nuni da wani pic a sama wanda bata ma gansa ba sai yanzu, a gefen pic din ta ƙasa anyi rubutu da jan alkalami *R,I,P FATHER*, gaban Abi'atu ya bada dam! Ta juya tana kallon su, taga su na share hawaye, Na'ila ta ci gaba da magana.
"Baban mu ne, shi ma kuma soja ne Allah ya masa rasuwa a bakin aikinsa na soja, kinga wannan pic din kuma, da Mama da Babbar Yayarmu Sunanta Anty Ummu, sai Yayanmu sunansa Ubaidullah sai Sismie sai ni, yanzu haka Yayan namu yana aikin sojansa a garin Abuja, wannan pic din kuma shi da Abokinsa ne wanda suka taso tare, gobe kuma idan Allah ya kaimu zaizo"
Sosai Abi'atu taji familyn ya burgeta taji kuma tana son ganin Ubaidullah ido da ido amma daga ganinsa za ayi ji da kai da miskilanci.
Hafiza ta ce.
"Muje muyi sallah fa kar Mama ta fito"
Bedroom suka shiga bayan sunyi Sallah Hafiza ta fita domin kawowa Abiatu abinci.
Abiatu ta kalli Naila ta ce.
"Sis amma Yayan kun nan yana da ji da kai ko naga baya dariya?"
Murmushi Naila tayi ta gyara zama gami da cewa.
"Yayanmu baya da ji da kai, amma ya kasance baya son hayaniya da magana, kuma yana da miskilanci, ga zuciya, amma yana da saukin kai ga wa inda suka fahimcesa suka san halinsa, yana da dadin zama domin kuwa yafi karfin Yaya shi ɗin Ubana a wajanmu har ma ga Mama dan itama da bakinta take fadi, Yayanmu yana yaƙi da abubuwa dayawa a rayuwarsa,duk yanda muka zama nagari da taimakonsa ne"
Dan murmushi Abi'atu tayi kafin ta tabe baki zata yi magana taji Hafiza na magana a bayansu wanda ta shigo dakin yanzu hannunta da tray din abinci.
"Tabbas haka ne duk abun da Naila ta faɗa miki akan Yayanmu,ba shi da girman kai, amma kuma duk wanda basu fahimcesa ba kallon mai girman kai suke masa kamar yanda ke ma yanzu na tabbata haka kike masa"
"Aa to kuyi hakuri karku min taron dangi dan da alama kuna son Yayan kun nan sosai" ta fada ta ciro wayarta ta danna video recording.
Murmushi Na'ila tayi ta ce.
"Idan har muna son shi sosai to shi kaunar mu yake, kuma ba da zuciyarsa yake sonmu ba, da ranshi yake sonmu, to idan har ya so mu da ranshi mu da me zamu so shi?"
Dariya Abi'atu tayi ta ce.
"To ai na bada hakuri, nace ayi hakuri kar a mun taron dangi a dakeni"
A tare suka sa dariya.
"Ah haba dai Anty Abi'atu taya zamu miki taron dangi mu da muke so ma idan yazo gobe ku dai-daita ayi yar gida, ko ba haka bane Hafiza?"
Hafiza wacce take dariya itama ta ce.
"Hakane kam wallahi dan sun dace"
Na'ila tana dariya ta ce.
"Allah yasa zanga bikin wayyo ni a ranar zan sha rawa bikin Yayana"
Nan dai suka ci gaba da hira kamar wanda sun jima da sanin juna, sai da akayi sallar isha'i kafin Yayan Abi'atu mai sunan Safwan yazo suka tafi gida.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
A bangaren Ubaidullah da Zaidu da KB kuka suka sha ba kaɗan ba suka taya Ubaidullah haɗa kayansa,tun a daren ya sa kayansa a booth.
Da washe gari misalin karfi goma A babban filin taro na barracks, dandazon Sojoji ne birjik yayinda, da ka ɗaga kai kaki ne ke kashe maka ido.
Ubaidullah tsaye akan Munbarin taro sanye yake da Baƙin wandon jeans da farin t-shart, fuskarsa fayau ba zaka iya gano me fuskarsa da zuciyarsa suka kunsa ba,cike da natsuwa da izza da jarumta ya fara magana cikin harshen turanci.
" _Assalamu alaykum da farko ina gaida manya na, tare da abokan aiki ina yiwa kowa fatan Alkhairi, sannan ina neman gafarar wa inda na batawa a barracks din nan, ni na yafewa kowa daga ciki kuwa har wa inda suka kulla min sharri, mahaifina yasha faɗamun lokacin ina yaro kafin yabar duniya,cewa duk wanda ya min sharri na saka masa da alkairi, da babu wanda ya isa yayiwa wani abun da Allah bai masa ba, sai dai idan ya fito acikin littafin kaddararsa, dan haka na dauki kaddarata, kuma na yankewa kaina hukunci, ba lallai dole sai kun yarda dani ba, idan na faɗa kukaji ma ya biya bukata, *BAZAN AURI RUMAISA BA, SABODA BANCI NANIN BA, NANIN BA ZATA CINI BA, A YAU KUMA NA AJIYE AIKINA NA SOJA*._
Maganar da ya gigita su General kenan wanda ya saka su kallon Ubaidullah yayinda hankalin jami'ai sama da dubu ya tashi dan Ubaidullah garkuwa ne a barracks ba za a fahimci hakan ba sai baya nan.
Juyawa Ubaidullah yayi ya ajiye takardan a gaban General Of The Army gami da sara masa, sannan ya sarawa su Major, wa inda suke kasa dashi suka sara masa bai jira cewar kowa ba ya wuce da sauri ya bar filin taron take wasu suka fashe da kuka wasu kuma suka shiga ruɗani, wasu kuwa zuciyarsu fes.
Cikin ɗimauta Rumaisa ta miƙe da kuka, kamar ta faɗi gaskiya amma wani zuciyar ya haneta.
Zeey kuwa suman tsaye tayi na wucin gadi kafin ta juya da gudu tabi bayan Ubaidullah har ya shiga mota su Zaidu su na tsaye, da sauri ta sun kuyar da kanta ta glass tana hawaye ta ce.
"Captain am very very sorry for what happen,don't worry i will try my best to find out true i promise, u will come back this barracks very soon"
Ta karasa, maganar tana hawaye, ta juya, Ubaidullah ya ce.
"Tnk u very much Zeey, but I don't want to come back, don't mind"
DA karfi ya figi Motar Sai ga Hawaye na bin fuskar Zaidu, Zeey ta ce.
"Captain Zaidu shin kuna tare dani? Zaku taimaka min mu haɗa guiwa mu gano gaskiya ko da Ubaidullah ba zai dawo ba, amma tabon da Rumaisa ta masa ya goge, shin zaku tayani?" Zaidu ya ce.
"Muna tare dake Zeey, nasan ma karya ne Ubaidullah yace bazai dawo ba dan yana son aikin soja, amma gaskiya bana tunanin ko zai dawo wannan barracks din, idan kuwa hakan ta kasance tabbas zan bar barrack din nan nima" ya na gama fadi ya juya da sauri KB ya bi bayansa Zeey ta kama gabanta domin ta fara bincike akan lamarin.
➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
Ta bangaren Ubaidullah kuwa yana fita ya kira Mama ya shaida mata cewa gashi nan ya taso Adduar Allah ya tsare hanya ta masa sannan sukayi sallama, ya kira Anty Ummu ya fada mata,itama ta mishi Allah ya kiyaye hanya.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Fitowa Mama tayi ta samu Hafiza zaune a Parlour ta ce.
"Hafiza wai nikam ina Na'ila ne kam tun safe ban ganta ba?"
"Wallahi nima Mama ban ganta ba ,dan tun da mukayi sallar asuba ta fice"
Salati Mama ta hauyi tana tafa hannu.
"Wato ita dai Naila ba zata taba shiryuwa ba kenan yanzu ina taje da safe dan Allah?"
Hafiza ta ce.
"Kiyi hakuri Mama bari naje gidansu Anty Abiatu na dubota" Hafiza ta saka hijab dinta ya fice.
Ko da taje Ummin Abiatu ta ce mata Naila tazo dazu amma ta tafi dan ko da tazo bata zauna ba, gida Hafiza ta dawo ta fadawa Mama, Mama ta kira Anty Ummu ko taje gidanta ne, Anty Ummu ta cewa Mama tazo amma bata jima ba ta tafi, Mama ta ce.
"To ai shikenan zanga ta inda zaki dawo ga Yayanku yana hanya idan da rabon ki sake cin wani na jakin a hannunsa ne to"
Naila bata dawo gida ba sai shabiyun Rana da dariyarta da shiga da sallama, Mama da Hafiza su na zaune jigum-jigum, Mama ɗago ta rufe Naila da faɗa.
"Yanzu ke Naila ba zaki yi hankali ba? Da za adinga miki magana amma ba zaki ji ba? Ace kullum a tayiwa mutum magana akan abu daya? Naila so kike sai kin kasheni da rashin jin maganarki ko? Ko maganar da kika daukowa Yayanki dani kwanaki ne bai isheki ba? Naila ina miki faɗa ne dan ki gyaru tun ina da raina kafin na mutu ki rasa wanda zai miki, kum...." maganar da Mama bata karasa ba kenan Naila ta rungumeta ta fashe da Kuka.
"Dan Allah Mama kiyi hakuri, wallahi ba yawo naje ba tun da nayiwa Yaya Alƙawari na daina ai ban sake ba, Mama ban fita a gidan nan ba fa sai wajan karfe tara, ina part din Yaya ne ina gyara masa,Idan ma baki yarda ba muje ki gani, ko kuma ki tambayi mai gadi, ko da na fita gidansu Umma naje na fada mata yau Yayanmu zaizo take tambayata akan cewa bata san da zancan zuwansu ba, nan muka sha hira dasu afnan, dana tashi shine naje gidansu Anty Abi'atu na fada mata Yayana zaizo yau, daga nan na wuce gidan Big Anty na gaya mata take cemin ta sani, to shine fa naje yelwa tsohuwar unguwarmu na fadawa Gwaggo Ladi Yaya Ubaidulllah zaizo, amma dan Allah Mama kiyi hakuri bazan sake ba" tana maganar tana kuka harda sheshsheƙ.
Mama ta ce.
"To naji kukan ya isa haka, ni dai so nake ki zama ta kwarai Naila kinga yau ace na mutu bana raye idan ba Ummu da sauran mutanen kwarai ba, babu wanda zai zaunar dake ya faɗa miki gaskiya"
"Mama dan Allah ki daina fadin zaki mutu, baba ya mutu kema kina