COLONEL UBAIDULLAH by Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢

Author :  Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category :  Romance

Chapter   16 / 25

45K to 48K   out of 74.6K words

zai tafi yadda akeso tinda akwai munafukai da yan hassada da makirai, yau ranar tonan asiri ne, a barracks din nan domin ance karshen alewa kasa, rana dubu ta b'arawo rana daya tak ta me kaya" gaba daya aka zubawa Zeey ido ta tsuƙe cikin kakinta fuskarta babu walwala hannunta dauke da wasu takardu.


Ta ce.
"Hakika ita karya fure take bata ƴaƴa, kuma kowa yasan gaskiya, dan haka zan tona asiri koya ya kasa kunnuwansa da kyau, sannan dole wanda aka zalunta idan ya ce bazai yafe ba, masu laifi su shiga kotu."




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



*TO HAR AN ZUBA IDO DA KUNNUWA DAN AJI TONAN ASIRIN DA ZEEY ZATAYI KO? L😉LZ TO BA ZA KU JIN BA SAI A NEXT PAGE*


A CI GABA DA KAFCE 🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️DAN AKWAI ƘURA




MOMYN AHLAN TA KU CE👍🏻😉🤾🏻‍♀️👯🏻‍♀️🏃🏻‍♀️[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*~UBAIDULLAHI~*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*_DAN ALLAH YAN UWA, A DIN GA SA HAKURI DA UZURI 👏🏻 WLH NI IDAN NAYI POSTING BANA SAKE BUDE GRP IN DAI BA GRP DINA BANE, AKWAI WASU GRPS DIN MA BANA BUDEWA IN DAI BA POSTING ZANYI BA, KO ZAN SHARE SAKONNIN, TUN BA YAU BA NAKE SON YIN MAGANA ALLAH BAI BANI IKO BA, IDAN NAYI POSTING KINA SO DAGA FARKO KI BINI PC NA TURA MAKI, KARKI JI HAUSHI KIN MIN MAGANA A GRP BAN GANI BA KI JI,HAUSHI HAR GA ALLAH BAN JI DADIN WANI MAGANA DA AKA GAYA MIN BA, IDAN KUMA BANI NAYI POSTING DIN BA, WANDA SUKA YI KI MUSU MAGANA TA PC SU BAKI, ALLAH KA KARA MANA HAKURI DA UZURI GAMI DA FAHIMTAR JUNA, AMEEEN_*


( _GASKIYA YANZU YAN WATTPAD BAKU COMMENTS NA KUSA NA DAINA MUKU POSTING TUN YANZU BAKU SON BUK DIN_🤒🤒)

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


*_YAU FA PAGE DIN NA KU NE 💃🏻 MASU COMMENTS GASKIYA KUN SAKANI NISHADI A PAGE DIN DA YA GABATA DAN HAKA KU WATAYA DA WANNAN, GA KU NAN KAMAR HAKA_*👇🏻💃🏻


*princess*
*Surayya usman*
*Farhat mrs mj*
*Amina yayaji*
*Dr,herpsert*
*Ma'eeshatii twinkle*
*Fadheelatii*
*Asamau umar gajam*
*fareesatii*
*nafeesat*
*Mom ayman*
*Faeexetion*
*firdausi mrs mubarak*
*Maman zarah*
*Maman abdul*
*Bilkisu sulaiman*
*Maman yan 2*
*Kcubraah*
*Ummi suraj*
*Ummu imam*
*ummi*
*Mrs Faruq*
*Maryam abdullah*
*maman afreen*
_________________
*@⁨I LOVE MY FAMILY* 🥰⁩
*@⁨Hassana Suleiman⁩*
DUBAI FANS
_______________
😍 aha a fa duba da kyau, duk wacce bata ga sunanta ba, ban ga sharhinta bane, sai ta tareni a page na gama,a kara dagewa da sharhi, 😍 ni kuma zan din ga kyautar page gareku masoyana, a kafta. 🤾🏻‍♀️


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



*page°°°°°71&75*




"What do u want to say Zeey?" cewar General Of The Army, rai bace Zeey ta fara magana.



"Abubuwa dayawa sun faru, but babu wanda ya bada mahimmanci ganin an yi bincike an gano sahihin gaskiyar abun da ya faru, kowa ya yi watsi da case din Captain Ubaidullah tun da yabar barracks din nan, duk da kuwa ya yi aikin tuƙuru"


Wajan shuru ya dauka sai ka ce ba mutane ana sauraron Zeey, ya yinda zuciyar Rumaisa ji take kamar ana daka, dan tana tsaye a wajan itama, kuma Zeey da ta shigo ta watse mata wani kallo wanda ta kasa fahimtar me kallon yake nufi, dan haka ta miƙe subul zata bar filin taron, Hanan da Raihana da Doratie suka tare ta, Zeey ta ce.


"Hamshaƙiyar munafuka! Ina za ki? Tun ba ki jira kin ji abun da zan zayyano ba, kina neman haryar guduwa?"



"Duk da bincikena ya daukeni tsawon lokaci, amma alhamdulillah sai hakan ya zama alkhairi, dan yau ba ƙaramin yagaki zan yi ba."



"Idan lissafina ya yi dai-dai yau tsawon kimanin 9 to 10 months, da barin Ubaidullah aiki, and Rumaisa kin ce ya miki ciki, 4now i think ya ci ace kin haihu, kin haife abun da yake cikinki hakane?" zazzare ido Rumaisa ke yi ta kasa bada amsa, Zeey ta ce.


"Hanan, ku hauro da ita gaban kowa ya ganta yadda suka wulakanta Captain a bainar jama'a, haka su ma yau karyarsu zata kare, dan kare fure take bata ƴaƴa" ai kuwa su Hanan suka cafko Rumaisa suka daura ta saman mumbari sai zufa ne ke keto mata ta ko ina, a sassar jikinta.


Zaidu duk abun da ake yi yana video recording, dan kuwa tare suka haɗa baki yau za ayi tonon asiri.



KB kuwa ya sakawa S Ema Ido dan shi ma duk ya daburce tun ba a je ko ina ba, dama hausawa su na cewa marar gaskiya ko a ruwa gumi yake.



Gaban Rumaisa Zeey ta tako ta zo, fuskarta tamau, ta ce.
"Ki bamu amsa Rumaisa, and ko da sau daya ne da Captain ya bar barracks din nan ban ga kinyi wani laulayi irin wanda masu ciki ke yi ba, idan ta samu ciki, akasari ma ban da iskancinki da kike sheƙawa a barracks din nan, wanda nan gaba zan ambato sunan abokin cin mushen naki! Rumaisa ko da sau ɗaya ne ban ga ciki ya girma a jikinki ba, shi kuwa ciki, ko da ka boyesa baka faɗeta ba, ita zata bayyana kanta dan ciki bata b'uya, ko wani anan ya ga Rumaisa da katon ciki tsawon wannan watannin?" nan jama'a aka hau girgiza kai masu cewa a'a su na fadi, sai yanzu suke bin abun daki-daki, da hankali da basira, ya yinda manya suka shiga ruɗu na ganin babbar kuskuren da suka tafka, in dai Ubaidullah na da laifi su sun fi sa laifi a matsayinsu na manya da basu bada mahimmancin bincike ba.



"Rumaisa!!" Zeey ta ambata da karfi, wanda sai da hanjin cikin Rumaisa ya kaɗa sabida tashin hankali, nan mahaifin Rumaisa ya fito yana yiwa Zeey katsa'landan, Zeey ta ɗaga masa hannu.
"Dakata! min tsohon najadu, kowa tarrr nake kallonsa a barracks din nan, ban zo kanka ba tukunna , karka katsemin hanzari, dan yau ko da General ne ba zai dakatar dani wajan fadin gaskiya ba balle kai stall sergeant" shuru Baban Rumaisa ya yi yana wulli-wulli da ido.




"Rumaisa da ke nake yi, ina labarin cikin da kika ce Captain ya miki?" cikin in'ina Rumaisa ta ce.
"Ai cikin ya zube ne"
"Au haba? Da gaske cikin ya zube? Tun da zubar ciki tamƙar fitowar fitsari ne da har zai zube baki kwanta a gadon asibiti ba? Amma fa ba wai ina nufin na karyata ki bane, yaushe cikin ya b'are?"


"Ammm uhumm hummm eh wata biyar da suka wuce"

"Au da gaske? Shi kuma cikin da yake jikinki kimani wata biyu yanzu na waye ne!?"

Dum!dum!dum!dum!
Gaban Rumaisa ke bugawa, zazzare ido take yi, ya yinda zufa bai fasa tsatstsafo mata ba, hannu Zeey tasa ta shafo zufar fuskar Rumaisa ta ce.
"Rumaisa, wannan zufar duk na menene uhum?, mai gaskiya fa hankalinsa baya tashi, kuma fa naga ba tsareki akayi da bindiga a kai ba, yo ni ko tsareki akayi da bindiga ai ba zakiyi wannan zufar ba in dai kina da gaskiya, da ga tambaya? Cikin da yake jikinki yanzu watan shi biyu shi kuma na wanene? Ko shi ma na Captain din ne?"



"Kee! Ya isheki haka Zeey! ba fa tsoronki nake ji ba!, da zaki wani sakani a gaba kina min tambaya sai kace wata Uwata! Uban waye ya ce ina da ciki, babu wani cik...." maganar da Rumaisa bata samu damar karasawa ba kenan, sakamakon wata gawurtacciyar marin da Zeey ta ɗauketa da shi sai da ta kifu ta buga baki sai ga jini.



"Ke har kin isa ki daga min murya Rumaisa? Da kika cewa ni ba uwarki bace bana fata Idan nayi aure Allah ya bani ƴa kamarki mashanranciya munafuka!, sannan a ta wani fanni ni nafi karfin uwarki! ko ubanki!, dan kinsan duk matan barracks din nan babu wacce ta kaini zafi, idan kuma akwaita ta ɗaga min hannu, tambayarki nake yi dan musan gaskiyar lamari, kuma ni ban daga miki murya ba, me yasa ni za ki daga min murya? Ko ni mate dinki ce?"



Filin taro kamar ba kowa, dan kuwa rashin gaskiya ya bayyana ƙuru-ƙuru a fuskar Rumaisa, dan haka su General Of The Army, General, Major General, General, Colonel, Brigadier lieutenant Colonel duk manyan wajan babu wanda ya dakatar da Zeey ko kuma ya katseta ko ya ce abun da take yi bai dace ba, sabida yanzu mafita suke nema, dan nadama ta fara kamasu, su na so su san gaskiyar lamari dan a samu a ba wa Captain hakuri ya dawo bakin aikinsa dan a samu a ceto rayuwar yan matan da aka yi garkuwa dasu, sabida rayuwarsu tana cikin hatsari.



Marin da Zeey ta kifawa Rumaisa sai da ta ga gittawar wasu taurari a idanuwanta da fuskarta, network din kanta sai da ya je hutun wucin gadi, kafin da kyar ta miƙe tsaye tana dafe mararta wanda ya murɗa mata lokaci guda.



Kuka Baban Rumaisa ya saka gami da cewa ana so a tozarta sa shi da ƴarsa, amma babu wanda ya sauraresa.


Ganin badaƙalar tana yin yawa ne, kuma ga shi asiri yana gaf da tonuwa ya sa, S Ema neman hanyar da zai fece daga filin taron, amma me tuni KB yasa masa kafa ya fadi gami da cewa.
"To Almirin'jaki, baƙin munafuki algungumi, ina zaka je?" nan aka juyo ana kallon S Ema, Zeey ta ce.
"Shi ma wai guduwa zai yi ko? Hahaha ina son irin haka, KB riƙesa da kyau ban zo kansa ba tukunna"


"Rumaisa ke muke saurara?"


Cikin rawar murya Rumaisa ta ce.
"Ni kam sharri! Kike so ki min, amma ni kam bani da wani ciki."


"Au haba? To shi kenan, Dr Mark!?" Zeey ta kwalawa Dr kira wanda dama yana kusa, babban likita ne a cikin asibitin dake barracks yawanci idan ciwo ya yi tsanani shi yake duba marasa lafiya masani ne sosai ta fannin aikinsa, kuma babban mutum ne dan a kalla shekarunsa zai iya kai wa 69 yawanci ana girmamasa a barracks din sosai.


Tun da Zeey ta ambaci sunan Dr Mark, hankalin Rumaisa ya sake tashi, fitowa Dr Mark ya yi, dan shi ma Ubaidullah mutuminsa ne sosai, kuma yana son Ubaidullah, sabida kamun kai din Ubaidullah yasa yake birgesa,duk da yana barracks din amma bai san abun da ya faru da Ubaidullah din ba, tun da baya shiga hidimar fannin aikinsu yafi zama wajan fannin aikinsa, hawa kan mumbari Dr Mark ya yi, sannan cikin girmamawa Zeey ta zo gabansa da takardun hannunta ta ce.
"Baba Mark, kai ne ka gwada Rumaisa shekaran jiya har result ya fito jiya,a in da ka gano tana da jaririn ciki na tsawon wata biyu haka ne?" cikin harafin turanci suke magana.


"Shakka babu, nine nan na au'na ta kuma ga result din a hannunki, tana da jaririn ciki na wata biyu"



"Good! Ko Rumaisa ta taba yin b'ari wata biyar da suka wuce? Tun da dai nasan babu wani asibitin da zata kwanta in dai bana cikin barracks ba?"


"No, bata kwanta ba, cox 2years kenan yanzu ban yi tafiya ba, ina nan, balle ace ko bani nan wani Dr ya dubata."


"Tnk u sir" cewar Zeey, kafin ta juyo ga Rumaisa, wacce hankalinta ya kai ƙoluluwa wajan tashi, dan tasan karyarta ya kare yau.



"Rumaisa lokaci ya yi, da za ki bude baki kiyi magana, shawara ce nake baki,tun kafin na bayyana wani video kuma idan har na bayyana videon nan ba kiyi magana ba hummm! Rumaisa ni a karan kaina bansan abun da zan iya aikata maki ba, gwanda ki bude baki kiyi magana, First Lieutenant KB ka hauro da S Ema."



Nan KB ya hauro da S Ema wanda shi ma yake zare ido, Zeey kallonsa take yi ranta bace ta ce.
"Zaku yi bayani ne ko kuma sai na saki videon? Kunsan halina wajan bincike bana sanya barin ma wanda na saka kaina, akan Captain zan iya muku komai, dan haka zaku faɗi gaskiya ne ko har yanzu zaku ci gaba da kauce-kauce da neman hanyar guduwa, ko kuma kokarin shirya drama, kai za kayi bayani ne, ko kuma karya za ka yi kamar yadda ita...b sai na karasa ba dan ka fi ni sani abun da nake nufi ko?"


Shuru S Ema ya yi gabansa na faduwa suka haɗa ido da Rumaisa, sai zufa suke yi, Zeey ce ta ce.
"Bana son aiki da bata lokacin dan hak..."

"No! Pls!" cewar Sergeant Ema.
"Zan fadi gaskiya duk abun da na sani."



"Yauwa dan gari, muna sauraron ka?"


"Lokacin da nazo barracks din nan Captain baya nan amma ina jin labarinsa, kasancewar ni mutum ne mai ƙyashi da hassada, da haka har alaƙa ta shiga tsakani na da Rumaisa, har take bani labarin Captain Ubaidullah da yanda take son sa take sha'awarsa, ko da Captain Ubaidullah ya dawo daga tafiyar da su kayi na ganin gida, na ga yanda ake ba da labarinsa yana da kyau da gwarniji kamala, haiba, nasaba, kamun kai, ji da kai, jarumta, gwarzon maza, ƙi gudu sa maza gudu, dana gansa sai na ga duk yafi yadda ake bada labarinsa, da haka ne Rumaisa ta zo ta sameni wata rana da wani video karami wanda ta rungume Ubaidullah har ya wanka mata mari, to wannan videon ne muka haɗa lokacin ne muka kwanta da Rumaisa a karo na farko sabida ta ce tayi alwashi sai ta muzguna masa, fuskata ne muka yi amfani da shi muka saka fuskar Captain, wanda da shi ne aka samu madafan dafawa domin a tozarta shi ya aureta, shi kuma ya ƙi, ko bayan faruwar hakan da ya bar aiki bamu daina mu'amala da Rumaisa ba, kuma babu wani ciki a tare da ita lokacin, munyi wannan videon ne dan mu kawar da tunanin manya dan kar ace aje a au'nata, kuma munyi nasara a wancan lokaci, kuma ko yanzu cikin da yake jikin Rumaisa nawa ne, wannan shi ne gaskiya abun da ya faru wanda na sani amma dan Allah ayi hakuri bazan sake b..."


"Shut up!!'' Cewar Zeey ta katse sergeant Ema idanunta sunyi ja, juyawa ta yi ta kalli manya ta ce.
"Kun gani ko? Kun gani ko? Abun da muka ta fama ku fahimta kenan tun kwanaki amma kun kasa fahimta, ba iyakar binciken da nayi akan Rumaisa ba kenan, domin tun lokacin da Captain ya bar barracks na fara bibiyar rayuwar Rumaisa da duk wani shige da ficenta, ko da muka je bauchi nice kawai bani nan amma duk abun da ke faruwa ina sane dashi, idan wannan hujjar bai isheku ba, sai na sake muku wasu wanda zaku gansu ƙuru-ƙuru, kuma Wallahi Rumaisa idan har ba ki buɗe baki kinyi magana ba ko, Rumaisa idan na rufeki da duka sai na kaiki lahira kuma na kashe banza! Idan kince wasa ne to mu zuba mu gani!"


Nan Rumaisa ta zube kasa tana kuka, tana cewa ta tuba a yafe mata, Major Usman ya ce.
"A tafi da Rumaisa da S Ema a saka su a guardroom, kafin a san abun yi" nan Rumaisa ta hau ihu tana kuka tana magiya, Babanta ma yanayi, amma ina babu wanda ya saurare su, nan fa aka ce an kira secret meeting a secret room wanda manya ne kawai zasu yi wannan meeting din, dasu Zaidu da KB, amma daga ciki har da Zeey.




Ko bayan da aka shiga secret meeting magana ce ake yi akan ya za ayi aje a bawa Ubaidullah hakuri ya dawo bakin aikinsa.



Zeey ta ce.
"Captain Zaidu ka kira mana Captain Ubaidullah"

Murmushi Zaidu ya yi, ya ce.
"Nasan halin Ubaidullah sarai, ba zai taba yarda ya dawo ta dadi ba, but let me try my best" Zaidu ya faɗa yana kokarin kiran Ubaidullah.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




Tsaye take a gaban dress'mirror ta fito wanka ranta bace, rigimar da suka yi da Ubaidullah ne idan ta tuno yake bata mata rai, sabida maganar da ya gaya mata duk da a gabansa bata nuna taji haushi ba.


Towel ne a jikinta ta sincesa ya fadi kasa, tunowa da maganarsa ta karshe tayi in da yake ce mata.
"Kwaila, yo ke miye kike rufewa? Yaushe kika girman? Me kike dashi wanda za ki burgeni ko ki tafi da hankalina,miye a kirjin naki abu fili, yarinya yar firit dake sai baƙar jaraba da iyayi, ji be ki fa, yar abu dake!"


Rintse ido tayi ta ce.
"Hummm! Ni ce ka kira da yar abu? Zaka gane shayi ruwa ne, wallahi sai kayi yaren garinku in dai akwaita" ta dauki towel dinta ta daura ta bude wardrobe ta dauki english'wears dinta wando da riga, duka-duka wandon da kaɗan ya wuce mazaunanta, sai kuma wata yar fingilar riga marar hannu, wanda ko saman shafefen cikinta bai sauƙa ba, ta sharce gashinta ta zubo da wasu ta gaba, ta hada sauran ta tufke a tsakiyar kanta, ta shafa lipstick ta goge fuskarta, nan ta juyo ta kalli kanta a madubi tasan fa ta gama kyau ne, murmushi ta yi ta saka flat'shoe ta dauki humra wanda Ummi ta bata, ta mulkawa jikinta nan ta hau wani tashin ƙamshi wanda duk namiji mai lafiya idan ya ji sai tsuminsa ya tashi, wayarta ta dauka ta dauki earpiece ta saka, ga shi dai ba waƙa ta saka ba, a'a kawai zata je neman rigima ne tun da yanzu tasan ya shigo.



Ubaidullah na kwance a dogon kujerar parlour, ya baya tv baya, haka kawai yake jinsa wani iri, bai yi auni ba ya ji wani kamshi ya daki hancinsa wanda ta haifar masa da kasala gami da sha'awa, kamshin ya dakesa ne a lokacin da ta bude kofar ta fito, tana taku tana jijjiga, ga shi dama bata sa bra ba, ga wandon da ta saka sunan shi yaka muna wando ne.



Tsakiyar parlourn ta zo tana dan taka rawa tana lumshe ido tana satar kallonsa,a hankali Ubaidullah ya juyo ta yi saurin juyawa tana ci gaba da rawar tana jujjuyawa.


Dum!dum!dum! Gaban Ubaidullah ya buga sadda ya yi tozali da sintima'sintiman cinyoyin Abi'atu, a ransa ya ce.
"Wallahi wannan yarinyar ba za ki kasheni lokaci na bai yi ba."


"Keeeeeeee!" ya buga mata tsawa, amma ko gizau Abi'atu ba ta yi ba, balle ta gwada masa alaman ta ji, a fusace Ubaidullah ya miƙe ya fizgota, ya fincike earpiece din ya jefar gefe yana aika mata da harara.



"Keee! Wannan wani irin iskancin shiga ne!? Na ce wani sabon iskanci ne!? Da za ki kama ki fito tsirara!?"


"Au yanzu kai dama tsirara ka ganni saboda filin yaƙi

16 / 25