COLONEL UBAIDULLAH by Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢

Author :  Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category :  Romance

Chapter   6 / 25

15K to 18K   out of 74.6K words

ya ƙare ku, gabanku da bayanku dama da hagunku, Allah yasa kuje aikin da aka tura ku lafiya ku dawo lafiya tare da manyan nasarori, Allah ya muku Albarka gaba'ɗayan ku"


Sosai jikinsu ya sake yin sanyi duk da sun saba da nasihan iyayen nasu, amsawa su Ubaidullah suka yi da amin, sannan suka ƙara da cewa.
"In sha Allah zamu kiyaye Mama, mun gade Allah ya ƙara girma da nisan kwana"

Mama ta amsa da amin tana murmushin karfin hali dan hawaye ne ya cika tam a idonta, juyawa tayi zata koma cikin gida, ta ji muryan Ubaidullah, "MAMA"
ya kira sunanta, tsak Mama ta tsaye amma bata juyo ba.

Takowa Ubaidullah yayi yazo gabanta sannan ya rungumeta idonsa yayi ja sosai,baya so ya kashe mata jiki gashi dama tana fama da hawan jini so yake ya ce mata, ta yafesa idan har yayi mata wani laifi amma yaga alamunta ma hawaye take son yi dan haka ya canza akalar maganar ta hanyar cewa.

"I gonna miss Mama"



Nan ma murmushi tayi ta shafo fuskarsa, "miss u more son Allah ya maka albarka kuje yanzu kam, karku makara uhum?"

Ɗaga kai Ubaidullah yayi, sannan ya saki Mama ya juya ya koma wajan su Anty Ummu da suke tsaye, Anty Ummu tana yiwa Zaidu tsiya , sai dariya yake yi yana sun kuyar da kai ƙasa yana satar kallon Na'ila, wacce suka takure waja daya ita da yar uwarta wanda da kaga alamun su kasan ƙiris suke jira su saka kuka, dama sun saba duk zuwan Yayan nasu idan zai koma sai sun masa kuka tun da yana shafe watanni kafin yazo idan kuma yazo baya wani jimawa zai koma ,idan har ya jima shine yayi 1week ya koma.


Kallon su Ubaidullah yayi sannan ya bude bakinsa ya hankalin ya kira sunan su. "My flowers" sannan ya bude musu hannayensa da gudu suka rungumesa suka sa kuka, ita ma Anty Ummu bata san lokacin da hawaye ya wanke mata fuska ba, hawaye ta hau yi, Ubaidullah ya sake su Hafiza ya juya yana kallon Anty Ummu girgiza mata kai yayi alamun tayi shuru, sannan yasa hannu ya goge mata hawayen,da sauri ya shige mota Zaidu ma ya shiga yaja su Anty Ummu dasu Hafiza su na ɗaga musu hannu , mai gadi ya bude musu gate suka bar gidan suka ɗauki hanyar birnin tarayya Abuja.



~~~~~~~~~



Sallah ce kaɗai ya tsaida su Ubaidullah a hanya.


Sai karfe 4:30pm su Ubaidullah motar su tayi parking a *9JA BARRACKS ABUJA*.

da K,B suka fara haduwa nan Zaidu ya fito da sauri suka rungumi juna,amma kafin Ubaidullah ya fito sai da ya gama shan kamshinsa tukunna har K,B yana cewa. "wai ina guy din nan yake ne,ko bai dawo bane shi?"

Murmushi Zaidu yayi sannan ya ce.
"Amma dai inaji K,B ka manta da waye Ubaidullah ko? shiyasa bai fito a mota ba kake tambaya idan bai shaƙi kamshi ba kafin ya fito taya za a gane cewa Captain Ubaidullah Abdullahi ya dawo?"

Suka sa dariya su na tafawa, dai dai nan Ubaidullah ya zuro kafafunsa ƙasa ,fuskar nan tamau ba annuri, K,B yazo suka rungumi juna Ubaidullah yayi wani miskilin murmushi sannan suka jera har part dinsu.


Bathroom Ubaidullah ya wuce direct domin yayi fresh up bcox a gajiye yake, ya kwashi kusan 30mnts kafin ya fito daure da towel a kugunsa, juyawa yayi ya kalli Zaidu wanda ya baje a bisa katifa ya ce.

"Hey guy oya get'up kaje kayi fresh up ka samu relief, dan ni yanzu ji nake babu wanda ya fini jin dadi da nayi wanka."


Dariya K,B yayi ya ce.
"To nifa na kasa ganewa, Abokina ai na ɗauka zaka dawo da mata amma kuma sai na ganka daga kai sai jakarka, ya haka to?"


"Mtssww hummm don't wast u tym , ashe duk karyan banza ce da yake cewa zai yi aure yanzu"

Cike da rashin fahimta K,B yake bin su da kallo daga Ubaidun har Zaidu.

"My guy ban gane ba, fahimtar dani kamar ya karyan banza?"


"Ba gashi nan a gabanka ba, kuma yana da baki ya fada maka da kansa"

Juyawa K,B yayi yana kallon Zaidu wanda yake kwance yana aikawa da Ubaidullah harara.


K,B ya ce.
"Ni dai yanzu ka bar wannan hararan nasa ka bani labari hararan kayi masa anjima, meya faru?"


A hasale Zaidu ya miƙe zaune ya ce.
"Wallahi Yaya Captain ka kiyayeni dan ma ka samu yanzu zan dinga kiranka da suna Yaya shine kake min tsiya?"


"To ƙanina Captain Zaidu yanzu hakuri kake so na baka ko miye?"

Tashi Zaidu yayi ya nufi hanyar toilet ba tare da ya kula Ubaidullah ko K,B ba.

K,B ya ce.
"Ni fa tambaya nake yi."

Juyowa Zaidu yayi ya ce.
"Subhanallahi wai miye haka ne kam K,B mun dawo ko gaisuwa bamu yi ba, baka je ka nemo mana abinci ba balle ruwan sha, amma zaka wani tsareni da tambayar gulma kana soja,a sojan ma first lieutenant, gaskiya na yarda da batun nan da ake cewa gulma ya koma kan maza" ya fada yana shigewa toilet, tashi K,B yayi yana dariya yana cewa.
"Ah haba dai Captain kace min yunwa ka kwaso, ai dole naje nemo muku abinci tun da Allah yasa baka dawo da matar ba balle ta girka mana muci duka kaga daga nan ma idan ka koshi kaban labari"


Murmushi Ubaidullah yayi ganin sun haɗa kansu abotan su yana birgesa, ba bakin ciki ba hassada balle kuma ƙyashi.


K,B na fita da yan mintina ƙalilan sai ga Rumaisa kamar an jefota daga sama, kafin Ubaidullah yayi wani yunkuri ta shige jikinsa tana sauke a jiyar zuciya, wani dadi ne ya ratsata a duk wani sansa na gangar jikinta, a hankalin ta hau furta kalman.
"I miss u i miss u over my lyf, pls say u miss me too?"

Da iyakacin karfinsa Ubaidullah ya ban gaje Rumaisa ta fadi kasa, sai huci yake yi shikenan ai yanzu kam ya dawo, zasu ɗaura daga inda suka tsaya.



"Oya get out!of this room Rumaisa b4 i open my eyes leave now!"

Smiling tayi kafin ta miƙe tsaye ta ce. " never" ta sake shigewa jikinsa tana ƙokarin haɗe bakinta da nasa, sosai suka shiga kacaniya ita dashi harta kaisu ga zubewa bisa gado sannan ta kashe masa ido daya ta ce.
"Zaka ga yanda ake makirci Captain zaka sake tabbatarwa da cewa tabbas mata makirai ne ka zuba idonsa ka gani, ai duk wanda yaƙi sharan masallaci ba shakka zaiyi ta kasuwa..."



~~~~~~~~



To fa mai Rumaisa take nufi da kalamanta masu zafi ga Ubaidullah?


*MAH FANS ALLAH YABAKU IKON GYARAWA IDAN KUMA BA HAKA BA WANNAN SHINE LAST POSTING DINA*🙌🏻


COMMENTS
&
SHARE

BY MOMYN AHLAN MRS IS OK✍🏻👯🏻
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: I just published "part 19&20" of my story "COLONEL UBAIDULLAH". https://my.w.tt/jFpvO64SS4


follow me on my wattpad pls



*COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)



*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻


*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~~•~~
TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116)

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘
____________________
_Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*page°°°°19&20*



Zaka ga yanda ake makirci Captain zaka sake tabbatarwa da cewa tabbas mata makirai ne,ka zuba idonka ka gani, ai duk wanda yaƙi sharan masallaci ba shakka zaiyi ta kasuwa..."


Maganar da Ubaidullah yake ta nanatawa kenan a cikin ransa zuciyarsa tana masa suya, yana tunanin me Rumaisa ta shirya masa, da har take masa bazarana da kalamanta?"


tambayar da yake ta yiwa kansa kenan amma ya rasa amsarta ,wani ban gare na zuciyarsa ya ce masa. "Haba Captain Ubaidullah jarumin soja abin alfahari, karka tsorata, tsoro baya cikin ɗabi'unka, duk wata sharrinta zai koma kanta ne."


Da wannan karfin guiwar Ubaidullah ya sake ture Rumaisa kasa wacce take kwance a jikinsa tana faman shafa masa jiki.


Ko da ya tureta bata saduda ba, ta sake tsalle ta haye jikinsa, zip din rigarta ta gaba, ta zugesa kasa take ƙirjinta ta bayyana, da karfi Ubaidullah ya rintse idonsa gami da cewa.

"Innalillahi wainna ilayhirrajiun! Subhnallahi! A'zubillahi Minash'shaiɗanirrajim! Allah ka shiga tsakani da wa innan bayin naka"

A zafafe ya mike ya ware hannayensa, a lokacin Rumaisa tana shirin rungumarsa, da iya karfin ya taska mata marin da sai da ta kifu da baki ,dai-dai nan Zaidu ya fito yana fadin.

"Subhanallah My Man me zan gani haka meya faru wannan mari haka?lafiya me Rumaisan ta maka?"


Mikewa Rumaisa tayi taja zip din rigarta.

Da kyau Zaidu yake dubanta yana son gano wani abu, sannan ya juya yana kallon Abokinsa wanda ilahirin jijiyoyin jikinsa sun miƙe sun fito raɗa-raɗa, kunnensa yayi ja, saboda bacin rai da tashin hankalin.

Rumaisa ta shafo bakinta wanda yake fitar da jini tayi wata killer smiling, gefen idonta kuwa ya taro da jini, ta kallesa a fakaice ta ce.

" Captain Ubaidullah , you slap me?"

"Rumaisa get out right now!"

"Humm Captain Ubaidullah, i wiil, but u will pay for this" sannan ta dauki wayarta akan dress'mirror tasa kai ta fice.


Kallonsa Zaidu yayi yace.
"wai meya faru ne kam Ubaidullah? Meya haɗaka da Rumaisa kuma?"

Kasa magana Ubaidullah yayi ban da jikinsa dake rawa kamar mazari, a haka KB ya dawo ya same su, Ubaidullah zaune bakin gado ,Zaidu na tsaye daure da towel a kugunsa, da kallon tuhuma KB ya bisu dashi , ya ce.

"Lafiya kuwa meya faru?"


"Rumaisa"

Zaidu ya bawa KB amsa da haka.

KB ya ce.
"Rumaisa dai? To meya hada su da Ubaidun?"

"Nima wallahi ban sani ba, kuma kasan yanzu ko sama da kasa zasu haɗe Ubaidullah bazai yi magana ba, mu bari ya sauko tukunna"

Cike da mamaki KB ya ce.
"Kamar ya bazai yi magana ba?"

Murmushi Zaidu yayi ya ce.
"Nasan Ubaidullah fiya da yanda nasan gadon bacci na, mutum daya ce zata iya sa Ubaidullah ya sauko *MAMA* ita ma sai tayi da kyar kafin ya huce"




Nan KB ya ajiye abinci tare da lemon da ya kawo musu, ya nemi guri gefe daya ya zauna, Zaidu kuma ya hau shafa mai, bayan ya gama ya saka jallabiyya shima ya zauna suka zubawa Ubaidullah ido.

har yanzu idanunsa bai washe yayi haske ba, jijjiyoyin jikinsa ma basu koma ba, babu abun da yake masa gizo sama da kirjin da Rumaisa ta bude masa, nan ya sake rintsa idonsa da karfi cike da takaicin kallon haramun da Rumaisa ta saka shi yi.


Zaidu gajiya yayi da jiran Ubaidullah ya dawo normal dan haka a sab'ule ya mike ya dauki ruwa mai kankara a karamin freezer din dake dakin nasu, ya shiga toilet ya dau karamin bowl tare da karamin towel yazo gaban Ubaidullah ya watsa masa ruwan, amma ko gizau Ubaidullah bai yiba sai kace ba ma shi bama aka watsa wa ruwan.


Sai da Zaidu ya watsa wa Ubaidullah kusan sau uku kafin ya bude baki ya saki ajiyar zuciya bakinsa yana fitar da hayaki, cike da tsoro da mamaki KB ya ware idanunsa yana kallon Ubaidullah ya ce.

"Tabɗijam tashin hankali Captain Ubaidullah anya akwai macen da zata iya zama da kai kuwa? Irin wannan zuciya haka ,harta maza na firgita inaga mata?"

Murmushi Zaidu yayi ya ce.
"Wallahi mace kadarace mai tsadar gaske duk zafin zuciyar namijin zaki da yazo gaban mace zai koma ɗan tsaƙo, kuma zaka ce na gaya maka,ai su mata matsayin su da darajar su daban yake domin su hijabai ne kuma rufin asiri garemu wawayen maza ne kawai basu san da haka ba, suka mai da mata bayi marasa daraja da galihu, to wannan idan ka duba rayuwar su bata wani albarka"


Jinjina kai KB yayi, ya ce.
"Haka ne wallahi maganar ka, gashi maza yanzu sun ƙaro wulakanci da an tabasu
Sai su ce matan sunyi yawa yo ai su ma mazan sunyi yawa tunda dayawar su su na so suyi aure amma babu halin yi"

Dariya suka kwashe dashi yayinda Ubaidullah ya buga tsaki ya tashi ya shige toilet, kusan 20mnts ya fito jikansa sharkaf da ruwa, towel ya dauka ya koma toilet din, da kallon Zaid da KB suka bi bayansa, Zaid ya girgiza kai a ransa ya ce.
"Allah ya kyauta ya sauƙaƙa maka wannan zafin zuciyar"



Bayan 5mnts ya sake fitowa ,jallabiyya shima ya saka ya kwanta ba tare da ya kulasu ba.


Zama Zaid yayi ya ce.
" am very very hungry wallahi"

KB ya ce.
"Yo to ba ga abinci a gabanka ba ai saika sunkuya"

murmushi yayi ya juya yana kallon Ubaidulllah wanda idonsa yake rufe gam kamar mai baccin wuya, amma ba baccin yake yiba kalaman Rumaisa ne yake masa guɗa a kunne, haka kawai yaji kalaman sun samu matsuguni a zuciyarsa.

Zaidu ganin yana cikin yanayin wani irin hali ne sai ya sa jikinsa sanyi, tashi yayi ya matso kusa da shi cikin sanyin murya ya fara magana.

"Haba My Man bai kamata ace mace ta firgita ka haka ba duk abin da Rumaisa ta maka zaka iya hukuntata a matsayinka na ɗa namiji, duk da bansan me ya haɗaku ba"



Sosai Zaidu ya dinga dannar Ubaidullah har ya sake,amma ba sosai ba, sai da aka kira sallar magriba tukunna suka fita izuwa masallaci bayan sun dawo suka saka kakin su na sojoji suka dauki hanyar Office din General Of The Army, da sallama suka shiga bayan sara musu da sojoji suka dinga yi.

Bayan sunyi sallama ne, Ubaidullah shine a gaba, ba zato zaji sunyi karo da wata, tayi baya baya zata fadi da sauri ya tarota da ta faɗo faffaɗen ƙirjinsa take ta sauke ajiyar zuciya ba kowa bace face *Hanan* yar gidan *Ganeral of the army*
Da sauri Ubaidullah ya matsar da ita daga kirjinsa ya gyara mata tsayuwarta bisa kafafunta, sannan ya haɗe ran nan tamau, gefe ta koma Ubaidullah da Zaidu suka ƙame su na sarawa Shugaban su, sosai General yaji dadin ya hau tambayarsu ya hanya da mutanen gida suka amsa da lafiya lau, nan ya sake musu ban gajiya gami da tuna musu yau saura 1wk kacal suyi tafiya suka amsa masa da cewa eh su na sane, kafin suka yi masa sallama har sunje bakin kofa, General of the army ya ce.

"Captain Ubaidullah zan aikeka Abacha Barracks gobe wajan major Salihu"
Da ok sir Ubaidullah ya amsa suka fita da Zaidu a hanya suka haɗu da Raihana ita ma sai da ta ƙunsawa Ubaidullah haushi kafin ta kama gabanta.


Kafin su Ubaidullah su koma part dinsu sai da suka yi sallar isha'i kafin suka koma part dinsu, wayarsa ya dauka ya kira Mama suka sha hira kafin ya kira Anty Ummu suka dan taba hira sama -sama sannan sukayi sallama.

Duk yanda Zaidu da KB suka so yin hira Ubaidullah yaki dan haka suka kyalesa.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




Washe gari da safe bayan Ubaidullah ya shirya cikin kakinsa wanda suke matukar yiwa jikinsa kyau, ya fito ya nufi office din Ganeral ya karba sakon a hanya suka hadu da wani shi da Rumaisa bisa alamu kuma sabon Ma'aikaci ne, kuma ba musulmi bane, dan a jikin rigarsa an rubuta *Sergeant Ema* kallo daya Ubaidullah ya musu ya dauke kai, yayinda S Ema ya ga Ubaidullah duk sai ya sake masa kwarjini, tabbas yanda ake fadinsa yafi haka, haka kawai yaji baya kaunar Ubaidulllah.


Aiken da aka yiwa Ubaidullah Abacha Barracks direct ya wuce sai yamma ya dawo suka ci gaba da aikin su.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


After 6days

da dawowar su Ubaidullah gobe ne kuma suke shirin tafiyar su, a wannan kwana shidda Ubaidullah yayi mari yafi a ƙirga, barin ma Rumaisa, da Raihana, ita kuma Zeey bata nan sun tafi wani Course a America, gashi yanzu yan matan sun kara yawa harda wa inda ba musulmai ba duk hari suke kawo masa, a daren ana gobe zasu tafi Rumaisa ta cewa Ubaidullah.


"You know what Captain? Humm ina so ka tara hankalinka waje guda domin dawowarka daga tafiyan nan babu alƙairi a ciki za kuma ka gani"


Kasa magana Ubaidullah yayi banda uwar kallon da yake bin Rumaisa dashi har ta fice daga parlourn.

Tambayar kansa yayi wai me Rumaisa take nufi dashi ne kam.?



@@@@@



Daga wannan page din na tsaida littafin nan zuwa nan da sati biyu.





CMMENTS

&


Share

By



MAMYN AHLAN MRS IS OK✍🏻
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafinmu na Bakandamiya, danne nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*page°°°°°21&25*




"Wai me kike nufi dani ne kam Rumaisa? Mena tare miki? Ya Allah ka kawo min sauki cikin lamarina, Allah ka shiga tsakanina da wa innan bayin naka,Ya Allah na kawo ƙaransu gareka,Duk abun da kike nufi ya koma kanki Rumaisa, aniyarki ta biki" cewar Ubaidullah, ya zube a kujeran parlour yana sauke ajiyar zuciya, KB da Zaidu ne suka shigo da sallama, a haka suka samu Ubaidullah cikin damuwa, zama sukayi kusa dashi Zaidu ya ce.


"My Man what's wrong with you?"
Dogon numfashi Ubaidullah ya sauke gami da sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Nothing !
am just feeling bad, that's why"




Girgiza kai Zaidu yayi gami da cewa.
"No ba halin soja bane,ina lura da kai tun abun da ya shiga tsakaninka da Rumaisa na fahimci kana cikin damuwa, Ubaidullah ka sha faɗamin akan cewa duk wanda zai saka tsoro da fargaba a cikin zuciyarsa baya zama gwani haka ne?"


Lumshe ido Ubaidullah yayi gami da cewa.
"Eh hakane matsoraci baya zama gwani, Amma kaidin mata yafi kaidin shaiɗan ina yawan faɗuwan gaba wanda nima bansan dalilin hakan ba Zaidu"


numfasawa Zaidu ya yi, a tare suka dafa kafadarsa shi da KB ya

6 / 25