Author : Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category : Romance
yi rubutu akai a samu mafita, bansan cewa nayi shishshigi bane, kayi hakuri idan ka sake ganina a gidan ku na yarda kayi min duk abun da ka gadama" tana gama fadi ta fice da gudu.
Duk wannan draman da suke yi Hafiza tana tsaye a bakin kofa tana jin su, har san da Abi'atu ta fice da kuka.
Rimtse ido Ubaidullah yayi wani bangare na zuciyarsa bai ji dadin kuma yanda ya mata ba.
Yana tsaye hannunsa ɗaya a kugunsa daya kuma a fuskarsa ya ji sautin muryan da yau kusan kwana nawa bai jita ba, a hankali ta furta.
"Yayana"
Da sauri Ubaidullah ya juyo yana kallonta da sauri yazo ya rungumeta yana hawaye ya dago fuskarta ya ce.
"Kanwata ke ce? Ke ce kikayi magana? Faɗa min?"
Jinjina kai Hafiza tayi ta ce.
"Yaya baka kyauta ba abun da kayiwa Anty Abi'atu, shin kasan kalar kokarin da take yi kuwa, wajan taya ka gano wa inda suka kashe min sismieta? Ita da Yaya Safwan kullum su na fadi tashi ,su na iyakar kokarin'su, Yaya, Anty Abi'atu tana da matukar kirki fiye da tunaninka bata da matsala ko kadan, ya kamata ka bata hakuri akan abun da ka mata."
Ubaidullah ya ce.
"Kina so na bata hakuri?" Hafiza ta gyaɗa kai alamun eh, ya ce.
"To shikenan idan tazo gobe zan bata hakuri kin ji?" Hafiza ta sake gyaɗa masa kai sannan suka fito a tare suka shiga dakin Mama.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da sallama ta shiga parlourn gidan su Abba da Ummi su na zaune duk da fuskarta babu walwala amma sai da ta danyi fara'a tazo kusa da Ummi ta zauna, kafin ta gaishe da iyayenta, suka amsa Abba ya kara da cewa.
"Ah ai na dauka zamu bi ki da kayanki ne ai yau kusan kwana uku ina tambaya kina ina wai kina gidan'su Mama" dan murmushi tayi ta ce.
"Haba dai Abbana gani na dawo ai" Ummi ta ce.
"Ya jikin Mama da Hafizan?"
"Alhamdulillah Mama da sauki, itama Hafizan Alhamdulillah amma har yanzu bata magana"
"Allah sarki! Zata ware a hankali Allah ya basu lafiya" cewar Ummi suka amsa da ameen, Yaya Safwan ya yi sallama ya shigo ya ce.
"Ah journalist yau an dawo kenan" hararan wasa ta masa sannan ta miƙe ta shige ɗakinta bata kula Yayan nata ba, kwanciya tayi tana tunanin maganganun Ubaidullah, sake rimtse ido tayi ,ta dauko wayarta ta shiga wajan video nan ta ci karo da videon Na'ila, kukanta tasha kafin ta tashi tayi sallar isha'i ta kwanta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da washe gari Ubaidullah ya yi shirin faɗawa mahaifiyarsa cewa yabar aiki.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*DA BABU GWARA BA DADI, KU LALLABA DA WANNAN KARKU ZAUNA SHURU PLS WLH YANZU BANI DA LOKACIN TYPING BUK BIYU, BAZAN IYA CE MUKU GA LOKACIN DA ZAKU DINGA SAMUN UPDATE BA, SABODA SABON BUK DIN DA NAKE TYPING, FATAN ZAKU FAHIMCENI, NGD*
GA MASU BUKATAR SABON NOVEL DINA NA KUDI MAI TAKEN SUNA *_ITA CE ZUCIYATA_* SAI KU NEME NI TA NUMB TA KAMAR HAKA, 08165550116 KIRA KO WHATSAPP NGD.
COMMENTS AN SHARE.
MOMYN AHLAN TAKU CE👍🏻,
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)
*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻
*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻
_dedicated to my brother_
*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~
_my wattpab_@Fateemah0
_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*page°°°°°61&65*
Da misalin karfe tara da rabi na safe.
Da sallama ya shiga
dakin, Mama tana zaune akan sallaya da carbi a hannunta tana lazimi da alama ta idar da sallarh walha ne.
Amsa sallamar tasa tayi, ta shafa adduar kafin ta fuskancesa dan kuwa kallo ɗaya ta masa ta ga akwai magana shinfiɗe a fuskarsa.
"Lafiya kuwa Yaya Babba? Daga ganin fuskarka akwai damuwa haka ne?"
Gyaɗa kai Ubadullah ya yi, ya matso kusa da Mama ya kama hannunta sosai gabansa sai faduwa yake yi cikin sanyin murya ya ce.
"My Momma, akwai abubuwan da suka faru a wajan aikina, wanda shi ya yi sanadiyyar dawowata gida, ina dawowa dan naji da ciwo ɗaya , sai kuma na iso na tarar da babban miƙin da har na mutu ba zata taba warkewa ba, Mama bansan ya zaki dauki labarin da zan ba ki ba, amma ni dai nasan mahaifiyata ta yarda dani, kuma tasan bazan taba aikata abun da ba shi da kyau ba, Mama ke da bakinki kin sha faɗamin cewa samu da rashi duk na Allah ne, idan Allah yaso zai baka abu sannan ya kwace a duk lokacin da yake so, inajin tsoron faɗa miki amma kuma duk daren ɗaɗewa dole ki sani, ban son ki sake shiga damuwa a ta sanadin hakan mahaifiyata" ya karasa maganar hawaye na zuba a idonsa.
Sosai jikin Mama ya yi sanyi, hakika Ubaidullah wani abun na damunsa amma daurewa yake yi kawai, kallonsa tayi ta ce.
"Yaya Babba, karka ji shakku akan abun da zaka fadamin, a yanzu yadda nake jin kaina, babu abun da za a fadamin wanda zai tayar min da hankali, domin kuwa idan tashin hankaline na gansu sau biyu a gabana, na gansu kwance su biyu a gabana, ba komai bane fa ce gawar mahaifin ku da kuma gawar yar uwar ku, dan haka naga gawar mijina naga na ƴata wanda ko wata ba tayi ba kwance a cikin kasa, ka faɗamin abun da kake son faɗa min."
Ajiyar zuciya Ubaidullah ya sauke kafin ya sun kuyar da kansa kasa ya ce.
"Mama na ajiye aikina na soja, yanzu ni ba ma'aikaci bane" nan Ubaidullah ya shiga bawa Mama labari tun abun da ya fara shiga tsakaninsa da Rumaisa bai boye mata komai ba harda yan matan da suke bibiyarsa a barracks din ,duk ya faɗa mata, daga karshe ya kara da cewa.
"Mama iyakar gaskiya ta na fada miki, na ajiye aikin ne saboda gudun a min wulakanci a ci zarafina, ni kuma ba zan dauka ba, kar nazo nayi abun da zai jawo a kasheni saboda zuciyar da nake dashi, shi yasa na ajiye aikina.
Sosai Mama ta fahimci maganar Ubaidullah, duk da zuciyarta sai ƙuna take yi, a hankali cikin dauriya Mama ta kalli Ubaidullah wanda kallo ɗaya tayi masa ta hango tsananin damuwa da tashin hankali a tattare da shi.
Kasa magana Mama tayi sai da Ubaidullah ya sake cewa.
"Mommana ke ma baki yarda dani bane? Naji baki ce komai ba, wallahi Momma da gaske nake fada miki idan ma baki yarda ba ki kira abokaina Zaidu da KB su zasu faɗa maki gaskiya , da wannan yarinyar da suka zo ta'aziyyar Kanwata.
Share hawaye Mama tayi dan kuwa ba karamin sake shiga damuwa tayi ba , da Ubaidulllah ya fada mata da cewa yabar aiki, a hankali Mama ta ce.
"Allah yana tare da mai gaskiya ni nasan hali ɗana a matsayina ta mahaifiyarsa, kuma na yarda da ɗana, karka damu Ubaidullah dukkan mumini sai Allah ya jarrabesa dan a gwada imaninsa, Allah yabamu ikon tawakkali da rungumar kaddarar'mu hannu biyu" shi ma Ubaidullah hawaye yake yi ya kifa kansa akan cinyar Mama yana kuka tamƙar karamin yaro, zai yi magana suka ji Hafiza na shashsheƙar kuka a bakin kofar Mama.
Ubaidullah ya ce.
"Kanwata!?" da gudu ta bude kofar daki ta shigo da alama taji duk abun da Ubaidullah da Mama suke magana a kai ne, rarrashinta Ubaidullah da Mama suka shiga yi
Amma taƙi tayi shuru, sosai hankalin'su ya tashi, da kyar Hafiza ta taƙaita kukanta , tana jan zuciya ta ce.
"Yaya shi kenan kai ba Soja bane yanzu? Wa in da suka kashe min yar uwata suka barni ina rayuwata ni kadai sun kasheta a banza kenan? Yanzu Yaya ba zaka daukarwa Yar Uwata FANSA ba, yanzu Yaya kai ba soja bane ba zaka nemo wa inda suka kashemin Sismieta suka rabani da ita ka kashe su ba yanzu Yaya b...." bai bari Hafiza ta karasa ba ya rufe mata baki da hannunsa gami da cewa.
"Kul! Wa ya gaya maki cewa bazan nemo su na hukunta su ba?ai kullum cikin neman su nake, Dole na, na nemo wa innan azzaluman bayin na kashe su da hannuna nayi alkawari sai na ɗanɗana musu azabata, duk abun da na koya na training soja sai na sauke musu shi, ki daina wannan maganar kinji ko?" ya karasa yana rungumeta, tashi Mama tayi ta fice tana share hawaye, ta bar Ubaidullah da kanwarsa a daki su na kuka ita ta koma parlour tana nata kukan.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da yamma Ubaidullah ya shirya zai fita, har ya shiga mota dan kuwa ya sanar da Mama cewa zai fita, da gudu Hafiza ta fito ta tsaya tana kallonsa.
Fitowa ya yi a motar yana tambayarta akan menene ko tana son wani abu ne,amma ta tsaya sai tura baki take yi kamar zata yi kuka.
Da sauri ya karaso gabanta ya kama hannunta ya ce.
"Wa ya taba min ke?" dan kuwa Mama da Ubaidullah da Anty Ummu basu son su ga Hafiza a damuwa dan tafi basu tausayi.
"Yaya, ya muka yi da kai?"
Daga kai Ubaidullah ya yi, alamun tunani amma ya kasa tunawa, dan shi gaskiya har ga Allah ya manta da wani magana.
"Am sorry Lil'Sis wace magana ce? Namanta tuna min pls."
"Na hakurin da zamu je mu bawa Anty Abi'atu mana, tun abun nan da ya hadaku bata sake shigowa ba fa, amma kullum tare muke wuni kuma tana ɗebemin kewar sismieta duk da ba zata taba zama kamar ita ba, amma Yaya ina son Anty Abi'atu sosai, Mama tana sonta idan taji abun da ka mata kasan Mama ba zata ji dadi ba, kuma idan aka yi kwana biyu bata zo ba Mama zata fara zargin kayi mata wani abu ne tun da agabanta ka fara yiwa Anty Abi'atu magana da ihu tun a gidansu Yaya Zaidu" ta karasa maganar tana dukar da kanta kasa.
Ubaidullah yasan duk abun da Hafiza ta faɗa gaskiya ne dan haka ya ce.
"To shi kenan, shiga mota muje" girgiza kai tayi ta ce.
"Yaya, nan da nan shine sai mun je a mota? ni kam kawai ka zo mu taka mu shiga."
"Ohh Allah na, Hafiza kin koya rigima wallahi, anya ba wannan yarinyar mai iyayin ba ce ta koya maki rigima?" duk a cikin zuciyarsa yake faɗin wannan maganar, a fili kuma ya ce.
"Haba Hafiza baki ga zan fita bane?"
" ni dai Yaya muje da kafa" ba tare da ya sake magana ba ya kulle mota suka fita a tare.
Tun da Hafiza suka fito daga gate dinsu ita da Yayanta ake bin su da kallo, ga kamannin da suke yi wasu yan matan unguwa ma ba su san Ubaidullah ba tun da ba zaman garin yake yi ba idan yazo ya jima da yawa shine ya yi sati ɗaya ya koma, kuma idan ya zo fitar su kullum a mota ne shi da Amininsa Zaidu.
Wasu ma idan suka ga Hafiza sai su dauka Na'ilah ce dan ita ce mai jama'a, sai ka matso kusa tukunna zaka gane ba Na'ilah bace dan kuwa Na'ilah tafi Hafiza fadin Fuska, sai sake yi musu ta'aziyya ake yi su na amsawa, wasu ma yan mata da gayya suka zo yiwa Ubaidullah ta'aziyya dan kawai ya yi musu magana saboda yau ne karo na farko da suka fara ganinsa, basu taba ganinsa ba sai dai su ji labarinsa, ba yabo ba fallasa yake amsa gaisuwar ta su, da haka ya ja hannun kanwarsa suka wuce dan sauri yake akwai inda za shi.
A gate din gidansu Abi'atu Hafiza ta kwankwasa karamin kofa, rabonta da fita tun rasuwar yar uwarta, sai kuma fitan da suka yi a mota da Yayanta, shi yasa take ganin komai daban yake mata.
Mai gadi yana ganinta ya saki murmushi, nan suka gaisa shima ya sake yi musu ta'aziyya.
Sai da Hafiza ta shiga tayi sallama Ummi ta fito daga bedroom dinta zata shiga kitchen ta ga Hafiza na Sallama, tsantsan farin ciki Ummi kasa amsa sallamar tayi da saurin tazo ta rungumi Hafiza tana cewa.
"Hafiza ke ce?" gyaɗa kai Hafiza tayi ta duka ta gaisheta, Ummi ta amsa cike da farin ciki da jin dadi.
"Ummi ni da Yayana ne mu ka zo, yace na rakosa wajan Anty Abi'atu zasu yi magana."
Da mamaki Ummi take kallon Hafiza ta ce.
"Tooo! Ina Yayan naki yake ,shine bai shigo ba? Sai kace wani bako ai da nan da gidanku duk ɗaya ne"
Murmushi gefen baki Hafiza tayi tana kashe ido ɗaya ita kadai tasan plan din da tayi, yar uwarta ce ta fado mata a rai ana gobe zata rasu da suke hira akan cewa idan Yayansu yazo sai sun san yanda suka yi suka haɗa shi aure da Anty Abi'atu dan kuwa sun dace.
"Allah sarki! Rayuwa baki da tabbas, Sismieta nayi alƙawari ko babu ke ni saina cika wannan burin In'sha Allahu" duk wannan maganar a zuciyarta take fadi a fili kuma ta ce.
"Am uhum Ummi wai kunyarki yake ji" rike baki Ummi tayi gami da cewa.
"Lallai kam ai sai ki ce masa ya shiga ƙaramin parlour, sannan ki zo ki kira Abi'atu tana daki, dan tun jiya na kasa gane mata bansan meke damunta ba" Hafiza ta amsa da to, sannan ta fita ta kai Yayanta karamin parlour, ta dawo da sallama ta shiga bedroom din Abi'atu.
Abi'atu kwance ta lumshe ido kamar wata mai bacci, kamar a mafarki ta ji muryar Hafiza da sauri ta bude ido ta ga Hafiza a gabanta tana tsaye tana dan murmushi kaɗan-kaɗan, sake mutsintsike idonta Abi'atu tayi ta ce.
"Ko dai gizo take min ne?"
Hafiza ta ce.
"A'a My Anty In-law ba gizo bane ni ce Hafiza ce" wani ihu Abi'atu ta saka wanda harta Ummi dake kitchen sai da ta tsorata, dirowa a gadon Abi'atu tayi ta zo ta rungume Hafiza har da kwallanta na farin ciki, Ummi ta shigo da sauri tana cewa.
"Abi'atu lafiya kuwa? wannan wani irin ihu ne haka? Duk kin cika gida?"
"Ummi wallahi ita ce ta fara magana."
"Mtsww! Amma dai ke kam Allah ya shiryeki maimakon kiyi hamdala sai ki saki wannan kara haka, ai mun fara gaisawa da ita kafin ta shigo wajanki, hamdala za ki yi ba ihu ba"
"Wallahi Ummi bansan nayi ihun ba, murna ce ta saka ni yi" Ummi tayi murmushi ta fice tana cewa idan kun gama dai karku manta kun bar mutum a parlour.
Zama suka yi Hafiza ta ce.
"Shine kika gudu ko?"
Shuru Abi'atu tayi ta ce.
"Aa ba guduwa nayi ba , akwai aikin da nake yi ne shiyasa baki ganni nazo ba"
"To tashi muje Yayana ne yace na rakosa wajanki."
Zare ido Abi'atu tayi da mugun Mamaki take kallon Hafiza, ganin haka yasa Hafiza ta miƙe ta ce.
"Ki kawo masa abun sha ki same mu a ƙaramin parlour" tana gama fadi ta fice, Abi'atu jiki ba kwari ta tashi ita ma tayi hanyar kitchen.
Da sauri Hafiza tayi wajan Yayanta, dan karya kwafsa mata dan tasan zai aika, a yau kuma bata son tayi missing din plan dinta.
"Am Yaya ga Anty Abi'atun zuwa, Yaya karka bani kunya, karka bawa Mama kunya ka ji?" guntun tsaki Ubaidullah ya ja ba tare da Hafiza ta ji ba ya ce.
"To na ji" ya fada a takaice dan yan halin sun fara tashi.
"Am Yaya idan tazo zan tashi na baku waje sai ka bata hakurin a sirrince" da mamaki yake kallon Hafiza, shi kenan ta koyawa Hafiza kisisina.
"Um" shine abun da ya iya fadi, Hafiza zata sake magana Abi'atu tayi sallama cikin zazzaƙar muryarta wanda sai da ya daki dodon kunnen Ubaidullah, wani kamshi yaji na tashi wanda sai da ya sanya idanunsa kaɗawa suka koma ja, da sauri ya tamƙe idonsa, yana so su washe dan yanda ya ji sunyi masa ya tabbata yanzu kam sun yi ja.
Abi'atu tana shigowa Hafiza ta mike da sauri ta fice dan kar ma Abi'atu ta tsaidata.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*kun matsa ne amma banyi niyyar sakin page din ba, saboda page din baya na samu korafi ta pc akan cewa yy kadan na kara, kuma na fada muku cewa bani da tym din typing buk biyu lokaci daya*
Momyn Ahlan Taku Ce👍🏻
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)
*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻
*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻
_dedicated to my brother_
*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~
_my wattpab_@Fateemah0
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*_CIKIYA CIKIYA CIKIYA, DAN ALLAH WANDA YAKE DA BUK DINA (HALITTA DAGA ALLAH NE) PLS A TAIMAKA MIN A TURO TA MY NUMBER WLH NA RASA SHI NE SABIDA WAYATA DA TA SAMU MATSALA KWANAKI, 08165550116 PLS._*
*Kacokar wannan page din na mallaka muku shi halak malak, yan COLONEL UBAIDULLAH FANS, idan kun so ku hana wasu grps din karantawa 🤪🤪 ni dai ba ruwana har da yan Wattpad ma*
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*page°°°°°66&70*
Fitan Hafiza da yan mintuna su na zaune babu wanda ya cewa kowa komai, Abi'atu ganin darajan Mama tayi a idonta sannan ta ga girman Anty Ummu, sai kuma Ubaidullah din da ta gansa kamar Yayanta Safwan dan haka ta daure a takaice tana kau da kanta gefe tana tabe baki ta ce.
"Ina wuni?"
Yadda tayi masa gaisuwan ne ya tsaya kallonta yana jinjina iyayinta, sai da ya ɗibi kusan minti sha'biyar,har ta fidda ran zai amsa, kafin ya amsa a takaice shi ma.
"Lafiya"
Daga haka ko wanne yaja baki ya yi shuru, Ubaidullah wayarsa ya ci gaba da dannawa Abi'atu tana zaune tana jira ta ji meya kawosa, har tsawon minti talatin su na zaune ba tare da sunyi wata magana ba tun bayan gaisawar da suka yi.
@@@@@
Hafiza kuwa parlour ta koma ta zauna tana addua Allah yasa haƙanta ya cimma ruwa, tun da burin Mama, fatan Anty Ummu ne.
Ko da Ummi ta fito daga kitchen ta ga Hafiza zaune ta ce.
"Ah Hafiza ya na ganki anan kuma? Ina Abi'atu da Ubaidullah din?"
"Su na karamin parlour Ummi, cewa ya yi na tashi na fita magana mai mahimmanci zasu yi shiyasa na dawo nan na zauna"
Jinjina kai Ummi tayi tana tunanin dama akwai abu tsakanin Abi'atu da Ubaidullah ne.
Hafiza tana nan zaune har Safwan ya shigo ya ganta ya yi mata magana, ga mamakinsa sai ya ji ta amsa ta gaishesa,