Author : Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category : Romance
b'aci, cikin murya mai cike da taushi gami da lallashi ya ambaci sunanta, dan ba zai iya jurar kukan da take yi ba.
"ABI'AH!" yana kiran sunan nata ta ji kukan nata ya ƙaru, sake ɗago fuskarta ya yi, ya sake ambatar sunan nata kafin ta ɗago jajayen idanunta ta kallesa ta sake fashewa da sabon kuka dan kuwa ta kasa daina kukan, ga uban faduwar gaba, kuka take har tana shiɗewa ga shi yanzu ta kafesa da ido sabida fuskarta da ya tallabo da ambatar sunanta da ya yi, Ubaidullah idanunsa suka sake rinewa ganin yadda take kukan tana karawa, a hankali ya jawota ya haɗeta da kirjinsa yasa hannuwansa duka ya zagayeta da shi gabansa na faduwa, jinta a jikinsa yasa sautin kukanta sake canza kala, dan kuka take mai cike da ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro, da kyar ta fara magana mai cike da ajiyar zuciya da shesheƙa.
"Shi ke nan! Zan rasa Yayana, mutuwa zai yi shi ma ko? Zan ras....." da sauri ya sake matse fuskarta a ƙirjinsa sai ga hawaye na zubowa daga idon Ubaidullah kuma ya ƙi yarda ya ɗago da fuskarta, sosai Abi'atu tasha kuka lokaci ɗaya wani azabebben ciwon kai ya dirar mata, sai da ya tabbatar ta yi shuru kafin yana rungume da ita suka koma cikin asibitin.
@@@@@
Sai wajan gaf da magriba Likitar da Ubaidullah ya sakata bincika masa lafiyar Hafiza ta fito, da sauri Ubaidullah ya yi wajanta yana tambayarta ya lafiyar Hafiza, nan take shaida masa lafiyarta kalau basu yi bata komai ba, wani wahalalliyar
Ajiyar zuciya Ubaidullah ya sauke, ya juya ya sake rungume Abi'atu wanda idanuwanta suka ƙanƙance sabida kuka da ciwon kai.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A dayan bangaren kuwa.
Ko da Mama ta zo gidansu Ummi take cewa ina Abi'atu da Hafiza, Ummi take cewa ita bata ga Hafiza ba, amma ba mamaki da zata zo sun hadu dasu Safwan da Abi'atu a gate sun fita tare, dan Safwan da Abi'atu sun tafi karb'o sako, da haka ne suka shiririce da zancan, har can yamma lilis ba Safwan ba Abi'atu balle a saka ran gani Hafiza tana tare dasu, abun bai damu Ummi ba, sai ana kusan sallar magriba tukunna wanda za a karba sako a hannunsa ya kira waya ya ce fa ga shi ba a zo an karbi sako ba, Ummi ta fara mita tana yiwa Safwan faɗa sai kace yana gabanta, har tana cewa, ya kama sun tafi da Abi'atu da shike itama mai kafar yawo ce da auranta sai da nace mata zauna ta ƙi, waya Ummi ta ɗauka ta fara kiran layin Safwan a lokacin ita kuma Mama ta koma gida ta ce gidan ba kowa sai mai gadi idan su Abi'atu da Hafizan sun dawo sa sameta a gida, lokacin da kiran Ummi ya shigo wayar tana aljihun wandon Ubaidullah yana zaune Abi'atu tana kwance a kafadarsa, ɗan ɗagata ya yi kaɗan, sannan ya duba wayar ya ga sunan Ummi na yawo a screen din, gabansa ne ya fadi dan baya so ya kirasu ya gaya musu halin da ake ciki sai likitoci sun fito an faɗi a wani mataki Safwan yake, babu yanda Ubaidullah ya iya haka ya ɗaga wayar Ummi jikinsa a matuƙar sanyaye, tun kafin Ubaidullah ya yi magana Ummi ta ri ga sa da cewa.
"Haba Safwan! Wani irin rashin hankaline haka!? Tun wajan karfe uku saura ku ka fita amma har yanzu baku dawo ba fisabilillah!? Kuma kasan Abi'atu matar aurece yanzu ko!? Ba kamar da ba ce, wai ma tukunna ba ku je kun amso min sako ba, sannan ku baku dawo gida ba, ina ku ka biya ne kam? Hafiza tana tare da ku ne!? Dan Mama ta zo nace mata banga Hafiza ba, amma watakila kun hadu da ita a gate ku ka tafi tare" duk a lokaci daya Ummi ta jero magana da tambaya, jin shuru ba amsa ne ya sata kara faɗin.
"Hlo Safwan ba ka ji nane?"
"Ummi mu na asibiti!" cewar Ubaidullah muryarsa kamar zai sa kuka, jin muryan Ubaidullah yasa gaban Ummi bugawa da karfi,a kiɗime ta ce.
"UBAIDULLAH!? meya faru!? Baka tafin bane!? Waye kuma a asibiti!?" shuru Ubaidullah ya yi ya kasa ba wa Ummi amsa, ya kalli ido Abi'atu wacce take shirin sake saka masa kuka, girgiza mata kai ya yi alamun kar ta yi sannan ya sake kifa kanta a gefen kirjinsa, da kyar Ubaidullah ya ce.
"Ummi, ku taho Specialist Hospital yanzu pls da Abba da Mama" yana gama faɗi ya ajiye wayar, a kiɗime Ummi ta hau neman layin Abba Allah ya so bugu biyu ya daga nan ta shaida masa Ubaidullah ya ce yanzun nan su taho
Specialist Hospital, shi ma Abba a zabure ya ce dama Ubaidullah din bai koma aikin bane, waye ba lafiya, Ummi tace itama bata sani ba, Abba yace dama yana kusa da gida ga shi nan zuwa, Ummi ta ce ya dauke su kawai ita da Mama a bakin gate din gidansu Ubaidullah din, Abba ya amsa da to, ko da Ummi ta yi Mama magana hankalin Mama ya tashi in da take cewa dazu da ta shigo gida Zaidu ya kirata akan ina Ubaidullah ta ce masa tun karfe biyu da yan mintoci yabar gida ya tafi airport yake ce mata yana ta kiransa baya dagawa, Mama tace masa, ba mamaki yana jirgi da haka suka yi sallama da Zaidu, yanzu kuma ance ana asibiti to waye ba lafiya? nan dai cike da zullumi suka fito gate suka tsaya su na tunanin waye ba lafiya da har su ka je asibiti, sannan ya akayi Ubaidullah shi da ya kama hanyar airport ya bige da zuwa asibiti, to ma ya akayi suka hadu dasu Safwan har wayar Safwan ta shiga hannun Ubaidullah? Wannan shi ne tambayoyin da Ummi da Mama da Abba suke yiwa Zuciyoyinsa amma babu mai basu amsa sai sun isa asibitin, basu fi minti bakwai da fitowa ba Abba ya iso nan suka burma motar su na jimamin meya faru, a cikin da kankanin lokaci suka iso asibiti Abba ya kira wayar Safwan dan ya kira na Ubaidullah bai daga ba, nan Ubaidullah ya ɗaga ya gaya musu inda suke gami da yi musu kwatance, tafiya sukeyi da sauri-sauri kamar zasu tashi sama, su na shigowa suka hango Ubaidullah da Abi'atu, ga jikinsu duk jini da sauri Abba ya karaso yana kiran sunayensu Abi'atu tana kallon Ummi ta sake barkewa da kuka ta tashi da gudu ta rungume Ummi, sosai jikin Ummi ta yi sanyi, kallon Ubaidullah Mama ta yi wanda ya dukar da kansa kasa, Mama ta ce.
"Ubaidullah meya faru!? Hatsari aka yi ne!? Ina Safwan da Hafiza!? Wai meke faruwa ne!?" Abba ya kama Ubaidullah ya ce.
"Mama kiyi masa tambaya a hankali, Ubaidullah meya faru, karka ji komai faɗa mana?" ganin Ubaidullah ya kasa magana yasa Mama dago Abi'atu daga jikin Ummi ta ce.
"Abi'atu meya faru!? Hatsari ku ka yi ne? Ina Safwan!? Kun fita da Hafiza!?" cikin sheshsheƙar kuka Abi'atu ta gya ɗa kai ta fara basu labari da dasheshshiyar muryarta wacce tasha kuka ta godewa Allah, tana gaba basu labari Ummi ta yi baya-baya zata faɗi da sauri Abba ya tarota ya yinda Mama ta zube kasa sharab irin zaman yan bori sabida tsananin tashin hankali, Abba ya kalli Ubaidullah ya ce.
"Yanzu ina Hafizan!?" da kyar Ubaidullah ya ce.
"Tana ciki, likita ta ce basu yi mata komai ba"
"Safwan din fa!!!!? Cewar Mama da jikinta ya ɗauki b'ari, a sanyaye Ubaidullah ya ce.
"Tun da suka shiga da shi har yanzu basu fito ba, balle mu ji ya yana yin jikinsan yake" Abba ya ce.
"To su yan iskan su na ina!? Ba dai barinsu ka yi ba!?" murmushin baƙin ciki Ubaidullah ya yi ya ce.
"Abba taya zan barsu!? Mutanen da na dauki tsawon lokaci ina nemansu *RUWA A JALLO* sunyi sanadiyyar mutuwar kanwata, abun bai ishesu ba, sun sake zuwa suka dauke dayar, ga shi yanzu a garin taimakonta ga Ɗan Uwana yana cikin emergency ban san a wani hali yake ba, taya zan barsu Abba!? Su na can na daure su, so nake na san halin da Ɗan Uwana yake ciki kafin na koma garesu" Abba ya yi ajiyar zuciya gami da cewa.
"Bari na kira Police" ya fada yana kokarin kiran waya, da saurin Ubaidullah ya rikosa ya ce.
"Abba wani police kuma zaka nema bayan ga Soldier a gabanka? Mai mukamin Captain? Ba bukatar police Abba, nine nan zan hukuntasu da kakina, na godewa Allah da aikina ya dawo ababen farauta ne suka bayyana, sai na dandana musu azaba kafin na kashesu!!!!" ya faɗa bakinsa na hayaki,jinjina kai Abba ya yi, babu wanda ya sake magana a cikinsu illa fargaban da suke ciki, nan suka koma suka tsaya cirko-cirko, kafin likita ta fito ta ce Hafiza ta farka, su na shiga suka sameta tana kuka tana shirin wafce drip din da aka ɗora mata tana ambatar sunan Yaya Safwan, Abba ne ya dakatar da ita akan cewa karta cire Safwan yana lafiya, kallon Abi'atu ta yi wacce itama ke layi sabida matsanacin kanta dake mata ciwo kamar zai rabe gida biyu, Hafiza ta ambaci sunanta, Abi'atu ta zo ta rungumeta su na kuka tare abun tausayi, matukar tashin hankalin haƙiƙa hankalinsu a tashe yake, sai wajan karfe sha ɗaya kafin wasu Doctors su biyu ne suka fito su na sharce gumi, da sauri Ubaidullah ya tare su yana tambayar jikin Safwan, ganin yadda hankalinsa yake tashe ne suka dafasa sannan suka ce shi da Abba su biyo su office, hakan kuwa aka yi, ko da Abba da Ubaidullah suka zauna Dr ya ce.
"Alhamdulillah! Aiki muka yi masa but mun sha wahala sosai, sabida da kyar jinin da ke zuba ya tsaya, dan bayan wajan ƙeyar kusa da wujan wuyarsa gurin ne
Ya fashe dan kuwa abun da aka buga masa mai karfi ne gaskiya, saukinta ma bata wajan kwakwalwarsa bane da ya mutu ko ya samu tabin hankali, a gaskiya ya zubar da jini sosai, yanzu jini muke bukata dan da kyar muka samu muka tsaida jinin kafin muka yi masa aiki" da sauri Ubaidullah ya mika hannunsa yana cewa.
"Dr ku auna nawa idan zai masa ku ɗiba a saka masa!" murmushi Dr ya yi ya ce.
"Ka kwantar da hankalinka, Nan da 2days Dan Uwanka zai iya farkawa da zarar mun saka masa jini, dan mun ga ka damu sosai In sha Allah he will be fyn very soon" gauron ajiyar zuciya Ubaidullah ya sauke yana hamdala, nan aka auna jinin Ubaidullah amma bai zo dai-dai dana Safwan ba, dan haka Abba ya ce a dibi nasa, nan kuwa aka ɗibi na Abba aka jonewa Safwan, ranar babu wanda ya rintse haka suka tsaya a asibitin, kuma likitoci sun hanasu ganin Safwan din.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A BARRACKS.*
ko da sojojin da aka bar wa Ubaidullah suka ga har jirgi ya ɗaga basu ga dawowarsa ba, nan suka kira Major Usman suka shaida masa ga yadda Captain ya bar airport, Major Usman kasancewar yasan halin Ubaidullah ya saka shi basu umarni akan su bar airport din su koma barracks, bai damu da ya kira Ubaidullah dan yasan shi baya wasa da aiki, barin ma idan abu ya shafi ceton rai, duk abun da zaisa ya bar airport to hakiƙa babban abu ne, sabida haka ya bada lokaci zai kirasa ko da zuwa yamma ne ko dare, tun da tafiyar ma sai nan da 2wks but su na bukatar ganinsa a barrack ne, babu wanda Major Usman ya sama da maganar sai Captain Zaidu da first Lieutenant KB,nan yake shaida musu kamar yadda shi ma aka shaida masa, dan haka ko da Zaidu ya yi waya da Mama ya bar amsar da ta ba shi kawai dan yasan yanzu sai Mama ta tashi hankalinta, dan haka tun yamma ake neman Captain Ubaidullah amma shuru, Major Usman ne ya bada excuse wa Ubaidullah a barracks kowa kuma ya karba, ko bayan da Dr ya yiwa su Ubaidullah bayanin Safwan zai ji sauki soon sai a lokacin ya duba wayarsa ya ga tarin miss call na manya manya sojoji, ga na Aminansa, sai da ya fara kiran Major Usman bai boye wa Major Usman komai ba, nan take Major Usman ya ce zai yi magana da General Of The Army amma kafin nan Ubaidullah ya kira Lieutenant Genaral ya masa bayani, hakan kuwa aka yi bayan sun gama magana da Major Usman ya kira L.G, nan ya nemi afuwa na rashin dawowarsa yau sannan ya karo uzurinsa, nan kuwa L-General ransa ya b'aci ya ce wa Ubaidullah ya ba shi permit ya taho dasu barracks ya hukunta yan iska, gobe zai ba wa sojoji umarni a taho dasu shi kuma ya sake bin flight, Ubaidullah ya amsa da ok sir gami da cewa ayi masa uzuri nan da kwana biyu idan Brothernsa ya farka, L-General ya ce ba komai zai yi magana da General da kuma General Of da Army, Ubaidullah ya yi masa godiya, kafin ya kira Zaidu ya basa labarin duk abun da ya faru, Zaidu kamar zai yi hauka, haka ya dinga buge-buge yana Allah Allah a kawosu barracks su ci kwal ubansu dan kuwa sun tanadar musu azaba da gwale-gwale dan kuwa basu son wa suka tabo bane, dama ance kwana dubu ta barawo kwana ɗaya tak ta mai kaya.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da washe gari da safe aka kira Ubaidullah, ya ga bakuwar number yana dagawa aka sara masa cikin girmamawa kamar yana gaban mai sara masan, nan yake cewa.
"Sir Captain Ubaidullah, Sir L-General ne ya ce mu kiraka, zamu tafi da masu laifi, ka fada mana in da kake mu zo mu dauke ka" a takaice Ubaidullah ya gaya musu, cikin ɗan lokaci sai ga su sun zo, nan Ubaidullah ya yiwa su Ummi, Abba, Mama Abi'atu da Hafiza wacce take zaune, sallama ya musu gami da yi musu bayanin yadda suka yi da manyansa Abba ya jinjina kai ya ce.
"To ba komai, nima yanzu gida zan wuce tun da sun ki yarda mu ga Safwan din kuma ku zo muje sai muyi wanka ayi girki a taho da shi, ga shi mun bar baƙi a gida, ina ga dai bikin nan ɗagawa za ayi tun da ga angon a kwance" Ummi ta jinjina kai, kafin Ubaidullah ya kalli Abi'atu da gefen ido ya ganta itama kamar wata marar lafiya so yake ya yi mata magana amma ba zai iya ba a gaban iyayensu dan haka suka fito a tare har da Hafizan, su na fita ya ga sojoji da wata babbar mota da kuma wata madaidaiciya duka kuma barracks car ne,yana fitowa suka ƙame su na sara masa, sannan suka bude masa gidan baya ya shiga ya zauna, suka tada motar suka fice daga asibitin, su ma su Abba mota suka shiga suka dauki hanyar gida.
A hankali suke tafiya hakan yasa Ubaidullah gaya musu su ƙara gudu, su na tafiya yana musu kwatance har suka iso,bude masa kofa sukayi, ya yi gaba suka take masa baya, ko da ya shiga ya gansu a galabaice, nan ya kunce musu baki yana binsu da wulakantaccen kallo, da kyar suke iya bude idanunsu, su ga sojoji tsaye a bayansa, ɗaya ne wanda yake ɗan dama-dama ya fara magana cike da tsoro.
"Dan Allah! Yallabai kayi mana rai kayi hakuri, wallahi bamu san kai soja bane, ba zamu sake ba mun tu ba, Dan Allah ka......" wani wawan naushin da Ubaidullah ya dunƙula hannu ya kai masa shine ya yi sanadiyar rashin karasa maganarsa wanda take jini ya taho da haƙorinsa uku, dan hannun Ubaidullah bai da kyau, ko ya ya ne ya taba mutum da shi sai ya fito ga hannunsa da mugun zafi, to balle wannan da ya kai masa naushin azafafe, kallon sojojinsa ya yi ya basu umarni da su tafi dasu, sannan duk wanda ya yi musu abun da bai musu ba a hanya su parker motar su ci Ubansa! Nan suka sake sara masa sannan suka dauki samarin suka fita dasu, wasu kuma ya sakasu kwashe masa lapton din yace a sama a mota ,amma kafin nan sai da suka yi ma abubuwan hoto har da kayan shaye-shayen, duk wasu kayan maye yace su tafi dasu but lapton da wasu memories ya ce a kaisa gida dasu,nan suka babbar motar ta dauki hanyar Abuja, wasu sojoji mutum biyu suka ja Ubaidullah izuwa gida.
Horn suka danna mai gadi ya bude musu gate, part dinsa ya wuce kai tsaye, yana shiga ua watsa lapton din akan kujerar parlour, bedroom din Abi'atu ya shige ya kwankwasa ya tura kofar bai ganta ba, nasa bedroom din ya wuce ya watsa ruwa shap-shap, ya sake saka kaya matasa nauyi ya fito ya yi part din Mama, a parlour ya samu Hafiza tana zaune Mama tana gefenta Abi'atu kuma tana zaune a kasa ta takure ga abinci a gabanta ta kasa ci, zama Ubaidullah ya yi kusa da Hafiza Mama ta ce.
"Har ka dawo? An tafi dasun?"
"Eh sai da suka wuce kafin aka maido ni gida" Mama ta jinjina kai ta miƙe ta yi kitchen,Ubaidullah ya sake sacin kallo Abi'atu wacce ta yi kamar bata san ya shigo ba, mai da idonsa kan Hafiza ya yi, ya shafo kanta a hankali ya ce.
"Are u feeling much better?" ta jinjina masa kai kanta a sunkuye dan videon da aka nuna mata na yar Uwarta yayi mugun ɗaga mata hankali dan har yanzu ba wai ta koma nml bane, a hankali Hafiza ta kama hannun Yayanta ta yi masa nuni da Abi'atu sannan ta miƙe ta shiga daki tasa kuka, Hafiza na shiga daki Ubaidullah ya miƙe ya zo gabanta ya kamo hannunta bata yi masa gardaman ba zata tashi ba,ya dauki abinci ya jata suka fita ya yi hanyar part dinsu, yana shiga parlourn ya zaunar da ita, yaja stool gabansu ya ajiye abinci, gamin yadda idonsa duk sunyi luhu-luhu ta lumshe da bude, dafe kanta ya yi ya ji da zafi raɗau, abinci ya fara mata amma ta ki bude baki ta ci, da kyar ya samu ta bude bakin amma tana shirin saka masa kuka ya yi