COLONEL UBAIDULLAH by Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢

Author :  Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category :  Romance

Chapter   7 / 25

18K to 21K   out of 74.6K words

ce.
"Kaƙi ka faɗa mana meya haɗaku da Rumaisa"

Sai da Ubaidullah ya gama shaƙar iska kafin ya fara basu labarin yanda sukayi da Rumaisa, riƙe baki KB yayi ya ce.
"Dole kaji ɗari-ɗari a cikin ranka amma inaso ka sani duk ba zata haifa maka ɗa mai ido ba, Ubaidullah kana tare da Albarkan Mama, Rumaisa bata isa tayi maka abun da Allah bai maka ba, sai dai idan ya fito a cikin littafin kaddaranka, to wannan babu yanda ka iya dole ka karbi kaddararka hannu bibbiyu, amma zamu tayaka da addua In sha Allahu ma babu abin da zai faru"

Jinjina kai Ubaidullah ya yi, ba tare da ya sake furta ko da kalma daya bane, KB da Zaidu ne suke hiransu amma babu bakin Ubaidullah a ciki, dan shi haka yake magana bata damesa ba, karshe ma da suka ishesa tashi yayi ya basu waje ya shige bedroom.

Zaidu ya bisa da kallo ya girgiza kai ya ce.
"Mutum sai kace mai iskokai, ga uban canza kala sai kace hawainiya, nidai bazan fasa fadi ba zanga kalar macen da zata iya zama da kai"

KB ya kwashe da dariya ya ce.
"Kai fa kace min tsab mace zata gyara Ubaidullah ya dawo saiti shine kuma yanzu kake wannan maganar? Ko kamanta kace min mace kadara ce mai tsada?"

Dariya shi ma Zaidu yayi ya ce.
"Ban manta ba, amma lamarin Abokina sai shi wallahi" nan dai suka ci gaba da hirarsu.


Ko da Ubaidullah ya shiga ya kwanta ba jimawa bacci ya kwashesa ba tare da yasani ba, su ma da suka gama abun da sukeyi suka wuce bedroom dinsu kasancewar gobe asubanci zasuyi.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Tun kiran sallar farko suka farka, wa inda basu sallah har sun shirya, nan ma sai da akayi daru da Ubaidullah shi da commander Victor wai sai dai su Ubaidullah su tafi ba tare da sunyi Sallan asuba ba sai suyi a hanya, Ubaidullah ya ce.
"Sam bai jiba bai gani ba, ko da General Of The Army ne yazo akan cewa su tafi ba tare da yayi sallah ba, wallahi sai dai a tafi abarsa, a fasa tafiyar nan dashi.


Haka kuwa suka hakura bayan sun gama shiryawa, ga barracks bus yayinda sojoji suke tsaye sun ƙame waje guda General Of The Army yana musu addua tare da tuni abun da zai kaisu kwana uku kacal ake bukata suyi su dawo, sara masa sukayi sannan suka shiga bus, General ya ce musu.
"Goodlock."



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Tafiya suke ana hira amma ban da Ubaidullah, wanda fuskarsa jiya iyau, karshe ma wayarsa ya ɗaga ya kira Mama a lokacin karfe 9:00am sun ɗanyi nisa tun da sun fita daga garin Abuja, airpiece ya saka Mama da ta idar da Sallan walha tana lazimi taji wayarta na neman agaji, a hankali ta janyo wayar dan tasan bazai wuce ɗanta Ubaidullah bane, tana dubawa taga shine, ɗagawa tayi, tun kafin tayi magana ya ce.

"Assalamu alaykum My Momma fatan kin tashi cikin koshin lafiya? Yasu Sister's?"


"Lafiyar mu kalau Alhamdulillah Yaya Babba Soja mazan fama, har kun kama hanya ko?"

Lumshe idonsa yayi domin idan yana waya da mahaifiyarsa, har wani farin ciki da Annushuwa yake tsintar kansa a ciki, yakan manta da damuwar da take damunsa ya fuskanci mahaifiyarsa su sha hiransu abun sha'awa da birgewa.


"Eh My Momma dan har ma munyi ɗan nisa tun da gamu nan a jos yanzu haka"


"To masha Allah Ubaidullah ya Zaidu da wanda muke gaisawa dashi din nan ma? Ubaidullah ya ce.
"KB"

"Yauwa Eh shi fatan su na lafiya ko?"

"Eh lafiyar kalau Mama ba kiji, suturun su ba?"

Mama ta ce.
"Aifa dai kam akwai surutai kala-kala dan bana ma jin maganarka sosai saboda hawaniya"




Dogon tsaki Ubaidullah yaja gami da juyawa ya kalli KB da Zaidu wanda suke zaune kusa dashi, a hasale ya ce.
"Malamai ku sararamin dan Allah, surutunku yayi over, waya nake amma saboda maganganunku yasa bana jin abun da Mama take cewa"ya karasa maganar yana mai kara jan tsaki.

Girgiza kai Mama tayi ta ce.
"Ubaidullah Allah ya shiryeka, dan Allah ka dinga sassautawa zuciyarka kana saka mata salama kaji?"

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce.
"To Mama In Sha Allahu ki dinga tayani da Addua"

"Addua Ubaidullah kullum a cikin yi muku nake,Allah ya shirya min ku ya muku Albarka" da ameen ya amsa yana tambayarta su Hafiza da Na'ila, Mama ta ce.
"Sunje makaranta" hira suka dan taba kafin sukayi sallama.




Anty Ummu ya kira suka sha hira, bayan sun gama ya kira Umma (mahaifiyar Zaidu) nan yaji muryan Inna sai sababi take ita dasu Afnan wanda basu gida su na makaranta abun da suka mata tun kafin su tafi shine take ta mitansa har yanzu, Girgiza kai Ubaidullah yayi a cikin zuciyarsa yace wannan tsohuwa ba dai jaraba ba, ita kullum masifa ko gajiya bata yi.


Addua Umma tayi musu dan Ubaidullah ya faɗa mata gasu a hanya, kuma dama tasan da tafiyar tasu, tun da Zaidu ya sanar da ita, bayan sun gama wayar ne Ubaidullah ya lumshe idonsa gami da jinginuwa da sit, Zaidu kallon Ubaidullah yake saboda kirkinsa, duk ji da kai irin na Ubaidullah yana son jama'a amma miskilancinsa ne yake hanasa sakin fuska, Uwa Uba zafin rai, da haka kowa ya ci gaba da hidimarsa a cikin bus babu mai kula wani, tun bayan da Ubaidullah ya daka tsawa.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Ba su Ubaidullah da isa bordern Niger ba sai karfe tara na dare, su na isa ba tare da bata lokaci ba suka kai wa yan ta'addan da suka zo kamawa farmaki, yayinda suke kokarin guduwa su kuma ,amma cikin ikon Allah suka kamasu sannan suka damƙasu a hannun jami'an tsoron bakin border din.



Rundunar sojojin bakin bordern Niger sunji dadi sosai ganin aikin da suka kasa tsawon wata daya amma a ɗan kankanin lokacin da bai wuce awa biyu ba rundunar sojojin Murtala barracks na garin Abuja suka kamasu, sannan suka damƙa musu masu laifin, hakan ne yasa shugaban rundunar sojojin Niger ya bawa su Ubaidullah masauki mai rai da kuma lafiya.



Kwanansu Ubaidullah biyu a Niger sannan suka kama hanyar dawowa Abuja.


Asubanci sukayi, dan haka ana sallan isha'i suka shigo Abuja saboda gudun da suka dinga shararawa akan titi.



Masha Allah sun iso lafiya, yayinda sojoji aka taro domin tarbansu, daga ciki kuwa harda General Of The Army da matarsa da Yarsa Hanan.


San da su Ubaidullah suke fitowa a mota daya bayan ɗaya kowa sai ya sara musu, Ubaidullah shine karshen fitowa a mota, da kyar yake iya ɗaga kafarsa fuskar nan babu walwala.




Yana fitowa yayi tozali da Zeey ta sakar masa murmushi, a zuciyarsa ya ce.
"Another trouble don come back,Oh Allah ni Ubaidullah"

Sai da yazo gaban General Tukunna ya dan sakin murmushin gefen baki, hajiya Jamila matar General sai yamutsa fuska take, Hanan kuwa ta gama mutuwa akan Ubaidullah bata san ta inda zata fara tunkarar mahaifinta ko Ubaidullah ba, ta rasa ya zatayi da Soyayyar Ubaidullah wanda kullum kara ruruwa yake a cikin Zuciyarta, gashi ta fuskanci Ubaidullah dan ji da kai da shan kamshi ne, dan duk yanda take da ji da kai Ubaidullah ubanta ne.


Nan General Of The Army ya jinjinawa kwazo da jarumta irin na su Ubaidullah sannan suka mika masa lambar yabon da suka samu daga shugaban rundunar sojojin Niger.



Sosai jama'a aka tayasu murna, masu tayasu bakin ciki ma duk sun musu,kafin suka wuce part dinsu, Zeey taso tayiwa Ubaidullah magana amma ina bata samu damar hakan ba.



Sai da suka watsa ruwa sukayi sallan Isha'i, kafin KB da Zaidu suka nemi waje suka kwanta,a lokacin Ubaidullah na tsaye jikin mirror juyowa ya yi ya kallesu yaja tsaki.

"Nifa lokaci ya yi da zaku barmin part dina ku koma naku especially kai Zaidu Mijin yarinya" ya fada maganar yana nuna Zaidu da yatsa.


Zaidu dake kwance ya tashi ya zauna yana zubawa Ubaidullah harara ya ce.
"Bazan koma ba Yaya Captain sai kazo ka mai dani"

Me KB zaiyi in ba dariya ba yana kallon draman su.


"Mtswwww! To nikam na gaji da ajiye ku a part dina, haba kowanne ku fa da nashi part din amma duk kunbi kun tare a nawa,abun haushin ma, ku kama, ku wani haye min bed dina ku barni akan kujera, tun da kunsan ni bana iya kwanciya da mutane bana son naji motsi kusa dani"



Miƙewa tsaye KB ya yi yana cewa.
"Gaskiya Ubaidu halinka akwai gyara baka son kaji motsi kusa da kai, idan kayi aure kuma fa,ko me kake nufi?"
Zaidu ya ce.
"Tambaye shi kam"


"To sai aka ce muku ni mayen mata ne kamar ku?"


"To mu ma kuma sai aka ce maka mayun matan ne?" cewar Zaidu yana haɗa rai.


Murmushin gefen baki Ubaidullah ya yi ya ce.
"Yes of course especially ma kai
Dan kafi kowa son aure da maganar aure"


Duk haɗa ran Zaidu sai da ya dara, dan maganar Ubaidullah ya basa dariya, ba kadan ba, kallonsa ya yi ya ce.
"To wa ka taba ganina da ita a barrack din nan uhum? Da sauki ai tun da aure naso kaga kuwa alamun ni lafiyayye ne"ya karasa maganar da sakin dariya shi da KB, iyakar ƙuluwa Ubaidullah ya ƙulu, da haka ya fatantake su a bedroom din ya kulle yana cewa.
"Wallahi sai dai ku kwana a parlour"

Su na dariya suka wuce part dinsu, amma duk ƙura dole ce tasa suka dawo suka kwanta a parlourn Ubaidullah da niyyar gobe zasu sa a gyara nasu.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




Da washe gari misalin karfe tara na safe Ubaidullah bayan ya dawo daga training, dan ya zame masa jiki da yayi sallan Asuba zai fita judging shiyasa jikinsa duk ya murmuɗe da ka gansa sai kayi tunani wani ɗan shekara 30 ne, amma bai kai ba.


Yana isowa kofar part dinsa ya ga su Zaidu tsaye cirko-cirko da wasu sojoji fuskar su dauke da tashin hankali, shi ma Ubaidullah a kiɗime yake tambayar su. "Meya faru?" da kyar Zaidu ya yi karfin halin cewa.
" Ubaidullah muje ana nemanka a filin taro, barracks meeting yanzun nan"


Duk faduwar da gaban Ubaidullah keyi ba shi ya hanasa juyawa cike da karfin hali da kwarin guiwa ba, dan shi dai yasan bai aikata komai ba.


Jiki a sanyaye KB da Zaidu suka rufa musu baya.


Yana isa ya samu General Of The Army tsaye fuskarsa ba annuri ya haɗe rai ,ya rikiɗe ya koma asalin sojan, a gefensa kuwa Major Shehu ne shima ransa bace,a takaice dai dik manyan sojoji fuskar su ba walwala.

Gefe ya kalla ya ga sergeant first class Ƙasimu, (mahaifin Rumaisa) a ɗayan gefen Rumaisa ce zaune sai kuka take kanta a sun kuye, cike da Jarumta Ubaidulllah ya sara musu amma babu wanda ya kallesa, dama mahaifin Rumaisa haushin Ubaidullah yake ji saboda daga zuwansa Allah ya daukaka shi, yanzu kuma ga abun da ya faru ga abun da yayiwa ƴarsa, ai dole ya wulakanta Ubaidullah ya tozarta shi.


Cikin Tsawa da ɗaga Murya General Of The Army ya juya ga Ubaidullah yana masifa yana nunasa da yatsa.

"Kaban Mamaki Captain Ubaidullah! Kayi mugun bani Mamaki! Ban taba tunanin haka daga gareka ba, kai da kake yaƙi da wanda suke yiwa Yan mata fyaɗe amma ace yau kaine kayiwa Rumaisa fyaɗe har ka mata ciki!!!"

Maganar General sai da ya girgiza duniyar Ubaidullah, ya kasa tantance a wace duniyar yake, shi yaushe ya taba kama mace ya runguma balle har ya kusanceta har ya mata ciki? Macen ma kuma Rumaisa wanda ko ɗaura masa ita akayi a kafa zai kunceta ya jefar balle har wata tarayya ya shiga tsakaninsu ya mata ciki? Innalillahi wainna ilayhirrajiun!" shine kalman da Ubaidullah yake iya nanatawa kenan ya kasa magana.


Kallonsa Lieutenant General Musbahu ya yi gami da cewa.
"Captain Ubaidullah shin da gaske kaine kayiwa Yar gidan Sergeant first class Ƙasimu ciki? Dan tace kaine Saurayinta kuma da kai take mu'amala.




Ban da juyin da kwakwalwar Ubaidullah keyi, amma ya kasa katabus, juyawa yayi yaga sojojin da suke tsaye da zaune ga Rumaisa dake kukan munafurci har yanzu, kafin kace mai Idon Ubaidullah ya rikiɗe ya koma jajur ga jijiyoyin jikinsa da suka miƙe tsantsaye.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



*_YA ALLAH MUN TUBA ALLAH KA YAFE MANA ZUNUBANMU ALLAH KA YAYE MANA CUTAT COVID19 ALLAH KASA MU GAMA DA WANNAN DUNIYAR LAFIYA AMEEN🤲🏻🤲🏻_*


*MASOYA BOOK DIN COLONEL UBAIDULLAH,INA MAI BAKU HAKURI NA RASHIN JINA TSAWON SATITTIKA, NGD DA KAUNAR DA KUKE NUNAWA WNN BUK DIN NAWA*👏🏻👏🏻




COMMENTS

AND


SHARE


MOMYN AHLAN✍🏻
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*page°°°°°26&30*


Jikinsa sai kyarma yake yi, Alluran Soja ya miƙe dama ya lafiyar giwa balle tayi hauka, gadan-gadan yayi kan Rumaisa yana shirin kai mata cafka, da sauri Babanta ya tare Ubaidullah ya kai masa naushi a baki nan take bakinsa ya fashe sai ga jini tare da haƙorinsa biyu sun faɗo.




Hannu Ubaidullah ya kuma kaiwa zai kamo Rumaisa Commander Victor ya sha gabansa gami da kaiwa Ubaidullah duka a ciki, zafi sosai Ubaidullah yaji amadadin ya duƙa sai ya rufe Commander Victor da duka, nan fa fili ya rikiɗe tamƙar filin yaƙi nan aka shiga kokarin riƙe Ubaidullah amma duk wanda ya tabasa zai zubar dashi kasa, hakanne ma yasa wasu sojojin suka samawa kansu lafiya ta hanyar komawa gefe suyi kallo,cakwakiya tayi cakwakiya dan Ubaidullah ya zubar da sojoji sun kai ɗari da wani abu a kasa sai kace yaje filin yaƙi, cikin zafin rai ya fara magana.




"Ni za kiyi wa Sharri! Rumaisa? Ni za kice nayi miki ciki ? Ni zaki tozarta Rumaisa? Mena tare maki da zaki min ƙazafi? Nace mai na tare miki!" yana maganar yana kai duka yana tunkarota tana ja da baya.


General ganin fa idan ba da gaske akayi ba wajan tare Ubaidullah idan ya kama Rumaisa to sai dai wata amma ba ita ba, da sauri General da Major suka riƙo Ubaidulllah ta baya, har Ubaidullah ya juyo zai kai duka sukayi ido hudu da General Of The Army nan ya sauke hannunsa da sauri sannan ya sara masa,jikinsa sai b'ari yake yi jijiyoyin jikinsa sun sake fitowa raɗa-raɗa, cikin tsananin bacin rai General Of The Army ya ce.
"Aje a kulle Ubaidullah a saka shi a guardroom" da sauri Hanan ta ce.
"No pls Daddy kar a a saka shi a guardroom sai kace wanda yayi sata ko yayi wani babban laifi, daddy da muƙamin shi da komai dinshi a saka shi a guardroom?"

Tsawa General Of The Army ya dagawa ƴarsa wanda ya sakata firgita har sai da taja da baya tana zare ido, Major ya ce.
" Captain Ubaidullah yayi babban kuskure na dukan da yayiwa Sojoji dan bai kamata ace ya dakesu ba, dan ya fisu muƙami,sannan ba a yarda da maganar da Rumaisa ta faɗa ba sai da ta gabatar mana da hujjar wani video recording wanda suke mu'amala tare, dan haka a tafi dashi" da karfi Raihana da wata yarinya christen mai suna Doratie suka mike gami da cewa.
"Na lie! Ubaidullah he can't do this" amma babu wanda ya saurare su, Zeey kuwa mikewa tayi idonta jajur ta bar wajan, tashin hankalin da Zaidu da KB suka shiga kuwa bazai misaltu ba, dan suman tsaye suka yi,duk wannan budirin sun kasa yin katabus,
Sai da suka ji General yana umarta kama Ubaidullah a tafi dashi guardroom tukunna suka fara roƙon General amma ina bai saurare su ba, sojojin da zasu kama Ubaidullah cikin tsoro da shakkarsa suka kamasa, dan Ogansu ne, uwa uba kuma mai karfi ne,dan su na jin tsoro karya zubar dasu ya ja musu kwanciyar asibiti.


Rumaisa hankalinta ne ya tashi dan ita ba haka ta so ba, taso ace General dasu Major su bawa Ubaidullah Umarnin ya aureta ne, amma bawai a kullesa ba, tunani ta shiga yi, yanzu ya za tayi,Da sauri ta miƙe tabar filin wajan ta dauki wani hanya,tana tafiya hankalinta baya gabanta, batayi auni ba ta ji saukar naushi a bayanta take ta faɗi kasa, dagowar da zatayi taga Zeey tsaye a saman kanta fuskarta tayi ja.


Cikin zafin rai Rumaisa ta miƙe zata rama naushin da Zeey ta mata, dan dama sun saba in dai dambatuwa ne,ta kaiwa Zeey naushi Zeey ta riƙe hannunta ta murɗeshi ta baya ta shaƙo wuyanta, ta fara magana cikin bacin rai, da tsawa.


"Makaryaciya! ashe son da kike ikirari kina masa duk karya ne! Wallahi Rumaisa baki son Captain tun da har zaki iya zubar masa da mutunci a filin jama'ar da sun kai Fiye da dubu, Rumaisa karya kike kice son shi kike,tun da gashi kinci zarafinsa kinsa an kullesa a guardroom"



"Rumaisa me Captain ya miki da zaki saka masa da ƙazafin *ZINA*? Haba Rumaisa! Haba Rumaisa! Wallahi ko rantsuwa dubu zanyi idan na karyata ki ba zanyi kaffara ba,saboda nasan halin Captain kema kuma kinsan halinsa, Rumaisa idan ma karya kike akan cewa kina da ciki alhalin babu, to saina miki la'anannan duka ta yanda sai ciki ya shiga jikinki, idan kuma akwaita na wani dan iskan ne a cikin barracks din nan kikeso ki liƙawa Captain to sai na miki kafurin duka ta yanda sai kin haifi cikin nan baki shirya ba"

Nan Zeey ta rufe Rumaisa da ƙazamin duka dan ranta yayi mugun baci, tana cikin jibgarta kenan sai ga Hanan yar gidan General Of The Army da Doratie da Raihana, su ma sun biyo bayan Rumaisa su lakaɗa mata duka ne, amma me nan suka ci karo da Zeey dake jibgar Rumaisa kamar zata kasheta dan Zeey mugun karfi gareta, dan harta mazan barracks wasu shakkar Zeey suke saboda ba ƙaramin abu ne a wajanta duk dan iskan da ya taƙaleta ta nuƙuskushesa, ta ƙara gaba abunta.


Hanan ganin Zeey tana shirin kai Rumaisa lahira nan suka shiga kokuwar kwatar Rumaisa daga hannun Zeey, da kyar da suɗin goshi suka kwaceta amma kafin nan sai da su ma sukaci duka.


Gefe Zeey ta koma tana huci, yatsar hannunta manuniya ta nuna Rumaisa dashi gami da cewa.
"Wallahi!Wallahi!Wallahi! Rumaisa kinji na miki rantsuwa uku ko, idan har baki je kin warware kullin da kika yiwa Captain ba, sai na miki *LAHANI* sai na miki *ILLA* sai dai duk

7 / 25