Author : Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category : Romance
riƙeta ba, a ranta ta ce "laifina ne, zan ba shi hakuri" baya ta gama ne ta haɗa masa coffee mai kauri da madara tasa a karamin trey ta yi hanyar dakinsa da sallama ta turo kofar ta ga Hafiza na ba shi magani, nan jikinta ya sake sanyi ta ajiye tray din hannunta akan karamin center table din dake dakin tana cewa.
"Hafiza ba kiyi bacci ba?"
"Eh wallahi Anty da har zan kwanta Mama tace Yaya na nemana" jinjina kai tayi ba tare da ta sake magana ba, Hafiza tana gama ba shi maganin tayi musu sai da safe ta fice abunta, ko kallonta bai yi ba ya fara shirin gyara kwanciyarsa ta ce.
"Ga shi fa nayi maka girki ne shap-shap" ya ce.
"Am ok, bana jin cin abinci" shuru ta yi kafin ta miƙe a hankali ta dauki tray din ta fice ta koma kitchen ta dau supboil ta zuba masa kadan sauran kuma ta juye a rabo ta sa a freezer dakin ta dawo ta haura gadon nasa ta kwanta, Ubaidullah da ya rufe ido kamar mai bacci ya ji shigowarta bai gama mamakin me ya dawo da ita ma ya ji ta hayo gado ta rungumesa cikin sanyin murya ta hau basa hakuri tare da alkawarin ba zata sake ba, da kyar ta shawo kansa ya kalleta ta dinga rokonsa ya ci abinci, kafin ya tashi yaci ta taimaka masa ya yi brush suka kwanta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da washe gari sun makara sallah dan bacci ya musu dadi, rabon da su yi bacci kamar haka sun manta, sai karfe goma suka yi sallahn asuba, bayan sun idar suka sake komawa bacci basu da farkawa ba sai karfe biyu, nan ma sai da Anty Ummu ta aiko Hafiza ta duba ko su na lafiya, tukunna suka tashi, ta taimaka masa ya yi wanka ta shirya shi, itama ta yi ta shirya sannan ta kama shi suka yi part din Mama, tun daga kofar parlour hayaniya ke tashi, su na shiga kuwa suka iske mutane, su Ummi ne dasu Umma, Inna, Zaidu, Anty Ummu, Yaya Safwan da Matarsa Shafa'atu, da sauran maƙotan arziƙi, su na shiga aka hau gaishe-gaishe, Inna ganin Ubaidullah ta ce.
"Ohh Allah Ubaidu? Sannu ansha fama,an wuce da kyar ko? Yanzu sabida rashin imani haka suka yi maka? Dan ma kana da taurin rai inaji da yanzu zaman makoki muke yi, ina dalili da wannan aikin soja, kun bar mu cikin firgici da tashin hankali, gaskiya ni kam abun ya isheni" ta karasa maganar tana haɗe rai, Ubaidullah suka yi dariya shi da Zaidu, ba tare da sun bawa Inna amsa ba, aka ci gaba da hira su na bada labarin tashin hankalin da suke gani kafin Zaidu ya fara bada labarin yan ta'addan da aka kashe da sojojinsu da aka kashe duk da sunji a labarai amma ance waka a bakin me shi yafi dadi, yawancin mutanen da suke wajan fatan Alkhairi suka din ga yiwa sojojin nigeria, tare da adduar Allah ya daga nigeria, su Safwan ne suka miƙe su na yiwa jama'ar dake wajan sallama dan Shafa'atu bata jin dadi tana faman da laulayin karamin ciki, tun da Ubaidullah ya fahimci Shafa'atu na da ciki ya ji shi ma fa a duniya yana son ya ga Jininsa kwanan nan, inda ya kudirta a ransa kafin ya koma barracks sai ya mai da Abi'atunsa cikakkiyar mace, hira aka sha da Ubaidullah kamar ba shi ba, duk da azaban ciwon da yake ji a jikinsa, sai dare kafin jama'a aka watse.
Haka aka din ga yi har na tsawon sati daya ana cika a gidan Mama tamkar wanda ake shagalin biki, jikin Ubaidullah Ma sha Allah yana samun sauki kasancewar Hajiya Abi'atu an zage dantse wajan kula da miji, abun da yasa ta kara mai da hankali sabida yan matan da ta ga su na shigowa masu baki kamar na jab'a wai su na zuwa gaishe da mijinta ko wacce da kalar fari da idon da take masa, shi yasa ta sake ƙaimi wajan ba shi kulawa, da haka har ya yi sati biyu, kuma yanzu alhamdulillah yana iya daga dayar hannun nasa, wajan ciwon ya fara kamewa, yau ma kamar kullum ta fito daga kitchen shi kuma yana zaune kasar carpet, zama ta yi kusa da shi hannunta dauke da cup, fara ba shi kunun ta yi a baki yana sha, ya dan ja kumatunta, ya ce.
"Abi'ah?" kallonsa ta yi ba tare da ta amsa ba, ya kuma cewa.
"Abi'ah, *KINA SO NA?*" gabanta ne ya faɗi, tabbas tana son shi mana, amma sai ta tsinci kanta da kasa ba shi amsa, shi ma ganin ta yi shuru bai sake ce mata komai ba, illa zullumin da zuciyarsa ta shiga, tashi ta yi sabida ya gama shan kunun, tana tashi ya bita da wani kallo wanda ya haifar masa da kasala da jan ido, hakika Abi'atu tana da sirhitaccen kyau, jinginuwa ya yi da kujera ya lumshe ido yana taro yadda take tafiya halittar jikinta yana motsawa, har ta dawo ta zauna kusa da shi bai sani ba, sai da ta da fa shi ta ce.
"Lafiya kuwa?" bude ido ya yi, ta ga yadda idonsa ya rine, ta zaro ido ta sake jefo masa tambaya.
"Ya salam! Me ya same ka ne? Ko wani waje na maka ciwo ne?" bai bata amsa ba ya sake lumshe idonsa, kamar da, 5mins haka ya ce.
" *ABI'ATU*, nayi miki tambaya amma ba ki bani amsa ba, ko me yasa?" sake yin kasa ta yi da kanta tana wasa da fingers dinta, ji ta yi ta furta masa tana son shi ya mata tsauri a baki, fizgota Ubaidullah ya yi ta zube a kirjinsa wanda sai da ta bugi ciwonsa da sauri ta ce.
"Ciwon ka fa?" zata sa hannu da hannunsa marar lafiyar ya ture hannunta kamar zai yi kuka ya ce.
"Ban damu da wannan ba kawai ni ki bani amsata, do u luv me?" Shuru ta yi tana dan wani nazari kafin ta gya ɗa masa kai alaman eh, sake matseta ya yi a jikinsa dan farin ciki,duk da dai ya so ta furta ne a baki ba wai da kai ba, amma ya san ta da kafiyar tsiya kuma sai ta furta da kanta, magana ya fara mata ya ce.
"Yauwa, ni dama magana nake so muyi dake ko nace ina so ne muyi yar wata shawara,kinsan matarka itace abokiyar shawararka hakane?"
"Eh, haka ne, ina jin ka to"
"Yauwa, ina so ne Zaidu ya yi aure kafin mu koma bakin aiki, dan kin ga ance za a karrama mu ne, zan so ace yana da mata shi ma, dan haka ina so ayi aurensa da Hafiza kafin mu koma, amma ke ya kika gani?" gyara zama ta yi ta riƙe hab'a ta ce.
"Maganarka abun dubawa ne, amma kai kana ganin auren nan zai yu kafin ku koma? Yanzu fa saura sati biyu ne kawai, har za ayi shiri kafin ku koma?" murmushi ya yi, ya ce.
"Me zai hana, sati biyu ai da lokaci, da kudinmu fa a hannu, kuma kin ga auren gida ne ba na waje ba, daga yau zamu fara shiri in dai kin bada shawarar ayi, to ki koma gefe kiyi kallo" dariya ta sa ta ce.
"Na bada goyon baya dari bisa dari, na bada shawarar ayi, amma mijina bai ji sauki ba fa?"
"Wa ya gaya miki Mijinki bai ji sauki ba?"
"Au yanzu kai a ganinka ka ji sauki?"
"Ke ba ki yarda da naji sauki ba?"
"Taya zan yarda?" tashi ya yi ya kamo hannunta ya ce.
"Zo muje bedroom dina na gwada miki naji sauki, za ki sha mamakina yau" ba tare da ta fahimci abun da yake nufi ba ta hau binsa, har sunje bakin kofa zasu shiga ta gane me yake nufi da sauri ta fizge hannunta tana dariya ta sa gudu tayi hanyar bedroom dinta har tana riƙe kirji, shi ma dariya ya yi ya ce.
"Ai da kin tsaya na nuna miki yar nema kawai" kaya ya shiga ya canza ya fito ya kwankwasa mata kofa "matsoraciya, fito muje wajan Mama" da sanɗa ta fito su na haɗa ido suka saki murmushi a tare, kafin suka jera izuwa part din Mama, a dakinta suka sameta, nan Ubaidullah ya mata bayanin shawarar da suka yanke, Mama ta yi na'am da hakan, sannan ta ce ya nemi Zaid din su yi magana, yanzu ita ma zata nemi su Umma su yi magana sai asan abun yi, amma yana ganin jikinsa ya warke ne da zai bullo da maganar biki, ya amsata da shi baya jin komai ciwon ne kawai da basu gama hadewa ba, Hafiza dake tsaye kofar Mama ta ji shigowarsu Yayanta tazo ta gaishesu taji su na maganar da ya daga mata hankali, da gudu ta koma dakinta ta sawa kofar key ta dauki pic dinsu ta kifa a kirjinta ta hau rare kuka.
"Anya zan iya kuwa? Zan iya auren wanda ya so auren yar uwata? Kuma har kwanan gobe yake sonta? Anya nayiwa kaina adalci nayiwa yar uwata adalci? Anya idan na yarda na aure sa banci amanar yar uwata ba? Kai inaaa!!! Gaskiya bazan iya auren Yaya Zaidu ba, zanje na sanarwa su Mama ba zan auresa ba" duk maganar zuci take yi tana kuka, har wani ciwon kai ya sauka mata nan bacci mai nauyi ya yi gaba da ita, tare da mafarkin Na'ilah tana ce mata.
"Sismieta!! Yaya Zaidu yana da kirki karki kuskura kice ba za ki auresa ba, idan kika yi haka na yarda baki sona, ki auresa za ki ji dadi zakiyi farin ciki, idan ba ki auresa ba kinci amanata, kuma bamu ni babu ke dan haka kin ga tafiyata!!!" a bacci Hafiza ke mikawa Na'ilah hannu tana "sismieta ki tadawo na amince zan auresa dan Allah karki tafi ki barni" Na'ilah tana b'acewa Hafiza ta farka gami da kwala wa Na'ilah kira da karfi wanda Mama da tazo wucewa zata shiga kitchen ta ji, da sauri ta zo ta hau bugawa Hafiza kofa dan ta tura ta jita a garƙame, da kyar Hafiza ta rarrafa tazo ta budewa Mama kofa, jikinta sai kyarma yake yi gashi duk ta jiƙe da zufa, kuka Hafiza ta saka ta kwanta a jikin Mama tana yi, rarrashinta Mama take yi ba tare da tayi magana ba, dan ta sani har abada Na'ilah ba zata taba fice musu arai ba, Mama ta ce.
"Dama kina daki kina bacci har magriba? Ba dole ki din ga mafarkai ba, idan kinyi mafarkin yar uwarki ki daina mata ihu ki din ga mata addua, yanzu ki tashi ki watsa ruwa kiyi sallar magriba kafin a kira isha'i, anya ma kinyi azahar da la'asar?" ta girgiza alamun aa, "to ki tashi ki yi yanzu ko?" ta amsa da "to" Mama ta fice jikinta a sanyaye dan har an gama maganar bikin Hafiza da Zaid, inda za ayisa nan da kwana goma, ko da Hafiza ta watsa ruwa a daddafe ta yi sallah sabida mugun zazzabin da ya sauko mata, tana kife a wajan akayi isha'i, tana yi ta kwanta ta shige bargo, wajan takwas da rabi ta ji an banko mata kofa ana dariya, ji tayi har da guɗa, cikin zazzabi ta daga ta bude idonta ta kalli su Afnan da Manal da Afrah da Iman, kawayen su Afnan din ne, Afnan ce ta zauna a bakin gadon ta yaye bargon ta ji jikin Hafiza da zafi radauu ta ce.
"Subhanallahi!! Ba ki da lafiya ne? Manal je ki kirawo Mama" da sauri Manal ta fita, Afrah ta ce.
"Tooo daga saka aurenki shine har kin kwanta ciwo?" cikin zafin ciwo da tsananin mamaki Hafiza ta dago tana kallon Afrah ta ce.
"Aure kuma Afrah? Auren wa?"
"Keee! Kina nufin kice bakin an tsaida ranar aurenki yau ba? Nan da kwana goma? Yoo mu fa abun da ya kawo mu kenan mu fara shirye shiryen abun da zamu yi, dan aradun Allah zamu cashe, babu mai faɗa mana muji sai manya" suka sa dariya su na tafawa, yayinda Hafiza ta ji zazzabinta ya ƙaru, da haka Mama ta shigo ta dubata ta ce ko a kaita asibiti ne,amma firrr Hafiza ta ƙi, dan haka aka bata magani, su Afnan suka mata sallama da cewa zasu dawo gobe Allah ya kara sauki, suka fice abun su, su na fita Hafiza ta koma cikin bargo ta ci gaba da rera kukanta, abu goma da ashirin ne suka haɗe mata waje daya.
@@@@
Da washe gari ma haka ta wuni a daki ko parlour ta kasa fitowa ta bangare uku kuwa shirin biki aka fara ba kama kafar yaro, Ubaidullah ya kira KB ya sanar da shi auren Zaidu dan haka ya yi kokari ya ga ya halacci auren, KB ya fadawa Ubaidullah ai idan bai zo auren Zaidu ba, bai cika amini ba, Abba shine ya zama wa su Ubaidullah Uba a komai, ana biki saura kwana biyar KB ya sauka a bauchin yakubu, tun ranar da aka sa bikin Hafiza bata sake ganin Zaidu ba, bata yarda sun hadu ba, shi ma bai nemeta ba, dan ba a natsuwar shi yake ba, bayan KB ya iso nan ya saka Mama dasu Umma a gaba shi ma wallahi ayi masa mata a bauchi, yanzu fa shi kadai ne kawai baya da mata, wallahi zasu saka shi a gaba ne, Inna ta ce.
"Zo nan dan Albarka" dan kuwa jinin KB ya zo daya da Inna, kasancewar KB akwai barkwanci "ina dai mata kake so ko?" KB ya ce.
"Eh Innata, gaskiya nima mata nake so"
"Ma sha Allahu! Nayi maka mata, amma sai kayi hakuri da ita, dan ba jin magana take yi ba" dariya KB ya yi ya ce.
"To Inna wacece?" sai da Inna ta murguda baki ta ce.
"Na baka Ifritu" Zaidu dake zaune kamar ba ya wajan ya ce.
"Inna ki daina batawa ƙanwata suna"
"Yoo to ni ina ruwana da iskancin banza da wofi, jama'a ba zaku dinga saka sunan mutane ba sai na aljanu,kai kam ma naga take takenka, tun da aka saka lokacin aurenka naga kana min wani jiji da kai, ita dai Hafizatun bata fini a komai ba, kuma duk arziki duk tsiya nicevta farko ehe" yawancin yan uwa da ake zaune a wajan dariya ake yi, Zaid ya mike a hankali yabar wajan Inna ta ce "Kabeeru, ina dai ka karbi zabina ko?"
"Ahh sosai ma Inna na karba hannun bibbiyu" da haka shi ma ya tashi.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau ta kama alhamis gobe ne kuma za a daura aure, yau ana ta shirin zuwa Family and friends, Amarya Hafiza tasha kyau dan kuwa Ummi ce ta dauko mai gyaran jiki ta gyarata a kwana goman nan, yau ma kuma Ummin ce ta dauko mai makeup ta fentawa Hafiza fuska tasa kayanta golden color, kawayenta su Afnan kuma sun saka maroon, sunyi kyau sosai su ma, Tun da aka fara hidimar bikin Hafiza Ubaidullah da Abi'atu basu samu zama ba, basu nan basu can, har aka gama shiryawa aka tafi, ana ta neman su Ubaidullah da Abi'atu ba a gansu ba, sai bayan da duk jama'a ana can wajan taro, har an dibi awa daya tukunna ka ji wani kiɗa na musamman na tashi, yayinda maroƙi ke wasa Ubaidullah da Abi'atu, jama'a an zuba ido ana jira aga wasu taurari ne haka ake koɗasu, kamar daga sama sai gasu sun shigo su na dauke ido cikin shiga ta alfarma, farar shadda ce bugaggiya fara sol da ita anyi mata aiki da bakin zare, Ubaidullah ya saka bakin hula da bakin takalmi baƙin agogo kirar gucci, Abi'atu kuma ta yafa bakin gyale bakin takalmi da jaka, sakarta dasu abun hannu da zobe duk bakake ta saka, wayyo jama'a zo ku ga maching iya maching, ihu aka sa ana basu hannu, basu zarce ko ina ba sai wajan ango da amarya, su na isa Zaidu ya mike tsaye suka rungumi juna da Ubaidullah, sannan Abi'atu ta rungume Hafiza wacce kanta ke kasa tun zuwansu wajan ta kasa hada ido da Zaidu kamar yadda shi ma bai kulata ba ko a mota, nan aka ci gaba da event, yayinda hankalin KB ya tashi ya ji shi ma aure kawai yake so, haka akayi taro lafiya aka watse lafiya, da washe gari bayan an sauko daga masallacin jummaa aka daura auren Zaidu da Hafiza in da a yau wasu daga cikin manyan sojoji sun halaccin daurin auren, bayan an daura ne aka wuce reception da yamma aka yi walima, da washe gari kuma aka yi Soldier Day inda jama'a aka yi shigan sojojin har da harba bindiga, taro fa tayi kyau sai dai fatan Allah ya bawa ango da amarya zaman lafiya, Allah ya mai da kowa gida lafiya, haka aka watse da washe gari kuma suka fara shirin komawa barracks dan yau saura kwana biyu su koma, kuma da matan su a can zasu zauna dasu, kamar Hafiza ita ma kam ta tafi kenan.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da dare da sallama ya shigo bedroom dinta, tana tsaye a jikin madubi ta fito wanka daure da towel tana tsane ruwan jikinta da wani karamin towel din dake hannunta, tana ganinsa ta tsorata ta hau rurrufe wani bangare na jikinta,dariya ma ta ba shi, ya tsaya yana ƙyaƙyatawa, cikin tunzura ta ce.
"Me ya kawo ka bedroom dina har kake min dariya? Kuma ko excuse babu?" ta murguda masa baki, takowa gabanta ya fara yi yana cewa.
"Gani nayi na warke naji sauki, shiyasa nazo dan a ramawa kura aniyarta"
"Kamar ya?" ta tambayesa tana ja da baya yana sake matsota.
"Matsalata da yarinya rashin kunya ga uban tsoro kamar farar kura, idan za ki cire wannan tsoron gwanda ki cire dan soja kike aure"
"To sai aka gaya maka tsoronka nake ji ne?"
"Ahh dama ni ai bance kina tsorona ba" ya fizgota jikinsa da karfi, towel dinta ya tsince zai fadi ta riƙe towel din gam ,ihu ta kurma tana kankame jikinta " to ke Madam miye amfanin ihun bayan ba tsorona kike ji ba? Kwantar da hankalinki jarumar mata" ya hau shinshina wuyarta tare da fara sauke mata zafafan kisa-kisai, tun tana mutsu-mutsu har ta hakura ta sake masa jiki, tsayuwar gagararsu tayi, suka zube bisa