COLONEL UBAIDULLAH by Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢

Author :  Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category :  Romance

Chapter   2 / 25

3K to 6K   out of 74.6K words

ga ahalin margayi tsohon Soja Abdullahi galadima.

"Hakan ne ya sa Ubaidullah ya fiye zama a garin Abuja, sai dai ya zo weekend 2days ya koma Abuja bakin aikinsa, dan basu son Ubaidullah yana nesa dasu.

Duk yaƙi ,ko kuma kama yan' ta'adda su Ubaidullah ake turawa.

Shekararsu daya da dawowa daga libya suka sake komawa wani yaƙin, inda aka dinga ɗauki ba'daɗi, da kyar su ka sha kamar ba zasuyi rai ba, amma da ikon Allah suka ci yaƙin, yayin da Ubaidullah shi da Zaidu suka ƙarasa wannan yaƙi a ƙasar. Bayan sun dawo aka gayyatoAlhaji Adamu, inda ya tsaya amatsayin Uba,
aka musu ƙarin girma, inda suka lashe muƙaman *first lieutenant* sannan suka samu kudi.


Ubaidullah ya kawo shawara suka haɗa kudi suka canzawa Alhaji Adamu mota.


Ya ce "a'a yarana kun fini bukatar kudi ,dan haka wallahi na yafe."

Su ka ce "ai ba dan yana da bukata bane kawai dan su faranta masa ne amatsayinsu na 'ya'yansa, dan haka ya karba ya saka musu albarka."

A lokacin ne kuma aka mai dasu *9JA BARRACKS* bayan sun dawo nigeria kenan.

Nan suka hadu da KB kuma suka zama abokai.

Tun da Ubaidullah ya tako kafarsa izuwa 9ja barracks to'fa nan ladies suka sakosa a gaba, amma ko kadan baya ɗaga ido ya kallesu balle yasan dasu.


Gida Ubaidullah ya gina wa mahaifiyarsa mai kyan gaske, inda yanzu a nan suke rayuwa, dan yanzu kudi yana shigo masa, dan first lieutenant ba wasa ba, da ma ance bayan wuya sai dad i,babu wanda yake fata ya mutu a wuya ko a talauci.


Wannan kenan shi ne taƙaicaccan tarihin *First Lieutenant Ubaidullah* wanda a yanzu akayi
masa ƙarin girma ya koma *CAPTAIN UBAIDULLAH*saboda yaƙin da sukaje agarin maiguduri, yayin da da yawan Sojoji sun gudu wasu kuma an kashe su, hatta su Ubaidullah sai da suka sha harbi kafin suka tsira.
Dawowar su da wata biyu shine aka musu ƙarin girma, sannan za'a sake tura su border nan da wata daya, wannan kenan."




___________ *Wasa farin girki*



Gaskiya ba kullum zaku dinga samun littafin nan ba,
Ina barar adduar ku
Ngd ngd ina ƙaunar ku masoya a duk inda ku ke.💖




COMMENTS
&
SHARE

BY MOMYN AHLAN✍🏻🤗
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)



*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻


*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘
____________________
_Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻


_dedicated to my *Fans*_


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*page°°°°5&6*



Da washe gari suka fara fita ƙarin training a wajan commander Victor.


A cikin 2weeks Ubaidullah ya sauke nashi, dan shi baya wasa barin ma a wajan aikinsa na soja.


Ya fito zaije office dinsa suka hadu da Zeey.

sanye take da 3quarter na sojoji da black t-shart tana ganinsa ta taho da gudu tayi tsalle ta ɗaga kafarta,ta kai masa naushi amma ko gizau Ubaidullah bai yiba, yadan gota kadan ,a madadin ta fadi, sai tayi wani juyi ta ɗirko akan kafafunta tana kallonsa tana smiling, tahau bubbuge hannayenta tana cewa wow nyc, that's very good my hero,
that's why I love u always bcox u ar the best, ta karasa maganar tana kashe masa ido daya tana shirin hugging nasa.

Hannu ya ɗaga mata ciƙe da bacin rai ya ce.

Enough Zeey i said enough!
Don't even touch me! ya fada a tsawance rai bace idonsa har sun kaɗa sun kara zama ƙanana.

Ko a jikinta ta ce.

Oh my boo common kai meyasa har yau kaƙi ka waye ne kam?


Mtswwww Zeey u are very stupid oya get out of my way b4 nayi football dake.

Maƙe kafaɗa tayi alamun ko a jikina sannan ta ce.

"Anywhere I don't care about ur manner Ubaidullah , i just know 1 something, ta sake matsosa sosai ta ce kasan miye shi kuwa?"I love you"

U are always in my heart Ubaidullah, bansan adadin son da nake maka ba.

Ta, Gefenta yabi zai wuce yaji an kira sunansa, lumshe ido yayi a hankali ya ce. "Ya salam"

Juyowa yayi yana watsa mata harara ita ma, ba kowa bace fa ce Rumaisa.


A hankali take taku har tazo gabansa , ta ce. "My luv ina zaka je"?

A dan hasale ya ce.

"In'da kika aikeni jiyan nan da banje miki ba shine yanzu nake so naje miki Ma."


Turo baki Rumaisa tayi ta bude baki za tayi magana taji muryan Zeey tana cewa.


"Keeeee!
Dan ubanki waye sa'anki a nan wajan"?

A hankali Rumaisa ta waigo gefenta tana kallonta,kafin ta ce "eh gaskiya banga mate dina a nan ba infact mutane biyu ne a nan wajan"

" Rumaisa and her lover Captain Ubaidullah."

Ji kake

Tass!tass!tass!

Zeey ta faskawa Rumaisa maruka uku a gefe daya.

Kafin kace me dambe ya ƙaraɗe waje.

Ladies barracks ana bawa hammata iska.

Kowacce fada ta keyi cike da kwarewa a salon training din da aka yi mata.


Tsaki Ubaidullah yayi ya wuce gaba yana cewa karnuka kawai.


Yana gaf da shiga office dinsa yaji ana kiransa a baya.

Sir!Sir!Sir.

A hankali ya juyo ya ce.

What's wrong sergeant?

Sergeant ya ce.
Sir, "Major Usman ne ya ce na ce maka kaje , guardroom domin tambayar wani mai laifi an tambayesa yaƙi fadi."

Okay, ina Captain Zaidu? and First lieutenant K,B?

Sergeant ya ce Sir,
"Major General ya aikesu Murtala Barracks."

Okay kawai Ubaidullah ya ce sannan ya juya,ya dauki hanyar guardroom.


Yana isa guadroom ya samu wanda ake tuhuma da laifin yiwa yarinya yar 8yrs old fyade ana tuhumarsa amma ya kafe ya ce ba shi bane,ya aikata ,bayan shaidu sun tabbatar shi din ne.

Yana ganin Ubaidullah yaji gabansa ya fadi ganin fuskarsa babu alamun dariya

Ubaidullah ya ce.

Private first class?
Ya amsa ya shigo da sauri yana cewa "yes Sir"

Ubaidullah ya ce.
"Jeka kawo min kayan aikina"

Da sauri ya fita ko 4mnts bai yiba yadawo da sauri hannunsa dauke da ruwa jikin bucket da wayar wuta, ya a jiye, ya juya zai fita

Ubaidullah ya ce.

"Make sure ka rufe kofar nan da kyau."

Private first class ya ce "ok sir"

Kallonsa Ubaidullah keyi na yan wasu lokaci kafin ya sake rikiɗewa,alluran sojarsa ta miƙe dan shi a rayuwa idan akwai abin da yafi tsana a duniya,to ace anyiwa yarinya ko budurwa fyade.

Ba tare da bata lokaci ba,ko yin magana, ya dauki ruwan bucket din nan ya watsa masa rabi,sannan ya ɗauki wayar wutan ya fizge bakin ya jona masa shocking ,yaja table ya zauna yana kallonsa.

Nan mai laifi ya fara diskon dole ,yayinda babu in'da bata jijjiga a jikinsa

Sai da yaga ya kusan sumewa kafin ya ɗauki babbar maduki ya bugesa dashi ya fadi bakinsa harta koma gefe.


Captain Ubaidullah
ya durƙusa a gabansa fuskarsa tamƙe tamau( wai soja mala'ikun duniya) naushi daya ya kai masa a baki take haƙorin mutumin guda biyu suka faɗi ƙasa,Ubaidullah yasa hannu ya ɗauka , ya damƙa masa a hannunsa,idanunsa sun ƙara ƙanƙancewa.

Ya ce.

"Ka faɗa min gaskiya kaine kayiwa yarinyar nan fyaɗe"! a tsawance yayi maganar.

"Idan kuma kasan ba gaskiya zaka fada min ba, to ina baka shawara daka ja min tsummar bakin ka kayi shuru if not wallahi humm zaka sake ganin ainihin true color din Ubaidullah."

Cikin sarƙewar murya ya ce. "Yallabai kayi hakuri ni ne na aikata."

Ran Ubaidullah ya sake baci ya rufesa da duka, sai da yayi masa jina-jina, kafin ya fita yana huci.


Direct office din Major Usman ya wuce ransa bace, ƙananun Sojoji sai sara masa su keyi.

Ya shiga ya ƙame yana sara masa "Sir mai laifi yayi jawabi ya amsa laifinsa."

"Nyc job Ubaidullah keep it up Ina alfahari da kai, you can go."

Ubaidullah ya sake sara masa kafin ya juya ya fice.

ya tafi office dinsa yana zama kamar da 10mints sai ga su Zaidu, da K,B sunyi sallama ya basu damar shigowa, hannu suka bawa juna su kayi musabaha.


Zaidu ya ce.
Captain Ubaidu how is work?

Smiling yayi " we tnk god Captain Zaidu and u?

Zaidu ya ce.
"Alhamdulillah"

K,B ya ce.

"To abun kuma ƙi dangi ne"?

Ubaidullah ya ce.
"Menene kuma ƙi dangi"?

"Ah to ba dole na ce ƙi dangi ba, naga ni yau ba ayi niyyar yimin magana ba, ba'a kulani ba"

Gaba'ɗaya suka kwashe da dariya,Ubaidullah ya ce.

"Wallahi Allah ya shiryeka K,B yau kuma sharri kake ji dashi zaka ce na ƙi kulaka"?

K,B yana dariya ya ce.

"Ah to ba gashi yanzu na saka ka dariya ba, dama bana so naga ka haɗe rai sosai din nan."

Ubaidullah ya ce.

" ai ba a san soja da dariya ba"

Zaidu ya ce.

"Yes of course , ba'asan soja da dariya ba but today you look very sad what's wrong my dude"?


Ubaidullah ya numfasa yana jan iska mai zafin gaske yana fuzarwa,zuciyarsa yana masa soya.

Ya ce.

"Wallahi a rayuwata na tsani naji kalmar an'yiwa mace yarinya ko budurwa fyade, dazu an saka wani yaro matashi a gurdroom ana tuhumarsa da laifin yiwa yarinya, yar' 8yrs old fyade, dan rashin kunya ana tambayarsa ya kafe ya ce ba shi ya aikata ba, shine Major yasa naje na tambayesa, ina zuwa na jona masa shocking nan take yake gayamin akan cewa shi ya aikata, wallahi har yan zu abin yaƙi fita raina."

Zaidu ya numfasa ya ce.

"Naji case din tun jiya ake zarginsa yaƙi magana, ashe kai kana zuwa ya ƙoro maka jawabi"?

Ubaidullah yayi tsaki ba tare da ya kuma yin magana ba, illa Zaidu da K,B da suke jajinta lamarin, amma shi kam tunani ya keyi yanda za'abi a magance yiwa yan'mata da yara fyade a wannan zamanin ,dan yanzu abun ya zama ruwan dare, bata ya'ya' mata ta hanyar rabasu da budurcinsu, yana ta faman thinking about this matter, har su Zaidu suka yi masa sallama suka tafi office dinsu.


Da washe gari

Ubaidullah da Zaidu, suka shirya zuwa office din General Of The Army domin neman permission, zasu tafi ganin gida b4 suje in'da aka turasu kama yan'ta'adda, wato border.


Har office suka je amma yau general of the army bai zo office ba,nan ake shaida musu yau bai fito gida ba, dan haka suka juya suka fita.

Zaidu ya ce.

"Ubaidu muje gidansa kaga lokaci yana ƙure mana kuma kasan halin general, amma ya kace."?

Tsaki Ubaidullah yayi sannan ya ce."okay muje amma gaskiya ba son zuwa nake yiba"

Zaidu ya ce.

"Na sani ai"


Sunyi tafiya mai ɗan tsayi kafin su ƙaraso,gate din gidan General Of The Army,wanda duk inda ka wulla idanunka sojoji ne, ana ganinsu Ubaidullah aka ware musu gate ana sara musu, *CAPTAIN UBAIDULLAH & CAPTAIN ZAIDU*.

har suka karasa bakin kofa wani soja ya bude musu yana sara musu gami da cewa " wlcm sir Ubaidullah and sir Zaidu"

Zaidu ne ka dai yake amsawa , amma Ubaidullah sai dai ya jinjina kai da kar yake kallon kowa a barracks yasan wa inda suke sonsa da wanda basu sonsa.

A parlour sukayi sallama

Wata haɗaɗdiyar mata ce ta sauko daga kan step tana taku cike da izza da nuna isa da gadara ,kayan dake jikinta ma abun kallo ne, daka ganta kasan iyayi ya zauna ko ba a fada maka ba.

Humm, *HAJIYA JAMILA KENAN MATAR GENERAL OF THE ARMY ABDULKARIM*.

mata mai jida kanta gami da alfahari da nuna ita watace.

Tana karasowa su Ubaidullah suka sara mata su na gaisheta , sai da ta dauki som minutes kafin ta amsa.

Ubaidullah bai ce komai ba, Zaidu ne ya ce. "Madam Oga sir muke nema"

A hankali ta kira sunan yar'ta cike da yanga.


Hanan!Hanan!Hanan!

Wata yar budurwar yarinya mai ƙarancin shekaru dan ba zata gasa 17yrs ba ta fito tana yatsine fuska tana binsu Ubaidullah da kallon banza.

Hajiya Jamila ta ce.

"Hanan je ki cewa dadynki yaransa su na nemansa, turo baki tayi tana ƙunƙuni ta juya ta haura upstairs din daddynta, kamar da minti bakwai suka sauƙo tare.

Yana ganinsu yayi murmushi ya ce.

"Ah Captain Ubaidullah and Captain Zaidullah I hope dai everything is fyn,na ganku at this tym"?


Sara masa suka yi kafin suka haɗa baki wajan cewa "yes sir everything is fyn Alhamdulillah mun zo neman permission ne, b4 mu tafi border muna so muje gida."


General ya ce.

"Okay no problem kuna iya tafiya next 2morrow"

Godiya suka yi sannan suka miƙe zasu tafi har sun kai bakin kofa ,general ya ce.

Hope ba daɗewa zakuyi ba?

Zaidu ya ce.

"Eh sir 5days ne kawai"

Jinjina musu kai yayi sannan suka fice ,Hanan sai kallon Ubaidullah takeyi tasan tana da ji da kai da girman kai amma bisa alama Ubaidullah zai fita zafi ,duk da ta yi musu kallon banza amma taji wani abu aranta akan Ubaidullah.


******agurguje

Yau ne su Ubaidullah zasu je ganin gida sun shirya tsaf K,B ya ce.

"Wallahi da nasani dana tambaya na biku amma nasan halin general yanzu kam ba zai barni ba"

Zaidu ya kwashe da dariya ya ce.

"Sunan ka sorry kawai"
bye bye sai mun dawo, K,B ya kai masa dukan wasa ya kauce yana dariya ,a tare suka fito ya rakosu har mota suka shiga yana ɗaga musu hannu suka fice daga barracks , suka ɗauki hanyar garin *BAUCHI STATE*.....



~~~~~~~~

SAI FA HAKURI😢 MY FANS INA BUKATAR ADDUARKU AKAN WANNAN LITTAFIN DAN WLH TYPING ...YANA BANI WUYA




COMMENTS
&
SHARE


BY MOMYN AHLAN✍🏻👮🏻‍♀
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)



*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻


*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~~•~~
*MARUBUCIYAR*

( *HALITTA DAGA ALLAH NE*)
( *GUDU A JEJI*)
( *SHUHADA*)
( *NIDA ƘANNAN MIJINA*)
TYPING...( *WA'YA KASHE ZAHRA'U?*) *#200*

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘
____________________
_Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*page°°°°7&8*


Su na shiga garin Bauchi Ubaidullah ya jinginu da sit ya lumshe ido yana shaƙar ƙamshin garinsa, da shike yanzu Zaidu ne ke driving din motar, dan bayan sun tsaya a jos suka yi sallah Zaidu ya karbi driving din kasancewar Ubaidullah ne ya ja su daga Abuja to jos, shi kuma Zaidu ya ja su har garin Bauchi.

Dukkan su sun yi shuru babu mai magana wa dan uwansa, ko wannen su da abun da yake tunani.


Ubaidullah sai cool smiling yake saukewa a beautiful face dinsa , ga wani happiness da yake ciki.
Zaidu ne ya ƙatse shurun ta hanyar cewa.

"Ubaidullah dan Allah zan fara sauƙa a gida"

"Okay Captain Zaidu tun da kasan ni ai ban yi missing din gida ba, kai ne kayi missing,mtsww"

"Oh Allah, Ubaidu Allah ya shirye ka, ni fa ba wani abu nake nufi ba, kaga motar ka ce, ni kuma wallahi a gajiye nake ba zan iya mu fara zuwa gidanku ba, ka bar ni da wangale baki"

"Kai dai kasani," cewar Ubaidullah.

Har suka shiga sabon unguwarsu mai suna jahun, sai da Zaidu ya sauƙa tukunna Ubaidullah ya koma mazaunin driver yana shirin yiwa motar wuta, Zaidu ya ce.

"Ba za ka shigo ku gaisa da su Umma da Inna ba? iwarhaka na san baba ba ya gida."

Ba tare da yabawa Zaidu amsa ba ya fito yayi gaba Zaidu yana binsa a baya da jakarsa da ya rataya ta a kafadarsa.

Tura kofar suka yi su na sallama Umma (mahaifiyar Zaidu) ta ce ."ah maraban ku oyoyo mazan fama"

Kakarsu Zaidu (ta wajen Uba)ta miƙe da sauri har tana tuntube zaninta ya kunce amma ba ta bi ta kansa ba tana cewa .

"Oyoyo, oyoyo mugun mai gida sannu da zuwa mugu oyoyo mugu,ta zo za ta rungumesa, sai kuma ta fasa,Zaidu ya ce.

"Ah Inna me ya faru kuma, kin fasa oyoyo din ne"?

"Mtsww oho maka kuma ban sani ba sau nawa zan fada maka idan zaka zo ka daina zuwa da wannan kayan naku ( *kakin sojoji*) haba idan mutum ya kallesu sai zuciyarsa ta tsinke ai wannnan mugunta ne da rashin imani,ga shi yanzu kasa ina jin zawo, ta fada ta juya tana kan mita ,ai gwanda ma kai kana dariya akan wannan abokin naka mai fuskar zaki " ta shige daki.

Ubaidullah ya yi murmushi ya duƙa ya gaishe da Umma ta amsa cike da kulawa ƙannan Zaidu suka gaishesa tare da yi musu sannu da zuwa, Ubaidullah ya miƙe yana yiwa Umma sallama a kan cewa zai wuce gida.

Umma ta ce.

"Ah Ubaidu har za ka tafi gida ka tsaya kaci abinci mana "

" a'a Umma na gode na gaji ne ba na so na zauna ne kar na kasa tashi a kan lokaci ,dan wallahi bacci nake ji"

Umma ta ce.

Ai dole ku ji bacci kullum ana abu daya Allah dai ya kare mana ku"
Suka amsa da ameen

Ya juya zai fita, Zaidu ya bi bayansa ,ya ce" to kai kuma ina zaka je da ka wani rakoni a baya "?

Dariya Zaidu yayi
"Wallahi Ubaidu kai dai ba'a yi maka gwaninta wai fa zan dan taka maka ne"?

"No I don't needed tnx," ya fada yana wucewa gaba.

Zaidu ya ce.

"Ok ka gaishe min da mama kafin na shigo an jima"

"Ok za ta ji sai ka zo"

Zaidu ya juya ya koma cikin gida, daidai nan Inna ta fito tana yarfe zani tana riƙe ciki, Zaidu ya ce. "Subhanallah matar meya faru"!

"Uwarka ce ta faru mugu kawai idan kana so na kula ka , ka je ka cire wannan kayan naka sai ka zo mu yi gaisuwa, " ta fada tana murguda baki Zaidu ya kwashe da dariya,Umma ta hararesa ta ce.
"Ka fa dawo kenan ko? za ka fara saka Inna ciwon baki? to wallahi ba zan lamunta ba ka shige bangarenka."

Zaidu yana dariya ya ce. "To shikenan Inna kwantar da hankalin ki na tafi"

"Eh din na ji je ka mana, kar Allah ya sa ka dawo idan kaga dama, kafi ruwa tafiya"


2 / 25