Author : Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category : Romance
danneta mazan da suka hau kanta zasu kai biyar and she's to young ace maza biyar sun danneta a lokaci ɗaya gata virgin ce, babbar mace ko a first nyt tana shan wahala tun da ranar da aka fara buɗata kenan, namiji ɗaya, to balle ita wannan yarinya ce karama, kuma da karfi suka shigeta, duk sun dagargaza mat....." maganar da Ubaidullah bai jira likita ya karasa ba ya saki ihu ya kwanta kasa yana birgima.
Da sauri Abba da Safwan suka yo kansa, kuka yake yana toshe kunnuwansa dan ji yake sun gaza daukar jawabin likita.
Da kyar Abba da Safwan da likita suka ɗago Ubaidullah wanda duk ilahirin jikinsa rawa take ga jijiyoyin jikinsa da suka miƙe a tsaye kiƙam kana ganin su zara-zara, Abba ya share hawaye ya ce.
"Doctor yanzu miye abun yi"
Girgiza kai yayi ya ce.
"Gaskiya bazan boye muku ba, mu munyi iya yinmu sai kuma ta Allah" doctor yana gama fadi ya fice.
Haka suka tashi Abba yana riƙe da Ubaidullah, room din suka shiga tana kwance an rufeta da farin yadin asibiti fuskarta ce kawai a buɗe, wajan kasanta kuma an saka mata wani abu an rufe wajan dashi, kasa jurewa Mama tayi ta juya ta fice tana kuka.
Ubaidullah ne ya karasa jikin gadon ya kamo hannunta ya fara magana da muryarsa da bata fita.
"Na roƙe ki kanwata ki tashi ki faɗamin suwaye suka miki! " wata norse ce ta shigo ta ce musu.
"Pls ban da hayaniya dan anyi mata alluran hutu" tana gama faɗi ta fice abunta.
Umma da Inna da Ummi suka fice, suka yi dakin da aka kwantar da Hafiza, itama an ɗaura mata ruwa, anan suka zauna aka bar Ubaidullah da Abi'atu Anty Ummu da Abba da Safwan, Abba ya ce.
"Ɗana ku zo muje gida idan yaso mu kawo abun bukata" girgiza kai Yayi alamun A'a baza shi ba, babu yanda Abba bai yiba amma Ubaidullah ya ƙi sam, Abi'atu ma tazo suje ita ma tace sam ba zata je ba, haka Abba da Safwan suka baro asibitin da sunan zasu dawo da asuba.
Haka suka zauna cirko-cirko abinci kuwa babu wanda yayi tunaninta ko ya bi ta kanta.
Da asuba da kyar Ubaidullah ya tashi ya tafi masallaci, itama Abi'atu da Anty Ummu suka nufi dakin da aka kwantar da Hafiza nan sukayi Sallar asuba aka ɗan gaggaisa sama-sama.
Ubaidullah ya dawo kenan daga masallaci zai shiga ya duba Hafiza sai yaji yo ihun Na'ila da karfi take furta kalmar.
"Innalillahi wainna ilayhirrajiun!innalillahi wainna ilayhirrajun! Innalillahi wainna ilayhirrajiun! Yayana!! Mamana!! Hafizata!! Anty Ummuna!! zasu kashe! zan mutu! Wayyoo Anty Abi'atu! Innalillahi wainna ilayhirrajiun!!""
Da mugun gudu Ubaidullah yayi dakin da Na'ila ke zunduma ihu ,
Duk da ihun muryarta a dashe yake, ga wani baƙin azaban da take ji yana tashi a kasanta tamƙar ana hura mata wutar dalma.
A ɗari da saba'in Ubaidullah ya shigo ɗakin ya ɗagota cikin ɗimauta ya hau mata magana.
"Kan..kanwata! Gani gani! Gani a kusa dake" Mama da Anty Ummu matsowa sukayi suka kama hannunta gam.
Sai juyin azaba take a jikin Yayanta, tambayarta ya kuma akan cewa su waye suka aikata mata haka, amma azaban da take ji ya hanata magana.
Cikin dauriya da fizgar magana ta fara magana.
"Mam..Mamana..ina Hafizata?" kasa bata amsa akayi ta ci gaba da magana, tana fizge-fizgen azaba.
"Mama dan Allah ki yafe min duk abun da na miki Anty Ummu kema ki yafe min, Yayana kaima ka yafe min, Yaya su bakwai ne suka kamani suk....."maganar da Na'ila bata karasa ba kenan ta koma fizgan kalman shahada a bakinta.
Gabaki ɗayan su sun ruɗe da gudu Anty Ummu da Abi'atu suka fita neman likita, zuwa wani lokaci kuma tayi ɗiff ta daina murkususu da fizge-fizgen kamar cutar ya lafa mata.
A kiɗime likita dasu Anty Ummu suka shigo, nan doctor ya hau dubata ya gama tattabata sannan ya jawo farin yadin ya rufe mata fuska ya ce.
"Sai dai fa kuyi hakuri amma yanzu kam ta cika, ta amsa kiran mahaliccinta"
Mama ta kalli hannunta wanda suke sarƙame dana Na'ila ta riƙe gam, doctor yasa hannu ya raba hannun Mama da na Na'ila, tangal-tangal Mama tayi baya ta zube sharab a kasa Umma tayi kanta da sauri, yayinda Abi'atu ta kwalla karan da yayi dai-dai da isowarsu Abba da Safwan.
Ubaidullah tamkar almara yake ganin Abun,ihu ya saka gami da cewa.
"Haba Na'ila!! Haba Na'ila! Ya zaki min haka? Baki fa fadamin suwaye ba? Dan Allah ki tashi Kanwata!?Kanwata!?Kanwata!? Ki tashi kince su bakwai ne suwaye bakwai din!?" Da karfi yake magana yana jijjigata, su Abba da Safwan da kyar suka b'anb'are Ubaidullah daga jikin gawar Na'ila nan ya hau buge-buge, wannan shi ake kira tashin hankali wanda ba a sa masa rana, mutuwa kuwa bata sallama da lokaci yayi sai tafiya.
💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
ALHAMDULILLAH AM BACK MY FANS PLS KARKU BANI KUNYA, YADDA KUKAYI ALKAWARI TO KARKU KARYATA.
LATE COMER INA TAYAMU MURNAR ZAGAYOWAR SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEEN AMMA BA IRINTA 2020 BA.
ALLAH KUMA YASA IDAN KUKA KARANTA KUNA MIN SHARING DINSA.
ALLAH YABAR SO DA KAUNA MY PPLS
ZAHRA ABDUL
MOMYN AHLAN
TAKU CE😁
[8/19, 10:57 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)
*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻
*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻
_dedicated to my brother_
*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~
_my wattpab_@Fateemah0
_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*page°°°°°41&45*
Da kyar Abba ya jawo Ubaidullah suka fita haraban wajen asibitin, Abba ya ɗaga waya ya kira Malam Liman, na unguwar tasu yake sanar dashi akan cewa yarinyar ta cika,Allah ya mata rasuwa, Abba yana gama faɗawa Malam Liman ya kira wasu Aminansa ya ce dan Allah su zo da mota babbar asibitin Specialist za a dauki gawa ne.
Ubaidullah na tsaye lokaci guda ya nemi hawayen dake zuba a idonsa ya rasa, idonsa ya ƙafe babu ruwan hawaye, ajiyar zuciya ya koma saukewa ba ƙaƙƙautawa.
A can ciki kuwa Inna da Ummi sune suka kamo Mama sukayi waje da ita, yayinda Umma ta kama Anty Ummu da Abi'atu tayi waje dasu su ma.
Abokan Abba sun zo su uku da manyan motaci guda Uku da mutane biyar, nan aka tsaya maganar sa hannu a bada gawar Na'ila dan aje gida a mata sutura a kaita gidanta na gaskiya.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da misalin karfe bakwai da rabi na safe.
Tsaye suke sanye da kakin sojoji a jikin su, Zaidu sai jeka ka dawo yake yi ya kasa zama sai trying din numbern Ubaidullah yake amma yanzu kwata-kwata wayar bata shiga switch up ake ce masa, cike da damuwa gami da faduwar gaba ya ɗago suka hada ido da KB ya ce.
"KB har yanzu fa Ubaidullah shuru anya lafiya kuwa? Gaskiya ni jikina baya bani lafiya, rabon da muyi magana dashi tun da ya ce min ya kusan shiga bauchi I told he will call me so that ya sanar dani cewa ya isa lafiya, but shuru fa" ya karasa maganar kamar zaiyi kuka, KB ya ce.
"Gaskiya nima jikina yana bani ba lafiya ba, jiya na dauka gajiyar hanya ce ta sashi mantawa damu shiyasa bai kira mu ba, amma kuma Ubaidullah baya makara wajan sallarh asuba,kuma baya rabuwa da wayarsa a kusa dashi, kuma da asuba din nida kai duk mun kirasa bai ɗaga ba, gaskiya ya kamata ka kira Umma ka tambayeta tunda itama Mama ka kira bata ɗaga ba, gaskiya bana tunanin akwai lafiya"
Zaidu ya ce.
"To taya Umma zata sani? Ko da yake bari na kiranta idan yaso saita aiki Afnan da Manal su je su gani ko lafiya" Zaidu ya hau dealing din Numbern Mamansa, cikin sa'a kuwa a lokacin ita wayar yana hannnunta su na tsaye a waja ana jira Doctor yazo yasa hannu a bada gawar Na'ila, ta ji wayarta na neman agaji, tana dubawa ta ga Zaidu ne ke kiranta, ita tama manta da kiransa shakaf ta fada masa abun da ke faruwa, inama aka ga natsuwar kiraye-kirayen.
A lokacin Anty Ummu tana rungume a jikin Umma ita da Abi'atu su na Kuka mai ban tausayi, Umma ta dan ɗaga kansu ta tashi ta koma gefe tana sharbe hawaye da hijabinta kafin tayi karfin halin ɗaga wayar Zaidu.
Sallama ya mata ta amsa, a yanda yaji muryarta nan take ƙirjinsa ya bada dam!dam!dam, cikin damuwa ya ce.
"Umma lafiya kuwa? Ya naji muryarki kamar kina kuka meya faru? Dan Allah Umma ki fada min meke faruwa,haka kawai naji jikina yana bani gida ba lafiya ba, jiya Ubaidullah ya taho bauchi inata kiran wayarsa bai ɗaga ba yanzu kuma bata shiga, harta Mama na kirata bata ɗaga ba, yanzu kuma na kira ki naji muryarki kamar kina kuka dan Allah Umma meke faruwa?" ya karasa maganar kamar zaiyi kuka.
Duk yadda Umma taso ta daure karta yi abun da zaisa Zaidu ya gane amma ta kasa, bata san lokacin da wani sabon kuka ya b'arke mata ba, cikin kuka ta ce.
"Zaidu, duk abun da kakeyi ka ajiyeta ka taho bauchi yau din nan kuma a yanzu, Zaidu babu lafiya,Zaidu ba kalau ba, Zaidu Mama ba zata iya daga waya ba, na tabbata bata san ma inda wayar take ba, Zaidu Abokinka yana cikin babbar damuwa da tashin hankali,Zaidu *NA'ILA TA RASU!! NA'ILA TA RASU!!* Zaidu" Umma ta sake fashewa da kuka.
Zaidu bai san lokacin da wayar dake kunnnansa ta fado kasa ba, ya zube a kasa ji yake kamar mafarki yake yi, gabaki ɗaya wani duhu ne ya ziyarci kwakwalwarsa da idanunsa, ganin haka yasa KB saurin ɗaukar wayar yasa a kunnansa, banda shashshekar kuka babu abin da yake ji na tashi, cikin tashin hankali KB ya ce.
"Umma lafiya kuwa me yake faruwa ne?"
Cikin kuka Umma ta ce.
"Rasuwa aka yi ƙanwar abokin ku ce ta rasu, yau da safen nan ta cika a asibiti yanzu haka ma muna asibitin muna jira Likita yazo yasa hannu abamu gawarta muje gida, idan da hali dan Allah ɗana ku taho yanzun nan ku samu jana'izarta , ka taimakawa Zaidu dan nasan yanzu ba zai iya wani ƙwakƙwarar motsi ba" tana gama fadi ta ajiye wayar dan tasan da maganar Zaidu na cewa yana son Na'ila zai jirata ya aureta.
Kallon tausayi KB ya hau bin Zaidu dashi ganin yadda ya zube a kasa kamar ba shi ba, tunani KB ya hauyi yanzu ace zasu tafi a mota ai ba zasu samu jana'izar ba, "yanzu miye abun yi?" ya tambayi kansa, nan take ya fice da sauri har yana tuntube.
KB bai zarce ko ina ba sai gidan General of the army, dan ma shine yasa aka barsa ya shiga.
Nan ya samu ganin General Of The Army yake faɗa masa abun da ya faru, duk da yana jin haushin abun da Ubaidullah yayi na barin aiki amma bashi ya hana General jajantawa ba, KB ya ce.
"Sir, nazo neman permission ne zamu tafi bauchi yanzu saboda mu samu jana'izar"
"Taya zaku ce zaku tafi bayan kunsan yau akwai meeting ? Wanda ya mutu ai ya mutu Allah ya jikanta, but babu inda zaku je, ina shi Zaidun yake?"
Wani kallon rashin imani KB ya bi General dashi kafin ya ce.
"Zaidu yana can a ɗaki baya cikin hayyacinsa"
General zai sake magana yaji muryar matarsa Hajiya Jameela tana cewa.
"Allah ya jikanta amma dole sai kun bisa ne, wai ma ba jiya shi yabar aikin ba?"
Kafin General yayi magana sai suka ji muryar ƴarsu Hanan.
"Haba Daddy!? Haba Daddy!? Anya Daddy akwai imani kuwa a ranka?" ta fashe da kuka lokaci ɗaya, ta ci gaba da magana.
"Daddy ka sha yabon Captain Ubaidullah a lokacin da yake saɗaukar da rayuwarsa domin ya ɗaga darajarka, dan kaddarar sharri ta gitta masa? Wanda duk idanuwan ku suka rufe ku ka kasa fahimtarsa? Na ɗauka kowa a barracks din nan ya fahimci halin Ubaidullah ashe duk ba haka bane, shi da ko maza baya kulawa taya zai kula wannan kuchakar kauyen Rumaisa? Yarinyar da ko class bata dashi,gudun wulakanci ya saka shi ajiye aikinsa duk da so da kaunar da yake yiwa aikinsa, yanzu kuma ance kanwarsa ta rasu zasu je Daddy kace ba zasu je ba, to wlh sai sunje idan kuma kana neman daƙushewar wannan barracks din nan Daddy bismillah ga hanya nan, amma tafiya dole sai sunje ni ma kuma zan bisu!"
Tana gama faɗi ta haura sama aka bar General da matarsa baki sake su na kallon yarinyar tasu, juyowa General yayi ya kalli KB, KB ya sara masa ya juya ya fice ,komai ta fanjama fanjam, dan yaji zuciyarsa ta ƙiƙashe shima.
Part dinsu ya koma ya samu Zaidu zube a kasa yanda ya barshi.
Basu wani tsaya daukar kaya ba, KB ne dai ya sauya kayansa daga kaki zuwa kayan gida riga da wando, amma Zaidu ya kasa wannan, sun fito kenan sai ga wani sergeant da sako daga wajan ɗiyar General Of The Army.
Karban Sakon KB yayi ya duba yaga ashe latter ne tayi rubutu kamar haka.
" _KB Daddy ya hanani fita karshe ma yasa sojoji tare ni, amma kuje filin jirgi yanzu na siya mana sit mu uku jirgin zata tashi nan da 1hr, tsakanin Abuja da Bauchi indai a jirgi ne 2hrs ne kawai dan haka ku tafi yanzu na bawa Zeey tawa kujerar In sha Allah zaku samu jana'izar na kira Zeey na faɗa mata, yanzu Sergeant Montie zai kai Ku airport ku hanzarta pls_"
KB yana gama karanta sakon yayi murmushi gami da cewa.
"Allah ya biya ki Hanan, harka da ƴaƴan manya akwai dadi, komai nasu a saukake"
KB ya juya zai yiwa Zaidu magana sai ga Zeey kamar an wullota, cikin tashin hankali ta ce.
"Yanzu Hanan take faɗa min mummunar labari"
KB ya ce.
" muje dai yanzu tukunna kar mu makara"
Mota suka shiga Sergeant Montie ya dauki hanyar airport.
Zaidu tun da Umma ta ce masa *NA'ILA TA RASU* ya kasa banbance yana duniya ne ko akasin haka, burinsa kawai yaje yaga karya ne Lovely dinsa tana nan.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sai wajan karfe tara kafin aka samu Doctor ya zo yasa hannu aka bada gawar Na'ila.
Ubaidullah na tsaye aka fito ana tura gawarta, ganin abun yake kamar shirin film, har aka sakata a daya daga cikin motar Abokan Abba wasu mutum biyu daga cikin mutanen da suka zo, sune zasu ja motar Ubaidullah da wanda Abba da Safwan suka taho dashi.
Bayan an gama komai Inna ta ce ita zata zauna da Hafiza, su wuce kawai, haka kuwa akayi har sun fita sun fara jan Mota Hafiza ta farka a haukace drip din da aka daura mata ta fizge shi ta diro daga kan gadon.
Da mugun gudu ta dauki hanyar wajan asibiti tana ihu tana cewa.
"Wayyo Allah na Na'ilata!! Wayyoo Allah yar Uwata! Ina Yar Uwata!? Wayyo zan mutu!"
Da gudu Inna ta bi bayanta a lokacin motar su Ubaidullah ne bai kai ga barin asibitin ba, amma har sun bata wuta, yana cikin motar yaji ihun kanwarsa da sauri ya fito.
Can ya hangota kuwa tana gudu tana ihu bata ma san inda zata je ba.
Inna tana cewa.
"Dan Allah yan uwa ku taimaka min ku riƙe min ita" wasu kuma sun ƙi riƙeta ne dan sun dauka mahaukaciya ce.
Da mugu Ubaidullah ya taro kanwarsa tana ganinsa ta sake rushewa da Kuka, jawota jikinsa yayi yana bubbuga bayanta sannan suka jira Inna ta karaso wajan suka shiga mota sai gida.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Unguwar su Ubaidullah kamar an buga tambari haka jama'a suka cika har ba matsaka tsinke, saboda lokacin da Abba ya kira Malam Liman ya faɗa masa yarinyar ta rasu, shi kuma ya fadawa Jama'ar unguwa shiyasa kafin su iso unguwar ta cika da mutane, barin ma Na'ila da take da jama'a saboda gagararta ta shiga nan ta fita can, ga hidima da jama'a shiyasa nan da nan jama'a suka cika layin unguwar tasu.
Da kyar aka samu aka wuce bayan an wangale gate din gidan gabaki ɗaya.
Direct aka wuce da gawar Na'ila ɗakin Mama domin ayi mata wanka.
Lokaci ɗaya Mama ta nemi kukan da ke idonta ta rasasu ,ji take idon ya bushe ƙamas, tana zaune a gefen gawar , su Umma da Ummi(mahaifiyar su Abi'atu) suka shigo da ruwan zafi wanda za'ayiwa Na'ila wanka dashi suka ajiye, suka dubi Mama wacce ta kafe Na'ila da ido ko giftawa bata yi, Umma tazo ta zauna kusa da Mama ta dafata ta ce.
"Mama dan Allah kiyi hakuri, ki tashi ki fita, zamu wanketa nida Maman Safwan"
Girgiza kai Mama ta shiga yi gami da cewa.
" A'a Umma zan tsaya na yiwa ƴata wanka dan muyi sallamar karshe, ku zo muyi mata kawai, zan wanke ƴata, kin gani ko Umma jiya iwarhaka ina tare da ƴata wasa da dariya amma wai yau gata nan kwance a gabana ina so nace mata ina sonki ƴata ko da sau ɗaya ne ta bani amsa amma ina hakan ba zai yu ba, jiya har faɗa sai da nayi mata ashe duniyar ma gabaki ɗaya zata tafi ta bar min, Umma kin ganta kalli fa ki gani kamar bata mutu ba ko zamu koma asibitin ne a sake duba min ita?"
Mama ta karasa maganar tana duban Umma.
Duk yadda Umma ta so daurewa amma ina ta kasa, sai da Mama ta bata tausayi ta fashe da kuka, itama Ummi hawayen take yi kafin tayi karfin halin cewa.
"Dan Allah kuzo mu suturta yarinyar nan a kaita makwancinta,Dan Allah Mama kisawa zuciyarki salama, kiyi dangana, kiyi tawakkali, ki dauki wannan kaddarar,ki ta nanata kalmar INNALILLAHI WA INNA ILAYHIRRAJIUN! a cikin zuciyarki Dan Allah!" ita ma ta karasa maganar tana sake share hawayen da suka kasa tsayuwa a idonta, Mama ta ce.
"To" a sanyaye.
Nan suka yiwa Na'ila wanka amma Mama ta kasa tsayawa a shirya Na'ila, dan haka Ummi tayi waje da ita, wani bedroom wanda yake kusa da nasu Na'ilan nan aka saka Mama a ciki ,Mutane sai dannarta suke suna bata hakuri, amma sai dai ta ce.
"Uhummm"
Dan ji take Numfashinta ya fara Of and down.
Hafiza kuwa bayan sun iso gida Inna tana tare da Ita a dakin su, dasu Anty Ummu, Abi'atu, Afnan Manal, sai kuka suke yi, Anty Ummu na zaune bata um bata um um,Hafiza kuwa ta raku'be a jikin Inna jikinta sai rawa yake yi.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Karfe goma da rabi jirgin