COLONEL UBAIDULLAH by Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢

Author :  Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category :  Romance

Chapter   20 / 25

57K to 60K   out of 74.6K words

saurin toshe mata bakin ta hanyar haɗewa da nasa yana tsotsa cike da salon kauna wanda bata taba tsammanin hakan daga garesa ba, take ta nemi kukan ta rasa, sai wani bakon yanayi da ya ji ya ziyarceta.





✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




😭😭😭😭😭😭😭
*DAN ALLAH MASOYA LITTAFIN COLONEL UBAIDULLAH KUYI HAKURI, WLH ABU NE KAMAR WASA YANA SHIRIN ZAMA GASKIYA 😭😭😭 KWATA KWATA LITTAFIN YA FITA A RAINA SAI KACE WACCE AKA MIN ASIRI, BA WAI LOKACI NE BAN DASHI DA ZAN GAMA KAFIN SALLAH BA AA 😭😭😭 BUK DIN NE KAWAI NAJI YA FICE MIN FITTTT!!!! DAN ALLAH KU TAYANI ADDUA NA GAMA MU HUTU, KU KU HUTA NIMA NA HUTA 😭😭😭 ALLAH YASA MU DACE AMEEN.*




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



😡😡😡😡😡😡😡😡😡😡😡
*_WANNAN JAN FUSKAN SHIMA BANGARENSA DABAN, A WAN CAN PAGE DIN NACE KUBAN SUNAYENKU NA BAKU KYAUTAR PAGE KUKAYI KAMAR BAKU SANNI BA KO 😡😡😡 AI KUN HUTA SAI DE KU NEXT PAGE, ZAKU JI SUNAYENKU HAR DA MASU MIN SHARHI A WATTPAD, UMMU AHLAN TANA GODIYA GAREKU MASOYA ABUN ALFAHARI_*💃🏻💃🏻






Anya kuwa ma kuna sharing din buk din idan kuka karanta? 🙄


Sorry 4 d typing..error ycn bazan iya editing ba 😪😪🥺🥺



Momyn Ahlan Taku Ce👍🏻
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*~UBAIDULLAHI~*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0
~~•~~•~~•~~•~~•
*Special gift to my 5 ☆stars★*
_Samira bint Abdallah_💋
_Fatima bintu Sagir_💋
_Farhat Mrs M'J_💋
_Princess (Nafeesat)_💋
_احلام فاطمة_💋

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*_HAPPY HAPPY HAPPY💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻, HAPPY ANNIVERSARY KAINUWA WRITERS ASSOCIATION, 3YRS ALHAMDULILLAH, YA ALLAH KA KARAWA KAINUWA DARAJA DA DAUKAKA, ALHAMDULILLAH KAINUWA DASHEN ALLAH MAHASSADANKI FADAWANKI 💪🏻💪🏻 KOMAI SU KAI KI BARSU DA ALLAH, YA ALLAH KA KARA BAMU IKON TSARKAKE ALKALUMANMU WAJAN RUBUTA DAI-DAI, ALLAH KA TSARE ALKALUMANMU DAGA RUBUTA SHIRME ABUN DA BA ZAI AMFANE ALUMMA ANNABI MUHAMMAD S,A,W BA, INA MIKO MIKI JINJINA DA DUBUN GAISUWA TARE DA FATAN ALKHAIRI SHUGABA JA GABA ANTY FAUZA YAR AMANAR KAINUWA, ALLAH YA IYA MIKI, INA GAISHE DA KOWA DA KOWA NA KUNGIYATA, ALLAH YA KARA HAƊA KAWUNANMU YA KAƊE FITINA A TSAKANINMU, ALLAH YA KARA MANA HAKURI DA FAHIMTAR JUNA, (ZAHRA ABDUL MOMYN AHLAN INA YI MANA FATAN ALKHAIRI) UP UP UP UP UP KAINUWA WRITERS ALLAH YA KARA BASIRA DA DAUKAKA_*💓💓💞


*_YAU PAGE DIN FA NA KU NE_* 💃🏻
@💞💞 MEMCY💞💞 and........😟 yasin sis bansan asalin sunanki ba 😢 (Oriflime ne ko miye ne uhum 😢) sonso fisabilillahi. 💞👏🏻

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


*page°°°°°96&100*




Duk yaƙin da zasu je,da ya ga an kashe wani soja,ya kan shiga damuwa da tausayin iyalansu halin da zasu shiga, har misali yake yi da kansa yanzu ace gawarsa ce za a dauka a kai gida ya Mama za ta ji? Gaskiya sojoji su na matuƙar bakin kokarinsu, da zarar ka shiga aikin soja, to fa ka din ga rayuwa da sanin cewa za a iya farmaka ko wani lokaci,shi yasa da yawan wasu mata basu cika son auren soja ba, dan zaka yi sallama lafiya lafiya da Iyayenka da matarka amma ka je yaƙi a dawo da gawarka.




@@@@


Kwanarsu uku a kasan babbar rafin kashmeer ba ci, sai dai sha, haka suka sake komawa aka ci gaba da takaddama, ya yinda sojoji sun kashe yan ta'adda da yawa, kuma rundunar sojojin india na yankin kashmeer sunji labarin sojojin nigeria sun kawo farmaki dan anyi garkuwa da yan matan kasarsu, amadadin su kawo musu dauki tunda su ma yan ta'addan sun addabesu amma sai suka labe dan tsoron makaman da yan ta'addan suke dauke dasu, sunji labarin wani jami'in soja wanda ke zubar dasu miyagu izuwa kasa wanda shine ja ragamar yaƙi,wa hakan ne suke son ganin wanene wannan jarumin.


Nan fa sai dai suka sake share sati daya ana yaƙi, nan da kwana goma an kashe sojojin Nigeria guda goma sha uku, in da mutane ishirin suka ce su kam guduwa za su yi, Ubaidullah yace shi kam ko zai mutu babu inda zai je dan ya ɗau alkawari sai ya kubutar da mata da yardan Allah.



Sojoji 20 da suka koma gida su ne suka bada labarin tashin hankalin da sojojinsu suke ciki, tare da sunaye da hotunan wa inda aka kashe, sosai hankalin General Of The Army da sauran manya ya tashi, dan kuwa sojoji masu nagarta aka zaba aka tura, Major Usman ne ya ce.
"Su Captain Ubaidullah fa?" nan wani soja ya ƙame yana bawa Major Usman amsa da cewa.
"Haƙiƙa Captain Ubaidullah jarumi ne yawancin yan ta'addan da aka kashe shine ya kashesu, kuma yace ba zai dawo ba ko da kuwa zai mutu sai ya karbo yan matan da aka yi garkuwa dasu, gaskiya shi din jarumi ne gagara gasa" murmushi Major Usman ya yi, nan aka fara shawarar ƙara tura wasu jami'ai amma kowa saffewa yake yi, dan ga shi nan wasu sun gudu, su kuma sai su kai kansu.




Tun basu dawo ba, labari ta baza duniya na mutanen da aka kashe a india, wanda suka yi jarumta suka mutu a fagen yaƙi.



@@@@

Zaune take gabaki ɗaya ta rame tayi duhu, da ka ganta kasan bata cikin walwala da kwanciyar hankali, hayaniya ke tashi bisa alamu dai shagali ake yi, dago ido tayi ta kalli Mama wacce take ta murmushi a cikin jama'a amma a zahirin gaskiya idan ka kalli cikin kwayar idonta kasan itama ba bata tare da natsuwarta, yan uwana ake ta shige da fice, ana shirin zuwa lunching na Safwan da Shafa'atu, Ummi ce ta ratsa cikin mutane ta zo gaban Abi'atu tana kallonta, ita kam ma Ummi kallon mai ciki take yiwa Abi'atu,
"Ke Abi'atu ba za ki je lunch din bane? Kin zauna da kayan bacci kin kasa wanka? Ga jama'a da yawa a gida, ki tashi kije kiyi wanka ki cire wannan kayan bacci da hijabin ki zo, idan ma ba zakije lunch din ba kiyi wanka ki zama mutum a cikin mutane, ke ma Hafiza kin zo kin zauna a nan tashi kije ki shirya kema, tun da babu igiyar kowa a kanki, ita da take da igiya a kanta take fama da guntayen ciwuka sai ta zauna a gida" mikewa Hafiza ta yi ta amsa da "to Ummi" ta fice daga parlour tana fitowa gate wani soja ya rakata har izuwa bakin gate din gidansu kafin ya tsaya a gate din, Abi'atu kuwa haɗe rai tayi sosai ko kallon Ummi ba ta yi ba, Mama ta yi dariya ta ce.
"Ummi , ki fa bar min yarinya tasha iska"
"Haba Mama wani irin shan iska dan Allah, gida da mutane amma ta zauna da kayan bacci da hijabi?" Mama ta sake murmushi dan itama ta dauka Abi'atu ciki ne da ita, amadadin Abi'atu ta tashi sai ma gyara kwanciyarta da tayi dan wani irin haushin yan shagalin bikin take ji, Mijinta na can yau kusan wata ba ta ji lafiyarsa ba, amma wai su na shagalin biki, shagalin banza shagalin wofi, to wallahi ba zata yi wankan ba ma yau gaba ɗaya, har wa inda zasu tafi lunch suka gama shirinsu suka tafi abun su Abi'atu tana kwance bata saka lahadin tashi ba, rintse ido tayi tana taro dukkan moment dinsu da Ubaidullah har izuwa ranar da zai tafi ya furta mata kalmar yana sonta, wasu zafafan hawayen ƙauna ne suka wanke masa fuska, ta yi saurin gogewa ta jawo wayarta ta shiga cikin galary, pics dinsa ta hau kalla tana murmushi dan abun da yake iya sanyaya mata zuciya kenan, pic dinsa ta saka a wallpaper na screen din ta da kuma na WhatsApp dinta, kunna data ta yi ta shiga media, abun da ta fara karo dashi shine yayi matukar gigita mata hankalinta da natsuwarta Facebook twitter Instagram yawancin kafofin sada zumunta hotunan sojojin da aka kashe a india ne, Abi'atu tana gani ta saki wani kururuwan da sai da gidan gaba ɗaya ya amsa,a kiɗime aka yi kanta, ihu take tana " wayyo Allah Mijina!" Ummi ce ta zo da sauri ta rirriƙeta tana tambayarta menene, nan ta nuna musu abun da ta gani, Ummi ta ce.
"Haba Abi'atu sai kace ba musulma ba?za ki saki wannan kururuwa haka, su yan uwansu da suka ga gawarsu su kuma su yi yaya kenan? Ko kin ga Ubaidullah a cikinsu ne?, ki ci gaba da masa addua a matsayinki ta matarsa, Allah ya basu narasa su dawo a sa'a, su kuma wa inda suka mutu Allah ya gafarta musu, sosai Ummi ke lallashin Abi'atu dan hankalinta ya kwanta duk da itama Ummi hankalinta a tashe yake bata so ta nunawa Abi'atu hakan ne, dan Abi'atu bata iya tsorata ba, yanzu sai ta ri ga Ubaidullah din ma mutuwa idan shi bai mutu a yaƙi ba, to Abi'atu sai ta mutu a fargaba, ga shi tana tsoro kar wani abu ya sami abun da yake cikinta, a cewar Ummi, bata san babu abun da ya taba shiga tsakaninsu ba balle aje ga ciki, lallashi iya lallashi babu wanda ba ayi wa Abi'atu ba amma sam kamar ba da ita ake yi ba, tace ita tana so ne ta ga mijinta, har yan lunching aka dawo aka saka Abi'atu a gaba, dasu Mama, nan dai aka nemi number ta barracks din su Ubaidullah aka kira, Safwan ne ya yi magana akan cewa ko akwai hanyar da zasuyi magana da Ubaidullah? Da taimakon Major Usman aka tura dan sako zuwa ga Ubaidullah ana so aji lafiyarsa, su na tsaka da yaƙi sako ta iskesa, dama shima yayi missing dinsu amma baya da halin zaman da zaiyi waya dasu, abun da ya sani shine kullum su na zuciyarsa, da kyar ya koma gefe ya samu nertwork ya kira gida, Mama ce ta fara ɗagawa tana jin muryarsa ta kasa magana, da kyar ta iya bude baki ta ce.
"Babban Yaya kana lafiya?" murmushin karfin hali ya yi ya amsa da ina lafiya Mommana, fatan kuna lafiya dukkanku?" Mama ta amsa da eh sannan ta mikawa Abi'atu, tana karba ta saka masa kuka, ya rintse ido a hankali ya ce.
"My Muahh, menene abun kukan?" kasa magana ta yi, jin ba zata yi shuru ta daina kukan da tayi masa magana ba ya ce.
"Idan ba ki min magana ba, zan ajiye wayata, me kikeso?" cikin sheshsheƙa ta ce.
"Ina so ka dawo"
"Bayan wannan fa?" ya tambayeta cike da damuwa.
"Ina so na ganka"
"Okay bari na kiraku video call" ya fada ya tsinke wayar ya kira ta video call da suka gansa da ace a hanya suka hadu zasu rantse ba shi bane, dan wani baƙin da ya yi ga wani uban rama, Mama bata san lokacin da kuka ya kubuce mata ba ta tashi da sauri ta fice, Ummi ma sai da suka share hawaye, nan kukan Abi'atu ya tsananta ganin yadda mijinta ya koma duna baƙin wake, nan ta shiga yi masa magiya ya dawo, da kyar ya kwantar musu da hankali, su na kan magana nertwork ya dauke, Zaidu ma ya samu ya yi waya dasu Umma, Inna kuwa itama harda kukanta dan basu taba tafiya yaƙi mai azaba irin wannan ba.




@@@@


Abu kamar wasa yau watansu Ubaidullah uku, idan ka ga yadda suka koma abun ba a cewa komai, an kashe sojoji ashirin da uku, yayinda da yawansu suka gudu suka koma gida, acikin su dari da saba'in da bakwai, saura mutum sittin da tara, kuma yanzu alhamdulillah sun gano inda yan matan suke kwacosu suke son yi, su yan ta'addan sun kashe sojoji 23 amma su an kashesu ta yadda ba zasu kirgu ba, kuma ogansu ya gane Ubaidullah dan a cikin kashi dari na wa inda aka kashe musu Ubaidullah shi ya kashe kashi tamanin, dan haka suke son kashe shi amma abun ba mai sauki bane.



Cikin dare su Ubaidullah suka dirƙa musu ya yinda suka sake kashe wasu daga cikinsu, da kyar da gumurzu Ubaidullah ya fidda yan mata kwantena daya, wanda a daren suka baro kashmeer, inda Commender Isa Bala ya sanar da L-General nan kuwa da washe gari aka kwashi yan mata aka mai dasu kasarsu, inda wasu ke kukan murna da farin ciki dan har sun fidda ran zasu dawo mahaifarsu, a 9ja barracks aka ajiyesu inda ake musu tambayoyi su na kuka suke bada amsa, kafin su fara bada bayani sai da suka ta zubawa Ubaidullah addua, inda suke jawabi akan cewa siyar dasu ake yi a matsayin ƙaruwai, ko a siyar dasu bayi marasa galihu, su ma kuma idan bukatarsu ta tashi su na zuwa su zaba wacce suke so su keta mata haddi idan kuma ta ƙi amincewa su kasheta, sosai aka dinga naɗan rahotanninsu, inda a kwana biyu labarai ya karaɗe media, aka haɗa wasu da iyayensu.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Ubaidullah sai da suka sake diban kwana shaɗaya kafin da kyar da suɗin goshi suka sake kubutar da kwantena daya saura daya, inda sun sha baƙar wahala kafin su fidda na biyun, inda da yawan sojoji suka ce wlh ba zasu iya ba sunyi wa inda zasu iya yi, nan kuwa da yawa aka koma gida, su Ubaidullah wanda suka rage basu fi su ashirin da bakwai ba, Ubaidullah ya ce In sha Allah sai sun kubutar dasu, a wannan yanayi fa yan ta'adda sun ragu ba kaɗan ba, abun farautarsu kuma wanda suke nema ido buɗe ba ido rufe ba, shine Ubaidullah, wannan kwantena ɗayan da ya rage su Ubaidullah sun ji jiki matuƙar jin jiki, inda mutane goma suka sake mutuwa, nan suka rage su goma sha bakwai inda mutane goman su ma suka ce wlh su ma sun gaji suka gudu, su Ubaidullah suka rage su bakwai.


A ranar da Ubaidullah ya ballo kwantenar karshe su na kokarin guduwa ne ogan yan ta'addan ya harbi Ubaidullah yana kan gudu bayan yasa sojoji hudu sun gudu daga kashmeer da yan matan, sannan tun kafin ya fiddosu sai da ya kira rundunar sojojin yankin kashmeer akan azo a tafi da sauran yan ta'addan sun yi musu aiki mai wahalan, kafin sojojin su karaso shine ogan yan ta'addan wanda ake kira Zaffar ya harbi Ubaidullah a kafaɗa, dama su uku suka rage daga shi sai Zaidu da KB, dai-dai nan sojojin indian suka karaso, kafin su yi wani yunkuri Zaffar ya sake harbin Ubaidullah a damtsen hannu, da karfi Zaidu ya kira sunan Ubaidullah, ganin haka yasa Zaffar saita bindigarsa a saitin Zaidu zai harbi Zaidu ganin haka Ubaidullah cikin ɗauriya yasha gaban Zaidu aka sake harbinsa inda bullet din ya shige wajan gefen ƙirjinsa wanda yasa numfashinsa tsayawa cak!!, Zaffar na shirin sake harbi da gudu KB ya shaƙosa, kafin sojoji suka kamasa da sauran yaransa, Ubaidullah na tsaye sai zufar dake keto masa ta ko ina sabida azaba, sai da ya kalli Zaidu ya saki murmushi gami da cewa, *"ALHAMDULILLAH!"* sannan idanuwansa suka ƙisfe nan ya zube kasa wanwar.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


A lallaba 😪


UMMU AHLAN TAKU CE👍🏻



Nayi nan sai kuma gobe in Allah ya kaimu 👏🏻🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*~UBAIDULLAHI~*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0
~~•~~•~~•~~•~~•
*Special gift to my 5 ☆stars★*
_Samira bint Abdallah_💋
_Fatima bintu Sagir_💋
_Farhat Mrs M'J_💋
_Princess (Nafeesat)_💋
_احلام فاطمة_💋

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*


*_SAKON BARKA DA SALLAH GA DAUKACIN YAN KUNGIYATA ABUN ALFAHARINA, TUN DAGA IYAYENA YAYUNA, ƘANNENA, KAWAYENA ANA TSAFTAR TARE KO BA WUYA, ALLAH YA KARAWA KAINUWA BASIRA DA DAUKAKA_* 👇🏻

Anty Fauna ƴar amana
Batul Adam Jattako
Ummy On top
Kadija Usman Ta me gari
Maryam Umar (mmn Yusuf)
Ummu Fatima
Hauwa'u Salisu Haupha
Real Nana Aisha
Manab ƴar baba
Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)
Fauziya Auwal Alin Baba Jingau
Nabilancylv
Fiddausi S.bak'i (Smart Feenat)
Haleemat Hassan Leemat
Jamila Sumaila Yusufa
Zahra Faruk
Hussy Sani
Amina Fistlady
Pretty Mardy
Maryam Marsad
Deeja Alkali
Maman Noor
Nimcylv

*_INA YINKU, ALLAH YA KARA HADA KAWUNAN MU_* 💞💞💞


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


*page°°°°°91&95*




Azaba iya azaba, sun sha ta a wajan Ubaidullah da Zaidu, har wajan kwana uku, a yau ne kuma zasu bakunci lahira, videos din fyaɗe Ubaidullah ya kira Abi'atu ya bata aikin yaɗawa a ƙafofin sada zumunta, sannan ta yaɗa labarin masu ta'addanci da b'arna a doron ƙasa, masu lalata ƴaƴan jama'a, wanda yake sanadiyyar mutuwar wasu daga cikinsu, da yawan mutane anyi commemts inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa, yayinda mutane da yawa suke bawa sojoji goyon baya akan idan an kama masu laifin a kashesu kawai ko za a samu a rage mugayen iri a cikin jama'a, dan har yau bamu ji wani hukunci mai tsanani da ƙasarmu nigeria ta dauka ba akan masu fyaɗe, yayinda rundunar sojojin su Ubaidullah ta samu ƙwarin guiwa dari bisa dari, mota suka shiga dasu, sannan suka dauki hanyar jejin nasarawa, tafiyar awa daya ce da yan mintoci ta dauke su, ya yinda suka isa jeji suka fito dasu, jera su suka yi, Ubaidullah yana binsu da kallo yana kallon videon yaran mutane masu ihu su na neman akawo musu dauki, daga cikin har da na kanwarsa NA'ILAH, abun da yake kara tunzura shi, da aka tambayesu wai tsautsayi ne da sha'awa, to idan sha'awa ne why not ka je gidan karuwai ka dauko karuwa ka biyata kayi da ita da son ranta? Amma sai ku din ga bin yaran mutane ƙanana kuna keta musu haddi, a kalla wa inda suka mutu sun kai hamsin, dan ko wata babbar mace ba lallai bane ta iya dauke bukatun Namiji balle yara kanana wanda babu wa inda suka haura shekara sha hudu ƙasa da haka a cikin yaran da suka yi wa fyaɗe, Ubaidullah ne ya saita bindigarsa akan saitin goshin daya daga cikinsu, har yaja kunnaman bindigar zai saki ya ji wayarsa ta dauki ruri, da kamar ba zai duba ba, sai kuma ya duba ya ga bakuwar number, nan zuciyarsa ta shiga waswasi ya ɗaga ne ko kar ya ɗaga, nan dai wata zuciyar tace masa ya ɗauka, yana dagawa yaji ana gargaɗa masa kasheɗi da kakkausar murya.
"Hloo!!! Da Captain Ubaidullahi nake magana!?" sai da Ubaidullah ya shaƙi iska kafin ya amsa cike da izza ya ce.
"Wanene kai!? Me kake neman Ubaidullah din zaka masa!?"
"Kaiii!! Yaro!! Dama ance min kana da ji

20 / 25