Author : Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category : Romance
shi ma farin ciki ya yi, daga haka ya zauna yana dan janta da hira tana amsa shi sama-sama har Abba ya dawo ya gan su a haka, har kasa Hafiza ta sauko ta gaishesa dan kuwa Abba maƙoci ne na gari dan ya musu halacci da rasuwar Na'ilah.
Cike da fara'a Abba ya amsa gaisuwar yana tambayarta ya jikinta ta amsa da sauki ya ce.
"ina Abi'atun taki?"
"Su na tare da Yayana a ƙaramin parlour shi ya ce na rakosa wajanta" Safwan yasa dariya cikin wasa ya ce.
"Ah Alhamdulillah! Ashe dai maganata zata zama gaskiya kenan, ga Journalist ga Army" itama Hafiza murmushi tayi Abba ya ce.
"To Allah ya sanya alkairi mu bamu da ta cewa" Ummi ta ce.
"Wallahi kam, ameen" daga haka Ummi suka wuce ita da Abba, shi ma Safwan mikewa ya yi ya ce.
"Hafiza nima zan shiga ciki na watsa ruwa."
"To Yaya Safwan a fito lafiya" daga haka Safwan ya shige part dinsa.
Hafiza ta juya tana kalle-kalle a ranta ta ce.
"To yana ji su shuru haka? Ba dai Yaya tafiya ya yi ba? Dan zai aika, to ko naje na duba ne? Kai A'a bari na kara musu lokaci kadan mu gani tun da, da ya tafi dole Anty Abi'atu ta dawo" da wannan tunanin Hafiza ta koma ta zauna.
@@@@
Kusan awa ɗaya, Abi'atu tana zaune Ubaidullah bai ce da ita ƙala ba, tun gaisawar da suka yi.
Guntun tsaki taja ba tare da ya ji ba, a ranta ta ce.
"Ni Abi'atu yau na ga salon wulakanci har gidan Ubana, mutum ka zo, ka sa a kirani amma ka mai da ni tamkar wata poster? To wallahi baka isa ba, idan baka da abun yi ni ina dashi" tana gama faɗin haka a zuciyarta ta miƙe zata fita har ta kai kofar fita ya ɗago shi bai ma san ta tashi ba, da sauri ya ce.
"Amm keee! ABI'AH."
Cak Abi'atu ta tsaya saboda yanda ya kira sunan nata wai Abi'ah take tsiƙar jikinta ya tashi ga wani kasala da ya sauke mata.
"Subhanallahi! Wannan bawan Allah akwaisa da fi'ili" duk maganar zuci take yi.
Tasowa Ubaidullah ya yi ganin yanda ta tsaya bata da alaman juyowa balle ta sa niyyar dawowa,gabanta ya zo yana dan kallonta sama-sama dan bai son ya cika kallon mace saboda kar zuciyarsa ta ƙitsa masa abun da ba shi kenan ba.
"Uhum amm dama na zo ne na baki hakuri akan maganar da kika fadi akan cewa ba zaki sake zuwa gidanmu ba, ko ba komai saboda ke Hafiza ta fara magana, na yi farin cikin haka sosai, ga shi Mama tana yabonki sosai ko ma ba danni ba ya kamata ki janye maganar ba zaki sake zuwa ba, tun da naga alama duk kin sace zukatan yan gidanmu, fatan kin fahimci abun da nake nufi?"
Tun da Ubaidullah ya fara magana dodon kunnen Abi'atu yake mata guɗa, yanda yake furta magana ɗaya bayan ɗaya abun ba karamin burgeta yayi ba, barin ma sexy voice dinsa wanda taji yana shirin sakata bacci, a fili kuma, motsa dan ƙaramin bakinta tayi ta fara magana, zubawa bakinta idon Ubaidullah ya yi, a cikin ransa ya furta. "ya salam! Yarinya yar ƙanƙanuwa amma sai kisisinar tsiya"
"Dama ai ba dan kai din bane zan koma, fatan kai ma ka fahimceni?" ta fada gami da juyawa zata fita a ranta ta ce.
"Ka ji fa, wai ya zo bani hakuri amma bai furta min yi hakurin ba" juyawar da ta yi suka yi karo da Hafiza zata shigo ita kuma, tsayawa Hafiza tayi tana musu kallon tuhuma, daga masa gira Hafiza tayi ya kau da kansa gefe ya ce.
"Hafiza muje ko?"
Caraf ta ce.
"Yaya, muje ka gaishe da Ummin, Abba ma ya dawo, Anty Abi'atu dan Allah karasa sai na biku a baya" da mamaki suka kalli Hafiza ta tura baki, dukkan'su basu ce komai ba, Abi'atu tayi gaba Ubaidullah ya bi ta a baya, har cikin parlourn su.
Abba da Ummi su na zaune, su Abi'atu su na shigowa Safwan yana fitowa, nan suka yi musabaha da Ubaidullah ya yinda Ubaidullah ya dukar da kansa kasa sosai ya russuna ya gaishe da Abba da Ummi tamkar ya je gaisuwan surkai.
Amsawa Abba da Ummi suka yi cike da fara'a, sannan Ubaidullah ya mike da sauri ya fice Hafiza tayi musu sallama tabi bayansa, Abi'atu ta zauna Ummi ta ce.
"Ke Abi'atu wannan wani irin shirme ne? Mutane su zo wajanki zasu tafi ba zaki taka musu ba?"
Ba dan Abi'atu ta so ba, ta miƙe ta fito wajan gate ta ga har sun dan yi nisa, tsayawa tayi na wasu lokaci kafin ta koma cikin gida.
Ubaidullah su na zuwa sai da ya ga Hafiza
Ta shige kofar parlour kafin ya shiga motarsa yabar gida, dan kuwa sauri yake yi akwai aikin da zai je mai muhimmanci.
Ubaidullah bai dawo ba sai tsakar dare wajan sha biyu da rabi, amma duk da haka sai da ya fara shiga ciki dan ya ga lafiyar Mahaifiyarsa da Kanwarsa, Hafiza a dakin Mama ta yi bacci, Mama kuwa idonta biyu,har sai da ta ga Ubaidullah kafin ta ji karfin guiwar samun damar kwanciya.
@@@@@
Da washe gari bayan Ubaidullah ya shigo sun gaisa da Mama yake faɗa mata in da ya je jiya, akan cewa ya samu wasu manyan shaguna ne a kasuwar wunti guda hudu ya siya, har ya bada other za a kawo kayayyaki yau za a zuba, sabida ya san yana da wani sana'ar da zata din ga kawo masa kudi, dan kar kudin hannunsa ya kare su rasa yadda zasu yi.
Adduar Allah ya sanya alkhairi da Allah ya rufa asiri ya kara buɗi Mama ta yi masa, ya amsa da ameen, har ya tashi zai fita Mama ta ce.
"Ubaidullah, shin Alhaji Adamu yasan da cewa kabar aiki?"
"A'a Mama, bai sani ba, yanzu kusan shekaransa ɗaya da rabi kenan baya ƙasar, shi da iyalansa,su na Cairo"
"Ayya, sai yau she kuma zasu dawo?"
"Wallahi, Mama ban sani ba, duk da muna waya dashi lokaci zuwa lokaci muna gaisawa, amma ban faɗa masa abun da ya faru ba."
"To shi kenan, Allah ya zaba abun da yafi alkhairi a rayuwa"
"Ameeen Mama, ina Hafiza ne?"
"Ba su jima da tashi anan ba ita da Abi'atu" jinjina kai ya yi, ya fice.
@@@@@
Masha Allah kwana hudu aka dauka ana gyaran shagunan Ubaidullah ya yinda aka zuba kaya masu kyau da tsada da arahar kudi, wanda ana ta neman sunan da za a sa wa shagon amma an rasa, Hafiza ta tambayi Abi'atu sunan da ya dace a sawa Shagunan.
Nan Abi'atu ta ce, a sawa Shagunan suna, ABDULLAHI'S FAMILY, sosai kuma sunan ya burge Ubaidullah dan ya ji dadin sunan sosai.
Cikin ɗan ƙankanin lokaci Allah ya sakawa shagunan albarka, nan da nan Abdullahi's Family Shop jama'a aka san da zamansa a garin bauchi, barin ma yan mata, dan kuwa an zuba su kyale-kyale, jakukkuna ne takalma atampopi shaddadu materials su cosmetics, babu abun da babu a shaguna guda hudun ne.
Haka rayuwa ke tafiya da sauri-sauri duniya tana gudu, yau shagunar Ubaidullah watansa ɗaya da budewa kuma Alhamdulillah yana samun kudi sosai kudi su na shigo masa masha Allah, dan har mota ya siyawa MAMA da Hafiza, duk da shi ba zaman shagon yake yi ba ya samu masu zama masa dan shi har kwanar gobe baya da sha'awar wani aiki ko kasuwanci wanda ya wuce aikin soja, duk abun da ke faruwa Ubaidullah su na magana da amininsa Zaidu, ba laifi Zaidu ya fara warewa amma ba sosai, ta bangare daya su na kan bincike akan wa inda suka yiwa Na'ila fyaɗe, yanzu tsawon wata hudu kenan, da rasuwar Na'ila amma babu wani haske, Ubaidullah ya yi kukan baƙin ciki dan kuwa ya fara cire rai, a wannan wata hudun ne kuma Mama ta je ta samu ƙanin mahaifin su Ubaidullah akan ya je ya nemawa Ubaidullah auren Abi'atu, hakan kuwa aka yi, inda Ƙanin Baba ya je nemawa Ubaidullah auren Abi'atu ba tare da sanin Abi'atu ko Ubaidullah ba, amma kowa ya sani daga ciki kuwa har da Hafiza duk da Mama tace babu wani gayyar da za'ayi daura aure ne kawai, Hafiza kuwa ita ce ma a kan gaba wajan ganin auren ya tabbata.
Abba cewa ya yi, ai Ubaidullah tamƙar Safwan yake dan haka ba komai ai, ya basa Abi'atu, har aka tsaida ranar biki ba mai tsayi ba, wata daya kacal.
Mama tasa Ubaidullah ya haɗa akwati a shagonsa kayan lefe masu rai da lafiya, amma ba tare da ya tambayeta nawaye bane, dan ko da kayan shagon duka Mama tace tana so, zai kwaso ya kawo mata balle ta ce ya hado lefe ya kawo, har biki ya rage sati daya Ubaidullah bai sani ba tun da bai cika zaman gida , Abi'atu ma bata sani ba, tun da ba shale aka yi ba, yan uwa ma da suka ji suka ce tun da ba taro za'ayi ba, wasu ba sai sun zo ba.
Ko da aka tashi ranar daurin Aure Ubaidullah baya nan tun da ba wani jama'a aka tara ba, sai su Umma dasu Inna da sauran yan uwa da abokan arziki haka ma gidan su Abi'atu.
Ranar da aka daura aure Ubaidullah ba a gida ya kwana ba, sai da ya yi kwana biyu baya gida har yan uwa wa in da suka ɗan leko suka fara watsewa, tun da Mama ta ce babu wani shagali da za'ayi yanzu sai ta tashi tarewa.
@@@@@
Ko da Ubaidullah ya dawo gida babu wanda ya gaya masa cewa anyi aurensa, Hafiza ce dai ta kira su Zaidu ta fada musu amma ta ce kar su fada masa dan shi ma bai sani ba auren yazo a baibai ne, ai kuwa Zaidu ya din ga yiwa Ubaidullah tsiya shi da Hafiza da KB su na dariya.
@@@@@
Yau sati daya da auren Ubaidullah da Abi'atu, yau kuma ta kama jumma'a, an daura ranar jumma'a ne, sauri take yi zata fita aiki dan akwai labarin da take son yaɗawa sannan tasa a buga a jarida, labarin wani da yasa aka shiga aka yiwa matar makwabcisa fyaɗe.
Har ta gama shirinta ta fito ta samu Ummi na zaune a parlour tana cin abinci, durkusawa Abi'atu ta yi ta gaida mahaifiyarta, da kallo Ummi ta bita da shi ta ga tasa hijab dinta, murmushi Ummi ta yi ta ce.
"Yar gidan Abba sai ina kuma?"
"Wallahi Ummi sauri nake yi zan je aiki akwai labarin da nake son yaɗawa yanzu ne, shi yasa nake sauri na je."
"Ayya Abi'atu kiyi hakuri kar ki fita, ki kirawo Shafa'atu (cousin sistern Abi'atu ce wanda suka yi skull tare, kuma waje daya suke aiki, Shafa'atu bata cika zuwa gidan su Abi'atu bane yanzu, saboda kunyar Ummi da take ji, tun sadda Safwan ya ce yana sonta har aka musu baiko) sai ki bata ta je ta yaɗa."
Gaban Abi'atu ne ya fadi ta ce.
"Haba Ummi me ya sa, kwana biyun nan na lura kina son hanani fita meyasa to?"
"Akwai dalili ne Yar Abbanta,yanzu dai yi hakuri ki koma ki kirawo Shafa'atu" tashi Abi'atu ta yi kwalla taf a idonta.
"Ko dai su Ummi su na so na bar aiki ne?" take tambayar kanta bayan ta koma daki tayi wulli da takardun hannunta ta zube a gefen gado, sai da ta gama tunaninta kafin ta kira Shafa.
Su Ummi kuma so suke su bata mamaki dan sun dauka akwai soyayya mai karfi tsakanin Abi'atu da Ubaidullah ne, ba su san da cewa kullum idan suka hadu sai an kai ruwa rana ba.
@@@@@@
Yawancin kullum Hafiza idan Yayanta na gida to fa, sai ta ja shi izuwa gidan su Abi'atu, kuma idan sun je sai sun jima, duk da Ubaidullah yanzu baya zaman gida sosai, sabida binciken da yake zuwa yi yana sa ana kama miyagun mutane, dan ya ce ko ta haka Allah zai sa ya kama wa inda suka yiwa kanwarsa fyaɗe.
Ko da Ubaidullah ya je gidan su Abi'atu ba wani shiri suke yi ba, akwai ranar da Hafiza ta ja shi bayan sallar isha'i suka je gidan, tana ƙirawo masa Abi'atun ta saffe ta koma gida ta kwanta ta hau baccinta abunta.
Ranar har wajan karfe sha'biyu Ubaidullah su na zaune da Abi'atu ba tare da sun san dare ya yi haka ba duk da ba magana suke ba zaman kurame ne, su Abba da Ummi kuma basu damu ba tun da mata da miji ne, sai da Ubaidullah ya duba agogo ya ga sha biyu kuma ya ji shuru din Hafiza ya yi, yawa yau bata leƙo tace Yaya muje gida ba, sai da ya yatsine fuska kafin ya mike ya cewa Abi'atu ta je ta dubo masa Hafiza su tafi gida.
Ba tare da Abi'atu ta amsa va ta je ta gama dube dubenta bata ga Hafiza ba, dawowa tayi ta fada masa, hankalinsa ta shi ya yi, da zai kira Mama sai ya fasa ya kira mai gadi nan yake shaida masa Hafiza ta dawo tuntuni.
Tafiya Ubaidullah ya yi,ba tare da ya ce mata sai da safe ba, itama tabe baki tayi ta ce.
"Allah ya raka taki gona" tana shiga sukayi karo da Ummi gabanta ya fadi ta dauka Ummi zata mata faɗa ne harta fara tunanin kalar abun da za ta yiwa Ubaidullah idan Ummi ta yi mata faɗa sai ta ji ta ce.
"Ahh yar gidan Abba sai yanzu, ina Ubaidullah din sai yanzu ya tafi?"
Sosa keya Abi'atu tayi saboda kunya ta ce.
"Eh Ummi" daga haka ta shige dakinta da gudu Ummi tayi murmushi, itama ta fito daukowa Abba ruwa ne.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Ko da Ubaidullah ya koma gida sai da ya fara shiga duba Mama dan hakan har ya zame masa jiki, Mama ta ce.
"Daga Ina kake ne Yaya Babba?"
Ba tare da tunanin komai ba ya ce.
"Daga gidansu Abi'ah nake" ya fada yana masa sai da safe,Allah ya kaimu Mama ta ce dashi.
Tana tunanin ai gwanda matarsa ta tare kawai, ya fi wannan sintirin da yake yi kullum kar su jawo kansu abun magana tun da dai har an daura aure ai babu abun da ya yi saura.
@@@@@
Da washe gari Mama ta kirawo Ubaidullah ta ce ta ba shi nan da sati ɗaya ya gyara part dinsa *Matar shi zata tare*, cike da rashin fahimta ya kalli Mama ya ce.
"Mama ni da banyi aure ba wace mata ce gareni da har zata tare?"
"Ka ji shashancin banza, in ji waye yace baka da mata, to auren yau kwana goma kenan, kuma har fada musu zata tare nan da sati daya yau din nan, idan ma akwai wani abun da zaku shirya kuyi gwanda kuyi sirkata ta dawo gareni gabaki'daya"
Ka sa fahimtar maganar da Mama take fadi Ubaidullah ya yi, ya ce.
"Mama kina ta maganar ina da aure wacece matar kam?"
" *ABI'ATU*"
dum!dum!dum gaban Ubaidullah ya fadi sai kace mace, zai kuma yin magana Hafiza wacce take maƙale tana jin maganar da Mama da Ubaidullah ke yi ita kuma su na waya da Zaidu tana fada masa abun dake faruwa saurin katse wayar ta yi ta ce.
"Yaya zo ka ji" ta ja hannunsa suka fita waje nan ta kwashe komai ta fada masa yanda auren nasa ya kasance, kwafa Ubaidullah ya yi, ya fice dan shi baya da ra'ayin aure yanzu amma yarinya ta mayince sai da ta aure shi, to zata gane kuranta ne.
Ta bangaren Abi'atu itama drama aka yi da ita sosai da aka fada mata cewa tana da aure zata tare nan da sati daya nan ta dinga musu bori ,abun har mamaki ya din ga bawa su Ummi, suka hau tantama ko da ma ba soyayya suke yi ba, sunyi kuskure ne da basu tambayeta ba, wai su a nufin su zasu bata Mamaki dan tayi farin ciki ashe comedy ne za a kwasa.
Ana saura kwana uku babu yanda su Afnan ƙannan Zaidu ba su yi ba, akan zasu yi party amma Ubaidullah da Abi'atu sun ƙi ƙememe, an dai samu anyi walima ƙayatacciya wannan ma Anty Ummu ce ta hada Inna kuwa sai cewa take yiwa Abi'atu.
" Yarinya kin shiga uku an haɗaki da mala'ikan duniya."
Mama da kanta ta kai Abi'atu ɗaki tayi mata nasiha sosai, tace kuma karta dauke ta a matsayin surka dan tana auren ɗanta har kwanan gobe ita tamkar mahaifiyarta ce wacce ta haifeta a cikinta.
Abi'atu tasha kuka Anty Ummu sai tsiya take mata tana cewa bayan ko ihu kikayi Ummi zata ji ki, ai ke kam auren dadi kikayi, dan ma za ki ji ki kamar ma ba aure bane duk da aure ya wuci wasa ayi hakuri da juna, sosai Anty Ummu ta yiwa Ƙaninta da Matarsa fadan su zauna lafiya, su Zaidu basu samu damar zuwa ba.
Hummm ango shi ka dansa ya zo ko kallon dakin amarya baiyi ba, itama amarya ana watsewa ta rangaɗa wankanta tabi lafiyar gado.
Tun da aka kawo Abi'atu a matsayin matar Ubaidullah rashin shirinsu ya sake bunƙasa, dan kuwa zaman doya da manja suke yi.
A badadi su na gara juna har aka ɗibi wata uku.
Mama kuwa da Hafiza da Anty Ummu sosai suke jin dadin zama da Abi'atu, duk lokacin da taso zuwa gida kuwa zata zari hijabinta suje ita da Hafiza, yanda Hafiza take mu'alama da yar uwarta Na'ilah haka Abi'atu ta zama dan ta farantawa Hafiza rai, hakan kuwa Abi'atu ta kara samun daraja a idonsu Mama.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tsaye suke sun ƙame waje guda, daga kansu kasan meeting ake yi, yayinda General Murtala ke jawabi.
Ban da kakin sojoji babu abun da yake kashe maka ido.
Cikin tashin hankali General Murtala ke magana akan yan matan nigeria kwantena uku da aka yi garkuwa dasu a kasar india a yankin bangalo, ana neman jami'ai wanda zasu je domin su dawo da wa in nan yan mata, nan aka shiga lissafo wa inda zasu je, amma abun takaici yawancinsu sun ce ba zasu iya zuwa ba, saboda mutanen da suka yi garkuwar su na da mugayen makamai.
Ran General Of The Army ya baci sosai, nan ya hau masifa, har yana cewa, tun da Ubaidullah yabar barracks komai ya daina tafiya yanda ake so.
Muryar Zeey aka ji tana cewa.
"Taya kuwa komai