COLONEL UBAIDULLAH by Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢

Author :  Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category :  Romance

Chapter   3 / 25

6K to 9K   out of 74.6K words

~~~~~~~

Ta bangaren Ubaidullah ,parking din motarsa yayi a bakin madaidaicin gate din gidansu, black shadow din dake face dinsa ya cire,yana smiling.

Turo ƙaramin kofa na jikin gate ya yi gami da sallama, amma shuru bai ga kowa ba, abun har mamaki ya basa, ko ina mai gadin da ya a jiye oho.

Har ya kai kofar parlour kafin ya hau kwaɗa sallama, amma ya ji shuru ,har ya juya zai tafi part dinsa, sai ga Hafiza ta fito da hijabi, tana ganinsa ta saki dariya ta taho da gudu tana cewa.

"Oyoyoo Yaya, rungumeta yayi sannan ya saketa tana ta murmushi (Allah sarki dan uwa gudan jiki) ya ce."ina Na'ila"?

"Wani faduwar gaba ne yazo ma Hafiza ta hau tsilli-tsilli da ido dan Na'ila dazu kawarta ta zo ta jata wai sun tafi walimar wata kawar, kawarta.

Ba ta kai ga ba shi amsa ba, sai ga mama ta fito,
da sauri Ubaidullah ya mai da hankalinsa gareta,cikin murna da farin ciki ya je ta rungumeta, mama ta ce.

"Oyoyo ɗana na kaina , barka da zuwa, bana kai kadai ka zo ne ,ina Zaidu"?

Murmushi yayi kafin ya ce.

"Zaidu na a jiyesa a gida amma ya ce na gaishe ki kafin an jima ya zo"

"Ayya dan albarka Allah ya kawosa lafiya,ya amsa da amin kafin ya ce.

Mama ina Na'ila ?

Mama ta ce.
"Hafiza ina Na'ila dan dazu tare na bar ku"?

Cikin in-ina Hafiza ta ce.
"Dazu bayan kin shiga daki kawarta Munira ta zo ta jata wai sun tafi walimar wata kawar Munira"

Mama ta hau salati tana tafa hannuwa," Oh Allah na me Na'ila take son zama ne ? shi ne ta kama hanya ta fice baza ta iya zuwa ta fadamin ba? ko dan ta san ba zan barta bane?"

Ita dai Hafiza ban da zare ido Babu abin da take yi,ga wani uban tsoron da ya lullubeta ganin yanda fuskar yayansu ya rikid'e ya canza kala jijiyar wuyarsa duk sun tashi da ka kalle sa ka ga bacin rai k'arara, jinjina kai yayi sannan ya hau wurgawa Hafiza harara ,ai nan Hafiza ta k'ara tsurewa.

Ta kanta ya fara
"A kan me kina kallo za ki bar Na'ila ta fita iye?

Hafiza tayi shuru sai zare ido take yi ta kasa bada amsa, sai ja da baya ta keyi yana binta, ganin yana shirin cafkota ne ya sa ta ɗiba a guje ta yi bayan Mama ta saki kuka.

Mama ta ce.
" a'a wallahi karka taba Hafiza in dai Na'ila ce ba jin magana take yi ba, dan da tana jin magana to wallahi ba za ta fita a gidan nan ba,tun da nice nan na hanata fita da kuma kai, to ba ta ji maganata da taka ba, har za ta ji maganar Hafiza?"

"Kuma na tabbata bata san za ka zo yau ba, da ba za ta fita ba."

Ba tare da Ubaidullah ya yi magana ba ya juya ya fice ransa ɓace.


Har yayi wanka ya shirya ya kwanta, Hafiza ta kawo masa abinci amma ko kallon abincin bai yi ba har aka yi sallar magriba, Na'ila ba ta dawo ba hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba.


Ya je daki ya samu Hafiza tana karatun Alƙu'ani kasancewar sun kusan yin sauka, tana ganinsa ta dasa aya.

Tambayarta yayi, ya ce.
"A ina ne suka walimar"?

Jikin Hafiza na kyarma ta ce.
"Nima ban sani ba yaya."

Ba tare da yayi doguwar magana ba ya juya ya fice.


Yana fitowa ya samu,Mama a parlour ta kasa zaune ta kasa tsaye.

Nan suka zauna jingum-jingum
Har akayi sallar isha'i, su Na'ila basu dawo ba.

Kafin wannan lokacin, Captain Ubaidullah ya fara tunanin kalar salihin dukar da zai yiwa ƙanwarsa.


Sai wajan karfe tara suka shigo gidan.

Ubaidullah,Mama,Hafiza duk suna zaune a parlour.

Na'ila da kawayenta su biyar suka shigo

Sun fara sallama kenan.

Assalamu alay.....!!

Sallamar ta tsaya a maƙogaron Na'ila sakamakon tozali da yayanta, yana mata kallon za ki ci Ubanki yau!!




==============


*GASKIYA ZAN AJIYE TYPING DIN LITTAFIN NAN, ZUWA WANI LOKACIN DA NI KARAN KAINA BAN SANI BA,*


*GA MASU ƘORAFI AKAN ABUN DA NA FADI DUK INA SAURARONKU........*



COMMENTS
&
SHARE


BY MOMYN AHLAN
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)



*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻


*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~~•~~
*MARUBUCIYAR*

*HALITTA DAGA ALLAH NE*
*GUDU A JEJI*
*SHUHADA*
*NIDA ƘANNAN MIJINA*
TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116)

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘
____________________
_Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*page°°°°9&10*


A hankali Ubaidullah ya tashi yana ci gaba da yi mata kallon yau na lahira sai ya fiki jin dadi.

Ba iyakar Na'ila wacce ta yi laifi ba har ta Hafiza sai da hantar cikinta ya kaɗe ganin yanayin Yayan nasu.

Juyawa yayi ya kalli Hafiza murya a daƙile ya ce.
"Go and close the door"

Jikin Hafiza na kyarma ta wuce a sabule, ta je ta kulle kofar, har ta juya ya ce. "ciro keys din, ki kawo min"

Hafiza ta cire keys ta kawo masa, ta miƙa masa jikinta na rawa.

Na'ila da kawayenta Allah ne kadai ya san kalar tashin hankalin da suka shiga, Na'ila har ta fara zikiri a cikin zuciyarta dan ta san ba makawa sai taci ubanta yau, yanda ya sa aka kulle da kawayenta ta san su ma yau sun kawo kansu, dan yanda zai jibgeta, haka zai jibgesu.


A hankali ya kalli Mama wanda ta buga tagumi tana kallonsu dukkan'su, tana hararan Na'ila ,wacce ta kama hanya ta fice tun rana sai yanzu karfe taran dare ta dawo da sunan wai sunje walima.

Durƙusawa Ubaidu yayi a gaban mahaifiyarsa hannun da ta sa a kumatunta ya cire sannan ya ce.
"Mama pls ki shiga daki" ya fada ya kamo kafadarta ya miƙar da ita.

Har cikin daki ya kaita ya zaunar da ita a bakin gado, sannan ya juya ya fita ya kulleta da waje.

Yana fitowa parlour ya samu Hafiza har ta fara kuka ganin ya kai Mama daki ta san yau babu mai taimakon su Na'ila sai Allah.

Wani harara ya galla mata da wani irin kalar ido wanda ba ta taba gani ba, kafin a tsawance ya ce.

"Keee!!! Dan ubanki!! shiga daki idan kuma kina so na haɗa dake to bilmillah!"

Ai da gudu Hafiza da ta yi daki har tana tuntube kafin ya juya ga Na'ila wacce ta fara kuka wiwi tun ba a kai ga dukarta ba.

"Dan Allah Yaya ka yi hakuri na tuba ba zan sake ba wallahi ba zan kara ba Yaya ka yi hakuri kar ka dake ni"
Nan Na'ila ta hau magiya kamar ranta zai fita, ganin ya ciro belt ya sakata fara kiran sunan Mama da Hafiza.

Ya ce.
"Wato tun baki tafasa ba kina so ki ƙone ko? tun baki kai ko ina ba kina so ki ƙarawa Mama hawan jini a kan wanda take dashi? Na'ila tun baki kai ko ina ba kina so ki gwada kamar kin fi karfinmu ko?"

Yana maganar yana matso su , su na ja da baya.

Na'ila ta ce.
" a'a Yaya wallahi ba zan ƙara ba,am really sorry"

Shut up!!
Ya fada da karfi.

Kawayenta suka haɗa baki su na cewa . "dan Allah kayi hakuri mu dai a barmu mu je gida"

Su na gama fadin haka Ubaidullah ya rufesu da duka.

Shata musu belt din kawai yake yi, ta ko ina ya samu dan idonsa a rufe yake, ba'a son ransa yake dukan Na'ila ba, zai so Na'ila ta zama kamar yar'uwarta Hafiza amma ya ga alama sai ya mata dukar da zata yi jinya tukunna.

ya gwammace ya karyata idan ya so ya kaita asibiti ya yarda, ya kashe kudi akan wani abu ya sameta wannan rayuwar da bata da tabbas din.

Tun su Na'ila da kawayenta su na kuka su na ihu, har ya zamto basu iya katabus.

sosai Captain Ubaidullah ya musu rugu-rugu.

Sai da ya ga ba su motsi sosai tukunna ya dakata yana huci.

Mama tun tana kiran sunansa tana bugun kofa, domin jin yanda yaran mutane ke ihu su na cewa zasu mutu,da ta ji abun nasa ba na ƙarewa ba ne ,ta hakura ta koma ta zauna, ta zubawa sarautar Allah ido.


Bayan ya gama jibgarsu ya ga sun kasa ihu da kuka basu motsi tukuna,ya kwashe su ya saka su a mota, sai RIMI HOSPITAL.

Su na isa a ka basu taimako tare da yi musu,treatment saboda ya faffasa musu jiki da belt.

Gado a ka basu, sai karfe uku na dare Ubaidullah ya koma gida, bayan ya tabbatar an yi wa su Na'ila allurar bacci sunyi bacci.

Yana zuwa ya je ya bude Mama ya sameta zaune ta buga tagumi, har wannan lokacin ta kasa bacci, (ALLAH SARKI UWA).

Da sauri ya isa gareta, ya cire hannunta daga kumatun'ta, kafin ya ce.

"Ki yi hakuri idan na bata miki Mama, I don't mean to hurt you pls, but Na'ila tana bukatar hakan, bcox duk abun da ya same ta, ya same mu ne, amma ba za ta gane haka ba, ba zata iya hango tsananin son da muke mata ba, Mama har nawa Na'ila take duka-duka shekarunta goma fa Mama, amma take neman fin karfin mu?"


Mama ta share hawaye ta ce.
"Haka ne yanzu su na ina"


Na kai su asibiti"

Mama ta dafe ƙirgi ta ce.
"Ubaidu asibiti dai, asibiti fa kace? har da ƴaƴan mutane ka daka fa? shi ne duk ka kai su asibiti?"


"To Mama ai hakan shi ne daidai, baki ga ba saboda rashin kula irin na iyayensu akwai wanda ya zo nemansu ne? ba su zo ba ,ni a tunani na hakkin iyaye ne idan ba su ga y'ay'an su ba ko min dare ya kamata su je nemansu, amma ba su zo ba."

Shuru Mama tayi kafin ta ce.
"Ni fa wallahi bana son tashin hankali da ka bar yara sun tafi gidan iyayensu, bana son abun magana da ƙanwarka kaɗai ka hukunta."

Wani murmushi ya saki kafin ya miƙe ganin har karfe hudu ta gauta ,ya ce.
"Mama ba ki jin dadi ,ba ishashshiyar lafiya gare ki ba, yanzu ki kwanta ki huta gobe sai mu koma asibitin mu dubo su"

Mama ta ce.
"Yaran mutane kuma fa?"

Ya ce.
"Mama sai magana kike yi a kan yaran mutane , na ga fa harda Na'ila"

Girgiza kai tayi ta ce.
"Je ka huta, yau ka zo amma ko hutawa baka yi ba, Allah dai ya sa ka ci abincin ma"

Dan sosa ƙeya yayi.
"Wallahi Mama banci ba, zan ci idan Allah ya kai mu anjima", yana fadi ya sa kai ya fice a dakin,Mama ta bi bayansa da kallo kana ta ce.

"Allah ya daɗa shirya min ku"

~~~~~~~

ta ban garen Hafiza ma ba ta yi bacci ba, tana jin yadda y'ar uwarta ta dinga ihu tana kuka, ita ma haka ta dinga kukan a daki, ko da taji shuru tsoron fitowa take yi karya haɗa da ita.



~~~~~~~~~


Da washe gari.

Da safe misali karfe tara.

Ubaidullah ya dan koma bacci bayan yayi sallar asuba kafin zuwa sha biyu su je asibiti" ana tunanin kenan.

Cikin bacci yake jin kamar hayaniya na tashi, amma sai ya danganta hakan da mafarki, jin abun bana ƙarewa ba ne ya saka shi tashi ya dauki jallabiyyarsa ya saka ya fito, can wajan gate ya hango Mama da Hafiza tsaye gefe daya mai gadi da wasu samari su uku da yan mata biyu.

Cike da takun isa da izzan jarumtaka na ƙarfeffen soja ya ƙaraso mai gadi na ganinsa ya sara masa ya koma gefe.

Hafiza tana ganin Yayan nasu tayi saurin matsawa gefen Mama.

Cike da ɗaure fuska ya ce. "lafiya kuwa meke faruwa?"

Daya daga cikin samarin ne ya nuna Ubaidullah da yatsa yana cewa.

"Kai dalla malam, ma su waye zaka fito kana ciccin magani, idan kana gadara kai namiji ne ai muma ba ka ganmu da jan baki ko dan'kwali ba, ina ƙannan mu?su muka zo nema, kuma ance sun zo nan tare da ƙanwarka, yanzu kuma mun zo muna jin wata zance da bamu ganeta ba."


Ran Ubaidullah ya baci sosai ya tsaya yana masa wani kallon raini,

Kafin ya kalli Hafiza ya ce.
"Wuce ki shiga ciki"

Da gudu ta juya tayi abin da ya umarceta kafin ya kamo kafadar Mama ya juya da niyyar ya shige da ita ciki ita ma, sai ya ji daya daga cikin samarin yana cewa.

"Kaiiiiiii! ina ga baka san su waye ake kira da yan'bakaro ba, babu unguwar da ta kai mu sara suka a cikin garin Bauchi, idan baka fito mana da ƙannan mu ba, to wallahi sai mun yi gunduwa-gunduwa da kai."

Cak Ubaidullah ya ja ya tsaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur jikinsa ya ɗauki b'ari.



==============

MANAGER PLS


COMMENTS
&
SHARE

BY MOMYN AHLAN✍🏻👮🏻‍♀
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)



*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻


*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~~•~~
*MARUBUCIYAR*

*HALITTA DAGA ALLAH NE*
*GUDU A JEJI*
*SHUHADA*
*NIDA ƘANNAN MIJINA*
TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116)

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘
____________________
_Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*page°°°°13&14*



A hanya su na tafiya Mama sai mita take a ina Ubaidullah ya tsaya.

Zaidu ya ce.
"Mama maybe akwai abun da ya tsai dashi ne shiyasa a yiwa abokina uzuri"

Mama ta girgiza kai kawai, ta ce.
"Mu fara biyawa mu a jiye ƴaƴan mutane kafin mu wuce gida"

"To Mama" abun da Zaidu ya furta kenan.


Sai da suka a jiye yaran mutane a gidan iyayensu, Mama da kanta ta shiga tayi musu jawabi, wanda zasu fahimta sun fahimta, masu toshewar kwakwalwa kuma sun kasa fahimta, suka rufe Mama da ruwan bala'i, ganin yanda jikinsa ƴaƴansu ya kumbura da shatin belt, bisa alamu duka ba bana wasa ya musu ba.


Mama har sai da ta ji dadi da Ubaidullah bai zo ba,dan tasan wani abun kam sai dai a kunna ƙaramin yaƙi.

Zaidu ya ce.
"Mama wai mai ya faru ne kam haka na kasa fahimtar komai fa?"

Mama ta ce.
"Ai gata nan a gabanka sai tsilli-tsilli take yiwa mutane da ido, na rashin gaskiya, ai tukunna ma sai mun koma gida ki sake haduwa dashi"


Na'ila tayi rau-rau da ido alamun zata yi kuka.

Zaidu ya ce.
"No no my lovely kar kiyi kuka kinji ai gani nan ina nan bazan bari ya sake dukan ki ba."

Da haka har suka koma gida.

Mama tana tambayar mai gadi akan cewa "Ubaidullah bai dawo gida ba?"

Ya ce.
"Eh Mama ai tun da ku ka fita shi ma yaja mota wanda ya sakani tsinkewar zuciya ya fice bai dawo ba."

Girgiza kai Mama tayi sannan ta ce. "Allah ya kyauta"
Suka shige cikin gida, Zaidu ya ce.

"Mama ni zan koma part dinsa na zauna kafin ya dawo"

"To Zaidu ka huta kafin ya zo ma na gama muku girki, tun da yanzu kam sai dai abincin rana."


~~~~~~~~~~



Ta bangaren Ubaidullah ko da ya je hospital din aka tabbatar masa da an sallamesu, sun tafi tun dazu.

Wayarsa ya dauka ya bugawa Zaidu, a lokacin Zaidu na zaune a 2sitter yana latsa systerm dinsa.

Daukar wayar yayi yasa kunne.

Ubaidullah ya ce.
"ya ne, kun koma gida ne"


"Ah no Captain Ubaidullah muna hospital muna jiranka."


"Mtswwwww, Zaidu bana son raini fa"

Wani dariya Zaidu ya kwashe dashi wanda yasa Ubaidullah rumtse ido, kuma da gangan Zaidu yayi dan kawai ya sake ƙular dashi.

"Oh Allah, Yayana Ubaidu baka son raini, ni kuma kasan ai ina son raini, ka ga idan zaka dawo gida ka dawo, dan mu kam har mun manta da wai munje hospital yaran jama'a kuma mun kai su gida."

Ubaidu bai sake magana ba illa tsakin da ya ja, ya katse wayar.

Zaidu ma dariya yake yi, ya a jiye wayarsa a gefensa ya ci gaba da aikin da yake yi a systerm dinsa.


Sallaman samarin yayi gami da cewa su tafi gida, ƙannan su an kai su gida,kafin shi ma ya shiga motarsa ya dauki hanyar gida.


~~~~~~~~~


Wajan Mama ya fara wuce wa,tana ganinsa ta hau mita.

"Tun dazu muka fita tare da kai Ubaidu,amma kai sai yanzu ake ganinka, ina ka tsaya ko kuma nace ina ka wuce?"


Dan sosa gefen wuyarsa yayi dan shi bai cika son yiwa Mama karya ba amma yanzu ya zama dole ya suturta maganarsa.

ya kafin ya ce.
"Am so sorry my Momma, ina fita wani kiran ya taso min shiyasa dole na je nayi wancan aiki tun da nasan kun fita da Zaidu zai yi abun da ya kamata."


"Oh Allah to da Zaidun bai zo ba kuma fa?"

"Kiyi hakuri Mama tun da ya zo ai shikenan, yanzu ina Zaidun ya ke?"


Mama ta juya ta shiga kitchen tana ba sa amsa tana kiran sunan Hafiza.


Fita yayi ya je ya samu Zaidu zaune a kujera ya duƙufa akan systerm, sallama Ubaidullah yayi, Zaidu ya ɗago ya kallesa ya amsa, ganin sai wani cin magani yake yi yasa Zaidu ɗauke kansa shi ma ya ci gaba da abun da yake yi.


Can zuwa anjima Hafiza ta shigo da sallama, suka amsa kafin ta ce.

"Mama ce ta aiko ni na zo na tambaye ku, a kawo muku abincin nan ne ko zaku zo ku ci?"

Zaidu ya kashe systerm din dake cinyarsa ya tashi yana cewa.

"No my sister nikam a wajan Mama zanje na ci amma bansan wannan Yayan naku dan zafin kan ba"

Tsaki Ubaidullah yayi shi

3 / 25