Author : Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category : Romance
su ya sauka a airport din Bauchi State, ba tare da bata lokaci ba, suka nemi tazi sai a lokacin Zaidu yayi magana.
Maganar kuwa unguwar da za akai su ne.
Tun da Zaidu ya sauka a Bauchi faduwar gabansa ya tsananta, idonsa kuwa ya zubata kachokar a hanya.
Zuciyarsa bai sake tsinkewa ba sai da suka doso unguwar su Ubaidullah tun daga farkon layi yaga jama'a, nan yaji ya fara yaƙi da numfashinsa, drivern ne ya ce sai dai su sauka in ba haka ba, idan ya shiga ba zai iya fitowa da wuri ba.
Haka kuwa suka fito, KB ganin yanayin Zaidu yasa shi riƙe Zaidu wanda yake tangali kamar zai ci kasa.
Lokacin da su Zaidu suka iso an gama shirya Na'ila tsaf tana kwance a cikin Makara(gadon mulkin kowa kenan Allah kasa mudace Allah kasa mu gama lafiya) parlour aka fito da ita domin yan uwa da abokan arziƙi su mata addua.
Mama Anty Ummu Hafiza Ummi Umma Inna har da su Manal da Afnan, wanda tsoro ya gama kamasu.
Mama durkushewa tayi a gaban gawar tama rasa wani Addua ne zata fara karantowa, jikinta sai kyarma yake yi, cikin dauriya bakinta na b'ari ta ce.
"ALLAH YA YAFE MIKI NA'ILAH, NA YAFE MIKI DUNIYA DA LAHIRA, ALLAH YA SADAKI DA ANNABIN RAHMA S,A,W, ALLAH YA SAKA MIKI ƳATA!" daga haka Mama ta nemi maganar dake bakinta ta rasa abu ɗaya zuciyarta ke nanatawa shine kalmar Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!.
Anty Ummu cikin kuka ta yiwa Na'ila Addua tare da kalamai masu ban tausayi da karya zuciyar duk wani mai imani, haka ma su Afnan ba abarsu a baya ba sun yiwa kawarsu addua, su Umma da kowa da kowa anyiwa Na'ila Addua amma banda Hafiza da take bin mutanen wajan ido.
Ubaidullah da su Safwan suka shigo ya duƙa a gaban gawar Na'ila, Hannunsa ya ɗaga sama yana kwararo addua in da a karshe ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, kukan da Ubaidullah ya saka yayi dai-dai da shigowar su Zaidu KB da Zeey.
Turus Zaidu yaja ya tsaya yana kallon jama'ar dake wajan, da karfin ya ce.
"INNALILLAHI WA INNA ILAYHIRRAJIUN!"
Take Ubaidullah da sauran mutane wajan suka ɗago suna kallon Zaidu.
Da rarrafe Zaidu ya karaso gaban gawar yana binta da kallo kafin ya kalli Amininsa cikin fitar hayyaci ya ce.
"My Man !pls karka ce min Lovely ne kwance anan zuciyata ba zata iya dauka ba, pls Mama Umma ku bani amsa mana, dan Allah ina my lovely take" ya juya yana kallon Hafiza wacce ta kurawa mutane wajan ido tana bin su da kallo tamƙar tab'abb'iya, tun fitowar su bata ce komai ba, dan bata yarda yar uwarta bace kwance a gabanta ba.
"My sister ina lovely take nasan ke ba zaki min karya ba?"
Umma ta ce.
"Zaid ban son shashanci!"
Ummi ta ce.
"A'a bari a buɗe mata fuska su gani"
Nan Ummi da wata mata makwabciyar su Mama suka warware likafanin fuskar Na'ila ya bayyana, Zaidu kusan haukacewa yayi ganin abun bana kare bane yasa su Umma sake rufe fuskar Na'ila sannan suka yiwa mazan dake waje magana azo a dauke ta, ganin haka yasa Hafiza sakin ihu gami da riƙe makaran gam, tana cewa.
"Wayyo Allah na! Wayyo na shiga ukuna! Ina zaku kai min yar uwata! Dan Allah ku ajiye min ita, ba mutuwa tayi ba bacci fa take dan Allah ku ajiye min yar uwata! Wayyo Allah zan mutu, Na'ilata! Wayyo Allah Na'ilata! Yar uwata! Dan Allah karku tafi min da yar uwata! Ina zaku kai min ita mugaye azzalumai! Mama kina gani ko? Yaya zasu tafi min da Yar Uwata! Anty Ummu kice su ajiye min yar uwata!"
Da kyar aka b'anb'ari Hafiza daga gawar Na'ila aka fice, ana fita da gawar Mama ta yanki jiki ta fadi, Anty Ummu itama tayi baya-baya ta zube kasa aka bar Hafiza tana ta kururuwa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Comments
Share
Momyn Ahlan
Taku ce😟
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)
*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻
*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻
_dedicated to my brother_
*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~
_my wattpab_@Fateemah0
_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*_jinjina da dubun gaisuwa gareku masoyana dan Allah ku ce min kun amsa 🙋🏻 Alkhairin Allah ya kai muku har garin da kuke har cikin ɗakunar ku, masu cmmnts ina yi muku sonso domin Allah, marasa cmmnts kuma na gaisheku 🙋🏻, babbar kyauta ga wa inda suke following dina a wattpad, jinjina gareku masu min cmmnts a wattpad 🙋🏻, kar de ku manta da cewa Momyn Ahlan TAKU CE 😁_*
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*page°°°°°46&50*
Da sauri jama'ar da suke wajen suka yo kan Mama aka hau jijjigata amma shuru, cikin Kuka Ummi ta ce.
"Ina ga fa asibiti zamu kai su, ina Abi'at..." maganar da Ummi bata karasa ba kenan ta ga Abi'atu shame-shame ita ma a kasa, salati Ummi ta saka tana share hawaye, nan dai matan da suke wajan suka taimaka aka ɗaga Mama aka kwantar da ita akan dogon kujera aka cire hijabin dake jikinta aka hau mata fifita ana yayyafa mata ruwa.
Haka ma Anty Ummu da Abi'atu ruwa aka yayyafa musu suka farfaɗo,tukunna aka maida hankali kan Mama sosai ake yayyafa mata ruwa ana mata fifita, amma ina kamar ba a yi mata komai, wata mata ce a cikin yan gaisuwa ta ce.
"Gaskiya ni a nawa shawaran ya kamata ace a kira Likita yazo gida ya dubata, dan gaskiya bai kamata a kaita asibiti ba, hankali ne zai rabu ko ya ku ka ce?"
Umma ta ce.
"Eh haka ne akwai wata kawata Likita ce tana aiki a Rimi Hospital bari na kirata" Umma ta ɗaga waya ta kira kawarta cikin sa'a kuwa ya shiga ta shaida mata cewa zata zo kafin suka yi Sallama.
A daki kuwa Hafiza ta gama haukacewa Inna da wata tsohuwa su ne suketa kokarin lallashin Hafiza amma ina kamar ba da ita suke ba, ihu kawai take yi tana cewa a dawo mata da yar uwarta.
Inna ta kamo fuskarta ta ce.
"Hafiza!HafizaHafiza! Kalleni nan kalli fuskata, ina so na tambayeki ki jini da kyau, kina jina?" ta gyaɗa kai alamun eh tana fizge-fizge.
Inna ta ce.
"Hafiza kin yarda da Allah?" ta gyada kai.
"Kin yarda kullu nafsin za'ikatil maut ne?" ta sake gyaɗa kai.
"Kin yarda da kaddara mai kyau da marar kyau?"
Nan ma sake gyaɗa kai tayi.
Inna ta ce.
"To Hafiza tun da kin yarda da Allah kin yarda da akwai mutuwa kuma kowa zai mutu babu wanda yazo zama a wannan duniyar, kuma kin yarda da kaddara ina so ki daina yiwa yar uwarki kuka kina ihu, itama ba zata so haka ba, ki dinga mata addua Allah ya jikanta da rahma Allah yasa can yafi mata nan kinji? Barin ma Na'ila baki ga yadda tayi jama'a bane, ko ba kiji ance mutanen da suka yi mata sallah sun kai kusan dari da wani abu bane? Ai abun farin cikin mu ne, uwa uba kuma wasu azzalumai ne suka yi sanadiyar barinta duniya kinga kuwa da yardan Allah ita kam ta dace kinji? Ki daina ihu da kukan nan ki tayi mata addua kina yawan fadin kalman Innalillahi wainna ilayhirrajiun! Kinji Hafiza?"
Ta ce.
"To Inna na bari" shuru tayi na wasu lokaci kafin zuwa anjima da ta ɗaga kanta ta hango hoton su wanda suka yi da Sallah sun rungume Juna su na dariya, nan Hafiza ta sake birkicewa ta sake sakin wani ihun.
"Wayyo Allah Yar Uwata!! Wayyo Na'ilata dan Allah ki dawo!"
Inna hakurinta da dauriyarta ya kare dan haka suka fice tana share hawaye aka kulle Hafiza da su Afnan a daki su na kuka babu mai ce ma dan uwansa yi hakuri.
Parlour wajan karban gaisuwa Inna suka koma suka zauna wata makwabciyar su take tambayar Inna akan cewa Hafizan tayi shuru kuwa, Inna ta ce.
"Ina kuwa , da kamar tayi shuru da muka lallasheta amma tana ganin hotonta da yar uwar ta sake birkicewa" Matar ta girgiza kai gami da cewa.
" Allah Sarki! Dole ta fita hayyacinta, kullum zaki gansu tare, idan makaranta ne ko aiken su aka yi, ko wani waje ne tare zaki gansu, gashi itama Hafizan yarinya ce bata saba da mutuwar ba, tun da ko lokacin da Mahaifinsu ya rasu su na yara ne, Na'ila kuma basu taba rabuwa ba, ko wani garin zasu je indai kwana ne tare suke tafiya, amma lokaci daya mai yanke kauna ta yanke a tsakaninsu dole sai an haɗa mata da rubutu, gashi irin wannan mutuwa na farat ɗaya tafi shiga jiki, Allah na tuba gwanda ace mutum ka ganshi yasha jinya a gabanka,amma ka rabu da yaro lami lafiya adawo maka da gawa, abun akwai tashin hankali gaskiya, Allah dai ya karawa yan uwanta hakuri da juriyar rashinta" aka amsa da Amin.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Bayan an yiwa Na'ila Sallah a kofar Masallacin Jumma'ar dake unguwarsu kafin suka wuce maƙabarta.
Aka siya kabari aka yi komai,amma kafin nan sai da aka faɗi sunanta aka rubuta da date din da ta rasu da cutar da ya yi sanadiyar mutuwar tata da shekarunta.
Ubaidullah da Zaidu da KB Safwan da wasu samari Uku tsaye a gefe, wani Malami ya ce.
"Ita mai rasuwar tana da miji ne?" Malam Liman ya amsa da.
"A'a"
"To ina Mahaifinta?"
Ubaidullah ya rintse ido yana karanto "Innalillah wa inna ilayhirrajiun!"
Wani ƙanin Baban su ne ya ce.
"Mahaifin su ya rasu da ɗaɗewa"
Malamin ya ce.
"To ina wani ɗan uwa makusancinta ya matso kusa ya sakata a kabarinta"
Jikin Ubaidullah ya dauki kyarma, sai da Abba da Baba (Yayan Baban su) suka dafa Ubaidullah kafin ya wuce ya kamo kanwarsa yana yi mata kallon karshe a cikin likafani, zuciyarsa ce ke cewa.
"Yanzu Na'ilata kece wannan? Kece zan shinfiɗaki a karkashin kasa?" nan hawaye ya shiga wanke masa fuska har yana ɗiga akan likafaninta, babu abun da ya faɗo masa sai ranar da suka fita ya jibgesu ita da kawayenta, kuka sosai Ubaidulllah ke yi yana kwantar da ita a cikin kasa, yana gama shinfiɗeta ya ce.
"Allah yasa Annabi S,A,W, yasan da zuwanki Kanwata Allah yasa Annabin Rahma S,A,W, ya karbi baƙuntarki, ki yafe min Kanwata nima na yafe miki!" ya karasa yana kuka har da sheshsheƙa.
Zaidu ma Kuka yake yi kamar ranshi zai fita ya duƙa yana cewa.
"Allah ya haskaka ki My Lovely, Allah ya yafe miki..!" kasa karasa sauran adduar yayi kuka yaci karfinsa nan aka hau mai da kasa akan Na'ila yayinda Ubaidullah da Zaidu suka koma gefe suka rungume juna gam su na kuka mai ban tausayi.
Tun su na kallon likafanin Na'ila har aka gama tula mata kasa a kai ya yi tsini.
( _Hummm Rayuwar kenan fa, ta bakin hausawa suka ce karshen alewa kasa, duk kudinka duk mulkinka dun kyawunka, duk kasaitar ka, duk izzarka, da zarar ance wannan ran ya fita a gangar jikinka nan ne madakatar ka, Allah kasa mu gama da duniya lafiya Ameen_)
An juma ana yi mata addua kusan awa daya kafin jama'a suka fara watsewa.
Sai da kowa ya watse aka bar Ubaidullah Zaidu KB Safwan Abba da Abokan Abba mutum biyu.
Da kyar aka lallashi Ubaidullah da Zaidu suka tashi suka baro maƙabartan, su na tafiya su na kallon maƙabarta har suka daina ganinta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A gida kuwa Likita tazo ta duba Mama har anyi mata karin ruwa, ta farfado amma bata um bare um um, saboda hawan jininta ya tashi sosai.
Hafiza kuwa sai da aka yi mata alluran bacci kusan biyar kafin bacci ya dauketa.
Su Ubaidullah su na dawowa daga maƙabarta nan fa sabon kuka ya tashi.
Anty Ummu ta shiga dakin su Na'ilan tana kallon pic dinsu da Hafiza, kuka Anty Ummu keyi kamar ranta zai fita tana cewa.
"Yanzu shi kenan fa kin tafi kenan, Allah sarki kanwata ashe ban kwana kika zo min jiya da safe, Allah sarki Na'ila Allah ya gafarta maki kanwata" ta ci gaba da kuka.
Ubaidullah part dinsa ya wuce kai tsaye bayan an dawo daga maƙabarta ana parking din mota ya fice, Zaidu da KB suka bi bayansa.
Yana shiga parlour ya fara fashe-fashe yana ihu, ba mutuwar bane abun da yafi ɗaga masa hankali da ɗimauta shi ba, a'a yadda mutuwar kanwar tasa ta kasance yasan mutuwa dole ce, baƙin ciki ne ke cin zuciyarsa idan ya tuno sanadiyar abun da ya kai kanwarsa kasa yau.
A rayuwarsa ya tsani yaji kalma mai kaman ceceniya da *FYAƊE* idan aka kawo case akan fyaɗe sai inda karfinsa a kare amma sai gashi kanwarsa sanadin fyaɗe ta mutu ta rasa ranta,sunyi sanadiyar kaita cikin kasa, taya zai yafe? taya zai daina yaƙi da masu fyaɗe? taya ba zai kara tsanar fyaɗe ba?
Taya zai gansu? Gashi bai san su ba, bai san ina zai samu mutane bakwai din nan ba, idan ma yace bincike zai yi ta ina zai fara? Ita ce ya kamata ta gaya masa suwaye amma Ubangiji ya karb'i abunsa hannunsa biyu ya zuba a kansa yana kuka mai ciwo, babu abun da ya sake faɗo masa rai sai lokacin da take fizge-fizgen azabar fitar rai take ce masa.
"Yaya su bakwai ne!"
Ihu Ubaidullah ya sake gami da dauƙar glass din table din da ya fara nan take ya farke hannunsa dashi, kuka yake ina faɗin.
"Ina zan gan kuuuuu!! Wayyo Allah ni Ubaidullah! Ya Allah kabani ikon cin wannan jarabawar da ka ɗaura min! Lokaci ɗaya na rasa abu biyu masu mahimmanci a gareni mafi soyuwa wanda ka karb'eta a gareni itace kanwata, Ya Allah hakika ina son yar uwata amma ka fimu sonta, Allah kai ne ka halicce mu, kuma dole zamu koma gareka, ya Allah nasan kanwata daka ɗauketa yanzu bata yi sauri ba, mu kuma daga barmu ba muyi jinkiri ba, Ya Allah ka sassauta mana raɗaɗin rashin baiwarka Kanwata Na'ila, ya Allah ka bayyana min ta inda zan ga azzaluman bayinka, hakika bazan gushe ba, bazan gajiya ba wajan nemo wanda suka aikata min haka na hukuntasu da hannuna ko da kuwa shine abun da zanyi na karshe a rayuwata, Ya Allah ka nuna min suuuu!!" ya zube kasa gami da kifa kansa akan kujera ya ci gaba da kuka.
Tun da Ubaidullah ya fara magana Zaidu da KB suke tsaye su na jin maganar tasa tana shiga kansu ɗaya bayan ɗaya, Zaidu ne ya matso kusa da Ubaidullah idonsa jajur ya duƙa gaban Ubaidullah cikin dasheshshiyar muryarsa wanda yasha kuka ya ce.
"My Man, ban fahimci maganganunka ba, ina bukatar karin haske, meya samu lovely? Me aka yiwa lovely? Kashe! Lovely aka yi!? Sannan suwaye suka kasheta? Duk tambayar da na yi maka ina bukatar amsar su!?"
Shima Ubaidullah ɗaga rinannun idanuwansa yayi wanda idan ya kalleka dasu zaka iya rantsewa idanunsa basu taba fari ba, miƙewa tsaye yayi cikin ƙaƙƙausar murya ya ce.
"Zaidu Kasheta suka yi!"
Shima Zaidu mikewa yayi jikinsa har na b'ari cikin zaƙuwa ya ce.
"Su waye?"
Hannu Ubaidullah ya ware.
"Nima abun da nake tambaya kenan, SU WAYE!? Zaidu abun da na fi tsana a rayuwata wai yau shine ya faɗo akan kanwata, Zaidu FYADE FA AKA YIWA KANWATA! FYAƊE!FYAƊE!FYAƊE!"
Saurin toshe kunnuwansa Zaidu yayi take ya ji jiri na ɗibarsa maƙogoronsa ya ji har wani ɗaci-ɗaci take masa, kishi haushi baƙin ciki duk suka haɗe masa waje guɗa har wani duhu-duhu yake gani.
"Whattt! Fyaɗe!? Fyaɗe!? Fyaɗe!? Wa matar da na zauna jira zan aura din? Yanzu lovely fyaɗe aka mata?" yayi maganar hawaye na sake wanke masa fuska yana kallon Ubaidullah.
Jinjina kai Ubaidullah yayi ya ce.
"Ta ce mutum bakwai, amma bata faɗa min su waye mutum bakwai din ba, amma abu ɗaya na sani shine zan bazama neman mutum bakwai din nan na kashesu da hannuna duk da yanzu ni ba jami'i bane"
KB ya ce.
"Innalillahi wa inna ilayhirrajiun! Hakika wa inda suka aikata abun nan basu san su wa suka tab'o ba, basu san sun taba yar gidan soja kanwar soja wanda yake sa ran auranta soja ba, amma komai muyi hakuri mu kuma dage da addua Allah ba azzalumin bawansa bane sai dai bawa ya zalunci kansa amma zasu gane basu da wayo, ni dai abu ɗaya na sani shine duk rintsin rayuwa duk tsanani duk wuya muna tare da kai Ubaidullah"
Kuka suka saka a tare gami da rungumar Juna.
Sallama aka yi, wanda ya saka su sakin junansu suna share hawaye, Abba ya girgiza kai ya ce.
"Haba Ubaidullah, zaman gaisuwar kanwarka fa akeyi amma ka dawo ciki kana kuka kayi hakuri dan Allah mu dauki kaddara kowa lokaci yake jira Allah yasa Na'ila ta huta"
Suka amsa da ameen, kafin Abba ya saka su a gaba suka koma kofar gida ana karban gaisuwa amma kallo ɗaya zaka yiwa Ubaidullah shi da Zaidu ka fahimci kalar tsananin tashin hankali da damuwar da suke ciki.
Sai bayan sun fita ne KB ke sanar da Ubaidullah ai da Zeey suka taho nan KB ya basu labarin yanda sukayi da General Of The Army, girgiza kai Ubaidullah yayi gami da cewa.
"Dan Adam kenan, ba komai rayuwa ce, ta ishe kowa ishara, Hanan kuma Allah ya saka mata da alkhairi.
Tun da suka dawo daga maƙabarta basu koma cikin gidan ba,dan haka Ubaidullah bai san halin da Mama take ciki ba, sai da aka yi sallar la'asar tukunna suka shiga cikin gidan dan su gaisa da Zeey, nan Ubaidullah ya ga Mama tamƙar ba ita ba harta canza kamanni, nan hankalinsa ya sake tashi fiye da na da.
Hafiza ma haka ta koma bata um bata um um sai illa rungume pic dinsu da tayi a ƙirjinta duk wanda ya ganta sai ya zubar da hawayen tausayinta, harta Anty Ummu ta koma tausayin Hafiza.
Da dare kuwa ta shiga Kitchen dan ta dauko ruwa ma wata mata nan ta ci karo da tashin hankali.
ba komai bane illa girkin da suka fara shiryawa Yayansu babu wanda ya taba abinci yadda suka ajiye haka yake, da gudu da kuka ta fice tayi hanyar part dinsa.
Suna zaune jingum-jingum shi dasu Zaidu, sai ga Hafiza da Kuka kamar an wullota, tana zuwa ta faɗa jikinsa, ta ƙanƙame shi tana kuka mai mutukar tashin hankali.
Ɗauriya iya ɗauriya Ubaidullah ya ɗaure kafin ya ɗaga Hafiza daga jikinsa yana share mata hawaye yana girgiza mata kai alamun tayi shuru, tama kasa magana illa hannu da take masa nuni dashi akan