COLONEL UBAIDULLAH by Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢

Author :  Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category :  Romance

Chapter   17 / 25

48K to 51K   out of 74.6K words

ya cinye maka idanu?" ta faɗi tana murguda masa baki.


"Ki wuce ki je ki sa kaya bana cike da iskanci!"


"Ni babu kayan da zanje na saka bayan wa inda suke jikina, to wai ma ina ruwanka ne kam? Da shigar da nayi, idan na gadama na fito ma tsiraran miye damuwarka,balle ma ba tsarara na fito ba da kaya a jikina, ni da nake ƴar abu kuma yarinyar yar firit barni nayi shigan da raina yake so, kuma wallahi idan na....." maganar Abi'atu ne ya tsaya mata a maƙogoro bai karasa fitowa ba, sakamakon murɗe mata hannu da Ubaidullah ya yi, ta saki kara "wayyo Allah Mama hannuna, wayyo Mama zai karyani."



"Eh ba dole ki ambaci sunan Mama ba, tun da kin lashe mata zuciya, duk babu wanda yake ganin laifinki,ai basu san marar kunya suka ɗaura min ba."


Duk da zafin murɗe mata hannu da ya yi, ba shi yasa bakinta mutuwa ba.

"Dama INNA ta fada an hadani da mugu, ga shi yana shirin naƙasani, yo da kake maganar na lashe zuciyar Mama idan ma hakan ne alhamdulillah naji dadi, su Mama basu ga munina ba ehe."


"Dama taya zasu gani tun da ba zama suke yi dake ba?"


"Ai kuwa sun fika zama dani, mutum dai marar godiyar Allah dama shi ai ba a taba masa abun....." cak maganar ta tsaya sakamakon bakinta da Ubaidullah ya cafka yana aika mata da wasu zafafa kiss, sumar tsaye Abi'atu tayi jikinta ya dauki rawa, kafafunta suka gaza daukarta nan tayi yunkurin sulalewa kasa ya bi ta,kokarin turesa take yi amma ance karfin mace da na namiji ba ɗaya bane, kuma ya mata haka ne dan ya yi maganin rashin kunyar da take masa, dan wani lokacin idan su na cacan baki da ita har mamakin kansa ya ke yi, amma yana cafkar bakinta wani dadi ne ya ziyarce shi har ya manta da in da yake da wacce yake tare, ga humra da ta mulka a jikinta mai fizgar hankali.


Tun tana turesa tana kai masa duka har ta fara kuka.

Ubaidullah baya cikin hayyacinsa, karar wayarsa ce ta dawo da shi hankalinsa dan kuwa ita ce ta katse masa hanzari, da kyar ya saki bakin Abi'atu ya mirgina gefe idonsa lumshe yana sauke ajiyar zuciya, yana ɗagata ta mike da gudu ta yi bedroom har da saka key, dariya ce ta kwace masa ya ce.
"Ashe ke ƙaramar marar kunya ce, nan gaba abun da zan din ga miki kenan idan har zan faɗa ki fada" daga bedroom din ta ce.
"Mugu an gaya maka tsoranka naji? Kawai dai na ga kana shirin aikata abun kunya ne da yar abu, kuma wallahi kaci bashi abun da ka min"


Ubaidullah zai kuma yin magana wayarsa ta kuma yin kara, a hankali ya saka hannu ya janyo wayar dan jikinsa a mace yake murus, da jajayen idonsa na jaraba ya kalli screen din ya ga sunan My Man na yawo, da kyar ya dauki wayar ya saka a kunne ya kasa magana, cikin zolaya Zaidu ya fara gyaran murya mai cike da tsokana, Ubaidullah ya fahimci abun da yake nufi dan haka ya ja tsaki, cikin dasheshshiyar murya ya ce.
"Ka ga bana son iskanci, fadi abun da ke ranka ko na kashe wayata"


"Dama tun da na kiraka kam ai dole na fadi amma dai ina Madam bata kusa ko? Ko tana kusan ma ai abun farin'ciki ne" cikin tsokana Zaidu ke magana, shuru Ubaidullah ya yi, bai bawa Zaidu amsa ba, Zaidu ma baya da lokacin tsayawa su yi shirme tun da ga su General a wajan, nan ya shiga zayyano masa abun da ya faru tun daga AtoZ amma abun mamaki Zaidu na gama basa labari sai cewa ya yi.
"To sai aka yi me?"
"Sai aka yi ana so ka dawo bakin aiki mana"
"Bazan dawo ba! Na ri ga da na hakura da aikin soja!"
"Karya kake yi Ubaidullah! Sai dai ka fada ma wani amma ba dai ni ba, na san ka, ka sanni!"
"Ko da zan ci gaba da aikin soja ba dai a garin abuja ba, ba zan dawo barracks din abuja ba Zaidu pls ka kyaleni"
"Pls Ubaidullah ana bukatar taimakonka" nan Zaidu ya ba wa Ubaidullah labarin yan matan da aka yi garkuwa dasu, murmushin takaici Ubaidullah ya yi, ya ce.
"Sai da amfanina yazo kafin za a nemeni ko?"
"No, Ubaid.."
"Bana son jin komai Zaidu, magana ɗaya ce, bazan dawo ba!" ya katse wayarsa, ya cillar da ita ya rasa me ke masa dadi, tunanin yan matan da aka yi garkuwa dasu ya shiga yi, yanzu ace akwai kanwarsa a ciki ya zai ji? Kuma yasan dole fasikanci za a din ga yi dasu ana bata musu rayuwa ta hanyar yi musu fyaɗe, rintse ido ya yi, take a ransa ya ji babu dadi saboda tuno halin da kanwarsa ta rasa rayuwarta, kwalla ne ya cika a idonsa, dan Ubaidullah duk fadin ransa yana da rauni sosai ta wannan fannin, ya shiga tunanin mafita, kuma baya son komawa barracks din nan, tashi ya yi ya fice ya bar gidan gabaki daya, dan zafi uku ne suka hadu masa waje guda.




Duk yanda Zaidu suka yi da Ubaidullah su General sunji,ya yinda Major Usman ya ce.
"Kunsan dole ne ya ji babu dadi, dama kuma ga shi yana da mugun zuciya, ni a ganina ya kamata mu shirya tafiya gobe ko jibi muje har Bauchi mu basa hakuri a matsayinmu na manya wanda kuma basu kyauta ba, idan ba haka ba rayuwar yan matan nan su na cikin hatsari, kuma da an rasasu durkushewar barracks din nan yazo" kowa ya yi na'am da shawarar Major Usman, in da aka ce su General da brigadier lieutenant colonel da Major General zasu je har gidan su Ubaidullah,da haka meeting din ta watse in da Zaidu da KB suka din ga godewa Zeey su na jinjina mata, duk inda ka wulga zancan Ubaidullah ake yi yau a barracks, sai Allah yawadaran masu hali irin na Rumaisa da S Ema ake yi, masu son shi su na fatan sake ganinsa a barracks very soon.


Ko ba komai yau Ubaidullah an wanke shi da ga zargi, kuma ana jira ya dawo ya maka su a kotu.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




Sai dare Ubaidullah ya dawo, part din Mama ya wuce ya sameta zaune a dakinta, nan ya shiga ya zayyano mata komai bai boye mata komai ba, Mama ta ce.

"Duk hukuncin da ka yanke dai-dai ne, amma ina so ka je kayi tunani da kyau, idan zaka koma fyn idan ba zaka koma ba duk daya, Allah dai ya zaba mana abun da yafi alkhairi" ya amsa da ameeen sannan ya mata sallama ya wuce part dinsa Mama murmushi kawai tayi ta bi bayansa da kallo dan tasan har kwanan gobe yana son aikinsa na soja.


Ko da ya shiga yau bai ga abokiyar tawayen tasa ba, kuma shi ma bai bi ta kanta ba, dan yana bukatar hutu da tunani.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Da washe gari ma bayan sun gama cakwakiyarsu ya fice dan yau yana so ya je ya dubo shagunarsa ne.


Da yamma ya dawo yana dawowa ta tashi da gudu ta yi bedroom, kuma kayan da take sakawa kenan yanzu guntun wando da yar fingilar riga.



Bai jima da shigowa ba ya sake fita, bayan ya sake fita tana daki ta ji ana zabga mata sallama da gudu ta fito da ta ji muryar mai mata sallamar ba kowa ba ce face Shafa'atu rungume juna suka yi cike da murna kafin Abi'atu ta saketa tana harararta.


"Wallahi Anty baki da kirki inace sai yau kikayi niyyar zuwa inda nake? Wata na nawa da aure?"


"Kai mitau, ai wata ba shekara bane, balle ki sakani a gaba da mita, tun da yanzu nazo ai shi kenan, bikin da ba muyi shiri ba kawai sai ji muka yi anyi wuff da ke" suka kwashe da dariya nan suka hau hiran yaushe gamo, sai dare Safwan yazo ya dauki Shafa'atu ya kai ta gida.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Da washe gari misalin karfe goma na safe, Ubaidullah yana shirin fita ya ji, jiniyar motar sojoji na tashi a gate dinsu, abun ba karamin mamaki ya ba shi ba, ba zato ya ga shigowarsu Zaidu da KB kafin nan sai ga Manyan sojoji, da sauri Ubaidullah ya karaso gabansu ya kame yana sara musu dan Ubaidullah yana da ladabi.


Nan ya musu jagora har parlourn Mama, kafin kace me an cike musu gaba da kayan motsa baki Abi'atu da Hafiza.


Bayan an gaisa suka ɗan taba kayayyakin motsa baki aka kawo musu, Mama zata mike nan Major Usman ya dakatar da Mama, sannan suka zayyano wa Mama da Ubaidullah abun dake tafe dasu, sannan suka hau ba wa Ubaidullah hakuri su na masa magiya, ji yayi duk sun dauresa da jijiyoyin jikinsa, harta Mama sai da ta sa baki da kyar Ubaidullah ya ce ya hakura nan ma sai da Zaidu ya saka baki, nan take aka miƙawa Ubaidullah takardan komawa bakin aikinsa tare da bindigarsa da sabbin kakinsa sannan aka ce masa jirgi na jiransa gobe sojoji zasu zo su dauko sa, sun jima a gidan kafin suka je gidansu Zaidu aka gaisa sama-sama dan sun bata lokaci gidan su Ubaidullah dan yau zasu sake komawa Abuja tunda a jirgi ne ba bata lokaci.



Har airport Ubaidullah ya rakasu sannan aka bar masa wasu sojoji wanda zasu daukesa su kaisa airport gobe, rungume juna suka yi shi da abokansa sannan suka daga masa hannu alamum sai sun gan shi a barracks gobe, murmushi kawai ya yi, sai da jirginsu ya daga kafin ya dawo gida ya ba wa sojojin da aka bar masa umarnin su tafi barrack din bauchi gobe idan ya shirya zai neme su,suka amsa cike da girmamawa.



Ba karamin dadi Ubaidullah yaji ba, har sai da ya yi hawaye, Mama da Hafiza Anty Ummu Matarsa Abi'atu da iyayenta da iyayen Zaidu babu wanda bai masa murna ba.



Da dare yana kwance Abi'atu tazo ta same shi ta zauna kusa dashi yau ba kamar kullum ba ,cikin sanyin murya ta ce.
"Hakika nayi farin'ciki da komawar ka aiki Allah ya taimaka ya bada sa'a, Allah ya daɗa daga darajanka" sosai ta din ga kwararo masa addua, wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar shi, har da yi mata murmushi ya amsa da ameen gami da cewa ya gode, murmushin itama ta yi ta tashi ta koma dakinta.




Da washe da safe Abi'atu ta roƙi Ubaidullah tana son komawa aikinta, nan ya amince mata tayi masa godiya, jirginsa karfe uku zai tashi, Abi'atu ta shirya har ta je aiki abun ta.




A safen ranar Hafiza ta fita ta kai sako gidansu Abi'atu wa Ummi.



In da wasu samari mutum bakwai a baƙar mota sun shigo layin sukayi arba da Hafiza tana tafiya ta fito daga gate din gidansu zata koma gidansu Abi'atu Mama ta aiketa, wani daga cikin samarin da suke motar yace.




"Kai Bahba kalli wancan yar flawern"

Wani ya ce.
"Kai daga ganinta zata yi dadi, zata kai yanda ake so" wani ma ya ce.
"Amma fa kamar mun taba operation a wannan gidan fa?"
"Anya kuwa?" cewar wani daga cikin su.
"Eh mana Bahba ka tuna mana , nidai ban manta ba wata yarinya tasa farin less muka sunkuceta a nan kofar gate din, kuma na ga su na kama ko dai yar uwarta ce?"

"To kai Bangis yaushe ka fara tuna yaran da muka farke?" magana suke yi irinta yan iska b'ata gari.


"Nima dai ban sani ba, amma dai nasan na tuna yarinyar."


"To dai ku bar wannan maganar mu san yanda zamu dauke wannan yarinyar ko yau ko gobe in dai tana fita" haka kuwa suka zauna suka tsara plan.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Karfe sha biyu Abi'ah ta dawo daga aiki, gidansu kuma ta wuce dan an fara shirye shiyen bikin Yayanta, sai karfe biyu da rabi ta koma gida ita da kanta ta hadawa Ubaidullah kaya suka yi sallama, da kuka suka rabu da Hafiza, har Abi'atun ma sai da tayi kuka a boye, ba tare da ya gani ba, shima duk sai ya ji ba dadi, da haka dai ya shiga mota sojoji suka ja shi suka dauki hanyar airport.



Da Ubaidullah ya tafi Abi'atu ma, magana ta yiwa Mama zata je su gaisa da wasu y
Yayun Babanta Mama tace babu damuwa sai ta dawo itama zata shigo anjima.



Abi'atu tana tafiya tayi gidansu ba jimawa Hafiza tacewa Mama itama zata bi Abi'atun gidansu dan gidan ya mata Shuru Mama ta amsa da to Hafiza sai nazo.



Fitowa Hafiza ta yi, dai-dai lokacin da wannan samari su bakwai motar su tasha kwana, nan suka hango Hafiza tana tafiya, da sauri suka fara dan jan motar tasu, itama kuma har ta sha kwana wajan gate din gidansu Abi'atu, daidainan Abi'atu da Safwan suka fito a mota an bude musu gate zasu karbo sako me zasu gani? Wasu kartin maza ne suka finciki Hafiza suka ɗurata a mota ihu Hafiza ke yi tana tirjewa tana neman taimako suka toshe mata baki suka turata a motar da karfi.



Cikin ɗimauta Abi'atu da Safwan suka saki ihu, da mugun gudu Safwan ya take mota ya bi bayansu sannan ya cewa Abi'atu ta kira Ubaidullah idan jirginsu bai tashi ba ya dawo, duba wayarta tayi taga ashe ma bata da lambarsa, ta ce.
"Yaya babu lambarsa anan"
Wayarsa Safwan ya wulla mata ya ce kira shi da nawa, nertwork din wayar Safwan ce ta dauke, da sauri ta dauki lambar a wayar Safwan ta shiga kiransa lokacin har ya fara taka matattakalar bene ya ji wayarsa na ringing ya dubawa ya ga bakuwar lamba ya yi tsaki bai daga ba.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️ Cakwakiya.



Momyn Ahlan taku ce👍🏻
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)

*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~

_my wattpab_@Fateemah0

~~•~~•~~~•~~•~~•~~~•
*_Tun daga wannan page din har izuwa karshen wannan book din na ku ne my 5 stars._*✨

*My Doter Samira bint Abdallah*✨💋
*Dear Fatima Bintu Sagir*✨💋
*Sisina Farhat Mrs M'J*✨💋
*Antyn Ahlan Princess (Nafeesat)*✨💋
*Habibty احلام فاطمة*✨💋

💞💞 Naji dadin karar'ku a gareni son so domin Rabbi, Allahu ya taya muku.💞💋🙌🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*_Na so na kira sunayenku wa inda suka min sharhi a page din da ya gabata kafin wannan amma Allah bai yi ba, dan haka duk wacce ta min sharhi ta saka a ranta wannan page din kyauta ce gareta, kuyi yadda ku ke so da page din dan naku my ppl's ina so ku sani ni Zahra Abdul Momyn Ahlan taku ce inayinku._*💋

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


*page°°°°°76&80*



Kira Abi'atu ke yi ba ƙaƙƙautawa, sai da ta yi masa kira wajan takwas amma bai daga ba, dan lokacin da ta yi masa kiran farko da ya gani yayi tsaki sai ya mai da wayar cikin aljihun wandonsa, ya juya yana ba wa sojojinsa umarni.


Kukan tashin hankali Abi'atu ta saka gami da cewa.
"Yaya Safwa bai ɗaga ba fa, wayarka kuma netwrk ya dauke ya ƙi kawowa kwata-kwata!"

A fusace Safwan yana jan mota yana kan bin wa inda suka kwamushe Hafiza ya hau saukewa Abi'atu ruwan bala'i yana mata masifa dan hankalinsa a tashe yake ,domin ko da ya iskesu ance sarkin yawa ya fi sarkin karfi, su bakwai, shi ɗaya ai ba zai iya ba, idan aka taki rashin sa'a suka kashesa suka jinkiɗar da Hafiza da Abi'atun ai an bata goma ɗaya bata gyaru ba, sannan ace zai fara biyawa kiran yan sanda ai kafin su iskesu sun yiwa Hafiza Illa idan ma an kamasun kenan, dan yasan by tym da zasu iso idan aka ta ƙarƙare sun gudu.



"Iskancin banza da hauka! Numbern Mijinki amma ba ki da shi?Mijinki fa!? Da ace kuna da number juna har za ki din ga yi masa wannan kiran bai ɗaga bane, da ace kuna da numbern juna ya ga wannan kiran da kike masa yasan babu lafiya, ai sai ki ci gaba da kira, ko kuma ki nemi nerwrk a wayana ki ci gaba da kira, in kuwa ba haka ba, muna karasawa sai su kashemu duka a huta, mtswwww!"
Kira Abi'atu ta ci gaba da yi tana kan kuka.


Ubaidullah jirgi ya shige ya zauna, ana jiran jama'a su gama shiga jirgi ya tashi da zarar lokacin tashinsa ya yi, dabara ce ta faɗowa Abi'atu da sauri ta tura masa saƙo da cewa.
" _*KAYI WA ALLAH DA ANNABI S,A,W) KA DAUKI WAYAR NAN, IDAN HAR BA KA ƊAGA BA, ZA A RASA RAYUKA (ABI'ATU CE)*_" ta tura masa, Ubaidullah ya ciro wayarsa yana shirin kasheta gaba ɗaya ya ga tarin miss calls da numbern dazu, mamakinsa bai gushe ba sai ga shigowar saƙo buɗe sakon ya yi, ya karanta sannan ya shiga wajan history yana shirin kiranta sai ga kiran nata na sake shigowa, ɗagawa ya yi, muryar kukan ne ya fara kaiwa dodon kunnensa naushi, gabansa ne ya shiga bugawa a kiɗime ya ce.
"Abi'ah! Meya faru? Meya sameki? Wa ya taba miki?" cikin sheshsheƙar kuka ta ce.
" *DAN ALLAH! DAN ALLAH! IDAN HAR JIRGIN'KU BAI ƊAGA BA KA DAWO AKWAI BABBAR MATSALA AN DAUKE HAFIZA!*" wani wawan zabura Ubaidullah ya yi ya miƙe da gudu yana buge mutane, yana sauƙowa daga step din jirgin Sojojinsa ne suka kallesa "Mota" shi ne kawai abun da ya iya furtawa, nan aka miƙa masa Mota ya shige ya bata wuta, cikin tashin hankali Ubaidullah ya ce.
" *SU NA INAAAAA! INA ZASU KAI MIN ƘANWATA!?*"
"gamu nan mu na kan bin su ni da Yaya Safwan, kayi amfani da location, Dan Allah kayi sauri kar su cutar da ita, ga mu nan dai sun dauki hanyar fita daga cikin gari" da sauri Ubaidullah ya yi connecting yana bin su da gudu, sai ka ce zai ta shi sama jikinsa sai bari yake yi, hankalinsa idan ya kai dubu to a tashe yake.


Su na ta binsu har suka yanki kwanar bayan gari, sun dan yi tafiya kaɗan cikin wata yar jeji, kafin suka iso wani kangon gida, daga nesa Safwan ya parkar motarsa suka fito da Abi'atu, ya kamo hannunta su na tafiya a hankali su na labewa, maƙalewa suka yi, in da suka hango samarin sun fito da Hafiza sai fizgarta suke kamar kaza suka yi cikin babban kangon nan

17 / 25