COLONEL UBAIDULLAH by Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢

Author :  Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category :  Romance

Chapter   25 / 25

72K to 74.6K   out of 74.6K words

gado, zafafan sakonni Ubaidullah yake aika mata dasu masu wuyar fassara, tun tana dan biye masa tazo ta ji abun nasa ya fara zarce tunaninta, hankalinta bai gama tashi ba, sai lokacin da taji ya ja towel dinta ya yi jifa da shi, ya haye saman kanta tukunna ta shiga sambaɗa ihu da iyakacin karfinta tana ambatar sunan Mama dasu Ummi, Ubaidullah ya yi nisa dan kuwa yau a shirye yake da ya kashe arnan sama, ban da sambatu marasa kan gado babu abun da yake mata, wanda ita bata fahimtar me yake fadi, san da zai shigeta ta saki razananniyar kara ta shaƙo shi tana kai masa duka, naushi yaƙushi, cizo, amma Oga Captain ba shi da wannan labarin, sai da ya ji ya samu natsuwa kafin ya sauka a kanta ya koma gefe yana sauke nannauyar ajiyar zuciya, wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarsa wanda bai taba jin kamar shi ba, a hankali yasa hannu ya jawota ya ɗaurata a bisa faffaɗen kirjinsa yana shafa bayanta a hankalin alamun lallashi, kasa katabus Abi'atu tayi dan ji take yi gangar jikinta tamkar ba nata ba, bakinsa ya kai satin kunnenta ya fara mata magana cikin tsigar lallashi da dukar da kai tamkar ba shi ba.
"Am! Am! Am so sorry my everlasting, and i'm very happy today, Abi'ah kedin ta musammance a gareni, bansan me zan faɗa miki ba, kawai na gode, na gode, na gode, Allah ya miki albarka, farin cikin da kika sakani a yau, Allah ya dauwamar dake har gaban abada" ya sake rungumeta tsam a jikinsa, a hankali ya miƙe ya shiga toilet ya hada mata ruwan zafi ya zo ya dauketa cak ya shige da ita, sannan ya sakata a ruwan, ji tayi wani zafi ya sake ratsata da dasheshshen muryarta ta furta " wassshhhh Allah na, Ummina ya kashe! Ya kasheni, wayyo ya kasheni" tana yarfe hannu, saura kiris ya rage dariya ya sub'ucewa Ubaidullah, amma ya yi saurin hadiyewa dan idonta ya kalla ya ga tana jin zafinsa sosai, tana mugun jin haushin abun da ya mata dan haka ya maida hankali wajan gasata, sosai ya gasata kuwa, daga karshe ya fita ya barta ta yi wankan tsarki, yaje ya gyara bedroom din ya canza bedsheet, sannan ya koma toilet din ya sameta zaune a bakin bath ta daura towel sai gyangyadi take yi, ga zazzabin da yake shirin rufeta, kallon tausayi ya bita dashi kamar zaiyi kuka ya zo ya dauketa ya mai da ita bedroom ya zaunar da ita ya dauki rigar da tayi niyyar sakawa Allah baiyi ba a lokacin, ya saka mata sannan ya gyara mata kwanciya shi ma ya kwanta ya rungumeta, sai da ya ji ta yi bacci kafin ya mike ya zo ya yi wanka yayi alwala ya yi sallah raka'a biyu ya hau rokon Allah ya basu zaman lafiya da matarsa Allah kuma ya kaɗe musu fitina, Allah kuma ya sa musu albarka a wannan raya sunnar da sukayi Allah ya azurta su da haihuwa, bayan ya gama adduoinsa ne ya tashi ya hau gadon ya kwanta ya jawota jikinsa ya sumbaceta kafin ya lumshe ido, nan bacci mai dadi ya kwashesa, da asuba shi ya fara tashi ya yi alwala ya tafi masallaci sai karfe shidda ya dawo, bayan ya dawo a hankali ya fara tashinta daga bacci, da kyar ta bude ido, murmushi ya mata ta galla masa harara, tashi ya yi ya sake haɗa mata ruwan zafi ya sake gasata kafin ta yi wanka ya daukota ta zo ta yi sallar asuban da ba tayi akan lokaci ba, bayan ta idar a wajan bacci ya dauketa, sai sha biyu ta farka ta ga abinci kala kala a dakin, dama bakar yunwa take ji, nan ta zo ta hau bubbudewa nan taci karo da wata gasheshshiyar kaza wanda taji yaji, gasu drinks kala kala, yawu ta hadiye ta sauko ta hau cin kazan nan ido rufe, tana ci har lumshe ido take yi, dan kazar tayi mata dadi, har ta kusan inciye ta ji muryarsa yana cewa.
"Kazar da dadi ko? Ta yi dadi sosai? Kuma kina jin dadinsa?" harara ta galla masa ta ci gaba da ci dan ya mata dadi, murmushi ya yi ya ce "gaskiya kam kazar nan da dadi, kuma dama haka nake so kiji dadinsa, dan nima naci dadi jiya da daddare, dan haka idan ma bai isheki ba a shirye nake na kara zuwa na siyo wasu ranki shi dade, dan kuwa kazar amarcinki kike ci" tofar da wanda yake bakinta tayi ta zo zata mike a masifance amma me kasawa ta yi ta zauna tana matsar kwalla.
" ahh yi hakuri, na tuba, yanzu dai zo kisha magani" ya fada yana zama kusa da ita, maganin ya bude ya bata, ba gardama ta karba dan tana bukata, sha ta yi sannan ta hau hauma alamun bacci, a hankali ta mike ta koma ta kwanta a gado ba jimawa bacci ya sake kwasheta, wunin ranar Abi'atu bata leka ko parlour ba, da an tambaya tana ina kuma Ubaidullah zai ce bata da lafiya, su Mama da Hafiza sun zo dubata tana bacci, dan Hafiza bata tare ba, bayan an gama hidimar biki a gida ta zauna tun da gobe zasu wuce Abuja in da zata zauna dindindin, shiyasa Umma tace a barta kawai tunda duka za a wuce kuma ita ba zata dawo bauchi ba.




Yau da daddare sun gama shirinsu tsaf sai tafiya kawai ya rage musu.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




Jirgin safe suka bi dukkansu, MAMA, UMMA, INNA, UMMI, ABBA, UBAIDULLAH, ZAIDU,HAFIZA, ABI'ATU, Safwan bazai samu damar zuwa ba sabida matarsa ba lafiya, KB kuma dama ana gama shagalin bikin Zaidu ya koma, karfe shaɗaya su na airport din abuja, yayinda sojoji birjik aka zo tarbansu, amadadin a wuce dasu 9ja barracks sai aka wuce dasu Abachan barracks, basu zarce ko ina ba sai babbar filin taro na abacha barracks, inda an ƙa wa ta wajan ta yadda bakin ba zai iya faduwa ba, hotunan sojojin da suka je yaƙi ne a wajan,har wa inda suka mutu tare da iyalansu, murna a wajansu Ubaidullah abun sai wanda ya gani, nan Major Usman ya rungumesu yana saka musu albarka, Major General ya umarcesu da suje su canza kaya zuwa kaki, haka kuwa akayi nan aka shiga gabatar da abun da ya tarasu, inda aka shiga jinjinawa jarumai musamman Ubaidullah, inda aka shiga yiwa wa inda suka rasa rayukansu addua tare da bawa iyalansu abubuwa, inda a karshe lieutenant colonel ya karbi jawabin da cewa za a fara kiran sunan jarumi na farko wanda shine zaƙaƙuri a wannan yaƙin wato Ubaidullah wanda za ayiwa karin girma a halin yanzu, dan haka ana bukatar ganin Captain Ubaidullah a fili, nan Ubaidullah ya fito cike da zarra da jarumta yana taku mai dauke hankalin maza da mata, nan ya bayyana a fili, yayinda General Of The Army ya miƙe ya bawa Ubaidullah hannu, sannan Major General tare da wasu manyan kasa masu fada aji da yan gwamnati suka mike, nan aka yiwa Ubaidullah karin girma daga Captain Ubaidullah kai tsaye ya koma *COLONEL UBAIDULLAH* nan jama'a aka hau ba shi hannu jikake rab rab, inda aka bukaci matar Ubaidullah ta fito, nan Abi'atu ta miƙe da kyar dan har yanzu bata iya tafiya yadda ya kamata, har tazo kan mumbari Major Usman ya bata wasu stars yace ta daurawa mijinta, nan kuwa ta daura mi shi tana murmushin farin ciki, su Mama murna har da hawaye, Zaidu kuma nan aka ba shi mukamin major inda ya koma *MAJOR ZAIDU* Hafiza ce ta saka masa tambarin girma a matsayinta ta matarsa, KB kuma a lokacin ya karbi matsayin *CAPTAIN* baya da mata kanwarsa ce tayi masa jagora kamar zaiyi kuka Ubaidullah sai dariya yake masa, sauran sojoji kuma suka samu lambar yabo da jinjina, taro ta yi kyau sai son barka inda aka watse lafiya, ranar murna ta hana wa in nan family bacci, kwanarsu Mama biyu kafin suka baro Abuja, ranar da zasu koma Hafiza tasha kuka, kamar ranta zai fita, dan ta kasa gane kan Zaidu kwata-kwata sosai Mama ta danneta kafin su tafi, Abi'atu ma komawa gida bai yuba dan Ubaidullah yace sai dai a biyota da kayanta.



Wannan kenan.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Yau kusan watansu daya da dawowa barrack komai na tafiya dai-dai, inda KB ya samu Zaidu da Ubaidullah akan shi fa da gaske yake yi yana son Afnan, Dan Allah su ba shi ita, Zaidu yace indai Ubaidullah ya amince shi kam baya da matsala dan Ƙanwar Ubaidullah ne, Ubaidullah cikin farin ciki ya ce ya amince kuma zai gayawa Abba, abu kamar wasa magana ta fara girma inda aka tambayi Afnan tana son KB cikin kunya irinta hausa fulani ta amsa ta hanyar rufe fuska, Inna ta ce ja'irar yarinya tasan cewa na iya zabe, magana ta yi magana in da aka tsaida auren KB da Afnan wata hudu masu zuwa, yau kuma watansu uku kenan da dawowa, Ubaidullah da Abi'atu soyayya ake zubawa kamar ba za a mutu ba, kaffa kaffa suke yi da juna basu son b'acin ran juna, ta bangaren Hafiza kuwa zata iya kirga sau nawa suka hadu da Yaya Zaidu bayan dawowarsu garin nan, inda yau ta sakawa ranta zata jira ta ga shigowarsa dan akwai maganar da take son masa, tana son ci gaba da zuwa makarantarta ne ko hakan zai rage mata kewa, dan ba zata iya wannan rayuwa ba, ko ina sojoji, da misalin karfe goma ya shigo babbar parlourn nasa kwata-kwata baya jin dadin jikinsa bai ma lura da ita ba sai ji yayi tace masa "sannu da dawowa Yaya Zaidu" cikin san sanyar muryarta, juyowa ya yi ya kalleta ta sun kuyar da kanta kasa, gabansa ne ya fadi, dan kuwa yasan bai kyauta ba, kuma idan har aka fahimci baya bawa Hafiza kulawa tabbas ya ci amanar Mama da Amininsa Ubaidullah, ganin ta ƙi kallonsa kanta a kasa ne yasa ya kamo hannunta suka zauna dan ya fahimci akwai magana a bakinta.
"Hafiza kina son wani abu ne?" shuru ta danyi tana rausaya kanta da idanunta wanda suka ciko da kwalla, dan ita har ga Allah bata yi farin cikin wannan hadin ba, a hankali ta fara magana ta ce.
"Yaya Zaidu, nasan bai kamata ace ni matarka bace, dan nasan irin son da kake yiwa Yar Uwata, ni kawai inaso ne muyi rayuwa da kai kamar da, har kwanan gobe ni kanwarka ce ba matarka ba, idan nayi girki kadin ga ci pls, ina so kuma dan Allah na ci gaba da zuwa skull amma bana son na cikin barracks" duk cikin sanyin murya take maganar, sosai jikin Zaidu ya yi sanyi ya ce.
"To wa ya gaya miki ke bana sonki? Kema ina sonki sosai" murmushi tayi tace.
"Wannan maganar ta wuce Yaya Zaidu" ganin yadda tayi maganar yasa shi kara shan jinin jikinsa.
"To shi kenan, gobe zansa master sergeant ya duba min skull mai kyau, are u happy now?" ta jinjina kai tana murmushi " na gode Yaya Zaidu, sai da safe" ta tashi da gudunta ta haura sama, da kallo Zaidu ya bita dashi "wai ma miye banbancin Na'ilah da Hafiza ne kam? Me yasa a yanzu bazan karkato da hankalina akan Hafiza ba? Anya hanyar da na dauka zata b'ille min kuwa? Amma kuma taya zan fara rayuwar aure da Hafiza? Tayi yarinya da yawa, duka duka sai yanzu Hafiza take 15 anya zata iya dauke min bukatuna kuwa? Wayyo Allah ni Zaid" tunani yake yi kala-kala da kyar ya tashi ya haura sama ya wuce bedroom dinsa, da washe gari ya bawa master sergeant umarnin binciko masa skull mai kyau, haka kuwa akayi inda ya zakulo masa wata makaranta ta yaran manya, a sati daya aka yiwa Hafiza komai ta fara zuwa skull sojoji ke kai su dawo da ita, Ubaidullah ya ji dadin hakan sosai, tun daga ranar kuma Zaid ya canza mata idan ya dawo daga office zasu zauna suyi hira su yi wasa da dariya, kuma ya ƙi yarda ya fara jin feelings akanta dan wai kar ya jawowa kansa bala'i, sosai amince ya shiga tsakanin Ubaidullah da Zeey da Abi'atu dan ba karamin shiri sukeyi ba, Zeey ma kam ta kusa aure zata yi aure a America ta hakura da Ubaidullah duk da ta so shi tsakaninta da Allah, Hanan kuwa ta ƙi aure har kwanan gobe Ubaidullah ne a ranta shi take so.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




Bikin KB ya matso, abun ba wuya a wajan mai rai, inda aka fara shagalin bikin a garin abuja, Abi'atu bata samu damar yin komai ba, dan kuwa laulayin ciki take yi Ubaidullah ko kasa baya bari ta sauko wai karta bawa yaronsa wahala, da haka har aka yi bikin KB da Afnan inda nan ma aka sha shagali, ita ma ta dawo barrack da zama tare da mijinta, rayuwa sai dai ace alhamdulillah, Shafa'atu ta haifi Ƴa mace, duk yadda Abi'atu taso zuwa amma firrr Ubaidullah ba kunya ya hanata, har aka yi suna sai dai ta ga su pics, in da yarinya taci sunan Ummi su na kiranta da Amal, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya duniya tana gudu, inda cikin Abi'atu ya girma ya shiga watan haihuwa, Mama ta matsawa Ubaidullah akan ya dawo da Abi'atu gida ta haihu, amma Ubaidullah ya murzawa idonsa attargu yace babu inda Matarsa zata je, Mama kam abun Ubaidullah har mamaki yake bata, wata ranar jumma'a da dare Abi'atu ta haifo santalelen ɗanta mai kama da mahaifinsa sak dan babu inda Ɗan ya baro Ubaidullah, sai bayan ta haihu ne suka je asibiti inda aka gyara Uwa da Ɗanta, kafin kace me gabaki daya barrack ya ɗauka matar *COLONEL UBAIDULLAH* ta haihu, da yamma aka sallamota daga asibitin da yake a cikin barrack din, da kwana biyu Mama tazo da kanta ta tattari Abi'atu tayi da ita bauchi, ihu ne kawai Ubaidullah bai yiba, amma babu yadda ya iya, haka akayi shagalin suna inda yan uwa da abokan arziki aka halitta, inda yaro yaci sunan Babansu Ubaidullah, wato ABDULLAHI, amma za a dinga kiransa da ABRAR yaro ya yi goshi inda ya samu kyaututtuka daga waje daban daban, sai da Abi'atu ta yi arba'in kafin ta dawo wajan mijinta, tasha gyara kam sosai kamar ba ita bace ta haihun a ranar ta gurzu a wajan ogan nata har sai da ta gane cewa Allah daya ne, komai yana tafiya yadda ya kamata sai dai ace Alhamdulillah Ma sha Allah, sosai suke rainon Ɗansu Abrar cike da so da kauna, ga kulawa.




TAMMAT BI HAMDULILLAHI.


TO BE BEGINNING👉🏻


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Alhamdulillah bayan dogon zango da wanga book ya ɗauka yau na kawo karshen wannan littafi nawa da yardan Allah, abun da na fada daidai, Allah yasa mu amfana kuskurena kuma Allah ya yafe min.


Ina miko sakon gaisuwa ga masoyana wanda suka bibiye wanda littafi nawa, alherin Allah ya kai muku har garin da ku ke, na gode sosai.


Ku tare ni a ci gaban littafin nan dan ba ayi komai ba ma tukunna wato👇🏻.



*GAWURTACCEN SOJA* ci gaban _COLONEL UBAIDULLAH_

ga masu bukatar ci gaba zasu same shi akan farashin #300 VIP KUMA #500, SANNAN KARKU MANTA AKWAI WANI KUMA MAI TAKEN SUNA *AHLAN* WANDA SHI MA ZAKU SAME SHI A FARASHIN #200 VIP #500 ga masu bukata sai su tuntubeni a lambata (08165550116) sai na jiku masoyana, na gode sosai Allah ya sadamu da alkhairi 🙌🏻



UMMU AHLAN TAKU CE🤙🏻

25 / 25