Author : Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ Category : Romance
abun da zai faru ya faru" tana gama faɗi tayi gaba kamar zata tashi sama.
Cirko-cirko su Hanan suka Tsaya su na kallon juna, ga Rumaisa kwance a kasa tana sauke numfashi da kyar, Doratie ce ta kalli Rumaisa cikin hausarta da bata iya sosai ba ta ce.
"Shame! Kinji kunya! Rumaisa, kince kina son Captain Ubaidullah for what reason zaki masa sharri? Sanin kowa ne a barracks din nan Captain Ubaidullah baya kula mata, infact har mazan ma baya shiga Hidimar su amma zaki masa wannan sharri! Walahi kinci sa'a amma kinga zugan mun nan, dama mun zo ne mu lallasaki sai kuma muka samu maiyi da gaske ta tumurmusheki, dan haka ki kiyayi gaba.
**********
Da sauri KB da Zaidu suka bi General su na magayi, amma ya dakatar dasu, dan shima ya shiga cikin zullumi.
Haka suka juya ba dan sun so ba, wajan Major suka je Zaidu ya ce.
"Sir a duba lamarin Ubaidullah na miskilanci da rashin magana da kula mutane, ta ya wani mu'amala zai shiga tsakanin su da Rumaisa har ya mata ciki? Sir, idan mafaɗin magana wawa ne ai majiyinta mai hankali ne, pls Sir a duba lamarin" Zaidu ya karasa maganar kamar zaiyi kuka saboda tashin hankali.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da babu gwara ba dadi ko my ppls?😁
COMMENTE
AND
SHARE
BY
MOMYN AHLAN✍🏻
[8/19, 10:57 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)
*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻
*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻
_dedicated to my brother_
*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~•~•~
_my wattpab_@Fateemah0
_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*_HAHAHA MASHA ALLAHU, IDAN KAJI WANE KO WANCE BA BANZA BA, KUNA INA MASOYAN KUNGIYAR NAN ƊAYA TAMƘAR DA DUBU, WATO KAINUWA WRITERS ASSOCIATION? WANDA SUKA SABA KAWO MUKU LITATTAFAI DAƊA ƊA, MAZA MAZA KU MATSO KUSA GA DAMA TA SAMU, A YAU KUNGIYAR TAYI SURFE DA DAKA, TA TANKAƊE TA RAIRAYE, TA REGE TA BUSHAR, TA ZAƘULO MUKU JIGA-JIGAI HAZIƘAI NAGARTATTU MASHAHURAI,BASIRARRU, A YAYINDA ZASU GWANGWAJE KU DA FASAHAR SU, DAMA SUN SABA ILMANTAR DAKU NISHAƊANTAR DA KU GAMI DA FAƊAKAR DAKU, KU DAI KU KASANCE DA WAINNAN FASIHAN MARUBUTAN GUDA BAKWAI DUK A CIKIN LITATTAFANSU MAI TAKEN SUNA ( 𝕊ℍ𝔸ℍ𝔸ℝ𝔸ℝℝ𝕌 𝔹𝔸𝕂𝕎𝔸𝕀 ) AKAN FARASHI MAI SAUKI DA RAHUSA #500 KACAL YAN UWA, KU DAI KARKU BARI A BARKU A BAYA, NI UWAR AHLAN INA GAYA MUKU NE DAN KU HANZARTO KU GARZAYO, KU NEMI NAKU, KU SHA KARATU, A ISO LAFIA._*
💕💞💕💞💕💞💕💞💕💞
*page°°°°°31&36*
Major ya ce.
"Ok Captain Zaidu kuje zanyi magana da General Of The Army idan yaso a tara meeting sai asan abunyi" Zaidu ya ce.
"Tnk u Sir Allah ya kara girma, but pls kar abar Captain Ubaidullah ya kwana a guardroom "ya karasa maganar cikin roƙo da kasa da murya gamj da kwantar da kai.
Major ya ce.
"Kuje zan san yanda za ayi" sara masa sukayi, sannan suka sa kai suka fice daga office din Major.
Su na barin office din Major hanyar guardroom suka nufa kai tsaye, su na tafiya su na tattauna lamarin, KB ya ce.
"Amma dai gaskiya wallahi Rumaisa ta cika babbar makira, ban taba tsammanin zata yiwa Ubaidullah wannan ɗanyen aikin ba"
"Hummm KB kenan wasu matan kam ai sai a hankali, kai a tsammaninka Ubaidullah zai kyaleta ne? Tab Ubaidullah bazai barta ba, sai ya koya mata hankali, shiyasa dazu da yake kokarin cafkota banyi tunanin katse masa hanzari ba, so nayi yayi mata shegiyar duka, amma sai wannan tsautsayin ta gitta, ko ba komai naji dadi da Ubaidullah ya fasawa Ubanta baki har yayiwa hakorinsa biyu sanadin zubewa kasa a cikin jama'a, kuma kasan sergeant first class Ƙasimu(mahaifin Rumaisa) ba kaunar Ubaidullah yake ba"
KB ya ce.
"Yes i know, ai naji dadi da Ubaidullah ya jibgi Commander Victor, dan kasan ba kaunarsa yake ba shima, ni na rasa me Ubaidullah ya tare musu"
"Ai na lura wa inda basu son Ubaidullah a barracks din nan su na da yawa, gashi da mahassada kuma shi ba ɗan siyasa ba, da sunan shi Soja, kai gaskiya abun yana damuna"
KB ya ce.
"Hummm Zaidu kenan sai kace baka san halin *RAYUWAR BARRACKS* ba? Duk nan ne fa ma tattarin *HASSADA, KYASHI NUNA FIFFIKO* barin ma idan mutum ya fika muƙami, ga *SHARRI* ga *GA BA*"
Zaidu ya ce.
"In dai sharri ne kam na shaida tun da ga Abokina a kulle" ya faɗa maganar su na shiga wajan Ubaidullah dake tsaye ƙiƙam sai kace bishiyar itace, sallama suka masa amma da kyar ya iya amsa sallamar a cikin zuciyarsa.
Rungumansa Zaidu yayi yana buga bayansa,Ubaidullah ya fizge jikinsa,dan ransa yayi ƙololuwar wajan baci, dan ko a mafarki bai taba tunanin zai shiga halin da ya shiga a halin yanzu ba, wai yau Ubaidullah shine a guardroom? Bama zaman guardroom din bane ya harzuƙa shi ba, ƙazafin zinan da Rumaisa ta ɗora masa shine yake sake ingiza zuciyarsa ta sake dulmiyawa cikin tashin hankalin da bai misaltuwa, dan shi ya tsani zina a rayuwarsa, hawaye ne maƙale a cikin idonsa amma fir yaƙi yarda su zubo kasa, rimtse idanunsa yayi mutanen da suke filin barracks yake tunawa a gaban su Rumaisa taci mutuncinsa.
Mama zaune a bakin Gado ta ga yau Ubaidullah bai kirata ba kamar yanda ya saba kullum, dan ya kan kira mahaifiyarsa kusan sau goma a rana,hakan ma idan yana busy ne,dan shi baya haɗa Mama da kowa, dan ita ce haske kuma farin cikin rayuwarsa.
Sosai gaban Mama yake faɗuwa wanda ta rasa dalilin hakan, ga kuma wayar a hannunta tana so ta kirasa amma kuma ta kasa, saboda faduwar da gaban ƙirjinta ke yi, sai jujjuya wayar take a hannunta tana kallon wayar, zuwa can anjima tayi jahadi ta dannawa layin Ubaidullah din kira,a lokacin su Zaidu su na tsaye su na kan bawa Ubaidullah baki amma ko gizau bai yiba.
Kiran Mama ne ya shigo, wayar yana hannun Zaidu yana dubawa ya ga Mama ne,Ubaidullah kuwa daga ringingtone ya fahimci mahaifiyarsa ce, dan yasa mata ringing daban na waƙar larabawa, wanda ake cewa, *HAYATI YA MAMA*.
Gaban Zaidu ne faɗi ganin Mama tana kiran Ubaidullah dan bai san me zai cewa Mama ba, gashi ita ba lafiya gareta ba, yanzu ciwonta zai tashi idan tasan halin da Ubaidullah yake ciki, kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Zaidu da KB, wannan ya kalli wannan.
Har sai da Mama ta yiwa Ubaidullah 3 miss call, ana 4 ne Zaidu yayi karfin halin ɗagawa kafin nan kuma hankalin Mama ya tashi ganin Ubaidullah bai kirata ba ita tana ta kiransa bai ɗaga ba, ta shiga zullumin meya samu ɗanta.
Zaidu na ɗagawa Mama ta sauke ajiyar zuciya wanda har sai da Ubaidullah yaji, dan Zaidu ya saka wayar a hands'free ne.
Ubaidullah jin yanda mahaifiyarsa ta sauke a jiyar zuciya, yasan hankalinta a tashe yake, dan haka ya wafce wayarsa daga hannun Zaidu yasa a kunne cikin sanyin Murya Mama ta ce.
"Assalamu Alaykum, Ubaidullah fatan dai kana lafiya ko? Lafiyarka kalau?"
Hawayen da Ubaidullah yake maƙale su nan take suka zubo da yaji muryan Mama.
"Ubaidullah wai meya same ka ne kam? Ka faɗamin mana? Yanzu Ubaidu idan baka faɗamin damuwarka ba kana da wanda zaka faɗa mata sama da nine? " duk wannan maganar cikin damuwa Mama tayi su kasancewar tasan halin ɗanta.
Kusan 10mnts su na tsaye a haka ban da Ajiyar zuciyar da yake saukewa, karban wayar Zaidu yayi yasa a kunnensa yayi sallama, Mama ta amsa suka gaisa,nan Mama ta shiga tambayar Zaidu me ya faru da Ubaidullah, cikin in'ina da inda-inda Zaidu ya ce.
"Amm Uhum humm dama Mama ba wani abu bane, matsala aka samu shiyasa,amma ba komai ki tayamu da addua komai zai zo mana da sauki"
"Adduata kullum kuna tare da ita Zaidu,sannan dan Allah ka dinga tausasan Abokinka kasan dai halinsa"
"In sha Allahu Mama, karki damu, a gaida Na'ila da Hafiza" Mama ta amsa da "zasu ji" da ga haka sukayi sallama.
Hannu Ubaidullah ya miƙawa Zaidu alamun ya basa wayarsa, ba musu Zaidu ya miƙa masa wayar ya karba,KB ya ce.
Zaid muje musan abunyi dan gaskiya bai kamata Ubaidu ya kwana a nan wajan ba shi ba mai laifi ba" Zaidu ya jinjina kai alamun eh haka ne, juyawa sukayi zasu fita KB ya waigo ya ce.
"Am Ubaidullah kawo wayarka Mu tafi dashi kasan ba a zama da waya a guardroom"
Sai yanzu Ubaidullah ya bude baki da kyar yayi magana cikin kakkausar muryarsa wanda yake a dashe cikin tsawa.
"Duk Uban da ya isa yazo ya karbe min wayata daga hannuna!" ai da gudu KB ya fice yana sauke ajiyar zuciya, shima Zaidu fita yayi yana dariya ganin yanda KB ya arce da gudu.
Waje ya samesa yana tsaye dariya sosai Zaidu ke yi har yana riƙe ciki, cikin dariya ya ce.
"Haba Soja kana matsayin First Lieutenant Amma shine dan Captain ya maka muzurai shine ka fece da gudu sai kace walƙiya?"
"Uhm uhm Zaidu Ubaidullah ba kamar sauran mutane bane, ko hawainiya ba zata gwadawa Ubaidullah canza kala ba"
Nan ma Zaidu ya sake fashewa da dariya ya ce.
"Muje ko?"
"Ina yanzu zamu je to?"
"Eh to nima dai yanzu ban san inda muka nufa ba,amma inaji kawai muje Abacha Barracks wajen Major Usman muyi magana dashi ko ya kace?"
KB ya ce.
"Eh hakan ma yayi ka kawo shawara muje din kawai"
Wajan da motar su yake suka nufa zasu shiga daga bayan su suka ji kira, juyowa suka yi a tare, Raihana Hanan da Doratie ne ,tsayawa Zaidu da KB sukayi har suka iso.
Hanan yar gidan Shugaban sojoji ita ce ta fara magana.
"Captain Zaidu yanzu ya za'ayi da case din Captain Ubaidulllah? Naje na samu dadyna amma ya ƙi ya saurareni at oll,now I don't know what can do to protect Ubaidullah" ta karasa maganar tana hawaye dan soyayyar Ubaidullah ya mata mugun kamu.
Zaidu ya ce.
"Don't worry Hanan everything will be better OK?" ta jinjina kai, Raihana ta ce.
"Yanzu Zeey ta gama dukan Rumaisa har bata iya motsi da kyau.
KB ne ya kwashe da dariya ya ce.
"Kai Dan Allah fa? da gaske?"
Doratie ta ce.
"Seriously Rumaisa ta daku a hannun Zeey, u know Zeey She's very strong woman"
Cikin dariya KB ya ce.
"Yes I know She's very strong, wow gaskiya Zeey bata taba burgeni irin ta yau ba,ya zama dole nayi mata kyauta"
Doratie ta ce.
"gaskiya kam ta cancanci kyauta daga wajan Captain and First Lieutenant"
Murmushi Zaidu da KB sukayi kana suka bude mota KB na cewa.
"Bari muje Abacha barracks zamuyi magana da Major Usman ne" da ok suka amsa sannan su ma suka ci gaba da neman solution ta yadda Captain Ubaidullah zai fita a guardroom.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Ta bangaren Rumaisa kuwa hankalinta ya tash da maganganun da Zeey ta faɗa mata, kuma tasan halin Zeey zata iya sarai, kuma ko a muƙami mahaifin Zeey yafi mahaifin Rumaisa Muƙami dan shi matsayin Second Lieutenant ne, gashi ita kuma Zeey CBI ce ita wato jami'ar bincike, shiyasa Rumaisa tasha jinin jikinta gashi taci mugun duka, dan ba karamin horo Zeey ta samu ba daga wajan margayi commander Shafi'u, Uncle dinta ne kuma, Commander Shafi'u ya bawa Jami'an Sojoji ingantacciyar horo ta yanda zasu zama na kwarai su kare kansu da kasar su, dan sai mutum yasan matakin kare kansa kafin ya kare wani, a wajan wani yaƙi aka kashesa lokacin da sukaje yaƙin maiduguri nan yan boko haram suka yi masa kisan wulakanci, tun daga lokacin ba a sake samu wani jarumin Commander ba kamar shi, kuma ba a sake samun cikakken mai tsayuwa da kafarsa da zuciyarsa yayi yaƙi ba har sai da Ubaidullah yazo shi barracks din, da wannan tunanin Rumaisa ta rarrafa da kyar ta tashi tana jan kafafunta da gangar jikinta wanda suke mata tsami.
Wajan Babanta ta wuce ta same shi a office dinsa,tasa masa kuka ita ba so take a kulle Ubaidullah ba, ita so take a saka shi ya aureta idan kuma ya ƙi asan abun da za ayi masa amma a buɗesa daga guardroom.
Baban Rumaisa duk da yaga jikin ƴar tasa duk a fashe amma bai damu ya tambayeta ba, dan yasan ba zata faɗa masa ba, ya ce.
"To shaleleta je ki abunki bari naje na samu General"ya faɗa yana mai ficewa daga office din yabarta tsaye a wajan.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Ta bangaren su Zaidu kuwa sun samu Major Usman sunyi masa bayani abun da ya faru dalla-dalla kuma sosai ya fahimta ya ce.
"Gaskiya banji dadin abun General ya aikata ba, duk da Captain shi ma yayi ba dai-dai ba,but ba komai ku tashi muje can din"
Fitowa sukayi yana gaba su ba binsa a baya, kafin suje kuma an sake kirawo Ubaidullah, a secret meeting room,wanda manya ne kawai a wajan kamar su General Of The Army, General, Major General, sai Brigadier da Colonel da Lieutenant Colonel, ga Uban Rumaisa a gefe da ita Rumaisan, ga Kuma Ubaidullah Zaune a gefe.
Ko da su Zaidu suka iso bayan Major Usman ya kira General Of The Army yake gaya masa akan cewa gashi nan yazo ganinsa ne akan case din Ubaidullah,General Of The Army yake cewa Major ai gasu nan yanzu suka shiga secret meeting room su same su acan.
Su na zuwa Sojoji suka saka musu gami da bude musu kofa suka shige,sara musu Major da su Zaidu suka yi kafin suka samu wajan zama suka zauna.
General Ayuba shine wanda ya fara gyaran murya alaman zaiyi magana.
"Amm Ubaidullah am not happy with ur action,dan takanka zan fara, da hankalinka taya ka bari har hakan ta faru tsakaninka da Rumaisa,ni nasan ba akan ka aka fara wannan abun ba, but am very surprised ta yanda naka ya baza barracks din nan, yau aka fara yiwa yara fyade ne? Ko kuma yau ne mace ta fara yin ciki a barracks iye? this is the not the first time da hakan take faruwa, wasu ma basu kai Captain Ubaidullah stars ba, amma ba'a saka su a guardroom ba,duk da ba'a barsu haka ba an hukunta su, gaskiya Sir banji dadi da kuma faruwan hakan ba"
Nan Major Usman shima ya karbe maganar daga wajan General Ayuba.
"Eh tabbas maganarka haka ne Sir Ayuba bai kamat ayiwa Captain haka ba,domin shi mutum ne mai matukar amfani a wajan mu"
Brigadier Rashid ya ce.
"Duk wa innan maganganun ma basu taso ba, ya kamata muji ta bakin Ubaidullah shin da gaske ne shi yayi mata ciki ko ba shi ya mata ba, na biyu idan ma shi ya mata cikin fyaɗe ya mata ko kuma ason ranta ya kusanceta, ya kamata a dinga bawa kowa hakkinsa, dazu da abun ua faru bana nan ne da duk bata kai ga haka ba"
Lieutenant Colonel Aliyu ya ce.
"Captain Ubaidullah akwai wata alaƙa ko mu'amala tsakaninka da Rumaisa ne?"
Ubaidullah wanda tun zamansa kansa yake duƙe yana jin maganar kowa yana shiga kansa a hankalin, idonsa kamar anyi b'arin jini,ko ɗigon fari babu a idanunsa, ya ma kasa magana sai girgiza kai kawai da yake yi, ganin haka yasa Zaidu riƙe hannunsa gam ba tare da wani ya gani ba.
Tattaunawa akeyi yayinda kowa yake tofa albarkacin bakinsa,duk wata tambayar da za ayiwa Ubaidullah da kai yake amsawa,Rumasa kuwa da an tambayeta zaia karkata baki ta shankaɗa karya da ƙarairaki dan duk abun da take faɗi babu gaskiya ko ɗigo a ciki.
A karshe dai hukuncin da aka yanke shiya girgiza Ubaidullah bama shi kadai ba, harta Abokansa na Amana sun girgiza, hukuncin kuwa shine wai Ubaidullah *YA AURI RUMAISA* maganar da ta doki dodon kunnensa,a zabure ya miƙe yana girgiza kai gami da cewa.
"Noooo! Naverrrrr! and Everrrrr! Impossible na aureki Rumaisa wallahi bazan aureki ba!"
Nan Baban Rumaisa ya fashe da kukan munafurci yana cewa.
"To me kake Sir Captain? Kana nufin shikenan kaci banza kenan? Ka kyatawa yarinyata budurcinta kaƙi aurenta? Dan kaga ka fini muƙami? Sai ka zalunceni" ya ci gama da kukan gulma,ran Ubaidullah ya gama baci matuƙar baci, wani wawan camuƙa ya kaiwa Uban Rumaisa.
"Ni zaka yiwa Sharri !!! Yaushe nake mu'amala da yarka da har zan mata ciki!?" da kyar su Major da General da Brigadier suka banbare Baban Rumaisa daga hannun Ubaidullah.
A fusace General Of The Army ya miƙe dan Abun da yake haɗa shi da Ubaidullah kenan saurin zuciya duk da hakan shine dai-dai a matsayinsa na Soja magana yake cikin bacin rai, kuma yawancin mutane an yarda da Baban Rumaisa da ƴarsa ga kuma wani Video wanda aka haɗa Ubaidullah da Rumaisan da wanda tayi ranar da ya wanketa da mari,shi har ga Allah bai san lokacin da tayi wannan video ba.
" Captain Ubaidullah ya zama dole ka auri Rumaisa, idan ba haka ba zaka fuskanci hukunci mai tsanani gobe idan Allah ya kaimu" General Of The Army yana gama fadi ya fice, yayinda Brigadier ya bada Umarnin kar a sake a mai da Captain guardroom, da haka kowa ya watse, tashi Ubaidullah yayi da Sauri Zaidu da KB suka bi bayansa.
Bai tsaya a ko ina ba sai part dinsa, gashi duk inda yasa kafarsa sai an nunasa da tsaya ana gulmarsa, da ya juyo kuma kowa zai kama bakinsa,wannan ne ya saka hassala shi,ganin yanda lokaci ɗaya mutuncinsa ta zube.
Zubewa yayi akan gadonsa ya kifa kansa da pilo ya lumshe ido sai hawaye shar-shar, tabbas army shine burinsa amma ya zama dole ya ajiyeta idan ba haka ba Allah ne kadai yasan kalar abun da za a masa gobe, a haka Zaidu suka shigo suka samesa su ma hankalinsu a matuƙar tashe.
Zama sukayi gami fa dafasa amma sai ya miƙe ya nufi toilet ya watsa ruwa yayi alwala sukayi jam'in sallar la'asar bayan sun idar ya ɗaga wayarsa ya dannawa Mama kira, cikin sanyin jiki Mama ta ɗaga wayar saboda haka yau ta wuni bata jin dadi ga mummunar faduwan da gabanta keyi, gashi bata saba baccin rana ba, amma sai da tayisa yau, tare da mummunar mafarki.
Sallama Ubaidullah ya mata ta amsa lokacin Hafiza da Na'ila su na zaune a gefenta, Mama ta ce.
"Ubaidullah fatan lafiya kake ko?"
Da kyar ya tattaro jarumta yayi murmushi mai sauti ya ce.
"Eh My Momma am fyn,ina nan dawowa gida gobe idan Allah ya kaimu"
Dam!dam! Gaban Mama da Zaidu da KB suka