Author : Queen Safiyyert Category : Romance
kan ta goge hawaye
wani na kara zubar mata.
Kawai sai ta tashi ta fita da result na "urine test"
a hannu.
Ba'a jima ba ganin an sa ai da sauri suka fidda
ma Furen result.
Ido rufe ta fito, tana mai fatan in ta bud'e taga
"positive".
A d'an gefen "lab'' d'in ta t'saya,matar nan ce
zaune tana cigaba da kukanta, sai ta juya mata
baya tare da bud'e ido, sai ta ware "result",
Da sauri ta rint'se ido sai ga hawaye.
Bata nufa ba taji kuka ya su6uce mata wanda
batasan ma na meye ba, ta kusa minti d'aya kan
ta t'sagaita jin ta kusa da ita tai shiru, sai ta
juyo ta k'alleta, itama Matar ita take k'allo
hawaye na zuba, sai Furen tai mata murmushi
tare da sa bayan hannunta tana goge ido, da
mamakinta sai taga matar itama na murmushi
tare da itama goge hawayenta.
Sai ta taso tazo gun Furen, tare da ce mata "ina
fatan ba matsalar mu d'aya ba y'ar uwa?
Murmushi Furen tai tare da k'ada mata kai, dan
batasan tata matsalar ba.
Hannu matar tasa ta k'ar6i "result'' d'in hannun
Fure ta duba.
Da mamakinta sai taji tai murmushi mai sauti,
wanda agun Fure wani hawayen ne ya kara
saukar mata.
k'allo Furen tai,kan tace, "hala kina gudun a kira
ki da JUYA ne sister? Da sauri Fure ta dago tana
k'allon matar, da mamaki tace "ya akai kika
sani? Murmushi matar tai,kan tace "za kiga likita
ne koh gida zaki? Kai ta girgiza mata, "yace in
"Negative'' ne ba sai na dawo ba.
Kai matar ta k'ada, tare da mika mata nata result
d'in, "Pt=positive" taga, sai ta dago ta k'alli
matar da mamakin toh mey yasa ta kuka bayan
nata ya nuna "positive"?
Hannun Furen ta kamo, "muje,nasan za kiyi
tunanin mey ya sani kuka? Tafiya suke tana
sanarta "nima irin kice da,kullum nazo asibiti
naga "Capital Negative" sai nai hawaye, amma
na yau na daban ne, rakani na kai mishi result
d'in kiga. Ita d'ai Fure binta kawai take,dan sosai
ta kosa taji meye dalilin kukan matar nan.
Da mamakinta likita d'aya suke gani da ita, sai ya
juyo ganin su tare da Fure, tuni sai fara'ar shi ta
karu, zaton shi Furen ta samo "positive" ne.
Sai d'ai yana k'ar6a ya girgiza kai, "madam kiyi
hakuri,ki kara adu'a, kin ga nan y'ar uwarki, in
kinji nata zaki gode Allah ne.
K'allo matar, kawai dan ya hucer mata da zuciya
yasa kullum tazo yake bata "pt'', amma shi yasan
sai wani ikon Allah.
Sai d'ai yana bud'e result da sauri ya d'au "glass"
ya kara dubawa,sai ya k'allo matar fuska d'auke
da mamaki, "madam,
result d'in kine wannan? Kawai maimakon amsa
sai ta kara sakar kuka.
Ita Fure har matar ma ta fara bata haushi, dan a
ganinta abin farin ciki ne wannan ba wai na kuka
ba.
Sai dai jin abin da likita yace yasa ta K'allonshi.
Abin yai matukar d'aure mishi kai ne, har bai san
sanda ya kara k'allon result d'in ba yace"how is
this possible? Tashi yai, kawai yace su biyo shi,
ita kam Fure sai ta bi su.
D'akin"scanning" suka nufa, Fure zata t'saya
yace ta shigo itama, taga ikon Allah.
Ido yasa ma allon "machine d'in scan" d'in yana
k'allo. A hankali ya furta"lalle d'ukkan ya6o ya
kara tabbata ga shugaban halitta.
Take ya tuno da kalmar shi ta "how is this
possible, nan take ya Istigfari ga mahaliccin shi,
take ya kara gaskata k'arfin iko na Allah,domin
gareshi " everything is possible ", gashi cikin
ikonshi yace "KUUm..sannan FAYA KUM
d'in,matar da suka sanar da mijinta cewar bazata
haihu ba gashi Allah gagara misali yai iko nashi
kanta.
Ajiyar zuciya ya sau, kan ya k'allo su, "madam
kinga ikon Allah koh? Mai iko akan d'uk abinda
yaso.. " a gaskiya "case" d'inki shine na biyu da
ya ta6a bani mamaki tun fara aiki na. "Yanzu
kam kuka ya kare miki, 4 good ten years yau
Allah ya nuna ikon shi akan ki, kiyi murna da
godiya ba wai kuka ba.
Kai ta k'ada, ita d'ai Fure ta kasa gane inda suka
suka dosa.
Ta d'ai gane matar shekararta kamar goma ne
bata samu haihuwa ba sai yanzun.
Kan Furen ya dawo, "matar "pharmacy" ki dad'a
hakuri, dan tabbas matar nan ta ishe ni ishara.
"Kisa a ranki in har baki haihu ba Allah ne kawai
bai nufa ba.
Kai kawai ta k'ada mishi, tare da k'allon matar,
sai yai rubuce-rubucen shi da taimakon tambayar
da ya yai mata, da murmushi ya dago, "in har
lissafin nan d'ai-d'ai ne toh cikin nan ya ma shiga
wata na hudu fa,right? Kai ta k'ada mishi, dan
wata hudun shine karshen y'in period nata,d'uk
dama ba wai "regular" bane.
By
Feenat Ja'afar.
[4/27, 1:59 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
31_Iyanzun ta d'aina kukan, sai d'ai takan k'alli
Fure da itama kawai k'allon matar take cike da
tambaya.
Sai tai murmushi, d'ai-d'ai wata mota ta k'allo
Fure, "zan so k'warai in kin yarda ki bini in dai ba
mai d'aukar ki
na baki labarina,nayi imani daga yau kin d'aina
wahalar da kanki a asibiti, da daga yau kin d'aina
kula zancen jama'a har yazo suna saki a bak'in
ciki, da na zame miki Aya a rayuwar nan tamu.
Kai Furen ta k'ada, kan ta d'au waya ta buga ma
Ahmad dan neman yardar shi. Mota ta
shiga,halamun ya barta,yayin da matar ma ta
shiga tata, a hanya take binta,har suka t'saya a
d'ai-d'ai wani gida, sai taga ma matar batta nisa
da unguwar su Umma.
"Horn" matar tai aka bud'e musu "gate". Gidan
bai fi rabin nasu Fure a girma ba, suna "parking"
matar ta fito, da murmushi tace ma Fure
"Bissmillah.
Kawai ta rasa dalilin da ya sa ta nacewa matar
d'uk da bawai ta santa ba.
Suna da rufin asiri d'ai d'ai g'warg'wado, ta kama
Fure ruwa da lemo kan ta d'aura musu abinci.
Nan da nan itama taji kawai ta aminta da
Fure,sannan da taimakon jin likita yasanta.
Zama tai kusa da Fure lokacin da ta fito a
kitchen, sai tai mata murmushi, ganin tun dazun
Fure na ta binta da ido,ita so take ta gano inda
cikin ya makale har na wata uku, sam sai ka
zata cikinta ne,dan d'uk yabi jikinta.
"Da farko d'ai sunana Fatima,ina da shekara 29,ni
y'ar Kano ce, aure ya kawo ni nan, k'anin Baban
mu ne kawai na sani a garin nan, sannan a wani
hutu nazo garin nan muka had'u da Salman,Allah
d'ai yai ikon shi har na yarde wa auren shi, sosai
ya nunan so tamkar ba gobe,har hakan yasa na
mance da kad'aicin iyayena, abu d'aya na fara
fuskanta shine sam y'an uwanshi basu son kular
da yake nuna min, a hankali ya rage wasu
abubuwan tun kan aje ko'ina, sai d'ai d'uk da
haka ban nemi komai na rasa ba.
"Abi na biyu da fara fuskanta shine jinkiri na ta
gun haihuwa ta, dan tun ana min abu da kawaici
har ya zamo kiri kiri ake min, wasa wasa har na
shafe shekara uku shiru, dan ko 6ari ban ta6a
ba. Duk da a bangaren Miji na ban samun
matsala sam har na shekara uku.
Mukan je ganin likita d'uk wata ni da Salman,ace
mu g'wada na gargajiya,muyi na rubutun, amma
sam babu cigaba.
A wannan lokaci nayi iya hakuri na naga na fita
harkar y'an bani na iya dangin Salman sai d'ai
sun kaini bango.
"Sai ya zama ina d'ari-d'arin shiga cikin su, dan
d'uk wani zama bazai kare ba sai an gorata min
kan ban haihu ba.
In takaice miki sai da na shekara biyar muna
jelar asibiti ni da Salman.
A wata rana da bazan ta6a manta ta ba munje
ganin likita kamar yadda muka saba,tare da
"result" na "X-Ray" da aka min "HSG" a wajen
mu, shima kuma Salman yazo da abinda za'a
g'wada lafiyar k'wanshi, tashin farko farko likita
ya tabbatar wa da Salman ai d'uk wai "tubes"
sunyi ''blocking". Duk da banyi science ba, amma
na gane maganar shi ta karshe wai "there was
no chance of conceiving naturally Ever... Wai zai
de had'a mu da Ogan shi.
"A time likitan dake dubani yaje karin karatu,
ranar naci kuka na gode Allah, yayin da Salman
ke ta aikin lallashi, ya na iya, kinga d'ai ba wanda
zai kaini damuwa, amma in sanar ki a satin har
gida akazo aka wanke ni ciki da bai, kan na zama
JUYA naki sakar ma mijina mara ya kara aure.
Biyu sai tazo ta had'e min,bani inda zanji sauki
sai agun Allah da gun Salman, dan ko gidan
k'anin Baban mu naje sun dunga fad'in "Allah
sarki Fati,shiru koh? Sai tai murmushi, hakan
yasa suma na rage zuwa gidan sun, dan sosai
suke kara min damuwa.
Har ranar da likita ya dibar mana ta cika banji
Salman yace na shirya muje ga likita ba.
Sai da dare nai mishi magana, d'uk da naga yana
ta cika da bat'sewa. Budar bak'inshi sai yace shi
ba inda zashi.
A lokacin nai mamaki, dan sam bai ta6a min
haka ba, Washegari sai ni naje, da ikon Allah
wannan likitan ya had'a ni da Ogan su, ni d'ai naji
yana mai bayani da turanci kan wai ai min
"laproscopy to "unblocked" my tubes.
A lokacin da ido nake binsu,sai dai suna fad'in
zasu dan min aiki kad'an na t'sure.
Tun daga ranar ban kara bi takansu ba, shima
kuma Salman bai tambaye ni ya akai ba.
I yanzun kam na ma fidda rai ga haihuwa, tunda
sun sanar ni in dai ba'a bud'e ba ba zancen
haihuwa.
Haka na cigaba da toshe kunne na,ranar ana biki
gidan k'annin Baban mu naje, kusan d'uk y'an
uwa sunzo, sosai nai farin ciki a ranar,muka
rankaya gidan amarya, chan kusa da y'ar gidan
k'anin Baban mu naje dan ganin kujerar da take
kai ce kawai da waje.
Da zuwa na dama ta fara ta6e baki, cikin wasa
na kula take watsan magana musamman in naje
gidan ta.
Zama na kenan tai saurin mikewa tana fad'in "a
Fatee kar ki min illah man, d'uk na k'alli y'an
d'akin kowa na sabgar gaban shi, sai nace " mey
kenan hakan yake nufi cikin wasa. Sai yamutsa
fuska, "kinsan cikin ba irin naku bane.. Sai tai
waje ta barni da k'allon bayan ta,sai a sannan ne
na kula da karamin cikin jikinta.
Ranar har nazo gida ina mamakin maganar
Maryam y'ar k'anin Baban mu, tun daga ranar
nasa a raina na dena jin haushin kowa dan ya
kirani da JUYA, tunda ga nan y'ar uwata ma ta
jini ta ya6an magana.
Sosai abin ya t'saye min a rai,har na sanar ma
makociya ta lokacin muna a tsohon gida. Sai ta
sanar ni ak'wai wani Malami ya ta6a yiwa
yayarta aiki irin nawa,a watan ta samu ciki.
Jim nai,zuwa wani lokaci nace zanyi shawara.
Ina fita naji sam abin bai k'wanta min ba,dan in
da abinda da nat'sana bai wuce bin malamai ba.
Wasa wasa har muka shiga shekara ta shida
aure, sam Salman ya sauya, abu kad'an hanci ni,
ba makawa ya fara d'aukar zigar y'an uwan shi
kila.
A satin ne kuma naje gidan su duba Umman shi,
sam ban kawo zan sami y'an uwan shi a gidan
ba.
Kusan sai nace d'aya ce bama y'ar tsama da
ita,sai ko Hajiyan shi.
Tana a k'wance a gado suke ya6an magana, sam
bata hana su, sai d'ai ma ta d'auke kai, shi yasa
na kasa gane inda ta dosa.
Da gan gan d'aya ta k'allo d'aya kamar yadda
suka saba, sai d'aya tace ma d'ayar tana ta
had'a kiba ina zata kai, duk ina kallon su, budar
bak'in ta sai cewa tai "ai ni tawa kibar da dalili,
ba kashi kawai take sau wa ba gidan Miji.
A ranar na kasa hakuri,har na sanarwa d'an
uwansu irin maganganun da suke ya6a min.
Sai tai murmushi ta k'allo Fure tana hawaye.
"Kin san mey yace min? Kai Fure ta k'ada, sai ta
tashi tai kitchen tukun ta dawo.
Har yanzun hawaye na binta, "budar bak'in
Salman sai cewa yai waye bazai so ganin
k'wanshi ba a rayuwa..
A ranar ya tabbatar min da cewar shekarun sa
na ja, a gaskiya zai kara aure dan wai ya min
kara...
Kuka ta fara Fure na lallashi, "wallahi a yadda
nake son Salman in ta gunshi ne wannan
matsalar zan zauna dashi har karshen rayuwa.
Ranar nayi kuka kamar nai mey,dan a fili ya nuna
ya gaji da Gaza wata ta rashin haihuwa.
"Zuciya batta kashi, Washegari na tambayi
unguwa, ba musu ya barni,ban zame ko'ina ba
sai wajen makociya ta, dama kamar tana jira,har
da ita mu kaje gun malamin da yayarta.
Zuwa na farko ya bani turare da layu kan in zan
k'wanta na d'aura layar a mara ta na shafa
turaren,in dai har mun kasance tare da salman
zan samu ciki.
Har yana fad'in wacce ta fini matsala ma ta
haihu bare ni. Hawaye ta goge,halamar abin da
ta tuno bai ba.
By
Feenat Ja'afar.
[4/27, 3:30 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
31_Haka ina jin ina gani nai "shirka", dan na
had'a Allah da wanin shi, sam ba yadda zaki ce
wannan mutumin Malami ne ba boka ba.
Ana nan ana nan,har wata na biyu ya kama
shiru,ba ciki ba dalilin shi, har na hakura, sai d'ai
in na tuna da gorin jama'a nakanji k'warin
g'wiwa.
Haka na nad'a muka koma wajen bokan nan chan
bayan gari, tuni sai ya fara sirkulen shi, kan ya
k'allo ni yana fad'in dole sai an min babban aiki,
ba musu nace na yarda,duk ban san meye
babban aikin ba,ni d'ai burina na fita sahun JUYA.
Turare ya kaini wani d'aki ya banka min, d'uk sai
da yasa na cire kaya na gaba d'aya, ganin na
t'saya gardama yasa yace in cire g'yale na da
dank'wali.
Sannan yace lalle-lalle gobe na dawo in ina son
haihuwa, sannan kar nai mishi gardama.
Har muka fito makociya ta da yayarta suna min
fad'an mey yasa na t'saya gardama? Kasa da
kaza,kasance war mun gaji yasa muka sauka
gidan yayar makociya ta.
Muna a gidan zaune sai ga nan y'ar matar ta
farko ta shigo tana masifar kan wai uwar bata
bar musu abinci ba. Yarinya har murguda baki
take, sai uwar taji kunyar gani zaune ta tashi ta
jata waje tana nad'a.
"Wato abinda naji yarinyar na fad'a wa uwar ba
karamin tsorata nai ba, ina k'allon makociyata
itama ta fita tana kumfar bak'in wai ta kara
mata.
Yarinya sai ashar take maka musu ita da uwar
tana Allah ya isanta.
Hakan ne yasa na leka dan ganin shin da uwar
take wannan zagin ko wa?
A inda nake ban mat'sa ba ina mai k'allon yadda
ake dam6e t'sakanin matar nan da y'arta tana
karo mata zagi da Allah ya isa, tuni nai d'aki na
suri jakata na barsu nan,ina jin makociya na kira
na gaba d'aya na rikice.
Tabbas Allah ya soni da har ya nunan wannan
abin da ido na, ba shakka wannan irin yaran su
ne wanda naje nema na kusa 6atar da kaina
wato " Y'AY'AN ALLAH BANI.
Tun daga ranar gani nake na ma Allah butulci,na
ci amanar Miji na dan na tu6e g'yale da dank'wali
gaban wani kato, sai d'ai nasan rashin abokin
shawara na gari ne ya ja min da son zuciya.
Ranar nai kukan nadama har naji ba dad'i, cikin
zafi na d'akko laya nasa mata kalanzir na kona,
sannan na tittilar da turaten yabi shadda.
Sam al'amarin haihuwa nama jingine ta gefe,na
hau istigfari zuwa ga Allah,bisa had'a shi da nai
da wanin shi.
Ana haka Salman ya gama gininshi muka tare,
sai d'ai da kaga gida kasan na zaman mata biyu
ne.
Anan ne na samu makociyar k'warai, mai nuna
min komai nufi ne na Allah, ita kad'ai nake kaiwa
kuka na naji dad'i.
Sam na nisanci kowa, in kinganni a gun dangin
Miji ko gidan k'anin Baban mu toh biki ake koh
suna.
Shima a tsatssaye zan shiga na fito, da wannan
kawai na soma samun sa'ida, sai kuma aka dawo
fad'in dan mijina yai kud'i shi yasa yanzu na fara
dagun kai.
Sai kawai na bisu a hakan. Har na shekara
takwas da aure.
Anan ne nake jin labarin dawowar likita gun
makociya ta, kan yanzu ya karo karatu ana ji
dashi.
Zuwan farko yai mamakin jin har yau ban haihu
ba, hakan ne yasa ya kara rubuta min ''HSG",
sannan ya k'ar6i numbern Salman.
Ran litinin sai naji yace na shirya muje asibiti
yana dan 6ata rai.
Kamar wanchan yauma na wahala gun wankin
cikin, sai d'ai g'wajin da ya fito ne yasa daga
ranar Salman ya d'aina zuwa asibitin, dan likita
ya tabbatar mishi da a gaskiya ba wani "hope",
wai k'allemun mahaifata d'uk sun ru6e,wato
"tubal damage" a gaskiya likita bai sanar ni ga
matsalar ba, amma na tsinkayi wayar Salman shi
da wani abokin shi,
Gaskiya karan nan ban "losing hope" ba,na
sanarwa Umman mu tace nai ta adu'a dan tanaji
ajikinta tabbas za naga dan kaina InshaAlllah
k'wana kusa.
Ana cikin haka Salman ya t'siri abin kirki,tashin
farko mu kaje Umara, muna dawo wa ya fara
koya min mota.
Sosai naji dad'in yadda baya damuwa a rashin
haihuwa ta yanzun, sannan in nace zani asibiti da
kanshi zai kaini ko ya ban mukulli. Kullum abu
d'aya ne in naje,sai likita ya rubuta min awun
fitsari d'uk karshen wata.
Sai ta karasa da d'an murmushi mai kamar kuka.
"Ranar ina zaune parlour ni da makociya ta ina
fad'a mata irin abinda Salman yake min na alkairi
tana murmushi sai gashi ya shigo da murna.
Wai nazo naga abin mamaki, a ranar salman ya
mallaka min mota tawa ta kashin kai. Sosai nai
murna,marar na baki misali, ana nan koh wata
biyu ba ai da yin haka ba naji a gari wai Salman
aure zai yi, har ma an kai sadaki.
Hawaye ta goge wanda ya zu6o mata, kan tai
murmushi, "kawai ni kuma sai na sa mishi ido
naga iya gudun ruwan shi.
A ranar wata laraba sai ga y'an gidan su nan
kusan su biyar wai sunzo ganin d'akin amarya
yadda yake tun kan tazo.
Ina jinsu suna yadda magana wai alkadari na
akan d'an uwansu ya karye tunda gashi da kanshi
ya nemi aure.
A ranar naji takaici, dan Salman ya nunan ni ba
komai bace, abu tun inaji a gari gashi har ya
tabbata.
Ranar kamar kullum nai shiri na nai d'akinshi,
yana a k'wance yana waya.
Yana ganina sai ya fara kiran wai zai kira, zai
kira, tuni na gane da amaryar yake waya.
Sai nai murmushi na zauna a gefen shi, tare da
d'aura kaina a kafadarshi, dak'yar na iya saita
hawaye na basu zubo ba, wai yau har Honey
Salman ke ce min? Dan takaici kawai sai na
zame na k'wanta.
Sai ya mat'so da tambayar koh lafiya? Kai kawai
na K'ada mishi, "kai kad'ai za ka iya bani
mutuncin da kowa zai ga d'auka Salman, kai ne
kawai za ka bada kofar da wani zai k'alleni yace
min ban isa ba... Sai na fara kuka.
Nan ya hau wayan ce wa,kan wallahi kunyar
fad'a min yake, sai nace mey fa? Sam sai na
nuna ban ma san komai ba.
Anan ya sanar ni komai ba ko kunya, kuma wai
saura wata biyu tazo. Kai kawai na k'ada, tare
da mai fatan alkairi.
Sam tunda aka fara rad'a rad'en auren Salman na
ma manta da zuwa asibiti na d'uk wata.
Sai da jiya ta ciwo ni akazo wai za'a kai kayan
amarya gobe ga nawa, harda fad'in fatan su ta
cika musu gida yara.
Sai nai murmushi kawai, a lokacin ne na tuno da
asibiti.
Fure ta k'allo tana goge hawayenta, itama Furen
harda kuka, ashe nata nafila ne akan wasu?
Hannunta Fatima ta ruko, "kinsan mey ya sani
kuka da naga "positive" a result na? Kai Fure ta
k'ada tana mai k'allonta.
Sai ta juya gefe da fuskarta, "wallahi tunda nake
ban ta6a jin kunya ta mahaliccina ba irinta yau,
na sa6a mishi, nai kuka,har nakance Kila wani
lefi nai wa Allah shi yasa bai ban haihuwa. "Nayi
kuka ne saboda Allah ya nunan komai lokaci ne,
gashi kuma na gani, cikin da ban ma san dashi
ba,gashi a zuwa d'aya ya saukar da Ayarshi
akaina.
By
Feenat Ja'afar.
[4/27, 5:31 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
32_"Sam na manta da cewa bawai rashin so
bane yasa Allah bai ban haihuwa ba,da So ne,da
na tabbatar ya bawa Nana Aisha(R A), dan Allah
na son d'uk wani abinda Manzon sa ke so, na
kuma sani