Author : Queen Safiyyert Category : Romance
ba,da sai
yace daga kan Pretty ya dat'se aure, hmm,wa
yaga "MIJIN MACE D'AYA na sis (Rufaida Omar).
Sai d'ai yasan K'ADDARAR shi ba a hannunshi
take ba,kawai d'ai "hope" ne. Lalle Fure kin ciri
tutar zama "MAR'ATTUS SALIHA",, wace
k'allonta ke sanya miji a farin ciki,wace rashin ta
a kusan shi ke sashi k'ewar ina ma tana kusa..
Wace ya yabe ta g'wana ce gun iya girki, sannan
k'wararriya gurin iya lafazi mai k'yau da ma'ana.
Tuni shima ya hau t'sara mata nashi salon,yasan
bacci kad'ai ke sa Pretty kashe waya,burin shi in
ta tashi ta bud'e ido da "hot message" nashi gare
ta. By Feenat
9/29/16, 2:36 AM - Queen Safiyyert馃憫: [4/26, 7:41 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
28_Sai kusan d'aya ta tashi,warai taji ta,a hankali
ta sako kafarta kasan gadon ta zura ta kalmin
sosonta na "bedroom"tai kitchen, mai sanyi
tasha,kan ta dawo d'aki ta d'au waya,tana
bud'ewa kuwa sai ga nan "text" nashi, sosai ya
ware ta cikin nutsuwa, kamar yasan a "mood"
d'in da take a ciki.
Sai da akai azahar kan sai ganan kiranshi.
Cike da murna ta d'auka tare da sallama.
"Y'an mata na ta tashi lafiya? Dariya ta sau mishi
cikin wata siga, tasan an so tsokana, kan taja
numfashi ta sauke,tsaf a k'unnenshi, tuni ta kara
narkar da murya,
"lafiya d'an samari na,"hope" kun sauka lafiya?
Shiru yai mata kan ya juyo, "lafiya,sai k'ewar ki,,
mey kike yanzun? Numfashin ta kara ja,kan tace
"k'ewar ka nake nima, sai kam ya ji dad'i, nan
suka cigaba da lalacewa cikin birnin su na su
kad'ai.
Kan su farga kusan 1hr suna a manne da wayar
juna.
Gida yace ta d'akko koh Maryam ne,dan Abba
har la'asar bai dawo ba,harda da d'an kukan
shag'wabarta, tuni ya hau lallashi kan yau ne
kawai.
A gida ta samu su Aisha,Adama ma sai gata ita
da yaronta kalil dan shekara 2,ganan tsohon ciki,
sai ta hau mata tsiya,
"A Yarinya,yi a hankali,in dai labor room ne tana
jiranki, kai tai kasa dashi, an tabo mata inda ke
mata kai kayi, Aisha ta k'allo ta," wai Furera ni
har yau kina sa zancen mutanan nan a ranki?
Baki Adama ta ta6e, "wallahi Aisha har mamakin
Pretty nake, wannan kananan kadagarun wallahi
in ni ce tuni an shani na warke,, dan ba wacce ta
isa takani na k'yale.
Murmushi tai, "bazaku gane ba ne ba Ada, ak'wai
ranar tankawar, tana nan zuwa.
K'wafa Adan tai, "amma kinsan nafi mamakin
yadda kika bar Hassana nacin tuwo a kanki? Ke
da kike da abin fad'i ahannu? Ki sau mata d'aya
kiga yadda bak'inta zaya rufe malama, ita da
miki gori wallahi har abada.
"Y'ar gidan tsohon najadu kawai.. Dariya suka
sau, "shege Adama,au Aunty,labari na tsoron ki,
kai Adan ta k'ada, "ai ni tun ranar Dinnern ku naji
komai gun Hanna.
Yau sirrin da Fure bata sani bama na gidan su
Hassana ta sani ka'f.
Sai dare ta d'au Maryam Ya Suleiman ya sauke
su.
Waya suke da AAAn ta tana d'an k'allon Maryam
itama dake waya tana d'an y'atsine wa kamar an
mata dole.
Data gama ta k'allota itama ta gama, "Oh ni
kam, Maryam anya bakki Aljanu? Baki Maryam
d'in ta ta6e, "Kila toh, sai Furen tai murmushi, ''ni
d'ai ki rufawa kanki asiri ki bar ruwan ido,kowa
yazo kice bai miki ba, tashi Maryam d'in tai tana
rage kayanta, kan ta hawo gadon, "ni fa bakar
k'arya ce ban so, wai fa in munyi aure d'uk
bayan sati zaina fita dani waje,mota sai wacce
na ga dama, hala k'aruna ne uban shin.. Dariya
Fure ta hau,kan tace "Allah shirye ki,tace "yoo
Allah kuwa,in gani a kasa man,ko katin dubu bai
ta6a turan ba.
Ita d'ai tana ta dariyar yadda Maryam ke zage
samarinta, ka'f ciki babu g'wanin ta.
Washegari da t'ar6ar Oga suka tashi, sosai take
yaba zafin naman Maryam, d'uk da d'ai ita ke
binta,t'sakanin su shekara biyu ne, Umma
takance Maryam guntun Fure tasha,dan ita harda
taso fin Fure a iyayi da rashin barin ta k'wana.
Matsalar d'aya ita tafi zama a Zaria, dan da sosai
zata k'ar6a ma Fure y'anci.
Kusan biyar d'in yamma sai gasu sun shigo shida
Mohammad mijin Hassana mey bin Ahmad, Fure
na d'aki sai Maryam dake kan dining tana ajiye
ruwan wanke hannu.
Da fara'a tai mishi sannu da zuwa,kan ta dire kan
mai cewa "Matar yaya mey aka mana ne? A
dirare take K'allonshi, Ahmad na kula dasu,sai ya
k'ada kai yai ciki.
Shikam k'allonta yake ganin wannan tafi Fure
fari,tsayi,jiki,da kuma k'yau. Ita kam ina wuni
kawai tace,sai ga nan Fure da fara'ar ta, ganin
irin k'allon da Moh'd kema Maryam yasa ta k'ada
kai, "a Abban Jidda tare ku ke? Da d'an wayan
ce yace eh,sai kuma ya d'an saci k'allon Maryam
dake ko'k'arin cire chargy, "yau,nifa tafiya
zanyi,ai ya dawo, Umm,sai ya ji har muryar su
d'aya da Fure, " toh ki jirani, sai ta dawo kan
Moh'd, "Abban Jidda zauna kan nazo,yau kam
mutuminka ne. Sai ta koma d'aki gun mijinta
tana mai ina ma ina ma..
Maryam na ganin haka ita tai d'akin
bak'i dan kimtsa kayanta sannan da gujewa
k'allon Moh'd.
Sai da ta jiyo hayaniyar su ta fito rataye da jaka
tana yafa g'yale, dan tsaf in ba haka tai ba yanzu
zasu ce sai ta kara k'wana.
Da murmushi Ahmad ya k'allota, "madam
kenan,kamar muna koranki haka? Fure ta k'alla,
kan tace"ai na muku, g'wara na tafi gun Umma
ta.
Ta sauke kan mutuminta,karan nan suna had'a
ido sai yai kasa da kai da murmushi yana d'anna
waya, sai ta d'auke kai tare da dan ta6e baki.
Sudai su Fure na ganin ikon Allah.
Dak'yar Ahmad yasa ta kara k'wana, harda d'an
bubbuga kafa kan bata so hakan ba, "eh munji,
kawo jakar, Fure ta k'ar6a takai d'aki.
Ba sai ga mutuminka ya dawo Washegari ba, tun
goma sai gashi sun shigo shida yayan nashi wai
daga "jogging" yake bayan da mota yazo...Lol.
Ita d'ai Fure sai dariyar ciki take,ta Allah Amin,
wallahi zata so wannan "dramar" dan zatai dad'in
k'allo t'sakanin ta Hassana.
Anan yai break yana d'an k'allon d'akin da
Maryam ta shiga jiya, d'uk Ahmad na kula
dashi,zai so zargin shi ya tabbata,amma kawai
sai ya basar dan ganin iya gudun ruwan shi.
Sai k'wa gashi ya k'allo yayan nashi,"ni yaya
bakuwar ku ta tafi ne? K'allon da Ahmad ke
mishi ne yasa ya hau sosa keya, "no'' ba fa wani
abin bane,,atoh, sai ya d'au tea ya kai baki,bai
zata ba ya ji yayan nashi ya k'walo kiran
Maryam,tuni sai ga Moh'd ya k'ware, dan fa
Maryam ta bashi tsoro jiya da wannan k'allon
nata.
Fitowarta a wanka kenan ta sa kaya, hijab ta zira
ta amsa da d'an k'arfi kan tai waje.
Ganin Moh'd yasa ta d'an kama kai, "Na'am
yaya,tashi Ahmad d'in yai yaja kujera, yana
murmushi ya nuna Moh'd,"ga nan mai kiran
ki,ruwan wankin hannu zaki bashi wai.
Sai ta k'allo Moh'd d'in da yai tsuru tsuru yana
k'allonta. Dariyar shi AAn ya kunshe, ganin zata
tafi yace,"au,ma manta,k'ani na ne fa, mai bi
min,yake tai musu,tace "ina k'wana.
Bata jira mey zai ce ba tai kitchen debo ruwan.
"Haba bros, wallah tsoron yarinyar nan nake fa,
kuma.. Sai yai shiru yana sosa keya, kai yayan
nashi ya k'ada.
Sai ya bashi gu yana dariya jin motsin Maryam
zata fito.
Yanayin da yake ne yaso ya bata dariya,d'uk ya
susuce, ruwan na hannunta ta mika mishi,kawai
sai yai sakare! Yana k'allon ta,kai ta ka'rkatar
tana dan mishi fari cikin murmushi tare da
matsar da ruwan kusan dashi.
Sai ta bashi dariya tare da kai hannu zai wanke
ta d'ang'warar kan table d'in tare da yin gaba
kamar ba ita ba. Kai ya k'ada, shi yasa yace
tsoron ta yake.
A gaskiya Maryam ta mishi,sosai ba k'arya sai
d'ai taya zai fara tunkarar ta da tsoron?
K'wada wa masu gidan kira yai kan shi zai wuce.
Sai ga nan Fure ta fito tana d'an dariya jin mitar
Maryam kan k'allon da Moh'd ke mata.
"A,ka bari ya fito,yanzun,ina zuwa, sai ta nufi
d'akin su.
Kusan a tare suka fito da Maryam, masu gidan
sai y'ar dariya suke,shi yana k'allon Moh'd ita na
k'allon Maryam, "wai mintsinin ki ake ne
maryam,? Baki ta turo, ''nifa tafiya ta zanyi,
kawai ku barni, ta karasa tana dan magana
kamar mai shirin kuka.
Ahmad ya k'ada kai, "toh munji, amma gobe zaki
zo?
Kai k'ada,"nikam gobe zan bar garin,Zaria ma
zan gudu.
Yin duniya taki zama, suna k'allon yadda suke
dan k'allon juna,ita Maryam na basar wa. Moh'd
bai zata ba ya ji Ahmad yace "d'an sauke ta da
Allah Bros, sai ya k'allo Maryam d'in da tai kicin
kicin, sai Ahmad yace," koh zaki bari mu fita
anjima? Da sauri ta k'ada kai, dan tasan yanzu
sai su kara rike ta.
Shikam kamar an mishi gafara yaji, da azama ba
musu ya tashi yana musu sallama.
A mota suna tafe yana murmushi shi d'aya, ji
yake kamar ma ace man Maryam ta zama tashi
ne zai kaita unguwa.
Kanta duk'e ta ce mishi "left" k'allo ta yai, kanta
na waya, sai yai yadda tace, suna dan kara gaba
ta kat'se shi da "right".
Sai yai murmushi, yana son mace mai aji. Da
"left'' right" suka zo inda zai sauke ta.
Da mamakin shi sai yaga ba gidan su Furen
bane,dan rabon shi da gidan tun suna na kasa,da
ta barshi chan zai kaita.
Godiya ta mishi zata fita yace "Maryam, sai ta
juyo tare da tsare shi da ido, sai ya kuma hau
kame kame.
"I thought ke K'anwar Matar yaya ce? Kai ta
k'ada, "K'awarta ce.
Zata kara fita yace, "OK, ok,nan ne gidan ku? Sai
ta kara k'ada kai, "Umm Umm.. Sai ya marairaice
mata, "dan k'watanta min, K'allonshi tai, kan ta
k'ada kai, "a unguwar zana nake,layin y'an kara..
Ido ya waro, zata kara fita yai saurin tsayarta,
"meye zana da kara? A takaice tace mishi
"Unguwa ce.
Bata jira ba tai waje ta barshi baki sake.
Har ta shige gida yana k'allonta.
Da yaje gida kuwa Allah-Allah yake yamma tayi.
Yadda ya dinga k'waliya kai kace gun d'aurin
aurenshi zashi, har Hassana dake K'allonshi ta
kasa jurewa. "Wai Abban Jidda yau ina zuwa
haka da wannan irin d'aukar wankan? Murmushi
yai, ba tare da ya k'alleta ba yace "waje mai
mahimmanci, sai ya juyo, "ke d'ai nayi k'yau?
Baki ta ta6e, kan tai mai banza, shi ko kula da
cikar da take bai ba,burin shi kawai ya isa ga
unguwar Zana layin Y'an kara.
By
Feenat Ja'afar.
[4/27, 12:10 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
29_Sukam su Fure tun fitar su tai gun tarairayar
mijinta,sai d'ai tana ga kamar Maryam zata bata
shirin, wallahi har ta gama hasko Maryam a
matsayin kishiyar Hassana, ita d'ai kawai burinta
Allah kai Damo ga Harawa.
T'saye suke gaban madubi tana 6alle mishi
ma6allin rigarshi suna cikin nishad'i.
Sai kamshi yake zubawa.
Hannu ta mika tare da d'akko hula tana kafa
mishi, sai ta d'an mat'sa tana dubanshi tana rike
ha6a, "ummm...MashaAllah.. Murmushi yai,kan
ya tako gareta, "ke ne Mashaallah, sai kara k'yau
kike kullum, ya rukota,''meye sirrin.. Baki ta kai
k'unnenshi ta rad'a mishi a hankali "So da kaunar
ka ne. Murmushi yai, kamar kar ya fita, kawai sai
ya ruk'unk'umo ta yana d'an shinshina wuyanta
tana dariya.
Sallamar Moh'd ce tasa shi dagowa yana k'allon
Furen, "Oh Allah,, waye wannan? Dariya ta sa,
"bari na dubo, sai ya k'ada mata kai "no bari
naga.
A bak'in gado ta zauna tabi shi da k'allo har ya
fita,sai ta sauke nauyayyen ajiyar zuciya, tana
matukar son Uncle d'in ta, sam bata kaunar yai
mata nisa.
Da dariya ya dawo,yana "fito kiga abin mamaki,
yafo g'yale. Cikin azama ta biyo shi.
Muh'd ne yai k'ankane akan kujera. Yana ganinsu
ya g'yara zama. A kujerar mai mutun d'aya suka
zauna suna fuskantar shi,ita na kan hannun
kujerar, haba,shi yasa suke ba shi sha'awa, sam
shi ba'a g'wada mishi soyayya a gida, tuni ya ji
ya kara zumudi akan K'awar Fure.
"Kin ganshi wai Maryam ya karade nema wai bai
same ta ba,shine yazo ki mai dalili..ya karasa
suna dariya, k'allo su yai, gaba d'aya ya gaji
neman wani unguwar zana layin Y'an kara.
"Matar yaya ki taimake ni, da gaske K'awar ki ta
wahalar ni, mai na har ya kare a neman Unguwar
Zana Layin Y'an kara... Dariya sosai ya basu, har
ya soma k'uluwa kuwa.
Dak'yar Fure ta t'sagaita da ta ta, "kai amma
tasha da kai fa, Ahmad ya k'ada kai, "Maryam
ake fad'a maka, sosai "style" nata ke burgeni fa
Allah, , sai suka kara sa dariya.
K'wafa yai,kan ya tsiyaya ruwan dake roba a
dining ya dawo,
"Au,dariya ma na baku ina sanarku abinda K'awar
ku ta min? Kai Fure ta k'ada mishi, tana d'an
ta6a Ahmad kan yai shiru.
Kawai sai ya sa musu ido.
"Maryam K'anwata tace fa,UWA D'AYA(na Aunty
YBK),
"sannan ba wani layin zana ko kara da take, sai
ta k'allo shi, "toh kai wane unguwa ka kaita? Ba
zuciya kuwa ya fad'a mata cikin mamaki, sai ta
kara kunshe dariya, "nan take da zama,iskancin
Maryam ne kawai.
Ahmad yace "toh mey ta ma irin wannan nema
haka bros? Waya ya ciro,"ku ban numbern ta
kawai, daga baya zaku ji komai.
Wasa sukai ta mishi da hankali,har sai da ya fito
6aro 6aro yace shi fa Sonta yake.
Tab,yau ake yinta inji Fure a ranta, lalle lokaci
yayi dazata danawa Hassy Bom, fatan ta Allah
yasa Maryam ta yadda da Moh'd kawai.
Sam bata nuna ma Ahmad murnar ta a fili ba, sai
ma shi ke nuna tashi, tunda muh'd ya biyo sahun
shi.
Wasa wasa kullum sai yazo ma su Fure, dan
Washegari Maryam ta wuce Zaria da zummar
karasa satin ta biyu.
Sai d'ai kusan kullum sai ya kirata a waya kan
wani bawan Allah ne mai kaunar ta Fisabilillahi.
Binshi take a haka, dan Fure ta bata komai "in
details".
Kamar yadda suka saba shawara da Momy in
abin su ya tashi yauma nan Muh'd yaje da kokon
shi, dan mud'in yasan in Momy ta yarda toh
kamar kowa ya yarda da batun karin auren shi.
Sosai yai mamakin Amin cewar Momy a take,sai
d'ai ya boye matar da zai aura jin Momyn na
mishi fad'an kar ya kara jaju6o musu irin su
Hassana.
Dan tuni ta dawo a rakiyar ta, ganin uban Hassyn
bai ya tabuka komai ko ta haihu,a ganinta da ita
da y'ar matsiyata Fure d'uk d'aya.
Sai d'ai yai shiru yana jinta, fad'i take "karan nan
a ni koh AAA a gidan nan, sam ban ta6a cin ka'ro
D'a mai taurin kan Ahmad ba, in banda haka ina
gami t'sakanin waccan kod'dadiyar matar tashi
da Rukky? Kai ya k'ada mata, "Momy babu kam,
sai tai k'wafa, "atoh,ka d'ai za6a ka darje karan
nan,kar ka kara bamu kunya. Kai ya k'ada, yana
mai tunanin randa Momy zata san wa zai yayu6o
musun.
Gida ya koma cike da farin ciki,tana a parlour
yara na ta tsula ihu, amma sam ita ko a jikinta,
cikin fad'a ya fara mitar tabani bazata kula su
ba?
Sai ta ta6e baki tare da sau mar harar haushi,
"tunda kace baza'a d'akko musu "Nanny" ba toh
mey yai ruwanka acikin ihun su? Sunkuwa yai zai
d'au mahma yana k'ada kai, a ranshi yana "kin
kusa gama na kud'in ki.
Sai d'ai yana daga babyn ya kawar da kai, kashi
tai a "pampers" har ya fara fitowa.
Kamar ya rufe ta da duka ya ji, "mey kike ji dashi
ne Hassy? A y'atsine ta k'allo shi, "da akai mey?
Kai ya jijjiga, kan ya komarta ya k'wantar, "kin
kusa gama na kud'in ki, kiyi komai ba komai,
amma ki tabbatar kan na fito kinsan nayi da y'ar
nan. Da harara ta bishi har ya kule, kawai
haushin shi take ji,dan tayi tayi ya sai mata mota
fir yaki, ga nan Fure karamar d'angarta tana
murza mota, shine fa k'wana biyu take sakar
iskanci son rai, a ganinta hakan zai sa ya sai
mata.
Fure ce k'wance ta k'allon kofa lokaci-lokaci, da
halama mai gidan take jira, ga ya manta
wayanshi a gida.
Hannu ta kai kan wayar jin ana kira, "Huwaila"
taga an rubuta, sai ta ajiye taki d'auka har ta
yanke, tunanin dabi'ar Huwailan take a gare ta,
sai ga nan wani kiran ya sake shigowa.
Kamar kar ta d'auka, sai d'ai ta share ta daga da
zummar sanarta baya gidan.
Ba ko sallama ta sau kuka cikin wayar, "Bros dan
Allah ku dawo, gashi nan yana kara kirarin shi
wallahi yara biyu yake son ya tara sai dai nai
"abortion, daga magana har mari na yai.. Furen
naji daga cikin wayar mijin Huwailan na fad'in ta
sanarwa kowa ma, amma shi kam bai san da
wani ciki ba, kuma in aka takurashi zaiyi rashin
mutunci.
Da sauri Huwailan tace "kaji koh Bros, kaji da
k'unnenka... Da sauri Fure ta kat'seta da "za'a
sanarshi in ya iso, sai ta kashe ta bar Huwaila da
baki sake.
Fure cike da mamaki tai t'sam da tunanin fad'an
Huwaila da mijinta, chan AA ya nufa kenan tun
dazun?
Tab,yau ake yinta, yanzu dama irin mugun zaman
da Huwaila take a gidan miji akan haihuwa? Wai
bai son tara yara, kuma harda mari? Shin ina
gatan nata da isar? Lalle ta kara gode Allah,
wasu nan suna nema,gashi ita mai gorin tana
haifa amma mijin bai so, mey kenan akai?
Kai ta kara jinjina mata, kawai sai taji tausayin
ta, dan sosai taci a tausaya,daga mari gaba ai
sai duka.
Tana haka sai ga nan mai gidan ya shigo shida
Mohammad, har yanzun mita yake akan mijin
Huwaila.
Har suka zo k'wanciya yana na nata abu d'aya,
dan tsaf ya nuna musu shifa ga ra'ayin shi. Ga
nan wayar da sukai da Huwaila dazun har marin
ta sanar shi.
Dak'yar Fure ta samu ya dan lafa tana dan
"massaging'' kanshi.
"Allah Pretty mutum wani bai da godiyar Allah
sam, tsam tai tana jinshi, "ki duba wani ya samu
Allah ya k'wace au duk'a, wani koh d'aya bai
samu ba nema yake amma lokaci bai zo ba, sai
shi ne dan t'sabar butulci ma Allah ya bashi
su,sannan yai mishi wadata sannan yace bai so?
Wace iriyar rayuwa ce Furii?
Tsam ta k'wanto kanshi cinyarta cikin nutsuwa
take dan shafa kanshi, "kai hakuri, nasan da
ciwo, amma ka d'auka wannan kad'an daga
dabi'ar dan Adam, kawai adu'a yake nema Allah
ya shirye shi Dear.
Kai ya k'ada, "da k'yar ne,dan fa ra'ayinshi ne na
rashin son tara yara, sam tun farko banso auren
Huwaila da mutumin nan ba, amma fir ta dage ita
sai shi,irin abinda nake hanga mata gaba kenan.
Murmushi tai,kan tace "adu'a zaku mata,Allah
kawo mata sauki.
Kai ya k'ada,"toh Amin.
Har suka k'wanta tunani ne fal a ranta.
Hakan yasa ta kara gode ma Allah,dan ya bata
Ni'ima sosai a rayuwa. Wanda in zata butulce
dan Allah ya tauye mata d'aya batai ma kanta
adalci ba.
Dan tayi imani tafi Huwaila k'wanciyar hankali a
gidan Miji.
By
Feenat Ja'afar.
[4/27, 12:10 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
30_Abu kamar wasa maganar Muh'd da Maryam
ta tabbata, dan ko gare ta bata ta6a jin wani
saurayi a rayuwarta ba sai Moh'd, bayan dan jan
ajinta daga baya ta yarde, tuni suka dinke.
Sosai Fure tai matukar Farin ciki da wannan
had'i, zata so ganin yadda Momy zataji wa Muh'd
zai aura, sannan za taso sui ar'ba da Hassy ido
da ido.
Dan fa har anje tambaya, d'uk da Abba yaso da
yaki yarda ganin yaushe ma yayi aure da zai kara
mata? Sannan ga nan sauran yayunshi ba mai
mata biyu.
Yau ne ranar da likitan da take gani yace ta
dawo,d'uk da tasa a ranta daga yau ta bar jelar
asibiti, ga nan Ogan baya gari.
Kamar kullum yau ma ya gama dubata yace
komai "normal" lokaci ne d'ai bai yi ba.
Sai ya bata kan taje tai "blood test", dan shi kam
bai gane ba, gashi tace period nata ya wuce da
k'wana yau goma.
A "lab'' ta zauna rint'se da ido za'a d'au jikinta.
Sosai ta t'sani ganin allura,amma dake abinda rai
ke so ne shi yasa ta yarda.
Auduga ya bata ta d'anne gun yace ta zauna a
chan ta d'an jira.
Kusa da wata mata ta zauna,a hankali taji kamar
matar na shesshekar kuka kanta duk'e. Da
mamaki ta zata ko batta lafiya ne, sai tace mata
"sannu baiwar Allah, kiyi adu'a ki bar kuka.
A hankali matar ta dago,zata fi Furen da shekaru
kusan bak'wai, idonta ya k'ada yai jajir halamar
tai kuka har ta gode Allah.
Sai tai ma Furen murmushi