JUYA Lokacin da Kaddara Ta Sauya Komai by Queen Safiyyert

Author :  Queen Safiyyert Category :  Romance

Chapter   16 / 18

45K to 48K   out of 51.2K words

sauri sukai kanta, "Momy lafiya? Hannu
take kaiwa baki,da sauri Huwaila ta d'akko mata
ruwa ta bata,zuwa chan ta nutsu. "Yau Alhaji ya
nunan karshe na,yai min tozarci... nan ta
k'washe yadda sukai da Abban ta sanarsu, tuni
suka hau zigata kan ka'r taje ko'ina, su d'in wa??
~~~~~~~~~~~~~~~ "Allah takaddarmu zaku
bamu, ka sanar da ya Ahmad ma tun wuri...
K'allon Maryam d'in Furen kawai take yadda ta
rufe ido tana y'arfawa Muh'd masifa cikin
waya,Kai ta k'ada, ina ma zata iya yiwa AAA
haka ko taji saukin zugin zuciyarta? kawai sai ga
nan hawaye ya zubo mata,bayan hannunta tasa
ta goge, tun jiya AAA yake aiko text amma ta
kasa ma k'allon wayar bare ta d'auka ta gani.
kamar had'in baki kuwa Maryam na gama waya
sai ga nan call na AAA akaran farko tun jiya.
Sautin "Ringtone" nashi na ("nothing gonna
change my love 4 u") ne yasa ta k'alli
wayar,maimakon taji sanyi kamar kullum in AAA
na mata baitin koh kidan na tashi kawai sai taji
wani haushi da t'sanar wakar ya rufe ta. Cikin
zafin nama da masifa ta d'au wayar ta seta
bango da niyar k'wad'a ta Umma ta shigo da
Hussein na kuka... A hankali ta zame wayar ta
fad'i kan gado, kawai sai ta sa ma wayar kuka,
ga Kukan Hussein. Da k'allo Umma ta bita baki
sake, tasan Fure bata huce ba, ita so ma take
taji tai koh masifar irinta Maryam koh taji
sa'ida,amma ina,tun jiya take kuka da tunani.
Cikin nut'suwa Umma ta zauna a kusanta, sai ga
nan Hasna ma an kawota, tuni sai suka karade
gidan kuka, har sun ma rasa wa zasu lallasa. Sai
da tai mai isarta Umma da K'anwarta na
k'allonta kan tai shiru,sai ta hau goge ido kan ta
mika ma su Umman hannu, ba musu suka d'aura
Hussein, dan Hasna har ta gaji da kuka tasa
hannu a baki. D'uk sai suka basu tausayi. Ajiyar
zuciya tasau, tuni sai ta dan samu sa'ida ganin
yaranta yayin shayarsu, tasan koh su zasu iya
maye mata g'urbin AAA a farin ciki. Zuwa wani
lokaci har ta ware,sai d'ai d'uk ta koma marar
baki,ido kawai ne nata. Haka AAA yai ta kira ba
d'auka, gun abincintq ma suna ta neman ta, daga
karshe ta d'auka, sun hau mata lissafi kenan ta
kat'sesu da cewa su rufe "restaurant" d'in su
kaima AAA mukulli, bata jira su ba ta kashe ma
wayar d'uk tana huci. Da yamma ta fito a
wanka,d'uk kanta sai sara mata yake, har wani
jiri-jiri ta fara ji,a hankali ta nemi gefen gado ta
zauna tare da rintse ido, ji take tamkar kan zai
rabe biyu. Kukan Abulkair ne da kamshin turaren
AAA yasa ta d'an dago kai da sauri, yana t'saye
rike da Hasna duk ya marairaice fuska. Gefe tai
da kanta,sai kawai ya kut'so kai, wato tana
wanka suka shigo?amma ba mai yinkurin fitarsu
a gidan nan?... "Pretty"... A zabure ta mike ido
rufe tana tuna mishi hanyar kofa,sai d'ai ta kasa
furta komai sakamakon wani sarawa da kanta
yayi. Cikin sanyin murya tace "fita.... Da azama
ya k'wantar da Hasna ya yo gunta ganin ta fara
layi hannu rike da kai, cikin k'arfin hali da ganin
dusu-dusu tace"kar ka ra6e ni... Maganar ce ta
sarke jin K'wak'walwarta ta bar aiki,dulum take
gani ba koh dusu dusu, a chan nesa take jiyo
AAAn na kiranta yana dan girgiza kafad'arta, sai
d'ai ina,d'uk ta sake mishi jikinta tamkar wata
macacc....... By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 3:01 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 52_Da rige rige su
Umma suka doshi d'akin jin irin kiran da AAAn ke
ma Fure, turus sukai ganin yadda AA ke jijjiga ta
amma bata koh mot'si, kawai sai Umma ta ju ya
jiki a sanyaye,ta saddakar sunyi ajalin y'arta ta,
Maryam tai saurin karasa wa tana kiranta,a
yanayinda take yasa Muh'd fita a d'akin, tuni
cikin kuka ta fara in sun kashe mata y'ar uwa
wallah su kuka da kansu... Ganin ba nasara yasa
AAA ya zame rike da Furen yana kuka tamkar
wani yaro... Ya ma manta da wani asibiti, yasan
harda sa hannunshi a mutuwar Fure.... Tamkar
had'in baki su Hasna suma suka sau kuka,
Hussein dake gado shima ya fara. Tamkar wani
zautacce haka yake surutai rike da Furen yana
kuka. Tamkar an hankad'o Ya Suleiman sai gashi
cikin d'akin, shi bai fuskanci abin da Umma ke
fad'a a waya ba,yasan d'ai tana ta ambaton Fure
cikin kuka. "Subhanallah.. Mey ya samu Furera?
Da sauri AAAn ya dago kai ido jajir, tuni Maryam
ta amshe,"yaya sun kashe mana ita ne,sun
huta... Cikin azama ya Suleiman ya kamo hannun
Furen,sai ya k'allo su, "muje asibiti, ku kamata,,
AAA ido kawai ya zira mishi,sai da ya kara fadi
kan Maryam ta d'akko ma Furen doguwar riga
suka zira mata.. Ya Suleiman zai d'auke ta AAAn
ya rigashi, kamar Yarinya ya sunkuceta sukai
waje,da ido Umma ta bisu,dan tasan sai wani
ikon Allahn Fure, ga ihun yara na yunwa. Anyi
sa'a likitoci sun k'ar6e ta taimakon gaggawa,tuni
Muh'd ya sanar ma Mama halin da ake
ciki,lallashi kawai Ya Suleiman ke mishi,dan ya
gano a halin da yake ciki, ba'a jima ba sai ga nan
Mama da Ummi. Sun samu ta farfado, sai d'ai
har yanzun ido rufe amma tana numfashi,
halamar an mata allurar bacci. A hankali ta fara
juya kanta tana mot'si da ido halamar tana son
bud'e su, cikin hankali ta bud'e idon ta sauke su
kan sling,ba abinda take ji sai karar bugun agogo
da d'an ajiyar zuciya a kusan kanta. Sai ta sauke
idonta kan waje,AAA ke rike da hannunta mai
allura ya d'aura kai a gefen gadon.. Tuni ta fara
tuno abinda da ya wakana,kawai sai ta fashe da
kuka tana ko'k'arin zame hannunta, a ka'ro na
biyu ta t'sallake rijiya da baya. Da sauri ya dago
cikin magagin bacci,ganin Furiin ta farfado yasa
yai saurin tashi. "Pretty... "Sannu..."in ke miki
ciwo?.. Ido ta rint'se tare da juyar da kanta,tuni
sai ya rikice mata, burinshi ta bar kuka koh dan
yadda Bpn ta ya hau.. "Ki yafe ni Pretty,ki
taimaken ki bar kuka ko dan lafiyar ki,dan Allah...
Shima sai ya sa mata, "kar ki maishe ni da yara
na marayu please Furii...please. Chak kukan ya
t'saya jin ya ambaci yaranta, tasan d'uk inda
suke suna chan suna neman ta ko dan abincin
su.. Tamkar an t'sikareta ta mike tare da k'allon
agogo, sha biyu na dare,sai ta cije le6e tare da
furta "Hasna... Ido ta sauke kan AAA, yadda ya
kusanto ta yana hawaye yasa d'uk sai ya kashe
mata jiki,t'sanin mace da mijinta sai Allah, tuni
sai ta ji haushin shi ya ragu ranta,hannu takai
kan kuncinshi da hawaye ke sauka tana girgiza
mishi kai itama hawayen na zuba... SO HANA
GANIN LEFI.... K'allon-k'allo kawai suke kowa na
goge ma d'an uwanshi, yasan akan Furii komai
zai indai zata d'aina fushi dashi,sai ta k'wanto
shi kafad'arta kamar yaro ta hau lallashi,tuni sai
ya kara samun k'warin g'wiwar sanarta sirrin
ranshi a kullum har sai da ya tabbatar ta saki
ajiyar zuciya ta gamsuwa da hasashen shi. Kanta
ya dago,kan ya hau sanarta kan tai hakuri bisa
fad'in da yai taje gida,yasan mey yake nufi da
hakan ba wai rashin so bane. "Pretty ina son
k'ar6a miki y'ancin ki gun su Aunty Jidda ne,su
san darajarki su martabaki, ni nasan wataran
zakiyi mamaki,dan da kansu zasu zo bikonki....
Murmushi tai tare da kara lafe mishi a jiki, tasan
fad'i yake dan ta kara sanyaya, wannan bikon sai
d'ai cikin mafarkinshi. "A jiki na ina jin su Hasna
na chan suna kuka, ni kam da an kawo min su...
Sai ta karasa da kalar tausayi,jijjiga ta ya fara
halamar rarrashi, ("I know), amma dazun kusan
takwas naje ni da Mama, an siya musu madara
da taimakon Dr,gaskiya suna da wayo,barin
Hussein, da ya ji an sa mishi (feeder) zai fara
kuka, dak'yar d'ai muka samu suka sha kad'an da
taimakon Umma da Mama sukai bacci. Ajiyar
zuciya ta sau,kan tace "Aiya,ni nafi tausayin
Hasna, mai rauni ce... Dak'yar ya lallaso ta ruwa
ya kare ya fidda Mata ruwan kan ya bata abinci
suka ci tare kan suka k'wanta. Washegari tun
asuba yaje gidan su Umma. Da Abba sukai ka'ro
ya dawo masallaci, sun gaisa yake tambayar Mai
jiki yaga sai sunke kai yake,sai Abban yai
murmushi, "Amadu shigo daga ciki, yau bamui
bacci ba sam yaran nan masu wayo.. Ai kam
suna shiga Muryar su Hussein ce ta fara amsa
musu sallamar su,Abba yace "kaji ba? Fur sunki
shan madarar sai karamar ke sha. Umma yai ma
magana suka fito parlour,ba su ko jima ba
Maryam da K'anwar Umma suka nufi gun Fure
dasu. Tana ganin yaran ta ajiye kofin shayin,
Hasna ta fara k'ar6a suna mata t'siyar tafi ji da
ita,sai d'ai ita baccinta ma take, ana bata su
Hussein tuni suka kama mikis kake jinsu ba
kuka. Sai tai murmushi tare da k'allo AAA..
Idonshi na kanta yana jijjiga Hasna a hankali
yana murmushi, sai itama tai mishi,Maryam dake
k'allonsu ta ta6e baki. By Feenat Ja'afar. 庐NWA.
Feenat.mywapblog.com
9/29/16, 3:02 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 53_D'uk da Mama ta
sanar ma su Momy Fure na asibiti ba wanda
yaje,d'uk Abba na hankalce dasu. K'wana biyu
aka sallame su da sharadin ba taron suna. Kusan
gidan Umma ya dawo wajen zaman AAA,dak'yar
yake samun lekawa Store, d'uk ragamar ya
barma su Hassan da wani dan K'anwar Mama,
d'uk sai ya same su masu amana. Sannan ya
danka ma masu kula da restuarant kan su cigaba
da gashi. "Abbansu yau na tura banki ance
account na ya d'aina aiki,sannan an sanarni da
sa hannunka, shin zan iya sanin dalili?... Abincin
shi kawai yake ci yaki tanka mata yana d'anna
waya. "Alhaji magana nake fa?... Tuni ta fara
kuluwa, dan yau k'wana biyu kenan ya d'auke
mata wuta, wanda tasan d'uk bai rasa nasaba da
kin bikon Fure da taki yi. Sannan bata tunanin yi
ko da a gaba ne. Sai da ya cinye abincin shi tass
kan ya k'allota fuska ba walwala. "Ince d'ai ni
nan na bud'e miki shi? Kai ta k'ada mishi, "toh
daga yau na rufe shi, kuma ya zama rana ta
karshe da zaki min magana akan shi.. Tashi yai
ya barta baki sake ya rufo d'akinshi, mey kenan
hakan yake nufi? Ita Alhaji zai ma wannan
wulakancin? Bayan ya hanata d'uk wasu
mukullan motar gidan sai d'ai su Huwaila su
kaisu a tasu shine ya bullo tanan? Kai ta k'ada,
"mu zuba toh. Bangarenta ta koma, sosai take da
bidar kud'i a wannan lokacin, tunaninta ina zata
samu? Dan d'ai ita kam tafi k'arfin aro... Tanan
parlour d'uk abun d'uniya ya isheta sai ga nan
Huwaila ta shigo mata da kuka. "Momy kiji Abba
ya sa an k'ulle gidan da ya ban ya kuma K'wace
mukullin motata, ina haushin wannan na wuce
cirar kud'i Momy chan ma yai blocking.. K'allonta
kawai Momyn take,mey wai hakan yake nufi?..
"Momy daga zuwa jin ba'asi ya k'ar6e min
mukulli,kuma wai wallahi kan gobe na tattare na
koma gidan mijina.... Dan Allah Momy ki taimake
ni, har mari yau nasha gun Abba... Da sauri
momyn ta k'allo ta, ta ma kasa cewa komai,
abinda Abba bai ta6a ba yau ta gani. Kan ai sati
harta Y'an aikin gidan Abba ya koresu,Momy ita
zatai girki,shara da wanke-wanke,dad'inta d'aya
wanki inji ke mata sai shanyawa, tuni Huwaila ta
koma gidan miji, nan ta tarar da wata t'siyar, dan
fir yace aure zai kara ga mai bin t'sarinshi na
rashin son yara. Ga Aunty Jidda itama ya tada
mata wuta,har gida ya bita shida mijinta, kan ta
tattara ta bashi mukullin gidanshi da mota tabi
mijinta, dan ya sanarsu tun ba yau ba shi bai
saki Jidda ba,ba kuma zai saki ba har abada...
Ranar Aunty Jidda kuka tai taima Abba kan ita
zamanta ita kad'ai yafi mata, Abba yace toh ba a
gidan shi ba. Gaba d'aya Abba ya sasu a kasa
mai wuya, an saba jin dad'i da fashaka yanzu
komai ya yanke, tun Momy na fushi dashi har ta
fara neman sulhu sai d'ai shi yace bai san
wannan ba, ta cika sharadinshi akan su kawai.
Zaune tai a kan dining tai tagumi da hannu d'aya,
sai chakala abinci take,yanzu cin abinci ya zama
sai d'ai taci dan yunwa, abinci in ba na gidan
AAA ba jinshi take salam ko da kuwa nata ne...
T'sawan sati uku kenan tai missing abincin
Fure,wanda har in taga AAA a sashenta takan
k'alli hannunshi, sai d'ai tasan Fure tai musu
nisa.... Ajiyar zuciya ta saka,kan ta ture abincin
gefe,komai ya t'saya musu chak ita da
yaranta,musamman Huwaila da Miji ke shirin aure
wannan satin, sam bai da mutunci shi,dan ko
Momyn baiya ragarma sai d'ai Abba,dan in
takamarsu kud'i shima yana dashi,amma yanzu
fur ya rufe aljihunshi gun Huwaila... Kullum cikin
yi ma Momy korafi take,gasu basu aro ko dan
ka'r ace sun gaza. Dafata akai a cinyarta, da
sauri ta k'allo gun, AAA ne d'uk ya marairaice
fuska, d'uk tausayin ta ya fara ji,dan yasan Abba
ya takureta da yawa... Kai ta k'auda, dan har yau
fushi take dasu da Mama,a ganinta d'uk su suka
ja mata Alhaji ya maisheta Talakar k'arfi da yaji..
D'uk da yasan ko ya gaidata kamar kullum ba
zata amsa ba, hannunta ya ruko yana daga
t'sugunne, "Momy nah... Cikin sanyin murya ya
kirata, bata juyo ba,amma yasan tunda bata
K'wace hannunta ba yau zata saurareshi. Cikin
nut'suwa ya fara lallashinta kan bashi da uwa
sama da ita ta yarda,yasan haifarshi ne kawai
batai ba, ta tausaya ta d'aina fushi dashi koh ya
samu komai ya tafi mishi cikin nasara... Sosai
yau ya k'wada Momy har sai da ya tabbatar ta
gamsu a gunshi baida kamarta ko da kuwa Mama
ce... Kai ya d'aura cinyarta har da hawayenshi,
"Sam bani kaunar ganin ki cikin wannan yanayin
Momy na,nakan shiga wani hali in na ganki ba
k'ya walwala.. Cikin siyasa yai ta nuna mata kan
damuwarta tashi ce har kullum. "Momy ki ce
komai kin isa,amma dan Allah ka'r ki rabani da
yarana da Mamansu, ina neman ki yafe musu in
sun sa6a miki,ki musu afuwa ki ce su
dawo,nasan ke mai son farin ciki na ne a kullum
Momy, amma in kinga basu dace dani ba Momy
zan bi d'uk yadda kika ce,zanyi... Ya karasa yana
saukar mata da hawayenshi bisa kafarta...
Sassanya ne Ahmad, ko a yaranta batajin dan
wanda bai kaunar ganin damuwarta sama da
AAA, tasan ba wanda yake jin maganarta sama
da AAA, sannan bazata ce ga abin da Fure tai
mata ba har ta ji bata kaunarta,gashi tana mata
ladabi iyakar iyawarta, koh dan duba ga yadda
sirikarta kishiyar Rukayya ke yi a gidan, gata d'ai
y'ar masu kud'in ce,kuma jinin sarauta,amma
sam bata ganinsu da daraja bare mutunci,
asalima ba gidan su take zuwa ba ko da abu ne
kuwa ya faru, ga nan mijin Huwaila, arziki kamar
suyi ihu amma ba k'wanciyar hankali, baya
darajasu su iyayen Matarshi. In d'ai haka auren
mai arziki yake toh tabbas tasan g'wara su
Fure,masu karamin k'arfi amma suna k'yautata
musu iyakar iyawarsu, sun san darajarsu, sannan
bassu girman kai.. Sai yanzu ta banbance dabi'ar
talaka da mai kud'i... A dalilin su Fure ta
banbance t'sakanin t'saki da t'sakuwa... Ajiyar
zuciya ta sau, kan ta kai dubanta kan AAA da har
yanzun yake hawaye yana kuma nema musu
gafara shi da Furiin shi, a hannu takai kan sumar
kanshi tana shafawa halamar yai shiru,sai ya
k'allota, murmushi tai mishi tana girgiza mishi kai
tare da goge mishi hawaye.. "Momyn ka na
kaunar ka da iyalanka Ahmad, tabbas nasan kai
D'a ne,har da kari, na gode sosai sannan zaka
sha mamaki. Murmushi yai wanda har
hak'waranshi suka baiyana,sai ya kara k'wantar
da kanshi yana k'wararo mata godiya tana
murmushi. Bai tunanin zai samo Momy da y'ar
guntuwar ban hakurin nan ba... Mama da tazo
ban hakuri itama yau dan ta gaji da wannan
gabar sai ta goge idonta, fatan ta Allah yasa
Momy ta gane kuranta game da Fure. By Feenat
Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com
9/29/16, 3:04 AM - Queen Safiyyert馃憫: [5/17, 10:20 PM] Feenat Ja'afar: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
54_"Ya zanyi Sis Fatee? Abinda hakuri bai baka
ba,nasan rashin shi ma bazai baka shi ba, adu'a
ta a kullum Allah ya shirye su su gane...
Dan t'saki Fateen tai, "Ba komai kake ma hakuri
ba Furii,mutum shi kad'ai ke nemawa kanshi
y'anci, ace yau har sati uku ba ko kayan suna,
toh mey suke nufi? Murmushi Furen tai, dan bata
sa a ka ba,wai an T'sikari ka'rkausa.. Maryam
dake gefe da sai hararar Fure take tace "ki barta
Aunty Fatee,ki ma d'aina bata yawun bak'in ki,
dan ni tun daga yadda ta sau jiki da mijinta
nasan tabbas Ya Fure batta zuciya, tunda nan ya
korota gidansu cikin bainar jama'a.
K'allon Maryam d'in kawai take,yadda take ta
kumfar baki, sai ta k'ada kai, "ba zaku gane inda
na dosa bane Maryam.. Rayuwa y'ar hakuri ce,
AAA na da dalilinshi na yin hakan, believe me...
Har kusan magriba suna zaune tattauna
mat'salar gidan su Momy, kukan su Hasna ne ya
kat'se su suka fara aikin lallashi.
K'allon yaran take,yadda sukai bul bul dasu,barin
acici su Hussein.
"K'allon yaran nan kad'ai ya isa mantarni d'uk
wani bak'in cikin rayuwa Allah... Ku manta da
zancen su Huwaila, kema Maryam ki kula mijinki
fa yaron ki,sosai na kula har yau baki sakar ma
Abulkair, ki sani basu laifi, haka Muh'd bai da
laifi,ki fuskanci zahiri,mijinki na son ki, kar ki fara
huce haushinki kansu..
Karan nan da halamar ta d'au zancen Furen,
suna cikin haka suka ji a chan t'sakar gida
Umma na fad'in Sannun ku da zuwa Hajiya
Maryam... Da sauri Fure ta k'alli Maryam, tabbas
muryar su Momy take ji, da sauri suka tashi
kowa rike da d'aya suka leka waje, su d'in ne
kuwa.
Tuni Maryam ta had'a girar sama da ta kasa ta
kama k'ugu da hannu d'aya tana girgiza ganin irin
k'allon da su Huwaila ke ma gidan tasan ba
zuwan mutunci sukai ba, "mey kuma aka biyo a
ma ya'yan masu t'siya har gida?... Da sauri
Momy da Umma suka k'allo Maryam.
"Umma ki sanarsu su bar mana gida kan muyi
ta'asa dasu wallahi... Da sauri Umma ta kat'seta
"Maryam... Ban son shashancin banza...
T'saki Huwaila tai,kan ta harari gun su Furen, "ba
dan Momy ba wallahi da ba abinda zai kawo ni
gidan nan... Har meye abin tinkaho a wannan
akurkin? Cikin tunzara Maryam zatai kanta Fure
ta rike ta,, Momy kai kasa bata hana ba, Umma
ta sau baki, sam batasan yaran bassu tarbiya ba
sai yau...
Gaban Momy Fure tazo, har kasa ta tsuguna ta
d'aura mata Hussein a cinya, ta juya ta k'ar6o
Hasna da Hassain ta jere su kasan dardumar a
gaban Momyn.
Kowa k'allonta kawai yake, cikin nut'suwa ta
fara fad'in "Momy, dan Allah yau ka'r ki
kat'seni,ki barni at least na fad'i son raina, ki
bari yau d'aya nai magana in yaso in na gama ki
min hukunci koh da na marin ne, wallahi zan
d'auka...
Ta karasa kamar mai shirin kuka.
"Huwaila.. A wulakance ta k'allota tana
y'atsina,kai in ka ganta d'uk ta fita hankalinta ta
fige, d'uk dan tashin hankalin gidanta. Murmushi
Furen tai tare da girgiza kai, "kin san Allah
d'aya? Toh wallahi mun fiki k'wanciyar hankali..
Baki ta Huwailan ta ta6e, "ina wata k'wanciyar
hankali a talauci?..
Murmushi Furen ta sake, "haka ne, amma zai fi
k'yau ki t'saya a talaka a yanzun da wannan halin
da kike ciki.. Zai fi miki k'wanciyar hankali
zaman ki a JUYA,sama da zama mai haihuwa
gun miji... Kowa ya kalle ki yaga marar
k'wanciyar hankali, ga dai daular, amma kin gamu
da gamanki, kin gamu da wani irin Miji, wanda da
ke mai hankali ce da kin gane Ayar da Allah ya
saukar kanki... A tunzure ta k'allota,sannan ta
k'alli Momy, kanta na kan su Hasna.
Sai ta samu kanta da kasa fad'in kalma ko d'aya
ga Furen.. Hakan ya bata damar cigaba da
bayaninta.
"Kasantuwa ta a JUYA a da a gunku,hakan bai
hanani samun soyayyar Miji ba,naci takaicin
ku,d'uk a ban haihu ba,na zata in na haihu gori
zai kare ma d'an kada.. Ban san aibu na gare ku
ba, ban san da mey na rage ku ba?..ban sani ba
Momy.
"Momy in har na ta6a sa6a miki dan

16 / 18