JUYA Lokacin da Kaddara Ta Sauya Komai by Queen Safiyyert

Author :  Queen Safiyyert Category :  Romance

Chapter   17 / 18

48K to 51K   out of 51.2K words

Allah kimin
afuwa... Bazan iya kankare asalina ba, bamu
zama d'aya ba, ba kuma zamu zama ba.. T'sit
kake jin su, tamkar wasu mummunai sun kafeta
da ido,mamaki ne koh meye oho.
By
Feenat Ja'afar.
[5/17, 11:31 PM] Feenat Ja'afar: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
55_Kan Aunty Jidda ta dawo,cikin aminci ta fara
mata magana.
"Aunty Jidda.. A gani na ke ce mutum ta farko
da ya kamata ace kin min uziri yayin da ban
samu haihuwa ba.. A gani na kalmar nan ta
JUYA bai kamaci fita a bak'in ki ba ma.
"Na sani da kila ke baki gano matsayi d'aya Allah
ya bamu ba a da, wallahi sai nake ga kamar abin
kunya ne kai ma mutum gorin abinda kaima baka
samu ba, ko dan ance g'wanau bai jin warin
jikinshi sai na wani... Kiyi hakuri Aunty Jidda, ba
fitsara nai miki ba.. Amma kinfi chanchata a
kiraki da JUYA sama dani, ban fa ja da ikon Allah
ba.. Na fad'i raina ne kawai,kiyi hakuri in na 6ata
ranki.. Ta karasa tana mata murmushi.
Kan su Huwaila ta dawo,
"Bari kuji,ba wai dan ina da lokacin ku bane zan
tanka muku,kai ta girgiza,"nasiha ce,Kila tai
muku amfani,,
D'uk k'yaun ka,d'uk dukiyar ka,da d'uk wata
K'awa ta duniya, mud'in kika rasa halin k'warai,
wallahi, "u r nothing, don babu ma ta fiki mat'sayi
gun Allah,
"Ku kuna kawai hoping 4 dis Duniya, wacce ba
komai acikinta face t'sant'sar nadama,da da na
sani.
Ku sani...
"Wani yana chan a k'wance a asibiti ba lafiya,kila
ma ko kudin sayan magani bai da shi, wani gidan
sa yau ko na safe basu samu abinci sun sa a
bak'in sallati ba,wani ko kud'in gidan haya bai
dashi, amma ku Allah d'uk ya baku wannan.
"Sosai k'yawawa ne Ku,farare" hurul ein" koh? Da
ido ta kafe su, jin basu tanka ba yasa ta k'ada
kai.
Tabbas banni k'yau,
sai d'ai ku sa ni, ban ta6a dana sanin hakan
ba,cos ina duban na kasa dani sannan na gode
Allah,saboda yayi min Ni'imar da bai ma wasu ba,
yai muku k'yaun da bai ba wasu ba,ya baku lafiya
da bai bawa wasu ba,ya baku d'uk wani farin ciki
na duniyar nan, "mind you, ba fa wai dan yafi son
ku bane ya muku hakan? Kai ta girgiza,"no,wal
lahi talaka,daya riki Allah da manzon sa,sai ya
sami mukami babba a gun Allah wanda ku ba
d'ayan ku ba zai samu ba.
"Domin da kanshi yace wanda yafi wani a guna
shine wanda yafi tsoro na,ba wai wanda yafi
dukiya da k'yau ba, amma "instead of you to
thank Him,,umm..um u r ungrateful... Kun gode
mishi ne ta hanyar gorantawa wanda ya tauye.
Ku sani,ak'wai mutuwa,
"and wallahi,you will leave all these behind.
" In kin ta6a jin "k'aruna" wanda a tarihin duniya
ba ai mai kud'in shi ba, ba kuma za ai ba,
amma da ya mutu sile biyar bai tafi da ita
ba,daga shi sai halinshi, yanzu kam arzikin da
komai babu, da an turmusa ki kabarin ki k'yaun
shi zai fara zag'wanye wa,karshe ki zama kasa
abar takawa.
"Kinga ba bu Alfari,babu Dukiya,babu
k'yaun,yanzu kam sun zama kasa.
"Toh ku fad'an, wanda zai zamu haka a
gaba,meye nashi na tunkaho da wannan
duniyar?? Kai ta girgiza..
"Malamai,wallahi you better seek ur "Jannah"
sannan ku gode Allah da baiwar da ya muku, ta
hanyar fad'in Alhamdulillah, ba wai ta gorantawa
wanin shi ba,da nuna isa da fariya..
Shiru tai, jin sallamar Abba cikin gidan, tunda
yaci ka'ro da motar AAA ya sanar shi su Momy
ne jikin shi yai sanyi, sai d'ai daga shi har AAAn
sun sha mamakin jin gidan t'sit sai tashin nasihar
Fure cikin nut'suwa.
A hankali ta tashi tai gun Abban d'uk suka bita
da ido.
Kayan hannunshi ta k'ar6a cikin girmamawa tana
leka wa, sai ta dago da murmushi, "har kullum
ina alfari da kasancewar Abban mu makanike
mey ci da gumin shi, kun ganshi nan, a kullum
cimarmu mai dad'i ce, dan ta Abba ba mai cin
k'wananen abinci, burinshi ya samu ya kashe su
kanmu, dan haka a kullum ya zama abin alfaharin
mu,dan haka ne nake yaki da d'uk mai neman
taka min shi...
Jin kuka zai K'wace mata yasa da sauri ta lafe a
gefen kafad'ar Abban,d'uk sai ya kara kaunar
Furenshi, tabbas sun cika yara na halali,masu
takama dashi a d'uk yadda yake..
Tashi Maryam tai tana goge hawaye tai gun su
Abban,d'uk sai ya hau lallashin su.. Ba zata suka
t'sinkayi muryar Ya Suleiman.
By
Feenat Ja'afar.
[5/18, 12:31 AM] Feenat Ja'afar: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
56_"Yanzu kam komai ya kare ai.. Dan haka ku
tashi tun da guntun mutuncinku Hajiya ku
tafi,d'uk din su ba wacce akai ma auren sadaqa..
Rayuwar y'anci muke yanzun, haka nake bid'ar
ganin k'anne na ciki.. T'sit sukai ba mai mot'si
cikin su, ciki ya karaso cikin bacin rai, da dan
k'arfi yace "ku tashi nace koh?.. T'saki Rukayya
tai, kan ta hau neman tashi, "Ga'iyar... Saukar
mari taji yasa da sauri tai shiru ta zauna d'ai d'ai
rike da gun,Momy ce.
Hannu ta nuna ta dashi, "ka'r na kara jin bak'in
cikin zancen wani anan... D'uk k'allonta suke
cikin mamaki musamman Huwaila da Rukayya da
Fure.
"yanzu Momy akan wa'enan Mat's... Wani marin
ta kara sakar mata,wanda ba shiri ta g'imtse baki
tana shafa gun.. "Ki kiyaye ni,in ba zaku iya shiru
ba ku tashi ku ban gu.
Kamar masu jira da suka d'au jakukkuna sukai
waje suna kunkuni. Ita d'ai Aunty Maryam ido ne
nata, yayinda Aunty Jidda takaicin duniya ya
isheta ganin abinda Momy tai,gashi tace bata
yafe ba in ta tofa tun suna gida.
Hawaye Abban ya goge ma su Fure kan ya juya
ya koma yana mai kiran Ya Suleiman, fatan shi a
wanye lafiya.
Tashi Momyn tai tazo inda su Fure suke, ido
kawai Fure ta zuba mata, Maryam kam kai ta
k'auda, dan Allah yaga taki jinin Momy.
Hannu ta daga zuwa fuskar Fure dake hawaye,
da sauri ta rint'se ido tana mai jiran saukar mari
a kuncinta,yayinda da sauri AAA ya ju ya baya
shima ya rufe ido.. Sai d'ai har wani lokaci bai ji
saukar mari ba,hakan yasa ya d'an ju ya.
Abinda ya gani ne ya sashi juyowa gaba d'aya,
Momy ke sa hannu tana goge ma Fure hawayen
fuskarta tare da girgiza mata kai halamar ta
d'aina kuka, da sauri ya sau ajiyar zuciya tare da
washe baki yana murmushi.
Kan Maryam ta koma wacce ta zumburo baki tai
gefe da kai...
"Kuyi hakuri kunji ya'yan nan.. Takanas nazo
bikonku ku koma... Nasan ba ku samu yadda ya
dace ba a zamanku na baya ba gun mu.. Ban rike
ku sirikai ba sam, amma ku kun rike ni uwa...
Shiru tai tana k'allon su,wanda su ma k'allonta
suke baki sake, wai Momy ke basu hakuri? Kuma
cikin sanyin murya? Ido Fure ta ka'rkad'a, tana
fatan in mafarki ne ma lalle ta wat'sake...
Tamkar Momy tasan tunaninta ta ruko hannunsu
tana murmushi suka zauna.
Chan ta nisa ta fara magana,"Furera... Ido Fure
ta rint'se, a ka'ron farko da Momy ta ta6a kiran
sunanta.. Hakuri ta fara basu dasu Umma cikin
nuna nadamar abinda tai musu,da alkawarin ba
maimaici InshaAllah.
Tun suna ganin abin kamar da wasa har suka
ware da yardar lalle Momy tai nadama,sai
rarrashin Hussein take dake kuka tana fad'in
"wannan na Umman ku ne, nawa mai gidan gashi
nan.. Tana nuna Hassain, kamar mai jira shima
ya kama kuka,baki sake tace "au,au,kaima hakan
take?
Banda murmushin jin dad'i ba abinda Fure ke yi,
a hankali ta daga kai ta k'alli gun da AAA
yake,shima idonshi akanta yake,tuni ta hau mishi
godiya cikin yaran su nasu kadai da kurmanci, ido
ya lumshe mata halamun ya ji dad'i.. Sai ta
kawar da fuska tana murmushi. Tasan wannan
aikin na AAAn tane, a karshe yai nasarar gashi
har gidan Momy tazo wai bikon sun a zahiri ba
mafarki ba,tuni ta kara jinjina wa hakuri.
Ai Aunty Jidda tuni ta bi bayan su Huwaila, dan a
ganinta Momy ta ma gama badasu gun su Fure,
gashi Fure ta sha da ita ba damar magana,sai
Taxi suka hau dan da motar AAA kad'ai da Aunty
Maryam suka zo, ita kam Rukayya gida ta wuce
tana tunanin yadda yau Momy ta mata,kai ta
girgiza.. Su zuba toh.
Har dare Momy tana gidan ita da AAA, Aunty
Maryam ta tafi, sai ga nan Momy tana zukulkular
tuwan hatsi miyar d'any'ar ku6ewa tana santi..
Har ta kasa shiru sai da ta tofa. Shi dai AAA
bak'in nan kamar gonar audiga dan murna, yasha
mafarkin ranar nan sai yau tazo da ikon Allah,
fatan shi Allah sa su Aunty Jidda ma su gane.
Ba karamin farin ciki Abba yai ba da jin zuwan
Momyn,ganin yadda AAAn shi ke farin ciki yasan
yau Maryam ta wanke laifinta, hakan yasa
Washegari da kanshi ya shirya dan zuwa har gida
kara bada hakuri, abinda bai ta6a ba sai kansu
Fure.
Lokacin Abba ya dawo suna a t'sakar gida kamar
kullum Familyn g'wanin ban sha'awa AAA yai
sallama.
Jin da wa yake tafe yasa su tashi zuwa neman
mayafi, da t'sabar kunya shima Abba suka
gaisa,dan bai ta6a tunanin zuwa domin gaisuwa
ma sirikin nashi ba koh a hanya, asalima shi bai
san waye Abban su Fure ba koh a hanya, sai d'ai
da mamakin shi yaga Muhammad ne ma, cikin
mamaki yake k'allon Abban,shikam murmushi
kawai yake.
"Wai da gaske ne koh ido na ne Muhammad?
Murmushi Abban yai mishi, sai Abban su AAA
yace ma Ahmad d'in "lalle ka lalubo zumuncin da
Baba na, dama su Furera yaran ka ne? Ikon
Allah, gaskiya har naji kunya, nasan da Nasir na
raye da yau zan d'au query, shi d'ai Abba
murmushi kawai yake.
"Ke nan kai ka gane ni Muhammad, kai ya k'ada
yace "sosai ma Yaya,tun a auran Furera na gano
dangin Nasir ne ke nema, toh a gun d'aurin aure
na gano ashe ma kaine Abban Ahmad.
Abba yace "ikon Allah, amma baka k'yauta ba
Muhammad, sosai Hajiya tai k'ewar ka har ta bar
duniya....
Shi d'ai AAA an sashi t'sakiya, ya k'alli Abban su
ya k'alli Abban su Fure, da halama yana neman
karin bayanin a fiddashi duhu.
By
Feenat Ja'afar.
庐NWA.
9/29/16, 3:05 AM - Queen Safiyyert馃憫: [5/18, 11:45 PM] Feenat Ja'afar: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
57_Irin firar da sukai ne ya gane sun jima da
sanin juna,koh dan yanayin yadda kowa ke
tambayar bayan rabuwa.
A mota d'ai AAA ya kasa hakuru yai tambaya,
cikin murmushi Abba ya sanarshi ai sun san juna
da Abban su Fure da jumawa tun zamanin jami'a,
a dalilin k'aninshi Nasir sukai sabo sosai,d'uk da
ba t'saran shi bane.
"Sosai sunyi abota da kawunka,wanda har ya
zamana Hajiya ta d'aukaki Muh'd d'in, dake shi
Nasir ba mai nisan k'wana bane tun bayanan ban
kara ganinshi ba...
Kai ya jinjina, yana mai farin cikin wannan rana
da jiya,burinshi Furii ta dawo mishi dan zaryar
nan d'aurewa kawai yake, amma da kunya.
Tuni Abba ya dawo ma su Momy komansu harda
karin kud'i a (account), har sashen Mama Momy
taje dan jin shawarar irin kayan da za ai ma Fure
na suna, dan fa fur tace sai ansha shagali kamar
na kowa, sosai Maman tai murna,har ta kasa
6oye wa.
Aunty A'i Momy ta bama k'wanigilar had'a kayan
goyon Furen, tuni kuwa ta hau 6adda kud'i tana
narko ma (Babies) da Furen kaya na azo a ga.
Sosai sunyi rawar gani,dan naira ta ci kasa.
Baki kawai su Umma suka zira lokacin da kaya
ya iso musu, tabbas gidan su AAA sunyi wuta.
Haddadiyar walima suka had'a a harabar gidan
su AAA, su Fatee kan gaba Wai dan ma ciki yai
yawa.
Lalle ne bayan wuya sai dad'i, ga nan Fure sai ji
da ita da yaranta suke,ita kam bata cewa komai
sai godiya ga Allah.
D'uk da su Aunty Jidda su basu yadda makaman
yakin nasu ba a kanta,amma sosai ta sarara,dan
fur Momy ta toshe d'uk wata kofar da zasu
muzgunawa Fure, ga kuma tsoron ka'r Abba ya
kara k'wata musu ta da.
Tuni Maryam ta koma, amma gida daban Muh'd
ya sa ta,yanzu kan ita da Hassana sai gani daga
nesa.
Lokacin arba'in d'in su Fatee ta juye nata, sai
abin ya zama biyu,ga shirin komawa gidan
AAA,ga jelar gidan Fatee.
Tuni likafa ta hau,yanzun kam kowa a dangin
Salman nanike mata yake son yi, sai d'ai ita tace
ina, wai takai-takai.
Huwaila d'ai aure yaki dad'i, dan fur Miji ya juya
baya shi sai amarya, wai ta zama chus,ga gida
d'aya ya gamasu da kishiyar, da ta hau mata
fallin amarci take tada hauka, a haka har ta
k'wata ya jibgeta had'i da saki ya kuma bar
kasar.
Da wannan Momy ta kara tir da wani auren mai
kud'in.
Yanzu kam Rukayya ita aka sa gaba, dan tuni
lakabinta gun su Aunty Jidda ta fara amsa sunan
JUYA... Ga kishiya mai dan uban isa da gadara,
ita a dole jinin sarauta, ita ke da (remote) a
hannu sai yadda tace ai ake yi, da ta nemi yi
mata rashin kunya zai taka mata burki,dan fa wai
yana ji da Matarshi tamkar t'soka d'aya cikin
miya...
Ga sharadin Babanta na in ta kaso aurenta toh
kar ta tunkari gidanshi, ga Momy tun daga abin
Fure da tai mata zuciya itama Momy ta nuna
kamar ba ai ruwanta ba.. Tun Rukayya ta shiga
t'saka mai wuya, ko ina ba dad'i, ga yaran gidan
kadai sun isheta hawan jini, rayuwar dai sai a
slow gun Rukayya.
Ita kam Aunty Jidda tuni karan nan Abba ya
bud'e mata wuta kan sai ta koma gidan
mijinta,tunda yace shi bai Saki ba.
Karshe tana ji tana gani ta koma gidan da tai
rantsuwar ba komai cikin shi.. Wanda a zahiri
jarabar uwar mijin su yasa taki auren fur,dan
sosai take wanke ta ciki da bai d'uk wai ta cika
musu gida ga ba wani fus,.. Amma dake Dan
Adam ce ita wai har take huce takaicinta kan
wata.
**********************
K'wance take cikin d'aki gaba d'aya yau jinta
take wani iri, dak'yar ta samu ta lalla6a su
Hussein ta basu ball kan su fita sui wasa zata
huta.
Tana t'saka da bacci ta zabura har tana shirin
fad'o wa a gadon, jiri take ji,ganan kuma karar
zubar abu,wanda tasan babu tantama daga
kitchen ne aka zubo mata (plates) suka fashe.
Kawai sai tasa kuka tana mai dan buga gado ba
koh hawaye, kai da gani kasan kukan 6aci ne,
yara tamkar beraye kullum cikin 6arna suke
mata...
By
Feenat Ja'afar.
[5/19, 12:50 AM] Feenat Ja'afar: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
58_Parlourn tai dank'wali a hannu tana sakar ma
su Hassain harara,tuni suka fara raba ido ya 6era
a buta..
Hussein da ke a bak'in kitchen rike da ball yace
"momma hakuli...
Harara ta kara mishi rike da k'ugu, kan tace "mey
ya kai ku kitchen? K'allo Hassan yai sai ya k'allo
Furen..
Cikin maganar yara suka ce ai ita tace su je sui
ball,shine suna ball ta fad'a kitchen ta bigi
farantin kofuna..
Kai ta dafe tare da fad'in "oh Allah,, wato g'wari-
g'wari kullum zan ta muku kan ku gane ummm?
Parlour ne waje? Kai suka k'ada mata.
Sai ta fara dube tana "yau zan zane ku son rai ba
mai k'watar ku... tuni suka fara t'sula mata ihu
ganin ta zari tsinken k'wak'wa suna kiran
Daddy...
Zagaye suka fara ta ma kasa kama su, bak'in
nan kuwa yaki mutuwa da ihu tamkar ma d'ukan
nasu take.
Shigowarshi kenan ya fara jiyo ihun yaran, ko
karasa cire mukullin mota bai ba yai cikin
gidan... Ina,ai tuni sun galabaitar da ita dan
shegen ziliyarsu, kasa tai tana haki tana nuna su
bulalar hannunta..
Da d'an gudugudun shi ya shigo, ai suna ganinshi
suka runtuma gunshi suna nuna mishi Furen,
ganin bulalar hannunta yasa ya fara daga
rigunansu ya ga koh ta dake sun.
Shiru kakeji sun bar ihun,tuni ya hau fad'a yana
ta kiyaye shi kan dukan yaranshi, dan takaici
kawai sai ta sa mishi kukan shag'wa6a, harda
buga hannu kan (carpet), tamkar yarinya ta koma
mishi, sai ya sau baki yana k'allon borin
nata,suma su Hussein k'allonta suke d'uk sunyi
narai narai da ido.
Bai nufa ba ya ji sun sa mishi suma kukan, sai
sukai gun Momman d'aya na girgiza mata kai
halamar tai shiru sun d'aina, d'aya na goge mata
idon da ba koh hawaye.
Kawai sai ya harde hannu yana k'allon su.
Shiru tai tai tana k'allon su,jin yadda suke ta
fadin sun d'aina, cikin shag'wa6a tace "promise?
Da sauri suka k'ada kai, sai tai murmushi tare da
janyo su.. Tuni kuma aka hau dariya jin
chakulkulin da take musu.
Kai AAAn ya k'ada yana musu murmushi ya juya
kashe mota.
Yasan 6arna kenan sukai mata.
A kitchen ya t'saya jin hayaniyar su,k'washe
fasassun kufunan take tana su mat'sa kar su
taka. Kiran su yai suka fita,tuni ya had'a kowa
da t'sarabar shi suna t'sallen murna yace su je
gun Baba mai gadi kan ya fito suje gun Hasna,da
murna suka fita shi kuma yai d'aki.
Jin an bud'e d'akin yasa ya k'alli kofar,rufe wa
tai kan ta jingina kanta a jiki tana K'allonshi, d'uk
ta marairaice mishi fuska halamar ya agaza
mata.
Rigar da ya cire ya ajiye kan ya tako gunta cikin
lallashi, a gefen gado ya zaunar su tai lamo
jikinshi.
("My Furii what's wrong?) Uhnmm?.. Cikin
marairaita ta hau ta6e baki kamar zatai kuka,tuni
ya hau lallashi tamkar Hasna ke gabanshi, rad'a
ya fara mata yana ka'r ta sare man tun a su
Hussein... Kai ta k'ada, tasan bazai gane ba ne,
amma tun yanzun har ta fara galabaita da cikin
tun kan yai k'wari.
Lallashi yai ta yi kan ta gode Allah da k'yautar
da ya kara mata, ka'r ta sare tun yanzun..
Kai ta k'ada, "hutu nake so fa Daddyn su, yaran
nan sunki su barni, ni kam a kaisu Allo private ta
tun safe sai yamma koh na huta da kiriniyar su
Hussein... Dariya yai, kan a hankali ya k'wantarta
ya g'yara mata pillow, har da ja mata bargo.
Kanta ya shafo yana mai bata (favorite)nata
cikin nut'suwa.. Tuni har ta fara lumshe ido da
jin dad'in sautin abin.
Jin tai shiru yasa yai tunanin tai bacci ne, cikin
nut'suwa ya duk'o ya dan bata (peck) tare da
g'yara mata bargo.
Kayanshi ya d'auka cikin sanda ya bud'e kofar
dan gudun kar ya tada ta yai dakinta dan wanka.
Da k'allo ta bi bayanshi ganin yadda yake jan
kofar a hankali, sai tai murmushi.
By
Feenat Ja'afar.
[5/19, 7:09 AM] Feenat Ja'afar: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
59_Hannu takai kan cikinta tana mai shafawa,
tabbas bazatai butulci da Allah ba dan ya bata
ciki a kusa,ai ma ta raka, tunda su Hasna sun
kusa shekara uku,tasan yasan zata iya ne ya
bata, fatan ta su rabu lafiya.. A hankali tai bacci
cike da kaunar gidan ta da mai gidan.
Basu suka dawo ba sai kusan taran dare,da kaya
niki-niki.
Tana zaune kuma d'uk sai kewarsu ta dameta,
sai maka mishi kira take kan su dawo ta
huta,murmushi yai,dan suma Hasna ta mat'sa
mishi da fad'in Momman ta.
Da sauri ta tafi gunta kuwa tana mata oyoyo,
kanta ta shafa da yasha (twists-stick) tana mata
sannu da zuwa.. Ita kam batta da k'warafniyar su
Hussein.
***********************
Rayuwar na ta kaima Fure,ta haihu lafiya su
Hussein sunyi k'ani, zo kaga k'walo kusa da
baby,wai nan d'uk murna suke.. Kawai sai ta
tasasu gaba tana k'allo cikin murmushi, AAA na
d'aura ma Hasna babyn suna dariya.. Wai yau ita
ke da yara hudu a rayuwa??.. Tuni ta fad'a
duniyar tunanin da,har AAAn ya kula da ita.
K'allonta shima ya hau yi,bai san karan nan da
mey zai sakama Furiin shi ba? Ya d'ai san a chan
kasan ranshi kaunarta kad'ai ke kara nunkuwa da
k'yawawan yaranshi da take sum6ulo mishi, abin
sai d'ai godiya ga Allah kawai.
K'wanan su d'aya aka sallame su,tuni gida ya
debi su Fatee da nata bataliyar uku,yanzu kam
zumunci ya kara yawa har sun zama y'an uwan
juna.
Ita kam Fure bata cewa komai ga Allanta sai
godiya a kullum, ga bud'I da take samu gun
abincinta, har yau tana nan da bama su (special
dishes) d'inta.
Yanzu kowa mutuntata koh dan tsoron Momy da
Abba dake bala'in ji da ita da iyalanta, ga kuma
yadda ita kanta ta bunkasa ta zama hajiyar
kanta.
Sai gani sai kuma harara daga nesa, dan yanzu
bata ragarma uban kowa t'sakanin su Huwaila,
take suna fad'a mata d'aci zata basu mad'aci.
Sai ya zamo suna shakkar fad'a a gabanta.
Sunzo barka har gida suna d'an y'atsinar nan da
ta zame musu tamkar dole, aciki suke mata
barkar, ita kam Rukayya ji take kamar ta d'auke
babyn, d'uk tai laushi.
Tashi tai tana sanarsu

17 / 18