JUYA Lokacin da Kaddara Ta Sauya Komai by Queen Safiyyert

Author :  Queen Safiyyert Category :  Romance

Chapter   12 / 18

33K to 36K   out of 51.2K words

Aisha da Adama taki
d'auka, gani take yau kowa ya t'saneta, sai d'ai
kana k'allonta kasan tai kuka. Jingina tai a jikin
kofar tana k'allon yadda ya t'saya a gaban
madubi yana kunce "link" d'in hannunshi. K'allo
d'aya ya mata ya d'auke kai zuwa ga abinda ya
ke, d'uk sai ta kara jin ta samu karaya. D'uk ta
marairaice fuska. Karasa wa tai gun da yake kai
a kasa taki duban shi, d'ayan hannun ta ruko
tana tayashi cire wa,ido ya zuba ma fuskarta
yana dan kunshe dariya ganin yadda ta
marairaice. Jin burbushin kunshe dariya yasa ta
d'an dago tana k'allon shi, suna had'a ido ya
kasa jurewa,dariya yake irin ta ketar nan, kawai
sai taga an ma mayarta mahaukaciya, cikin fushi
ta y'ar6ar da hannun da ta rike ta ta turo baki
tana shirin sakar kuka. Maimakon ya t'sagaita
dariyar tashi kawai sai nunata da hannu harda
rike ciki, tuni k'wa sai kuka ya k'wace mata, bai
nufa ba kawai ya ji tana k'wada mishi pillow ta
ko'ina ko zata huce takaicinta. By Feenat
Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.co
9/29/16, 2:48 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 38_Karewa yake,yana
mai cigaba da dariyar, ganin ba gajiya zatai ba
yasa ya fara ko'k'arin kar6ewa ya rukota, tun
tana tirjewa har tai lumm yana jijjiga ta tare
fad'in sorry,sorry. Dak'yar ya samu tai shiru sai
ajiyar zuciya take. Kanta ya dago, sai ta rint'se
ido d'uk k'walliya ta baci, sai ya sa hannu yana
goge mata hawayen sannan ya cigaba da jijjigata
da mata kirarin da ke sa ta nutsuwa. Luff,kake
ji,ba ko shesshekar, sai yai murmushi, shi kad'ai
yasan lagon Prettyn shi. "Pretty"... Ido rufe ta
dan mot'sa, sai yai murmushi, "you know.. "My
destiny is taking me where my love is. "Kin riga
da kin tare ko'ina nawa Furii..har ma ban iya
k'allon wasu mata a mat'sayin sun isa balle su
kamoki,cos I can see only one thing..hear one
thing..and think about one thing... That you
pretty.. Ido ta bud'e, sai ga nan hawaye ya
zubo,k'allon cikin idon shin take,so take ta gano
akasin zancen shin,amma ta kasa.. Ko haka ya
barta tasan yai mata lallashi da son shi, sai d'ai
kan ta farga taji dan hayaniya a kusan k'unnenta,
kamar kuma na d'aurin aure a waya yai
"recording". Sai ta mat'se ido,dan jin maroki na
fad'in sadaki kamin yace "na auren Rukayya da
Nasir.... Da azama ta bud'e ido tana k'allon shi,
gira ya daga mata yana murmushi.. Da sauri ta
karbi wayan ta kara taro wa, abu d'aya ta kara ji,
sai ta k'alloshi wai kuma ta hau kukan dad'i.
******"""" MU D'ANNA BAYa.. Tun bayan fitar
AAA da ang'waye dan halartar d'aurin aure suka
sauka gida inda za'a taru a tafi nasu Muh'd. Gida
ya shiga,"direct" yai d'akin Mama, ganan y'an
biki wasu a "parlour", su Ummi yaga,ya tambaye
ta Mama, sai tace tana bangaren Abba, sam
itama haushin za ai ma y'ar d'akinta kishiya take.
Da sallama ya t'saya bak'in kofa, daga ciki Abba
ya bashi izinin shiga, suna a parlour Mama na
had'a mishi "tea" d'uk yai wani iri, ji yake sam
bai zatan samu nasara ba. Bayan ya gaida su yai
shiru, Abba ya K'allonshi, "Har kun iso? Kai ya
k'ada, kan ya dago kai, da sauri Abba ya ajiye
kofin shayin, "Subhanallah, Abba na, kuka fa? Ido
Mama ta zuba mishi, kawai sai ya goge yana
kara zubo da wasu, tashi Abban yai, dan a duniya
ya t'sani ganin ran kowa ya baci a yaran shi bare
Ahmad t'dokarshi. "Haba Baba na.. Maza da
kuka? Fad'an wa ya ta6a min kai? Mama ya
k'alla, da mamaki itama take K'allonshi, kawai
sai yace shi baison auren nan, sam baison
Rukayya... "Abba yaushe akai auren namu da har
za'a kosa na kara aure dan bata haihu ba, nan
yai ta mishi, kan tana chan wai ya barta sai bori
take ta rufe kanta a d'aki tana kuka. T'sam
Abban yayi, sai yace Mama ta miko mishi
wayarshi. Momy ya kira, cikin k'ank'anin lokaci
tazo. Ganin Ahmad durkushe yasa tasan da wata
a kasa. Waje ta samu ta zauna, sai Abba ya
sanarta abinda Ahmad yace, tuni ta hau 90, kan
aure ba fashi, wallahi tunda har yau d'aurin aure,
yau ya nuna mata bata isa ba, yau harda Mama
ta balbale, tuni ta bawa Abban haushi, "t'saya kiji
Maryam, ki cire son rai, yaron nan kar mui mishi
dole, in aure yake bida zai ne in lokaci yayi, sam
ban zata ba had'in zumunci kike son kulawa ba,
kiyi hakuri, suma zasu haihu ne, amma a bar
auren nan... Kuka Momy ta sau, yau wai an nuna
mata karshenta, sannan an nuna mata ba ita ta
haifi Ahmad ba.. Shidai gogan yai kasa da kai,
fatan shi komai ta fanjama fanjam, yai lallashi
daga baya. "Momyn su kiyi hakuri, sam abin bai
ba, ranar aure kace ka fasa... ''Rufan baki, ai da
saninki a haka, kuma dad'inta na haifa, aure yau
za'a d'aura da d'aya a wanda na isa... Sallamar
Alhaji Nasir ce ta kat'se ta, "lafiya kuwa Abba?
Hayaniya har t'sakar gida fa... "Yauwa Nasir,
shigo, cewar Momy,shi d'ai Abba da ido kawai
yake binta, "Momy kuka? Mey toh yai zafi haka?
"Komai nace kawai kace toh Nasir,, hawaye ta
goge, "ina son ka auri Rukayya, ka fanshen bak'in
cikin da ake son dasa min akan Ahmad.. Da
mamaki ya k'allo su Abba, suma shi suke k'allo,
"haba Momy, aure fa? Ni? Kai za... "Ban san
musu Nasir,in dai ba kana son ku hallakani bane..
Kawai sai Momy ta hau haki.. Asma ta mot'sa,
da sauri suka rukota, Nasir dama ya sani yake
bai shigo ba t'saut'sayi ya fad'a masa.. Haka
yanaji yana gani ya yarda dan Momy na fad'in in
wai bai yarda ba wallahi zata mutu...Lol Ko su
Rukayya basu san zance ba sai da aka d'auro
suka ji, dan chan gidan su akaje. Bori ta hau
yiwa Momy kan ya za'a ta mata haka? Tana
k'wance asmar ta d'an saketa take bata hakuri.
Fur Rukayya tace batasan wannan ba, mey zatai
da tsoho, dan farin gidan, tuni ta tattare tai gidan
su tana kuka. ********************** Da sauri
Fure ta ruk'unk'umo abinta tana kukan murna, sai
kara kakank'ameshi take har tana shirin fad'arsu
kasa sai sukai kan mai laushi. Karan nan bai
hanata ba, dan yasan na murna ne, sai ma yahau
tsokanarta da fad'in, "haba uwar gida, yau fa ba
ranar kuka bace... Dariya ta hau yi kuma kuka
kuka. Sai ya zame dank'walin tare da mirgina ta
kasa suka zuba ma juna ido, mey zata ce da
abun nan? Lalle Allah bai had'a maka zafi biyu,
gashi an so a muzguna mata Allah bai yarda ba,
sai ta hau matso hawaye. Kanshi ya d'aura a
kafad'arta yana goge hawayen, sai ta hau kuma
sunne kai cikin kunya. "Sosai bayan na fita zuwa
kawai zanyi na auri Rukayya tunda naga ni kad'ai
nake k'ida na, sai d'ai ina fita na t'saya a bak'in
kofa, ina ji kika sa key kika zube, wai kuma harda
kuka, kinyi dauriya fa, ko irin y'ar haukar k'aryar
nan da mata suke ke baki ba.. Hakan ya nunan
ta ciki yana cinki, kawai sai nai jahadi na tunkari
yakin dake a gaba na... Kat'se shi tai ta hanyar
d'aura "lips" nata cikin magand'ar sa tana jin
kamar da haka zata biya shi. By Feenat Ja'afar.
Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 30
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 39_Lokaci sosai suka
d'auka, kan a hankali ta fara ko'k'arin zame
kanta ido rufe,shima nashi haka, "thanks" shine
abinda ta furta, sai ya ware ido cikin nata, lalle
yau ya biya ta ba kad'an ba. Tuni kuma ya hau
tsukanarta tana dariya.. A mota suke,yau shi ma
zai kaita gidan bikin, hannunshi d'aya na nata
kawai ta juyo tana ta aika mishi murmushi yana
k'ada kai. Lalle kishi masifa ce, sannan batasan
haka son AAA ya kai ba cikin ranta sai yau da
ake neman a k'ak'aba mishi auren dole. Hannu
yasa yai tagumi yana k'allonta da murmushin
yadda ta zuba mishi na mujiya. Kawai sai taje ta
lafe tana d'an mishi dariyar kauna,t'sam ya
rukota yana sauke ajiyar zuciya. Yau d'aya ya
kara tabbatar da son da Pretty ke mishi. Dak'yar
ta dago tare da d'aukar wayanta, hannu ta daga
mishi, tare da fad'in ''Bye... Sai taji yai shiru yana
k'allonta kawai. Ta kara fad'in "hello", a hankali
yace "I love you.. Kai ta k'ada tana murmushi,
sai ta k'arkata kai da fad'in "I know... Cikin
shag'waba, bak'inshi ya nuno mata, ba gardama
ma ta nashi mai zafin, tare da fad'in "bye" ta suri
jakarta zuwa waje, dan tasan in ta biye mishi a
motar nan zasui ta zama. Zagawa tai ta
bangaren da yake, ta daga mishi hannu, kai ya
leko, "Remember that...Nothing gonna change
my love 4 you... Sai ta k'ada mishi ido tare da
d'aura jaka a kafad'arta.. Tace "really? Kai ya
k'ada, tare da jero Nothing..Nothing... Hannu
tasa a bak'inta tare da d'an wata munafukar
dariya, sai ta manna wa hannunta "long kiss''
Muahhh... ta nuno shi da hannun "love you... Da
farin ciki suka rabe, har sai da ya kule kan ta
k'ada kai ta shiga gidan su Umma. Da gudunta ta
karasa tana kiran su Adda da Aisha. Tuni suka
fara mata barka,reshe ya juye wai da mujiya.
Fatee ce ta kira ta, kan itama gata a hanya
bayan azahar, tana ta mata dariyar keta kan wai
d ansha da ita, ai ta fad'a mata taji a jikinta
auren nan babu shi, itade murmushi take kawai,
amma tasan da k'yar ta t'sallaka rijiya da baya.
Sai dai kuma ta tushe k'unnenta a gun su Momy.
Lafiya aka gama biki, sosai sun ma Maryam
bajinta har ta ninka Fure, kayan kitchen guda
Fure ta d'au nauyi, Ga nan AAA ya ma su Umma
gudunmawar kayan abinci da drinks, dan fur suka
ki k'ar6ar kud'inshi, Abba d'ai ya zama d'an k'allo
da Umma. Aisha Bedsheets, Ya Suleiman kam an
kafu sosai, d'uk kayan parlour shi yai,sosai ya
ka'r mata nera, kamar kullum yau ma kawu ya
d'au nauyin gado, ganin haka yasa ya sai mata
babba mai t'sada da k'yau. Koh y'ar gidan wani
mai kud'in karshenta kenan. Amarci sukaci ba
k'arya a gidan Hassana, yanzun ne Muh'd yasan
yai auren so da tararaya, sai yanzu yasan sirrin
dake cikin auren y'ar masu karamin k'arfi da
suka rena. A gun Momy kuwa, kowa ta d'aina
kula shi dan a ganinta an mata babban
wulakanci. Kullum sai Ahmad yazo gabanta
neman gafara, yau d'ai har da d'an guntun
hawayenshi dak'yar ya shawo kan Momyn. Ta
bangaren Rukky kuwa tuni babanta yace bazata
zauna mishi gida da aure kanta ba, su Momy su
ne iyayen ta,dole haka tanaji aka yayimeta aka
kaita gidan Nasir. Hassana na gida, fur Muh'd
yaki zuwa biko, yace ai ba shi yace ta fita
ba,zata iya dawo a d'uk lokacin da taso, ganin ba
sarki sai Allah yasa ana wata da bikinsu ta
tattaro ta dawo,sai d'ai ganin Maryam a gidan ba
karamin bala'i ta tayar ba, a fafur sai d'ai ya
sauya mata gida. Shikam yace amarya tace had'i
take bida. Komai yi suke a gaban Hassana,haka
zai ta biye wa Maryam suna guje guje a parlour
akan abu kad'an. Hassana sai a ta6e
baki,"mahaukata kawai.. Sam Maryam bata bin ta
kanta, sai d'ai da taga zata shiga gonarta zata
taka mata birki. Sunan Huwaila ake yau, wannan
ce rana tafarko tun bayan auren su Maryam da
Fure suka had'u da Familyn gu d'aya. Murmushi
kawai take, jin ana chakarta kamar kullum,ga
rashin auren Rukayya ya dad'u,tasan batta bak'in
komai. Muryar Hassana tafi ta kowa tashi a
d'akin maijegon. D'ai-d'ai su Maryam da Ummi na
shigowa suka t'sinkayi Hassana na fad'in "bar
mat'siyaci, nima ana chan anga guri ana ta
6arkan hauka, cewar Hassana. Da sauri Maryam
d'in ta karasa d'akin, sai da taje d'ai-d'ai kan
Hassana tukun ta k'alli Fure,"sha kurumin ki
sister, sai tai gefen Hassana da hannunta tukun
tace "dan tuni t'siya ta kare kan t'sohon nan na
gida mai kud'in LUKUD'I ... Wanda da iyalanshi
su ci k'wada K'adangarun BARIKI suci... "Sannan
t'siya ta kare ga uban yana da kud'in, amma in
ya dire buhu masara, daga ranar ba sauyin abinci
har sai ta kare. Sai ta k'allo Hassana, "toh indai
kikazo nan, toh k'wa t'siya ta kare a gun ubale...
A tunzure Hassana ta mike, zatai kanta, da sauri
Maryam d'in taja baya tana k'allon Hassanan
kamar taga kashi, ilahirin d'akin sun zubawa
Maryam ido suna k'allo baki sake, ''ni fa t'siya ta
da y'ar gidana akuyanci, yanzu sai fa kice zakiyi
dambe dani? A kuma cikin taron jama'a.. "Toh
wallahi ki iya bak'inki... Chan ta mat'sa kusa da
Ummi ta zauna, tai banza da Hassana wacce ke
nad'e tabarmar kunya cikin jama'a. Har dariya
Aunty A'i yau tayi, lalle wai "GABA DA GANTA...
Tun zuwanta gidan Maryam d'in ta tarar da
fad'an su da Hassana tasan za'a buga da
Maryam. Yayinda maijego ta ta6e baki, badan ta
kanta take ba yau da ta takawa Maryam burki.
D'uk da tabbas batai ma Hassana sharri ba, dan
fa sai da ta ciwo maganin zama da ita ka'f kan
ta yarda a had'a su zama tare, tai alkawarin d'uk
d'an uban da baiji kunyar taka mata y'ar uwa ba,
toh itama bazata ji kunyar take shi ba. Ita kam
Fure kasa tai da kai tana murmushi, tabbas
tasan wataran KARE na yawo, KURA na yawo
tasan dole za'a a had'u. Batajin da wanda
Maryam zata dagawa K'afa a ka'f Familyn su
Huwaila. Lalle kam,dole ta zama y'ar k'allo, dan
k'wa badai ita ta takawa Maryam burki ba sam.
Fatee ta haihu babyn ta mace, da zumudi ta
gama abinda zata kai mata tai gidan, dan ta ce
an sallame su. "Drama" taje ta tarar, wanda
sosai taci dariya. Fatee na band'aki taji sallamar
y'an gidan su Salman, da sauri ta wat'sa jin sun
shigo d'akin da ake shirya baby. Cike da murna
suka zauna a gama su k'ar6i baby. Da d'aurin
kirji ta fito, nad'e da towel a kanta, d'ai-d'ai za'a
basu Baby da sauri ta karaso ta shiga t'sakani,
"Wa? Ai wallahi na rant'se ba shegen da acikin
ku zai d'au y'ar JUYA.. "Dallah mat'sa min daga
nan, ta warce y'arta ta d'ane gado tana bala'i.
Gaba d'aya sun kasa cewa uffan, Fure da tazo
ganin ikon Allah yasa ta ma kasa sallama, Ashe
da gaske FATEE take da tace ba mai d'aukar
y'arta acikin k'annen Salman sai d'aya? "Ido ko
kunya babu wai kunzo ganin Y'a? Toh g'wara ku
d'au fagon wani gu ku barmin gida, tuni wasu
suka fusata, har sun manta, ana haka y'ar k'anin
Baban su tazo da y'an gidan, jin yadda Fatee ke
ma dangin mijin wankin babban bargo yasa taja
tai shiru, aikwa sai da ta wanke ta tas! Kan d'uk
taji sanyi. Zuciya sukai suka fita suna ta jika y'ar
tasha.. "Eh zan jika...aje d'ai, gaiyar na aiya.
Salman sai da yazo bada hakuri,yana dari dari,
ganin yadda take cika, ba shiri yai shiru. Suna
zuwa suka sanar da Umman su Salman d'in, da
mamakin su sai su ka ga tai dariya. Sosai Fatee
ta burgeta, sai ta k'allo su, "kuna nufin kunji
haushi? Kai suka k'ada mata, sai tai murmushi,
"da zaku san adadin shekarun da na d'auka kan
na haife ku da baku kara kiran wata JUYA wai
dan bata haihu ba, na zuba muku ido ne, dan
nasan dole wataran zaku d'au darasi. Kowa
k'allon kowa yake, su d'ai tun ba yau ba suna
mamakin yadda Umman su ta t'sufa kuma wai
ya Salman ne d'anta na fari. By Feenat Ja'afar.
庐NWA. Feenat.mywapblog.com
9/29/16, 2:49 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 40_Rayuwar tana tafiya
ma Fure cikin godiyar Allah, domin a kullum ta
Allah tana matukar samun cigaba a rayuwa. Bata
da tawaya ta ko'ina ta bangaren jin dad'i ko
zamanta da mijintan, sai d'ai har yanzun Allah bai
nufi samun ciki ba, a kullum batta kalmar fad'i
ga Allah da ya fice "ALHAMDULILLAH" domin ya
bata d'ukkan farin cikin rayuwa... Tawaya ta
rashin D'a, bazata tai ma Allah butulci
ba..InshaAlllah, Abadan. Ga wani karin farin cikin
budi da ya same ta,AAAn ta ya bud'e mata
"Restaurant" nata na kanta. Jere suke, anyi
rubutu cikin "bord" d'aya da symbols.. "AAA
pharmacy & stores Ltd. Yayin da nata dake
makotanshi yasa mata "Mr's AAA Restaurants"
tamkar tag'waye abin g'wanin ban sha'awa. Toh
mey zata ce da Allah? Sai Godiya. Ajiyar zuciya
ta sau, lokacin da ta kara g'yara mak'wancinta
tana mai zuba ma AAAn ido wanda ke murza mai
a gaban "mirror" yana mai dan k'allonta. A zahiri
shi take k'allo, amma sam hankalinta yayi kan
dumbin Alkairin mijinta gare ta. A hankali ya tako
zuwa gefenta ya zauna, tai kur'i da ido ba ko
kiftawa. Ido ya zuba mata, ba t'sammani sai ga
nan siririn hawaye ya zubo bisa kuncinta. Hannu
taji a fuska ana goge hawayen, cikin nutsuwa ta
waiwayo da duban ta gare shi, murmushi yai
mata, kan cikin zancen karatun kurma ya tada
kai halamar mey ne ne? Murmushi tai,kan ta
k'ada kai halamar babu, sai ta matso tare da
d'aura kanta kan kafafunshi tana k'allon
fuskarshi,sai ya kai hannu yana mai tattare
gashin da ya bazar mata, sai ta ruko hannun tare
da rint'se su cikin nata tana k'allon shi. D'ayan
hannun takai fuskanshi tare da murmushi tana
shafo ta,shikam murmushi yake mata,cikin
sanyin murya ta hau mishi godiya bisa ga
k'yautatawar shi gare ta.... "Life is really not
worth living without you! You make me feel so
special and complete! I can鈥檛 find words to
utter,but I just want to say 鈥淭hank you and I love
you much more Dear... JazakALLAH. Ajiyar
zuciya ya sau, tare da k'ada cikin da jin dad'in
kalamanta, cikin salon shi dake sata taji tamkar
ita d'in "Queen" ce a "Universe"... Tuni ta sa
mishi ido kawai tana k'allo,ganin d'uk yadda tai
taga tafi AAA iya lafazin a fagen kaunar shi,sai
d'ai ina,tuni ya mata nisa. Dariyar suke,lokacin da
ya bud'e mata''bott" tana d'aukan k'wandon
abinci,sam bazaka ce su ne suka shekara 4 da
aure a tare ba, sun fi kama da irin sab'bin auren
nan dake ji da junan su. Mika mishi d'aya tayi,
kamar kullum ta d'au na Momy. Chan ta fara
yada zango kamar kullum, suna "parlour" ta tarar
Huwaila na kuka tana fad'in ta gama aure.. Suna
jin sallamarta sukai shiru, waje ta samu, sai ga
nan Rukayya ta fito a kitchen da abu a hannu,
kamar kullum cikin girmamawa ta gaida Momy,
sai da ta k'au da kai tukun ta amsa da "lafiya,
kan Aunty Jidda tazo, ita kam harara ma ta sakar
mata, su kam sauran ba wanda ya tanka ta, shiru
kake ji ba mai cewa uffan. Takan rasa a rayuwa
mey ta t'sarewa bayin Allahn nan, sam yadda
suka ki jininta ko Maryam da bata barinsu basu
t'saneta haka ba. "Mtsww.... T'saki Rukkay
taja,kan ta samu gefen Aunty Jidda ta zauna.
"Gaba d'aya anyiwa mutum dabaibayi duk an
hanashi rawar gaban hant'si. Ta karasa tana
y'atsine fuska, murmushi ta mata,kan tai kasa da
kai, Aunty Jidda tace "wai ni ba naji an bud'e
Restaurant da zummar nata ba? Hala tun yanzu
ya fara raba gado tunda ba D'a bare kwai? Baki
Momy ta ta6e, "shi fa ya sani, ni ina ruwana, su
had'u su talautashi ma shi ya sani. Kasa tai da
kai kawai tana jin su, tana jin Rukky ta amshe..
"hmm, matsiyaci kuke ji,ai bai iya samun gu ba,
sam yadda zaki san abin nan da agumau yadda
yaya ke rawar kai akanta, wallahi shi yasa bazan
ta6a harka da mat'siyacin mutum ba, sam.
K'allonta take, sosai nata sai ido, Fure lalle Allah
ya yarfa wa zuciyar ki hakuri, dama Maryam na
gun. Tamkar masu huce haushin mijin Huwaila a
kanta haka kowa ke mata, sai d'ai wai harda
Huwailan a zaginta? Abinda da mamaki, indai har
zata kirata da haka. Ita d'ai murmushi ne kawai a
fuskarta, sai ta janyo "basket" d'in abincin ta
mika gaban Momy tace ta tafi, ba wanda ya
tanka,sai ma t'saki da Rukayya taja mata. Sai da
ta t'saya a gefen "corridorn'' ta goge hawaye kan
ta karasa gun Mama. Anan ne kawai ta

12 / 18