JUYA Lokacin da Kaddara Ta Sauya Komai by Queen Safiyyert

Author :  Queen Safiyyert Category :  Romance

Chapter   1 / 18

1 to 3K   out of 51.2K words

9/27/16, 7:56 PM - Messages you send to this chat and calls are now secured with end-to-end encryption. Tap for more info.
9/29/16, 2:11 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
1_A gaban mudubi take tana k'yali,ta shafa
nan,ta shafa chan,ta mudubin kuma tana d'an
k'allon ta cikin shi tana murmushi, ganin yadda
mutuminta ya zuba mata ido ta ciki.
Juyowa tayi,yai d'ai-d'ai akan gado yana
k'allonta, d'uk rashin k'yau na abu,toh mud'in
kana muradin shi mai k'yau ne a wajen ka.
Babban mamakin shi yadda ya kasa ganin munin
Matarshi a kullum, yakan shafe "seconds" dan
gano ta inda "Prettyn"shi ta gaza, kai ya girgiza,
dan shi baiga makusa ajikinta ba ko kad'an.
D'uk a kullum dangin shi suna mishi gorin d'uk
k'yawawan garin nan,amma ya rasa wacce zai
jaju6o sai Fulera,ga ta "JUYA",ta bare suce ko
dan haihuwa taci darajar so,,d'uk ta tare gaba,ta
tare baya, ta hanashi ganin d'uk wani makusa
tata a gare shi,balle yai tunanin gazawarta na
zama "JUYA".
Asalima shi in d'ai zai tozali da Fureran
shi"Pretty" toh yakan manta komai.
"Pillow" ya sake jawo wa,lokacin da ya g'yara
k'wanciya yana cigaba da k'allonta, d'ai- d'ai da
dak'ika d'aya baya fatan yaga "Pretty" ta
barshi,yana matukar k'aunar ganinta kusa dashi.
Bai aune ba ya ji ta hure mishi ido da bak'inta
tana murmushin nan wanda ke sashi murmushi
ko da bai shirya ba,, kamshin "lestrine" ya buge
shi, had'i da kamshin alawarta ta kullum,"splash".
Take ya sau ajiyar zuciya, kan ya k'allota.
Hakika yana kara godiya ga Allah mad'aukakin
sarki da ya bashi "Pretty" a matsayin "Matarshi"
kuma "Sanyi ga Idanunshi". Tabbas yana daga
cikin maza masu t'sant'sar sa'a a rayuwa na
samun "mace ta gari'',wacce ganinta kad'ai, ya
isa wanke maka bak'in cikin rayuwa,har yai
hamdala da mahaliccin shi,dan ya mishi
baiwa,irin wacce ba Kowanne namiji ke da ita ba,
a ganin shi,dan ya hanashi "D'a" bazai zamu ya
masa butulci ba.
Murmushi ya sakar mata,kamar kullum ya fara
yaba mata wankanta. "Kinyi k'yau sosai pretty, a
kullum ranakun duniya kamar ana dad'a kawata
min ke ne,kamar ki zauna nai ta k'allon ki kawai.
"Ko zaki fasa zuwa sunan?
Murmushin jin dad'i tai,gashi d'ai kullum irin
kirarin nan tana shan su,amma baya hana taji
dad'in jinsu.
Zama tai, tare da ruko hannunshi ta kai baki
tai"kissing" take k'wa ya sauke ajiyar zuciya,tare
da d'aura d'ayan hannunshi kan nata..
Tsaf ta riga da ta gama samo abinta cikin ruwan
sanyi, ta riga da ta gama sanin d'uk wani "week
points" nashi akanta, mai lafazi mai k'yau ce ita
da sanyin murya, takan ko'k'arin tauna
zance,sannan ta ya6a mishi"gold" da "lu'u-lu'u
kan ta bashi.
Cikin salon ta da wata irin murya ta fara magana
tana lumlumshe mishi ido da d'an lallashi. Ji yake
mar rad'a take mishi a kullum.
"Kar kaji kom "Nawan" ni taka ce ai,k'walliyar ma
taka ce, zan rintse ta ga ganin kowa,sai d'ai in
mata y'an uwa na, badan sanin mahimmancin
sunan nan a gare ni ba,da zan ta zama,kai ta
k'allo na,har sai kace na ishe ka.. Ta karasa tana
fari da idonta, take k'wa ya sau ajiyar zuciya.
Unguwa ko bai niyar barin prettyn shi ba,da
kalam kawai zata sa ya firta "Toh".
Kai ya girgiza kan ya tashi ya zira rigarshi.
Ita kuma ta sa hijab da Nikaf dan rufe k'walliyar.
Tafe suke a mota,suna ta faman firar duniya
cikin nishadi,har ya faka a kofar gidan
sunan,wanda matar K'aninshi take gare shi.
Hannunshi na cikin nata,tambayarta yake sai
yaushe zai zo d'aukan ta? Ganan wasu na
shiga,wasu kuma na fita a gidan sunan,sai d'ai in
sun fito,maimakon su tafi,sai suja su tsaya
k'allon su prettyn.
Tana shiga ta tsaya ta cire nikaf d'in, kan tai
bangaren mai jego.
Da sallama ta shiga d'akin fuska sake, fal cike da
jama'a, kowa ya zuba mata ido, ta samu gefen
gad'on ta d'an dosa na,tana kula da hararar da
wasu ke sakar mata,"ina yinin ku.. Fuska mai
jegon ta yamitsa,kan tace"sai yanzu? Dad'i Miji..
Murmushi tai,dan tasan da ta tofa yanzu za'a
fad'a mata magana. Cigaba tai, "shidai cin tuwon
kishiya ramako ne,ehee. Kai ta k'ada, lalle
mutum.
K'anwar mijin tace ta amshe,"ba Kowanne tuwan
bane na ramako..kar ma kisa a ka,a yadda tai
shirim d'in nan ne zaki sa rai? Baki ta ta6e,kan
tace suna ga wata wai "JUYA" tashi tai "parlour''
tana hararar prettyn,wacce ke mata murmushi.
By
Feenat Ja'afar.
9/29/16, 2:12 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 3_Asalin su y'an
Kaduna ne,a karamar hukumar Zaria,Baban ta
Muhammad "mechanical engineer ne,Matar shi
d'aya,Mama Dije,da yaran su takwas, tun samun
aikin shi ya dawo cikin garin Kaduna da zama da
iyalen shi,a lokacin yaran biyu ne rak!, Suleiman
shine babban d'anshi,sun dan jima kan su samu
Aisha,sai Furera,Maryam, Hassan da Husaini da
k'annen su. Tun su Furera suna yara Abban su
ya shiga "missed call" sai ya zamo baiya aikin
Gomnati sai makanikanci, rumfa ya bud'e dan
wannan harkar, ko dan burin shi na sai yaran shi
sunyi karatu, da taimakon Allah,da taimakon dan
uwanshi dake Zaria ya kafu,, sosai ya iya g'yara,
dashi yake samu ya biya ma yaranshi karatu.
Tun tashin yaran yai musu sa6on dad'i, sai kuma
akazo ya rasa aiki,d'uk da haka yana iya kok'arin
shi yaga ya wadata yaran shi da d'uk wani abin
jin dad'i, ta yarda bama zasuyi kukan baida shi
ba,d'uk an neme shi daga baya yace ya d'aina
bautawa Government, g'wada yaci da gumin shi.
Mama Dijee itama takan yi su su6o da sauran
kayan sanyi. Sosai suna k'wata ma yaran su
tarbiya,kuma sun taso ba laifi, d'uk dunsu ba
masu son k'warafniya bane,in banda d'aya da ta
fita zakka cikin su,wato "Fure". Tun tashin Fure
sam bata d'aukar wargi,ita sha yanzu ce,magani
yanzu,sam bata barin ta k'wana. Gidan haya na
biyu kenan suna yi,yanzu su biyu ne aciki,sai d'ai
shi baban su sai ya kewaye bangaren su da
langa-langa, d'uk ba jin dad'in zaman suke,d'an
fa d'ayar matar sam batta kirki, d'uk hakurin
Mama Dijee sai da ta kaita bango,a kan yaranta
t'saf sai taci damara. Ga yara zagi a bak'insu
kamar ruwa. " Fure ki wuce mu tafi yanzun nan
kan na had'a ki da Umma. Kara chakumar wuyan
y'ar gidan matar tai, "wallahi bazan cikata
ba,mey yasa zata zagi uwata? Sa'ar ta ce? Jin
kok'awar fad'an ne ya fito da Larai daga daka,
tuni Aisha tai gefe,dan tasan ba abinda zai hana
ta rufar musu a ka. Zaune ta samu Furera akan
y'ar tana nad'a kamar Allah ya aiko ta, sarai
Umma naji, amma tai kamar bataji ba, Larai batai
wata-wata ba ta rufar wa Fure,tana dukanta ita
kuma tana narkar y'arta, wanda a zahiri ta fita
girma da komai,amma ihu take a taimake ta a
hannun Fure. Ganin zatai wa y'arta illah yasa ta
bar dukan Furen ta hau ko'k'arin fincike ta akan
y'ar. " uwata Sa'ar ta ne,ai dama na fad'a mata
wataran sai na fasa mata baki agidan nan, shegu
dangin maguzawa... Da gudu ta zuba, ganin larai
taiwo kanta tai zaure, g'walo tai ma yarinyar, da
tana kuka tana kuwa k'wararowa iyayen Fure
wasu mugan zagi ba ko dad'in ji, tana daga
zauren tace "oho d'ai, ko banza na koya miki
hankali, kuma zamu had'u anjima. Umma dake
d'aki suna jin ruwan ashar din da Larai da y'arta
suke watso musu.. tai shiru ita da Aisha da
sauran k'annen ta. D'a ne ka haife shi baka haifi
halinshi ba,ko ta hana Fure kula Larai da yaranta
sam bata jurewa,barin in suka zage ta,amma abin
na yau yafi k'arfin ta,dan d'uk tsiya sai d'ai suyi
chachar baki,amma yau Fure harda dam6e. Tana
zaure har taga shigar Larai da y'arta d'aki kan ta
arto da gudu tai kewansu. Harara Umman ta
sakar mata, uffan bata ce ba tai shiru, amma
dole yau asan nayi, dan sam zaman gidan nan ba
nasu bane, dan tsaf Larai zata gur6ata musu
tarbiyar yara, musamman Fure, zama da Larai
bak'inta yai masifar kara bud'e wa,ga fad'ar
magana kamar y'ar makafi. Da dare kuwa Abban
su yana dawo wa ta kora mishi bayani, kamar
kullum ci kanki bai cewa Fure ba,wanda ita
Umman ta zata zai ja mata k'unne. Tun daga
ranar jaraba ba kama hannun yaro tsakanin
ya'yan Larai da Fure, sam bata ko shakkar
girman su, haka zasu kamata su mata taran
dangi har uwar amma uffan Umma bazata ce ba,
kuma inda zasu k'wana dukanta sai ta rama
kuma ba ko hawaye, tana zuwa d'aki Umma ta
kara mata wani. Ba shiri Abba yasai fili ya kuma
ta dasu a gidan Larai kan suka samu lafiya.
Gidan su kad'ai ne a ciki,mai d'aki biyu da
baranda, yanzu burin Abban su kawai ya tara
kud'in gini, dan k'warai ya gaji da bin haya,in
yaso ko na kasa ya gina musu. K'wance tashi su
Fure har an shiga secondary, day d'uk yaran
suke,yayinda Yayan su Suleiman ya kammala
secondary sai jami'a. Sosai y'an gidan suna da
K'wak'walwa, barin Fure uwar rawar kai, Kasuwa
kam ta bunkasa wa Abban su, dan har ya bud'e
wa Ya Suleiman shima wajen g'yaran kan ya
samu g'urbi a A.B.U Zaria. Anyi hutu suka
tarkata sukai Zaria ziyara, anan ta samo yaran
kawunsu sa'aninta suma sun dawo a Queen
Amina, yadda suke bata labarin makarantar da
"boarding school" kawai tai sha'awar zuwa,,
Uncle d'in nasu achan yake aiki d'ayan, tuni Fure
ta tada bal'li ita sai Boarding. Da taimakon
Kawun ta biyu da Abban su ta samu g'urbi a
makarantar Queen Amina College. Haka Abba
yake fafutukar nema kodan biyan makarantun
yaran. Fure a Boarding, k'warai rayuwar ta
mata,d'uk da tana k'ewar gida wataran, nan ido
ya kara bud'ewa, daga "Furera" ta koma "Pretty".
A d'uk dabi'ar ta bata nuna cewa ita y'ar wani
ce,asalima ita irin k'aryar nan ta y'an boarding
sam bata d'ad'a ta da kasa, dan sosai tana alfari
da Abbanta, kuma bata 6oye mazaunin ta d'uk
fafar ta. K'wance tashi ba wuya a gun Allah,ga
nan su Fure har an shiga SS1, Cikakkiya ce
Pretty,ta bun kasa,d'an ba ramammiya bace ita
sam, t'sirinta da tsabar iyayinta su ke boye
muninta, bata sahun farare, sai d'ai sahun
bak'ak'e, sai d'ai a cikin bak'ak'en ma iya kiranta
wankan tarwada, a fuska kam ba wata
k'yak'yawa ta azo mu gani bace, d'an karamin
k'yau gare ta, sai d'ai a jiki a dire take. Babban
sirrin k'yaunta" gashi" dan ko a fuska "eye
lashes" d'inta da girar ta sunfi d'aukar ta tazamo
mai k'yau. Yadda k'wa take far-fara su in tana
zance, kai kace da ga'iya take,dan tamkar tai
"fixing". By Feenat Ja'afar.
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Apr 10
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 4_A jiki "Full option" ce
kam,abun da a yanzun tafi jin haushi a kira ta
dashi kuwa shine "Fure". Yana d'aya daga dalilin
da yasa a school suka k'ak'aba mata" Pretty "
dan kam ita k'yau ce da wanka. D'uk yanzu y'an
unguwa yawanci da Pretty suke kiranta, a gida
ne kawai sunan ya gagara k'arbuwa gun su
Umma,dama shi Abba bai san da sunan ba.
Ak'wai lokacin da Abban ta da ya Suleiman suka
je musu Visiting, shaf sai suka manto visiting
card d'in a gida. Da alfarma aka kira wata mate
d'in su Fureran kan su fad'a mata sunan ta kira
ta da y'anuwanta. Sunan ta tsaya tana maimaita
wa, halamar tama rasa mey shi, sai da yasa
sunan uba da unguwa kan tace"au Pretty ce, bari
na kira ta,, da d'an gudunta ta tafi tun daga
wajen ta fara k'wala mata kira, Abba ya girgiza
kai, kan ya k'alli yayan nasu,"yanzu wai kaji Fure
har sunan k'arya ya shafe na gaskiya? Murmushi
yai,kan yace"Abba makarantar kenan,sai a
hankali. Tana hango su Abban da gudunta ta
nufo su, har ta baro sauran a baya,"da gaske
k'wa kaga ita d'in ce suleimanu, dariya yai,
lokacin da ta karaso tak'wa tukuikuye Abban,kan
ta koma kan Yayan nasu. Bayan sun gaisa yace,
"Yanzu Fure ke ce kika koma pretty saboda
Allah? Da sauri ta matso tana marairaita mawa
baban kan ya d'aina cewa Fure,sai wai school ta
d'auka. Yace" ungo naki, shi dai ya Suleiman
dariya kawai yake musu. "yasu Umma? Yaya ya
makaranta? Yai murmushi, "suna gaida ku, " yaya
ka kusa gamawa ai? Kai ya k'ada mata,''InshaAll
lah, murna take kan yayan ta shima zai zama
engineer. Sunje hutu sun dawo,wanda a shine
suka shiga ss2,anyi sabin coppers, yayin da
iskancin su pretty ya motsa. Sun bala'in raina wa
coppers hankali, d'an su kam mayun mata ne.
Ranar d'aya ya shigo ajin,Hausa yake d'auka, sai
fafa yake musu shi nan a dole yana gaban y'an
mata. Bayan ya gama darasi ya k'allo su, dariya
kawai suke mishi, amma shi ko a jikin shi, sai ma
wage musu baki da yake. "If you hv questions
queshh" or additional information... Haba wa,mai
su Pretty zasuyi inba dariya ba. Har aka buga
"next period" ya bar ajin ba wanda ya kula shi
sai shakiyancin su suke. Yana fita su pretty ita
da y'ar desk d'inta suka fito k'waik'wayar shi,, ta
d'au alli"if u hv questions quashhhhh... Or
additional information. Yadda kasan shine a
gaban allon. Fad'i suke in banda malam,mey ya
kai turanci kai da kake koyar da hausa? Tuni sai
suka fara tariyo na d'ayan coppern da yai musu
mathematics, dariya Fure take harda rike
ciki,d'an yin irin in'inar da d'an NYSCn yake.
Tsitt! Ka ke jin ajin sai dariyar Fure da Adama ke
tashi. Zungurar ta Adama ta fara,lokacin da tai
ar'ba da abinda yasa class y'in shiru. Hard'e
yake da hannu a kirji,rike da "text book" an
rubuta"chemistry" a jiki,sanye yake da fara sol
d'in rigar NYSC da siririn farin glass a
fuska,fuskar nan sam ba annuri,, tunda suke ko a
malamai basa jin da wanda ya ta6a musu
k'warjinin wannan, balle a wanda suka raina. Ajin
ya shigo,har lokacin idon shi nakan Fure da ta
kame a gun baki sake, tuni ita Adama tasan
nayi. A gabanta ya tsaya tamkar wani soja rai a
had'e. Takarda Adama ta nannad'e,sai ta seta
Furen ta hulla mata, a tsorace tabar K'allonshi
tai gun zamanta. A t'sanake ya karewa ajin
k'allo, tabbas nan Garba ya shigo dazun,dan daga
iskancin su yasan sune, yana jin lokacin da
malamin Hausa yake sanar da sauran iskancin
da suka masa. Ya kai a k'alla minti biyar yana
karantar ajin su Furen,yana k'allo takadiran cikin
d'aya na zungurar d'aya. Kai ya k'ada, kan ya ju
ya kan allo ya fara rubutu. "Chemistry" Shine
abinda ya rubuta. Fure ta ta6e baki. Juyowa
yai,kan ya bud'e baki cikin murya mai sanyi.
Cikin turanci yace sunan shi "Ahmad Abba
Ahmad", shi zai na d'aukan su Chemistry daga
yau. Bayani yake musu,wanda tsit ka ke ji kamar
anyi ruwa an d'auke, dan d'uk iskancin su nasan
kure Malami a turanci yau sun gamu da bokan
turai. Class mastern su har zuwa yai leken ajin
dan jin yau shirun su da yai yawa, a tunanin shi
discipline master ne a ajin,da mamakin shi sai ya
ga Ahmad. Kai ya k'ada, lalle wai gaba da gaban
ta,Aljani ya taka wuta. Ko da aka tashi gulmar
Uncle Ahmad suke ta yi,daga suce mai girman
kai,sai su ce ya had'u amma. Suna hanyar tafiya
"hostel" suna ta shakiyancin su, kasancewar ss3
suna "practical'' a "hall'' yau su suke cin karan su
ba babbaka. Ko "lunch" basu tsaya k'ar6a ba
suka taho. A bak'in "gate" suka tsaya, ganin
Baba mai gadi na d'akin shi bai kuma gate d'in a
datse da "key", maimakon suce ya bud'e musu
su shiga,kawai sai suka hau mishi wakar su ta
kullum,wanda har ya riga ya gane su Fure. "
Baba a bud'e "gate" ko mu taru mu 6alla "gate"...
Shima kamar mai wakar daga d'akin nashi ya
basu amsa, "Ku taru ku 6alla,tunda gate d'in na
uban ku ne... Dariya su Fure suka sa, lalle ashe
mutumin su ne " on duty". Kawai sai suka bashi
amsa dan kawai suyi ta deban shi,, "K'warai na
uban mu ne,tunda Gomnati ta siya.. Da gora ya
fito daga d'akin yana bam-bami," yau zan kawo
karshen iskancin nan naku,, "au Fure? Nasan
kece gandi lida, yau za kuyi bayani.. Dariya suka
sa mishi," Baba namu,mukwa na Allah, muga
Annabi... Da gudu suka zuba, ganin ya bud'e gate
d'in yai Kansu da gora,, wuuu sukai "gate" d'in
kamar zasu 6alla suna mishi dariya,tun daga nan
aka fara yin d'ai-d'ai da kaya, daga su sai
underwear suka isa hostel. Washegari kuwa da
safe sai ga kira daga principal tana kiran Fure da
y'an Eysla d'ukansu.. Principal kam tasu ce,ba ko
shakka suka nufi office, sun san bazai wuce
fad'a akan surutun aji ba. Masinja ne yai kiran
Furen ita kad'ai zuwa ciki, yana zaune su biyu a
kujerar da ke gaban principal d'in, da ladabi ta
gaida principal, kan a ciki ta gaida su,d'ayan ne
kawai ya amsa,yayin da d'ayan ya d'auke kai.
Dagowa principal d'in tai,ganin Fure ce yasa ta
k'ada kai,"Furera" kai sunkuye ya ta k'warai
tace"Yes Mom, kai ta k'ada, kan tai murmushi, "
Trouble marker" kenan,ai tunda naji SS2 ne nasan
sunan ki sai ya fito ciki. "Wai zaku 6allawa Baba
gate koh? Kai ta kara kasa dashi, "sorry Ma, kai
ta k'ada, " ai kinfi kowa rashin ji, sannan kinfi
kowa tsoro. By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 2:13 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 5_Tuni tai narai-narai
da ido kamar zatai kuka tana k'allon PCn, "Momy
kiyi hakuri, kai momyn ta k'ada, " last warning "
kar na sake jin haka daga gare ki "Fure" kai ta
k'ada, kan tai godiya tai waje tana murnar ba ko
"punishment". PC ta k'allo su Ahmad, wanda
suke k'allon yadda momyn ta bi Fure da k'allo
tana murmushi, " yaran sun matukar shiga raina,
tun jss1 d'insu aka kawo ni, tun a sannan nasan
dasu,fitina, tsokana,ilimi d'uk yan su ne. Kai su
Ahmad suka k'ada, tare da mamakin saukin kan
principal d'in. An dawo a break yake da su, d'ane
wasu suke akan desk a zaune, wasu sun had'a
group ana shewa, chan ya hango Fure a tsakiya
tana ta zuba k'wainane, kofa ya buga,da sauri
kowa ya nemi waje ya zauna. Kamar jiya,yau ma
ya kare musu k'allo, magana principal ya fara tan
tama na anya yaran suna da kok'ari? Akan Fure
ya dire idon shi wace ke fito da irin "Text book"
d'in shi a jaka. Ciki ya shiga,kan zasu gaida shi
ya zaunar su. Daga inda ya tsaya jiya ya
tashi,suna tsaka da karatu ya k'allo desk d'in su
Fure, ture-ture suke kamar wasu yara kanana.
Alli ya saita su dashi ya hulla musu, da hannu
yace su mike, kan ya tambayi sunan su, "Fure"
ya kira ta, da sauri ta daga tana k'allon Y'an aji
da har sun fara kunshe dariyar su, tuni ta kicin-
kicin da fuska kamar zatai kuka. Gaban allo yace
ta fito. Hannu ya hard'e tare da zuba mata ido
cikin glass,ita tuni hankalinta yai kan y'an ajin,
bata zata ba ta tsinci tambayar shi gare ta. "can
you name the first 20 elements of the periodic
table pls?" Tsayuwa ta g'yara,dan yasan dak'yar
in ma ta sansu bare ta rike su.. Sai d'ai kan ya
karasa zancen zuci ya tsinci muryar ta cikin
sauri-sauri tana jero su kamar ma ita wasan yara
ta d'au ka. "Hydrogen,Helium,Lithium, Beryllium...
Ba ko shan numfashi ta dire masa su tana du6en
shi. Kai ya g'yada, kan ya sake jeho mata wata
tambayar,kiris yake jira ya sata kneeling. "
electronic configuration of firs.... Da sauri ta
katse shi tare da karanto mishi, "Boron,carbon,
Nitrogen... Suma ta dire cikin sauri ba tare da ta
bari ya gama maganar ba,dariya y'an ajin suka
fara,tun itama tana dake wa har suka sa ta yi,
ajin ya k'alla, sai sukai tsit,itama ta kunshe tata,
bak'in kofa ya nuna mata da hannu, da mamaki
take k'allon kofar,wai tai "kneel down" ta daga
hannu ta rufe ido, tuni kuma ido sai ya raina
fata, dan taki jinin punishments,ga ya had'e rai
ba damar bada hakuri. Daga yin minti 5 ta fara
raki, shikam dalibai ya cigaba da koyarwa,jefi-jefi
yana d'an k'allo ta. Hawaye ta fara,da gefen
hannu take gogewa,gaba d'aya hannunta ya fara
sage wa, sai motsa K'afa take halamun ta gaji,
ya juyo da zummar kara k'allonta yaga tana
kuka, sai ya d'auke kai, y'an aji tuni aka shiga
taitayi,ganin Fure na kuka,dan sosai sunsan abin
da zai sa Pretty kuka babba ne. Ba'a fi

1 / 18