Author : Queen Safiyyert Category : Romance
zaka
sansu, sai ya k'allo Fure da murmushi, itama ta
k'akalo murmushin dole. "she's my.. Da sauri ya
tare mashi numfashi da fad'in" I know, sai yai
murmushi a takaice, kan ya k'allo Furen, Ya
Suleiman yace"ok,kun ta6a had'uwa a gidan ne
hala? Kai ya k'ada, duk sai ya ji tsayuwar ta
gundure shi,Aisha ce ta katse shi da fad'in
"Ina Angon ka barmin shi? sai kuma ta rufe fuska
ganin yadda Yayan su ya kafa mata ido, " iyee!
Lalle fitsaru. Shikam murmushi yai kan
yace"yana a masaukin shi,zai zo bada jumawa
ba.
"Zan wuce, dama Ilyass ne yace na tabbatar da
lafiyar Madam d'in shi,sai mun had'u a " Dinner ".
K'allo su Fure yai,"toh amare zan wuce,sai mun
had'u anjima, kai Fure ta k'ada mishi, kan ta d'au
ledar su ta shige gida,da tsabar takaici,ashe ma
ba dan ita yazo ba? Ajiye dilkar tai da suka
k'ar6o, tai ciki ta bar y'an biki a t'sakar gida.
Shikam a mota d'uk ya rasa sukuni, Fure ita ce
mace ta farko da ya fara jin " feeling'' akanta,
hatta Maman shi tasan da zancen Furera,yau da
ya sanarta yaga Furera k'warai ta tayashi
murna,har yaje gida sukuku yake jin kanshi. Sam
baida kuzari.
D'akin Maman shi ya zu6e, wanda indai maganar
mace ne toh dole sai wajen ta,amma sauran
lamari Momy ce ja gaba sama da Maman tashi.
Mata biyu ne ga Baban shi, Momy itace Uwar
gida,yayinda Mama ke amarya, d'uk a zankuwa
aka haife su, sai d'ai lokacin su Ahmad na yara,
kamin suka dawo Kaduna da zama gaba d'aya.
Baban su Alhaji Abba Ahmad "costom" ne kan
yai "resining" ya zama d'an k'wangila.
Sosai yana da kud'i, sannan da dattako, Momy
nada fad'a, sam taki jinin talaka,dan baban ta
babban "costom" ne lokacin da Alhaji Abba ya
aure ta.
Ga matukar dagawa da raina mutum,ga son fasa
taro,komai ita ke ju ya shi son ranta a
gidan,yaranta 3,Hauwa(Aunty Jidda), itace babba
a gidan,sai Nasir,da Huwaila, sai y'ar K'anwar ta
da take ruko Rukayya.
Kan aka auro Mama, d'uk itama gidan su ba
laifi,gata mace ce har mace,mai hakuri da
t'sabar sanin ya kamata,tana da kawaici, kullum
zaka samu fara'a k'wance kan fuskarta, da fari
Momy ba taso zama da kishiya ba sam ita,
sai d'ai kuma wani had'in Allah, kawai sai tasu
tazo d'aya, dan komai ta sakar mata ta
mallake,hatta yara in ta haifa toh sun koma
zaman d'akin Momy,ita kam dake mai hakuri
ce,d'uk sai ta sallama mata su, yaranta
shida,Usman, wanda shine mijin Aunty A'i, sai
Aunty Maryam,Ahmad,da Ummi autar ta rasu.
Amma d'aya kawai ta rike wato Ummi.
T'sakaninta da sauran sai gaisuwa koh in taje
bangaren Momyn,sai ko randa ta motso musu
suzo bangaren ta,dan ita k'wa6arsu take matuka,
amma a d'akin Momy sunan ka"kai komai ba
komai na".
D'uk da mugun hali irin na Momy sam batai ma
yaran Mama mugunta,batta da mitar ta,hakan ne
yasa ita maman sam bata damuwa,sai d'ai abu
d'aya, duk yaran kad'an ne basu kin talaka da
raini,wannan dabi'ar ita kad'ai ke ciwa Mama
tuwo a k'warya.
Dan tamkar fad'an Allah d'uk yaran gidan sai mai
kud'i, in maza ne sai ya'yan manya masu k'yau.
Hudubar Momy kam tai aiki,Ahmad shine ya fita
daban,wanda sam baiya burin auran y'ar masu
dashi,sannan kuma k'yak'yawa.
Asali ma tun tashin Rukayya Momy tace itace
Matarshi, shikam fur yaki, dan ka'f ba abinda ta
bari a halin Momy,tamkar ita ta haifo ta.
Gadai k'yau har k'yau, amma sam ba hali. Shi
yasa ko dariya Ahmad bayayi a gaban ta,
asalima ita d'uk gidan shi tafi tsoro.
Takanyi ma Momy kukan sam Ahmad bai kula
ta,sannan ga hancinin tsiya. Momyn takance ta
k'wantar da hankalinta,Ahmad kamar ya zama
nata an gama.
Haka kowa yana da burin fita kasar waje yai
karatu a gidan amma banda Ahmad.
Rayuwa mai sauki shi ya za6arwa kanshi, kuma
a zahiri kowa a gidan naji da Ahmad, har sukan
kira shi da mai "ra'ayin kanshi".
Anan ya had'u da Ilyasa,yayinda shi Ilyass yake
abokin Ya Suleiman. Nan suka k'ulla abota, duk
da kowa bangaren shi daban,sannan ba yadda za
ai ya nuna maka shi d'an wani ne,dan ko mota
bai ya zuwa da ita cikin A.B.U.
Ko Abban ne a yanzu d'ai da Ahmad yake yawo
ko ina zashi,tunda sauran manyan yaran kowa ya
kafu da K'afarshi.
Sosai Abban su yake son yaran shi,haka bai son
takura musu,yai musu sa6o da jin dadi,d'uk da
shi d'ai bai kin talaka,sannan baida wulakanci.
Mama ce ta k'allo Ahmad," ya d'ai? Har ka dawo
a gun Fureran? Kawai sai ya k'wanto cinyarta
"Mama aure zatai go6e.." Ya Salam! Shine
kalmar da maman ta fad'a.
Kamar ya k'urma ihu haka yake ji.
"Ita ta fad'a maka? Kai ya girgiza, " A'a, Aboki na
d'ai zata aura.
Kanshi ta shafa cikin sigar lallashi, "kai hakuri
toh,Allah yasa hakan shi yafi zama alkairi, Amma
sosai nima d'uk da banga Furan nan ba ta shiga
raina. Nan tai ta bashi baki,kan matar mutum
kabarin shi.
By
Feenat Ja'afar.
[4/16, 1:44 PM] Feenat Ja'afar: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
10_Da k'yar ya iya shirya wa zuwa wajen
"Dinner". Sosai yai k'yau cikin manyan kaya yau
da ya shige su,dan shi ma'abocin kanana ne.
Farar shaddar ta matukar k'ar6ar shi, ga hular
nan ta kama,sai kamshi yake kamar Angon ba
wai abokin Angon ba.
Parlourn Momy ya shiga,don sanarta ya fita.
Rukayya ce kawai a parlourn tai d'ai-d'ai a kujera
tana " 2go". Tana ganin shi ta mike da rawar kai
harda ce mishi yai k'yau, baki ya d'an ta6e kan
ya had'e rai''ina Momy? Da dan harara ta nuna
mishi d'aki ta koma ta k'wanta a ranta tana"ka'r-
ka'ra a d'aura mana aure ne,zaka shigo hannu.
Sukuku ta gama shiri tun jiya batta kuzari,
hakanne ma yasa Y'an uwan suke d'an sata
nishadi,amma da anjima zata dawo gidan jiya,su
sun d'auka koh rabuwa da Aisha ke sata haka.
Tsaye suke a gaban madubin su na katako a
d'akin su,kanta kawai take k'allo, matuka tai
k'yau tamkar wata k'yak'yawar. Tabbas in kana
da k'yau ance ka kara da wanka.
A d'uk k'walliyar k'ewayen idonta yafi ko'ina
d'aukar hankali.
Ma'abociyar ita gashin ido ce dana gira sune
tushen k'yanta. Yau sunsha" Mascara'' da "eye
liner''. G'yaran jikin da fatarta ta samu ita ta
fidda ta zama " Black Beauty",
net ne "gown" "combination" d'in fari da "pink" a
jikin ta.
Daga sama aka sa farin zuwa chan g'wiwa,
kasan aka mishi tattara da "pink" d'in, da "head'
na "pink" da k'yali-k'yallin "silver''.
sosai tai k'yau ainun kamar itace amaryar.
d'uk da su masu karamin k'arfi ne amma ak'wai
zuciyar yi,dan sosai sun fitar da kansu
kunya,d'ai-d'ai g'warg'wadon hali Abba da Ya
Suleiman sun fitar su kunya.
Kawun su na Zaria shi ya d'au nauyin gado da
kujerun Aisha y'an zamani,sosai y'an uwa ma
sun musu kara abin sai son barka.
Adama ma tasha lefe Ya Suleiman kamar ba
go6e,ranar albashi yai rana da taimakon
makanikancin.
Aisha ce ta shigo ita ma sanye da" net"
"brown".. Sosai tafi Fure k'yau,amma a yau d'uk
sun had'u sunyi k'yau sosai.
Gaban madubin taje tana murmushi, kanta ta
d'aura akan kafad'un Furen, " y'ar uwa tamkar
kece amaryar kinyi k'yau ainun,, murmushi Fure
tai d'uk tai laushi, "ku nake tayawa k'yau tunda
kunyi k'yau kuma. Tai murmushi, "dan Allah
Furare mey ke damun ki? Tun randa abin nan ya
faru d'uk kin dawo wata iri, kinyi sanyi sosai,
"dazun naji kince ma "pharmacy" Uncle, amma
kince min baki sanshi ba,bayan Ya Suleiman yace
anan yai "service'' a school d'inku,mey kike 6oye
min ne? Murmushi tai kad'an kan ta juyo, gaskiya
ta fad'a mata kan ta sanshi sosai.
Ido kawai ya zubawa kofar " Hall" d'in dan jin
ana sowar ga Amare nan, Asha da Angonta ne a
gaba,sai gata ita da Ya Suleiman, sai dai shi ya
ju ya waje lokacin da ya gane Adama ta tsaya.
Ido ya rintse dan ganin lokacin da Ya Suleiman
ya rad'a ma Furen wani abu tana d'an tushe baki
da dariya. Tsayawa su Aishan sukai,har ta
karaso bai daga kanshi ba.
Tana daga kanta tai ar'ba dashi ido rufe,da sauri
ta d'auke kanta jin wani abu na taso mata a
zuciya wanda tuni ta rufe bab'in shi.
Sowar daya kara ji ne yasa ya bud'e ido,sai ga
Adama sun shigo da Ya Suleiman, da sauri ya
k'alli wajen su Aisha yaga Furen na tsaye tana
d'an murmushi tare da d'an had'a hannu tana
musu tafi a hankali.
Wata ajiyar zuciya ya saki tare da sakar
murmushin farin ciki.
"Dama Adama ce matar Eng.Suleiman? Kai
amma ansha dashi k'warai. Tashi yai Shima yana
d'an tafa musu da murmushi a fuska,kan a
hankali ya ju ya ga Fure, wacce itama da sa'a ta
k'allo shi,murmushi ta sakar mishi wanda kamar
dak'yar ya fito,kan ta d'auke kai a hankali.
Sosai ya famo mata wani ciwo,ga wani uban
k'yau da ya mata cikin manyan kaya yau d'aya,
dak'yar ta saita kanta.
Chan inda aka warewa abokan Ango da na Amare
ta nufa kai d'uke, kujerar da ke k'allon shi kawai
ta rage" empty " shikam har yanzun k'allonta
yake har ta zauna.
Ana gabatar da abubuwa shikam Fure kawai ya
zubawa na mujiya,sosai tai mishi k'yaun ban
mamaki, ga wata nutsuwa da yaga tai bala'in
mishi, kamar ba Fureran da ya sani ba. Kowa ya
tashi,na taka rawa suna yi,na yawo nayi, sai ya
rage daga Fure sai Uncle Ahmad.
Kai duk'e ta gaida shi da sanyin murya,jin bai
amsa ba yasa ta dago,murmushi yake yayin da
idon shi ke k'anta. Sai ta samu kanta da kunyar
shi.
Da k'yar ta samu ta zame da wayyon Adama na
kiranta.
Binta yai da k'allo, yau d'aya Fure ta kara
mamaye zuciyarshi, bazai kuma kara sakacin ta
ku6uce mishi ba. Wa yaga "real Love'.
Daga ita har shi har aka tashi fara'a suke, ita
kam batasan tata ta meye ba.
Maimakon yadda suka zo su koma tare ita da
Amare,kawai sai mazajen su suka d'auke su,Ya
Suleiman yace ya had'a mishi da y'ar K'anwar
shi da wata cousin nasu.
Ba dan taso ba suka shiga motar,wata "civic"
baka mai k'yau.
Baya Sadiya tai saurin shiga,wai ita ta shiga
gaban. Haka tai sakare,kan ta bud'e ta shiga,ya
ja su.
A hankali yake tuki cikin nishad'i,ya kan d'an
k'allota kad'an kan yai murmushi, itama takan
d'an satar k'allon shi ta gefen ido, fuskarta
sake,sai d'ai ba walwala,kowa y kasa ce wa
kowa uffan.
"A.C ya kara,kan ya hankali ya kai hannu ya
k'unna wakar da in d'ai zai ji ta toh Fure ke fad'o
mishi, sai d'ai yau gata gare shi, a hankali ya d'au
"remote" ya d'anna "play" sai ga nan wakar
"Nothing gonna change my love you ta shigo.
Tsam ta nutsu, tare da sauraran b'aitin cikin
wakar,sai ta samu kanta da lumshe ido kamar
mai bacci,tare da jingina kai a kujerar motar.
k'allo ta yai,kan shima ya jingina a kujerar yana
tukin shi cikin nishad'i,tamkar ance an bashi
Fure.
By
Feenat Ja'afar.
9/29/16, 2:18 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 11_Ido rufe kamar mai
bacci taji sun tsaya,maganar sadiya ta tsinkaya
tana mishi godiya,kan ta fita,k'allo shi tai,kan
cikin sanyin murya tace"mun gode Uncle, ba ta
jira mey zai ce ba ta fara ko'k'arin fita,sai dai
gam, kofar a kule,tsam tai,kan a hankali ta juyo
ta k'alleshi da halamar tambaya. Shima idon ya
zuba ma ta,sai ita ta k'au da nata,kusan minti
uku ya ki magana, ita kuma tsabar haushin shi
ma take ji,wanda ita kanta bazata ce ga dalili ba.
Chan yai ajiyar zuciya, kan cikin nutsuwa
yace"Furera... Kanta na gefe ta amsa,sai kuma
ya kasa ce mata komai,mota ce ta hasko su,su
Aisha ne, gaba d'aya suka bisu da k'allo ganin
yadda suke a nishad'i, kawai sai ya d'anna
"unlock" kan yace"ki tsimaye ni gobe..dan
K'allonshi tai kan ta k'ada kai tai waje,da k'allo
ya bi ta, kan shima ya fito. Gun su Aisha tai,duk
jikinta yai lak'was,ganin ba Adama tasan sun
kaita gida. T'sakiyar su Ya Suleiman ta shiga da
Aisha, yayansu mai saukin kai ne,ba ruwan shi
da hantarar su ko k'yara, shi yasa k'warai ya
zama abokinsu. Murmushi kawai Ilyas yake
musu,ganin yadda Fure ke shag'wabe fuskarta.
Uncle Ahmad ya karaso yaga Ya Suleiman ya
kama hannun Fure,sai ya t'sinkayi maganar shi
cikin lallami,"wai Aisha mey ya samu Furii ne tun
jiya bata da walwala? Murmushi tai,kan ta k'alli
Uncle Ahmad wanda idonshi ke kan Ya Suleiman
a na Fure. "Na tambaye ta tace ba komai. Ilyas
yai murmushi," hala bata son ku tafi ku batta ne?
Gida su Aishan suka shiga,kan su kuma suka hau
fira a kofar gidan. Kasa d'aurewa Ahmad yai,"wai
ni Engnr. Meye had'in ku da Furera pls? Na kasa
gane wa fa.. Dariya sosai Ya Suleiman shida
Ilyass suka,kawai sai ya sa musu ido,shi d'ai
amsa yake nema. "Amma tambayar ta ban
mamaki "pharmacy", cos jiya ka ce min" you
know'' I thought ko a makarantar su kasan ta ai.
Kai ya k'ada, "Eh,amma bansan nan ne gidan sun
ba. Ilyass ne ya dafa shi da d'an dariyar shi,
"kana da abun dariya Aboki,hala neman iri ka ke
ka fara bamu girma tun yanzun? Murmushi yai,
tare da k'ada mishi kai, " toh abinda yai Aisha
shi yai Fure yai kuma Engineer.." Same Ma,
same Baba.. "Ko in ma ta d'an g'wari-g'wari? Kai
ya k'ada murna fal cikin shi,kan ya k'allo
Suleiman, wanda har yanzu yake dariya kasa-
kasa. " a gaskiya na wahala a neman K'anwar ka
Engr. Ashe tana a kusa ma ban sani ba?
Murmushi yai, kan ya k'ada kai. "Pretty".....
"Furera''.... Kai, yanzu na gane, ashe ita ce
wacce ake neman nan ido bud'e. Cewar Ilyass
cikin shakiyanci. "Shegen kaya, kai yanzu ko
kamar ai zaka d'akko hanya. Kai ya k'ada yana
murmushi, kan yace "a bar zancen kawai, amma
ni kam,naga gida. Dariya Ilyass ya sa
mishi,shikam Suleiman k'ada kai yai, dan sosai
yasan had'in yayi, lalle k'annen shi sun dace da
mazajen aure na k'warai. Dan Ilyass abokinshi ne
sosai,tun a Zaria, ta dalilin shi yaga Aisha,
sannan yasan Ahmad, sosai ya yaba da yadda
yaje gidan su Ahmad yasha k'allo, amma sam shi
bai ta6a nuna musu shi d'an wani bane. Kai ya
k'ada, yana mai adu'ar Allah sanya alkairi. Bak'in
nan kamar gonar audiga ya shiga gida," direct "
d'akin mama ya nufa,suna parlour ita da Ummi
suna k'allo, yadda yake fara'a ne yasa mama
K'allonshi itama d'auke da tata. "Ka dawo? Kai
ya k'ada, kan ya k'alli Ummi wacce tai likwas
cinyar Maman tana mishi sannu. Da murmushi
yace "Je kice Momy na dawo a kai min abinci
d'aki.. Kai ta kada kan ta d'au dank'wali ta yafa,
kusan Ummi halinsu d'aya da Ahmad, shi yasa
tasu tazo d'aya, dan rainon mama ce ita. Tana
fita ya k'allo mama. "Mama pretty ashe K'anwar
Suleiman ce uwa d'aya, ashe ni ne ban gane ba
sai yau. By Feenat Ja'afar.
Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 18
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 12_"mashaAllah, ashe
Furera na kusan mu ma. Kai yai kasa dashi yana
dan sosa keya yana murmushi, mama tace"toh
Allah sanya alkairin shi,sai d'ai bansan yadda
zaka kaya da Momyn ku ba Ahmad? K'allota
yai,kan yace"gaskiya mama Rukayya bata a
matan aure na,cos ba lalle muyi zaman aminci da
ita ba nasan. Kai ta k'ada, lalle tasan ak'wai
rigima a kasa,dan sarai tasan yadda Momy ta
d'aukaki had'in nan nasu Ahmad da Rukayya, ita
d'ai tasan nata ido, sai kuma tabi su da adu'a.
Washegari "10am" aka d'aura auren masoyan
biyu,basu samu kansu ba sai dare bayan ankai
amare gidajen su,d'uk anan suke. Shi yau ma ya
d'akko ta daga gidan amarya,yau da ita da autar
su,cikin nutsuwa yake sauraran surutun
Amal,bata fi "4yrs" ba, kawai sai ya ji babyn ta
shiga ranshi, sosai tana mishi kama da Furen shi.
Kawai sai ya fara bata tad'in Fure a schl. K'allo
ta yai,itama fara'ar take,sai yai murmushi, Amal
tace "Uncle, kuma kana d'ukan Aunty Fure in tai
surutu a class irin Uncle John? Harara Fure ta ju
ya ta sau ma ta jin tace mata Fure. Murmushi
yai lokacin da suka had'a ido da Furen. Kan yace
wa Amal "nop,sai d'ai na sa ta " kneeling" dan
kinga ai ta girma koh? Kai ta k'ada mishi tana ma
Furen dariya. "Toh kuma tana kuka? Sai ya k'alli
hanya yana tuno wani lokaci a baya.. Akan Fure
ya sauke idon shi, wanda take k'allon titi ta kasa
k'unne ta ji amsar shi. Sai yai murmushi, tare da
k'ada ma Amal kai, "sosai,har tana kiran Umma
tazo ta taimake ta.. Dariya suke mata, ita kam
kai ta lang'wa6e mishi, " kai Uncle A,ni d'in? Gira
ya daga mata,sai kuma ta d'auke kai. G'walo
Amal ta mata tana "woo Aunty Fure.. A karo na
biyu tace"wai waye Fure? Dariya yai har da
d'ukan sititari,ganin yadda tai da baki gefe Amal
ma ta mata. Yace!" No Amal,daga yau sunan
ta"Aunty Pretty... Baki suka saka,ita na
K'allonshi, Amal na k'allonta. Ido ya k'anne
mata,da sauri sai ta d'auke kai tana murmushi,ya
akai yasan Pretty? Ko a schl? Amal tace,"La!
Uncle "Pretty Zinta ta Jaduu? Dariya suka sa
mata d'uk, kai Amal. Haka har suka zo gida Amal
na musu abin dariya. Tsaida mota yai,kan suka
fito,ganan y'an kai amare wasu suna waje,sai
Amal tai gida wai d'akko mishi "sweet". Da k'allo
ya bita, har ta shige gida kan ya dawo kan Fure.
" pretty"...Buguwar zuciyarta ne ya dawo take
yau,dan jin ya ambaci sunan ta cikin sanyi, a
hankali ta amsa, "Ashe Engr. Yayanki ne? Kai ta
daga mishi,kan a hankali tace" Umm. "Sai ki ka ji
ni shiru ba? Kai ta duk'ar, ba tare da tace kom
ba. Tsayuwa ya g'yara, kan ya fara bata labarin
bayan rabuwa. " A motar haya na gamu da mai
yankan aljihu,waya na da "Address" naki da na sa
d'uk ya de6e, k'warai na fi jin ciwan 6atan
"address" d'inki sama da "phone'' na,karshe nai
"losing" "contact " na Abba,ko da nai "swapping"
still ban samu ba..kai ta dago,da mamaki ta
k'alleshi. " kin san dalili? Kai ta k'ada. Amal ce
ta dawo da alewa a leda tana bashi,sai yai
murmushi, maganar da bai gama mata ba ya bari
kan sai gobe sa had'u, ya kuma nemi number, ba
musu ta fad'a mishi. Sukai sallama Amal na
mishi "bye-bye. Tun da yazo k'wanciya zaro
wayanshi yana duba pic d'in da mai " photo" ya
tura mishi na pretty a waya. D'uk da halamun
bata ma san an d'auka ba, dan sam ba ta da wal
wala sosai,sai ya bada "style", sosai ranar ta
mishi k'yau, shi yasa yace mai hoto d'uk
motsinta ya d'aukar mishi ita. Murmushi yai tare
da shafo wanda takewa Adama murmushi, a
hankali ya furta "Furii pretty". Kawai sai ya raya
ya kira ta ya ji muryarta ko zai samu na bacci.
"Tea" take sha lokacin taga wayanta na d'an wal-
wal. Kofin ta sauke,kan ta kai hannu ta daga,
wayan ta kurawa ido, tasan numbern,sai d'ai ta
k'wanta mata. Saura kad'an ta kat'se ta
daga,shiru tai dan jin ko wacce take zargi
ce.."Assalam Alaiki Furiii...Ido ta lumshe, tare da
saita kanta da sauri,dan har ranta taji sunan,d'uk
da ta gane mai maganar, sai ta basar,''walaikum
salam.. Daga chan yai ajiyar zuciya, muryar Fure
na daga abinda yake son ji a tare da ita.. "Hope
kin gane mey magana? Kamar ta ce" eh, sai kum
tace, "ban gane ba kam.. Murmushi yai, kan ya ju
ya tare da rage karar *TV".Yace "coper Ahmad
Abba Ahmad, (AAA) " Chemistry " "teacher''..
Murmushi tai mai sauti,wanda har ya ji, sosai yau
tana a farin ciki,, cikin nutsuwa da wannan murya
ta pretty kad'ai tace" am sorry Uncle AAA,I
thought koh... Sai kuma tai shiru. Tashi yai
zaune, kan yace"koh wa? Kai ta k'ada, tare da
k'allon sadiya da tai mata kurii da ido. "Ba kowa.
"ka je lafiya? Ajiyar zuciya yai,kan yace"lafiya
lau,ina Amal? Ido ta lumshe, sautin shi na neman
zarar ta,a hankali tace "tana gun Mama. Fira ya
cigaba da mata,kan yai mata sallama kan ta
tsimaye shi zai zo mata da batu in y'an biki sun
watse har gida. By Feenat Ja'afar. 庐NWA.
Feenat.mywapblog.com
9/29/16, 2:20 AM - Queen Safiyyert馃憫: [4/19, 8:11 AM] Feenat Ja'afar 馃鉁嶐煆� :
"JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
13_Wayan take k'allo, sai ta samu kanta da
murmushi, ji tai gaba d'aya ya wanke kanshi a
gunta,tuni taji wani sabon lamarin da yafi na da,a
hankali ta zame ta d'aura kai kan "pillow" tare da
tariyo had'uwar su zuwa yau, fatan yasa yazo
mata