Author : Queen Safiyyert Category : Romance
minti uku
ba ya kara k'allo ta, ta cikin glass d'in ya d'an
rufe ido,bai so ta kaishi bango ba,kawai ya ki
jinin rawar kan nan na Fure ne. A hankali ya kira
sunanta ta bud'e ido, tuni har sunyi ja, d'aurewa
yai yace ta tashi taje ta zauna. A shag'wa6e ta
tashi tana d'an dingisawa, koh zama bata gama
ba aka k'ada, ya tattare kayan shi tare da d'an
k'allon yadda ta d'aura kanta akan desk hawaye
na zubowa. Da sauri ya d'auke kai dan kar su
gane yai waje, ai kamar jira suke sukai kan
Pretty suna lallashi. Har akazo k'wanciya in ta
tuno sai tai k'wafa, ita sam bata ga mey tai ba
da har ya sa ta kneeling. Shima d'ai Uncle
Ahmad d'in yana a d'akinsu dake cikin "staff
quarters" d'in, a ganin shi raini ne zaisa Fure yin
hakan,sai d'ai shi mai tausayi ne, tuno da yadda
take hawaye dazun d'uk sai ya ji ba dad'i. Ihun
y'an makaranta ne da ke "hostel" yasa shi tashi
da sauran y'an d'akin, tun zuwan shi wannan ne
na farko da akai ihun gardi,waje suka fitu,ganin
wasu malamai nayin hanyar hostel d'in yasa suka
bisu,ba kad'an ba yara ke gudu,wasu na fad'uwa,
d'uk anjijji ciwo wasu na kuka,kawai Fure ce ta
fad'o mishi,sai d'ai bai isa fidda ta cikin yawan
daliban ba. Washegari da safe a "area classis"
sai zancen jiyan ake, yana jin lokacin da aka ce
dayawa sunji ciwo,wasu na "dispensary ",kawai
sai ya samu kanshi da leka ajin su Fure,suma
d'ai maganar jiyan suke tayi,suna ganin shi suka
nutsu tare da g'yara zama. Juyawa yai,dan ganin
ba Fure a ajin,sai yai hanyar dispensaryn.
D'ang'walolo,tana k'wance sai wash! take tana
y'arfe hannu ana mata "dressing" d'in kafarta.
Murmushi yai, ganin dan ciwan amma take
wannan wash! d'in. Yana tsaye yaga an zaro
allura,Furen ya k'alla, ai kam ido ta zaro,"Allurar
mey za'a min? Tab! Baya ta ja kan ta mike tsaye,
"nifa na warke malam, na d'aina ma zazzabin,
mai allurar yace" kiyi hakuri kawai ki ju ya, dan
fa sai na miki. Kawai da mamakin shi yaga ta
6are baki tana kuka,kuma ba koh hawaye, dayar
y'ar "mate'' d'insu tace"haba Pretty,allurar? A
masife ta k'allo ta," eh din ina ruwan ki.
Murmushi yai,kan ya k'ada kai ya shiga cikin
"dispensaryn". By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 2:15 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 6_Tana ganin shi ta
juyar da kai tare da d'aina kukan, ya koma gefen
da take, bata nufa ba taji yace "sannu Furera..
Da sauri ta dago,sam batai tsammanin bahaushe
ne ba, yafi mata kama da y'an chan kudu,fari
ne,dan sosai ya fita haske,mai sage siriri,da
tsayin shi,dan ya kere ta da kusan kai uku,da
gani mai hakuri ne, sai d'ai bai d'aukan raini.
Sosai yake da k'warjini, musamman agun y'an
mata. A hankali cikin sigar lallashi yace tai
hakuri a mata,kai ya k'auda, sai ta samu kanta
da d'an daga wa, gefen nashi yake take k'allo,
halamar bai son ganin abin,ido ta lumshe,lokacin
da taji tsinin allurar, "shikenan fa an gama, ido ta
bud'e, tare da sauke rigarta tana k'allon Uncle
Ahmad da har yanzu yaki k'allon ta, magani aka
zuba mata,dispensarern yace gobe ta dawo,
juyowa yai,lokacin da take k'ar6a. Tare suka
fito,tana d'an dingisa K'afa, shi kuma rike da
maganin da k'walin lemon da y'an k'wanarsu
suka kawo mata, mamakin ta yadda ya zamu mai
saukin kai,har aji ya rakata, a bak'in kofa ya
tsaya,tare da kiran Adama tazo ta k'ar6i kayan,
sudai y'an aji da ido suke binshi,sam ba wasa a
fuskar shi bare su tanka,tana zama ta k'allo shi,
hannu ya dago mata yana murmushi, itama sai ta
murmusa,baki sake suke k'allon su har ya juya
ya fita. Da sauri y'an class suka zo jin
gulma,wasu na Sonta yake Allah,harara ta basu,
"wani irin so? Ku fa baku kai. Ina,sukam y'an ajin
har aka tashi suna pretty ta uncle Ahmad. Tun
tana masifa har ta fara binsu da ido. Sai d'ai fa
ana zuwa bacci ta kasa sukuni, dan har yamma
sai da yazo duba ta,harda drinks d'inshi mai
sanyi da cake. Takan yawaita murmushi in ta
tuno shi,wanda ita kam a nata wayon bata san
meye ba.m Sai ya zamo Uncle Ahmad sun d'inke
da Fure sosai,d'uk da bai ce yana son nata
ba,asalima in yana " teaching'' yi yake kamar bai
san kowa ba a ajin,,dama kuma itace "class
captain" ta y'an iska,d'an ita d'uk randa akace ai
''noise maker" ranar take cewa kowa yai surutu
son rai,randa ba'a ce ai ba kuma zata chunkune
kaji aji tsit,tari kai sunan ka ya shiga. "Records"
na exams nasu suke su da uncle Ahmad, suna
karanto mishi ita da Adama,ga nan wata na musu
firfita,har Adama ta gama nata pretty ta fara.
Yadda take fidda lafazin cikin murya mai dad'in
sauraro kai kace tun daga "primary" ta samu
"good foundation'', sosai yake jin muryar ta har
tsakar kanshi, yakan rasa mey yake ji a game da
" pretty" in dai zai tsinkayi muryar ta. Jim
tai,yana jiran ta fad'i "next" tai murmushi,
"Furera muh'd, murmushi yai kan ta fad'a mishi
mark itama tana murmushin, Adama ta zunguri
mai firfita suna gulmar su. A zahiri kowa na son
kowa,amma sun kasa gano hakan,shi d'ai uncle
yasan yana yawan tunanin Pretty, amma sam bai
kawo so ba. K'wance tashi har sun kusa gama
service d'in su,a dalilin uncle Ahmad Fure ta
nutsu sosai,har d'aurin karatun addini yake musu
ita da K'awayenta,da nusar su yanzu sun girma
su daina kaza da kaza,,sosai kamar K'anwar shi
haka yake ji da ita,randa yai k'wanan waje in
bata ganshi ba d'uk sai taji kamar tana jin
zazzabi, d'uk a tunanin ta ba d'an KD bane. Ana
gobe zasu tafi lokacin su Fure na ss3,kuma "
Head girl" Duk tabi tai laushi, a kofar aji suke a
dandamalin a zaune, kowa ya zuba musu na
mujiya,k'allonta yake ba ko kiftawa, ita kam kai
d'uke kamar ta sau kuka, a dan karatun littafin
soyayyarta ta zata sonta uncle d'in yake,ashe ba
haka bane,gashi har yau zai tafi bai furta mata
ba. In d'ai batai k'arya ba ita kan tasan ta rufta a
son shi,murmushi yake,"Furera" kai ta dago,da
dan murmushi a fuskar ta,''ki kula sosai,kinga kun
fara "practical", kiyi karatu ko d'an ki fita da
result mai k'yau. Kai ta k'ada mishi, wayan shi
ne ya k'ada kirar" Blackberry" da murmushi ya
daga kan ya ambaci sunan "Mama" sai ya d'an
tashi ya matsa, sai da ya gama ya dawo
fuskarshi d'auke da murmushi, "Mama na gaida
Furera, murmushi tai kan ta k'ada kai," ina
amsawa. Har address d'in Fure ya k'ar6a, da
alkawarin zai kawo mata ziyara har gida in sun
gama makaranta. K'warai ta d'aure ganin batai
kuka a gaban shi ba, sai d'ai yana tafiya ta k'ar6i
"pass" tai ''Hostel". Kuka take wanda da
biyu,itama d'ai ta zurma d yawa, amma irin su
Uncle Ahmad tasan ba ajin su bane,wai k'warya
tabi k'warya, yadda yake da aji da k'yau tasan
yafi k'arfin ta, zuciya kawai ke yaudarar ta. Tun
tana damuwa da son Uncle Ahmad har ta jingine
shi ta hau karatun ta. In har da rabon zasu gana
kila ta ganshi. Sun gama "exams" kowa ya tafi
gida da k'ewar juna da dunbin k'yaututtukan
ta,sa6anin Adama da suke kusan unguwa d'aya
da Pretty. K'allon Fure Umman su take,d'uk ta
rame kibar nan ta dawo y'ar chas da ita,"har yau
ina mamakin ramar nan taki Furera,ko A'i batai
rabin ramarki ba data gama makaranta.
Murmushi tai,kan tace"Umma karatu ne, zai
maida kiba ta har da k'ari, kai ta k'ada, sai dai
har yau tana mamakin yadda Fure ta nutsu gaba
d'aya, ta zama wata irin sassanya,a zaton ta d'uk
makarantar ne, sai d'ai gashi har sun shafe wata
1 da gama makaranta Fure na yadda take,kawai
sai ta bada girma ne ya shigi Fure. Abu d'aya ke
ci mata tuwo a k'warya yadda shiru ba labarin
Uncle Ahmad, ga yadda tsabar tunanin shi ke
hanata sukuni,takanji zuciyarta na wani iri in ta
tuno shi, gashi ko numbern shi bata rike ba,
dabara ce ta fad'o mata,fatan ta Allah sa Abban
su yai saving numbern, dan tana yawaita kiran
shi da ita. By Feenat Ja'afar.
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Apr 14
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 7_Da dare Abba ya
dawo a wajen aiki ta d'au wayan da nufin zata
kira k'awaye, d'akinsu ta kule,kan ta hau duba
"contact" "Fure schl" taga sunan wani contact,
tasan kenan numbern da take kiran Abba dashi
ne a makaranta, gabanta na fad'uwa tasa
numbern a "private" kan tai "dailing'' g'yara
k'wanciya tai,tana sauraron yadda wayan ke
"ringing" bugun zuciyarta na k'aruwa, sai da ta
kusa yankewa har ta sadddak'ar ta sinkayi
sallamar shi da muryar da ke sata cikin nutsuwa.
Ido ta lumshe tana sauke numfashi da sauri,
hannu tasa a d'ai-d'ai zuciyarta dake mata
barazanar fitowa fili. "Da wa nake magana pls?
Sai a sannan ta bud'e ido,tama manta da ya
d'auka,sai da ya kara sallama kamin a hankali ta
zare wayan a k'unnenta tana hawaye ta kashe.
"Ashe ita kad'ai ma ta damu dashi? Kila ma shi
ya manta kashin wata Fure a wani gu, zatan ta
baya ma kasar, dan yasha sanarta "England" zai
je masters, ashe yana kasar a garin amma bai ko
neme ta ba har tsawan wannan lokacin... "Fure
lafiya? Umma ce ta katse ta,da sauri ta goge
hawayen tare da k'ak'alo murmushi, "ba komai
Umma,, da mamaki Umman tace "ba komai ki ke
kuka? Jin dad'i komai? Kai ta k'ada,tare da
kawar da zancen da cewa "yaushe Aisha zata
dawo Umma? Zama Umman tai,kan tace" a satin
nan zaki ganta, ai tasha hutu kusan wata biyu
kenan,amma Furera tun dawowar ki na fuskanci
kin sauya, kin zama shiru-shiru, kodai ba ki lafiya
ne? Kai ta k'ada kan a hankali ta zame ta
k'wanta cinyar Umman, "Umma ba komai,
makaranta make ma son shiga Umma. Kai ta
k'ada mata," yana da k'yau, Allah shige
gaba,amma sai kin tsaida tunaninki waje d'aya,
gashi har yau kin kasa maida jikin ki,sai ma wata
ramar da naga kina yi. Kai ta k'ada mata,kan tai
ko'k'arin had'iye kukan ta. Gaba d'aya ta tattara
Uncle Ahmad ta jingine shi gefe,har numbern shi
ta ma goge,dan in d'ai ta motso mata in ba
muryar shi taji ba bata samun sa'ida, yanzu kam
Alhamdulillah, ta samu ta fara manta so,sai d'ai
"memoryn' baya yana a K'wak'walwar ta. Yanzu
karatun ta kawai tasa a gaba,a bangaren
''catering''. Yaya Suleiman ya kamalla karatun shi
har an bashi aiki,yanzu burin shi aure,sai dai har
yau bama budurwar,babban burinshi kamin na
yanzu bai wuce ya tara kud'i ya tada ginin Abban
shi ba,dan sosai yake da murad'in iyayenshi suyi
nasu su huta da haya. InshaAllahu zaya hutar da
Abba aikin makanikanci bada jimawa ba,yai
alkawarin ji da iyayen su da y'an uwanshi dad'i
na duniya in har Allah ya bud'a. Albashin shi na
farko Abba da Umma ya direwa,a ganinshi su yafi
kamata su fara ci kamin kanshi, musamman
Abban su mai arzikin zuci,ya sani da Abban su
mai jajircewa ne mai kuma nema da guminsa,shi
yasa yake kara alfari dashi yake kuma neman
koyi da dabi'un shi. Zaune suke da
yamma,dawowar shi a aiki kenan suna zaune a
katuwar darduma a tsakar gida shida Umma da
sauran k'annen shi,yakan yi nishadi in ya ji shi
cikin gida haka da d'uk Familyn shi,Abba kawai
ya rage baya a cikin su,tad'in bikin Aisha suke da
Umma, yayinda Fure ke zaune tana taya su
Hassan da Hussaini "Assignment",sai d'ai jefi-jefi
yayan nasu na sako ta cikin zancen. Ka gansu
g'wanin ban sha'awa, gidan su ba k'yara bare
hancini, kowa yana nan-nan da juna. Adama tai
sallama, cike da murnar ganin K'awarta ta shigo
gidan. Wani ihu da suka zuba kan Furen ta tashi
suka ruk'unk'umo juna, daga Umma har yayan
baki suka saka suna k'allon su,toh g'wara Umma
dama tasan halin Adama da Fure,amma shi da
mamaki kawai yake k'allon su musamman
Adama, sai da suka gama rawar kansu tukun
cikin kunya ta gaida Umma,kan ta sauke
k'allonta akan Ya Suleiman,da halamun kowa d'ai
yai katari da " soul mate " d'in shi, dan kasa tai
da kai,lokacin da ta gano waye shi,shikam
k'allonta kawai yake da murmushi,kai duk'e tace
"ina yini Ya Suleiman, Fure ce ta katse shi,"
Adama ce fa Yaya,ta girma koh? Murmushi yai
kan ya amsa,"ai sam ban gane Adama
ba,"2years" d'uk sun kara girma,koh Umma?
Murmushi ita d'ai Umma tai,da halamun ta gano
bak'in zaren. By Feenat Ja'afar.
Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Apr 14
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 8_D'aki suka shige,
suna firar yaushe gamo, "kawai ki kaje kikai
zamanki a Abuja abinki? Murmushi tai, kan ta
ware "pashminan" kanta, "k'awata Abuja tayi a
rayuwa, ke! Bari kawai, Allah kamar kar na dawo,
naci fa na k'wanta, hatta kayana wanken ake.
Hannu ta bata suka tafa tana "shege Ada,kinyi
k'yau ke kin ganki? " ke d'ai bari, zama ta g'yara,
"kai k'awata yayan kun nan fa Allah sai had'uwa
yake kara yi, d'uk yafi y'an gidan nan k'yau fa..
Dariya ta tuntsire mata dashi, kan ta bata suka
tafa, " dad'ina da k'awata ba fulako,ki ce munyi
kasuwa? Hannu ta kai bak'inta halamar tai a
hankali,"Allah dama ranar yace nai mishi
budurwa a unguwar nan,sai kuma naga shima
kamar ya zurma. Wasa-wasa d'ai zance ya
tabbata tsakanin Adama da Ya Suleiman, har
magana taje gidan su Ada, sosai ba wanda yakai
Fure son wannan had'i, sai kuma su da suka
k'ulla abunsu. Biki kam ya karato, d'uk da yazo a
lokacin da Fure ke shirin y'in Exams a school.
Tafe suke ita da Aisha da k'awayenta su biyu
daga saloon,ganan g'wagg'waran su a leda da
aka nad'a musu, k'awayen suka tsaida 'Taxi"
suna sanar da Aisha sai goben, sauri suke, ganan
magriba ta wuce amma hanya d'uk "go slow", sai
sunyi kamar zasu t'sallaka sai Fure ta
r'unkumota har wata motar ta taho, t'saki Aisha
tai," wallahi kamar tashin k'auye kekam, da tuni
mun wuce sai wani rirrike ni kike. "A ke,rai d'aya
ne, a yadda kowa yake saurin nan muje wucewa
da garaje kawai sui ciki damu? Kai Aisha Amarya
ta k'ada," toh ni kam zan t'sallaka, dan kinsan
Abba in ya dawo ya tarar bamu dawo ba fad'a
zai,in yaso randa mutane suka d'auke K'afa sai
kizo. Hijab d'inta ta rike,"wallahi baki isa ba.
Yanzun kam mota suna d'an nesa, hannun Furen
ta kama"ki biyo ni toh yanzun. Da d'an gudunta
Aisha tai gaba,sai jin Fure ta zame hannunta tai,
"tsaya ledar mu, ina, A'i har ta wuce,da sauri ta
ju ya da nifin ta t'sallaka t'saut'sayi, ashe wata
jar CRV ta kuts'o,da gani kuma sauri su ma suke,
gashi tazo t'sakiyar k'walta,ga ihun Aisha na tai
gudu ta karaso. Ga ihun "horn" din motar,d'uk sai
ta kasa gaba ta kasa baya,suka had'u da tsoron
k'walta suka rikita Fure,ido ta rintse,tare da
sakar ledar kayan a kasa ta rufe k'unnenta da
hannunta d'uk biyu, tasan ba makawa sai motar
nan tai ciki da ita. Jin shiru ba ai ciki da ita ba
saima hasken motar da ya dalle mata ido da dan
jin hayaniya yasa a hankali ta bud'e ido jiki na
ka'r-ka'rwa. "Da ke! ke da asara wallahi bamu
ba, so nai a yabimin ta kanki tunda kin gaji da
duniyar shi kuma ya tsaya.. Babbar mace ce,sai
d'ai da ka ganta zaka san isassiya ce mai ji da
kanta, k'allo d'aya zaka mata kasan naira na inda
take, fara ce mai kiba ba chan ba. Sam ita bama
ta lafiyar Furen take ba. Masifa take ma Fure
kamar ta rufeta da duka,gashi ita Furen ta tsaya
kem! Kamar an dasata a gun,har yanzu jikinta na
ka'r karwa, Aisha data karaso ita kad'ai ke bawa
Hajiyan hakuri,tare da ko'k'arin janye Fure. Wasu
da suka gaji suka zame bi ta gefe. Haka take ga
wanda yake " driving ",tunda ya taka birki yake
k'allon wacce yaso ya bige, kamar wani wawa ya
sau baki yana k'allon Fure ba ko kiftawa, ganin
suna neman tafiya yasa da sauri ya 6alle murfin
mota yai gunsu, Hajiyan ta zata k'addamar musu
zai yi sai taja baya,yace"Momy shiga mota in zo
yanzu. Sai da yaga ta shiga mota yai gunsu
Furen," Aisha. Da sauri Aisha ta dago,wanda
Fure itama tai saurin dagowa lokacin da zata
d'au ledar, "a pharmacy? Ba d'ai kai ne a motar
ba? Idon shi akan Fure yake yana murmushi,
yayin da itama Furen ta zuba mai ido ba koh
kiftawa. Tabbas itace,ya fad'a a zuciyar shi,sai
da Aisha ta kara magana kan ya juyo gare ta,
"kuyi hakuri amaryar mu,sam ban zata ku bane,
kan Fure ya dawo, " Furera da fatan bakiji ciwo
ba?....Momy ce ta katse shi da cewa "Kai dare
fa na kara mana a titi, kabar wannan yaran dama
y'an titin ne daga gani mu tafi. Wai waya wa
yai," toh Mom,coming. "Ku kara hakuri pls
Amarya, ya dubi Fure,da itama shi take k'allo ba
ko kiftawa, Aisha ma da mamakin ina yasan Fure
take, sai kuma mamakin uwar shi bala'e'iya,
Tana nan a haka har sukai sallama amma ita ta
kasa furta komai. Har ya shiga mota shima yana
waiwayen ta. Ko da suka je gida su Umma suna
ta tambayar su ina suka tsaya har haka? Furen
Aishan ta k'alla, "Umma amare ne sukai yawa a
garin,ga gidan mai kunshi ma acike. ''Toh ita
Furen mey ya same ta? Koh yunwar ce? Da sauri
Aisha ta k'ada kai, dan tasan in d'ai ta sanar da
Umma abinda ya faru yanzu zata rikice. Juyi
kawai take a katifa, har yanzun ta kasa
t'ant'ance murna take ko akasin haka? Ga Aisha
ta dameta da tambayar ina Ahmad yasan ta? Kai
kawai ta k'ada mata, kan tace itama bata sani
ba. Juyi ta kara yi,sai ga hawayen da tun dazu
take bidar su zubo sunki sai yanzun. "Dama
uncle Ahmad na garin nan har yanzu? Lalle
yanzu ta kara tabbatar da ihu kawai take bayan
hari, tunda har address ta bashi in yaso zai neme
ta. Haka ta lulluba tai mai isarta kan ta sa a
ranta indai tana da zuciya toh tabar tuna uncle
Ahmad. Suma chan su Momy tun a mota take ta
kara zagin su Fure,shi d'ai yai shiru,tunani ne fal
ranshi har suka zo gida. K'wance yake yana
k'allon" A.Cn d'akin nashi, kawai yanayin Fure
yake tuno wa, ashe Allah zai sa yaga Fure a
fad'in garin nan bayan rasa address d'inta da
wayar shi? Murmushi yai,a hankali ya
furta"Pretty" sai kuma ya gintse. Tabbas Fure na
matukar kama da Aisha,sannan sosai yasan
yayan Aishan a A.B.U,toh meye had'in su da
Fure? Dan tun dawowar Suleiman a dalilin auren
Aisha sau biyu yana zuwa gidan su,amma bai
ta6a ganin Fure ba... Gaban shi ne ya fad'i
sakamakon tunawa da zanchan su na jiya da
Suleiman d'in, kan wacce zai aura makarantar da
yai service tayi,kuma shekarun d'aya.. Kar fa ace
Furera ce wacca Suleiman zai aura? Kila koh
y'an uwa ne shi yasa suke kama... Cewar wata
zuciyar. Tashi yai zaune,dan tuno da g'yaran
amaren da suka sha ga uban lalle da kayan
g'wag'gwaro da suka fad'i kasa. By Feenat
Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com
9/29/16, 2:17 AM - Queen Safiyyert馃憫: [4/16, 12:30 PM] Feenat Ja'afar: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
9_Washegari "10am" a kofar gidan su Aisha ta
mai,a kofa ya same su, da halamun daga wani
waje suka dawo,tsaye suke da Ya Suleiman suna
ta nishadin su da dariya,tun a nesa kawai ya
bada hasashen shi ya zama gaskiya,toh amma
ita Furen wace tasu? Ina ne gidan su?
Tun tsayuwar shi Fure ta tsagaita dariyarta tana
dub'en motar,tabbas ta jiya ce, k'allonta Yayan
nasu yai,kan ya k'alli inda take k'allo, tuni fara'ar
shi ta karu tare da furta"A'a, AAA.. Kan yai
wajen shi,Aisha ma ta fara fara'a, ita kam kasa
tai da kai,dan ganin suna yin wajen su da Uncle
Ahmad d'in.
Idon shi na kanta,ganin yadda Yayan nasu ya
shiga t'sakiyar su ita da Aisha,da fara'a suka
gaisa da Aishan,kan itama tace"Uncle ina
k'wana.. Damm! Ya ji zuciyar shi ta buga,a
hankali ya amsa,tare da d'auke kai a kanta,
shikenan Pretty ta fita a rabon shi? Ido ya dan
rintse,"kai zurfin ciki bai ba a rayuwa, gashi yana
k'allo k'wado zai mishi K'afa.
Ya Suleiman ya k'allo shi, "nasan dama