Author : Queen Safiyyert Category : Romance
samu
farin ciki, mama tana ta sa mata albarka akan
abincin "weekend" na kullum. Abba da yazo
bangaren kamar kullum weekend sai ya tarar
dasu Furen, shima yaba mata yake akan ko'k'arin
iya girki dasu duk k'wana uku na weekend, sosai
Fure ta shiga ranshi, gasu da ladabi ita y'ar
uwarta.. Ka'f sirikan gidan daga kansu ne kawai
masu sanin ya kamata. Da dare ta biya dubo
Maryam da cikinta ya isa haihuwa. Ba ai k'wana
uku ba k'wa ta haihu,ta samu babynta namiji. Da
murna tai d'aki dan sanar da AAA, sai gashi
shima yana shirin sanarta har suna g'ware,
"Maryam ta sauka... Sai suka sa dariya jin sun
had'a baki gun albishir. Sosai Muh'd ke d'aukin
zuwan babyn nan, yayin da Hassana ke ta cika
dan wai ita yara mata ta haifa har uku,gashi har
an fara kiranta da "UWAR MATA.. Amma ga
amaryar shi tana zuwa har ya bata namiji a wata
goma.. Ranar Maryam tai dariya kamar ta mutu,
kai rashin ilimin Addini ne ma masifa ce, sam
yanzu ita gani take Hassana ta kunce. Suna a
parlour ana g'yara baby Hassana ta fito,gobe
suna fir taki zaman parlour, jin yadda ake ta
shigo da abubuwa. Fatee da Fure suka bita da
k'allo, sai kunshe dariya Fatee take,dan ganin
yadda Hassana ke hararar baby da uwar shi. Da
gan gan Fatee ta fara "Accountant" ba, yaro mai
goshi, sosai kazo da azziki. Baki ta ta6e, kan
cikin haukarta ta fara ma Jidda dake kusanta
"Jidda y'ar gatan Abba koh? Sai Jidda ta k'ada
kai, cikin zance ta kara da cewa, "Dad'in abin na
haifa, ba o o bace, nasan yau da Jidda ta iya
mota,nasan da dadyn Jidda ya mallaka mata
ita... Fatee ta k'alli Maryam, kawai bata nufa ba
sai ji tai sun sau mata dariya harda shewa da
tafawa, kamar wanda suka had'a baki wajen
fad'in "wa yaga takai takai,,cikin dariyar mugunta
Maryam tace "uwar Jiddan ma tai ko'k'arin
mallakar ta kamin nan ita Jiddan... "Wallahi ban
so ba,da tuni na mallaka.. Baki Fatee ta ta6e,kan
tace su shiga ciki kawai, ita d'ai Fure nata ido.
By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 2:50 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 41_Suna ya kayatar,
sosai maijego ta fito da yayarta, baby yaci sunan
Abba,an ka'r naira sosai, da yamma kamar kowa
aka kawo kayan maijego da baby na mey suna su
Aunty Jidda. Har kasa Fure ta zamo ta gaida su,
Maryam tana daga gado ta gaida su sam ba
fuska. Cikin fara'a suka amsa, Ak'wati biyu Aka
sheko musu, komai na k'arya da nuna su sune,
ganan wata katuwar leda da tarikicen su
pampers da da sauran su. Fure da Ada da Fatee
na duba kaya Maryam tai waje gun amsa kira.
Huwaila da ke kusan su Fure dake ganin kaya
cike da izgili ta k'allo Fure, "tunda y'ar uwa ta
kot'se sai a zuciya bana a diba.. Chak Maryam
ta t'saya wacce shigowarta kenan da masu duba
kaya, a fusace Maryam ta karaso, "Sa'a kike
ko... Da azama Fure ta tashi ta toshe mata baki,
sai ta girgiza mata kai. Sai d'ai kan ta farga har
Fatee taja t'saki. "Haihuwa ai kai inda ake
nemanta itace haihuwa a gani na.. In ta wuce
wannan, wallahi na yarda a kiramu da JUYA... A
wulakance Huwailan ta k'allo ta, "ke kuma a
suwa? Wai kare da gudun layya.. Mtsww, "Allah
ya fissheni zama JUYA. Dariya Fatee tai,kan tace
''oho d'ai, dan dake da babu agun mijin d'uk d'aya
wai karuwa ta haifo shege. Tuni ta tunzura
ta,har ta soma zagege su Aunty Maryam da
Jidda suka shigo jin ba'asi. D'aya ta fad'a sai
Fatee ta mayar mata goma, ita d'ai Fure ta
damke bak'in Maryam gam,dan yanzu tasan sai
ai baram barama ranar suna. "Ki taso toh mu tafi
ke Huwaila, banga t'saran yinki agun nan ba.
Cewar Aunty Jidda. Da t'saki Fatee ta bisu, tana
fad'in "a sauka da nauyi. K'allonta Aunty Jidda
tai,kan ta nuno, "ki shiga taitayinki dani,ba
JUYAR bace ita? Ta fad'a... Fatee tace "oho d'ai,
nima d'ai na fad'a, ka haihu inda ake mararin ta
ba inda aka maishe ka JUYA tafi ka mukami ba...
Janta Huwaila tai, tana "Aunty bar mahaukaciya,
ba laifinta bane, da k'arfi Fatee tace "Dawan'au
ce ma ni. Sai da ta tabbatar sun fita tukun ta sau
bak'in Maryam, kusan kowa na parlour, sai su
Ummi da kawayenta, suma ana farawa sukai
waje,dan taki jinin taga ana ciwa Fure fuska a
gabanta, dan d'uk yayunta ne. "Aunty Fatee kin
mun d'ai-d'ai wallahi, cewar Maryam, "sam Ya
Furera tamkar sun dat'se mata baki haka take, a
kusa da Fatee Fure ta zauna,cikin marairaita
tace"Fatee Aunty Jidda ce fa? Yayar su AAA..
Baki ta ta6e, "ke kika san wannan, ai d'uk tsohon
da baiji kunyar hawa Jaki ba,toh k'wa Jaki ba ya
ji kunyar nana shi kasa ba. Adama tace "sosai
kuwa. Sai ga nan Hassana ansha d'auri tazo, "ina
tajin hayaniya,da fatan lafiya? Harara Hassana da
Maryam suka k'wad'a mata, kan Maryam tace
"ba'a sani ba uwar gulma, Fatee tace
"Shishiganatu ba. Jiki sali6e Hassana ta juya
Allah sarki ta koma. Ita d'ai Fure sam bataji dad'i
ba, ta kuma sanarsu in dan ma ita sukai toh
wallahi basu burgeta ba, nan suka chake ta,kan
wai tsoron su take, "shi yasa kowa ke cin kashi
akan ki ai. Cewar Fatee. Aisha kam tai shiru, dan
sam ta t'sani hayaniya. Sai ta kama hannun Fure
suka fita su Fatee na kiran matsorata. Aisha ta
k'allo Fure dake kuka acikin motar da suka shiga.
"Ki kara hakuri Furera, wataran sai labari, ki
d'aina barin k'ananan maganganun su suna miki
tasiri, ak'wai Allah, ki sa ranki a inuwa, Allah yai
alkawari ga d'uk bawanshi ba wa d'uk wani abu
da ya tauye shi aka goranta mishi shi, mat'sawar
k'wa baka samu ba, toh ka d'auka wannan abun
ba alkairi bane gare ka da rayuwar ka. "Kar kisa
a rai,g'wada ki rama da ki barshi a ciki yazo yai
miki illah. Kai ta k'ada mata, "wallahi ban ta6a
da na sani akan hukuncin Allah ba sis, abu d'aya
na sani, d'uk ranar da hakan ta faru nakan ke6e
nai ta kuka,in na gama na share, ban kuma ta6a
fidda rai daga samun ra6o sam, sai d'ai bana iya
d'aure gorin jama'a, musamman dangin su AAA.
Sosai ta lallasheta, har sai da tace ta g'yara
fuskarta kamar ma ba ai komai ba, sannan kar ta
cewa su Maryam komai. Ko da suka koma k'ida
suka ji yana tashi a d'akin Maryam, suna shiga
Fatee da Adama na ta rawa suna bin kid'an Ladi
mai kid'an k'warya kamar basu ba. Murmushi
tai,sosai Fatee y'ar hau ce ita da Ada da
Maryam, sam ba zaka d'auka ba y'an uwan juna
bane. Suna ganinta Fatee ta kamo hannunta wai
ta shigo fili, ga nan y'arta sai k'yak'yala mata
dariya take daga zaune. Har gida karan nan ma
Momy tazo ita da Aunty Jidda suka sauke mata
ruwan bala'i. Lokacin AAA na d'aki yau tun safe
yake k'wance ciwan kai. Sama-sama yake jin
hayaniya, a hankali ya daga window, muryar
Momy da Jidda yake ji suna sauke wa Prettyn
shi tana ta fad'in suyi hakuri. T'sam yai bai ya
koh k'wak'waran mot'si, ya dace ya kawo
karshen kiyayyar da su Momy ke ma Furii,amma
ta ina? Tas Ummi ke sanarshi d'ukkan abinda ake
ma Fure kawo da gorin haihuwa. Lekawa ya
karayi, ga nan FURIIN ta duk'ar da kai kasa,a
ranshi yana kila ma kuka take... Sai ga nan
shima idonshi ya cicciko jin Momy na fad'in "ki yi
zuciya ki fita sahun JUYA toh.. Amma dole su
fad'a miki. Itama fit'sarun Maryam zani har gidan
tunda a dalilinta komai a afku,tun shigowar ku
dangin mu aka fara t'siya,saboda an yayimo
dangin t'siyar. Ya'yan makaniken mota.... Da
sauri ya sau labulen, tare da komawa kan gado,
bazai iya d'aukar jin wannan kalaman ga Furii
ba,tuni ya ji ciwan kai ya karu, shin Ina wai
Tauhidin su Momy yaje ne? Wannan tambayar
yau ita tazo kanshi, sai d'ai har suka gama
hayaniyar su bai samo amsa ba. By Feenat
Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com
9/29/16, 2:51 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 42_Tamkar marainiya
haka ta takure kanta a parlour tana kuka mara
sauti,sai da tai mai isarta ta kad'e tai d'aki cikin
sand'a, a zaton ta har yanzun bacci yake,dan
tasan da idonshi biyu da yanzu ya taso gaida su
Momy. A.c ta rage mishi, kan a hankali g'yara
mishi bargo tare da ta6a kanshi, da dan sauri ta
wanke fuska gudun ka'r ya gane tai kuka, sai ta
fita kitchen. Da k'allo ya bita yana mai tausayin
ta had'i da karin kaunarta. Tabbas Furii tai sanyi,
sanyin ma na ban mamaki,dan shi zaya bada
wace ce Fure? Amma yanzun tai hakuri tana ta
cin jarabawar rayuwa. Har bazai tuna rana ta
karshe da tai pt a gidan ba,gaba d'aya ta
faiwalawa Allah, tai hakuri, amma ya rasa mey
yasa mutane suka gaza hakurin da tai, wace irin
zamani ne yanzu Allah ya kawo mu? Bargo kawai
ya cire yai tagumi. Sai ana kiran Magriba tazo
tashin shi, sai ta tarar ya ma tashin, sai ta koma
kitchen. Yaga har anci abinci bata ce mishi kom
ba, dare yai sosai, sai ma dan tad'in da take
mishi tana "massaging'' d'in kanshi a hankali.
Yasan kawai d'aurewa tai kamar kullum dan
kwanciyar hankalin shi. "Furii...a hankali ta
amsa,tana cigaba da abinda take, sai ya ruko
hannun d'uka tare da zago da ita suna k'allon
juna,tabbas yasan d'auriya take, amma har
yanzun bata dawo d'ai-d'ai ba. Kasa tai da
kai,ganin yadda ya zuba mata ido, hannayen su
ya rint'se, tare da g'yara zama kan gadon. "Are
you Ok?.. Kai ta dago tare da saurin k'ak'alo
murmushi, sai ta k'ada kai, wato ba d'ai zata
fad'a ba? Sai ya sau ajiyar zuciya, ya fara abin
da yasan d'uk rashin walwalarta takan dawo farin
ciki. Ido kawai ta zuba mishi dan jin kalaman
kaunar shi gare ta. Bata nufa ba sai ga hawayen
dad'i ya zubo, cikin sauri ta isa gareshi ta lafe
tana murmushi, a hankali taji komai na warewa
har ta dawo cikin nutsuwar ta. Tasan in da AAA,
sam ba ita ba k'wanan bak'in ciki, Son shi kuwa,a
ganinta zai iya mantar ta d'uk wani gi6i da ya
tare mata gaba.. Fatan ta yasa kaunarshi ta
d'aure, dan shi kad'ai ke samota ko ta k'auce.
Zaune suke a parlour suna firar duniya, ta tasa
kanta da cinyarshi a kasan lallausan darduma.
Ag'waluma ke a hannunta d'aya, yayinda d'ayan
ta rike lollypop,jin yai shiru tana ta zuba yanzun
yasa ta k'allo fuskarshi. Kawai ya tasa ta gaba
kamar wata TV da murmushi yana k'allon yadda
take kai alawar tana zance. Sai kai alawar bak'in
shi, ba musu ya k'ar6a. Da hannunta take bashi
itama ya bata. Ta kawo hannu zata bashi taji ya
rike, sai ta k'alleshi, y'atsunta yake dubawa cikin
farcen,sai yai dan shiru. "Lafiya?.. Kai ya k'ada
mata, sai ya tada zaune,duben ta ya fara, d'uk
da ba bangaren shi bane, t'sam yai yana tunani,
ita d'ai Fure sai K'allonshi take,ganin ya sauke
idonshi kan rigarta. Sai ya k'ada kai, "yau period
naki k'wana nawa ya wuce? Baki sake take
K'allonshi, dan abinda bai ta6a mata ba kenan.
"K'wana shida,lafiya? Murmushi yai, kan yace
"yana kaiwa haka dama? Sai tai jim,kan ta k'ada
kai, ''sai d'ai ya wuce da biyu ko uku.
"K'wadayinki na k'wana niyun nan fa? Kai ta
lang'wa6e, "dama ina yi ai,musamman in na kusa
farawa. Hannun ya kai inda yake k'allo, "nan fa?
Su ma haka suke? Sai ta dan harareshi, "sosai
sukanyi suma in zanyi.. Lafiya? Tafin hannunta
ya shafa yana k'allo, sai ya kai hannu gemunshi
yana shafawa tare da mata wani k'allo.. "Ke ma
fa kin sauya a um um... Bori ta fara,ganin yadda
yake ta mata t'siya, dariya yai, sai yace "ina
zuwa ke d'ai. Sai ya tashi yai d'akin kayanshi na
tarkashen aikinshi. Tunani take, itama fa tana
dan jin sauyi a tare da ita,d'uk abubuwan nan da
take k'wadayi yanzun, ba su take ba in period ne,
sannan... K'allonshi tai ganin yazo da pt da abin
da wani abu, a dirare take K'allonshi, anya yau
mutumin lafiyar shi kuwa? Duk sai wani fara'a
yake,hannunta ya kamo,sai ta tsura mishi ido,
"meye wanchan?.. Da sauri ta juya inda ya nuna,
"ahh..tace da sauri,jin an soka mata wani abu a
yat'sa,da sauri ta juyo dan jin zafi, tana ganin jini
ta hau kukan baci,hakuri yake bata, kan ko yace
ta t'saya yasan ba zatai ba. Baki ta zumbura,
harda dan hawayen karya, yana sakar hannun ta
hau yarfewa cikin lang'wai, sai yai murmushi ya
k'ada kai, tukun ya hau abinda zai, da kamar
minti biyar fara'ar fuskarshi ta karu, yayinda Fure
take K'allonshi tana dan yarfe hannu. Bata nufa
ba taji ya ruk'unk'umota har suna yin kasan
carpet, "I knew it.. Ciki fa, Allah Pretty...
K'wak'waran mot'si ta kasa,baki sake take
K'allonshi, kan a hankali ta furta "ciki?.. Kai ya
k'ada mata, "sosai, tashi muje lab, dagota yai,
kawai d'uk sai ta zama wata doluwa, da ido
kawai take binshi ganin irin bak'in da yake ta
washe wa. A lab ana ta yi da Fure, da k'yar ta
sa kanta a jikin shi kan aka sa syringe aka zuki
jini, y'an wajen sai dariya suke musu, ganin
yadda yasa cotton yana goge mata gun harda
hurawa yana fad'in sorry,ya rasa meye a allura
da Fure take kinta? Tuni sai ya tuna mishi da
wani lokaci achan baya.. Basu jima ba aka fito
da "result". Kad'an ya rage ya dagata sama ta ja
baya tana k'allon y'an cikin "reception" d'in, d'uk
sai taji kunya, Hannunta ya kama sukai
waje,amma bai iya jurewa ba sai da rungumota
cikin murna,tayashi kawai take, kan a hankali ta
k'ar6i result d'in, ganin abin da ke jiki yasa ta
kafawa papern ido ba ko kiftawa. A hankali ta
dago da dub'enta gare shi, ta kasa furta komai,
kai ya k'ada mata yana shafa cikin. Tuni hawaye
ya cika idon ta, "ciki?... Bata nufa ba taji ta fara
jika pepern da hawaye, janyota yai yana "oh no
Furii...murna za kiyi,tana shiga jikin shi ta fashe
da kukan dad'i, ikon Allah, Fure ta ciwo
POSITIVE. By Feenat Ja'afar.
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 May 2
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 43_Dak'yar ta saisaita
ganin wasu za su nufi lab d'in, hawaye ya hau
goge mata, tai kukanta yasan na dad'i ne, ko ba
komai yasan farin cikin FURIIN shi yazo. Allah ya
yi,Alhamdulillah itace kalmarta ta kullum a gun
Allah,domin ya mata gata masu yawa,shi yasa
zai g'wada imaninta gare shi. Tuni ta hau istigfar
bisa kukanta da tai tayi a chan baya. Jiyan nan
ta gama mishi maganar su d'akko Amal,kuma yai
murna. Tafe suke yana ta d'an turo ciki da kama
k'ugu tana mishi murmushi, sai ganan wata mata
da tsohon cikinta, kawai sai ta maka mishi
harara, da sauri ya d'ai d'ai ta, dariya Fure ta
hau, sai tabi matar da k'allo,ko ta zata ta da ita
yake ne oho. Suna zuwa gida ya d'akko ta a
hannu kamar wata Baby, Baba mai gadi ya
girgiza kai yai murmushi, sosai suke burge shi,
dan gidan su babu hayaniya. A gado ya direta
suna dariya,kawai sai ya t'saya k'allonta daga
k'wancen, sai tai murmushi tare da miko mishi
d'uk hannunta halamar yazo gare ta, ba musu
kuwa ya taho,d'uk sai tai mishi dabaibayi cikin
hawaye. Fatee ta fesawa, kan su Adda suka ji
bayani, alkawari tace ya mata, kan dan Allah kar
kowa ya ji in ya wuce Mama, tana son kawai ya
fito ne,za su fi dauk'in shi. Kai ya k'ada, yasan
tana son ma wa jama'a ba zata ne, kuma
InshaAlllah ba mai ji sai d'ai in ya fito su ga. "Kai
k'awata nai murna wallahi har ba iyaka, gani nai
bazan iya k'wana ba sai nazo ganin ki. Murmushi
tai kan tai gefe da kai. Hannunta Fatee ta kama,
"ki min maganin t'sagerun dangin Ahmad d'in nan
dan Allah... Ki rama abinda sukai miki,wallahi ki
hana ko wacce t'sageriyar babyn ki ko k'ya huce
takaicin baya. Kai ta k'ada tana k'allonta, "sis
Fatee da k'yar ne, kowa yai nagari dan kansa,
abu d'aya na sani,shine ba mai ji bare gani, sai
d'ai dake kinsan d'an duma ne. "Hana su d'aukar
D'ana bazai iya hucen takaici na ba, asalima
Batool, nai alkawarin d'uk wanda baizo ya ga
D'ana ba zan kai mishi har gida. Kai Fatee ta
k'ada, "lalle kina da hakuri, tab, wallahi ba wanda
ya isa nai mishi haka. Murmushi kawai tai. Sai
d'ai a daren fure ciki ya shiga 5 weeks ta soma
matsala,tamkar an jangamo ta. Washegari taje
ganin likita,sai taya AAA murna yake,kan ya bata
magunguna kan in ya cika 3 month tazo yai mata
"scanning". Tun daga wannan rana Fure ta dage
da godiya ga Allah da kuma gode mishi, sosai
take wahala da cikin,d'uk ta rame tai fari abunta,
dole wacce bata so aka kawo mata, wato y'ar
aiki. D'ai-d'ai da abinci ta d'aina yi, sai d'ai
kullum daga restaurant d'inta a kawo wa Baba
maigadi da mai gidan,ita kam sai d'ai Umma ta
dafo mata tuwan hat'si,shi kad'ai ke shiga, mama
kawai ta sani, shi yasa bata rabo da aiko mata
kayan makulashe, koh ta aiko Ummi tai mata
k'wana biyu. Har gida Mama tazo ta duba ta,tare
da mata adu'ar Allah inganta. Ba wanda yasan
da jinyarta a gidan sai su biyu da Ummi,sai Abba
da ya ga an d'aina kawo mishi "delicious" na
Fure. Ita kam Momy ko rashin zuwan abincin bai
dame ta ba, sai d'ai su Huwaila dake fad'in kila
ta ware su ne yanzun cikin kason ta. Fir koh
jajen rashin ganinta basui ba har yau. A haka har
ta raka wata ukunta. Sunyi tafiya da Abba
Abuja,yayinda yace taje kawai dan cika umarnin
likita. Hawaye take sosai a kan gadon scan d'in,
shikam likita ya ma kasa cewa komai, sai chan
ya nisa, a gaskiya kuna da sa'a a rayuwa ke da
Madam Fatima, haa'a.. Sai ya maida kanshi jikin
allon machine d'in. "Malikul kuddus kenan,
gaskiya ina da babban tukuici in na sanar da
"pharmacy" wannan abin farin cikin. Da sauri ta
girgiza kai, "A'a Doctor, dan Allah ka riken ya
zama sirrin mu, dan Allah... ''Assistance" ta
kusan su tace "amma wannan abin farin ciki ne,
balle ga mijinki. Kai ta k'ada, "na sani, sosai ma
kuwa. Murmushi likita yai, "na gane Madam,
InshaAllah pharmacy bazai ji batun nan ba, I
promise. Kai ta k'ada, harda godiyarta. Tana tafe
a mota tana kara yabo ga godiya ga Allahu
subhanahu wata'ala,lalle Allah gagara misali ne,
ikon shi ya wuci komai, kuka ta fashe dashi
sosai, sai ta nemi gu tai "parking", lalle hakuri
wani abun ne a matakin rayuwa. Hannu takai kan
cikin, sai ta rint'se ido, hawaye ya k'waranyo.
Tuni ta fara ma wa Allah kirari, a cikin k'arfin
mulkinshi da iko, tasan wannan k'yauta ba kowa
ke samonta ba sai dan baiwa. Dak'yar ta d'ai-
d'aita ta karasa gidan su. Dan d'uk ji take in bata
dangana da Ummanta ba bazataji sa'ida ba. Ido
cike da hawaye itama Umman ke k'allon Furen,
"Kinga kad'an daga ikon Allah, ki bar kuka haka,
kiyi adu'a, Allah ya inganta miki. Kai Furen ta
k'ada tana goge hawaye a cinyar Umman. "Ki
d'auka wannan tukuici ne ga Allah zuwa ga
hakurin da kikai a jarabawar rayuwarki. Ki d'auka
wannan su zasu zama silar yayewar d'ukkan
kuncin rayuwar ki, nasan kin ari hakuri kin yafa,
Ubangi yai miki albarka Furera... Hawaye ta goge
tana fad'in "Amin Umma. "Umma amma mu
rufeta daga ni sai ke, ko AAA bazai ji ba, in
lokaci yai kowa ya gani, kai Umman ta k'ada, "ai
wannan ba abun fad'a bane Furera, abu ne a
6oye, sai lokaci yayi in sun baiyana a sanar. By
Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.my
9/29/16, 2:52 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 44_Koda AAA ya dawo
maganin da aka rubuta mishi kawai ta bada,
sannan ta sanarshi komai "normal". A haka tai ta
rakawa har ta shiga "2nd tremiser", yanzu tana
iya komai,har Abinci ta cigaba da yi ma su Abba.
Iyaka d'ai ita intai ne bazata ci ba sai tuwan
Umma har yau.