JUYA Lokacin da Kaddara Ta Sauya Komai by Queen Safiyyert

Author :  Queen Safiyyert Category :  Romance

Chapter   7 / 18

18K to 21K   out of 51.2K words

kamin Rukayya ta k'allo momy wace ta sau
baki tana k'allon su. "Momy yau kin mana mai
dad'i, kai,yaushe rabon da na ci irin wannan
abincin da yawa? T'saki Momyn tai,kan tace
"abincin kishiyar ki toh kika ci, kuma wai dan
iskanci suka hau k'ak'arin amai na gulma.
"Amma d'ai Momy da kin fad'a tun farko wallahi
bazan ci ba, cewar Huwaila, sai sukai kitchen
suna ta bala'i, wai y'ar neman gindin zama,sai
d'ai fa kan a wanke hannu har lashe wa akai
bama su sani ba..y'an Kot'ar nan. By Feenat
Ja'afar.
Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 24
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 25_Da ya je gida tai
mamakin yadda taji wai y'an gidan na santin
girkinta,sosai ya ji dad'i, dan murna sama yai da
ita suna hajijiya da tuntsura dariya. Shi yasa
yamma nayi tai wani abin,sannan tasa ya siyo
mata Aya da kayan had'i. Washegari ma
hadadden "meat pie'' da "doughnut" tai musu da
kunun Aya mai sanyi da k'ankara cikin kula,ya ji
K'wak'wa da kayan had'i da madara. Tun jiya da
yamma tai "doughnut", ta nika ayar ta,dake suna
da wuta "standard" ta samu k'ank'ara. Komai
Fure tai tana burgeshi matuka, ga nan kullum
cikin sabon t'sari take na girki. Fitowa tai daga
kitchen jin yana kiranta, da mamakin shi sai yaga
har ta gama shiri cikin "favorite" d'inshi wato
"Orange color". Wani dak'akken "swiss" ne mai
ruwan Orange da filawa fari, sai tai amfani da
wata "fashion" na kalar kayan,shi bai son
kit'so,sai ya had'u da mai son fakin,daga chan
kasan d'aurin tumin nad'in gashinta ya fito,sai ta
ja g'yale saman kan. Sosai tai mishi k'yau dan ta
lakanci abinda yafi so, karasa yai tare da k'ar6ar
abin hannun nata sai ya manne hannunta cikin
k'wanon da nashi, in ta ja sai shima ya ja,sosai
filawar tai k'yau ta hannun. Sai tai murmushi,
ganin hakan sai ya sassauta ta cire hannunta
tare da g'yara g'yalen, k'wanon ya ajiye sai ya
hau tayata g'yaran g'yalen. Ita d'ai nata
murmushi. Suna a mota hannunshi rike da lalle
yana dan dubawa tare da k'allon hanya,ita dariya
ma yake bata, dan tun safe da ya fita sauke
kayan "storen" shi da aka kawo bai dawo ba sai
dazun,shima yana wanka ya kara fita,sai waya da
ya mata gashi nan zuwa.. Sai zuwa yai yaga
lalle,mai yi har ta tafi, kuma ya kasa tambayar
yaushe akayi. Har suka je gidan suna a farin ciki,
sosai kamar wani rakumi,haka yake zama in yana
gaban Prettyn shi. "Part" d'in Mama suka sauka.
Ko jumawa batai ba tace taje wajen Momy,har
ga Allah tafi kaunar ganinta da Mama. Nata
"snacks" d'in ta ajiye Ummi ta d'au d'ayan sukai
"part" d'in Momy Gomnati. Kusan ilahirin gidan
da sirikansu a gidan ta same su,Aunty JIDDA ce
kawai bata a cikin su,harda amarya Hassana da
aka dawo daga "Honeymoon" ana ganinta aka
hau fikara. Har kasa ta gaida Momy,a ciki-ciki ta
amsa,daga nan kala bata kara ce mata ba tai
d'aki. Wajen y'an parlourn tai yo,bayan ta zauna
ta gaida su,d'uk sun amsa,amma biyu kam keya
ma suka juya mata. Aunty A'i ce tai mata
magana kan daga zuwa d'aya shiru, sai tai kasa
da kai tana murmushi,kan ta dago, "zamu zo
InshaAllah, Aunty Maryam ke harar su Sa'a,kan
su saita k'allon sun, sai suka d'an basar. Har
kusan azahar kan Momy ta dawo "parlourn''
samu tai suna alfari ma Fure, d'an t'sabar cin
fuska wai tarihin kanshi kowa zai bayar tunda an
hallara yau, kowa yasan juna, ita d'ai Aunty A'i ta
hakimce K'afa d'aya kan d'aya a kujera tana
d'anna waya,dan sam bata shiga haukar nan ta
k'annen mijinta. Amma jin Bayanin da Huwaila
take,kawai sai ta sau baki tana k'allon su da
mamaki. A ranta tana"Oh,thank God, Allah ya
gama su da sarakan dagawa da nuna su sune,
sai ta k'alli Momy,ko ajikinta, asalima murmushi
take musu ana k'wada arzikin gidan su. "Ni suna
na Sa'adatu.. (Huwaila) in bracket. "Ina da
aure,da yaro na d'aya, ta shafa ciki, "sannan ga
nan na biyu. Har wani k'ada ido take, "Abban mu
ya mallaki gida je har ba adadi,sannan kud'i a
"accounts" bamu san adadin shi ba,ga motoci sai
wanda ka kaga damar hawa, kowacce acikin mu
yakan mallaka mata mota in zatai aure,da gidan
ta na kanta,sannan mu fita kasar da muke so in
hutu ya t'saya, kai,kud'i yayi a rayuwa. Ta fad'i
tana k'allon Fure da ta sau baki. Sai ta k'allo
Hassana, " ke fa Matar yaya? Hassana ta g'yara
zama, tare da y'atsina, "ni baba na d'an Kasuwa
ne,sannan d'an siyasa ne ajahar nan da ma
Arewacin kasar nan,sannan yana aiki da
"Government'' nima ban san adadin kud'in da ya
tara ba,Abu d'aya na sani,shi sananne ne acikin
masu kud'in jahar nan. "Ga nan kuma t'sarabar
"Honeymoon" ta karasa magana tana wani k'ada
kai da shafa ciki kamar wacce tai abin kirki. Ita
d'ai Fure tai kasa da kai,abin har ya d'aina bata
mamaki, ya dawo bata dariya. Huwaila ce ta
k'allo ta, "Amarya ke fa? Dagowa tai tana k'allon
irin y'atsinar da mai tambayar take mata. Sai tai
murmushi, Ahmad da tun zuwanshi yai tsaye a
"corridorn" Momyn, har zai shigo,sai ya t'sinkayi
maganar Furen tana ce musu, "Ni? Sai suka daga
Kansu wasu harda murmushin keta. Su a dole
zasu tozarta ta. Sai tai murmushi kan ta k'alli
wani gefe. "Furera muh'd suna na. Baki suka
ta6e harda tafawa,wai "Furera"?? Sai tai
murmushi tace "Baba na makanike ne shi,mai
g'yaran mota ko babur.. "bai da kadara,sai
rumfar aikin shi guda biyu. Sannan ba fittacce
bane a garin nan balle ma akasar nan. "Tabbas!
ban tunanin yana ma da "account" ma,balle
kud'in shi har ya gaza kididdiga, sannan ko gidan
kanmu bammu dashi,a haya muke zaune,sai dai
Hamdala ga Rabba, abu d'aya na sani... "Baban
mu zaki ne,mai nema da k'arfin shi da Allah ya
bashi domin yaran shi, sannan ya bamu ilimi
wanda zai taimake mu anan duniya da kiyama, ya
bamu farin ciki, wanda har kullum in mun
k'alleshi mukan ce Alhamdulillah. "Sannan ya
bamu..... "Ke!!! ya ishe mu haka, kai ta dago,
Momy ce ta kat'se ta, sai sauran y'an parlourn
suka sa mata dariya,banda Aunty A'I da Aunty
Maryam, wanda tunda ta fara suka nutsu
sauraren ta jiki a sanyaye, tuni farad d'aya ta
k'wanta musu a rai,ita kam Ummi d'an karamin
t'saki tai ma su Rukaiyyan.. tana jin Rukayya
tace "Rubbish" cikin y'atsina. Sai ta k'ada kai,
tare da yin kasa da kai tana murmushi tare da
wasa da y'atsunta. Kai ya jingina a jikin
bango,t'sabar So da kaunar Furii ke kara shigar
shi, tabbas ya t'sani fari'a, sosai ta kara kima a
idon shi, d'an fed'e musu ainashin ita wacece...
Ji yai an dafa shi, da sauri ya bud'e ido ya k'alli
gun, Mama ce,har da d'an guntun hawayen ta
dan tun t'sayuwar shi ta t'sinkayi komai, sai ta
k'ada mishi kai, tare da ruko hannunshi suyi
"part" d'inta. Zama sukai,sai yai jugum, itama
d'ai shiru tai, chan ta kira shi ya dago,da
mamakinta sai taga idonshi ya k'ada kamar zai
kuka, sai ya marairaice mata, kafadarshi ta dafa,
"Ahmad, kai hakuri,ni ina ji a jikina matarka
alkairi ce gare mu a gidan nan, dole kaji ka toshe
k'unne ka, dan nasan zata iya bawa kowa
amasarshi d'ai d'ai shi tunda ta bada a wannan
karan, ,kar ka fara tunanin cire ta a y'an uwan
ka..kai hakuri, da sannu zasu gane nasan
wataran. Kai ya k'ada mata. By Feenat Ja'afar.
庐NWA. Feenat.mywapblog.com
9/29/16, 2:31 AM - Queen Safiyyert馃憫: Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 26_Ko minti biyar basui
da dawowa ba sai gasu ita da Ummi da Aunty
A'i. Fira suke cikin murmushi, sai Momyn ta dan
ji dad'in yadda Aunty A'in ta sau ma Fure jiki.
Aunty A'i tace, "dan d'aki ashe tare kuke da
amarya? Kai ya k'ada mata yana k'allon Furen da
murmushi. Sai mama tace Ummi ta zuba musu
doughnut dasu kunnun Ayar, sai tai ciki dan basu
gu,cikin murna tai kitchen da zamud'in zata kara
cin abincin Fure. K'allota Aunty tai tana taunar
"doughnut", "wai gaske ke ne ki kai ba aikatau
ba? Murmushi tai kan ta dan k'alli wajen
Ahmad,itama Aunty A'in sai ta k'alleshi. "Ok,kai
kayi kenan? Kai ya k'ada, "ya kika ji toh? Kai ta
k'ada tare da dauk'ar "meat pie", wannan ma ta
hau k'ada kai cikin santi, sai d'ai Ummi na zuba
mata kunun Aya ta hau g'yara zama, fad'i take
"kai,wannan kuma mey ne? Dariya suka hau
mata,ita kam ta dage da gaske take bata san
kunnun Aya ba,ita d'ai Fure kawai murmushi take
musu, dan tasan tsaf sai ta kasa sannin, dan
y'an gayu sai da lemon k'wali. Suma achan ba ko
kunya suna ganin Aunty Maryam ta fara ci suka
zira hannu, barin Hassana,kamar wacce bata
taba ganin filawa ba haka take narkar "snacks"
d'in. Rukayya ce bata ta6a ba,tabi Momy suka
zuba musu na mujiya kawai. Amma chan kasan
ranta bata manta daddadan abincin Fure ba.
Suna gamawa sukai bangaren mama,sai d'ai
yadda Aunty A'i ta had'e rai,shine yasa suka
gagara tankawa Fure. Sai da akazo sallah tukun
ta yaye g'yale da nufin zuwa alwala, baki Ummi
ta saka ita da sauran,ganin gashin Fure,ga nan
ilahirin shape nata ya baiyana cikin les din. Sai
tai murmushi, tana jiyo musun Huwaila da da
Hassana kan wai "attachment" tasa. Kawai sai ta
k'ada kai ta shige alwala. Har ta iddar ba wanda
ya motsa sai Ummi, Aunty A'i tace tana fashi,
Aunty Maryam kuma tana gun mama, kawai sai
ta zuba musu ido, da mamakin ta har uku suna
kan waya ana nuna kayan k'arya na d'aki wai
Huwaila zata sauya. Mama ce ta fito,sanyin hali
yasa ta tambaye su tukun sunyi sallah? Kansu na
waya suka girgiza halamar A'a, sai ta had'e rai,
''toh maza ku bar min nan, ace d'an musulmi har
uku bai sallah ba? Fure d'ai ikon Allah take
gani,ba musu suka bar parlourn sukai na
Momy,sai Hassana ce ke sinke kataje tai alwala.
Sam basu kaunar zama kusa da Mama,ita sam
bazata bar bawa ya wataya ba,ga nan Momy,suci
karan su ba babbaka ma ba ruwanta dasu.
Washegari kuma tai gidan su,sai dare ya d'akko
ta suka dawo. Sai dai koh a fuska har yau bata
nuna mishi abinda y'an uwanshi suka mata ba.
Sai d'ai a ranta tana fad'in ta d'aina tanka
musu,dan ta san rashin islamiya ke damun su.
Sai d'ai Hassana tafi bata dariya,mai tunkaho da
kud'in ubanta. Kud'in Tukudi, kud'in cizo,kusan
unguwar su d'aya da Y'an uwan su Adama, ta
bata sirrin komai ai, karya kuma ta kare. Tun
daga wannan ranar d'uk "weekend" d'in duniya
sai Fure ta aika ma Abba dasu Mama abinci,na
satin nan sai ya ninka na satin gaba dad'i. Sai ya
zama har Allah-Allah Abba yake ya ji ance
"weekend " tayi yana gida,dan ya k'washi garar
abincin sirikarshi mama na gefe tana mishi
murmushi. Dan sam Momy ta d'aina k'ar6a koh
an kawo mata. Ko ran girkin Momy ne kuwa indai
ya fad'a a ranar kawo abincin Fure Abba shi zai
ci. Bashi ba,hatta sauran mazan gidan irin su
mijin Hassana nasan girkin Fure. Dan ak'wai
lokacin da yazo ya samu Fure ta gama girki tana
"serving" yayan shi shima ta zuba mishi, da
hadd'en lemonta na kullum,tuni ya soma wa
Ahmad santi, nan tana daga d'aki taji yana
t'surkutawa Ahmad d'in wallahi ba abinda
Hassana ta iya sai dafa indomie da k'wai,kai
ranar Fure taci dariya ta gode Allah. Sosai zata
gode ma Allah a bisa yadda ya sauya rayuwarta
farad d'aya.. Babban farin cikin kuwa shine
yadda ta zama fitilar haskawa ga mijinta, ta
zama abar alfarin shi, ya zama abin nuna ma
sa'a, domin ya bata d'ukkan farin cikin dake a
gidan aure,ance zo mu zauna zo mu sa6a.. Toh
a gaskiya Fure sai anyi kure,kan taga sun sa6a
d'in, albarkacin mijinta ta leka garin manzo, ta
leka kasar da ko a mafarki batai tunanin zuwa
ba. Sai d'ai dake Allah ya kan jarrabi bawanshi a
d'uk farin ciki toh dole ak'wai bak'in ciki, ba
komai zaya had'a maka 100% ba a
rayuwa,matuka yanzu burinta haihuwa. Ko dan
ganin yadda har ta fara taka matakin gori daga
y'in shekara agun dangin Ahmad. Yanzun kam ta
kara samun matsayi, daga y'ar MATSIYATa ta
koma JUYA. Bata jin da taron da za ai a watse
lafiya ba tare da an wat'sa mata magana ba.
Hakan yasa ta halarci ganin likita,ko d'an ganin
mey matsalar. Duk da shi ta gun Ahmad d'in d'uk
kaunar shi da yara bata ga chanji ba, asalima
cewa yai yaushe ma akai auren? Kar ta tada
hankalinta, "soon'' zasu samu baby. Tanan kawai
takanji sanyi,har ta manta bakin cikin su
Huwaila. Ranar sun fito ziyara sukai har gidan
k'aninshi mijin Hassana, dak'yar ya yarda,shima
sai da tace bai fa je ganin baby ba. Suna a
"parlour" yana cin abinci, da murna ya tari d'an
uwanshi, itama Hassana ba laifi, ganin Ahmad ta
sau mutunci,dan sam bai bata fuska koh a gida
suka had'u. Sai dai motsi kad'an ta ambaci
sunan y'arta, ita a dole zata bawa mara D'a
haushi. Murmushi kawai Furen ke mata,shikam
Ahmad kamar an tsikare shi yace ta tashi su tafi.
Direct gidan Aunty Jidda suka sauka, hakima
isassa, Allah ya gani d'uk Familyn su Ahmad tafi
ganin tsanarta karara akan Fuskar Aunty Jidda.
Ba abinda ta bari na Momy,sosai in ka ganta sai
ka d'auka K'anwar Momyn ce ma,dan sosai tafi
Momyn tsufa. A kofa ya batta kan zai shigo Abba
na neman shi. Kai ta k'ada mishi, sai d'ai tana jin
jina shigarta gidan ita kad'ai. Rukayya da Huwaila
k'wa suna gidan,uku ta had'u mata. Tun daga
gaisuwa ta d'auke suka d'auke mata wuta,Aunty
Jidda ta had'e ran nan. A walakance Aunty Jidda
ta k'alleta ta wat'sar, sai k'alli su Rukayya,
"nikam ku tambayi Matar Yayan naku naga har
yanzu shiru,sai ban ruwa muke shuka na hau
hawa.. Baki Huwaila ta ta6e, "bari dai kiji ta
bak'inta Aunty, sai ta k'allo Fure wacce itama su
take k'allo cike da mamaki. Sai tai kasa da kai
tana murmushi. Tamkar wata Umman ta tace
"Wai ke har yanzu shiru ne Fure? Sai Rukayya ta
amshe, "Ki ka sani? Kila d'ai "JUYA" ce...Da
sauri ta k'allosu fuska d'auke da mamaki,kan ta
koma kan Aunty Jidda, baki ta ta6e,sai ta tashi
ta basu gu, su kam ko ajikinsu, asalima dariya
suka hau mata harda tafawa,, kamar kullum,yau
ma ta kasa tanka komai a game da maganar da
ake ya6a mata d'uk a rashin bata haihu ba cikin
shekara d'aya. D'uk da tasan tana da damar
ramawar a kansu, maimakon hakan ma,sai kawai
ta kara kasa tare da k'adashi tana murmushi. By
Feenat Ja'afar.
Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 25
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 27_Sosai tana
mamakin d'uk bak'inta da iya bada amsa a
zance, amma in an kira ta da "JUYA" sai tai
shiru. Ba shak'ka kila wataran Allah zai ara mata
rana ne acikin ranakun rayuwarta d'an zuwan
hakan.. Ko kuma baya rasa nasaba da ganin
darajar mijinta, wato Habeebinta Ahmad dake
d'an uwan su. "Kinga ai tai shiru, anzo an bake
gida,ana hura hanci anji sanyin AC,baki Huwaila
ta ta6e, "wallahi nafi jin haushin Yaya da ya
k'waso ma kanshi alakakai, k'alleki fa
Rukky,wallahi ke ki kafi da cewa da wannan
gidan ba ita ba,tuni suka hau zaginta cikin
turanci kamar kullum a nufin y'ar talaka ina zata
samu ma "foundation" mai k'yau bare ta iya
turanci. Sosai take nuna musu dolancinta, sai tai
tamkar bata jin mey suke fad'i, ko turanci aka
mata azance sai ta nemi su fassara maata. A
haka har Huwaila ta shigo ma da Rukky maganar
mijinta,kan ta kasa gane inda ya dosa,har ta gaji
da kai karar shi gun Abba. Fure na jin lokacin da
tace ta fad'ashi da Ya Ahmad, tunda k'aninshi
abokinshi ne. A ranta tai dariya har ta gode
Allah, ace y'ar mai dashi ta rasa gane kan Miji?.
Sannan k'warai in bata manta ba ta ta6a jin ance
Aunty Jidda har suka rabu da mijinta bata haihu
ba agun Ummi,toh wai shin g'wanau baya jin
warin jikinsa shi sai na wani? Ko kuma ji nai
batai ba yaran na gun Abban su? Da wannan
tunanin har Ahmad yazo suka je gidan Aunty
Maryam, ita kam maganar bak'inta ma gagarar ta
take,bare Furen ta gane inda ta dosa. Wasa
wasa Fure har ta k'ware a auna kanta da kanta
da pt,ko k'wana d'aya "period" nata yai "due''
yanzun zata d'au "strip", dan tun yana kawo mata
d'ai d'ai yanzu k'wali ya dire mata,shi d'ai kullum
burin shi ta ma d'aina g'wadi, takan k'alleshi da
mamaki,ita ya dace tai mishi lallashi,dan sosai
tana ganin yadda yake son yara koda in su
Adama sunzo mata. Tuni ta kammala makaranta
tun wata uku da suka wuce,ba wanda yasan tana
zuwa,daga Umma sai ummi,fatan ta "result'' ya
fito,yaya yayi alkawarin kama mata shago kan ya
tara kud'in bud'e mata karamin "Restaurant".
Magana ta kara karuwa ne lokacin da Hassana ta
kara samun ciki, sosai take d'anne ranta,har bata
kaunar abu ya had'a su zama waje daya, a gun
mama da Ummi kawai take samun sa'ida. Momy
kuwa, shekara biyu na cika ta tada ballin dole
Ahmad ya kara aure da Rukayya, tunda ga nan
yadda Matarshin tazo. Ko kad'an bai fara gigin
bari Fure taji zancen nan ba,shi yasa kawai yake
bin Momyn da toh, dan ganin Abba ma baice
komai ba. Ita d'ai taga fallin Rukky ya karu,
sannan Momy ta rage mata wani abin, maimakon
haka ma,sai ta t'siro da mata murmushi in tana
gaida ta ko in ta ganta, wanda kai kana gani
kasan mugunta ne. Allah sarki Fure baiwa ta
Allah. ************************ Doguwar ajiyar
zuciya ta sauke,lokacin da ta gama tuna baya,
tuni sai ta tashi ganin lokacin sallar "Duha" yayi,
yi take tana kai ku kanta gurin Allah, in har tana
da rabo na alkairi toh Allah ya bata. Harda dan
guntun hawayenta dan tuno da jiya a gun sunan
Hassana. Sai ta samu kanta da daga hannu, tana
mai rokon Allah indai tana da rabo na haihuwa a
gaba,toh dan t'sarkin mulkinshi ya aramata rana,
ya ara mata lokacin zata had'a kan kowa dan
bashi sakamakon abinda ya tusa mata. Tana
shafawa ta hau kuka, sai da tai mai isarta kamin
tai shiru taje ta k'wanta. "Text" tai ma AAAn ta
kamar yadda ta saba in tafiya shi da Abba sukai
bata kira. Sai ta kashe waya kan ta juya dan
rama baccin ta. Saukar su kenan ya kai Abba
gun taron da suka je yaji shigowar "text". D'aki
ya kama musu shida Abba "Hotel" kan yai wanka
yai "ordern" abinci. Chokali yasa yana jujjuwa
abincin yana tuna wa da "delicious" na Prettyn
shi, sai yai murmushi k'ada kai, Furii kam
"special" ce agun shi. Sai d'ai yana mamakin yau
har ya sauka baiji "text message" nata na "safe
journey" ba, hannu ya kai dan tunawa da sakon
da ya shigo wayan shi dazun. Baki ya wage
ganin ita d'in ce kuwa k'wace kan "screen'' an sa
Pretty. Cikin zumudi ya bud'e sakon fuska d'auke
da murmushi. Ajiyar zuciya ya sau, kawai sai
tuno da ta jaka kamar kullum, da sauri ya tashi
ya zuge jakar,sai ga nan abu cikin duguwar ruba
marar kauri nad'e a "wrapping paper". Yana dago
shi sai ga nan wani y'ar "paper", ajiye na hannun
nashi yai, da "pencil" ta "heart" tai "shedding"
nashi g'wanin k'yau, kan a ciki tai wasu mit'si-
mit'sin rubutu. "Ticking beats my heart, and the
desire to see the person that I love. I wish the
best for you in this journey, and I wish you a
speedy return.... Love you. Zame wa yai a
hankali yai k'wanta a gadon, yana mai shafa jikin
y'ar guntuwar takadar. A hankali ya mike,sai ya
ware wannan bowl d'in, cikin sauri ya fara ci,tuni
ya k'auda wanda yai "order" tare da jawo wayan
shi da zummar kiranta ya ji "switch up",a haka
yana ci yana kara k'allon heart d'in yaci kusan
rabi,ya kora da lemo. Ji yake kamar yai fuffuke
yaje ga FURIIN shi. A kullum ta duniya yana
alfahari da zaman Pretty mata a gare shi, sosai
ya sani ko a haka Allah ya barshi ya kaunace
shi, balle zai so yaga yaran shi da Pretty kad'ai a
duniya,badan bai san yadda hali zai yi

7 / 18