Author : Queen Safiyyert Category : Romance
da abu mai dad'i.
Da tunanin juna suka k'wanta, shi kam harda
mafarkin "FURIIN" shi.
Washegari suna t'sakar gida da sauran bak'in da
basu tafi Ang'waye sukai sallama,anzo gaisuwar
sirikai. Amal aka ce ta leka,sai gata da gudu tana
rad'a ma Fure"Aunty Furera Uncle... Murmushi
tai,kan ta k'alli kofa, Ya Suleiman ne ya shigo,
tare da sanar da su Umman,darduma suka sa
musu,kan tace ya shigo dasu.
Chan bak'in kofa ta zauna,har suka shigo, tana
jin lokacin da suka gama gaisa wa Ilyass na
tambayar ta.
Leko da kai tai kad'an,d'uk sai wani sunne kai
suke har mutumin ta,d'uk da yana d'an wayancen
dagowa neman ta. A hankali tace musu
"Ina k'wanan ku... Cikin nutsuwa ya dago kai
zuwa bak'in kofar da ya jita, ido suka had'a, da
murmushi tai kasa da kai suka amsa.
Amal kam tana manne da Ahmad,wanda
murmushi yake saka in sun had'a ido da
Fure,cikin kunyar k'allon d yake mata ta buya
d'aki. Har suka zo fita yana d'an leken ya ganta
amma ba hali.
A zaure ya tsaya bayan sun fito,dan gidan su
Adama suka fara zuwa.
Amal ya aika wai ta kira mishi Aunty Pretty, da
d'an dariyar ta ta tafi kiran.
Jim tai kad'an, kan tai murmushi ta tashi,zani ta
sauya,ta cire hijab d'in jikinta,sai ta samu kanta
da t'sayawa gaban mirror, gashinta ta g'yara, ta
d'aure shi t'sakiya da k'yau kan ta sa hijab akai
ba dank'wali. Gun Umma taje,tace ana kiranta.
A zauren ta same su shi da Amal yana rike da
hannunta tana mai wai karatun ta na islamiya"
Asma'uillahi Husna".
Kai ya dago da ya sauke su kanta lokacin da
take musu sallama. Murmushi ya sakar mata kan
ya amsa,yau kawai kunya ce tazo mata tashi.
Shikam k'yau ta mishi a hakan ma da ba make-
up, a chan kasa yake k'allonta, wanda tuni ya
kara mata wata kunyar. Rabin tad'in nasu da
Amal su ke,kan ya tambaye ta yaushe zata
Aisha,tai jim,yau kam ta gaji,tun dazu take mata
nacin tazo ta riga tace sai gobe, ga d'ai bak'i
zasu zo, "gobe InshaAllah.
Zauren ya k'alla, na kasa ne amma wata iska
yake ji mai sanyin dad'i, ji yake kamar yace ta
shimfida mishi taburma kawai ya zauna suyi ta
tad'in su yana shan iskar zaure.
Tabbas yana alfari da Suleiman da k'annen
shi,har ma da iyayen su,rayuwa suke cikin sauki
da rufin asiri,ga kowa ka gani a gidan mai fara'a
ne. Sannan basu raina kansu wai dan wani ya fi
su,shi yasa sosai ya fara abota da Suleiman a
dalilin Ilyass abokin shi. Sai yaji ya kara son
had'a jini dasu,
Kai ya k'ada yace "Allah ta kaimu,,a hankali
tace"Amin. Ya Suleiman ne ya shigo zauren shi
da Ilyass yana ta dariyar keta, shi kam Ya
Suleiman murmushi kawai yake, gaishe su ta
kara yi,tana tambayar ina K'awar ta? Sai yai
murmushi, kan yace tana gaishe ta.
Sosai suke bawa su Ahmad sha'awa ganin yadda
yake ji da y'an k'annen shi. Janshi Ilyass yai
yana mishi tsiya sukai waje,sai ya juyo tare da
kai hannu k'unnenshi a hankali ya furta"I will call
you". Murmushi kawai ta mishi tare da sunne kai.
By
Feenat Ja'afar.
[4/19, 9:28 AM] Feenat Ja'afar 馃鉁嶐煆� :
"JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
14_Washegari gidan Adama ta fara zuwa, ba
wata k'walliya tai ba,kawai "powder" ne da
janbaki sai "mascara".
Sanye take da "pink'' na doguwar riga kirar
'"Dubai'' wanda Ya Suleiman ya sai musu kan biki,
farin fashmina da ratsin pink ta faka gashin nan
kan ta nad'e shi cikin g'yalen, ta hau "hill",
matuka zaka zata y'ar wani mai kud'in ce,amma
tsabar rufin asirin Allah ne da had'uwa da iyaye
masu zuciyar yi.
Harara ta kai mata, "ai nayi fushi K'awa,
murmushi tai,a kiyi hakuri. Kai ta k'ada, "ya zanyi
toh? Ina su Umma? Murmushi tai, kan tace" suna
gaida amarya,jiya kad'ai har kin kara "shining "
dariya tai kan tace"dan ma yayanki ne.
Sai Bayan la'asar da k'yar Adama ta tabarta,dan
sau biyu mutumin ta na tambayar ko taje?.
A parlour ta same ta ita kad'ai, sai ta kara bin
parlourn da k'allo, tabbas iyaye sunyi rawar
gani,dan tsaf an fito da Aisha musamman
parlourn.
"Kai Allah sakawa iyayen mu da alkairi, Aisha
tace "Amin kam, sam ban tunanin zan samu rabin
kayan nan ba,Abba ga harkar gini shima yaya ga
auren shi,Furera k'warai Abba abin alfarin mu ne
wallahi... Kawai sai ta fara hawaye, tasowa tai
ta dawo kusan ta, kan ta goge mata ido, "Adu'a
zamu musu Allah ya kara musu bud'i,muma Allah
sa su more mu haka.
Kai ta k'ada tare fad'in "Amin. Nan ta hau kuma
fad'in kamar ta koma gida take ji,gaba d'aya tai
missing nasu.
" Ga nan ce fane muje man ki d'an d'aura min
daga inda kika t'saya y'ar K'anwata,,dan harara
ta sau mata,kan tace"kima zage,dan ba zuwa zan
nayi ba.
Sai k'arfe biyar suka shigo lokacin suna
kitchen,"Chief" tuni ta bud'ade gidan da kamshin
girki,"kai Furera mijin ki zai k'washi gara fa,
dariya tai kamin ta fara bawa Aisha shawarar
itama ko"Grace so amazing catering creations"
ta jona tunda "3month" ne. Tace zata tuntu6e
shi kuwa,bari a d'an k'wana biyu.
Da sallama suka shigo, sai d'ai ilahirin parlourn
ya d'ebi kamshin abincin amare. Zama yai yayin
da Ilyass yai hanyar "kitchen" yana zuba santin
kamshi cikin zolaya.
Shi kam gogan ido ya lumshe, sosai yana son
macen da ta iya girki,yasan tunda Aisha ta iya
toh prettyn shi ma ta iya.
Ita kam ganin ana neman mata fitsara a gabanta
yasa ta wanke hannu ta basu gu,a bak'in
"kitchen" d'in ta makale,tare da k'allon mutumin
ta yadda yake lumlumshe ido. Tsiyar Ilyass da
yake wa Furen ne ya sa shi bud'e ido,sai warai a
kanta,a hankali ya dago kai tare da zama d'ai-
d'ai, kanta kasa tana musu murmushin kunya.
Tabbas ance Wai ''in ka da k'yau, toh ka kara da
wanka" toh shi kam pretty da tayi wankan ko
batai ba tana burge shi matuka.
Sosai yake son karamin k'yau irin na "Prettyn"
shi,gashi ta iya dauk'ar wanka.
Murmushi yai tare da k'ada kai, Ilyass bai bar
kowa ba ashe? Hannunta Aisha ta rike tana
fad'in "rabu dashi sis,kan suka zauna a kan
kujera. Har suka gaisa da Aisha idon shi na
kanta.
Ilyass yace" madam, tashi mu basu gu su
sarara,dariya tai kan ta k'ada mishi kai sukai
d'aki.
Tasowa yai ya dawo kusa da ita ya tsugune tare
da d'aura yat'sanshi a kan le6en shi,ido kawai ya
zuba mata,kamar wanda yaga sabuwar halitta.
A hankali ta dago,tare da K'allonshi ido ciki-
ciki,sai tai murmushi tare da kara kasa da kai.
A k'alla ya kai kusan minti''5" kan tai
magana,"ina yini Uncle... Sai yai shiru bai amsa
ba, sai ta kara dagowa, kai ya k'ada mata,"Ba
Uncle daga yau Furii,ki bar wannan a makaranta,
K'allonshi tai, sai ya kara k'ada mata kai, "g'wara
ki ce ma AAA, "I like it,, murmushi tai, kan ta
k'ada kai.
Zama yai akan "center carpet" d'in, tare da
t'ang'washe kafarshi, kamar mai d'aukar
karatu,shi kanshi yakan rasa ya ake yake rasa
nutsuwar shi gun Furiin shi.
''Shin kina jin abinda nake ji a game da ke
pretty? Kai ta dago,kan ta zuba mishi ido,halamar
bata gane ba.
Murmushi yai,kan ya sada kai kasa,yana mai
fatan ta yarda dashi,d'uk da yasan mai wuya ne
ma taki yarda d'in.
"Pretty".. Ban san so ba sai a gare ki na samo,
tun wani lokaci achan baya zamanin "school"
nake jin irin " feeling " d'in nan, sai d'ai ban gane
meye shi ba.. Kai ya dago, idon ta a kanshi,ba ko
kiftawa, sai yai murmushi, "kar kiyi mamaki
Furera Muh'd,
Sai ya k'ada kai,kan ya tsare ta da ido,"I love you
more than you will ever know.. And I can't never
ever let you go again..
Ido ta rintse,tare da jin zuciyarta na tsanannta
bugu, kan ta farga ta kara jin wani sautin wanda
jinshi take tamkar waka yake raira mata dan
sanyin muryar shi... Da sauri tai kasa da kanta
kan tai ko'k'arin mai da kukanta.
Ya Ilahii.. Da gaske ne abinda take ji kuwa?
" ko d'ai yai batan kai ne? Kai anya? Toh ko
wannan shine batun da yace zai zo mata dashi?
A hankali ta sauke k'allonta a kanshi da shima
yake k'allonta dan jin tai shiru,zuciyarshi ce ke
faman buga mishi, tsoron shi d'aya kar dai Fure
tace bata son shi.
By
Feenat Ja'afar.
[4/19, 10:58 AM] Feenat Ja'afar 馃鉁嶐煆� :
"JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
15_"Ya ki kai shiru? Hope... Kai ta k'ada mishi,
"zan yi shawara.
Murmushi yai, " toh a son nawa za kiyi shawarar
ko a aure na? Murmushi tai kan tace"d'uk
Uncle..sorry.
Kai ya k'ada, "zaki ji ni gobe toh,amini kara d'ai.
Murmushi tai ganin ya ka'rkata kai.
Firar su suka ci gaba da yi ya koma kujerar kusa
da ita.
Waya ya zaro,kan ya bud'e" gallery" "you gotta
see this amazing
pictures.. K'ar6a tai a kunya ce, ganin ta a ciki
yai bala'in bata mamaki. Tana ina mey akai
wannan photonan masu yawa?
K'allonshi tai da halamar mamaki, gira ya daga
mata tare da kafada,sai ta marairaice mishi.
Sosai yake t'suma ta soyayyar shi,an ja aji kan ta
k'arbi tayin ta, sosai ta kara burge shi, dan bai
son budurwa mara kamun kai da aji, sai ya kara
bata wani girma na daban.
Gidan su yake mak'e kunya yaje,Amal kam kusan
kullum ranarta ce," ice cream " cheese " komai
ita,shi yasa sosai suka saba.
Ko kad'an bai nuna mata shi masu dashi
bane,asalima kusan kullum da mota d'aya yake
zuwa mata,sam bai kaunar rayuwar fa-fa.
Ba'a jima ba ya nemo k'anin Baban su da yayun
Mama suka zo tambaya, sai da ya tace su kan
yace su zasu,dan sarai yasan sauran yanzu sa
raina mishi tushen su Furen shi,d'uk da d'an
uwan Abban sai da ya tofa, sai d'ai ganin
dattakon Abban su Suleiman d'in yasa ya gane
d'an nasu gidan k'warai yabi ba wai dukiya ba.
Ginin su Abba da ya Suleiman yake musu yai
nisa sosai,har nashi a jiki yasa fili shima ya
had'a, dan haya shima ya kama.
Abba gidan shi na Zaria ya siyar wa yayan shi,
tuni ya chake mishi kud'i hannu ya bashi,har da
karin na bulo, d'uk da shi yana arzikin da zai iya
rike iyalin gidan k'anin nashi amma yakanyi
mamakin jajir cewa irin tashi,sam yafi son komai
yai da gumin shi da k'arfinshi.
Ahmad har gun aikin Abba yake zuwa in ya tashi
a shago suyi ta fira,tuni sai ya k'wanta mishi a
rai, dan ko motar da yake zuwa mishi da ita ka
gani kasan d'an masu hali ne,sai d'ai bai da
girman kai. Har aikin yakan ce zai taya Abba. Sai
kawai yai mishi dariya,dan sosai dan gayu ne,ina
shi ina aikin bak'in mai?.
Umma take tambaya kan wai Ahmad yace gobe
zasu gidan su gaida su Mama,tace ta bari Abban
su ya dawo tukun,. Ko da Abban ya dawo Umma
ta sanar shi yace ai ba damuwa,sai a had'ata da
wani rakiya.
A gado take suna waya kamar kullum, a hankali
maganar ke fita wanda na d'aki ma sai ya kula
kan yasan tana waya, idonta lumshe tana
saurararon yadda AAAn ta yake zuba mata
kalami masu sanyaya rai, tabbas yaci sunan shi
da ta kira shi da"SAHIBUL KALAM". Takanji wani
irin wutar sonshi na kara ruruwa cikin ranta,tun
tana kunya har ta ware tana aika mishi da nata
salon son.
Tunda ta sanar shi ya fesa wa Mama cikin
murna, tare da cewa Momy wai gobe zatai
bakuwa.
Sam bata kawo kom ba,sai tace mishi Allah ya
kaimu,har abin dad'i tasa tai mishi,"Momy pls da
hannun ki nake so,kai ta g'yada.. "Wannan k'wa
wacece haka? Hala y'ar makarantar ku ce?
Murmushi yai yace"eh kawai,dan yasan gobe da
budiri a gidan nan.
Washegari tana a gaban Amal tana g'yara mata
g'yaran gashin ta,ta zira mata "gown" "cotton
mai adon ja da yelo da ratsin fari,yana daga
kayan da tai fitar biki. Tai k'yau sosai,
tasa mata dan karamin hijab na yara fari da
takalinta choge fari,ba laifi,ko a y'ar masu kud'i
Amal ta fito,turare ta mika hannu ta bata wai ta
fesa mata na "Lailatul sahrA", kan itama ta hau
make-up, sosai tai k'yali iya k'yali, ga tasha
filawar baki da jan Rani.
Ak'wati ta bud'e tana neman kayan sawa, ta
fidda wannan ta kara ta ajiye,idonta kan material
ya kai wanda tama manta shi bata sa ba na fitar
biki,guda uku yayan su ya siya musu da amaryar
shi wai an kai office d'in su, dan " India " ne
"Orange", da filawa mai hoton ganye green an
gewaye shi da k'yallin"silver", murmushi tai dan
ganin" favorite " na Ahmad "Orange" musamman
a jikin mace. Zira su tai kan ta tsaya gaban
mirror ganin yadda d'inkin ya zauna mata cif!
Tuni ta hau d'auri, kai kace wata liyafar zata.
Tana cikin d'aura "buckle" d'in takalmin ta
"silver"data sa ranar "dinner" ta tsinkayi muryar
shi Umma na ya shigo. Da gudu Amal tai waje.
Tashi tai ta d'au g'yalen kayan da "poss" d'inta
ta yafa,gashin nan yai tum-tum a keya. Sai taja
g'yalen sama dan rufe gashin.
Tasan ko ina zata shiga a kasar nan, dan d'ai-
d'ai ruwa,d'ai-da'i t'saki.
Umma ce ta leko,"gashi fa,kai ta k'ada, sai
Umman ta karasa ciki d'uk.
Lalle tana yabawa da ya'yanta,sosai kamar sunyi
makarantar koyan k'walliya.
"Kinyi k'yau kam,sai d'ai naso hijab,amma ba
komai tunda an rufe kan, "ki gaida su sosai.
Kai ta g'yada, kan ta fita,a zaure ta sameshi shi
da mutuniyar,uwar magana,shi ko gajiya baya yi
da surutun Amal.
Sai d'ai suna ar'ba da ainashin madam d'in ya
kame,d'aidan wani, wai ka'rkataccen wani, a fili
ya furta "MashaAllah... Kai tai kasa dashi tana
murmushi, bata nufa ba taji "flashes" a hankali ta
dago,sai ya kara mata wani, kan ya d'auke
wayan ya k'alleta, sai yasa a ajihu,ya rike
hannun Amal suka jera, kamar wasu sabbin aure.
By
Feenat Ja'afar.
庐 NWA
9/29/16, 2:23 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 16_Shi ya bud'e mata,
cike da y'ar kunya ta shiga,ya bud'ewa Amal
baya. Cikin nut'suwa yake tuk'in, tamkar wanda
baison su isa inda zasu da wuri, firar Amal kawai
ke tashi, su kam murmushi kawai suke aika ma
juna,yau kam, tamkar siriki haka shima take d'an
kunyar shi, shi kam ganinta kawai yau na kara
mishi farin ciki. "Prettyn Uncle.. Da mamaki ta ju
ya,kan ta k'allo AAAn,sai ya daga mata gira, kai
ta d'an girgiza tare murmushi, kan ta dan harari
Amal wacce ke mata dariya," wa ya fad'a miki?
Da hannu ta nuna Ahmad, wanda ke musu
dariya,sai ta ju ya tare da d'aura kanta a kujerar
tana K'allonshi cikin wata siga. Yana "driving"
d'in ya ju yo kad'an, sai ya ga ta zuba mishi ido
tana d'an murmushi. Sai ya daga idon shi
halamun "ya akai? Kai ta d'an k'ada mishi tare
da sauke ajiyar zuciya. Sai ta koma kan titi tana
k'allo,wani irin farin ciki ta ji yana rat'sata. K'allo
shi tai lokacin da ta ga ya tsaya a gaban wani
waje kamar ''company" kato, sai yai murmushi,
kan yace "mun zo,yau za kiga Mama da Momy
da sauran k'anne na. Yake tai mishi, kan ta kara
k'allon yanayin gidan tun kan ma a shiga," Ya
ilahi!! Ina take shirin shiga? Mey ya sa Ahmad
bai nuna mata shi d'in d'an masu dashi ba ne har
haka?. " Gate" ne guda biyu a gidan,tafkeke ne
sosai, dan zai kai g'wan-g'wani d'aya, ita kam ba
mai shige-shige bace,sai d'ai gidan su k'awaye
masu d'an hannu da shuni,karara k'auyencin ta
ya so ya fito fili,bata tunanin ta ta6a shiga irin
wannan gidan a rayuwar ta. "Horn" yai,sai taji an
zuge ta ciki. "Subhanallah" shine kalmar da ta
ambata a bak'inta,lalle duniya na inda take.
"Flowers" d'in gidan su suka fara mata"welcome"
wanda suke a t'sare an musu "decoration " masu
ban sha'awa, d'uk gidan shimfid'e yake da
"interlock" tsari hudu ne a gidan,wato "parts" tsaf
sai ta karaya,da sauri tai kasa da kai gabanta na
fad'uwa. Ba d'ai Uncle Ahmad d'an gidan "Alhaji
Abba Ahmad" bane dan k'wangila? Sosai tana
yawan jin sakon gaisuwar shi musamman a radio
in Umman su ta kama, sannan ana yawan fira
dashi in harkar k'wangilar da aka bashi ta
kammalu musamman ta jaha. Kai ta dago,d'ai
d'ai yana "parking" kusa da wasu "arnun" ubansu
motoci,hankalinshi k'wance, sai ma murmushi da
yake ma Amal da take tambayar shi nan ne
gidan sun? Ummi yai ma waya,kan gasu kofa,
k'allota yai lokacin da ya gama wayar,"muje koh?
Kai ta k'ada mishi, sai ya fito ya bud'ewa
Amal,kan ya karaso ta ma bud'e, sai ya karasa
bud'e mata, d'an murmushi tai a takaice sai ga
nan Ummi ta fito. "Sannun ku Bros, da fara'ar ta
tai gun su, fara ce,kana ganinta ka ga Ahmad,
har fara'ar su d'aya. Itama da fara'a ta k'alleta,
sai ta k'alli Amal da tai wajen ta,dan fa d'uk
surutun ta toh a bakon waje miskila ce, ummin
ta d'an riko hannun Amal d'in sai ta make
kafada,sai ta mata murmushi tare da shafo
fuskarta da fad'in "fine girl". Murmushi yai,shi
yasa yake son Ummi a d'uk k'annen shi, ita
kad'ai ya yaba da nutsuwar ta,sannan yasan ba
zata bashi kunya ba. Bangaren Momy suka fara
shiga,kawai sai taji gabanta na fad'uwa tun da
suka doshi ciki. Kana gani kasan gidan y'an boko
ne,ko ina cikin tsari da k'yau, sosai yai k'yau,
kasan naira ta daku. Rukayya kawai ke parlourn
tana "chat" a "Facebook" shine a gaba,da
sallama ya shigo, a chan ciki ta amsa,dan jiya
tasu ta had'a su. Bai bi ta kanta ba yai d'akin
Momy. A y'atsine ta k'alli su Ummi,daga sama
har kasa ta ke k'allon Fure wacce Ummi take ce
mata ta zauna. Sam a d'uk y'an gidan basa shiri
da Ummi,dan ko k'allo suke ita ke damun su da
su tashi suyi sallah,gata sam bata raga mata,shi
yasa basa shiri,kai ta d'auke, da har zata tambayi
Ummin wacece ita??? Da fara'a Momyn ta fito
tare da shi, kai Furen ta duk'ar kasa,ita kam
Momy har ta zauna tana neman inda ta ta6a
ganin Fure. Sai ta amsa tare da k'allon Ahmad,
"daga ina bakuwar taka tazo? Dan sam ita bata
ga halamun wata hamshakiyar bakuwar da har ta
shiga kitchen dominta ba, duka-duka kayanta
basu wuce dubu 7 ba har g'yalen. Kai ya fara
sosawa yana d'an k'allon Ummi, sai tai
murmushi,kawai ba rufi tace" Momy budurwar
bros ce fa.... Wayar hannun Rukayya ce ta fad'i
kan tiles,wanda yasa d'uk suka zuba mata
ido,banda Momy dake k'allon Fure,a dirare tai
mata k'allon wulakanci,"ban gane budurwa ba
AAA?? A d'an takaice Fure ta juyo,dan tambayar
ta bata mamaki,sai d'ai mey,tabbas ta gane
matar nan,ita ce wacce Ahmad ya d'akko ta har
suka kusa maketa. Tabbas tai matukar tsorata
da yanayin Momyn,toh amma ya akai ta manta
da Momy uwar Ahmad ce har tazo gare su? Ido
ta rufe,dan kam bata ga halamun sassauci a gun
Momy ba tun wanchan karan bare yau. Dagowa
tai a hankali ta k'alli Ahmad d'in, dai-dai yana
rokon Momy da hannu kan tai hakuri kar ta bashi
kunya. Baki ta ta6e,kan ta tashi tai d'akinta. Sai
Rukayya ma ta tashi ta bita,tare da d'allawa Fure
harara, koh ta kan wayarta da ta fad'i bata bi ba.
Sanin hali, yasa Ummi tai saurin kat'se Fure da
cewa"muje bangaren Mama Auntyn mu,
murmushi ta k'ak'alo, wanda kana gani kaga na
dole. Sai ta k'allo Ahmad,kamar tace bazata
ba,dan a gun mahaifiyar shi ma bata samu
k'ar6uwa ba bare kishiyar ta? Sai d'ai yadda ya
marairaice mata yasa ta tashi,sai ya ruko hannun
Amal. By Feenat Ja'afar.
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Apr 20
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 17_Kuka Rukayya ke
ma Momy,ita kuma na aikn lallashi,"ki ma bar
6ata hawayen ki akan wannan mummunar, zai zo
ya same ni ne, wato dan t'sabar yaso ci min
fuska shine harda sani na zage a "kitchen" wajen
girkawa wata shegiyar da koh a y'ar aiki bazan
d'auke ta ba.. "Momy ki ganta fa,daga gani sam
bata ma kama kafar dacewa dashi ba, amma ni ki
dubi irin yadda ake kaiwa rana akan yaja soni
yaki. Sai ta kara fashewa da kuka, tuni ta kara
tunzuro Momy, "ai ni na miki alkawarin zama
Matar Ahmad bah? Kai ta k'ada. "Toh kiyi kamar
ma baki ga ba. A parlour suka tarar da
Maman,rike da waya a hannunta, cikin nutsuwa
da fara'a take k'allonsu tana cigaba da wayar,ita
d'ai Fure a dirare ta zauna a bak'in kujerar,dan
sam bata ma k'alli Maman ba. "A,sannun ku da
zuwa, a