Author : Queen Safiyyert Category : Romance
d'an hankali ta dago ta k'alli
Momyn,Ahmad na zaune kusan ta,kamar zai
shige mata,kamarsu har ta 6aci da Maman sama
da Ummi,da sauri ta sunkuyar da kai tana
murmushi, kan a hankali tace"yauwa, sai ta zamo
daga kujerar ta gaida ta. Ganin haka Amal dake
kusan Ahmad ma ta gaida Maman. Da mamakin
ta sai taji ta amsa cikin mutunci harda tambayar
y'an gidan su. Amal Mama ta ruko," ya sunan
y'an matan, da fara'a Ahmad yace"Amal mama,
sai tai murmushi, "Aiya,ina ta samun labarin
Pretty, yau gani ga ita. Kai ta kara kasa dashi
cikin kunya. Lalle abin da mamaki,anya ba mama
bace Maman Ahmad?.. Maganar ta ne ta kat'se
tunanin Fure, "ki saki jikin ki fa, d'an kinzo gida
ne, ita d'ai murmushi kawai take. Ummi tace ta
kawo musu abin sha. Sosai mama ta ba ma Fure
mamaki,dan mace ce wayeyya,ga saukin kai,
sannan fara'arta ita tafi komai sa Fure nutsuwa.
Dan har ta shiga ciki ita da Amal da ta yarda
fuskarta sake,ta yiyu anan Ahmad da Ummi suka
gadi sakin fuska. "Auntyn mu kisha fa, ga nan
lodin abinci na jiran ku. Murmushi tai mata,bari
naje na dawo,kila bros ni ma tana kunya ta ne.
K'allon Furen yake da murmushi, sosai Ummi da
mama sun wanke shi gun Fure. Tana fita ya
dawo kusan ta ya zauna,tare da miko mata
lemon, k'ar6a tai tana k'allon shi,fuskarta da abu
biyu zuwa uku. Na farko mamaki,na biyu
murmushi, na uku tsoro. A rayuwa taki jinin
wulakanci, ta kuma tsani t'saki. Gashi d'uk ta
gani a bangaren Momy. Sosai sun mata
karamci,har bata ma san ta saki jiki dasu
ba,musamman Ummi. Da zasu tafi mama ta
cikata da sha tara ta arziki,har kofa ta rako
ta,sai d'ai da yace suyi ma Momy sallama sai da
taji dan dar! Suna zaune a parlour ita da Rukayya
sun cika sun bat'se, sai harara Rukayya ke aika
ma Fure,koh da yace zasu tafi, a wulance ba tare
da ta k'allo Furen ba tace"ta gaida gida. Abinci
ma bata samu ba bare sinkin mai. A mota tai
kok'arin d'annne ranta, ko'k'arin shi kar ta sa
abin Momy da Rukayya a rai,shi yasa yake ta
d'auke hankalinta da fira. Har gida suka shiga
dashi,yana rike da t'sarabar mama. Har suka rabu
bai ko mata maganar su Momy ba, amma Allah-
Allah yaje gida ya jima Ruky. Amal ke bawa
Umma labarin gidan da abinda suka ci,har sai da
g'wa6e mata baki, dan sosai Umma bata son
yawan magana. Sai dai ita Fure d'uk jikinta yai
sanyi tunda suka dawo. Ido kawai Umman ta
zuba mata. Su Hassan ne suka bud'e kayan suna
shigo wa,baki sake Umma ke bin kayan da k'allo,
A hankali ta fara daga su, Atamfofi biyu ne da
less, d'uk da batasan kud'in su ba amma taga
ana daga irinta a na kayan Aisha, tasan masu
uban t'sada ne. Ga wani uban Le's wanda zai kai
ashirin zuwa 30,ga "cosmetics " har da kud'in da
mama ta bawa Amal. D'uk sai jikin su yai
sanyi,Umma ta k'alli Fure,Furen ta k'alli
Umma,kowa ya kasa cewa komai. By Feenat
Ja'afar. 庐NWA Feenat.mywapblog.com
9/29/16, 2:24 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 18_Suna nan har Abba
ya shigo ta tashi ta tafi d'aki, a dirare ta k'wanta,
anya zata tila kanta a irin wannan gidan kuwa?
Sam bata ga halamun samun k'wanciyar hankali
a gidan ba sai gun mama,toh ya sauran y'an
uwan nashi zasu t'ar6e ta? Tana tsoron
wukanci,musamman a gun mai kud'i. Anya zata
auri A A Ahmad?... Tuni wata zuciyar tace "Ya
ya zakiyi da kaunar shi fa? Shi kike so ba wani
abinshi ba, sannan dashi zaki zauna. Da wannan
tunanin yau tai bacci. Washegari sukuku ta
tashi,d'an ma wai bata fad'a wa Umma mey akai
ba. Ya Suleiman Umma ke nuna wa kaya wanda
ya shigo gaida su, d'uk yaga jikinta yai sanyi, sai
yake tambayar ba'asi tace ita wulakancin masu
kud'i take gudarma y'arta. Sannan tana gudun
bak'in jama'a. Baki yai ta bama Umman,kan ba
komai sai alkairi. Da mamakin ta da Abba yaga
kaya sai bai ce komai ba sai fatan alkairi, hakan
yasa itama Umman jan bak'inta tai shiru. Sosai
take jin fad'uwar gaba in ta tuno su Momy, Anya
kuwa? Sai d'ai so da kaunar AAA takan mantar
ta d'uk wani abu da zai je ya kawo. Shikam yana
komawa d'akinshi ya shige,dan yasan sarai
idonshi yau,idon Momy. Sai d'ai ita da taji shiru
da kanta tazo jin ba'asi. Dowawar shi daga
masallacin isha'i kenan ya k'wanta tare da bud'e
hoton Fure na dazun yana k'allo. Kofa ya ji an
turo, ba ko sallama, sai ya dago,dan dabi'ar y'an
gidan ce haka yasan,irin dabi'ar da ya t'sana, sai
d'ai da mamakinshi yaga Momy,tashi yai tare da
k'akalo mata murmushi, harara ta aika mishi kan
ta nemi waje ta zauna. "Wato dan ka'rma nai
magana shine ko abinci baka je ci ba? Toh ni na
zo, sanin k'anka zancen Rukayya ne a gidan nan,
ba wai na wata chan ba,amma abin
mamaki,yanzu Abban ku wai yasan da
zance,kenan har ina gidan nan aje maka tambaya
ban sani ba koh? Kasa yai da kai, hakuri kawai
yake bata, dan yasan Momy, in ta huce ya
lalla6a kayarshi. "Ba ma wannan ba, tukun ka
kula da k'yau kamin ka so yarinyar nan har kake
neman shigo mana da ita gida? K'allonta yake,
sai ya girgiza kai, "na sani ai.. "Momy ina sane
fa,Furera mun juma, ni ne kawai ban fad'a ba...
"Ka rufe min baki, in haka ne Rukayya ma kun
juma ai,kuma ni ita na sani. Kai ya K'awar, kan
yace"amma Momy tun ba yau ba na sanar ki
Rukayya ba kala ta bace fa,dan Allah ki bar
zancen ta,taje itama ta samu miji, ni na samu
m... "Ahmad, cikin t'sawa Momyn ta kat'se shi, "
ni zaka ciwa fuska? Kai yai kasa dashi, yau
zazzagar arziki ta mishi,harda dan ba ita ta haifo
shi ba.. sai ta tashi tai waje,yana ta kiranta ta
doko kofa. Kai ya girgiza, a gaskiya bai son
fushin Momy,amma akan Rukayya zai yi komai
dan ganin ba'a manna mishi ita ba. K'wanciyar
shi yai, yana mai tunanin iko irin na Momy,
tabbas lokaci yayi da zaiyi "breaking" wannan
t'sarin na shigo da y'ar talaka zuri'ar su, shi
Pretty yake so, kuma ita zata zame mishi mata
da ikon Allah, fatan shi Allah ya taya shi yakin
nan,dan maganar Momy da ita ake gudanar da
komai a gidan. Bangaren Mama yaje cin
abinci,tasan yau kam za ai haka, amma ita y'ar
k'allo ce a t'sakanin su. "Ya suka je gida? Baki
ya wage,tuni sai ya ji ya ware,"Mama lafiya. Sai
da ya gama ci kan ya k'allo Maman tashi, "Mama
ai d'ai tayi koh? Murmushi tai,tare da ajiye waya,
"tayi kam,sai d'ai ya zakai da Rukayya Ahmad?
Maman yake k'allo da nazari,chan yace "Mama
sam Rukayya bata min ba,Momy ce d'ai ta
dage... Sai jim, "amma Mama ki taimaken wajen
ka'rfafa Furera gun Abba,nasan Momy shi kad'ai
zai iya hanata yi min dole. Kai ta k'ada, sosai
take tausayin yaran ta,musamman yadda suka
k'waso dabi'ar Momy goyon Momy, guda d'aya
ya fita zakka ciki, akan Ahmad kam baza ta bari
Momy tai nasara ba InshaAllah, a wajenta da
talaka da mai kud'i d'uk d'aya ne. Sai d'ai tace
ya lalla6a Momyn. Sosai ya ji dad'i, shi yasa
yake kara kaunar Mama. Dan tana son abinda
yake so. Washegari kamar kullum yazo gaida ta
tai banza dashi tare da juyar da kai, sai yai
murmushi, kan yaje inda ta juya, tsugunawa yai
tare da dafa hannunshi a cinyarta, hakuri ya fara
bata,kan ba yadda ta d'auka yake nufi ba. Da
k'yar ya samu ta d'aina fushi,sai dai har yanzun
tana kan bakarta na Rukayya ta sani,k'yaleta yai
tare da lalla6a ta,dan a rabu lafiya. By Feenat
Ja'afar.
9/29/16, 2:27 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 19_Tun daga wannan
rana ya gama fito wa da Fure ainashin shi
waye,tarihin su,fa komai,har hamdala tai a
zuciyarta da taji ba Momy ce ta haifo shi
ba,hakan yasa ta ware suka cigaba da fahimtar
juna. Yanzu kam fachaka ya fara mata,sai d'ai
kullum in ya bata sai sunyi fad'a, wataran ma sai
d'ai ya kai wa Umma da kanshi. Sai dai sosai
yana jin dad'in yadda take nuna abin duniya bai
dameta ba. Chargy yasa a parlourn Momy yaje
masallacin azahar,Rukayya ce ta shigo parlourn
dan zaman charting. Sai ta kula da wayan
shi,kawai sai ta raya mata bincike cikinta.
Sunkuye take da kai tana murmushi ta d'an rike
g'yale,"eye lashes" nata sunyi zara-zara, hoton
ya manna a "screen" na wayar shi,
"Mtsww,banza kawai, sai ta k'ada kai, kawai sai
ta shiga cikin "gallery" ta hau "deleting" d'uk
wani hoton Fure da yai "editing" yasa "pretty".
Sai da ta goge d'uk "foldern'' kan ta shiga
"contact". Bataga wani sunan mata ba sai na
y'an gidan, ko numbern ta babu,sai ga "pretty"
ya fito, wayarta ta d'akko ta k'wafi numbern tana
surutu ita kad'ai, tana gama k'wafa tai "deleting",
ta ajiye wayar kamar ba'a ta6a tai ta zauna. Bai
shigo ba sai bayan la'asar, shima sai da ya
tabbatar ya gama shirin zuwa gun Fure yazo cire
chargy, "blank" ba komai kan screen d'in, sai yai
tunanin "memory" ne ya goce,yana k'allonta yai
kamar bai ganta ba,zama yai g'yara memory, ita
kam dariya take kunshe wa, yanayin shi d'uk ya
sauya,fuska had'e ya k'allo ta,da sauri ta gintse
dariyarta ta d'aina K'allonshi. A masife yai yo
kanta, "Kina hauka ne?...Yaushe na zama abin
wasan ki? Tashi tai tana k'unk'uni, "mey na ma
toh? Wayar ya k'alla,ji yake kamar ya rufe ta da
duka,ihun da yake wa Rukayya ne ya fito da
Momy, yana ganinta bai hana ya gama sauke
komai ba, "lafiya? Kai kawai ya gad'a yai
waje,yana fita ta hau dariya. Abinda y faru ta
fad'awa Momyn,tace ta mata d'ai-d'ai. A mota
t'saki kawai yake,Allah ya so shi ya tura su
"system" nashi, a hakan zai yarda da auran
Rukayya? Yarinya marar K'wak'walwa? Yai t'saki.
Da k'yar ya seta kanshi kan yaje gun Fure. Ita
kam Rukayya yana fita sai tai tunanin ba gun
Fure za shi ba, cewa Momy tai tana zuwa,
d'akinsu tai,ta k'wanta kan ta fara kiran layin
Fure. A zaure suke,kamar kullum suna tad'in su
cikin nishad'i,ga Amal a gefe tana mota. Wayan
Furen ne tai kara,sai ta k'allo shi da murmushi,
kai ya k'ada mata, dan ko shi aka kira in dai suna
tare sai ya nemi izinin Pretty kan ya daga.
Number ce, cikin nutsuwa tai sallama, sai d'ai ita
daga chan da zagi ta bud'e taron. Yadda fuskarta
ta sauya ne yasa yake k'allonta, sai ta k'ak'alo
murmushin dole tana cigaba da sauraran
Rukky,batasan speakern yana d'an ji kad'an ba.
"Kina magana da Rukayya matar Ahmad bada
jimawa ba.. "Y'ar matsiyata kawai, ai nasan
kinsan ba ajinki bane shi, ki fita gona ta,dan Ya
Ahmad nawa ne ni kad'ai... "Nice zabin y'an
gidan nan, so tun wuri kisan inda dare ya miki..
Tashi tai,da hannu take nuna mishi tana
zuwa,tana shiga d'aki tana jin yadda take aikawa
iyayenta zagi. Murmushi tai, kan tace "Furera
ikon Allah,toh a gaskiya bazan iya musayar yawu
da wacce bata isa inda take tunanin ta isan ba...
"AAA na Fure ne kad'ai, wallahi k'walelen
ki,tunda anyi k'wantai a fad'i haka man... " uban
wa yai k'wantai? T'saki Furen tai, kan tace"Allah
kat'se miki wahala, dan kin haukace... Kit ta
kashe wayarta. Kanta ta g'yara,kan tai zauren
d'auke da murmushi, kawai Rukayya y
bada,amma da mamakin shi sai tace wai "wrong
number" ne,shi d'ai yaji sunan Rukayya a
wayar,kawai sai ya share suka ci gaba da tad'in
su. "Sai rowar hoton nan ake min,yau d'ai a
d'akko min naga. Kai ta k'ada, kan ta tashi,
dama dan ya d'au number ne, cikin sauri yai
copying zuwa wayarshi yai dailing sai ya kashe
da sauri. Har ya tafi bata fad'a mishi komai ba.
Yana zuwa parlour ya zauna,lokacin Rukayyan
tasa chargy, dailing ya fara,sai yaji a rufe,kawai
sai yaje ya duba,a rufe take,dan ya tabbatar ya
k'unna, sai k'wa ga kira ya shiga. Da gudunta ta
fito,a zatan ta,murmushi kawai yayi,ya ajiye ya
wuce. Sai d'ai a ranshi ya sa zai bawa Rukayya
mamaki,dan ko zata mutu bazai aureta ba.
T'sawan kusan wata 7 yanzu kenan da had'uwar
su, biki saura wata d'aya dan tana exams, amma
naira biyar bata ta6a rokarshi ba, shi yasa yake
d'aukan Fure ta daban cikin mata. Hakan yasa
yau yace zai g'wada ta, suna a zaure suna tad'in
su cikin so ya k'allota. "Pretty, kai ta dago tare
da amsawa, sai ya k'alli Amal da ta zuba musu
ido,sai yai murmushi, " ga nan biki sai karato wa
yake amma baki nemi komai ba. Murmushi tai,
kan ta k'alli gefe, "Yanzun kam bana bukatar
komai gaskiya, in ma za'a bukata su Ummi zasu
ma magana. K'allonta yake, yasan in ya biye
mata da gasken bazata tambaya ba, "toh ke da
kanki ba ki bukatar komai? Nasan dasu Ummi, da
pretty nake. Murmushi tai, kan ta k'ada kai,
"eh,na sani. Kai ya k'ada, sai ya tashi yace ta
d'an jira shi, ya nufi mota. Da babbar leda ya
dawo,d'auke da k'wali a leda. Ita d'ai nata ido,
"karan nan pretty ban son musu, kai ta daga, sai
ya ajiye mata ledar kayan a gabanta kan ya
zauna da dayar. Zaro k'walin yai,sai ga nan waya
zankadediya ta fito, sai ya cire recit d'in kan ya
mika mata. Idon shi take k'allo, sai yasha
mur,dan yasan yanzu sai tai mai musu, k'ar6a tai
kan ta tsaya neman ba'asi. "Ta ki ce,en bana son
musu, wayar take juyawa,koh wata uku bai yi da
siya mata ta hannunta ba,sai d'ai ba bak'in
magana. Takalma ne kusan kala uku masu k'yau
dad'in zuwa "dinner". Sai kud'i aciki masu yawa,
text taji ya shigo wayan ta,wai ta amfani da
kud'in. Sai tai murmushi, ta kaima Umma su,dan
dama takalmi da sarka ne kawai bata siya ba.
Ginin su Abba fenti kawai ya rage, Umma tafi
kowa murnar su tare ko dan auren Fure. Ana
saura k'wana goma biki ya sanarta y'an gidan su
zasu suzo kawo kaya. Gidan Adama taje dan
Aisha tana fama da kanta suka musu pepee
chicken. By Feenat Ja'afar.
Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 23
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 20_Ganin kayan auren
Ahmad ba karamin kuka Rukky tai ba, bori take
na gaske,wannan karan kam anfi k'arfin
Momy,dan Abba ya shiga zancen dumu dumu.
Hakuri kawai take bata,kan ko ba yanzu ba
kamar ta auri Ahmad an gama ne. Washegari
mota hudu sukai dan zuwa kai lefen Fure,daga
nan zasu kai na d'ayar amaryar k'anin Ahmad.
Tunda aka t'saya a kofar suke tantama, "anya
nan ne? Waya Aunty JIDDA ta d'auka, kan ta kira
Ahmad d'in, "ka yi k'watancen nan d'ai-d'ai
kuwa? Jim tai tana sauraran shi, kan ta k'alli
sauran y'an uwan nasu da y'an uwan iyayen su.
"wai fa nan ne,har nanata min yake wani gidan
kasa mai zaure.. Tai k'wafa,tunda naji artabun da
ake dashi nasan ba haka aka bar yaron nan
ba,yanzu ki duba wai gidan da zamu kai wannan
uban kayan? Wato shi yasa yake boye ta fir yaki
kawo ta mu gaisa. T'saki Huwaila (Sa'adatu)tai,
"Aunty shi fa ya jiwo, ku y'an aike ne, suma
sauran d'uk jikin su yai sanyi,banda y'an uwan
mama, wanda ta sanar su komai. Bai fi mutum
uku bane sukai sallama,kowa fuska d'aure,sosai
suka rainawa Ahmad, karewa gidan k'allo
suke,Fure dake d'aki tana leken su ta window,
daga mai ta6e baki,sai mai y'atsine fuska,kalilan
ne aciki wanda fuskarsu a sake, zama tai a kan
katifa, ganan abinda taki jini,raini,wato sun raina
mazaunin ta? Zaman kirki basuyi ba aka basu
tsarabar su da tukuici,y'an uwan mama ne suka
k'ar6a harda godiya,sukam tuni sunyi waje. Allah
ya so su makociya d'aya ce,sai y'an uwan su na
Zaria, dasu Adama da Aisha, kowa jikin shi yai
sanyi da dangin mijin da Fure zata aura,barin
Umma. Kaya ne gasu kamar ba gobe Ahmad
yasa aka tulo su,sai san barka. Da dare suna
zaune har da Furen ana nunawa Abba kaya, ita
d'ai Umma roko take ai ai fenti su tare ko a
daina ma y'arsu gani gani. A ganinta wai Tuwan
girma miyarshi nama. Murmushi Furen tai da
d'an guntun hawayenta, kan ta k'allo su Umma,
"Umma d'an guntun gatarinka wai yafi sari ka
bani, ni d'ai ina alfari da tushe na... Hawaye ta
goge, k'warai auran nan ya fice mata aka, ji take
tamkar tace ta fasa. ''Abba dan Allah ko an
gama komai kar ku tare sai bayan bikin nan,
Umma nan ne asalinmu, dan Allah a min wannan
alfarmar, mu zauna anan, ba ruwa na da zancen
su, tunda d'ai shi ya ji ya gani. Murmushi Abba
yai, shi yasa yake alfahari da Furen sa, d'uk D'a
na k'warai mai kishin tushen shi ne k'warai. Kai
ya jinjina, kan ya k'alli Umma da jikinta d'uk yai
sanyi. "Nima nayi tunanin nan,kiyi hakuri Umman
su,kiji kawai ki kiji, har a watse lafiya. Kai ta
jinjina, sai Furen ta basu waje,bata jima da shiga
ba sai ga kiran Ahmad d'in. Yadda take amsa
wayar yasan tabbas tana a damuwa, wanda
yasan bazai wuce na y'an gidan su ba. Dan
yanzun barin cikin gidan suna ta kace nace akan
gidan su Fure,su basu ga abin zagwadi a y'ar
gidan ba da har zai ki Rukky. "Kiyi hakuri pretty,
ni ne mai auren ki,InshaAllah zaki same ni mai
rike amanar ki cikin aminci. Da mamaki take
sauararen shi, da sannu sai da ya wanke laifin
y'an uwanshi cikin lumuna, har taji zata iya ji ta
gani wajen zama dasu. Haka k'wa akai,gini ya
kammalu amma Abba yace sai bayan biki, y'an
uwa wasu na neman ba'asi sai yace musu kawai
ba dalili. Fatan shi Allah yasa alkairi cikin auren
Furen shi,kodan mutuncin Ahmad a gun shi, ko
da Ya Suleiman yace ma Adama su su tare sai
tace mishi abari su tare dasu Umma. By Feenat
Ja'afar.
Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 23
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 21_Gaban madubi take
a gidan Aisha,kowa yana yaba yadda tai k'yau.
Yake kawai take musu,sosai itama tasan tai
k'yau, "net" ne "brown" da ratsin "golden" na
doguwar riga yai mata cif-cif. An nada mata
g'warg'waro shima "golden", a d'aya a takalmin
Ahmad da ya bata kan biki ta d'au wani ubansu
"golden" ta sa,kai kace da "gold" akayi shi,rike
da "poss" irin takalmin. G'yaran jikin da ta samu
ne yasa fatarta kara gogewa ta dawo ruwan
itama "golden" d'in, sosai ta barar da k'yau a
wannan rana, idon nan kad'ai ke fari kamar tai
"fixing" na "lashes", ga yasha "Eye shadow" abin
ba'a cewa komai, a gaskiya in kaga Fure a ranar
bazaka d'auka ba bikin wata y'ar Attajirin
bace,komai ya ji,an t'sat'so k'yau sosai. D'uk
wani sukuku take jin ranta tunda aka d'aura
auren. "Dinner " za su, wayan ta ke kara
tsohuwarta ta da, sam a ganinta in ta rike
sabuwar kowa yasan daga gun shi ne, sai ta bari
sai ta shiga daga gidan shi ta fara amfani da ita.
Cikin sanyin murya tai mishi sallama. Sai ya
jingina a jikin kujera jin muryar har k'wanyar
kanshi,Ilyass dake tuki yai murmushi. Har cikin
gidan Ilyass ya shiga,kan amarya ta fito da
sauran k'awaye. Kanta kasa suka fito ita da
Aisha da Adama, da kanshi ya fito daga gaban
motar ya bud'e mata gidan baya. Shima sai ya
zaga d'aya bangaren, dariya suka hau mishi,sai
Ilyass yace Aishan ta shiga gaba suje Adama ta
jira mijinta, sauran suka shiga suma mota. Tafe
suke Ilyass na ta musu shakiyanci sukam sai
murmushi suke, a hankali ya k'allota,sai tai kasa
da kai tana murmushi. Yasha riga malum-malum
na farin shadda,an mishi aiki da zare brown, yai
k'yau sosai,hular shi ma "brown" sai kamshi yake
zubawa. Sosai yake k'allonta dan tun jiya rabon
da ya ganta har aka d'aura Aure, wanda ita har
kunya ya fara bata. Hannunta yake k'allo, wanda
suka sha "bangles" manya kamar na gold da
zobuna manya. Ga kunshin nan ya hau kasan su
sai suka mishi k'yau. Bata aune ba taji shi rike
da y'atsunta, tuni taji wani abu ya tsirga
mata,yayinda gogan ajiyar zuciya ya saka, yasan
ya kare iyakar Allah sosai,yau ne farin ta6a
hannun macen da ba muharama sa ba, gashi