Author : Queen Safiyyert Category : Romance
yau
ta zama mallakin shi halali. Shi ko wannan "pre-
weeding" pic d'in da ake d'auka a rungumi juna
sam bai mishi ba, dan a ganin shi duk abinda zai
kai ka ga sa6on Allah sam bai burge shi. Yadda
take lumshe ido d'ayan hannunta na kan bak'inta
sai ta kara kawatuwa mishi, dole yace"D'ukkan
godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, ya gode
Allah da yau Prettyn shi ta zama tashi a yau. Har
suka isa gun "dinner" yana rike da hannuntan.
Suna tsayawa akazo bud'e musu kofa, sai ya
daga musu hannu kan shi zai bud'e mata, hooo,
kowa ya birgisu, hannu ya mika mata wai ta rike
ta fito, ganin an d'aura yasa ba musu ta bashi,
sai d'ai fir yaki cika mata hannu,a haka suka jera
cikin "Hall" d'in kanta kasa d'auke da murmushi.
Tuni su d'ayan Angon sun hallara da amaryar shi
su kawai ake jira. "Flashes" ake basu ta ko'ina,
Fure fa ta bada kala,dan ko y'ar masu kud'in
bata fita da kom ba sai d'ai k'yau. Su kansu su
Aunty JIDDAN sai suka ga shigarta tafi k'yau,
amma haushinta ya hana su yaba. Barin Rukayya
ganin su rike da hannun juna kamar ta kurma ihu.
An fara program aka umarci ango da Amarya su
fito su yanka "cake". Hannunshi na kan nata
suka yanka, cikin jin kunya ta sa mishi a baki, da
wasa shima yake kokarin sa mata ya dan shafi "
lips " nata,kowa ya zuba musu ido,ba kunya ya
kai hannu zai goge mata sai ta dan k'alleshi, mai
hoto kuma ya d'auka a hakan. Sosai sunyi k'au,
Ahmad yana ta barin SO a hall, yayinda masu
t'saki nayi masu murmushi nayi,masu musu tafi
sunai,su Rukky kam baki ta ta6e. Rawa aka ai
bayan an cigaba da "program''. Kai ta girgiza
mishi, sai ta burge shi, ita kam d'ayar amaryar
sai taka rawa take ita a dole wayayya ba ko
kunya. Ana tashi ya k'arbi "key" wai shi zai kai
matar shi. Sukam su Ya Suleiman nasu dariya
ce. Ba musu ya mika mishi mukulli. A hankali
yake jan su a sabuwar motarshi da siya musu shi
da Prettyn shi, ita kam yau d'uk kunya yake bata.
Shi yasa kanta na k'allon glass d'in gefenta da
murmushi. Ba tasan irin farin cikin da yau take ji
ba. Ga wata kauna da taga Ahmad na nuna mata,
wanda a ganinta koh ita ta isa sata tai zaman
auren shi. Wakar shi ta kullum ya sauya, tuni ta
fara taken "Nothing gonna change my love for
you.. If I had to live my life without you near me
The days would all be empty The nights would
seem so long With you I see forever oh so clearly
I might have been in love before But it never felt
this strong Our dreams are young and we both
know They'll take us where we want to go Hold
me now Touch me now I don't want to live
without you. Jingina tai tare da lumshe ido cikin
murmushi, sosai baitin ke shigarta,sai ta tuno
wani lokaci achan baya,kawai bata nufa ba taji ta
dara,har hak'waranta suka baiyana, d'ai-d'ai taka
burkin da gogan yaci. Da sauri ta bud'e ido jin
sun tsaya,dan baici ace sunzo ba. Taga titin ba
abinda ya faru, sai ta juyo da k'allonta gare
shi,tagumi ya da hannu d'aya yake k'allonta, sai
ta daga mishi gira halamar lafiya?... Kar ya
fad'arsu yasa ya taka birki. Kai girgiza mata, tare
da sauke ajiyar zuciya. Shi kanshi bazaice ga
adadin son da yake ma Pretty ba,sannan wakar
nan tana kara rura wutar Sonta ne a kullum.
Matsowa yai da fuskar shi d'ai-d'ai tata har
numfashin su na had'uwa da na juna, sai taja
tata baya tare da K'awar da kai tana murmushin
kunya. Hannu yasa ya juyo da ita,sai tai kasa da
kai, a hankali ya rage "volume",tuni ya hau tsuma
zuciyarta da kalamai wanda bata ma san ta dago
tana k'allon shi ba. K'warai sakon aiken ido yafi
isa cikin sauri, hakan da tai sai ya bashi damar
aika sakon shi tanan. Gaba d'aya sai da ya gama
kashe mata jiki da tad'in shi,wanda ita bata san
ya iya irin shi ba,sosai yakance yana Sonta har
ba iyaka, amma kalaman yau na daban ne.
Karshe sai da ya sada ta da jikin shi ya samu
sa'ida,ita kam lum tai kamar ta samu pillown ta.
Chan kuma sai ta hau kiciniyar K'wacewa, d'uk
da glass d'in baki ne. Dagowa yai da lumsassun
ido yana duben ta," yanzu sai gobe za'a kai min
ke? Kai ta lang'wa6e mishi, cikin marairaita. Sai
ya zuba ma bak'inta ido wanda yasha janbaki mai
k'yau "brown'' mai shekin golden, ganin ya kawo
fuskarshi tata yasa ta saurin rufe ido. Sai ya
tsaya k'allonta da murmushi, ganin yadda ta wani
tamke ido,hannu ya kai kan idon sai ta bud'e a
hankali,bata aune ba taji sabon al'amari, ba shiri
ta kara rufe idon. Shikam kamshin strawberry ma
kamar yake ji a bak'in,ga dan zakin "lips" d'in
nata. Dan kanshi ya batta,kan ya hau cigaba da
kallonta, idon nan a rufe... "Horn" d'in su Ilyass
ne da har sun gama sa jama'a gashi har sun
cimmusu suna nan. Take sai tai gefe da kanta ta
boye cikin kunya,kai ya k'ada, kan yai murmushi
ya tada mota. Yasan yau sai d'ai ya toshe
k'unnenshi agun Ilyass,tunda har ya cimmasa. By
Feenat Ja'afar.
Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 23
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 22_Har suka rabu taki
bari ya ga fuskar, Ashe AAA haka yake? Hmm ita
kuma ga kunya. Haka ya hakura sukai sallama
yana fad'in "I Love you... Jim tai,kan ta shiga
gida kamin ya k'ada kai shima ya wuce. Lekowa
tai daga zauren da ta la6e , sai ta koma ganin ya
wuce ta jingina da bango cikin murmushi ta dafe
kirji tana maida numfashi,tamkar wacce tai wani
tseren. A hankali ta kai hannunta kan "lips" nata
tana tuno dazun, "Love you too AAA,wai kuma
sai tasa tafin hannu ta rufe fuska ita a dole
kunya, sai ta k'ada kai tai cikin gida. Tuki yake
yana shafo "lips" nashi,harda dubawa a "mirror''
yana murmushi. A hankali ya sauke ajiyar zuciya,
" Furii" "Pretty"..sai ya sau murmushi, kan a
hankali ya furta "I Love you" kamar tana k'allon
shi. Biki anyi cikin aminci, sai d'ai har aka gama
ba wanda ya kara leko kafarshi gidan su Fure sai
y'an uwan mama da Abba, hatta d'aukar amarya
basu zo ba,sai suka tafi d'aukar d'ayar amaryar.
Haka Fure naji aka tafi da ita ta rabu dasu
Umman ta. Sai d'ai fatan Allah kad'ai hau. Y'an
mata aka kai,ba tare da tsayawa wani siyan baki
ba,a ganin sun wuce ajin inji Ilyass. Wasu suka
tsaya yiwa Ango da Amarya fad'a. Yana rakasu
ta koma d'aki. A gaskiya iyaye sun mata ba zata,
sam bazakai t'sammanin ba y'ar masu dashi
bace,d'uk kamar wanchan karan karan nan ma
kawunsu na Zaria ne ya mata gado da
kujeru,shikam da zamani yake tafiya, shi yasa
koman su tsaf-tsaf. K'wance take tana kara
duben yanayin d'akin,sai ajiyar zuciya take na
wacce taci kuka, sosai ya mata k'yau, ga wasu
arnun labulaye, Allah sarki Abban ta da Ya
Suleiman, Yanzu ta yarda da wadatar zuci tafi ta
kud'i. Fatan ta Allah ya kaita lokacin da zata
rama musu itama. A haka har ya cimmata a
d'akin. Tsayawa yai yana k'allon ta, sai ta tashi
ta takure kanta tare da jingina a jikin allon
gadon. Sallama yai,sai ta duk'ar da kai ta amsa,
zama yai kusa da ita yana k'allon yadda d'uk ta
bata k'walliya da kuka,, shi a kullum yana da
tambaya ga mata,wai shin mey ke sasu kuka in
za'a kawo su gidan aure? A ganin shi farin ciki
yafi kamata suyi su kuma gode wa Allah. Hmm..
Bazaka gane ba AAA. Ya ya iyah,aikin lallashi ya
hau yi, sai d'ai dama bai ba,dan kuwa ya
jang'wa6o ta. Kuma fa ta manne mishi,amma
tana fad'in su Umma...Lol. Kamar wata yarinya
ya hau hura mata k'unne. Tuni k'wa sai ta nemi
kuka ta rasa,ya tafi garin su. Da dabara yai ta
janta har ta ware tana murmushi k'eta. A haka
har suka gabatar da da sallah kan ya d'akko
komai a "parlour" da "plate'. Haka ba dan dad'i
sai dan ya mat'sa mata taci kad'an. Ta tashi ta
k'washe kayan,a kitchen ta t'saya k'allo, lalle
duniya,wani abin ma bata san dashi ba. Ga nan
"gas cooker" da halamun mai gidan yasa. Dan
harda gidan ta. Ya shiga d'aki ta dawo parlourn,
shima ba laifi an mata bajinta d'ai-d'ai k'arfi,
kujerunta masu "Ledar" ne kalar 'Orange' da
"milky" labulan ma haka, ga dan "center carpet"
nata mai "grass" da "table" mai zanen "heart" a
jiki. Sai TVn ta "plasma" manne, sun had'a mata
"home theatre" dai,ga nan wata "flower" a tsaye
kamar g'wada da da ya'yanta "Orange''. Ajiyar
zuciya tai,jin an bud'e kofa. A hankali ta zauna a
kasa,yayinda shi kuma yai wajen TV, ashe har
sun had'a. Kujerar da take ya dawo da "remote"
a hannunshi, sai ya tasa kanshi a cinyarta yana
k'allon fuskarta da murmushi. Itama murmushin
take,amma cike da kunya, sai ya juya kan TV ya
d'anna "play". "Title" taga na "My heart will go
on... Wani page ya fito da ire-iren pic din da yake
d'aukan ta ta daga kai sama tana dariya har
hak'waran ta sun fito, Sai ya rubuta. To my
darling Furii.... Sai ga nan wakar "Celine Dion" na
"every night in my dream tana yi cikin "slow
motion" ta fara. Wani pic d'in ya shigo shima tai
k'yau, a kasa yasa.. "I have been in love with you
from the very moment I met you and every day I
continue to fall deeper in love with you".....
K'allonshi tai, tama kasa magana,dan sam wasu
ma bata san an d'auka ba,sukanyi dai fira
wataran taga kamar yana d'aukar ta hoto. Har ya
kare yana mai fallasa mata sirrin ranshi ne kawai
a gare ta,sosai ta gamsu da ganin abin, ya
kayatar ta.. K'allonshi kawai take tana tunanin da
gaske tun had'uwar su ta farko ya fara Sonta?
Ganin k'allon ba na karau bane yasa ya dawo
fad'i da bak'in shi, ina Fure bazata iya d'auka ba,
dan bataji ko ita tana mishi irin wannan son da
yake ta k'wadata da shi. Kan su farga har dare
ya ja sosai,tasan in zasu k'wana haka yana fad'a
mata irin kalaman nan toh bazata gaji da
sauraron shi ba. Ahmad kam karshe ne, ya kere
ta a komai, sai d'ai ya zame mata dole tai
ko'k'arin finshi iya kalami, a ganinta ita ya dace
ta haddace. By Feenat Ja'afar. 庐NWA.
9/29/16, 2:28 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 23_K'allon yaje ya
kashe,dan jin TV na kukan a kashe ta ta kare,
sai ya ajiye "remote" d'in tare da juyo wa gare
ta, shi take k'allo, sai yai murmushi tare da zuwa
da t'sugunawa a gabanta kamar mai neman tuba.
Abin ba na magana bane a gare su, sai yasa
hannu ya ware g'yalen da ta nad'a, ya cire
d'ank'walin, sai ya ciro da ribbons d'in da ta
tufke kanta da ya sha "relaxer'' d'ai-d'ai fankar
"parlourn" ta k'ada gare su,tuni sai gashin ya
fara tashi, ina gogan baki ya saka,ganin yalasha,
tare da fad'in "SUBHANALLAH.... Hannu tasa ta
rufe fuska,dan sai ya bata kunya ma, cikin ranshi
kuwa,fad'i yake "Lalle t'sarki ya tabbata ga
Ubangijin Sammai.. Ubangijin d'aya k'era mishi
FURIIN shi mai saukin k'yau a baiyane, sannan
mai t'sananin k'yau a ciki.. Ashe Allah idan ya
hana k'yaun fuska,sai kaga ya baka k'yaun jiki...
Yanzu ya yarda kowacce mace mai k'yau ce, ina
ma Y'an uwan shi zasu d'aina zaban k'yalk'yal
banza, suje su lalumo irin wanda basa so da yai
imani su da auren mai k'yau sai d'ai-d'ai... Shidai
yace "ALHAMDULILLAH.. Ganin irin "postern'' da
yai yasa ta zamu itama tai yadda yai, sannan ta
hau fad'in cewar ita ce fa,ba wai sabuwa ba. Sai
yai murmushi kan ya tashi t'saye,sai ta bishi da
k'allo, hannunta ya riko tare da tasarta t'saye
suna fuskantar juna. Jin ba zaya jure ba yasa
bata nufa ba taji ta asama ya d'auke ta kamar
wata baby, sai ta sunne kai kamar marar lafiyar
da aka d'akko ta kasa tafiya. Gun fanka suka
je,sai ta mika hannu ta kashe, tare da sak'alo
wuyan shi. A gado ya zaunarta, sai shima ya
zauna tare da shafo kanta, halamun d'ai gashin
ya mishi, sai tai murmushi tare da sadda kai
kasa tana wasa da awarwaron ta. Sai shima ya
kama hannun, a hankali ya kai shi d'ai-d'ai fuska
yana k'allon filawar da ta fito da taimakon
hasken "bed lamp",cikin nutsuwa ya fara zame
su a hankali, babu magana sai d'ai murmushi.
Sannu a hankali har d'an k'unne ya tayata cire
wa,,kan ya cigaba da rera mata wakar dake
mantar ta kanta ma, sosai in da so,toh komai ya
kan tafi a sauki, sai d'ai fa Furii rakin nan daga
baya yasha shi, tushe k'unne kawai yai, kan daga
baya ya ji da lallashin. Asuba nayi ta bud'e ido,
yana rike da hannunta ya durkusa gabanta,kamar
mai neman ta inda zai fara tada yake, murmushi
ya sau mata,tare da kai hannu ya g'yara mata
gashin ta,sai ta k'au da fuska itama da
murmushin,sai dai hawaye na k'waranya. Ganin
har za'a tada sallah yaki tafiya yasa ta yunkura
zata mike, sai ya taso dan taimako, kai ta
girgiza, kan tace zata iya. Da k'yar ta lalla6a ya
tafi,kan tai dabarar tashi. Yau d'uk sujjada sai
Furii ta samu adu'a, har bazai ce ga adadi
ba,fatan shi Allah ya basu zuri'a da Fure daiyiba
masu t'sant'sar tarbiya irinta. Kan ya dawo ta
kimt'sa komai har ta kara k'wanciya. Haka ya
shigo da allura daga d'akin shi, macen dake
kunyar shi sai gata ta hau waro ido... Sai ya hau
lallashi,kan tai hakuri ba da zafi zai mata ba, kai
ta k'ada, kan a hankali ta tashi, tsinin allurar
kawai taga ta fara yarfe yat'sa. Hmm,tana kai
miki Fure. By Feenat Ja'afar.
Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 24
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 24_Soyayya suke kam
kamar babu gobe, a satin su Umma da Ya
Suleiman suka tare a sabon gida, amma fur
mutumin yace ya gano mata gida ita sai tai
wata,sai dai satin ta biyu taje,gida kam yayi,d'uk
da ba wani kato bane amma d'ai ya ninka nasu
na Zaria ma na da,katon parlour yasa aka zana
ma su Umman,ba wani kayan azo mu gani ba
ne,amma tsarin yayi, y'ar TVn su "standard" da
"dish" domin k'allo, kujerun su ma d'ai dai
k'arfi,sai t'sakiya "Chinese carpet",da "tiles" sai
"shining" yake,aciki yai musu "3 bedroom"
Kowanne da bandaki a ciki,da kitchen din Umma,
sai waje yai d'akin su Hassan guda biyu, da
"public toilet" t'sakar gidan y'ar madaidaiciya, ya
zuba musu "interlock". Sosai ajiya tai rana, filin
makotan su Abban Ya Suleiman ya siya,katanga
kawai ta had'a su,sai ya fidda kofar yadda zai
iya zuwa ma kowa. Randa suka tare murna
gunsu ba a cewa komai,dan kam ko yaya sabon
waje ak'wai k'yau. Da ta cika sati biyu ya batta
taje ganin sabon gida,d'uk da shi zuwanshi 2.
Ana haka azumi ya kama, sosai yana taimakon ta
ga kuma Maryam, dan "store" gare shi na delar
magani babba, d'uk da yakan je asibiti jefi-jefi,
amma zuwa shagon yafi,sannan yana da masu
kullar mishi,yanzu burin shi su Hassan su gama
secondary ya d'aura su kai, duk da ko ita FURIIN
bai sanarta ba. An gama azumi lafiya yau ta
kama sallah, t'saye yake gaban "mirror" ya daga
kai tana 6alle mishi ma6allin rigan shi, tana
gamawa ta wuyanshi da hannunta tana
murmushi, sai ya dago jin ta gama, "kai k'yau
sosai.. Ta karasa tana k'allon wuyan, juyarta yai
gaban mirrorn suna k'allon Kansu aciki da
murmushi, sai ta bashi sarka,cikin nutsuwa ya ke
6alla mata,sai ta shafo wuyan ta mudubi tace"
thanks. Murmushi kawai yai tare da d'auro kanshi
a kan kafadarta, fuskarshi ta shafo, "hala yau
azumin magana kake? Murmushi yai tare da kara
juyo ta, "kinyi k'yau ne shi yasa banson kat'se
k'allon ki da magana,ki gane ke d'ai, ya ruko
k'ugunta,sai tai kasa da kai tana murmushi,
idonta ya manna "lips" nashi,yana son yaga tai
d'an kasa da kannan tana murmushi, sai yaga
kamar "eye lashes" nata na karu wa. Hoto yai
musu,kan sukai shirin zuwa masallaci. Ana idar
da sallah ana huduba ta ciro waya tana mishi
"Happy Sallah" sai ga nan nashi, sai tai
murmushi, tare da goge nata tai mishi mai
sanyaya rai ta tura. Yau wanda bata ta6a gani
bama a abokanshi sunzo k'wasar gara, Furiin shi
abar alfaharin shi ce wajen girki,shi yasa ba
musu ya barta ta cigaba da makarantar ta. Tana
daga kitchen ita da Maryam,suna jiyo santin
su,sai kara fasa mishi kai suke, bak'in nan har
k'unne, Furii ta fitarshi kunyar Abincin sallah.
Washegari tai ma su Mama da Umma lafiyayye
su ma, "flask" daban tai wa Momy, Mama ma
haka. Lokacin suna parlour Abba yana ta fad'an
jiya basui abinci ba, yauma da yunwa zasu
barshi? Sam ya t'sani abincin y'ar aiki,yar aiki
mai girkin taje hutun sallah,ga Momyn ce da girki
tun jiya,nufin shi tashi yai bangaren Mama sai ga
nan flask daga Fure, shak'e da sinasir da wata
hadaddiyar miya, taji kaji,da murmushi Abban ya
k'alleshi, lokacin da yake gaida su, a gaban
Momy ya ajiye k'wandon. Da fara'a Abban yace
mishi "mey muka samu ne Abba na? Baki Momy
ta ta6e, sai yai murmushi, "Abba abincin sallah
akace na kawo muku.. Da fara'a ya k'alli Momy,
"Maryam bani,zuban naci anan ma,dan fita zanyi,
yai nufi kan "dining room'' d'inta. Ba dan ta so ba
ta d'au k'wandon tai kan "table'' d'in, tana bud'e
"flaks" kamshi ya doki hancin su,tuni Abba ya
fara tattare hannun rigar shi, Ahmad dake gefe
ya girgiza kai yana murmushi, sai yai "kitchen"
d'in Momyn ya tarowa Abba ruwan wankin
hannu. Zai fito sai ga nan momy,itama shi zata
d'ebo,harara ta sau mishi kan tai hanyar d'aki
dan jin haushin zag'wadin uba da d'an akan
abincin Fure. A kusa da Abban ya zauna,sai wani
lumshe ido Abban yake yana k'wararo santi.
Shikam gogan abin nema ya samu, yasan ko
waye in yaci abincin Fure sai yai santi. "Baba na,
da murmushi Ahmad d'in yace "Na'am Abba, sai
da ya kara yankar sinasir ya d'ang'wala a miya
kan yace, "amma makarantar koyan girki iyalin ka
take.... Haba wa,mai Ahmad zai in ba dariya ba,
Abban yace"Allah kuwa,, dake Abba cikin yaran
shi Aboki yake zamar musu. Kan ya farga yaci
tayi biyar, kira yake abarnan kamar an sa mata
madara. Shidai Ahmad baki yaki rufuwa. Tare
suka fito da Abban, shi yai mota,shi kuma ya nufi
bangaren su Mama. Yau ita kad'ai ce, Ummi d'uk
sun fita dasu Rukayya. Kok'arin tashi take ta
d'aura girki sai ga nan sallamar Ahmad d'in. Suna
gaisawa yace ga nan abincin inji pretty, cike da
jin dad'i ta bud'e tana godiya. Abinda sirikan
gidan basu ta6a ba kenan, wai kawo abinci ko
abincin sallah, su ganin su bata lokaci ne ma.
Sai ga Fure da bata ma fi wata da sati biyu ba ta
kawo sabon sauyi. Labarin santin Abba yake ba
Mama suna dariya. Tace "nima dama ko'k'arin
tashi nake na d'aura kan yaran nan su dawo.
Sosai Mama ta yaba da zabin d'anta, ganan
yaran nasu da suka taso cikin d'aular ba wacce
zata ma abinci mai dad'i, su d'ai barsu a mai aiki
sai ko dafa indomie. Ita kam Momy su Abba na
fita ta dawo parlourn, d'uk kamshin miyar Fure ta
karad'e mata "parlour", sai ta hau t'saki, da
mamakin ta Alhaji yaci da yawa da ta bud'e,
gashi fa itama ranta ya biya, amma sam taki koh
ta6a miyar. Tana nan a parlourn taji hayaniyar su
Rukayya, kana ganin su kaga sun k'waso gajiya
da yunwa. A kan abincin Rukayya ta
sauka,Huwaila ta zauna kusa da Momy, tana kai
loma d'aya ta hau lumshe ido, taji abinci ba irin
na Iyabo mai aiki ba. "Kai,"delicious".. Hannu
baka hannu k'warya ta fara ci,sai ta k'allo
Huwaila, "ka'r kiyi missing.. Da sauri itama tai
kan table d'in, daga t'saye ta d'an dana, a zaton
ta ko ba dad'i, ai tuni ta ja kujera.. Sai da sukai
nak,