BACCIN SO BY M SHAKUR

Author :  Category :  Romance

Chapter   49 / 51

144K to 147K   out of 150.2K words

koda komi a mota har wayanta sun dauka ga daya na fitowa daga kitchen dinta dabatasan mesukajeyi a kitchen dinba, yace  bani tape the same ragowan tape da aka rufe bakin Ammi dashi dazu akai amfani dashi ya rufe nata gam, sannan yadaura hannuwanta da kafafunta tasss suka dagata aka bude kofan bayin dake nan falo ya ijiyeta yafito yarufe bayin yace  let s go kun dauki car key dayan motan dana gani a gidan yaran sukace yesss shi Ogan"

yashiga babban jeep na Daddy dayan suka shiga dayan motan lexus sukabar gidan ransu fessss.

"Maman Baby tai juyin duniya ta kwance kanta takasa ga baki arufe kuma sai warin gas takeji, ga sperm"

"dinshi daya zubamata kaman barkono gabanta is on fire sosai babu abinda yafi damunta kaman yanda takeso tamike ta wanke kasanta amman bahali tai kukan tai kuka saita ma fara tunani ramin mugunta suka fadane? Yaran nan ayanda sukasan da kudin nan da sunan Saleem dasuka kira kaman fa yan bangan da Dady yace zai nema yayi aiki dasu ne, to kashe daddy sukayi suka dauki motarsa yanzu sunzo sun kwace komi na gidan nan tassss kudaddensa sun kwashe da wayoyi da laptop daga ita sai gidan nan, Innalillahi hankalinta yatashi saitaji wani kalan tsoro yana kamata bangare daya na zuciyanta nagaya mata Allah ne yakamaki, Allah ne yakamaki, kun zalunci marainiya kunci amana gashinan yanzu bakisan inda mijin naki yake ba gashi kun rasa komi banda gidan nan tuussss taji karan abu kaman tashin bomb dabatasan menene ba, chan taga alamun wuta naci daga dan space na kofan bayin datake hangowa"

tafara kokarin ihu uhmmmm uhmmmm uhmmm amman ina!

kai jama a this is the first time in her life take ganin mutuwa mutuwa na ganinta wlh wlh gidan nan

"yakama da wuta batasan tayaya ba tafara Allah natuba, natuba Ya Allah, na tuba zuciyanta kaman zaiyi tsalle yafito ta idanunta ganin wuta papapaaa har wutan ya iso kofan bayi."

Yan anguwa da vigilante ne akaga wuta na kamawa agidan aka fara ihu ana kiran makota da fire service

jama a suka fito ama bada taimako GrA ne sunada tasu motan tanka na ruwa incase of incident haka na fire nan da nan aka kawo aka shiga fesawa wajen 30min wutan ta mutu aka shiga ciki aka dauko Maman Baby da gabaki dayan gefen jikinta ya kone bakinta ya kone sabida tape din ya narke abakinta aka daukota da ranta amman wani kalan numfashi take irin na mai shirin mutuwa aka wuce da ita asibiti ana

duba gidan ko akwai yara luckily ba yara ba kuma mijin& .. WANNAN KENAN

WAIWAYE BAYA KADAN!

Sanda yan sanda sukakai gidan taredasu Marwan cikin yaran akwai guda daya daya zaga cikin daji yaje

"yayi kashi dan agidan ba wajen kashi saisa ba a tafi dashi ba dayazo yaga key mota ga Motan Abba duk awajen daman he was planning yayi magana dasauran team din suyu sama da mugun mutumin nan sukwashi kudin dan yaji wayan dayake da Saleem all this while amman dayaga an kwashe sauran takira asalin boys nasa suka fito farautan nan da daddare, da gangan suka sama gidan wuta dan kar wata"

camera tanuna su they re using this money da dukiya suyi japa subar Nigeria.

EPISODE

Koda sukakai gida Lami ne ta taresu hankalinta yatashi tana kallon Ammi da Amirah zatai magana Ammi

"tace  samin ruwan zafi a wuta lami, kiramin Yaya yazo gida, tayani kiran Miemie itama, bansan inda wayata takeba kwata kwata Mama Lami kawai ta gyadamata kai ganin ba lafiya Ammi tawuce tashiga"

"dakinta Amirah tabiyota ahankali she s still crying, zama Ammi tayi bakin gado saita dago kanta ta kalli"

"Amirah data shiga tahowa wajen Ammi ahankali cikin fushi Ammi tace  wlh wlh kikazo wajena nan saina nakada miki mummunan duka Amirah, saina miki shegen duka yarinyar nan shigowa dakin Lami tayi da gudu dan bata tabajin Ammi na fada da Amirah hakaba, Lami tace  lafiya Ammi ?Ammi tace  dauki yarnan tabarmin dakin nan banson ganinta, ki taimakamata idan zaki iya ki hadamata da paracetamol kawai I m not ready to see her now kunga yanda Amirah ke kuka ga fushin Marwan ga Ammi na fushi da ita kalan wanda bata taba ganin Ammi tayi da itaba kawai saitaji dubiyan yamata zafi Lami tashiga dagata tace  muje muje Amirah me kikama Mamanki haka? Amirah bamata iya magana Lami ya fitar da ita taje tahada ruwan dan itama talura da condition na Amirah sukaje bayi ita ta taimaka mata ta gasu saida Amirah taji kamanma mutuwa zatayi suka fito Lami tawuce da uta dakinta tabata wasu kaya tasaka daidai lokacin Umar na sauke Miemie akan machine jin ayanda Lami tace mata Ammi tace yazo he was so supportive kawai yakawota yace  idan kun gama ki kirani nazo na daukeki gyadamai kai tayi daidai"

Baffa na zuwa shima Umar yashiga gaisawa da Baffa.

Kafin da Baffa da Miemie sushi go gidan tare yana rikeda hannunta suna hira suka shigo gidan da

"Sallama Mama Lami tafito ganin fuskanta kadai sunsan bakafiya tace  ku shigo nan shigowa dakin sukayi zata wuce takira Ammi taga Ammi tafito idanunta sunyi jajir, Miemie nashiga dakin taga Amirah ga tea agabanta bata tababa dagudu tai wajen Amirah tace  Ya Amirah? Menene meya sameki? Baki da lafiya ne? Mama Lami meya sameta haka fuskanta duk ya kumbura ? Daidai Ammi na shigowa dakin tace  sakinta tasa mijinta yayi atare da Baffa da Lami da Miemie sukace  mene! Zama Ammi tayi saitai shiruuuu saikuma tashiga basu labarin komi daya faru tassss har zuwa dawowansu saita kalli Amirah cikin zafin zuciya Ammi tace  open your mouth kifada mana dalla dalla abinda kikaje kikayi ma Marwan"

da iyayensa inba hakaba ranki zai baci

Sosai take kallon Ammi gabanta kawai faduwa yake ashe uwa wacce bata taba dukanka ba take riritaka

"duk randa zata rikida tai fushi dakai jikake kafi tsoronta kan komi aduniya, Amirah bata taba sannin haka take tsoron Ammi ba sai yau sabida yanda taga ran Ammi yabaci har rawa jikinta yake takasa magana, Ammi tadaka mata mummunan tsawa.  Bazaki bude baki kiyi magana ba Ameenatu rushewa dawani kalan kukan tsoro tayi kawai tashiga fadin abinda tayi ba karya dan ta dimauce, Ammi tafarfasa kawai takeyi, sanda Amirah takai wajen datace ita ta rungume Saleem dama yaga jikinta kawai Ammi ta taso Lami tana.  Ammi, Ammi Inaaa fizgo Amirah Ammi tayi tashiga dukanta, though bawai wani lafiyayyen duka take mataba but just soft beating haka na fushi dayake nunama yaro yayi abinda ba daidai ba Lami tarike Ammi tace  dan Allah kimata hakuri dan Allah Miemie ma ta tsorata bata taba ganin Ammi ta fusata hakaba har tana dukan Amirah tafashe da kuka itama tana rokon Ammi, Amirah nawani kalan kuka wlh har fitsari saida ya kufce mata, Baffa yatashi yazo wajen yace  saketa nace Ammi tasaketa Amirah ta kankame Baffa tana wani kalan ijiyan zuciya kaman zata mutu jikinta bari kawai yake tana kuka, Baffa yace  haba so kike yarnan ta mutu gabaki daya kihuta da wanne zataji? Akanki fa taje tai abinda tayi ran Ammi abace tace  banki takaba Baffa amman tarbiyan dana bata kenan, yaushe Amirah"

"takoyi fitsara eh? Kallon Babba tamusu rashin kunya, tama Mahaifinsa tama Mamarsa haba an kace"

"karna maketa, tarbiyan dana bata kenan, mijinki zaki cema kanin mata? Mijinki zaki gayama dan uwansa"

"kikeso yanaga jikinki eh? Sabida kinga yana sonki? Naji dadi ai yanuna miki shi dan halak ne daya sakeki, saikisha zaman gida shashasha kawai, shekara nawa yau kikasan halin ubanki, da baki daya zaki sanar da mijinki abinda ke faruwa zasu magance abin nan bagashi yanzu yana police station ba but you decided to use the foolish way, kinma manya fitsara kin kaso aurenki wacce batasan mutunci ba sanda uban naki yadaukeki yakai asibitin mahaukata ya watsar ko biyar bai ijiyewmb wannan bawan Allah data zaga daga kudinsa Yaya kudin aljihunsa yayi admitting nata all her drugs everything was from his pocket ama samin likita haka a duniya? Ko wannan abun kadai baici ki rangwantamai ki kasa kallon idanunsa ki gayamasa wasu maganganun ba, Marwan fa kudi yadauka yaba Miemie wanda ban mamcewa kudin nayi amfani dasu har na kwaso kaya nazo gidan nan dan banda ko sisi a lokacin the only person daya miki wannan"

"adalcin kikama haka I m so embarrassed ace diyata ce tai wannan abun wlh kuwa,"

Idan Matar dana tamin kalan abinda Amirah tayi saina cewa dana wannan ba Matar aure bace ita da kai

"har abada, yanzu ai kin huta ki sha zaman gida zawarci kikeso ko, kin dauka ana auren marasa kai ne Allah ya rufa miki asiri amman ke kin tonama kanki shikenan Baffa ya fizgo Ammi yace  keeee yakalli Miemie yace  dauki Amirah kuje chan dakin Miemie takama Amirah dake kuka suka fita Baffa yakalli Ammi daya dade baiga matan nan tai fushi hakaba yace  yakuri yakuri nasan yanda kikeji yakuri kinji yakuri sai alokacin kukan da Ammi keji tarushe tafashe dashi, Allah sarki ashe idan aka saki diyarka sakin yamafi yima uwa ciwo akan diyar, wlh Lami itama saitahau matsar hawaye taji bala in tausayin Ammi, Baffa yace  ya isa, kiyakuri, kimata afuwa, duka duka yaushe tasami lafiyan? Yaushe tai hankalin? Meta sani? Dole ta tafka shirme, ayanda Amirah ke sonki kome akace tayi kanki zatayi eh cikin kuka Ammi tace  nasani kawai tacima yaron mutunci dayawa ne maganganun data gayamai baisuyi kama da maganganun mara kan gado urinta ba yanda kasan an zaunar da 0ta an koyamata, kunyan Marwna nakeji, Baffa Amirah bata kyautaba, I can never excuse action nata koda kashenin akayi, she can simply go kobazata fada musu ga abinda ke faruwa ba tayi demanding sakin batare dataci musu mutunci da fuska ba Baffa yace  rashin hankalin kenan, amman ya isa, tayi abinda tayi yanzu ne mu manya zamu gyara kuskuren Alhamdulillah saki dayane, inhar matarsa ce zasu dawo su koma su zauna tare, gobe in sha Allah zamu shirya muje gidansu da safe mu uku mu bada hakurin abinda diyarmu tayi hakan zai nuna munsan me mukeyi, kiyakuri go easy on her kar fushinki ya maidata gidan jiya, correct her kinuna mata ga yanda rayuwa yake, ba a wulakanta masoyi, I m sure by now ita kanta tai nadaman actions nata, dan Allah kibita ahankali kinji, saki ba komi bane face kaddara wacce Allah yarubuta maka zai sameka, wani zubin sai bayan an sami matsala anyi saki ake dawowa a kulla soyayya wacce tafi nada so calm down"

kinji

Sosai Baffa da Lami suka dunga bama Ammi baki har fushin datakeyi yaragu sosai.

WAYYYOOO AMMI SAKIN NAN YAMATA CIWO WLH

EPISODE

Miemie da Lami ne suka kula da Amirah sosai tea kawai ta iya sha Baffa yaje pharmacy yasayo mata

"magungunan zazzabi tasha takara gashin yamma bayan sallan magrib bacci yakwasheta, taba su Miemie tausayi, tashi Miemie tayi ta tafi dakin Ammi, Ammi na zaune kan dadduma tana lazimi tabita da kallo saida tazo wajen ta zauna ahankali Ammi na kallonta tace  yaushe zaki tafi? Ahankali tace  bayan magrib Ya Umar yace zaizo muwuce Ammi ta gyadamata kai, suna zaune ahaka har aka kira isha sukai"

ishai.

Washegari still Lami tama Amirah komi tabata breakfast tadanci kadan taji sauki sosai wajen yarage

"mata ciwo kawai rayuwanta baya mata dadi ne, wuraren 10 suka tafi gidansu Baffa akabar Amirah kawai agidan dan bazasu dade ba."

"Around karfe goma na safe yasauka a garin Netherlands, fitowa yayi anan airport yasai, using WiFi saiya"

shiga WhatsApp yaturama Mami message.

" Mami I just arrived, I wanna remove my SIM card, go off social media for a while, when my mind is calm"

"and settled I will call you Mami, take care yana tura maganan yacire Nigerian sim nasa yasauke WhatsApp Wanda daman shine social media app dayake dashi, wani VIP car yashiga aka wuce dashi lafiyayyen 10star hotel dayayi booking ana tafiyan yana kallon hanya yana tunani, Amirah ce azuciyansa but he s trying yadake ya danna duk sanda zatai popping up azuciyansa saiya danne tunaninta he just want to close her chapter baimaso yadinga tunata balle yadinga tuna mai tace masa that s what is"

hurting him the most kawai saiyayi alkawarin hakan zaiyi.

**

Har gidan sukakai da tsananin farin ciki Mami ta tarbesu while Abba yashiga turama Alhaji Hamza

"message kan yazo, zama aka yiyyi Mami tace  bari akawo breakfast Mami Lami tace  ahh mun koshi Mami tace  wlh ban yardaba dasauri tawuce kitchen tana kiran Twins dasuka shiga saukowa sukazo suka gaida kowa na dakin sannan suka wuce kitchen saiga Alhaji Hamza yana sanye da manyan kaya milk color yana baza kamshi da sallama yashigo falon yar zuciyanta Ammi taji muryansa amman taki daga kai,"

Abba yamike yace  bismillah shigo shigo yashigo saiya nunama Baffa Alhaji Hamza yace  ga babban

"aminina Alhaji Hamza, tsohon soja ne toh kukan kirasa da general Baffa yabasa hannu suka gaisa anadan raha sai Alhaji Hamza yajuyo yakalli Ammi wani kallo dabaya boye soyayya yace  ina kwana"

"Hajiya, dafatan kin tashi lafiya, ya jikin? Akwai abinda ke miki ciwo? "

"Kowa na dakin saida yajuyo yakalli Alhaji Hamza kunya yasa Ammi takasa ko motsi, tamaki magana saiya"

"kalli Lami yace  ina kwana dan Allah tasha magani kuwa lami tawani washe baki tana kallon Ammi dataki magana tace  eh tasha Alhamdulillah lafiya kalau duk muka kwana anatse yace  diyata fa Amirah? Wani sanyi Ammi taji yanda ya tambayi Amirah, Lami tace  itama haka tasha shayi munbarta takoma bacci ma gyadamata kai yayi saiya juya yawuce wajen su Abba yazauna Baffa nadan binsa da kallo saiga abinci an shiga kawowa, Lami tadan matso kusada Ammi cikin muryan gulma tace  wannan general yakamu fa Maman Amirah yaushe kuka hadu? Dan dago kanta Ammi tayi ta saci kallonsa"

tadauke idanu dasauri ita kanta batamasan mesa takejin mutumin aranta ba daga ganinsa jiya.

EPISODE

"The last time wani namiji yataba shiga ranta was 22yrs ago tun mahaifin Amirah, that same feelings"

"takeji yanzu akan Hamza tarasa dalili sake dago idanunta tayi karaf suka hada idanu dasauri ta dauke kai Mami tafito tareda yan aikinta dakuma twins aka jera abinci, waina ce da farfesu sai kunu, da shayi dakuma dumamen tuwo da miyan kuka da man shanu da yaji sai ruwa tace  dan Allah ku sauko muyi kari babu Wanda yayi musu, duk aka sauko Hamza kaman zai cinye Ammi da idanu babu wanda bai lura a dakinba imagine Ammi na gidan in-laws dinta amman idanun Hamza yahanata sukuni, dumame taci bada wani yawa ba da kunu mazan ko sunci abinci da kyau, Abba ya warware yasaki jikinsa bai daurama kansa damuwan Saleem ba yashiga coma ance shock ne zai dinga zuwa yana dubasa kullum yabisa da"

addu a shiyasa kansa in this situation he pray Allah have mercy on him.

Gama cin abincin akayi tass akai clearing komi aka zazzauna Baffa yayi guaran murya yace  toh

"Alhamdulillah mungode da wannan karamci, zanso na tambaya ina Marwan saikuma shima Saleem din zanzo duk mugansa kafin afara magana dan gyaran murya Abba yayi yace  toh with everything that happened jiya konima nan kafin nakoma gida Yayarsa ke sanar dani Marwan yabar kasan! Abba yadanyi shiruuu sai ahankali yace  Ahhhh Marwan wani kalan mutum ne mai hakuri mara fushi, koni baimin sallama ba, I m sure yayarsa ma sabida ita tagansa saisa tasan da tafiyan, yatura mana message ya sauka"

"lafiya amman zai sauke komi na wayansa when he s ready zai kiramu, I know he s just hurting me for"

"now, but nasan waye d ana bazai taba rabuwa da Amirah ba aurensu zai dawo let s give him sometime"

"to cool off jikin kowa na dakin yayi sanyiii, Abba yace  akwai something daban fada muku ba, sabida bantaba daukan abin hakaba, Saleem kanina ne uwa daya uba daya, while Marwan kanin matana ne wanda tadaukesa tun yana shekara daya sakamakon hatsari da iyayensu sukayi toh a hannunta yataso, Saleem yataso a dayan matata shi yana shekara uku lokacin mahaifiyar mu tarasu, dukansu na daukesu a matsayin yarana dan a hannuna duk sukai girma, Abba yayi shiru yace  dukansu sun taso a hannuna as two opposite yara, while Marwan is a calm, nutsasstsen yaro, Saleem is opposite of that, mata, shayeshaye duddai irin abubuwan nan wanda akasan waje abokan banza duk anan ya koya, daidai gwargwado munyi iyakan kokarin mu amman ba riba, rana daya yaje wajen dan uwansa Marwan a asibiti yaga Amirah a office na Marwan, Allah ya doramasa kaunar ta, for the first time saiya fara kokarin ya chanza ya zama mutum na gari, Abba yadanyi shiru yace  mukaje muka nemi aurenta amman kash rannan daurin auren wata ta shagaltar dashi jama a sun taru narasa yanda zaiyi sainasa a daura auren da Marwan tunda nasan shi yarone mai hakuri da kawaici nasan bazai taba kunyatani ba Abba yasake yin shiru sai chan yace  bamu gansa ba sai bayan wata daya da auren Marwan ma yaganosa ashe yarinyar dayakebi tamai asiri yaje ya karya tom shine tunda Saleem ya lura Marwan ke auren Amirah rigima yatashi, yaki hakura, yaki imani yadage sai Marwan yasaketa shine yadinga abubuwa haryane yahade da babban su bansan tayaya suka zama team ba, yanzu dai haka Saleem na asibiti ita yarinyar datamai asiri ta yankemai gaba ta gudu! Kowa ya kalli Abba, murmushi yayi na manya yace  hmm Alhamdulillah jiya akai surgery yafito amman he s on coma I pray Allah yasa sanadin shiryuwan sa kenan, kuma one thing dana sani is alhakin raba auren nan ke kamasu duka Baffa yace  ba shakka, to Allah ya magance komi, daman munzo baku hakuri ne bisa ga abinda diyarmu tamuku mara kyau mara dadin ji kuma Abba yayi murmushi yace  mukuma namu dan dayayi nasa shirmen fa Marwan? Koko shi kanina da shine

49 / 51