BACCIN SO BY M SHAKUR

Author :  Category :  Romance

Chapter   45 / 51

132K to 135K   out of 150.2K words

Saleem ke kallonsa Allah yasani baisan ina Amirah take ba amman da Abba yafara maganan yaga damuwa kan idanun Abba wannan da neman Amirah yasa har an kura Abba yasan plan din Daddy yafara aiki ashedai tsohon nan shegen duniya ne, wow ya kwana da bakin ciki but is as if Abba yabasa golden news that just make his morning, kawai saiyaji wani farin ciki ya lullubesa, Abba kawai yaga Saleem na murmushi sosai. Kai Ya Allah! Wannan wani kalan tashin hankali ne wannan? Saleem wani kalan mutum ne wanda baisan mutunci ba da alkhairi? Wani kalan butulu ne Saleem? Wani kalan mara imanine Saleem, Mara Imani kuma da kaddara? Yanda zuciya yakawo ma Abba wuya baisan sanda yakai duka hannayensa gaban wuyan rigan Saleem ba yace  ina ka kaima Marwan mata Saleem? Eh? Tell me now Kona maka dan banzan duka ? Kawai Saleem yabushe dawani kalan matsiyacin dariya dayasa azuciye Marwan yataho zai wuce Mami ta taresa tareda girgizamai kai, she knows abinda Marwan keji"

"but ko mutuwa na kunyan mahaifiya, Abba shine yayan Saleem shima yana iyakan kokarin sa akan yaron, cin fuska ne Marwan yahau dukan Saleem agabansa kowani abu, mutunci da karamancin Abba shine Marwan yayi hakuri ya danne zuciyansa yabar yayan da kanninsa suyi magana batare da sun shiga ba, dukan Saleem Abba yashigayi Saleem yana wani kalan dariya na dadi da gidan ke amsawa sosai Abba saima yagaji yadena yana haki gwanin ban tausayi, Saleem dake dariya sosai yace  wait harka gaji Yays? Dan Allah cigaba da dukana kaninka ai yazama punching back na kowa, har kasheni aka kusan yi bakace komi ba, kaima yinaka yanzu yamikama Abba kansa, Abba ya tsaresa da idanu, Saleem dake dariya yace  kome zakamin yau I promise you bazan taba fushi ba cus I m the happiest man alive today yayi murmushi saiya dena yakalli Abba ido cikin ido yace  nine kanninka! Nidakai mun fito daga cikin mace daya, the same blood ajikina shine the same blood ajikinka amman in order ka faranta ma wanda baka hada komi dashi ba ka gwammace nayi rayuwa haka miserably, pathetically ,kana kirana da bunsuru, kana Allah wadai dani, meanwhile kana kyautatama kanin matarka, kana nan nan dashi, kana kiransa"

danka sabida yayarsa nashan maganin mata tana baka gindi kanaci& & .  Saleeeem! .

EPISODE

Abba ya dauramai mummunan mari jikake tassss! Abba na huci yace  don t you dare disrespect my

"wife! Saleem yashafa inda Abba ya mare yadan cije lips nasa yanama Abba wani kallon rashin kunya, saiya fashe da dariyan keta sosai, yace  you know I finally get wani point na wata karin magana da"

"jama a keyi, wato daka haifi gwanma gwara ka haifi Matar gwamna, look at me kanninka, look at him"

"kannin matarka yanuna Marwan dake kallonsu Mami ta taresa tahanasa komi, Saleem yace  you gave him better education than me, yanada masters, harda PHD, a Dr, kasamamai aiki da NGO ana biyansa in dollars, komi ka kawo Marwan, abubuwan ka shi kakesa yana duba maka yana managing maka, nasha ji kana praising nasa wajen abokanan ka kan idan baka raye shikakeso ya jagoranci gidanka da iyalinka, Marwan is your everything while ni kaninka I m just a photo daka tsana, I have just LLB na law shikenan, no masters, no NGO job, nothing, absolutely nothing Abba yadade yana kallonsa cus duka abinda Saleem yake fadi are lies, pure lies, ahankali Abba yace  Saleem bantaba banbantaka da Marwan ba, same school kukayi, kun gama same university, he proceeded with his masters kaifa? Kakiyi, kwanakin baya karyama kamin kaje dubai masters nan kana club, your entire life you choose clubbing da bin mata while Marwan is here working his ass off to be a better person to earn his own source of living not depending on my money, he established kansa da kansa, I only recommended him to the NGO tunda psychiatrist Dr suke nema, sunba Marwan aikin base on his merits, sun gansa sunka what he s capable of, sunga resume nasa, i didn t get him this job, he earned it, banda haka bazan iya tuna the last time Marwan yaci 5k tawa ba, he does everything for kansa, kona basa baya karba, kaiko you live and breathe on my money with my credit card nike maka komi, Marwan baida credit card from me ko guda daya, all"

this things baka gani ba Saleem?

"Saleem nawani murmushi yace  saikuma kayi, karya kake Yaya, you always show me and show the"

"whole world Marwan kakeso, ko baki kayi daga kasashe shi kakeson nunawa not me, abin yakaiga yarinyar danake so nake kauna kadauka ka aura masa just sabida kasa matarka dashi farin ciki ni ina cikin bakin ciki, baka taba tunanin for once how i will feel ba, and you think yau Amirah data bace I will not"

be happy?

"Ya kwashe da dariya yace  bari nagaya maka wani abu Yays, inhar banda peace of mind kaima bazaka"

"taba samin peace of mind ba same goes for the entire family, baka auramin Amirah ba shima bazai taba zama da itaba, kodai ni na aureta kokuma dukanmu nida shi muhakura inba hakaba wlh wlh bazan taba barinku ku zauna lafiya ba dukanku saiya juyo da kansa yakalli Marwan dake kallonsa Mami ta taresa tareda kama shoulder nasa idanunsa kadai ya kalla yasan yayi kuka yayi murmushi yace  remember rannan nace maka you will go to Mami and be crying like a Baby? Trust me bakama fara kukan ba wait for the things that await you, nizaka kwana kanacin yarinyar nan ina& &  Saleem! Abba ya fizgosa yana daka masa tsawa, Saleem shima azuciye yadakama Abba yace  dalla chan Yaya kabarni mana dakai nake eh yane, ahhh ka kyaleni fa mutumin nan ko zan sassaka maka hannu zuciyan Marwan tafarfasa yashigayi jin yanda Saleem kema Abba rashin kunya sosai, zai wuce Mami tasake rikesa tace  Marwan! , Abba ya tsaya turus kawai yana kallon Saleem da idanunsa suka juya kaman zai rufesa da duka, Saleem ya nunasa da yatsa yana ihu kaman zai daga gidan sama yace  Yaya after abinda kamin kafifita kanin matarka kan ni I loose all respect for you, girmanka yazube a idanuna Yaya! Kahanani wacce na keso kuma akan idanunka zan aureta, sannan ka tattara gadona kabani abuna na barka har abada, kabani share na na company kokuma I will go to media saina ci maka mutunci, saina tozartaka nasa kayi loosing respect akan idanun duniya and this our gold company will come crumbling right before your eyes, you"

hurt me I will not hurt you amman idan baka bani gadona da share dina ba wlh I will hurt you in the

"most painful way, kuma da yardan Allah amanata da Baba yabaka baka rikeba saita kamaka! Saika"

wulakance Yaya& & . Saleeem!

"Mami takirasa da karfi jin abinda yake gayama yayansa dayake matsayin uba a hannunsa, he s just 3yrs"

"old Abba yadauki Saleem, Saleem yajuyo yakalli Mami yace  baruwanki dani makira! Fizge hannunsa Marwan yayi zaiyi kan Saleem cikin tsananin fushi Mami tace  inhar kataba sa Marwan ban yafe makaba wallahi! Chak Marwan ya tsaya yana nishi da zafi zafi yana kallonsa, Saleem shima yakallesa yace  you all will pay for betraying me wlh! Da wanchan mutumin dakakema kallon mahaifi zan fara dayaci amanata, saina wulakantasa na wulakanta sunansa aduniyan nan, saikasan ni kaninka ka yar kaja kanin matarka a jiki ka maidasa da kaman ance Mami ta kalli Abba hannunsa tagani yadaura akan kirjinsa yanadan kyafkyafta idanu dan mugun jiri yake gani bana wasaba saiya fara tangal tangal zai fadi dasauri Mami tace  Alhaji! Alhaji tai wajensa da gudu Marwan yayi wajen da sauri Abba nawani kalan nishi he s finding breathing so hard and difficult Mami tafashe da kuka tana kiran sunansa tana kamasa, dudda Abba na in that condition Saleem yake kallo dakemai mugun kallo, Saleem yaki shiru yana kallon Abba in the eye yace  ko mutuwa ce in sha Allahu you will not die in peace! Sai Allah yasakamin abinda kamini! "

Yana maganan yajuya abinsa yafice.

EPISODE

Gidan sukakai dake bayan gari daga sama Daddy yaji karan motan mikewa yayi yaleka ta window daidai

"an budema Amirah kofa tafito ahankali jikinta bari kawai yakeyi tashiga dafa motan tana tafiya ahankali da kyar chan ta tsaya sabida zafi zai kasheta, mutumin yace  ke dallah jamuje tsorata tayi bashiri ta gwale kafafun tashiga tafiya tanajin radadi ahaka da taimakon Allah suka shigo dakin ana bude kofa ta hango Ammin ta kwance a daddaure, baki a rufe hakan yasa tawani kwala ihun kiranta ahaukace.  Ammiiiii  dauketa akayi da mari da saida taga stars guda uku ajere suna blinking, tawani zube"

"akasan wajen takai hannunta dasauri tadaura kan kumatu tana wani kalan sauke ijiyan zuciya da duka jikinta marin ya shigeta, Daddy yashiga yarfe hannunsa dahar zafi yake mai sabida yanda yazuba mata marin yana jan tsuki yace  nonesense kin dauka nakawo ki nan ne dan kimin ihune mahaukaciya, nasara da rayuwan GRA yace I hate noise and tantrums ahankali Amirah tadago rinanun idanunta takalli Daddy dake yarfe hannu yahade fuska hannunta na kan kuncinta ta tsaresa da kallo tana kallonsa da manyan idanun nan nata, bude idanunta Ammi tayi dan ihun Amirah har kasan zuciyanta tajisa abinda yasa ta farka kenan kanta na sarawa, tabi ko ina da kallo da yanda aka daddaureta dakuma Amirah data gani zube akasa tadafa kuncinta tana kallon Daddy da jajayen idanunta ga gardawa adakin saita fara yunkurin"

tashi zaune tana motsi sosai trying to talk so bad tace  uhmmm uhmmmmm dasauri daga Amirah

"har Daddy suka juyo, dasauri Amirah tace  Amm,i Ammi na, Alhamdulillah Ammi kin tashi ta yunkura"

"zatai wajenta, kafa Daddy yasa yawani tokare mata kirji saida tiles yaja Amirah kiiiiii ta buge da bango, Ammi tawani zaro idanu tareda mirginowa zata tashi takasa hawaye nafitowa daga idanunta tana uhnnn uhnnn ganin kalan haure Amirah dayayi kaman ya haure kwallo da ba aso, Amirah felt kaman zata mutu her chest got congested from yanda Daddy ya tokare ta, ko numfashi balle kuka saitama kasa tama kasa wani motsin kirki, Daddy dako ajikinsa yawuce Plastic chair yazauna yadaura kafa daya kan daya batare daya kalli Ammi ba yanuna Amirah datake ayanda take da yatsa kaman yana nuna kashi yace  ku dagota ku kawomin ita nan gabana gardawa biyu suka wuce hannu sukasa suka dago Amirah sharap ta biyosu suka kawota gaban Daddy suka ijiye yadaka mata tsawa yace  kalleni nan ko angaya miki yanzu zaman1n dakikemin haukan nan ne kallonsa Amirah tayi ahankali da jajayen idanunta dasukai laushi gwanin ban tausayi, Abba yakalli agogon hannunsa saiya kalleta yace  I don t care ko ke mahaukaciya ce koba mahaukaciya ba, if there s one language danasan kina understanding aduniyan nan shine mahaifiyarki dan haka yanzu ma we are using her as mode of communication, kalli mahaifitarki yanuna mata Ammi dake uhmmm ummm tana kiciniyan bude hannu ko kafa wlh duka takasa, idanun Ammi sunyi jaaaa Amirah ta tsare Amminta da kallo dake struggling in pains taji abu ya tsayamata a kirji, Daddy yadaka mata tsawa yace  kalleni nan! Kallon Daddy Amirah tayi ahankali, yace  you have one hour idan bakison mahaifiyarki ta mutu, inba hakaba kasheta zanyi! Amirah tashiga girgizamai kai zatai magana yadaga mata hannu yace  you have exactly one hour dot za a maidake gidanki, I don t care kome zakiyi, kome zakiyi kije kiyisa ki tabbatar kinsa Marwan ya sakeki! Wani kalan kallon Daddy Amirah tayi da sauri kanta nawani dundummm! Dum! Dum, Ammi tazaro idanu tace  uhmm, uhmmmmm, ummmmm Daddy daya tsareta da kallo ganin yanda take kallonsa just makes him realize tsaf tagane abinda yake cewa kuma tagane menene saki, sai taga yakalli daya daga cikin yaran kawai saitaga yawuce yashiga wani daki Amirah tabisa da kallo saigasa yafito da bulalan inji doguwa sharbebiya a hannunsa ya tsaya gefen Ammi, wani bugawa kirjin Amirah yayi tama kasa kallon Daddy sai mutumin dayake tsaye gefen Amminta da dorina zuciyanta na racing kaman zai fito, Daddy yayi wani murmushi cus ya karanci Ammi da diyarta kaman me, strictly yanajin kansa yau kaman sarkin duniya mai power da babu wanda zai iya takasa yace  yima uwarta shegen duka kai Goro! dawani kalan sauri Amirah tazare muryanta dabaya fita kawai yafito tagama kidimewa tace  Daddy, Daddy, Dady dan Allah dan Allah& & &  Pauuuuu! Kawai taji karan an zubama Amminta dake adaddaure bulalan injin Amirah ta kalli Ammi datai wani mikan bankara na tsantsan azaba da radadi ga ba bakin kuka, Ya Ilahal Alameen! Wuyan Amirah harwani girrrgirrrrgirrr yakeyi ganin yanda mahaifiyarta keyi agabanta in pains, tawani fashe da kuka wanda tunda aka haifeta bata tabayin kalansa ba harda majina, koda Marwan yake cinta ba irin kukan nan datake yi yanzu takeyi ba, tama haukace gabaki daya tawuce zatai wajen Ammi, Daddy ya fizgo hijabinta yajawota gabansa gardin yasake zubama Ammi bulala na biyu ihuuuu kuka Amirah tayi tana hada hannayenta biyu.  Daddy dan Yarasulullahi kadena dukan Ammi na, na rokeka da girman Allah kudena, ni kumin dukan amadadin Ammi na, na rantse da Allah zanyi kome kakeso, Daddy Kamin rai, ni ku dakeni kudena dukanmin Ammi na, Daddy nika daken, dukanku ku taru akaina ku daken, Daddy wlh wlh kome kakeso zanyi, zance ya sakeni kudena dukan Mamana now this is abinda yakeso ta tsorata har tsakiyan jinin jikinta, kuka harda majina har baki, tsawa Daddy yamata yace  bacewa nayi kice yasakeki ba kisa yasakeki, you have one hour zaki dawo wajen nan da takardan sakin sa, idan kinason mahaifiyarki araye inba hakaba kasheta zanyi babu abinda aka isa amini ke kin sanni, kinsan waye ni ahaukace Amirah"

"tagama kidimewa tana magana tana kuka tana waigen Ammi tace  toh, toh, naji, wlh saiya sake, Daddy"

"stop hurting Ammi na dan girman Allahhhhhhhhh yanda take kuka kaman zata shide, Ammi dudda"

"she s in pains jikinta namata radadi saida taji wani karfin hali da dakewa yazo mata, she needs to be her daughter strength, cikin karfin halin son yin magana tace  Amirah kibarsa ya kasheni ban yarda ki kashe aurenki ba amman ina Amirah bataji, Daddy yace  kina dawowa da sakin zan aura miki Saleem shin zaba miki, do this and I will let mahaifiyarki leave in peace, saikuma gargadin dazan miki wlh wlh kika wuce hour daya, ko kika sanar da wani ga abinda ke faruwa na rantse da wanda ke busamin numfashi yaune rana na karshe dazakiga mahaifiyarki aduniya, idan kina tantaman hakan ki gwada yi kiga Daddy yabuga kafa akasa irin buna mata he s serious Amirah ta tsorata har karshen zuciyanta yace  tashi kutafi tashi tashigayi mance ciwon tayi tayi wajen Ammi tawani rubgumeta tana shafa bayan Ammi da hannunta inda taga bulalan yasauka tana wani irin kuka, Ammi taji jikinta zafi kaman wuta, Amirah ta kankameta tace  Ammi ina sonki na yarda narasa komi na duniya bandake Ammi na, kene rayuwan Amirah, I will save you kinji Am& .. fizgota gardin yayi yajata Amirah na kuka suka wuce suka fita tana waigen Ammi"

tana share makinan hancinta da hijabi hankalinta yatashi na fitina yau.

BURA UBA NOVEL NA FIRE

A GANINKU MARWAN ZAI YARDA YA SAKETA???

A GANINKU AMIRAH ZATA YARDA KAR MARWAN YASAKETA??

JAMA A I THINK AMIRAH WILL DO KOME ZATAYI TA TABBATAR MARWAN YASAKETA SABIDA TA CECI

MAHAIFIYARTA AMMI KO???

KUSA KANKU A SITUATION NA AMIRAH KUBATA SHAWARA MEYA KAMATA TAYI YANZU TAKOMA

GIDA????

EPISODE

Tashi Daddy yayi yawuce ya tsaya jikin window saida yaga tashiga mota sannan yajuyo ya tsare Ammi da

"idanu da harga Allah baiso an dakaba but yasan idan baiyi hakaba bazai taba ruda yarinyar nan ba Amirah, Ammi nawani kalan kallonsa da idanu tanaso tai magana yashiga tahowa yana kallonta yazo har gabanta saiya duka yana kallonta sosai gabansa na faduwa batare daya cire tape na bakinta ba yace  me kikeso ki fadamin Amaryata saiya daga hannunsa yakai kan bakin Ammi yaja tape din yacire bala in zafi saida Ammi ta runtse idanu Daddy ya tsaya ya tsareta da idanu yanda ta runtse idanun kaman yacemata sannu amman saiyayi shiru yana kallonta bude idanunta Ammi tayi cikeda fada da tsananin masifa kaman ba Ammi ba tace  what do you think you re doing? Kana tura yata taje tacema mijinta ya saketa what are you up to? Meke damunka Baban Baby? Are you sick? Kai wani kalan mara Imani ne azzalamu eh? Tunda Ammi take masifan kallonta yake bayako kyaftawa saida tagama yace  wai tayaya ma akayi na sakeki eh kinyi fresh sosai yadaga hannunsa zaikai jikin Ammi, Ammi tace  wallahi wallahi inhar"

hannunka yataba jikina koda this is the last ting dazanyi aduniya saina gille maka hannu sannan zan rasu?

"Why are you back in my life? My y ata tamaka dakake cutar da ita kake azabatar da ita kallon Ammi yake sosai saiyadan sosa kai yace  bari na gayamiki asalin wanda yaga mahaukaciyar yarki yanaso Saleem ne, Saleem kanin Akhaji Gold ne uwa daya uba daya, Marwan ba dansa bane, kanin matarsa ne dasuka daura dun yana dan shakara daya sabida iyayaensa sun rasu ya girma hannunsu, Daleem akaso har gidana nemawa aure ba Marwan ba muka sa Rana, rannan daurin aure something happens Saleem bai hallara ba kawai aka daura da Marwan bayan sunsan Saleem ke sonta, to sai bayan wata daya yadawo shima ashe a_1r1 wata yarinya tamai, yanzu ni Saleem nakeson bata Ammi na kallonsa tace  sabida yabaka kudi kallon Ammi yayi irin tayaya kika sani, Ammi tace  Baka taba abu dan Allah, bazaka tana zuwa this limit hannu banza ba yabaka kudi shine kake kokarin bata

45 / 51