BACCIN SO BY M SHAKUR

Author :  Category :  Romance

Chapter   11 / 51

30K to 33K   out of 150.2K words

ta ari dadduman wacce ke next to bed nasu tai salla har akai isha i ma

"haka 8 daidai Umar yayi sallama yashigo Miemie tadan dagokai ta kallesa yana gaida marasa lafiyan yan dakin yana sanye da shadda blue mai kyau yasa hula sai kanshi yake hannunsa duka biyun rike da abubuwa sannan yazo wajen gadon ya ijiye basket din yace  Umma tace akawo miki Allah kara sauki gobe zasuzo dubiya ya ijiye dayan ledan wanda yan shopping ne yamata, Miemie da kanta ke kasa tace  an gode Allah amfana zama yayi akujeran daya bata yakalleta yace  bude kula ki debi abinci kici Dan kallonsa kadan tayi ganin ba wasa fuskansa saita sauka saga bakin gadon tabude kulan dafadukan shinkafa aka dafa musu da nama da zobo mai sanyi tadauki spoon da plate ta deba tadan kalli matan dake bata Aron dadduma ta kusa da su tace  ga abinci muna kwarya matan tace  ahh Alhamdulillah an gode dawowa tayi tazauna tafara ci duk kanta akasa Umar sai kallonta yake, haka take ta gansa taita kunya ko yazo zance awaya ne take bude baki tamai magana, today is the first day datake ganinsa in reality tayi magana shima sabida rudewan Ammi ne, cinyewa tayi tasha ruwa sannan ta ijiye plate din, Umar yamike yace  bari naje to gud night akwai sock da zanin gado kisa ki rufa da kyau sabida sauro gyadamai kai tayi tace  nagode agaida Umma dan kallonta yayi yace  muje kirakani akunyace ta sauke kanta kasa wucewa yayi yay gaba sannan tasauka tasa takalmi tafito awaje ta samesa wajen wani bishiya inda akasa kujeran zama haka tawuce wajen tana tafiya ahankali ya tsareta da kallo taje saita zauna amman tabar dan gab between them, sukayi shiru sai chan yace  Maryam dago kanta tayi takallesa, ahankali yace  how are you? Tambayan ya sosa zuciyanta sosai baki tabude zatai magana kawai saita daura hannayenta akan fuskanta kaman yar yarinya tafashe da kuka, she just feel alone, she feels ayanzu right in this moment batada kowa sai Umar, ba Ammi ba Amirah, mikewa Umar yayi saiyazo ya tsaya agabanta kafin yaduka gabanta ahankali yace  Miemie is this the promise dakika min? Yakikeso nayi da raina? Do you want to kill me eh Miemie, bakiso na ko? Girgixamai kai takeyi tana shesheka irin yanda yara sukeyi hancinta harda majina tace  Ya Amirah batada lafiya, bataci abinci ba nasan har yanzu dare yayi bazataci ba tunda bataganmu ba, jikinta was hot, bansan wani hali yar uwata ke ciki ba, Ammi gata itama a hospital banda kowaaa tana kuka numfashinta har neman daukewa yake Umar baimasan"

mezaiyiba sai kawai ahankali yajawota for the first time tunda suka san juna yayi hugging nata.

EPISODE

"Batasan metakeba kawai kankamesa sosai Miemie tayi back, Umar yafara patting bayanta yana mata"

"magana a kunne,  Maryam do you also want to loose me too? Cus kukan ki zai iya halakani kinga saiki"

"zama ke kadai aduniya uhn kankamesa Miemie tayi tana girgiza masa kai, ahankali yace  komi yayi zafi"

"maganinsa Allah, rayuwan nan babu wanda baya cikin wata jarabawa, I just want you kisan cewa Allah baya bacci, ki karfafa imaninki, kome ke damunki ki fuskancesa kiyi addu a, kima Amirah addu a wherever she s Allah ya tsareta ya kareta yakuma bata lpy, yadawo da ita lpy, sannan Allah yabama Ammi lafiya, everything is going to be okay I promise you, kinji, I m right here fa, I will always support you and be there for you no matter what kinji ?Gyadamai kai tayi tanajin wani natsuwa da karfi a zuciyanta, ahankali Umar yace  I love you so much be strong for me okay gyadamai kai tayi, cirota yayi daga jikinsa saita kasa kallonsa kuma ta sauke kanta kasa shima yatashi yakoma gefenta ya zauna saukai shiru sai chan ya kalleta yace  bari natafi uhm, saida safe tashi ki koma ciki tashi Miemie tayi da sauri kanta akasa tace  saida safe uhm nagode Ya Umar tawuce dasauri yabita da kallo yadanyi murmushi dan hug dasukai sharing nadawomai greasy azuciya yashafa kansa yamike ahankali yawuce yahau"

machine dinsa yabar asibitin.

**

"Wuraren 10 na safiya Ammi tashiga bude idanunta ahankali, dasauri Miemie dake gwfenta tawani"

"zabura tace  Ammi kin tashi, gani nan Ammi kina ganina ? Bude idanunta Ammi tayi ahankali tana bin ko ina da kallo kafin tasauke idanunta akan Miemie dake kanta, Miemie tace  Ammi murya chan kasa mara karfi Ammi tace  ina ne nan Miemie? Meya kawoni nan ? Ahankali Miemie tace  kanki ne yadan fashe tun jiya kike nan shiru Ammi tayi nan da nan abinda yafaru jiya yadawo mata dawani irin sauri tazabura ta mike zaune zata sauka daga gado Miemie tariketa tace  Ammi tsaya kinji dan Allah Ammi da zuciyanta yashiga bugawa dumdumdum tace  Miemie ina Amirah? Babanki yasa mazan nan sun tafi da ita? Ahankali Miemie ta gyadama Ammi kai, gaban Ammi yayi wani mummunan faduwa sai kawai ta kalleta tace  kira Dr a sallameni, bazan iya zaman asibiti bansan wace duniya Amirah take ba, kome zai samen ya samen gyadama Ammi kai Amirah tayi batare datai gardama ba tawuce tafita takira Dr sai gasu, Dr yace  Hajiya kibari agama miki treatment BP ki is very high maisa kikeso a sallameki cikin dauriya dan daurewa kawai Ammi take tace  nabar diya mara lafiya agida, lafiyanta shine gabana likita banawa ba dan Allah ka sallameni sauri nake, ganin yanda Ammi take magana sai kawai Dr yaji tabasa tausayi yace  okay amman ki dinga zuwa duk say1 sati dan mu dinga managing BP naki sannan you need to sign this discharge against medical advice form gyadamai kai Ammi tayi tai signing komi, Miemie tashiga hada kaya tass Mamie tazira hijabi ance subiya 5k suka biya suka fito Ammi bamatajin karfi"

jikinta amman tafiya kawai take har titi suka tare keke sai gida.

Shiga gidan sukayi bakowa agidan babu motan Daddy bangaren Maman Baby ma a kulle alamun

"batanan, Ammi kawai tafiya take tana shiga flat nasu koina tabi da kallo kafin tafada ban daki ta dauro alwala tai sallolin da ake binta dan Allah ne fark1 before anything saita shiga kiran Daddy wayansa na ringing baya dagawa, da kyar tasamu akaro na kusan 20th call aka dauka, muryan Maman Baby taji tadauka tace  dan Allah kadauki wayanta kar bakin ciki ya kasheta sweetheart muryan Daddy Ammi taji"

yace  tunda kin rokan mata ai hikenan yasa wayan a kunne yace  yi maganan ki da sauri dan tuki nake

Zainabu dakewa Ammi tayi tana rike abinda ke zuciyanta saita kalli Miemie dake gwfebta tace  bani

wuri Miemie ki rufomin kofa ta ashi Miemie tayi jikinta asanyaye tafita daga dakin tarufo kofa amman saita kasa wucewa ta tsaya tareda jingina kanta jikin kofan.

Da kyar Ammi tadaure tace  Baban Baby ina Amirah? Wani dan dariyan shakiyanci yayi harda shewa

"yace  har abada bazaki san inda Amirah takeba idanma abinda yasa kike kirana kenan gwara ki kashe dan bazan gayamiki ba wani abu Ammi taji yazo mata wuya ahankali tace  Baban Baby dan Allah dan darajan sa, kaduba girman Allah kagayamin inaka kai mini Amirah, karaman yarinya ce dabai kamata tana inda maza sukeba, idan suka keta mata haddi fa, ba hijabi ba takalmi ba hula jikinta, Amirah batasan komi akan rayuwa ba batada wayan kara kanta idan suka mata wani abu fa, katuna akwai Allah yarinyar nan marainiya ce, kafadamin ina ka kaita tsaki Daddy yaja yace  ai saikuma kiyi keda ganinta har abada dan wlh wlh wlh kinji na rantse miki mahaukaciyan nan bazata kara dawowa cikin gidana ba har abada wlh kuwa ki mutu idan zaki mutu munyi tafiya sai nan da yan kwanaki zamu dawo ya katse wayan Ammi tace  Baban Baby Babban Baby tai maza tasake dialing number taji akashe takira Number Maman Baby shima akashe duk dauriya irin na Ammi kawai saitaji kuka yazo mata tafashe da kuka sosai"

dayasa Miemie tadaura hannunta akan bakinta tana rushewa da kuka itama.

Takai morethan 20mins ahaka saita daga wayanta tai dialing wani number ringing daya aka daga wani

"dattijon namiji ne yace  Zainabu Abu muryanta adan shake tace  Yaya ina yini kai tsaye jin muryanta yace  meyasameki muryanki yake haka ahankali cikin sheshekan kuka tace  Yaya zankai Abban yaran nan kara a police station one thing he knows about his sister is she s a very very peaceful person ga hakuri hakan yasa yace  Subhanallahi meya faru haka Zainabu? Ina zuwa tsaya nasa kati na kiraki katse wayan yayi within one minute sai gashi yakira Ammi back tadaga yace  what happened Zainabu? Meya batamiki rai haka dahar zakikai mijinki kara police station eh ? Duk yanda Ammi taso ta daure takasa sai kawai tafashe da kuka tahau gayamai komi tace  idan wani abu yasameta fa? Wlh batada lpy, jikinta zafi kaman wuta, me mukamai ya tsaneta haka? Nagaya maka batun yau ba mutumin nan ba kaunata yakeba gadon yakeso yaci yasa ya aureni sabida komi yadawo hannunsa, zan kaisa kara yafito min da yata yasakeni yabata gadonta mubarmai gidansa anatse Yaya yace  Zainabu inaso kibani hankalinki nan, first of all nasan duk bakin hali irin nasa bazai kai Zainabu inda za a kasheta ba wani asibitin dai zai kaita bazai tabar barma gardawan nan yarki ba ko yaje ya zubar da ita kasan gada ko kan bola zan kirasa nayi magana dashi cikin kuka Ammi tace  ko ka kira baraka samesa ba yayi tafiya yakashe wayansa Yaya, ni ta Amirah nake kabarni na kaisa police station ahankali Yaya yace  Zainabu kome zamuyi aduniya dole fa zamu dinga sara muna duban bakin gatari, ni da ke munci zamanin mu kome zamuyi yanzu a matsayin mu na iyaye yaran damuka haifa zamu dinga kallo, Alhamdulillah diyarki daya miji yafito ana maganan aurenta nan da yan watanni aji kina case da mahaifinta a police station kin rabu da Babanta ba abin kunya bane, bar wannan gefe kika rabu dashi kinada tabbacin zaki karbe gadon naku? Gadon musulmai fa ba irin na kiristovi bane da ake rubuta will ba tsaf zai iya cewa yabaku kuma ya zauna, ni kina ganin banda wani karfi kika rabu da mahaifinsu kije ina gaki da yara mata dasuka dan tasa daya mai lallura daya lafiya kalau? Eh Zainabu? Lamarin aure hakuri ake wannan shine kalman danasha gayamiki shekara da shekaru wata rana sai labari duk abinda zaman lafiya bai kawoba tashin hankali bazai taba kawosa ba"

kaisa police station bazai amfaneki da komi ba saidai ya tarwatsa komi naki maybe ma har auren diyarki

Maryama haka kikeso cikin kuka tace  to yazanyi Yaya cikin muryan lallashi yace  Zainabu hakurin nan

"kinsha yinsa banso ki gaza, ki daure ko Maryam ne ki zauna ku aurar da ita tare daganan idan abun ba chanji sai asan yanda za ayi kinji, inaso kibani nan da zuwa dare zan nemesa zamusan inda Amirah take, addu an mahaifiya bata fadi kasa wlh babu abinda zai samiAmirah sai Alkhairi inhar kin mata addua, everything will be fine Amirah zata dawo wajwnki kinji?Banso kiyi komi kinji, kiyakuri kinji Zainabu na nafa sanki da hakuri ina ke ina zuwa police station dan Allah kiyakuri duk shedan ne kemiki huduba kibani zuwa dare kinji ahankali tana goge fuska tace  toh naji Yaya nagode Yaya yace  to zan kara kira anjima ya katse wayan Ammi tai tagumi saikuma takara fashewa da kuka bata tabajin tanajin bakin ciki"

da kunci kalan wanda takeji yauba in her life.

Bude kofan Miemie tayi ahankali tashigo tana kallon Ammi data shiga goge fuskanta dasauri ta kakalo

"murmushi tace  zonan yammata na tahowa Miemie tayi sai kawai ta zauna gaban Ammi, Ammi ta tsareta da idanu saitakai hannunta kan fuskanta tace  kuka kikayi ko? Hawayene suka zubo suna sauka tace  Ammi kiyakuri kinji karki sake kuka rungume ta Ammi tayi tace  maza dena kukan nan banso dataga yaranta na kunci gwara ita kadai ta shiga, burinta a duniya is to always see yaranta are happy, da kyar tai shiru Ammi tace  a ina kika sami kudin kaini asibiti? Murya chan kasa tace  Ya Umar ne tsareta da idanu Ammi tayi hakan yasa tashiga fadama Ammi all abinda yafaru sai kawai ta sauke ijiyan"

zuciya tace  anjima zaki kirasa saina masa godiya .

EPISODE

"Wuraren 9 nasafe Amirah ke bude idanunta ahankali kadan kadan, jikinta feels so relax, kanta feels so"

"light, wannan rashin dadin da jikinta keyi mata baya mata yau, sake lumshe idanu tayi tabude bakinta yayi motsi murya chan kasa tace  Ammi! Kaman ta tuna wani abu a firgice ta tashi zaune tanabin ko ina na dakin da kallo da hannunta da drip ke kai tana tuna duka abinda yafaru da ita cisge kanulan tayi saiga jini ga zafi dataji tahau yarfe hannunta tana goge jinin a riganta ganin yaki dena fita tabarshi tamike tasauka daga gadon kafafunta ba takalmi kafanta fari tasss da dogayen kumbunanta masu kyau, uniform ne ajikinta ko hulan yafita akanta ribon din shima yafita akanta tai wajen kofa datagani, so kawai take ta tafi wajen Ammin ta, saita shiga kokarin bude kofan amman kofan baya buduwa, tahau buga kofan sosai tana girgizawa sai jikinta yafara bari tafara kiran Ammi muryanta kasa kasa tana buga kofan da duka karfinta ga fitsari tanaji sosai rabonta da fitsari tun jiya maybe ma sabida bataci wani abu bane yasama"

bata fitsari tun jiyan ba.

Zuwa wajen kofan Iyawo tayi tabude kafinma takarasa budewa Amirah tabi da gefenta zata wuce

"dagudu kamata Iyawo tayi ta dagata sama Amirah takwada ihu fitsari na kufce mata, jin fitsari ajikinta yasa Iyawo tasaketa cikeda fada tace  ni kikema fitsari ? Ta dakamata tsawa dayasa Amirah takoma baya dasauri nurses na shigowa su uku, Iyawo tanuna musu jikinta tace  jibi yanda tamin fitsari ajiki? Bari nazo nacire miki kaya namiki wanka dasauri Amirah tawuce gadon ta kwanta tai lamo kawai tsoron"

matan take she s so big and strong kuma bataso kowa yamata wanka.

"Bude dakin yayi yashigo anatse hannunta da yanda yayi jini yabi drip din da kallo, yanda tajuya tana"

"kallon bangon gadon ta kifa kanta jikin gadon jikinta nadan bari ya kalla, dan gyaran murya yayi duk aka kallesa suna gaidasa anatse yace  what is going on here? Dasauri Iyawo tace  fada take dani kuma tayi fitsari ajikinta taki bari nacire mata kaya, taki bari natabata kuma takicin abinci strictly Marwan yace  why will you remove her clothes gaban everyone dake nan, part of your job is to understand the nature na patient and respect his privacy, just because she s like this doesn t mean you should naked her in front of all the nurses yayi maganan strictly dasauri Iyawao tace  ayakuri Dr strictly Marwan yace  Excuse me and page Baaba, kuma zaku iya barin dakin ya sallami all nurses din suka fice daga dakin aka maida kofan aka rufe, ahankali yasa hannu yadauki blanket dinsa dake kasan dakin yamike tsaye yataho gently ya warware yadaura akan jikinta dasauri Amirah takama bargon ta kankame tai lamooo like a helpless orphan, Marwan ya kalleta, ahankali yace  good morning Ameenah! bugawa kirjinta yayi tai shiru jin yanda yakira sunanta, hannunsa yazuba a aljihun labcoat dinsa yace  kinaso nakawo miki Ammi ? Dawani irin sauri Amirah tajuyo ta tashi zaune tajuyo gabaki daya bawai akwai farin ciki ko murna a fuskanta bane babu kodaya, amman gesture datasa na tashi tazauna datayi means this is the greatest news he has ever given her, saitakai hannunta tasa abakinta tana tauna yan fingers nata tana motsi da fararan kafafunta tar da babu slippers ko safa ajikinsu abakin gadon, ahankali Marwan yazo ya tsaya gaban gadon directly opposite her yana kallonta, bitting fingers nata take sosai, murya chan kasa yace  idan kinaso nakawo miki Ammi akwai rules dazansa miki inhar kinyi zan kawo miki Ammi, kinaso ki ganta ? Dan gyadamai kai kadan tayi tana kallon waje daya tana cizan hannunta, Ya Allah she looks so adorable and charming, yadan sauke gajeren ijiyan zuciya yace  stop fighting my nurses they re all here to take of you, yanzu za a miki wanka kisa kaya then I will come back muyi maganan Kaganta this time bazakace da ita ake magana ba daidai Umma ta shigo wata yar dattijuwa ce sanye da uniform na ma aikata tace  sannu Dr M Gyadamata kai yayi yace  yauwa Umma, please ki taimaka mata tai wanka ta chanza kayan nan Umma tace  tom shikenan yammata tashi muje sai kawai Amirah ta sauko daga gadon ahankali har lokacin hannunta na baki tana cin kumba ga fitsari duk a wandonta tasauke kanta kasa kaman tanadan jin kunya tafiya agabansa ahaka, juyawa Marwan yayi yafita daga dakin batare daya karaba jikinta second look ba cus uniform din sundan kama jikinta shape nata yafito sosai hips dinta da boobs nata, yace  Baaba adinga samata uniform dasuka danfi wannan girma part of job nasu is protecting features na patients nasu ta yanda suransu bazai wani fito sosai dahar zaisa wani patient ko"

"Dr ko worker yaganka yayi sha awanka ba,"

"Wucewa yayi yashiga duba other patients nasa, bayi suka shiga Baaba tahada mata ruwan wanka tace"

" yauwa zo ayi wankan toh make mata wuya Amirah tayi saita shiga tafiya ahankali ta duka ta rungume buket din irin kaman kunya takeji, Umma tace  ohh kunya akeji to maza yi wankan, ni bari na gyara gadon fita Umma tayi hakan yasa Amirah tacire kaya ahankali tashiga watsa ruwan ta shafa sabulu batason soso dama gamawa

11 / 51