BACCIN SO BY M SHAKUR

Author :  Category :  Romance

Chapter   30 / 51

87K to 90K   out of 150.2K words

sahu da alamun gudu, gently yadaga kafansa yayi one step closer to kofar gidan, kirjinsa na bugawa yanajin wani kotsawa na ganinta kaman yayi shekara bai gantaba, just 3weeks zuwa 4weeks dinnan dabai gantaba but it feels like forever, daidai Amirah ta bullo daga zauren, wani kamshi da tunda yake arayuwansa baitabajin kalan kamshi dayamai dadi haka ba, kafin ita Amirah ma ta iso yay maza yataho dab gaban kofan cus yasan fitowa zatayi ahaka ba hula, ba takalmi, ya tsaya chak yazuba hannu a aljihun wandonsa yana kallonta, kirjin Amirah wani kara bugawa yake dum, dum, dum, ganinsa tsaye yazuba mata idanu cikin wani farin glasses din nasa, tanajin kamshin turarensa datai kewa kawai saitaji kaman ma bata gudu ayanda takeso tayi dan she feels like the little distance dayarage from inda take takai inda yake feels like forever, kara gudu tayi Marwan yawani lumshe idanu yabude su asanyaye yana sauke ijiyan zuciya bakinsa naso ya furta becareful karta fadi amman yakasa zuwa gabansa Amirah tayi saitaci birki tana kallonsa kirjinta na bugawa tana wani kalan numfashi irin na wayanda sukai game na racing dinnan, takai hannunta tasa abaki ahankali tana tsoro karya sake hanata rungumesa yanda yayi a hospital amman kawai sai jikinta yahau rawa, tana feeling wani mugun urge na hugging nasa, jikinta yayi wani karkarwa, kawai runtse idanunta tayi taciro hannunta daga baki batai wata wata ba kawai tai wani kalan hugging nasa tana daga feets nata sama sabida takai tsayin wuyansa dan Marwan nada tsayi bata wani kai ba amman saita kankamesa ta kwantar da kanta akirjinsa ahankali takai hannayenta duka biyun bayansa ta kulle ta kankamesa tana"

kara kankamesa kaman zata fasa jikinsa tashige ciki tana sauke ijiyan zuciya fast fast na gudu.

"Wani kalan bugawa kirjin Marwan keyi kaman zai fito, no one has ever hugged him like this irin real"

"intentional hug dake nuna mutum yayi kewanka, ga kamshin datakeyi gabaki dayanta da wanda gashinta keyi shima yana fizgansa, gashi shifa yana tsaye ne gaban kofan zauren yana daga waje ita tana daga ciki ga jama a and anyone daga gida ayanda ake kiranta dinnan zai iya biyota aka gansu ahaka fa, da kyar ya"

tattaro duka karfinsa dawani kalan murya da yaune rana na farko da ita kanta Amirah kejin muryan yace

" cikani! Juya kanta Amirah tayi a kirjinsa alamun no, ta daga takai hannunta tadaura saman kan inda nipples dinsa cikin that baby voice yar karama tace  ciwonka ya warke? "

Ya Rabbil Alameen wani abu Marwan yaji tundaga kafansa zuwa kansa baisan sanda ya gyara muryansa

"zuwa very strict ba yace  fitan mini daga jiki! Ahankali Amirah tafito daga jikinsa dan idan yamata tsawa ko ya maida muryansa so strick tsoronsa da shakkan sa take saitakai hannayenta biyu tasa abaki tasauke kanta kasa tadan turo baki, tundaga kan kafafunta dasuka sha kunshi ja da baki zuwa hannunta dake baki dasuka sha lalle yabi da kallo, yakalli kitson da akamata yaji wani abu a wuyansa, da haka zata fito har waje agama ganeta, strictly yace  ina hulanki? Hannunta tadaga takai saman kanta tai wani kwaba kwaba da baki kaman zatai kuka, ashagwaba tace  zafi yakemin, Amirah tayi kuka da ana mata kitso lumshe idanu da sauri Marwan yayi saiya dauke kai cus Amirah na neman halakasa, murya ciki ciki yace  go back inside kallonsa tayi shirin fashewmai da kuka take strictly yace  kikamin kuka ranki zai baci anan turomai baki tayi tajuya ahankali tawuce yabi bayanta da kallo dake juyawa zuwa kitson da aka mata dasuka zubo sosai, sai alokacin Mustapa yafito anatse yace  ance ka shigo gyadama Mustapa kai Marwan yayi saiya fara tafiya ya shigao gidan, ko ina looks extremely neat, har falo Mustapa yakaisa"

falon na kamshin turaren wuta Marwan yazauna.

Amirah dake dakinsu Ammi na mata fada tana yafa mata mayafi cikin yar karaman muryan nan tace

" Ammi ni zan tafi wajen Ya Marwan cikeda fada Ammi tace  zan makeki fa Amirah wannan wani kalan abune Miemie dake tsaye tace  ke baki iya jan ajiba ? Strictly Ammi tace  zauna anan da Miemie bari naje muka gama magana sai kije juyawa Amirah tayi da gudu saita wani fada jikin Miemie ta kifa kanta akirjin Miemie tawani fashe da kuka mai bala in ciwo, gani take Ammi nahana ta ganin Dr Marwan dinta, turus Ammi tayi ta tsaya tana kallon ikon Allah ganin kalan rigiman da Amirah keyi akan Marwan, Ammi kawai tajuya aranta tana zakici kankyanki nan gaba saikin dinga neman inda zaki gudu kije, anutse tai sallama tareda daga labule ta shiga dakin da Marwan ke ciki ganin Ammi ce tashigo dagudu Marwan yawani zame daga kujeran yazauna akasa, kansa akasa, murya chan kasa ya amsa sallaman Ammi, wucewa Ammi tayi tasami waje kan kujera ta zauna, cikeda Kamala tace  tashi ka zauna Marwan girgizama Ammi kai yayi alamun a a kansa akasa still murya chan kasa yace  ina yini Ammi wani irin kunyan Ammi yakeji da bazai iya hada idanu da itaba, he feels he wronged Ammi with abinda yayi, anatse Ammi tace  lafiya kalau ya wajen su Umman ka ? Kansa akasa still yace  suna lafiya sunce agaidaku Ammi tace  madallah muna amsawa daganan bata kara magana ba dakin kowa yayi shiru, sunkai wajen good two minutes ahaka sai Ammi ta mike tace  bari naje tai wajen kofa daidai tamika hannu tadaga labulen zata fice asanyaye Marwan yace  I am sorry Ammi yadanyi shiru kansa akasa sai chan yace  dan Allah kiyakuri juyo da kanta Ammi tayi ta kallesa yanda kansa ke kasa, calmly tace  bakomi, komi yariga yawuce, Allah ya albarkaci auren ku Ammi na maganan tawuce tafita tashiga dakinsu taga daga Lami har Miemie lallashin Amirah dake kuka ba wasa suke, har wani ijiyan zuciyan kuka take saukewa, Ammi tamata wani mugun kallo tace  tashi to kitaf& .. bata karasa maganan ba Amirah harta mike dagudu tayi kofa duk suka bita da kallo mayafin ma bata saka ba tadaga labule kawai"

tafice daga dakin abinta.

EPISODE

"Lami ta kwashe da dariya tana kallon Ammi datai turus kawai tabi Amirah da kallon mamaki, Miemie na"

"murmushi kasa kasa, Lami tace  yaran zamani ba kunya ko kadan, daga gobe ne ai mun kaita gidansa"

muhata da wannan darun datake mana Ammi batace komiba kawai tasami waje ta zauna tadauki charbi abinta tanaja.

Marwan na zaune a inda Ammi tabarsa Miemie tashigo dasauri ba kallabi still fuskanta kaman ta wanke

"da ruwa sabida kuka, Marwan yadago kansa ahankali ya tsareta da mayun idanunsa kirjinsa nawani kalan bugawa, tana tsaye gefen kofa batare data karaso wajen ba, she wants to hug him but tasan yahanata saisa batazo ba tawani turo baki ta lankwashe wuya ashagwabe kaman baby tana kuka still, Marwan ya tsareta da idanu ko kyaftawa bayayi, daga inda yake zaune yanajin kamshin datakeyi dake fizgansa sosai, bakinsa yabude ahankali yace  come kaman jira Amirah take dawani irin sauri tazo gabansa kirjinta na bugawa taduka zata zauna agabansa idanun Marwan suka sauka kan gaban boobs nata sabida riganta ya zazzago bawai yagansu full bane but yaga saman dasuke nan acike tammmm farare tasss, ya lumshe idanunsa dasauri, he s feeling kaman ya tsaga kirjinsa yasata aciki yahuta kawai, zama Amirah tayi agabansa dab dashi tana kara turo baki hawaye na zubowa bude idanunsa Marwan yayi ya tsareta da idanu kaman yanda take kallonsa asanyaye itama da idanunta dake kyalli na tears, cikin yar karaman murya yace  yaushe kika dawo rigimammiya ? Makemai kafada tayi another new hawaye na zubowa, duk yanda Marwan yaso yadaure yakasa hannunsa yakai ahankali yadaura saman fuskanta, wani sanyi Amirah taji da tafiyan abubuwa a cikinta da batasan sanda tawani sauke ijiyan zuciya ba da saida iskan yasauka akan fuskansa, yatsan hannunsa yakai ya sharce hawaye kaman yana magana da baby yace  why are you crying Little Meenah? Wani yammmm Amirah taji sabida yanda yakirata da batasan sanda takai hannunta takama hannunsa dake kan fuskanta ba tarike tana sauke ajiyan zuciya da sauri da sauri, wani irin abu takeji game da Marwan that s unexplainable but she knows kaman ta cinyesa, kota hadiyesa, kota koma jikinsa gabaki daya takeji, wani yarrrr Marwan yaji jin yanda Amirah takama hannu sa tarike hannunta bala in taushi gashi duk yayi zufa lallen da aka mata ya rabbi hannunta kaman ba hannun mutum ba tsabagen kyau, kawo fuskansa dab da nata yayi yana kallon"

kwayan idanunta dake kyalli sosai yace  rigiman me kikeyi ahankali like a little baby ke magana tace

 Ammiiiiiiiii murmushi kadan Marwan yayi Amirah tawani tsaresa da idanu ya rabbi murmushi yamai

"kyau sosai tana kallon glasses na idanunsa, shikuma yasauke idanunsa kan kitson da aka mata baisan sunan style dinba but baitaba ganin kitso mai kyau in his life like this one ba, tunda yake arayuwansa baitaba ganin kitso dayamai kyau like this ba sauke hanunsa yayi daga fuskanta ya ijiye kan fatan wuyanta, wani irin ijiyan zuciya Amirah tayi dan she felt cold har a bargon kashin dake jikinta, tsayawa yayi yanaso yacire hannun nasa daga wuyanta but yakasa, her neck is so soft, is so warm and very smooth, gently yashiga shafa wuyanta da hannunsa tsigan jikin Amirah yawani tashi dahar saida yagani yakai hannunsa yakamo gashinta dasuka azube so silky gashin bakin kirin tana wani kamshi, ahankali yakalli kwayan idanunta kaman yanda take kallonsa yace  kitson nan yayi kyau wani irin dadi Amirah taji kawai bazato tashige jikinsa tai hugging nasa tana manna fuskanta a kirjinsa, tanason kamshin dayake sosai bana wasaba, bugawa kirjinsa keyi nonstop kallon kofan dakin yayi da labulene kawai he will feel wani iri idan wani yazo yagansu ahaka, murya chan kasa Marwan yace  bana hanaki ba dago kanta tayi daga kirjinsa jikinta duk yamata wani iri, hannunsa yakai yadanja hancinta yace  ke mage ce? "

"Washemai Baki yayi saiya dagata daga jikinsa, mikewa yayi dasauri Amirah tamike itama tana shirin kuka,"

"saiya ciro kudade daga aljihunsa dayawa ya ijiye akan kujera yace  jeki cema Ammi zan tafi hannunta tasa abaki saita wuce tafara tafiya ahankali tafita, ijiyan zuciya Marwan yasauke saiya fito daga dakin"

EPISODE

Daga bakin kofan dakinsu Amirah ta tsaya tace  Ammi tajuyo tana kallon Marwan daya fito daga dakin

"idanunta yaciko da hawaye dan bataso yatafi, Miemie tafara fitowa akunyace tace  Ya Marwan ina yini ? Anatse Marwan yace  how are you Maryam ? He talks to her like an elder brother, ahankali tace  lafiya lau Lami tafito tareda Ammi, Marwan yasauke kansa kasa dasauri yace  saida safe Ammi Ammi tace  agida mutan gida gyadama Ammi kai yayi yay hanyar zaure zai fice, kawai Amirah tawani rushe da"

"kuka tana tsaye daga wajen kofan dakinsu datake tana kallonsa, chak Marwan ya tsaya batare daya juyoba, Ammi tadan kallesa sai kawai tawuce takoma ciki, Lami da Miemie suka bita suma cikin dakin, dan juyowa Marwan yayi suka hada idanu da Amirah dake kuka sosai, da idanu yamata alamun tazo, dasauri ta taho wajensa ta tsaya dab dashi tana kuka harda shesheka, ahankali murya chan kasa Marwan yace  why are you crying? da yar muryan nan nata dake fita da kyar cikin kuka yar karaman gaske sounding like a baby tace  zan bikaaaa hannunsa yakai yadaura kan fuskanta ya sharce hawayen ganin hawayenta kaman river basu da wahalan zubowa kuma nan da nan sun wanke mata fuska tass, murya kasa kasa ta yanda babu wanda zaijisu yace  we will be together tomorrow okay, stop crying, daga gobe i will never leave your side, I have to go yanzu kinji yayi maganan ataushashe da sigan lallashi, gyadamai kai tayi tana sauke ijiyan zuciya ahankali na kuka tana kallonsa, Marwan yayi shiru yana kallonta zuciyansa nabugawa sabida yanda yakejin sonta, kaman gobe tayi yanzu yatafi da ita kawai, ahankali ya"

kawo bakinsa wajen goshinta sai gently ya manna soft lips nasa kan goshinta ya sakin mata wata yar

"karaman light kiss wani yirrrrrrr Amirah taji da saida shi kansa yagani, dan komawa baya yayi anatse yace"

 go to your room now gyadamai kai tayi saita juya ahankali tana tafiya tana juyowa tana kallonsa shima yana tsaye bai wuceba har saida takai dakinsu tashiga sannan yajuya yafice yashiga mota yaja yabar

anguwan.

Komawa dakin Amirah tayi tana kuka ahankali Ammi ko kallonta batayiba ahankali tazo inda Ammi take

"tazauna, still Ammi bata kalleta bata kalleta ba, gently ta kwanto jikin Ammi, Ammi ta kalleta dasauri Amirah ta runtse idanunta bataso Ammi tamata fada takara kankame Ammi tai lamooo, ahaka bacci yayi awon gaba da ita Ammi sai kallon yaran take dan itama Miemie tayi bacci, she feels kaman kar gobe tayi"

tarabu dasu.

Ahankali Ammi ta kwantar da ita agadon tamike tafito alwala tadauro kawai tadawo daki ta shimfida

"dadduma tafara salla wanda yaranta kawai takema addu a Allah ya albarkaci aurensu, yabasu zaman lpy da mazajensu, Allah yaba Amirah lafiya completely har saida aka kira sallan asuba sannan ta tashi ta tada"

Miemie da Amira dan ayi salla Lami ma ta tashi makota har an fara shigowa daura abincin biki.

"Gabaki dayan rannan shima Marwan bai runtsa ba yakosa gobe tayi akawomai matarsa, yayinsa kowa na"

"gidan anyi lalle da sauransu, har lokacin no one knows whereabouts na Saleem."

Daga masallacin sallan asuba Marwan yafice abinsa dan baiso ma agansa atasahi gaba.

**

Wuraren 11 aka gama yima amare makeup wanda da kyar Amirah ta yarda dan she was feeling

"uncomfortable, makeup is something da bata taba yiba, Ya Rabbi ita karan kanta Ammi saida takara kallon Amirah cus yaune rana na farko datake ganin Amirah tazaman mata yar budurwa a ido dan she always sees Amirahnta as a baby, Amirah tayi kyau cikin black and gold lace data saka ana gama makeup din tazo wajen Ammi adaki ta zauna taboye abayan Ammi, batason yanda mutane keta kallonta da"

yanda taga mutane dayawa agidan acike ana hayaniya dudda babu kida ko DJ but she doesn t like it.

"Kallonta Ammi tayi tace  tashi muje ahankali ta tashi Ammi tariketa, saita kaita dakin Baffa wanda babu"

"kowa ciki tazuba mata abinci karba tayi tafara ci ahankali, Ammi na kallonta taci sosai sannan ta kalli Ammi tace  Ammi anjima zamu tafi gidan Ya Marwan? Gydamata kai Ammi tayi, murmushi tayi"

"tacigaba da cin abincin sosai taci tana gamawa sai bacci, gyaramata kwanciya Ammi tayi tafito daga"

"dakin tana kallon Miemie dake tareda kawayenta Miemie tayi kyau sosai, tadade tana bacci sai bayan asir ta farka Miemie tagani kusada ita tana kuka tana goge hawaye tashi Amirah tayi zaune ta tsareta da idanu saita matso ahankali tazo kusada ita murya chan kasa like a baby tace  menene? Cikin kuka Miemie tace  Amirah banson narabu da Ammi dake, banso saita rungume Amirah tana kukan wani iri Amirah tashigaji sai hawaye yashiga cikowa a idanunta, ahankali tadago Miemie saitakai hannunta kan fuskanta ta girgiza mata kai alamun tadena kuka, Miemie tadade tana kallon Amirah saita gyadamata kai, daidai Ammi tabude dakin tashigo takalli Miemie da idanunta sukai jajir anatse tace  kuzo ku shirya anzo tafiya daku daidai nan Lami na shigowa dakin tace  ina suke muje muje ga motoci sunyi layi a waje ana magrib zaku wuce, muje muje tai wajen Miemie tadagata suka fice, Ammi takalli Amirah tace  zomuje tasowa Amirah tayi saitazo dab da Ammi tana kallon fuskan Ammi sosai cikin yar karaman muryan nan tace  Ammi ai tare zamuje gidan Yaya Marwan ko ? Tsareta da idanu Ammi tayi saita gyadamata kai kawai, murmushi Amirah tayi ta rungume Ammi suka fito tare tana mammannewa jikin Ammi tana boye fuskanta wanka Ammi takaita tayi dawani ruwan turare sannan tafito da ita sukaje daki Ammi da kanta tashiga shiryata cikin wani lafaya black and red tasata tai salla Ammi bata mata wani kwalliya ba tasa mata kwalli saita zauna gaban Amirah tana kallonta hawaye Ammi taji zasu zubo daga idanunta dasauri tadauke kai dakin aka bude dasauri Amirah ta tashi taboye bayan Ammi tai lamo kaman yar yarinya,"

"Lami dasauran manyan matan wajen suka shigo da Miemie dake kuka sosai an lullubeta sukace  ammm Ammi ga Miemie za a tafi da ita tsareta da idanu Ammi tayi saita lumshe idanu bata taba sanin this is how a mother feels when she s saying goodbye to her children ba sai yau, she s feeling kaman ta taya Miemie suyita kuka tare sabida yanda takeji amman saita dake anatse tace  Maryama I know daidai gwargwado nabaki tarbiya mai kyau, ke yarinya ce mai hankali da bazaki taba bani kunya ba, baki taba kuntata min ko batamin raiba, I pray Allah yabaki farin ciki irin wanda baki taba tunanin zaki samu ba gidan mijinki Allah ya albarkaci aurenku, go start your new life kinji My Babygirl Miemie rungume Ammi Maryam tayi tama kasa magana sai kuka da kyar tace  Ammi banso narabu dake dariya akahau yi adakin itama Ammi tai murmushi tace  ai duk diya mace saita rabu da iyayenta mumanan duk hakane maza dena kukan nan Ammi ta dagota, bakin mayafinta Ammi takama ta share mata fuskan tasss saita manna mata kiss a goshi tace  go to your home Maryam wasu sababbin hawaye ne suka shiga zubo"

mata.

EPISODE

Lami tace  muje toh ahankali Miemie ta tashi saita zagayo bayan Ammi tai takalli Amirah dataga

"idanunta sun ciko da hawaye duk tayi wani irin kaman tasoma gane abin is getting real, ahankali Miemie"

"tace  kin haddace number na dana Ya Umar ko? Gyadamata kai Amirah tayi ahankali, Miemie tace  toki kirani idan kika sami waya kinji bazan iya rayuwa babu ke ba Ya Amirah, you re my best Sister kuma in"

sha Allah zaki warke Ya Marwan zai kula dake kinji gyadamata kai Amirah tayi tana kallon yanda Miemie

"ke kuka

30 / 51