Author : Billyn Abdul Category : Adventure
cike da dattako da godiya ma juna. Nasiru da Abdul-rasheed suka rakasu tasha suka wuce. Dan sunce bazasu kwana a Kano ba. Abinka kuma da duniya na kwance ba'a tsoron komai..
Akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI. Karatun Abdul-rasheed nata miƙawa, an kuma sake kawo kuɗi na biyu gidan su A'isha, tare da kayan sa rana. Huhun goro, farar alewa, sai cakuleti, sai cingam bazuka, sai alewa daima. Sai kuma tabarma karauni guda biyar, sai katifa da botikin ƙarfe da butar ƙarfe, sai zanin gado da barguna guda huɗu rigis abinsu. Kayan sarana dai sambarka dan duk wanda ya gani yasan dangin Abdul-rasheed sunyi ƙoƙari. Dan haka aka saka ranar aure watanni huɗu.
____________
Bayan wucewar baƙi dangin Abdul-rasheed iyayen A'isha ɓangaren dangin uwa dana uba suka baje kayan sa rana aka raba. Aka bama Inna nata da danginta, dangin mahaifinta suka ɗauki nasu. Sosai A'isha take a cikin farin ciki, sai dai wani ɓangare kuma jikinta duk yayi sanyi. Ko lokacin da ƙanwar Inna da suke kira Inna Haule tai kiranta akan ta faɗi suwa zata zaɓa matsayin ƙawaye da baranya akai musu kayan saka ranar kasa magana tayi, daga ƙarshe akace taje abinta ta sanar ma da Bashir ko Tasi'u su suzo su faɗa. Haka kuwa akayi, ta gayama Tasi'u ƙawayenta biyu da take son ɗauka matsayin babbar ƙawa Lantana da Jummai, sai baranya kuma, dan haka aka ƙulla kayan sa rana aka kai gidajen iyayensu kamar yanda ake ta rabo gidan sauran dangi da abokai da makwafta.
A kwana a tashi ba wuya wajen UBANGIJI, kwanakin aurensa da A'isha nata gabatowa. Domin kuwa sai anyi bikinsu da watanni bakwai ma zai kammala karatunsa. Gabatowar abubuwa dole ya shirya yaje gida Bauchi. Dan ya samu saƙon wasiƙa daga drivern da ake yo masa aiken kayan abinci. Baba ne kuma ya rubuto ta da Ajami.
ٱلسَّلَامُ عَلَيْكُمْ
إِنَا فَاتَن كَانَا فِي قُشِي لَافِيَّا عَبْدُ الرَّشِيدْ. يَا كَرَاتُنْكُو يَا جَمَاعَار دَا كَكَيْ تَرَّة سُو. تَوْ دَنْ ٱللَّهْ دُكْ أَغَايْدَا مِنْ دَا كُوَا.
إِنْ بَا زَنْ تَابَا مَاكَا كَرَاتُو بَا كَيْي قُوكَارِي أَ سَاتِينْ سَمَا كَازُو غِيدَا كُونَا كْوَنَا بِي يَنْ سَا كَا كُوْمَا. دَنْ إِنَا سُون مُي يِ مَاجَنْغَا، كَاغَا كُوْمَا نِي بَا إِي يَا زُو كَانُونْ نَنْ تَاكُو زَنْ بَا إِنَا فَمَا دَا شِكَرُونَا.
نَا بَرْكَا لَافِيَّا.
دَاغَا مَهَافِفِنْكُو. شَيْخُ إِيسَا كُوبِي بَوَتْشِي.
Assalamu alaikum.
Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya Abdul-rasheed. Ya karatunka ya jama'ar da kake tare da su. To dan ALLAH duk a gaida min da kowa.
Idan ba zan taɓa maka karatu ba kayi ƙoƙari a satin sama kazo gida kona kwana biyu ne sai ka koma. Dan ina son muyi magana, kaga kuma ni ba iya zuwa Kanon nan taku zan ba ina fama da shekaruna.
Na barka lafiya.
Daga Mahaifinka. Shehu Isa Kobi Bauchi.
Abdul-rasheed na gama karanta wannan wasiƙa baiyi ƙasa a gwiwa ba sati na zagayowa yayima garinsa na Baushi tsinke tare da asusunsa daya jima yana tarin kuɗin ɗinki a ciki. Sosai kuwa Baba ya nuna jin daɗinsa da zuwan nan. Dan a matse yake da son ganinsa. Bayan ya huta sun taɓa hira da Inna da ƙannensa ya fita gidajen yayunsa duk suka gaisa da matansu da su suma. Daga nan ya leƙa abokansa, sai bayan sallar isha'i ya dawo kasancewar yasan zuwa lokacin Baba ya shigo gida cin abinci. Hakan kuwa akayi, ya sameshi zaune a ƙofar ɗakinsa kan tabarmar karauni yana cin abincinsa a akushinsa. Sannu yay masa ya nema waje ya zauna, bai ƙara magana ba har sai da Baba ya kammala ya fuskanceshi dan kansa. Sun tattauna sosai akan batun bikinsa dake tunkarowa nan da wata ɗaya, sai batun gida da aka gina masa kamar sauran ƴan uwansa anan jikin gidansu, gini ne dai irin na wannan zamanin, wato ginin laka (ƙasa) kamar yanda aka sani ga talaka, an shafeshi da farar ƙasa ƴar aliya daga cikin ɗakunan, a waje an yarfa abin gwanin ƙyau. Abdul-rasheed yayi godiya sosai ga mahaifinsa harda hawaye, yay masa addu'ar tsahon rai da lafiya mai ɗorewa. Bayan ya lafa Baba ya ɗora masa da batun kayan lefe da dangin mahaifiyarsu suka kawo daga Maiduguri. Akwatin ƙarfe ne da irin na mutan da guda ɗaya ƙaton gaske, akwai kaya a ciki wato atamfofi irin na mutanen da sai takalma da kayan shafa kamar dai yanda ake haɗa lefe a wancan zamani. Baba ya sake da nuna masa kwalla guda biyu daga wajensa shima kuma kayan lefen ne dai a ciki, kamar yanda yayma sauran ƴan uwansa shima yayi masa tunda na dangin mahaifiyarsa daban nashi daban matsayin uba. Rasama tacewa Abdul-rasheed yayi sai hawaye kawai yake sharewa da godiya. Daga ƙarshe ya ɗakko asusun nan gaba ɗaya ya dire a gaban Baba.
Baba ya ɗan zubama asusu ido sannan ya kalli Abdul-rasheed a nutse. “Wannan asusun fa Abdul-rasheed?”.
“Baba kuɗaɗen da nake tarawa ne na ɗinki a ciki daman”.
“Masha ALLAH, ALLAH yayi maka albarka, amma ai naka ne, miyyasa zaka kawo min nan?”.
“Baba naka ne, kai amfani da shi domin rage nauyin abubuwa sun maka yawa. Nasan dai bazasuyi maka komai ba, amma dai za'a rage wani abu”.
Murmushi Baba yayi a karo na farko, ya sake saka masa albarka sannan ya ɗauki asusun ya miƙa mishi. “Abdul-rasheed bazanƙi amsar ƙyauta daga hannunku ba. Domin hakan ba nufin jinƙai da neman albarka. Kuma hakan da kai min ya sakani jin daɗi ƙwarai da gaske. ALLAH yayi maka albarka da sauran ƴan uwanka duka. Amma kaje da asusun nan ka cigaba da tara abinda kake samu, bayan ka kammala karatunka ka dawo gida akwai abinda zamuyi da kuɗin ni da kai. Dan haka ka cigaba da ajiye min su a hannunka kaji”.
Batare da Abdul-rasheed yay tunanin komai ba ya ce, “To Baba. In sha ALLAHU yanda kace haka za'ayi”. Daga haka suka cigaba da hira har lokacin barci..
>>>>>>>•<<<<<<<
Kwanakin Abdul-rasheed biyu ya dawo Kano makaranta, bai shiga anguwar su A'isha ba sai da sati ya zagayo kamar yanda ya saba. Sai dai suna tare da Nasiru a makaranta kullum. Shi ya bama tsaraba ma da ƙanwarsa ta bada a kawoma A'isha ya kai mata shi kuma sai ƙarshen sati ya shiga suka gaisa..
Rayuwa ta cigaba da tafiya bikin Abdul-rasheed da A'isha nata ƙara matsowa, ana shirye-shirye shi kuma hankalinsa nakan jarabawar da suka fara, wadda bai kammalata ba kuwa sai ana saura kwana huɗu ɗaurin aure. Zuwa lokacin gidan su A'isha ya gama cika da danginsu na nesa, har ma am sakata a lalle a safiyar yau ko muce da hantsi, wato an saka mata turare irin na al'ada matsayin kamu. Wannan yasa shima Abdul-rasheed bai ganta ba, dan a wannan zamani idan aka saka amarya a lalle keda ango kuma sai a ɗakin aurenku. Sam Abdul-rasheed bai so haka ba, dan tunda ya fara jarabawar nan basa wani samun zama da A'isha, zai iya cewa rabonsa da ita ma tun mako uku da suka wuce randa sukai hira harda Nasiru suka bata kuɗin ƙarshen zance da ake bama budurwa sule na gugar sule har sule biyar cif. To gashi kuma yau da yake son ganinta bamai yiwuwa bane, dole ya haƙura ya kama hanyar Bauchi tare da Nasiru ɗan amanarsa. Sai ana gobe ɗaurin aure zasu dawo Kano su sake komawa tare da amarya.
Koda su Abdul-rasheed suka isa Bauchi a can ma sai ya tadda gidansu taf da dangin mahaifiyarsa dana Baba, kai har ma da dangin Inna duk da ta kasance kishiyar uwa. Tuni an baje buhu-buhu na masara dana gero anata faman daka domin samar da garin tuwo harma dana MASA ƳAR BAUCHI, sai fura dama sauran nau'in abinci irin na wannan ƙarni da su shinkafa. Sun sami tarba ta farin ciki, inda abokan wasa dake dakon isowar ango dama suka lulluɓeshi aka fara zazzage masa kwalaben turare masu ƙamshi irin su ɗan duwala ana guɗa, hakan kuwa na nufin shima an saka shi a lalle kamar amarya.
*_KANO_*
A nan Kano ma dai ɓangaren amarya bari muɗan dawo baya kaɗan miji a yanda aka sakata a lalle da yanda suke shagalinsu da ƙawayenta. Zamuce amarya da ƙawayenta sun fara shagali tun a ranar data kasance saura kwanaki bakwai ɗaurin aure. Amma an sakata a lalle ana saura kwana uku. Ranar litinin Inna Zainabu ta bata umarnin tsefe kanta kamar yanda yake a al'ada, da taimakon ƙawarta Jummala ta samu ta tsefe shi. Daga haka suka cigaba da sabgarsu. Washe garin ranar laraba da mutanen Bauchi suka iso da lefen A'ishatu a washe garin randa su Abdul-rasheed suka tafi kenan, akwatin ƙarfe da kwalla biyu sai tabarmi karauni guda huɗu. Gidan ya cika sosai da maƙwafta, bayan an cika baƙi da shatara ta arziƙi na abinci, anyi gaisuwa irin ta mutunta juna, dama gidan su Nasiru suka sauka, dan haka suna kammala bada lefe suka koma can abinsu, kasancewar nisa dama su huɗu ne kawai suka kawo kayan, zasu zauna kuma har a ɗaura aure sannan. Masha ALLAHU kaya sai sambarka. Dan kuwa dai amarya tayi goshi. Atamfofi ne nagartattu irinsu mai tabarma, mai barewa, akwai oni-ƴasu, sai joji da ƴalle gwaggwaro, sai t-shirt masu ƙyau, sai sufa gwaldin, sufa shadda, akori-kura, kai kaya dai sai sambarka. Kayan kwalliya da sabulai suma dai tsaf, sai turaren alwalar uwar ɗiya ƙatuwar kwalba sosai, sai ƴarduwala, miski da sauran irin yan feshi. Sai kuma gyale da su takalma kaya dai rigijib-jib komai ka taɓa akwai irin na wannan zamanin..........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 10_
__________________
*_NACE ina kuke ne?!!. Al'ummar Gombawa nake magana 💃 fulanin asali ke nan 😘._*
*Shin kuna da labarin cewa kuma nesa ta matso kusa gare ku?*
_Maza kuzo ku sha labari da ɗumi-ɗuminsa, domin kuma fa NAKUN ya buɗe muku gidan gyara da ƙalƙale jikin mata ƴan kwalisa a kusa da ku gabb._
*_Idan kunji ana kiran maida tsohuwa yarinya to wannan katafaren shagon ne na👇_*
*ALIYU HAIDAR COSMETICS PLAZA*
_ADDRESS SHOP D80 WOMAN LINE GOMBE MAIN MARKET_
*_Zaku same mu a wannan numbers ɗin kamar haka👇_*
*07068210505*
*09133081313*
_DEALER IN all kind of skin care products such as:_
moisturizer
Sun screen
Face Toner
Eye cream
Face serum
Face wash
Face scrub
Face cream
Face marsk
Body lotion
Body cream
Shower gel
Body scrub
Tube
Body oil
Body spray
Perfume
Hair crm
Hair spray and many more
*_Harma da abinda bamu lissafo ba anan. Ku dai kawai karku bari a yi babu ku. Domin kayanmu garanti ne kuma dahir ne 💃_*
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/HCLn6awOrmP5WJmO9jPrgK?mode=ems_wa_t
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
........Bayan ƴan ganin lefe sun kammala kowa ya wuce an adana kaya ma sannan A'isha ta dawo daga maɓoyarta. Ganin yanda aka ɓata gidan ta ɗauka tsintsiya ta hau shara kamar yanda ta saba, tana tsaka da sharar tsakar gida duk da baƙi sun fara cika gidan nasu ƴan biki matar yayansu ɗan ƙanin babansu ta shigo gidan. Cike da shammata ta shiga zazzage mata turare a jiki tana guɗa.
Wani irin sakin tsitsiyar A'isha tayi a ƙasa, sai kuma ta fashe da kuka tana mai durƙaushewa a wajen. Kuka take sosai mai ban tausayi, har sai da akazo aka ɗagata a wajen. Abokan wasa kuwa sun samu nayi, sai binta suke da guɗa. An cire mata ƴan kunnenta da tsakiyarta ta wuya (Abin wuya, kamar sarƙa dai a yanzu). Hakama kayan jikinta ta cire an kawo mata tsohon zani da riga ta saka. Wannan alama itace amarya ta shiga lalle kenan, dan kuwa zuwa bayan sallar magriba wadda take matsayin Alwanka ɗinta tazo gidan, ƙawayenta dama tunda akai kamun sun cika gida abinsu domin zaman lalle ya fara kenan. Bayan gaishe-gaishe aka ɗakko ma alwanka tabarmin tirgeza guda uku ta kwashi amarya da ƙawayenta suka tafi gidanta. Da yake itama anan anguwar take da ƙafa suka taka abinsu. An zauna an ɗan taɓa hira kowa ya nema makwancinsa, makwancin kuwa wannan tabarmi ne da alwanka ta amso na turgeza (😂mutane na miye Turgeza? A amsa a comment akwai ƙyauta🤣, sannan miye Alwanka ma? Tambaya biyu kenan😂🙏). Biyu ƙawayenta suka kwanta, ɗaya aka bata ita kaɗai. Washe gari da safe aka dama musu koko aka sayo ƙosai aka basu sukai kari da shi. Daga haka suka koma ƙarƙashin bishiyar ceɗiya dake gidan suka zauna suna hirarsu, sai dai amarya daka ganta duk tayi sukuku, lokaci-lokaci ma takan share hawaye abinta.
A ɓangaren Alwanka kuwa ta tanadi lallenta na ƙunshi har kwano ɗaya da rabi ta kwaɓa tunda safe na TURGEZA kenan, zuwa goma ta bama ƙawayen amarya lalle da zunguru sai ledoji su ƙunsa mata. Tsaf ƙawayen amarya suka ƙunsheta kuwa da ƙunshi na tsohuwa ta faɗa kwata (🤣ina fatan kun san ƙunshin dai?), hakama a hannunta sannan aka saka mata zunguru a ciki (Miye zunguru?😂 Wanda ya faɗa akwai ƙyauta shima🤣🙏).
Bayan an gama sakama amarya lalle ƙawayen amarya suka fice zuwa gidan su Nasiru, dan kuwa ance duk abinda ake badawa na gidan anguna suje can su amsa. Bayan gaida Innar su Nasiru da baƙin Bauchi da suka samu a gidan aka danƙa musu shinkafa da manyan zakaru har huɗu, sai kayan miya da kayan magi da iccen girki da man gyaɗa, sai kuɗi wannan sune kayan kamu. Koda suka dawo gidan alwanka ɗanta Ibro ne ya yanka musu kajin, su kuma suka shiga hidimar girki amma dai Alwanka na duba musu da nuna musu yanda duk ya dace ace sunyi. Amarya kuwa na zaune da ƙunshinta har lokacin abinta. Zuwa azahar aka kammala abinci, shinkafa da miya da naman kaji zuɗu-zuɗu, mai kuwa. A ƙyallan har kana iya ganin fuskarka a ciki fes. Umarnin cire ƙunshi Alwanka ta bama amarya, dan haka ƙawayenta suka fara taimaka mata tai zaman cirewa kamar abin arziƙi, gefe kuwa manyan ƙawayen amarya sun shimfiɗa tabarma a tsakar gida, wanda suka taimaka mata ta cire ƙunshi suna gamawa ta miƙe da nufin barin wajen kawai taji an rufu a kanta, cak suka ɗagata sai kan tabarmar nan da aka shimfiɗa. A take ta birkice musu ta shiga bibbigesu da son ƙwace kanta, amma ina sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, tuni suka danneta a wajen, dama gashi daga ita sai zani ɗaurin ƙirji, dan sanda za'a saka ƙunshi sakata akai ta cire rigar. Tsaf ƙawayen amarya suka cire zanin nan kuwa daga jikinta aka barta zir sai ɗan kamfai (😂wato mutanen da anyi shagali da ɗanyen aiki gaskiya🤣). Sauran lallan da aka saka mata ya rage da wanda aka cire matan Alwanka ta kawo musu, nan fa ƙawayen amarya suka shiga ɗiba suna saka mata a jiki ana murjeta da shi. Itako tana kai musu duka da harbinsu ƙafa da hannu tana kuka. Har cikin gashin kanta ana raira waƙa, bari na ɗan raira muku💃🤣.
Ayye yara iye TURGEZA.
Ga Turgeza yazo, Turgeza.
A wanketa da sauri, turgeza.
Lallen iya ƙamshi, turgeza.
Ayye yara amarya turgeza.
Sai da ni bilyn ku😂 (magana ta gaskiya ni na ƙirƙiro muku waƙar, amma ta gaskiyar ba haka take ba, baitin farko ne kawai na gaskiya kada kakanin mu suce na musu sharri😂🤣🤣).
Sosai amarya ta dirzu da lalle. Masha ALLAH kuma sai tayi ƙyau abinta, sai dai fa kowa ya daku gwargwadon iko cikin ƙawayenta. Itama kanta ta jigata da kuka da harbe-harben data sha. Ana sakinta taja zaninta ta ɗaura, data rarumi icce tai kan ƙawayen nan nata sai gudu Malam. Tuni fa kowa yay waje, masu neman wajen ɓuya suka nema, masu haura katanga nayi masu yin hanyar zaure nayi. Da ƙyar Alwanka ta kamata ta riƙe, sai da duk suka baje sannan ta saketa, babu batun wanka, wannan lalle na jikinta haka kuma zai cigaba da zama a jikin nata har sai gobe, gefe ta koma ta dasa sabon kuka. Babu wanda ya hanata har tayi mai isarta ta gaji dan kanta ta haƙura. Bayan komai ya lafa ƙawayen amarya suka daddawo sai kuma aka ɗakko abinci da miya aka baje kuma a tsakar gida da turirrika na rabo. Haka aka raba abincin ƙunshi da nama kowa ya samu har maƙwafta, aka baje kuma aka fara ci ana hira da wasa da dariya. Bayan sun kammala aka aiko baranya ɗakko igiyar shillo, babu jimawa ta dawo, amarya ta tashi ta saka rigarta da kallabi suka kwashi igiyar nan suka fice bayan gidan wajen wata bishiyar ɓaure ƙatuwar gaske. Anan aka ɗaura wannan igiya ta ɗauru kam sannan aka fara shillo, idan wannan ya sauka wannan ya hau, har yamma suna a wajen suna waƙe-waƙensu na ƴanmata cike da nishaɗi. Sai gab da magriba suka dawo gidan Alwanka.
Washe gari alhamis ma haka suka sha shagalinsu aka ƙara yima amarya wankan lalle kamar jiya, dan kuwa yau ma zir akai mata sai ɗan kamfai aka shafeta da lalle har cikin kanta, tasha kukanta kamar jiya har yamma. Zuwa dare bayan sallar isha'i Alwanka ta tattarasu tai musu rakkiya aka maidasu gidan su A'isha. Gida kam ya gama cika da dangi tako ina. Bayan gaisuwa Alwanka tace “Ga aro na maido, ALLAH ya sanya alkairi ya fiddamu kunyar gobe. ALLAH Kuma yasa takai mutuncinta ɗakinta.